-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

INA ZAN GANSHI Hausa Novel

INA ZAN GANSHI Hausa Novel

 💞 *INA ZAN GANSHI?*💖





Rubutawa


©Xarah Bukar




®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION {NWA}




E-book creator:  D Young 




1 - 5




Banko k'ofar d'akin da k'arfin gaske ya firgita Hajjo dake k'ok'arin had'e tabarmin dake yashe gefe guda. 




   Fuska murtuk'e ta sak'alo k'afa ciki d'akin tana gunguni.


    Cike da k'unin rai Mahaifiyarsu Hajjo ta zuba mata idanu.


"Batula baki iya Sallama ba?"


  


Haushi ne ya kuma turnuk'e ta da sunan Batula da Hajjo ta ambata, tafison akirata da Fatima Zarah ainihin sunanta.


 


"gaskia Hajjo ana shiga hakkina a matsiyacin gidan nan, saurayina yazo daga fita ta Baba ya izo k'eyata, da alamun kuma da d'an maik'on sa, oh ni Fati naga samu naga rashi" karashe maganar tayi cike da tashin hankali, hannuwan ta biyu bisa kanta.




    Tak'aici ne ya cika Hajjo, wana irin k'aramar kwak'walwa yarinyan nan keda shi, "Batula miyasa baki da hankali, talauci ba hauka bane, ki kuma iyawa bakin ki, matsiyacin gidan nan gidan uwarki da ubanki ne ba yadda kika iya"


Shuru Batula tayi zuciyar ta na tafasa, banda harara talautaccen dakin da take.


"Maza jeki rumfar babanku ki amso kayan miya kafin ya kasa na kasuwa" acewar Hajjo batare data kula da yanayin ta ba.




   Ware idonu tayi, tayi tace "nikam bazani niba, ajira dawo wan su Hassan saisu karb'o"




"Dole kije dan bazan tsaya jira harsai sun dawo makaranta zan aza abinci ba, wuce ki karbo kafin na mazge ki" Hajjo ta fadi da niyyan kai mata dundu


Gunguni tahau yi bata da alamun tafiya saida Hajjo ta hada mata tsawa mai dauke da ashariya sannan ta fice ak'ufule bayan ta tsuri mayafin ta dake lank'aye bisa taga.




    Gaban karamin gidan nasu dako fenti babu ta iske wani yaro tsaye.


"Baba mai kayan miya na nan ?




   Yaro ya tambaye ta.


Idan akuya na magana to ta tanka bangajesa tayi ta wuce abunta cike da haushin yadda Baba ke zubar mata da aji, wai itace diyar mai kayan miya, dogon tsaki taja ta k'arasa can gaba da gidansu inda runfam Baba yake, bata kai ka zuwa rumfam ba ta mak'ale daga gefe inda baba bazai hango taba, amma tuni ya ganta ya dauke kai.


 


   Lawali ta kira yaron auguwan su ta aikesa amso kayan miyan.


Sabo da halinta yasa Baba bai nuna yaganta ba, jinjina kai kadai yayi, albasa batayo halin ruwa ba. 


    leda taf ya cikawa Lawali sannan ya damk'a mai.


Hankalin ta gabadaya ya shagala da kallon wasu yara da Mamansu cikin wata arniyar jeep, sai kallonsu take ji take dama itace acikin motar da tafi ko wace ya mace morewa, sai dai kuma aka samu akasin Baba talakana ne saidai su k'are da tumatur da albasa.




    "Butula gashi" taji yaro na fadi, harara takai ma sannan ta warce ledar tayi gaba




    Hajjo na iza wuta a gindin murhu ta shigo ta dire ledar tayi cikin kusurwar daki.


Girgiza kai Hajjo tayi, tunanin barkatai ke yawan mata a kwakwalwa, inda ba a gidan ta haifi Batula ba tana iya cewa an mata musanye, amma ba daman fadin haka kamarsu daya da Baba kamar an tsaga kara.




***




   K'asak'asa suke zantawa da alamun wata muhimmaciyar magana sukeyi, nisawa Hajiya Fatima tayi tace "Safara ya kikeso nayi kinsan Rasheed wani irin murd'add'en mutum ne da baa iya tank'wara shi, tun rasuwar ubansa ya koma hawainiyar da babu kala"




   Murmushin dabai kai zuci ba Hajiya safara ta mata sannan tace "yaron nan dai d'an kine ke kika haifeshi bashi ya haifeki ba sai kisan yadda zakiyi ya amincin da kudirin mu.."




