-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Tawa Tasameni Hausa Novel

Tawa Tasameni Hausa Novel

 Tawa Tasameni Hausa Novel

1-01

Posted by ANaM Dorayi on 12:09 PM, 03-Dec-15

________________NA _________________

__________ HALIMA ABDULLAHI K/MASHI_______

Na mike a hankali ina ninke sallaya ban kai ga ajiyewa ba

naji ana sallama,na juya cikin don san in dauki muryar

mai sallamar har kin shigo kenan?nace bayan na amsa

sallamar ta shigo sanye da kayan makarantar islamiya

masu launin farare kar,riga da wando da hijabi. Tace kina

kallona ba zaki yi sauri ba sai munyi latti ko?nace ko

munyi latti ai yau akwai layi na nufi daki dama nayi

wanka sai kawai na dauki kayan makarantana dake goge

kan gado nasa,Amira tace su mama basa nanne?nace eh

basa nan gashi har jamila ta tafi a lokacin islamiya yayi

amma basu dawo ba,na rungume takarduna da Alkurani

na na fito falo muka fita na mika ma amira ta rike min

littattafaina don zan kulle kofar,natura key din inda muke

sawa in mama zata unguwa ni kuma ban dawo daga

makaranta ba sai ta aje min a gun in kuma zan fita tace

in aje mata.Amira ta dube ni ta dubi dakin su mami tace

yau su mami ba zasu bane?nace da kyar ne don yau ko

makarantar boko bataje ba bata jin dadi in mun dawo kin

gaida ita.isarmu islamiya kenan muka tarar da an tare

yan latti ana yi masu bulala,Amira ta soma dariya don ta

sanni da tsoron bulala na dafe kirji ina fadin yau na shiga

ukku zamu sha bulala ni iman,Amira tace don Allah mu

karasa ba kece kika jamanaba?nace Amira ina jin tsoro

ta ja hanuna na bita muna isa gun muka tadda harda

Ahmed yayan Amira don shine Amir dinmu yace don

Allah ku zo inyimuku ku wuce don yan kwanakin nan kun

kware gurin yin latti.Nace don Allah yaya Ahmed kayi

hakuri yace wllh sai nayi maku kun fi sauran ne?da zan

kyaleku ya ci gaba da cewa kuna bata mani lokaci in har

kuka bari kowa ya gama shiga sai na zane ku tas,wani

kusa dashi yace to kai Ahmed ka bar su su wuce

mana,yace Allah Aliyu bazasu shiga ba sai na dakesu

wanda yaya Ahmed ya kira da Aliyu yace to bari ni in

dake su to,yy Ahmed yace sai dae kai na dake ka a

madadinsu,in ko ba haka ba sai dai suzo ni in dakesu da

kaina,Amira na da zuciya don haka sai taje ta mika

hannun shi ko bai bugi hannunba ya zuzzuba mata a

jiki,ganin haka ya sani na kuma rudewa ina faman

magiya don ni kowa ya sanni da shegen tsoro sannan

bani son abinda zai taba mani lfyata don haka ma

dawuya ka ga nayi laifi nakan yi kokari ganin nabi dukkan

dokar da aka shimfida a gida ko a makaranta.Amira

ganin zan bata mana lokaci taje gaban yy Ahmed tace

ka bige ni a madadinta shiko da gayya ya ringa tsala

mata har sai da Aliyun nan suka ce ya isa mana Ahmed

niko hawaye na somayi na kama Amira muka wuce ina

fadin me yasa kika je ya buge ki?ta soma share mani

hawaye muka wuce ajinmu,Shidda na yamma daidai

muka tashi dama mu yan aji biyar Ajinmu a sama

yake,don haka titin kan layinmu naji an kwala mani kira

cikin fada na juyo sai naga anty mariya gabana yayi

faduwa don na san ganin ta ba alkhairi bane hakan ce ta

kasance domin kuwa tana isowa gun mu sai ta hauni da

zagi wai na taho makaranta ban jira su kamal ba don

naga ba kannena bane shiyasa ta cigaba da zagina gami

dayi mani gorin gida wai shegiya agola yar kara nazo zan

fare,Amira tace mani don Allah iman zo muwuce taja

hannuna cikin fushi tayi maganar,anty mariya ta koma

kanta tace ke kar kiyi mani rashin kunya don zanci

ubanki a nan,Amira tace ba dai ubana ba kuma har kika

yarda kika buge ni zakiyi da kin sani,cikin rawar jiki na

rufe ma amira baki muna cikin wannan hali sai ga anty

hadiza da bilkisu da saade dukkansu sai zaginmu suke

yi,Sa'a har da dungurina,nan amira ta kai mata duka nayi

saurin rike amira don kar suyi mana taron dangi su bugi

banza don nasan kadan suke jira anty mariya tace wai

ke amira nan da dukan Sa'a zakiyi?amira tace yo da sai

in barta ta duke mu,don kunga bata ramawa ne,lman din

shi yasa ku ka raina ta, taci gaba da cewa,ai Sa'ar ba

girman lman din tayi ba,bilki tace to ta koma gidan

ubanta mana in kuma bata dashi bane mu sani,naja

hannun Amira muka wuce Amira ta cigaba da lallashina

sannan tace min,don Allah lman in tambayeki mana?na

share hawayen fuskata da gefen hijabina nace ina jinki

tace babanki ya rasu ne ko yana nan? In ya na nan ina

yake?na dan yi shiru sannan nace Amira baba na yana

nan bai rasu ba wasu hawayen suka kuma zubo mani

ban damu da in goge ba na cigaba da cewa yana tudun

wada ta nan kaduna,Amira ta ce to ki koma mana don

zaifi maki kwanciyar hankali komin talaucin ubanka ya fi

zaman agolanci y not ki koma can?nace uhhm Amira

mubar zancen nan wata rana zan sanar dake dalili mai

karfi da ya hanani in bar gidan nan sannan kisan

mahaifina ki kuma daina zargin ko kwadayi ne ya zaunar

dani a nan,Amira tayi sauri ta rike ni gami da tsaidani

wuri guda tace wllh ni ba nufi na kenan ba naga

wulakancin da su Sa'a ke maki yayi yawa ne shi

yasa,nayi mirmushin karfin hali nace no a

Amira karki damu na fahimceki sannan muka wuce gidan

su Amira,kamar minti goma na dauka gidan su Amira

sannan ta rakoni kofar gidansu tace min a cikin satin nan

ba zata shiga gidanmu ba,ina shiga naga su Anty mariya

sun rigani dawowa kuma sun fadi karya da gasky sai

faman fada suke su da iyayensu suna ganina ai dawa

Allah ya hada su ba dani ba suka hauni da masifa,Haj

Kulu mahaifiyar mami harda aibantani gami dayi min gori

sannan tace zata ga Amiran don ubanta sai ta gaya mata

dalilin da yasa ta zagi su anty mariya don ba sa'anin

yinta bane,ni dai sum sum na wuce daki

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

Mama na gani a falo ta zuba tagumi da alama taji duk

abinda suke cewa(kishiyoyin nata)ta dubeni fuskanta

cike da tausayina tace Iman menene dalilin da yasa kika

tsokanin mutanan nan bayan kinsan halinsu sarai nace

mama wllh ban san me nayi masu ba na dai ga anty

mariya sun zo da su Sa'a suna ta faman zagina wai ko

na taho makaranta ban jira su Kamal ba ko mene oho

mama tace to naji suna cewa kuna ta zaginsu keda

Amira nace Allah mama ni sam ban ma yi magana ba

Amira dai ce kinsan ta da zuciya shine fa ta tanka masu

amma sam bata zagesu ba,mama tace to don Allah ki dai

na kulasu sam musamman a kan titi in ma sun zo maki

da irin wannan ki dinaga basu hakuri kiyi wucewarki kinji

ko?nace to mama muka mike don yin sallar magariba.

