YADDA JIKINKI ZAIDINGA KAMSHI AKODA YAUSHE
YADDA JIKINKI ZAIDINGA KAMSHI AKODA YAUSHE
KAMSHIN JIKI
‘Yan’uwana mata ga wannan sirrin na kamshin jiki don Allah mu daure mu rika yi don wannan zafin al’amarinmu mata sai da mu’amalla da turaruka masu kamshi. Idan a ka rike wannan, a koda yaushe jikinki zai rika kamshi, ko kin yi wanka ko ma kafin ki yi.
Da farko a zuba lalle a tukunya a sa ruwa, a dora a wuta ya dahu sosai, sai a sauke, a tace, sannan a cire garin lalle gefe sai a mayar da ruwan kan wuta, a rage wuta sai a kawo madarar turare na.
Sandal Bakhur, damarar Ledus da madara Musk, sannan a bari ya tafasa sosai, sannan a sauke, in ya huce ki nemi jarka ko galan mai cin lita 4 ki juye a ciki, duk sanda ki ka yi wanka, in kin gama sai ki kawo wannan hadin ki zuba kadan a bokiti, sai ki kara ruwa kadan sai ki dauraye jikinki da shi, kar ki goge jiki ki bar shi ya bushe, za ki sha mamakin yadda kamshin zai zauna a jikinki.
Sannan kuma ku zamto masu yawan mu’amalla da turare a koda yaushe, in har kun san baku da hanyar wadannan to ku zama masu yawan sa turaruka a wurare shida kullum a jikin ku.
1.) Bayan kunnenku
(2.) Dantse
(3.) Sharaba
(4.) Wuya
(5.) Kasan nono da sauransu.
Gaban ku kuma ku dan samu auduga ku jikata da madarar misk (Aisha) sai a dinga matsi dashi, haka zaisa shima gabanki (farji) ya dinga diban kamshi duk lokacin da maigida yakai ga wurin.
0 Response to "YADDA JIKINKI ZAIDINGA KAMSHI AKODA YAUSHE"
Post a Comment