   Turo kofar tafkeken palon ne ya katse masu zance, sanye yake cikin black suit, hannunsa rike da karamin brief case, ciki ciki yayi sallama, basu amsa ba banda kallo da suke bisa da shi, maihaifiyar sa hajiya Fatima ce tayi karfin halin cewa my boy ka dawo.


"e" kawai ya amsa mata agajarce ya wuce hanyar dakinsa cike da haushin Hajiya Safara dake hakince kan babban kujerar palon, idan bai manta ba tun yana yaro yake ganinta saidai jininsu bai taba haduwa ba, ya rasa mai suke yawan zantawa tare da momyn sa akullm idan suka hadu, tsaki kawai yaja ya cusa kai ciki had'add'an dakinsa.




   Fitowa tayi daga kitchen, hannuta ruke da kwalin exotic ta karasa cikin palon cike da yauki da iyayi. "Mardiyyah mutumin ki fa ya dawo"


Acewar hajiya Safara,


"Dagaske " Mardiyya ta fadi tare da kwalalo ido tana kallon Momy dake mata murmushi, sai kuma ta kalli agogon hannuta tun 4 tabaro office amma shi sai yanxu 8 ya dawo.




   Tashi tayi da azama, zata bar palon, hajiya safara tace "kardai ki dade, dare yayi kar Abban ki yajimu shuru"


"Toh Umma" ta fadi tayi rushing zuwa kitchen ta sanya ruwa a glass cup sannan ta nufi kofar dakinsa gabanta na dukan uku, tasan sarai xai iya korota shiyasa tayi dabarar kaimai ruwa, ahankali ta tura kofar dakin ta shiga.




  Tsaye yake yana kokari cire neck tie bayan ya ajiye coat din gefe, ganinta da yayi ya dakatar dashi yanai mata kallon kina bukatar wani abune, kaman tasan abunda yake aynawa, girgiza kai tayi tace "Mr Rasheed sai yanxu ka kawo, ga ruwa kasha" ta fadi at once hade da mikamai glass cup, bai karba ba balle ya tanka, closet ya nufa yadau towel yabar ta tsaye ya shiga bandaki, ya rasa wace irin mayyace Mardiyya, at work bai tsira ba sai taxo har office yimai shishigi ya dawo gida kuma ta biyosa, wace irin rayuwace wanan, most annoying part of her shine yadda take kura mai manyan idanuwan ta da mak'e muryarta tamkar wata sabuwar farar kura


.


Rashin tankata da yayi ko a kwalar rigarta, inda sabo ta saba, sukanyi shafe awa hudu biyar ko tari bai yiba, duk wannan ba matsalarta bane koda ace ma wuka zai dauka yana datse naman jikinta bata damu ba, tana sonshi kuma ganin  kyakyawan fuskar sa ya ishe ta farin cikin shekaru ashiri.


    Murmushi tayi ta kwank'wade ruwan tas sanna ta fito palo, hajiya safara na ganin empty glass cup din taji farin ciki ya ziyarceta, komai yafara kankama tsakanin yarta da Rasheed kenan tunda har ya iya amsan abu gareta. 




  Duk aganinta shiya sha ruwan. sallama sukayi da Momy, ta rakasu har bakin motar su sannan ta dawo cikin gida ta wuce dakinsa.




   Gefe gado yake zaune yana brushing lausassiyar gashin kansa bayan ya fito daga wanka, zama tayi kusa garesa heda da amsan brushern tahau tazarmai lufluf tana fadin,


"my boy ya aikin ?


"fyn" ya amsa mata, fuska ba yabo ba fallasa.


"My boy ka girma, ga kudi ka tara ta ko ina, yanxu miya rage ?"




  Anxo gurin, daure fuska Rasheed yayi tamau, tacigaba


" sa'anninka masu shekaru talatin da uku duk sunyi settling banda kai, ya kamata kayi aure"


Murya can kasa yace.


"am not ready, infact ban samu wace nakeso ba har yanxu"


"wannan ba excuse bane, kana da alot of yammata masu sonka, ga Mardiyya yarinyar kirki masu hannu da shuni, itace daidai dakai, naira na gugan naira"


Kai ya girgiza "bana son Mardiyya infact banason ya'ya masu kudin nan yawanshi basu da isheshen tarbiya, it better nasamo wata can cikin talakawan nan"




   B'ata rai Momy tayi, inda akwai alumma data tsana bai wuce talaka ba, mikewa tayi tsaye tanai mai wani mugun kallo, cike da karaji tace "talauci badai a xuri'ata ba, na gwamma ce mutuwa ta akan naga ka auri dangin tsiya, ban haifi dana dan talaka suci arzikin saba, tunda ubana ya haifeni bansan miye talauci ba kayi na farko kayi na karshe koda wasa karka kuskura ka ambata kalmar talauci a gidan nan, Mardiyya kuma saika aureta" karashe maganar tayi cikin huci sanan tai wurgi da brushen ta fuce dakin afusace.