Misalin sha biyu da rabi muka taso daga harda yau ma

yan dakinmu ne kadai ni da jamila da sagir muka je,dama

sauran yan gidan zuwa islamiya bai damesu bane bare

ma hadda,gara ma mami takan je to amma tun fridy bata

jin dadi,muka tadda mama a kicin tana girki na shige

kicin din bayan na ba jamila Alkurani na da hijab ta wuce

daki nayi ma mama sannu gami da amsar albasar da

take yankawa,nace yau me kike dafa mana ne,tace dan

wake nayi in kin gama yanka albasar ga mai can sai ki

soya shi bari in dauko kular baban ku nasa mishi,don

yace zaya aiko a dauka nace dan waken za'a kai mashi

kasuwa mama?tace nima haka na ce mashi sai yace

yasan komi na dafa ba zaiyi shakkar kaishi cikin jamaa

ba,nayi murmushin jin dadin an yabi mamana ai kin iya

girki ne mama,ta fita tana dariya ina jin dadin yanda

mama take sakar mani fuska duk da kasancewa ta yar

fari a gunta sannan mama uwa ce mai wahalar samu

takan ki nata don duniya ta soshi bata fada da zagin

yayanta sai dai nasiha gami da lallashi.bani manta

lokacin da nake karama mama ta kan zaunar dani ta

nuna mani girman Allah gami da cusa mani tsoronshi

tana nuna mani abinda zanyi da tsira daga azabarshi a

wancan zamanin ta kance kar na zagi kowa ko an zage

ni kar na rama sannan kar na yarda sallah ta ringa

wuceni don haka ma tun ina karama nasan sunnoni da

farillai gami da mustahaban sallah da alwala sannan bani

zagi in ma wani yayi naji sai na gudu ince kar na sami

zunubi saboda jin da nayi shiyasa ban iya zagi ba,sannan

mama ta na da hakuri na ban mamaki zata iya zama da

kowa ga ladabi don ban taba ganin tana musu da

maigidanta ba komai yace tana yi sannan ga tsafta komi

namu daban yake duk inda muka shiga ni da kannena

mukan zama abin sha'awa gashi mama ta iya girki sosai

na zamani da na gargajiya shi yasa maigidanta ya kanyi

alfahari da ita baya shayin kawo baki ko shi akai mashi

kasuwa haka nan duk da cewar basu shiri da abokan

zamanta suma suna farin ciki da ranar girkinta don sunci

mai dadi sannan yayansu kanyi rigima a duk lokacin da

suka zo cin abincin kai ko ruwan tea ta dafa daban yake

don zaka iya shanshi ba sai kasa madara ba.nayi zurfi a

tunani bansan har mama ta dawo ba sai dai naji tace

haba iman har yanzu kina kan yankan albasar nan baki

tashi ba?nayi firgigit na juyo tace ai kina tunanin menene

haka?bata saba mana da karya ba don haka na sanar da

ita tunanin da nake na kara da cewa mama ina matukar

jin dadin zama dake kuma ina alfaharin kasancewarki

uwa a gareni tayi murmushi tace sai ki dinga koyi da

hakan kuma kiyi watsi da duk wani kuskure da kika ga

nayi sai da na zuba albasa a cikin man sannan nace wllh

mama ni ba taba ganin wani kuskurenki ba tace kar ki

kuma cewa haka babu mutumin da baya kuskure dan

adam ai ajizi ne nace to,sai da muka gama cin abinci

sannan na nufi dakin su mami don in gaisheta ina son

inje amma ina tsoron haj kulu mahaifiyarta ynxu ma

ganin ta shiga wanka shine dalilin da yasa xan je duk da

dai bayin a dakin yake amma nasan ta shiga wanka ne a

bakin kamal inda na tambayeshi ta na nan yace man ta

shiga wanka na samu mami zaune a falonsu tana cin kifi

nace yan jinya an samu lfy kenan tace kar kice man

komi komi tunda baki zo gaisheni ba nace wlh ina son in

xo gaisheki ina jin tsoro ynxu ma kamal na tambaya yace

mani mominku ta shiga wanka,um kina jin tsoro ne?nace

baki yarda bane tace na yarda nace Amira ta na gaisheki

tace tana amsawa tace ai naji sauki kwarai don naci dan

waken mama sosai kafin inyi magana sai muka ji

maganar haj kulu fuskarta a daure ta nuna ni tace

wannan yarinyar baki da zuciya in banda rashin zuciya

har yaushe zamuce ki bar shigo mana daki amma kin

kasa to yi nan ta nuna min hanyar waje.ta cigaba da

cewa kekasashiya marar zuciya anyi halin uwa mami

tace kai mama don Allah ta kaima mami duka a gadon

baya yi min shiru yar iska duk ba kece kika jawota ba in

na kuma ganinta anan sai naci ubanki ni dai nayi waje

cike da takaicin zagin da nasha.

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

washegari monday ga aladar gidanmu duk mai girki itace

zata tashi tunda asuba dafa ruwan tea ko wane daki

suna zuwa su dibi nasu a cikin flask su kai daki suje su

hada,yau haj kulu ce da aiki don haka sai da na bari ta

fita sannan naje diba bansan cewa madara ta kare ta

kicinba sai da nazo hadawa da sauri na nufi daki na iske

mama tana sa ma jamila safa nace mama babu da

madara ko kadan ta dubeni tace kash jiya.... amma ga

dari biyar can kan mirror dauki ki siyo yanda zata isa in

yaso kafin ya wuce sai in sanar dashi nace to na dau

kudin na fita,a tsakar gida na iske mami sanye da

uniform hannunta rike da safa tace har kun gama

karyawa?nace aah ya jiki tace da sauki yau dai zanje

makaranta nace da kyau kam ki leka ta dubeni ynxu ina

zaki?nace shagon sanita aje safar akan window din

dakinsu taje muje in rakaki nace kardai a nemeki tace

kedai muje,dashi ke shagon ba nisa nan da nan muka

dawo shigowar mu kenan haj kulu ta fito daga daki

ganinmu tare da mami ya yi matukar bata mata rai ta

hau mami da zagi gami da daukar alkawarin dukan

mami,haj yaya uwargida sarautar mata itace ta fito daga

dakinta tace ke kulu kina bani mamaki ga yar iskar da

zaki jibga nan ta nunoni sai ki hau yarki da zagi kinsan

fa ita da uwarta in mutum ya sarkafe masu baya ji baya

gani sai Allah da malaman gari indai zakiyi mata addua

to kawai kiyi mata,niko uwar tsoro jin ance zaa bige ni

sai nayi daki da gudu ko mama ban bari taji xancen ba

don bata son tashin hankali kuma Allah ya taimaka ta

kunna rediyo inda tasa kaset na kr2n Alkurani kira ar

sudes,a gurguje muka karya don kar muyi latti muna

cikin sallama da mama kamal ya shigo wai kuyi sauri ko

muwuce inji anty mariya mama ta miko mani naira

hamsin tace gashi sa jikka nace barta mama gafa ta jiya

nan ban kasheba sagir yace meyasa mu ba'a bamu kudin

mama tace ku ai ga kwandonku nan cike da kayan abinci

amma in kun girma zan dinga baku kuma,jamila tace kai

sagir mama tace babu kyau a ba kananan yara kudi yace

wai haka mama? Mama tace e mana nace kai muje kar

ayi ta jiranmu mama sai mun dawo tace to..

