-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Amfanin Kankana Ga Ya Mace

Amfanin Kankana Ga Ya Mace

Amfanin Kankana Ga Ya MaceKankana na daya daga cikin ‘ya’yan itatuwan dake dauke da sinadaren gyaran jiki da gautsin fata da kuma rage tsufar jiki domin tana dauke da sinadaren dake wanke maikon dake taruwa a magudanar gumi a fata wanda yawanshi ke haifar da fesowar kuraje da dama. Don haka, amfani da kankana a jiki na da matukar mahimmanci sosai ga rayuwarmu ta yau da kullum. A yau na kawo muku hanyoyi da dama da za’a bi domin yin amfani da kankana domin samin fata mai laushi da kuma sheki a kodayaushe:


==> Kodewar fuska: markada kankana tare da gurji sannan a rika shafawa kamar sau biyu a rana na matukar magance wannan matsalar. Sannan za’a iya markada kankanar zalla sai a dauko auduga ana tsomawa ana shafwa a fuska sannan a barshi ya bushe na tsawon mintuna goma sha biyar. Za’a iya markada kankana da ganyen na’ana’a sannan a rika shafawa a wannan wajen da fatar ta kode. Amma abu daya nake so a yi amfani dashi a cikin ababen da na lissafo.


==> Domin yankwanewar fata: A markada kankana sannan a zuba mata zuma kadan sai a rika shafawa a inda fatar ke yankwanewa sau biyu a rana. A samu kankana da ruwan lemun tsami da sukari sai a hadasu guri daya. Kafin sukarin ta narke sai a rika dirzawa a inda fatar ta yankwane domin mikar da fatar.


==> Rage shekaru: A samu kankana da man zaitun da kindirmo da kuma kwanduwar kwai sannan a kwaba a rika shafawa a fata a kullum domin samun sakamako mai kyau mai inganci. Za’a iya markada kankana sannan a samu ayaba a kwaba sannan a hadasu guri daya sai a rika shafawa a fata. A samu markadaddiyar kankana da madara da kuma fiya sannan a kwaba a rika shafawa a fata domin samun sakamako mai kyau.


==> kurajen fuska: a sami kwallon kankana a busar a rana sannan a daka yayi laushi sannan a tafasa ruwa a zuba sai a tace sannan a rika wanke fuska dashi.==> Gautsin fata: a markada kankana sannan a zuba mata man ridi da na kwakwa sai a shafa a fata a barshi ya kai tsawon mintuna ashirin sannan a wanke.

0 Response to "Amfanin Kankana Ga Ya Mace"

Post a Comment