Murmushi mai sauti yayi,


ya lura dai dabiar Momy bazata gyarabu, hatred dinta towards talakawa bazai canxu ba, ya rasa miye tsakanin dinta da takala, same story dinta kenan tun yana karami shiyasa yake da burin aurar talaka dan ganin miye illarsu da Momy ke masu kara tsana.




    Wayarsa dake kusa dashi ya dauka yayi dailing numbern Daddy Malam, bugu daya ya dauka suka gaisa. Yace "Mr  Rasheed kwana biyu, fatan kana cikin k'oshin lapia


"Am good, Aikuwa suka min yawa a office, kayi ready din komai gobe xan zo na cigaba a inda na tsaya"


"Toh sir, Allah ya kaimu"?


"Amin ya amsa mai sanan ya katse call din ya shingid'e bisa gado hade da lumshe idanu.


Safa da marwa Momy keyi adakinta, wana irin abun kunya my boy yake son jaza mata, ga Hajiya Safara duk ta daura mata zafi, wani zubin ma k'awarka ma tasan sirinka wani tashin hankali ne, dole ne ta tursasa Rasheed auran nan ko yanaso ko baya so...




D Young....

💖 *INA ZAN GANSHI?*💖




Rubutawa


Xarah Bukar..




®NWA




👉🏻E-book creator: D Young




6 - 10




    Tafiyar kusan minti goma  tayi kan babban titin Kawo dake cikin garin Kaduna.




    Hankalinta gabad'aya na bisa titin da babu alamun abun hawa na haya banda mayan motaci dake walk'yawa. 


   Ajiyar zuciyar mai dauke da wahala ta sauk'e, rashin abu hawa a unguwar tasu ba k'aramin ci mata ruwa a k'warya yake ba, ina ma ace tana da motar kanta saidai kawai yan polytechnic su ganta da ride dinta koda ma ace comot make i enter (One door).




   Jakarta irin wace ake sak'alewa a hammata ta bude ta ciro dubu biyu da Baba ya bata na siyan handout, kallon su tayi tana jinjina rashin k'yaun da dattin kud'in dayasha satalif, mai shesu tayi cikin jakar akayi rashin sa'a iska yayi sama dayan canjunan.


Da azama ta mike tahau tsintarsu, saidai kash, ashirin uku sun haura saman titi, tsabar rud'u bata ankara da SUV dake dannowa aguje ba tahau bin ashirin dinta dake tsilla tsilla a titin.


Kiiii!!!! Kakeji, yaja mugun burki da ita kanta saida ta razana, jiki na rawa take kalan motar da tunda uwarta ta haihefa bata taba gamo da irin taba, ko inuwar mutum bata hange ciki kansancewar tinted glass dinta, kallan motar kawai take tana imaging kanta aciki. Kallo daya yakai mata ya dauke kai yaja motarsa yabi gefenta ya wuce, RMD data gani cikin plate number yasata wage idanu, tanajin labarin family din a fulanin talla, yau gashi tayi gamo da motar, inama ace taga mai tuka motar yau da tayi kwanan farin cikin haduwa da mai kudi, duban kayan jikinta tayi ta buga tsaki, ta tabbata ya fola mata, ba mamaki kodaddiyar arabian gown dun jikinta ya kwafsa mata, last week kadai ta siyeta a gwanjan kasuwar bacci ganin sabuwar ita yan makaranta ke yayi.




   Cike da tausayin kanta ta ida tsince kudin sannan ta nufi k'aramar kasuwar dake gurin, tafi awa daya tana zagaye kasuwar kanan tasamu jakar swagger da ake yayi, cikin dubo biyun ta fidda duba daya ta siyeta, acewarta ta gaji da rike mak'ale mata.


Bayan ta ida dakyar tasamu achaba ya karasa da ita inda yan Marwa (keke Napep) ke tsayawa, aranta sai mita take tayi latti zuwa makaranta


 (sai kace wani ya aiketa kasuwan).




   "Ke tafiya ne" Ogan gurin ke tambayar te, amsa mai tayi da eh, yahau k'walla kiran Mamuda dake zaune can gafe yana gabtar rake.




   "Kaida kake layi maiya kaika da zama can" acewar ogan cikin muryar sa nayan tasha.