haka rayuwa ta cigaba da kasancewa kuma kusan ko

yaushe inada abunyi ban cika zaman banxa ba in bani

makaranta to ina kicin in ranar girkin mama ne don haka

nima babu girkin da ban iyaba na gargajiya ko na zamani

haka nan kuma na kan gyara dakin mama da namu da

falo sannan na kware gun wankin bayi nasa turaren wuta

shiyasa dakinmu kullum yana cikin kamshi da sanyayar

iska mai ddi na kan zauna nida yan kannena in koya

masu kr2 Alkurani da sauran littatafai haka ina taimaka

masu da homework dinsu shiyasa mun fita daban a

gidanmu komi namu tsaf tsaf,a ranar wata sundy lokacin

muna hutun islamiya, hadda ma don muna kusa da fara

azumin watan ramadan da safe misalin karfe goma da

rabi na gama duk wani yan gyare gyare nace da mama

bari na shiga gidansu amira dama nan ne gurin zuwana

tace to ki gaida mmn faruq nace to,na samu Amira tana

faman krtun littafin hausa a falonsu ko sallama ta bata ji

ba sai da na zabga mata uban duka sannan na fizge

littafin na duba sunan shi naga Allura cikin ruwa,nace

kedai kullum kina cikin krtu maman su ta fito na gaisheta

tace mani yasu mama nace tama ce a gaisheki tace ina

amsawa na dube ta nace mama wai baki hana Amira

krtun nan ne?maman su Amira tace nayi nayi taki bari

ynxu ma boyewa take don tasan in na gani yaga shi

nakenace in tana son tayi karance karancenta ta bari sai

ta kai ss sannan ta kijiba sai tayi tayi ba,maman tayi

shiru cikin bacin rai na harari Amira nace kinji ddi mama

ta bata rai saboda ke?mama tace ai ke kina da hankali

ba kamar ita ba ta shige daki Amira ta dubeni tace kinji

ddi kin hada ni da mama nace no Amira in iyayenmu

sunce mu bar abu muyi kokarin bari don gsky zan gaya

maki da ki kijin mgnr iyayenki gara ki bar duniya a guna

kenan tace to naji taja hannuna tace zo muje dakina

nace ke dai Amira baki son fadin gsky muna shiga na

zauna bakin gadon nace mata don Allah Amira kiyi kokari

ki barin krtn nan tun da mama ta baki damar yin krtn in

kinje ss.Amira tace nayi kokarin na bari na kasa ne,nace

ni ko kingani nan ko me mama tace na bari ko da zan

rasa raina ne ba zan bari don bani da tamkarta nai shiru

ina tunani hawaye ya zubo min na dubi Amira nace don

dai iyayenku duka biyun suna nan raye ko ince a tare shi

yasa baki san zaman agolanci ba cikin hawaye ban san

sanda nace.........

