-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Za'a fita neman jinjirin watan gobe Juma'a

Za'a fita neman jinjirin watan gobe Juma'a

Za'a fita neman jinjirin watan gobe Juma'aZa'a fita neman jinjirin watan Zhul-Hijja a kasar Saudiyya ranar Juma'a, 29 ga Dhul Qa'adah 1442 bisa kalandan Ummul Qura, wanda yayi daidai da ranar 9 ga Yuli, 2021, rahoton Haramain Sharifain.

Duba watan Zhul-Hajji ne zai bayyana ranakun Hajji ga Mahajjata da kuma Sallar Layya ga sauran al'ummar Musulmai a fadin duniya.

Za'a yi duban watan na farko ne a jami'ar Al Majmah dake Sudair, yayinda za'a sake dubawa a Tumair da kuma sauran wurare.

Kotun Kolin Saudiyya ce zata sanar da sakamakon gani ko rashin ganin watan da yammacin ranar Juma'a

Source: Legit

0 Response to "Za'a fita neman jinjirin watan gobe Juma'a"

Post a Comment