"gani zuwa" Mamuda ya fadi hade da mik'ewa kyakyabe jikin sa, wata tsohowar yadi mai araha ke sanye jikinsa da wata jar hula bisa kansa, jikinsa dukun dukun da bakin mai tamkar wani mechanic, fari ne dago dasai mai ido ne zai gane akwai farin, kacakaca da yake yasa na kasa tantance kamannisa.




    Tamkar wani shashasha haka yake magana, cikin maganar sa ta e'ena yace "shi shi gaaa muje"




   Tsulum Batula ta fad'a cikin marwan, ta k'agara tabar gurin.


Suna tafe tahau gyaran rolling din veil dinta dake nema warwaro, bayan ta gama kudin da suka zube tahau dirgawa dari uku da saba'in tagani, babu naira ashiri cikin, Allah ya isa taja, tana maganganu kasa kasa, yasata asara ya tafi yabarta.




   Duk abunda take yana kallonta ta circle side mirror, daure fuska yayi tamau had'e da dauke kai ganin ta dauko jarh  hoda tana shafawa, suna hawa booms hodar ta subuce hannuta, tas kake ji dankarariyar jar hoda ta fashe mai hade da madubi, baima lura ba, lailayo ashar da tayi yasa shi tsayar da Marwan.




   "Kan uban can, dan Marwa kamin babban asara"


Kallonta yayi sannan ya kalli inda idon ta yake, yace "ayi hakuri abisa rashin sani ne, banda ke wake shafe shafe a titi"


Harara ta kaima, "dayake titin na ubanka ne, ai dole kace haka, ina ruwanka kaine ke siyamin kayan shafan komi"


   www.realbashow@gmail.com




    "Allah ya wuce zuciyar ki, cikin kudin da zaki biya ki cire murtala uku da goma ki siya sabuwa"


Wani k'askantaciyar kallo ta aika mai, "bura ubar murtala uku da goma, nayi maka kama da talaka mai shafa hodar hamsi, banxa matsiyaci, talaka kun dauka kowa irin kune" tsaki ta buga tana cigaba da banka mai harara.


Kallonta kawai yake yana maimaita abunda tace, shidai baiga banbanci sa da ita ba da take kirasa talaka harda zagin dan tsohonsa dabai san hawa ba balle sauka.


Shareta yayi ya kunna Marwan yaja, tsine tsine tahau yi bai tanka ba.


"Kad poly xaka ajiye ni" yaji ta fadi cike da karaji.


Suna isa ta sauka ta fiddo tsofin goma da ashiri, naira saba'in tabasa, bata jira cewar saba tayi gaba abunta.


Mamaki da tsoron Allah ne ya turnuk'esa, yahau juya saba'in din, akalla daga Kawo zuwa gurin daya ijiyeta Jaka biyar ce, danta raina masa wayo ta basa saba'in tsabar tsiya, mai take nufi kenan, kudin hodar ta cira komi.




   Kai ya girgiza ya karasa gaba inda yaga passenger.




   B'angaran Batul kuwa dama saba'in tayi niyya basa koda ace hoda bata fashe ba, tana isa hall har angana 8 to 10 lec, ta tsaya jira na 12 to 2. 


  Jikin motar Minal yar ajin su ta jingine jikinta, duk wanda yaxo wucewa saiya tsamma nin motar tace, daga gefen motan taji murya Minal da kawarta Billy suna hira da dariya sam batasan sun kunno kai ba da alamu suma basu lura da ita ba, hirar wata magazine dake rike hannun Minal sukeyi.


"Amma fah RMD dinnan ya burgeni, duba fa kiga CEO ne a Mobile oil Nigeria(MON), one of the major petroleum product marketing companies amma ji yadda yake keeping low profile, ko picx dinsa baa gani, koda yake ance ma hardly 20 letter word ke fita daga bakin sa" acewar Billy


Murmushi Minal ta saki wanda babu tantama ta fola mai duk da sunansa kadai yaya appearing a magazin din.


   tau littafin yafar fah..




  👉🏻 "Ina zan Ganshi, na jima ina neman sa, ni wlh ganinsa kadai ya wadatar ni."




   Dan duka billy takai mata tana dariya, "ance komai nasa customised yake da sunansa, kila idan da rabo zakiga motocin sa ko wani abu nasa wataran.




   Tsur Batul tayi tana sauraran su, tana tuna motar RMD data gani dazu, dabarace ta fado mata ta saki murmushi, yawaci yaran masu kudi nan basu fiya sanyi kawace da talaka ba saidai iri iri su, balle ma Minal da take daukar kanta diyar shugaba, maganin su kadai zatayi ta hanyar raina masu wayo, tun shigowar ta poly bata samu kawaye ba yawanci yan kuci ku bamu ke manne mata, ita kuwa ta wuce ajin su.