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

sunana na gsky shine Amina kuma naci sunan kakata ce

mahaifiyar babana ,babana da mamana yan asalin wudil

ne a wani kauye da ake kira indabo a jihar kano,babana

gidansu sun gaji sarauta don babanshi ne dagacin

kauyen,yanxu haka itako mama yar malamai ce don

babanta shine limamin garin sunan mahaifina idris kuma

shine da na hudu a gurin mahaifinsu yana da yayye yaya

samaila sai yaya musa sai babana idi kamar yadda suke

kiranshi sannan sai kannanshi biyu bala da sani su

shidda ne a dakinsu matan dagaci biyu ne uwargida

Amina mahaifiyarsu babana kenan wadda naci sunanta

sai abokiyar zamanta basira wacce aka bashi sadaqarta

ita kuma yayanta ukku Auwal,salisu sai hindu,suna

matukar zaman lafy ba wani bambanci wannan shiyasa

yayansu hadin kai da son junansu gashi suna ma

mahaifinsu dagaci umar biyayya kuma dukkansu gidan

liman suke daukar krt mama ko a lokacin tana kaduna

gidan yayanta mai suna mal bashir ya dauko ta ne tunda

mahaifiyarsu ta rasu shi babban malami ne a tudun wada

daga yawan almajiranci Allah ya zaunar dashi a inda yayi

auren shi da baba uwa itama dai yar can din ce da yaje

ya auro ta,yana almajiranci a wani zuwa da yayi gida

shine ya tafi da wasu almajirai a cikinsu harda idi

babana kenan domin yayi sauka tuni,zai dora ne su ko

su mama su hudu ne a wurin liman kawu bashiru shine

babba sai kawu Aminu sai kawu kabiru sai mama ita

kadai ce mace tana da shekara tara mahaifiyarsu Allah

yayi mata rasuwa kasancewar ita kadai liman ke aure sai

kawu bashir ya dauko mama dama baba uwa bata taba

haihuwa ba ko ince har ynxu Allah bai bata haihuwa ba

sai ko ta rike mama,shi ko liman isuhu aka bashi sadaqar

mata guda biyu da taimakon baba uwa mama mai suna

habiba ta samu shiga firamare shi ko baba yana nan

yana hadda gidan sai Allah ya hada shi da makocinsu

Alh adamu a dalilin dan gwanjo ne a kasuwar bacci yasa

baba yana rubutu yana kai masa daga nan yace yana

yayi sanaa irin ta gwanjo alh adamu shima dai dan kn ne

ana ce mashi adamu garko duk girinsu daya sai dai shi a

garko yake bayan nemi izinin malaminsa wato kawu

bashir kawu yace tunda kayi sauka hadda kakeyi ba bu

komai ko da rana za ka iya haddar ka Allah ya bada saa

wannan sanaar itace hanyar arzikin mahaifina tun yana

kasawa a bakin titin kasuwar bacci in an kwance dila a

bashi ya kasa har ya koma kwance dilar shima kafin

shekara ukku har ya sayi rumfa kuma yana sayan diloli a

wannan lokacin ne Allah ya ba baba uwa ciki ta haifu da

namiji kuma mama a lokacin ta kammala primary shiko

babana duk da ba a gidan yake ba yanzu yana zuwa da

daddare haddar shi ya sanar da malam kamar yadda

suke kiranshi kawu shi dai habiba yake so mutumcin da

baba yake dashi a idon malam shi yasa har ya amince

koda kauye suka ji wannan zance sunyi murna don akwai

zumunci mai karfi tsakanin gidan dagaci da gidan

liman,kauye aka koma akayi biki sannan su mama da

baba suka dawo shekara biu da aurensu baba yayi kudi

sosai da gwanjo tuni ya gina gidanshi a unguwar sanusi

ga motocin hawa da na haya da ya sai ma mama sannan

ya tallafi yan uwa na kauye hakika yana da halin kanawa

na asali don akwai taimakon na kusa dashi haka ya debo

yayan yan uwa sa daga kauye ya sasu a makaranta dan

yana da haushin rashin bokon da baiyi ba danma

cudanya da mutane yasa ya fara jin dan turancin sa na

yan kasuwa matsalar baba da mama daya shine rashin

haihuwa har wannan lokacin mama ta fishi damuwa shi

ko ko a jikinshi yace Allah baya barci a gefen mama ita

ma tana taimakawa yan uwanta dama tuni daga dagaci

har liman sun keta hazo sannan angyra gidansu tsohuwa

Amina(kakata) sun kaita ita da abokiyar zamanta harda

yayyan babana,su mama dai kowa a kauyen ya gama

zuwa a cikin iyaye da yayye sannan suma suka je ita da

babana.kowa yaje sai ya roka masu Allah ya basu

haihuwa har cikin dangi sun fara korafi gami da nuna

masa ya kara aure ita ko tsohuwa Amina macece mai

nagarta da ibada da yarda da kaddara don haka itace

mai tsawatarwa sauran yan uwanta da kannen alh idi

(wato babana)takan mika lamarinta ga Allah don haka

kullum ma tana yi masu adduar Allah ya basu yaya na

gari masu albarka,shekaru goma da aurensu Mama na da

babana sun dawo ummara ta dawo da jinya mai tsanani

bayan jin jiki da jinyar asibiti sakamako ya fito cewa tana

da ciki fadar farin ciki ma bata baki ne,anan da kanshi

baba yake mata rubutu take sha..... Ku ziyarci blog

dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

Wata tara da 'yan kwanaki ta haifo ni sankaceciyar kowa

ya zo barka sai ya yaba girma da gashina sai dai ni baka

ce tamkar mahaifina tun ina yar jaririyata har yau ban

canzaba, dangin babana na dauko domin gaba dayan yan

uwanmi dangin baba kamar mu daya muna da dan kyau

daidai namu sai anan na dubi Amina nace kin dai ganni

har yau ban canza ba na cigaba da cewa dangi sun

kwararo daga kauye da birni anan naci sunan tsohuwa

Amina, kawar mama kuma makociyarta itace ta ba da

shawarar a kirani da iman,na taso cikin gata da tsantsar

so gun iyayena da yan aikinmu da yayyena wadanda

babanmu yake riko,shekara takwas na halarci makaranta

nursery mai suna salmat intl dake kasuwar santara

market makarantar yayan masu kudi ce don haka krt ba

wasa duk lokacin hutu babana ya kansa a kaini kauye

don yace asali mafari wannan yasa na saba da kakata

Amina da yan uwana 'ya'yan baba lami mata sa'anina

Hassana da Ussaina muna wasa dasu kuma sune suke

kaini ganin dangi a sauran kauyukan,ina matukar son

kauye musamman yanayin damina tayi min a garin

domin muna zuwa gona kakata tana ji dani don haka

nima ina sonta suma dangi kowa na sona kawunnaina da

liman suma ina zuwa in yi masu kwana biyu yau ina nan

gobe ina can gata dai gani nan cikin sai in hutu ya kare

zamu dawo wani sain da kuka nake dawowa a hado mani

tsarabar kauye mai yawa dangin uwa da na uba sannan

mu dawo tare da su yaya Ibrahim da yaya Abubakar,yaya

Abubakar dan baba lami ne shiko yaya Ibrahim dan Baba

Auwal ne(wato dan kishiyar kakata)tun kan a haifeni

suke gidanmu kuma suna makarantar gumi college SS2

don haka tare muke zuwa hutu kauye dasu,kuma muna

kama dasu don duk wanda ya ganmu yasan yan uwa ne

saboda kokarina a kai ta turanni gaba a makaranta

sannan kusan kowanne malami ya sanni don haka ina da