   Wayar ta chaina kirar S7 da screen yagama tsagewa ta fiddo ta dasa a kunnuwanta, da ganin wayyar sai ki rantse original dince.


"Hello RMd nayi fushi tun d'azo kace zaka xo"


"Toh ba komai, ka gaishe min dasu mama sai naxo gida gaidata" katse wayan tayi tana kallon su ta gefe ido, sarai sun jita, imani ya hanasu magana banda saki baki da sukayi suna kallon ta.




   Taku daya biyu tayi da niyan barin gurin, sukayi azama tarota, Minal tace "Fatima kin san shine ?




   A yatseni ta dubeta, aranta tana fadin shegia ashe tasan suna na, a fili tace "wa kenan ?


"Rmd mana, naji kin kira sunansa ne"


"Ayyo wai cousin dina Rmd, kina neman sane ?




   Kafin Minal tayi magana Billy ta janye ta gefe,




  Tana magana kasa kasa, alamun bata gamsu da Batul ba, kayan jikinta ma ya isa ya nuna class din data fito.




   Gyara murya Batul tayi tace "nasan bazaku yadda dani ba, amma kusani ni abun duniya bai dameni ba shiyasa nafison zama simple, dan kun ganni haka dat doesnt mean am poor" k'arashe maganar tayi dakai masu harara sannan tayi gaba.




   Da azama Minal tayi saurin taro ta tanai bata hakuri, harga Allah ta gamsu da kalamanta tunda shi kanshi Rmd din ance kudi bai dame saba same goes to his cousin kenan. 


   Dakyar jidda ta hakura bayan billy tasa baki, sai wani ja masu aji Batul take wai ita mai cousin, Minal dai sai kokarin chilling dinta up take, a lecture ma kuna da ita suka zauna bayan an gama suka wuce African dish cin abunci, nan ma sai yatseni take ko dogon surutu tak'iyi karsu k'ureta da tambaya, gabanta sai dauks uku uku yake karsu barta da biyan kudin abinci dan plate dinsu akwai tsada gashi ta cire kunya taci tayi nak, sa'ar ta Minal ta biya duka bill din sannan suka firo tafiya gida, ba yadda basuyi da ita su ijiyeta gida ba taki yadda acewar ta library xata shiga karatu, sai da taga sunja sun tafi da mintuna talatin sannan ta hau Marwa ta wuce gida murna fal zuciyan ta tasamu b'agas, sai dai tunanin ta daya


 "Ina Zan Ganshi?"




  Nima xarah nace Ina xan Ganshi, kuma Readers ina zaku ganshi ?


Ku biyoni muje Neman sa😂😂

💖 *INA ZAN GANSHI?*💖




Rubutawa




Xarah Bukar




®NWA




E-book Creator: D Young




11-15




  Cikin takun ta mai daukan hankali ta karaso tafkek'en had'add'an office dinsa, office mai shegen kyau. 




    Secretary dinsa Charles tayi kicibis ya fito rike da wasu doc a hannusa, da axama ya risina gaidata cikin harshen turanci.




Atakaice ta amsa.




" Mr Rasheed yana ciki ?


Yace "Baya ciki"


Bata jira cewarsa ba ta cusa kai cikin office din, binta yayi da duba ciki da mamaki halin rashin zuciya irin nata, ako yaushe saita baro department dinta taxo ganinsa amma ko kallo bata ishe shiba, ba kuma shi zai hana gobe ta dawo ba.




    Lumshe idanu tayi ta karasakan swivel chair dinsa ta zauna shakar hadaddiyar kamshi dake tashi daga bisa kuma ta shingid'e barawo bacci yayi awon gaba da ita.




    Agajiye likis yake driving harya karaso katafera building mai dauke da tambarin Mon, parking yayi, kafin ya fito guard uku sanye da black suit suka bude mai murfi hade da mika mai gaisuwa, ciki ciki ya amsa, ya fito hade da dagatar dasu ganin suna kokarin take mai baya, tsayawa cak sukayi ya wuce cikin building din, maaikatan ciki sai gaida sa suke cike da girmamawa bai tanka ba banda haryan office dinsa ya nufa cike mamakin abu daya da yake a kullum idan yaxo office, idan kai ba komai bane ko kallo baka ishe mutane ba, laila kuwa yaro da kudi abokin tafiya.