shekaru goma sha daya na kammala primary din tare

kyaututuka masu yawa muna zaman jiran fitowar

sunayenmu ne,na fuskanci matsala ta soma kunnowa

gidanmu in da mama ta tada hankalinta ni ban san dalili

ba amma nasan nasha ganinta tana kuka in nace mama

menene?sai tace idonta ke ciwo kuma koda yaushe

zanga anty yagana kawar mama tana zuwa gidan su

shiga daki da mama suna yan shawarwari,ni bansani ba

wai ashe baba ne zaiyi aure da wata banufiya mai suna

fati kuma ance ma mama bata da mutunci shine hankalin

mama ya tashi tace da baba gsky ya canza mata sai

baba yace karyar mutane ce kawai ya dinga lallashi gami

da ban baki sannan ya kara mata jari har na naira dubu

dari takwas dama tuni ya sai mata motocin bus guda

biyu da babura ana mata haya dasu,anty yagana

makociyarmu ce yar asalin maiduguri ce amma zama ya

kawo yayarta da mijin yar in da suke zaune kurmin mashi

yayarta ce ta aurar da ita ga wanda take so Alh shu'aibu

ma'aikaci ne a water board, tana da yara ukku kusan

tare aka haifemu da yarta ta fari mai suna saudatu,suna

amintaka da mama sosai haka ni da sa'adatu

makarantarmu daya,bayan haifuwarmu ne anty yagana ta

kara haifuwar yara biyu Nurfa da abida,Mama ko shiru

tun daga kaina,anty yagana itace ta ba mama shawarar

su hada jari su soma harkar yan kunnen gwal da jallabiya

da zannuwan gado suna bada sako ta hannun wani

abokin Alh Shuabu ne mai suna Alh Mukhtar Maska

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

Dan zinare ne a kasuwar sheikh Abubakar gumi yana da

shagunan jallabiya da gwala gwalai,shine yake kawo

masu kaya in ya fita dubai harka ta amsu don da an

kawo xaka ga matan manya suna zuwa suna dubawa

suna saya don haka mama ta cire hankalinta daga batun

auren baba,bayan auren amarya Fatima ta tare a dakinta

da farko ta kwantar da kai amma ganin yadda mama ke

facaka da kudi yanda baba ke ji dani sai hankalinta ya

tashi ta shiga tsiro fitintunu iri iri yau tace kaza gobe

tace kaza tasa su yaya Ibrahim da yaya Abubaar a

gaba,a nan mama ta taka mata birki tace kar ta sake ta

takura masu suma gidan ubansu ne in tana jin masifar

tata ta yi da wanda ya ajiye ta bada yara ba,wannan

rigima har gun baba jin bata sami gsky ba shi ne tayi yaji

sai da tayi wata sannan ta dawo,dawowarta shine ya

zama sanadin juya mana baya duk yanda baba yayi sam

baya sauraron mama da farko ban gane ba saida

sunanmu ya fito munci makarantar mu salmat da mama

ta sanar da baba sai yace kar mu dameshi ya gaji da

biyan kudin makaranta,ni ba wani kokari ba shi maimuna

gwarzo zai maida ni na ringa kuka ina rokonshi sai ce

min yayi inyi hakuri shi ya gaji,haka na cigaba da zuwa

islamiya da hadda boko kam ina ganin saudat tuni har ta

shiga SS1 niko ina gida ,anty yagana tace da mama ta

biya mani da ita tana da kudi tace ai ta mashi magana

yace bai yarda ba,wata rana na dawo daga hadda da

rana jugum na samu mama tayi a dole na zauna kusa da

ita na dafa ta nace wai mama baki da lafy ne?tace kaina

ke min ciwo iman,na tashi na nufi gun da muke aje

magunguna na dakko mata panadol na dibo ruwa a kofi

na kawo mata ta amsa tasha sannan tace kije dakin

yayan ki duk wanda kika gani cikinsu kice yazo zan

aikeshi wajen kawunku malam nace nima zanje mama

tace to amma sai kinci abinci ko?nace e nayi sashen su

yaya da gudu,a kofar dakinsu na tsaya nayi sallama yaya

Abubakar shine ya amsa nace in shigo?yace in dai

tsohuwa ce kar na ganta anan(haka su kan tsokane ni

wai tsohuwa)na shiga nace kaine dai tsoho bani ba yace

me yasa zaki sa mana tsufa daki don Allah kije waje

nace naki din aje wajen baka girmeni ba ma zaka ce min

tsohuwa,ya kwashe da dariya yace waneni da girmanki

kece fa kika haifi su kawu da mama da baba anan gidan

haushi ya kamani na hau tsaki irin na shagwaba ina son

inyi kuka nace sai na gaya ma mama na juya zan fita ya

jawo ni zo mana yar kanwata tawan zo mana kiji mama

ta aiko ki guna ne?nace eh tace kazo zata aikemu gidan

kawu malam ya mike ya dungureni shine baki fadi mani

tun dazu ba?ya rike min hannu muka tafi dakin mama

ban san me tace mashi ba na dai ga ta bashi kudi sanna

tace in tafi falo inci abinci kafin ta gama bashi sakon,na

kunna tv na kamo cartoon ntwk ina kallo ina cin abinci

sai naga anty Faty ta fito ni ban ma ganta ba sai gani

nayi an kashe tv din na dube ta nace aunty ina kallon

tom and jerry ne,tace na kashe ko zaki kunna ne?niko

ban san gatse ba sai nace eh cikin masifa tace to zo ki

kunna har ga Allah ni ban san gatse tai min ba sai kawai

na tashi na kunna tv din remote din na hannunta kafin na

juyo sai saukar mari naji dau na yanke da ihu sai ga

mama da gudu ita da yaya Abubakar dama shi akwai shi

da zuciya yace faty me tayi maki,anty faty tace in dole

sai kasan abin da tayi min to ka nemi sani daga gareta

dube ka dan kauye don kazo ka waye shine zaka kawo

mana raini ko?yace naji ni dan kauye ne ke baa ma san

asalin naku kauyan ba,don ba muga yanuwanki ba waya

sani ma ko daga sama kika fado banza yar iska haka

zaki kare a neman asiri,sai tayi kanshi da zagi harda

duka nan da nan ya sharara mata mari gami da ture ta

mama da tuntuni take tsaye tace kai Abubakar wuce

kasai kabar aiken sai anjima,ta nuna ni ke kyma yi daki

na mike sannan na jiyo mama tana cewa kin gani ko faty

wannan shine abinda na jima ina sanar dake ki daina

shige ma yarannan kinki ji to kinga irin.......kan mama ta

karasa sai ta katse mata hanzari da masifa ke munafuka

bake kika sasu ba?to albishirinki yau dinnan zaki san

matsayi na bakinsa Abubakar ya mareni ba?zaku gane

baku da wayo yau,nayi shiru a daki ina kuka mama tace

to ina jiranki da alkhairi anty Faty tace ni kuma da sharri

nake jiranki yau da nai nasarar rava alkhairi da tunanin

wata ya mace haka zan rabaku da gidan nan mama ta

ce to ai Allah ya fiki kuma ba ya barci kuma yana tare

da masu hakuri ta cigaba da cewa ke ko nasan baki san

haka ba tunda kin yi nisa ba zaki taba jin kira ba to sai

muce Allah ya shiga tsakaninmu da ke in kuma mai

shiryuwa ce Allah ya shiryaki,Ku ziyarci blog dinmu

domin karanta Littatafai masu nishadantarwa

Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

ta shigo ta sameni inata faman kuka ta zauna kusa dani

ta jawo ni jikinta tace iman wace adduar kike min,nace

ina rokon Allah yasa ki daina samun matsala da

baba,mama tace ki hada da babanki shima ki dinga yi

mishi ki roki Allah ya kareshi sannan ya raba shi da

dukkan sharri da ake mashi,nace mama wanene yake ma

baba sharri?tace aa mugun abu ai ba sai kasan me maka

zaka roki Allah ba,nace to insha Allahu zan dinga yi

mishi,da dare sai ga dan aiken baba,yaya Ibrahim ne

baba ya aiko wai muzo ni da mama babban falo babu

neman ba'asi ya dauki hannu a gaban mutane ya mari

mama ga yan aiki ga yayyena ga ni ga anty faty bayan

marin ya cigaba da fada wai kar ya kuma jin an taba

mishi mata inko ta kuma marinta ta mari aurenta mama

tana rike da kumatu sai nan tace cewa tayi maka na

mareta?yace to yau kuke me yasa tun da kuke tare bata

ce kin mare ta ba sai yau kuma tace tana son in rama

mata shi yasa mama tace shi kenan ni Allah ya rama

mani ta shige daki,duk da karancin shekaru na sai da

nayi mamakin baba wai ya rama wa anty mari?na juya

na dubi anty sai naga tana wani ciccika tana batsewa

wai an rama mata, na bi mama daki na iske tana kuka na

dafa ta nima na soma kuka ina cewa mama kiyi hakuri

Allah ya saka maki. Anyi haka da kwana biyu na dawo

daga kitso in da yaya Abubakar ya kaini tudun wada na

mari yaya Abubakr din da wasa don ya dameni da

tsokana tun a mota wai tsohuwa mai dan koko Allah

kashe ki musha gumba,nayi banza dashi sai da ya tsaida

mota sannan na dan kai mashi marin wasa kadan na

bude motar nayi cikin gida da gudu,yace ni kika mara?sai

na rama shima ya fito yana dariya ya biyoni yana kirana

nayi falo da gudu ina cewa so kake in tsaya ka rama ban

kula ba na bude labulen falon na fada sai kawai naji na

bige mutum lokaci guda kuma naji anyi jifa dani ashe

nayi karo da anty faty ne shine ta jefar dani kuma ta

biyoni da duka takeyi yaya da har ya juya da yaga na

shige falo sai kuma yaji kukana nan da nan ya dawo ya

iske anty nata faman dukana cikin zafin rai yake ma anty

magana yace don Allah me yarinyar nan ta yi maki kike

dukanta haka?yanzun nan fa muka shigo?ta juyo kanshi

da zagi da gori,jin hayaniga shi yasa mama ta fito ta

dubeni ta dubi yaya sannan tace Abubakr ba zaku daina

daukar min magana ba ko?yaya yace wllh mama bamuyi

mata komi ba niko sai faman kuka nake ita ko anty faty

sai zage zagenta takeyi jin mama bata kula ta ba sai

kawai ta shaki kwalar rigar mama tana cewa yau din nan

na tsara zaki bar gidan nan duk na cinki miji ya

wulakanta ki amma don bakin naci kin dage kin ki tafiya

ko,ta cigaba da cewa to yau din nan za'a kama kai a

koma wurin mai dattin hula,yaya ya fincike hannunta a

wuyan mama sannan ya daura mata mari yace marar

mutunci yar dangin jaraba rigima dai ta ki karewa har

yamma sai da tayi ma babana aike har kasuwa wai yazo

nan da nan sai gashi lokacin ma kowa ya kama gabanshi

yaya Abubkr bai ma nan ni kuma ina daki mama tana

koya mani karatu sai ganin baba mukayi ya shigo ko

sallama babu ya jawo ni a gaban mama ya hau duka da

wayar wuta ina ta ihu gami da neman taimaki amma ina

mama ko kallo ban isheta ba sai da ya gaji sannan ya

barni don kanshi,sannan ya dubi mam yace ke kuma in

tambayrki?mama ta dubeshi ba tare da tayi magana ba

yace dake muka hada muka sayi gidan nan?mama tayi

shiru yace ba dake nake magana ba mama tace ai ina

jinka yace to ina son daga yau na sakeki saki daya

sannan na barki minti goma ki barmin gidana.....Ku

ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

Duk da nike karama ina jin ya ambaci saki sai na kara

yanka ihu itako mama duk da dauriya da tayi don kar tayi

kuka ace gabana sai da kuka na ya sata hawaye koda

mama ta gama kimtsa kayan ta ta fito falo zata tafi na

biyo ta da gudu ina kuka babana yana zaune yana cin

abinci da bai tanka ba sai da anty tayi mashi wata

magana sai yace da mama ki tafi da yarki in kinji

shawarata don ni ynxu nafi son yaya maza daga tsatson

faty ga mamakina sai naji mama tace to Allah ya baku

sannan na gode da shawara amma ko mun tafi da iman

ai kanan nan a matsayin ubanta ko?maimakon yayi

magana sai kawai ya kalli anty faty komi tace mashi oho

sai ya juyo ya kalli mama yace kuje dai sai yanda hali

yayi idan nine ubanta to na aiko maki amma fa gunki

zata ci gaba da zama ba ba tare da mam tayi magana ba

ta jani ko takalmi babu mukayi waje,wannan fita da

mukayi itace fita ta karshe daga gidan babana mahaifi

kuma har yau ban kuma zuwa ba ban kuma ganin

babana ba ko anty fati ba. Muka koma gidan kawuna

marikin mamana daki guda kato bayan sati biyu babana

ya aiko ma mama da dukkan kayanta haka mama ta

cigaba da zaman iddarta har ta gama, itace tayi mani

komi na shiga SS1 a makarantarmu wato salma,ina jin

dadin zama da baba uwa wato matar kawuna suna da

yay biyar yaya suleiman shine babba sai yaya nura,anty

rukayya ke binshi sannan sai nana itace sa'ata sai

karamin su mai sunan kakanmu liman ake kiranshi don

sunan liman din yaci wato isuhu,nana maimuna gwarO

take itama js1,yaya suleiman tela ne kuma yana zuwa

poly ko da yake san da muke a maigidansu saura yan

kwanaki ya gama shi ko yaya ustaz ne don yanzu haka

ya na koyarwa a wata islamiya nan kusa da

gidansu,sannan shima zuwa tashi wato sanawiyya a

unguwar ma'azu,anty rukayya kuma tana aure ne a

badarawa yaya suleiman yana debe mani kewar su yaya

Abubakar don shima yana tsokanata kasancewar mu

abokan wasa ne ya kance mani matar ni kuma ince

mashi ya mani tsufa bana sonshi yaya nura baida faraa

shiya sa nima ban cika kulashi ba,Ku ziyarci blog dinmu

domin karanta Littatafai masu nishadantarwa

Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

wata rana ina zaune daki sai mama ta shigo lokacin

kuma gab da babbar sallah ne mama tace iman shirya

muje kasuwa nace to dama na riga nayi wanka sai kawai

na dauki hijabina mai less a kasanshi nasa takalmina

nace mama na shirya muka nufi kasuwa,bayan mama ta

gama mana yan saye sayenmu nida nana sai tace muje

wajen yan zinari zata sai wani nace to muka je shagon

shi makare da gwala gwalai kala kala da fara'arshi ya

tari mama,naji yana cewa haj Habiba sai yau kikazo

kasuwa?mama tace wllh ko Alh mukhtar maska inafa son

nazo amma ban samu lokaci bane sai yau ya turo mana

kujera yace mu zauna ya nunani yace wannan yarki ce

ko?mama tace aa yace ke yarta ce ko yan mata?nayi

murmushi yace ga murmushin nan irin naki ke ya

sunanki?nace sunana iman yace suna mai dadi,sannan

ya juya gun mama yace kin sami sakona a gun yagana?