    Da azama charles ya mike hade da risina, "Good afternoon sir"


Hannu kadai ya d'aga mai bai tanka ba ya wuce cikin office, ranshi ne ya kuma bacci ya karasa kan daya daga cikin sofa dake gefe ya zauna hade da daukar Wayar yana latsawa jifa jifa kuma yakan dago ya kalli yadda take baccinta anutse, yarinya kyakyawa tana bata lokacinta akansa shifa bazai aure taba amma ta kasa ganewa.




    Koda yake laifin hajiya safara ce da take bata hope game dashi.




     Charles ne ya shigo rike da wasu takaddau, ganinta yasashi ware idanu, sam ya manta Mardiyya ta shigo, idan bai tashe taba saidai kuwa ta kwana gurin yasan sarai Mr Rasheed baxai tashe taba, nufa yayi saitin ta yahau bubuga desk din, firgigit ta walka tana kokarin adjusting mayafin ta dake kokarin yarfowa kasa, kunya ce gabadaya ta kama ta ganin sa zaune saidai da alamun baisan tana gurin ba, mikewa tayi da azama ta gaida shi, bai tanka ba tayi saurin takawa bakin kofar xata fice taji yace karna kara ganin thin legs dinki agurin nan"


"toh" ta amsa cikin rawar ciki ta fice.


Kimtsa gurin charles yayi sannan ya ajiyemai takardun ya fice.




***




  Salati tayi hade da mik'a bayan ta farka daga baccin wahalan da tayi, k'iran sallah magrib ya tabbatar mata da tafi awanni uku tana bacci, duk da tasan bacci sakaliya zuwa magrib ba kyau hakan bai hanata shingidewa ba, wani mugun yunwa taji ya turnuke ta sai sannan ta tuna da tun abincin African dish dataji da rana bata lashi komai ba.




Fitowa tayi daga dakin ta iske hassan da husaini na alwala gindin rijiya, sai yusuf dan karaminsu dake zauna yana cin shinkafa da wake. Hajjo sai kokarin kankamta gurin murhu take.




   Mik'a ta kumayi akaro na biyu, tace "Hajjo kin gama abincin kuwa, har wani jiri jiri nakeji tsabar yunwa"


"


   Dayake ga uwarki baiwa ko, dan ubanki kizo kice tunda ke na girkawa, yar kusun uwa" Hajjo ta fadi cike da bacci rai, bata ko kalle taba tadau lankar samirar tayi cikin daki.


Dariya Hassana ya fece dashi, aranshi yaji dadi yadda Hajjo tayi mata, "toh ayi dai mu gani ko sabulu xai daina kumfa, "




   Harara Batula takai mai tasan sarai inda ya dosa, tsaki tayi tace "banza kawai, toh munyi da toka ma yayi kumfa, kuma wlh ka shiga taitayinka idan bakaso nayi kudi na manta ka kasan dai ni matar manya ce"


Dariya yayi "wazai kwashe ki badai ..


Katse mai xancen Hajjo tayi daga daki, tana fadin 


"baza ku wuce masallaci ba ko ?




"Zamu" husaini ya fadi hade da jan Hassan suka wuce, dan shi dama magana ce makiyinsa, idan kaga yayi doguwar magana toh da Baba ne.




    Cize baki Batula tayi danba karamin shak'a tayi ba, akalla shekaru shida ne tsakanin ta da hassan amma ya mugun raina ta, yaro dan shekara sha biyu sai ki rantse dan arba'in ne yadda yake tsaro xance. 




  kallon yusuf tayi da har yanxu ya kasa cinye yar lomar dake cikin kwanon, tace "Kai tashi amso min salad da tumatur gurin Baba"


Kafin yayi magana Hajjo ta fito, bazai jeba, "ajiye abinci ka wuce sallah" ba shiri ya karashe loman yayi waje. 




    Ganin ba mafita yasa batul yin alwalar tayi sallah sannan ta zauna tsakar gida jiran ace ga nata abinci amma taji shuru.




    Sallaman baba ne ya sata mike wa tsaye, ta amsa. "baba sannu da zuwa" ta fadi hade da amshe kwandon dake hannusa.


"Yauwa fatima, har kin dawo, ya makarantar ?


"Alhamdulilah"


Tabarma ta dauko ta shimfida ya zauna hade da shi mata albarka, itama zaman tayi tana kara mai sannu, baiyi mamakin abunda takeyii ba dan kuwa ta saba tarairayar sa, idan kuma halin nata ya motsa ko gaisuwa dakyar takeyi balle ta nuna su suka haifeta.