don tazo shekaranjiya ta kawo wasu karyayyun yan

kunne,mama tace bamu hadu ba gsky mun dai rabu akan

zata zo nan din yace sakona bai isa ba kenan?mama

tace eh sai ya dubeta ya ce zaki samu ganina zuwa

yaushe?sai nazo gidan naku,mama tace lafy dai ko?yace

sai alheri mama tace to ko yaushe kaxo zaka sameni sai

dai da safe ina zuwa islamiya yace ba matsala zan shigo

tudun wadan yanzu me kike so?mama tace ina son in

saima Iman dubai ne kasan da na daukar mata a cikin

kayan da ka kawo mana wancan sati ukkun da suka

wuce to sai na ga kuma sun mata girma sai naba yagana

tace kace mata sai bayan sallah shine nace bari nazo

gunka ko zan samu wani,yace ba zaa rasa ba in kuma

kinga ba wanda yayi miki to ki sai mata saudiyya mama

ta zabar kirar dubai na wajen dubu tamanin har da abin

hannu guda biyu yace gasky kina ji da wannan yar taki

mama tace kai maska don na sai mata yan kunne?yana

dariya yace sai nazo zan amshi kudin mam tace a'ah ga

dubu hamsin nan bansan zan sami masu tsada haka ba

mukayi sallama ya bani dubu daya yan hamsin hamsin a

cikin kudin nayi godiya muka tafi,bani manta ana jajibir

sallah Alh mukhtar maska yazo gun mama ni dai na

dawo daga kitson sallah nida Nana na iske bako a dakin

yaya suleiman da zai tafi mama ta shigo tace naje na

gaida shi don yana ta faman magana in na shigo nazo

mu gaisa,na zauna a kasa dashi na gaishe ahi yace kin

dawo muga kitson na nuna mishi yace iyye yayi kyau

sosai yasa hannu a cikin aljihun shi ya dauko kudi

sababbi yan naira ashirin bandir daya yace ga goron

sallah don kilan ba zaki ganni ba naki karba nace ka

barshi muna musu mama ta shigo jin musun da mu ke

ne tace sunyi yawa ne alhaji ka rage yaki dole na amsa

nayi godiya.Amira wacce tayi shiru tun da na soma

magana kamar ruwa ya cita sai da nayi shiru sannan

tace gsky iman ke yar gata ce to amma sai nan gaba

zaki sani in Allah ya kawo karshen muguwar matar

babanki,nace Allah yasa,Amira ta gyara zama sannan

tace anty faty matar babanki ta haihu?nace kai har

yanzu Allah bai basu ba tace to ina yayyenki Abubakar

da Ibrahim kuma?yanzu basa zuwa nan?nayi murmushi

nace kin cika tambaya Amira zaki yi kyau da yar aikin da

nake ra'ayi wato yar jarida Amira ta basar da abunda

nace tace baki amsa mani ba nace basu san nan gidan

ba don kwanaki baba uwa tace masu mama tayi aure,sai

kuma ta kuma cewa to ina yayansu mami abdul wa ma

kika ce mani?nace abdulrahim sunanshi mami tace yana

england shi dan wasan kwallo ne nima ban sanshi ba

amma ya sha masu aike nima na gani,shi kuma kabir

aikinsa shi dai amira tace haba nasan shi mana ba shi

ne yake karatu a kano ba,tace ai shi naga ba ruwanshi

don naga yana maki wasa nace gsky shi kam ba ruwan

shi ko zai zo hutune ya kanzo da yar tsaraba su sweet

biskit da yan kayan lashe lashe ya ba kannenshi tonima

yanda ya basu haka yake bani don haka nima nake

sonshi a raina ganin shi nake kamar yaya abubakar duk

da bai tsokanata irin na yaya abubakar din amma kinga

yayan nasu da ke waje ina tsoron ranar da zai dawo,ta

dube ni don mi kika ce haka?nace don ina jin yanda suke

lbr shi wai ya cika masifa ga duka sannan nasha jin

yanda suke bada lbr irin son da yake ma hajiya

yaya,sunce yana son mamarsa kamar ransa don bai hada

ta da kowa ba yanda mami take bada lbr sai kinyi

mamaki sosai abin kamar ba gaske ba to kuwa ai kinsan

dole ne ya kuma ki duk abunda taki gami da tsanar shi

tunda sunce komi tace mashi yayi,don haka ina jin ance

yau zai dawo zan hada ya nawa yanawa na kama gabana

na koma can gidan kawu na malam,Amira ta dinga man

dariya wai na cika shegen tsoro nace ai ke dariya ma

nabaki?lallai Amira, tana dariya tace dole ne nai maki

dariya ma naga dai komai son uwar shi sai kin mata abu

sannan zata sanar dashi sannan in baki sani ba su maza

ba yawancinsu basu da daukar zance na tsegumi haka

wannan sai mata sai ko sakaran namiji ina jin wannan ba

zai maki haka ba don shi dan boko ne nayi shiru ina

nazarin maganarta can nace wannan gasky ne to Allah

yasa dai kar ya kulani,Amira tace amin,mun kaure

munata zuba lbr sai kawai ganin yaya Ahmed mukayi

nace a'a yayanmu ustazi ba sallama ne?yace ku dai

bakujin sallamar to mama tace a tashi ayi sallah dama

masallaci zani,yasa kai ya yi waje na mike nace bari na

wuce gida kawai,Amira tace ai baki isa ba sai kinyi

sallah kinci abinci sannan zaki bar gidan nan,na kwace

daga riko da tai min nayi waje ina dariya nace yaushe

rabon da ki shigo gidanmu,ta biyo tana kira na gudu

gashi nayi sa'a mamansu tana daki tana sallah a

gidanmu ma mamanmu sallah na sameta tanayinima sai

na shige dakinmu naga jamila tana barci na tashe ta

muka yi alwala muna idar da sallah nima na kishingide.