   Fitowa da langar abincin Hajjo tayi, tamai sannu da zuwa sannan ta koma daki dauko furar data dama mai, sannu baba"


 Batul ta kuma fadi akaro na biyar,


"Kinci abinci kuwa


Tace "a'a, dama kai nake jira Baba"




   "Lailai kuwa kin cika yar baba, hada mata muci", ba shiri tahau zuba mai da yaji suka fara ci, Hajjo na fitowa tahau salati, dire furar tayi tahau Batul da dundun, "dan ubanki tashi nace, wannan abinci badake na dafaba, yar banxan yarinyar marar mutunci"




     Murtuke wa batul tayi bata da alaman tashi,


Cikin sanyi muryarsa baba yace "waike Bareera ban hanaki zagin taba, baki san cewa wana bakin naki shine xai iya kaita ga halaka ba"


Hajjo kam ta kule "Malam ai dole nayi magana, yarinyan nan na ganina ina aiki ko sannu balle ta temakamin, nagama kuma dan batta kunya taxo ta baje tana ci".


"Ki dunga hakuri, Fatima ai yarinya ce komi tayi bai kamata ki hurar da ita da yunwa ba"


Toh" kawai hajjo tace ta koma daki ta zauna, tana jinsu suna hirar da dariya har sauran yaran suka shigo aka barke da hira.


***


Washe gari dakyar tasamu wata bakar doguwar riga ta sanya,yawanci yan atamfofin nata sun sha jiki, kunyar sasu take kar su Minal su raina ta, mayafi karamin ja ta dauko tayi rolling, fitowa tayi ta leka dakin Hajjjo ta iske tana sharar, tace "hajjo saina dawo"


Zuciyar hajjo fawas ta amsa mata da


Toh batula, Allah ya temaka, ki dawo dawuri dai"


"Amin" butula tace tana murmushi, shiyasa takeson Hajjo sam bata da riko kaman ba jiya ta kama d'addaurewa ba.




   Zaure sukayi kicibis da Baba xai shigo ta gaidasa, yace da ita ta koma tasanya hijabi dan shigar ta tayau zam bata mai ba, ba musu ta sanyo hijab bayan ta saka mayafin cikim jaka, ta fito ta amshi kudin mota ta fice.




   Bata sha wuyaba tasamu marwa ya kaita poly, da sauri ta wuce girl toilet ta cire hijab din tasaka mayafin sannan ta wuce zuwa hall, already su Minal sun kama mata sit, zama tayi tana wani shan kamshi ana gamawa suka fito da niyya wucewa gida kasancewar lec guda garesu.


Minal tace "Fatima yaushe zamu je gaida cousin dinki ?


Yatsine fuska tayi tace "very soon, baya gari ya raka mamansa Abuja checkup suna dawowa zamu je"


Allah ya kaimu" Minal ta fadi.


Billy tace "y not muje gidan ku"


Gaban ta ne ya fadi, aita gwamma ce su mata duka akan suje gidansu, mazewa tayi tace "okay muje, saidai Daddy baya gari yaje paris"


"Ba damuwa" acewar Billy.


motar Minal suka shige, billy abaya, Batul ta babbak'e agaba suka kama hanya, tunanin karya da zatayi kawai take, tafiya mai dan nisa sukayi har suka iso Kawo, billy tace" Minal shigar mu layin can na siyi salad da tumatur mai kyau"


"Ki bari akwai wani can gaba"


"Nidai muje can din, customer din mama ne, can take turamu siyo mata"


"Tonaji", lemcy tace hade dayin ribas, Batul jiki duk ya mutu, Allah yaaa ba gurin Baba take nufiba, bata gama tsorata ba saida Billy ta nuna Baba dake nesa tana fadin karasa teburinsa....

💖 *INA ZAN GANSHI*💖




Rubutawa




Xarah Bukar




®NWA




16 to 20




Tashin hankali ne ya dabaibaye ta, tayi saurin shingid'e cikin kujerar hade da janyo mayafi ta rufe fuskarta.


"Bba ina wuni" suka gaida shi, ya amsa ciki da fara'a, dan kuwa ya taba ganin Billy. Salad da tumatir masu kyau ta siya ta bashi kudinsa, ba yadda batayi ba yabar canjin yak'iya yabata kudinta, sai sannan Minal ta tab'ota "bazaki siyi komai ba'. banxa tayi kaman bataji ba. Godiya suka ma Baba kanan suka bar gun, Baba yaso ya gane kaman itace sai kuma yayi saurin kawar da tunanin sanin cewa da hijab ta fita kuma ma ina Fatima ina yawo da manyan masu kudi haka.


Adan firgice ta yane mayafin fuskar ta, duban Minal tayi tace "kinsan mi ajiye ni nan, na msnta ashe mama ta aikeni chemist"


"Haba dai muje to" acewar Minal.


Cikin nuna damuwa tace "ku bari kawai, next tym sai kuzo, yanxu muna xuwa gida zatace na tsaya shad'anci a hanya".


"Eyya to ba komai, zaki gane gida daga nan" Minal ta fadi hade dayin parking


"Eh, gobe mu hadu skul, tnx"


Da sauri ta fito daga motan gudun karsu tsayar ta, Billy tai mata bye hade da dawowa gaba, itadai har yanxu ba wani yadda tayi da Fatima ba.


Saida taga sunja gaba sannan ta sauke ajiyar xuciya, "yan durun uwa halan hauka nake na kaiku gidan mu, yadda kuke nema Rmd nima nemansa nake, dan kuwa dani ya dace, ina xan Ganshi ?" Ta fadi hade da waiga wa kaman yana kusa.


Marwa tagani ya nufota tayi sauri tarar sa, leko dakansa yayi da niyyan tambayan inda zata sukayi ido ihu, atare duk suka ja tsaki, inda tasan wanslan matsiyacin ne da bata tsayar dashi ba, amma ba yadda ta iya.


"Layin yan wanzan xaka kaini "


Bai saurare taba ya kunna marwan sa yayi gaba, ya gwammace ya k'ona mansa akan ya dauki fitsararar yarinyar nan, yana ji tana xurfa mai zagi bai tsaya ba yayi gaba abunsa. Dakya tasamu wani ya kaita gida sam ta mance da sauya hijab, tana sauka idon Baba akanta daga can nesa yana kallonta, mamaki sosai yayi ganinta da gyale kuma babu tantama itace yagani a mota yammatan nan, ransa ya bacci ba kad'an ba, haka ya shigo gidan da magrib, yaran na gaida sa ciki ciki ya amsa, ya kira hajjo sun dade suna wata mahimmaciyar magana daga bisani kuma ya fice, Butul kam ko ajikinta aganinta can maganar da suka sabayi sukeyi, tun ba yauwa ba zataga iyayen suna tattaunawa k'asak'asa wataran harda sharar kwalla sukeyi, itadai bata san masu ba. Kayan da zata sa gobe take gogewa da dutsan guga na gwarwashi tana gama ta hange su, ta dauko sauran fanta dinta da Minal ta siya mata ta sha rabi, hade da tande baki, arziki akwai dadi da yanxu dan jolly juice zata jika tasha. Yusuf ta kwallawa kira ta bawa sauran yasha.


***


Zaune suke a dinning suna breakfast, babu mai magana cikinsu tsabar yadda suke bawa table manners dinsa, shiya fara gamawa ya mike zuwa palo ya zauna yana latsar wayarsa, sanye yake da kananun kaya dasukayi matukar amsar sa, tana gamawa Altine mai aikinsu ta kira kwasar kayan gurin itama ta koma kusa garesa ta zauna. "My boy bazaka office ba, Mardiyya tacemin kwana biyu baka zuwa da wuri ?


Fuska murtuke yace "xanje" ba tare daya dago kallan taba.


"Easy my boy, da Mom dinka fa kake magana".


Shuru yayi kaman bazaiyi magana ba yace "i know, did i say sumthing bad"


"No, amma ai saika kalle ni ko ?


Dagowa yayi ya kalleta, sam bayason yin fara'a yanxu saita kawo mai xancen Mardiyya, bama wana ba so yake kawai yasan meke tsakaninta da Hajiya safara danya tabbata itace ke uxura mata.


Kwankwasa kofar palo ne ya katse masu hanzari, Altine taje ta bude hade da gaida mai shigowa.


Murmushi Rasheed ya saki ganin daddy malam, dan saurayi ne mai shekaru 26 daganin kayan jikinsa kasan ba wasu masu hali bane sai rufin asiri. Dogon tsaki momy taja bai damu ba ya duka kasa gaidata bata amsa sa, ya nufi Rasheed suka gaisa cike da fara'ar sannan ya zauna, it seems urgent magana zasuyi saidai Daddy malam yayi shuru ganin hararar da Mom ke aikama sa,


"Muje waje " abunda Rasheed ya fadi suka mike tsaye.


Ba karamin haushi Momy taji ba, idan bata manta ita ta kawo daddy malam amatsayin mai wanke mata mota da dadadewa, tama manta dashi abunda bata sani ba ashe suna tare da Boy dinta har ila yau, ba yadda bata raba suba, sunki rabuwa. Tsaki ta buga akaro na goma tana fadin "mi xaai da talaka".....

0 Response to "INA ZAN GANSHI Hausa Novel"

Post a Comment