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

DOCUMENT CREATED BY

ZAHARADDEEN SHOMAR

WHATSAPP ,08168575100Tawa Tasameni1-02

Posted by ANaM Dorayi on 01:20 AM, 20-Dec-15

Under: TAWA TASAMENI

TAWA TA SAMENI

NA

HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

Ranar lahdi da daddare sai gasu yaya abubakr sunzo

nan muka sha fira, ynxu anty faty ta gama mallake

babana sai abinda tace gashi har ynxu Allah bai basu

haifuwa ba sai karyar bari,na tausaya ma mahaifina

kuma na yi alkawarin sa shi a addua insha Allahu zan

kuma roki mama ta barni inje na gaida kakata in munyi

hutu mun jima dasu sannan sukayi sallama damu suka

tafii,muna shirye shiryen soma jarabawa zango na ukku

don shiga SS2 aka yaye mu a islamiya inda mukayi

walima a gidansu Amira duk gidanmu ni kadai nayi

sauka mami kuma sai shekara mai zuwa don tayi wasa

da karatun mama da maman su Amira harda Anty

yagana duk sun mana bige bigen abubuwa irin su

kalanda da robobi,hankici da sauransu,da zamuyi rabon

katin walimar har su yaya Abubkr sai dana bawa Amira

nayi mata kwatancen taje takai masu kuma sunxo mani

da kyautututukan su inda suka bani waya a kwalinta

wai inji babana na amsa cikin fargaba na kai dakin

kwananmu na boye shima yaya Sulaiman yazo kuma

shine ya dinko mana kayan da muka sa ranar walima

nashi gudummuwar kenan wata shadda ce galila mai

kyau da hijabai. Sai da komai ya natsa sannan na

dauko wayar dasu yaya suka bani na kai ma mama na

mika mata leda ta amsa ta gami da tambayar menene

a ciki?nace su yaya Abubkr ne suka kawo wai inji

babana na fada mata cikin tsoro,ta saki ledar daga

tsaye tace ke kuma ki ka amsa to ko menene ma a ciki

zan maida musu ni,haka kuwa akayi ta kira yaya

Abubkr a waya ta bashi gami da yi mishi gargadin karta

kuma ganin wani sako daga babana da sunan wai nawa

ne tun daga nan suma su yaya Abubkr din ta daina

sakar masu fuska.mun shiga SS2 cikin sa'a da nasara

ranar wata jumaa mun tashi daga makaranata na tsaya

ina amsar sakon wani littafi da zan amsar ma Amira

gun wata yar ajinmu Hauwa aminu don yanxu in tana

karantawa nakan zauna ta bani lbr ko ta karanta mani

na amsa na isa gurin da Musa yake tsayawa wato

direbanmu ban sameshi ba na tsaya nayi sororo can na

hango wata yar ajinsu mami don yanxu ba aji daya

muke dasu ba ni ina A su suna C na isa gunta sai na

tambayeta ko taga su Sa'a?don mami bata zo ba tace

mani sun tafi abinsu nayi shiru na kuma ce mata motar

tazo?tace ba bus din gidanku ba?na daga kai tace to

sun dade da tfy,sai da nayi nisa a tfy kasa sannan wani

tunani yaxo mani na tsaida mashin na hau sai da muka

zo har kofar gate din mu sannan nace bari na shiga na

amso maka kudinka ina shiga harabar gidanmu naga

matasan layinmu sun cika a kofar dakin yaya Kabir har

da wadanda ban taba ganinsu a layinmu ba,nace a

raina ko yaya Kabir ya dawo ne?don ynxu yana bautar

kasa ce a Bayelsa na shiga gida na sanar da mama

abinda ya faru tace to a nawa ya kawoki?nace 40,ta

bani 50na kai mashi a hanyar dawowa cikin gida ne

nayi karo da Anty Hadiza dasu Anty Mariya suna dauke

da manyan tururuka da kuloli a kai,Bilkisu kuma tana

dauke da dauke da plates da cokula ga wani kwando

mai dauke da kayan shaye shaye na dube au na kauce

a hanya,amma duk da haka sai da anty Mariya ta daka

min tsawa ke akuya ban hanya,na matsa musu suka

wuce,na shiga ina mamakin wane bako ne yaxo ake

mashi hidima haka?bayan naci abinci nayi wanka nayi

sallah na shirya cikin riga da siket yan kanti ina zaune

a tsakar daki ina yin note sai ga mami da gudu ta shigo

tana kwala min kira iman! iman!!na tashi da sauri ina

fadin gani nan nace menene?don duk na tsorata sai

tace min ki tayamu murna yayanmu ne ya dawo ya

bamu waya nayi ajiyar zucya na dungure mata kai nace

har kinsa duk na tsorata na amshi wayar kirar nokia yar

karama mai murfi gsky ta burgeni sosai nayi mata

murna tace su dasu Sa'a iri daya ya sai masu don

dama ya sai ma su anty Mariya tun tuni,nace kunji

dadin wllh tace muje ku gaisa mana ko zai baki kema

na dube ta cikin sauri nace ki rufa mani asiri ai ni ynxu

ba zan taba yarda ya ganni ba bare da hankalin kaina

naje inda yake ta soma dariya gami da fadin kin fiye

tsoro me zaiyi maki?daga ganinki sai ya hau dukanki

sai kace mahaukaci?tacigaba da dariya na ture littafin

gabana na dube ta nace don Allah ki sanar dani wani

abu game da yayanmu mana, Tace Abdulrahim

sunanshi na gasky wato Abdulrahim mukhtar maska a

yanda naji ana cewa tun yana dan karamin shi sam

baida yawan fara'a ga miskilanci don zai iya kwana bai

damu da yayi ma wani magana ba in ana son aga

fara'arshi to a bashi kwallo sannan kwallonshi ta samo

asali ne tun yana makarantar primary inda yayi ta cin

gasar da aka sha hada su da wasu makarantun,haka

yacigaba har secondary,bayan kammala yaso a barshi

yaci gaba da kwallonshi amma sai babanmu ya kiya

sam dole yaje ABU zaria inda ya karanci politics har ya

samu degree bayan ya gama sai ya shawo kan

babanmu da kyar yayi wasanni da dama a nan gida

nigeria kafin ya fita england inda wani coach yayi mishi

hanya,

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

Na dakatar da ita nace ke ni ban tambayeki lbr kwallo

ba,kunce yana dukanku ko?mami tace Allah yana duka

sosai ma,amma sai ka mashi ba daidaiba,na dubeta

nace kamar yaya ba daidaiba?tace baya son ya saka

abu kaki ko kai shirme,bai son kazanta kuma in ka

ganshi yana son ka gaisheshi amma baison yawan

gaisuwa ,kana ce mashi ina kwana is ok,yana da cin

abinci kinsan yan kwallo gashi da tsafta yana son

kamshi ke gadai abubuwa nan,in har kin kiyaye komai

babu abinda zai faru tsakaninku ko ynxu ki tashi muje

ki gaishe shi mana,nace a'a mami gaisa wata rana

nace to ynxu ya dawo kenan?tace aah bai dawo ba

kenan,zai koma wannan zuwan ma in gaya maki haj

yaya ce ta matsa yazo don su gana da yar gidan haj

laure,anty mimi nace ita zai aura kenan?mami tace

kuma abinda baki sani ba yana matukar bin maganar

iyayenshi don ko wuta suka ce ya shiga zai iya shiga

musamman haj yaya bai hada ta da kowa ba yana

matukar jin maganarta,na dube ta cikin tsoro nace kinji

ko?tana ce mishi ya koreni zai koreni ko dai ma in tafi

ne?mami sai dariya take yi min,Kamal ne ya shigo ya

sanar da mami mamansu na kiranta.Bayan kwana biyu

ya raba tsaraba har su jamila da sagir ya basu,mama

ma ta samu less da shadda da takalmi sagir din ma

harda Jc shi da kamal,su mami english wax ya kawo

masu ni dai banje ba kuma bai sani dani ba don ban

yarda ya gani ba,ran da ya yi kwana ukku da dawowa

mama ta amshi girki da rana ina tayata aikin burabisko

mami ta same mu a kicin tace yaya yace a kai mishi

abinci,nace yana cin birabisko ne?tace oho nace to

inbazaki laifi ba kije ki ce mishi burabosko ne don kar a

yi mishi laifi,tayi musrmushi sannan ta fita,anty yagana

tayi sallama ta shigo na fito daga kicin na amsa,sannan

na gaisheta gami da tambsyarta saudat tace tana gida

sannan ta wuce ciki tana ce min maman naki na ciki?

nace eh,mami ta dawo tace yace akai ma abokanshi

shi kuma a dafa mashi indomie amma ke zaki dafa ko?

tace eh nace to don kar inyi kuskure mami tayi dariya

tace kai ke kam kin cika tsoro,sababin kuloli mama ta

bani na zuba masu birabisko da miyar kaji yaji curry sai

kamshi yake,na dauka na tafi nayi sallama a kofar

dakinshi aka amsa mani cikin faduwar gaba na shiga

nace sannunku mutum uku suka amsa kaina a kasa ban

kalli kowa ba nace a ina zan ajiye?cikin dauriya nake

magana gabana sai faduwa yake wani daga cikinsu

yace maska tana magana,da sauri na dan dubi wanda

aka kira maska yana ta faman danne danne waya

tamkar ba dashi ake magana ba,dayan yace ke ajiye

kan wancan table din,na dubi table din sai naga akai

yayanmu ya dora kafarshi ,na dubi mai maganar nace ai

yasa kafa a kai yayi murmuahi sannan yace ajiye ko

ina kinsan halin yayan naku sai hakuri na ajiye a

gabansa don mami tace dama su ne zasu ci na juya

zan tafi sai naji murya mai sanyi amma cikin fada

akace ke haka ake bada abinci a gidanku ko?na juyo da

sauri ga mamakina yana danne danne wayarshi kamar

yanda na sameshi,sai a lokacin ne ma na dan kalli

fuskarshi, kykkyawa ne na ban mamaki don duk gidan

yafisu kyau sak kamarshi daya da hajiya yaya,tsawa

naji in ba zaki zuba musu ba dauki ki tafi,da sauri na

duka jikina na kyarma na zuba musu nan dakin ya bude

da kamshin miyar kajin na mika wa kowa sannan na

mike dayan yace dan bamu ruwa nace to zan fita

dayan kuma yace ga fridge nan na nufi gun fridge ina

tunanin yanda zan bude dan ban taba ganin irinshi ba

cikin sa'a ina dafa shi sa i naji na latsa wani abu sai ko

ya bude kayan shaye shaye ne kala kala na rasa

wanda zan dauko musu sai na dauko musu ruwa a

babban gora na dauko five alive na aje masu da na

duba saman fridge din sai naga kofuna irin na wajen na

dauko tiran kofunan gaba daya na aje a gabansu,ina

kokarin mikewa ne mami tayi sallama suka amsa har

da yayanmu ta shigo dauke da kula da plate da cokali

na fita na dan tsaya a kofar dakin ina jiran mami

labarin abinda yayanmu yayi mani sai na jiyo itama

tana shan nata fadan,muryar yayanmu ne yana ce mata

yar iska haka ake dafa abinci?indomie ne din ba za ki

iya dafawa ba?ina cewa ganin kin danfi su mariya abin

kirki ashe kema useless ce,sam ban ga wani amfani ba

gun mace matsawar bata iya abinci ba,ko aure kukayi

irin abinda da zakuyi kenan ko?sai naji muryar wani

acikin abokan yaya yana cewa to kayi hakuri mana

maska,ai yara ne sai naji muryar yayanmu din yana

cewa no.......

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

Nasir kar ka goyi bayan wadannan yaran sam basu iya

komai na mata basu iya girki ba basu iya gyaran daki

ba,sam basu iya komai na mata ba yan iska sai dare

yayi ka gasu suna surutu da samari sannan ace masu

yara?yaci gaba da cewa bari kiji ba za'a yi asarar

wannan abincin ba maza ki dauka kije ki cinye shi ina

nan shigowa har dakinku inci ubanki in baki cinye shi

ba ina nan yanda kuka sanni ban canza ba fita useless

kawai,nan mami ta same ni a kofar daki duk na kara

firgicewa na dubi mami wadda ke zubda hawaye nace

mami yanzu ya zakiyi da wannan uwar taliyar don

Allah?tace zo muje sai da muka isa gun lungun shiga

cikin gida sannan ta dubeni tace don Allah iman ci

wannanabincin kiji nasa hannu na dandana daidai kam

yayi sai dai da ta dam kara wasu abu zai danfi wannan

dadi,nace yayi mana tace to kinji shiyasa ni sam bana

son ya sani wani aiki ga tozartani a gaban abokanshi

nace to ki kai ma masu wanke wanke su tafi dashi gida

mana tace wai in kaiwa su lami masu aiki?nace eh

tace baki san yayanmu bba kenan kar kiyi fata irin haka

ta hada ku kuma duk matar da ta aureshi ta shiga

uku,nace anty mimi zatayi fama muka wuce cikin gida

bansan yanda mami ta kare ba,sai washegari a school

take ce min zubar da rabi tayi ya sameta tana cin

rabin.Washe gari gab da magriba na dawo daga

islamiya da shike ina zuwa sanawiyya na shigo

gida,zaune a kofar dakin yayanmu samari ne su hudu

sai shi yayanmu yana tsaye yana daddana waya,nadan

yi mamakin yanda baya gajiya da danne danne waya

ban taba ganinshi ba waya ba kuma ko da yaushe cikin

danna ta yake tun daga nesa nake kallonshi sanye

yake da dogon wando da riga daga nesa nake kallonshi

sanye yake da dogon wando da riga mai gajeran hannu

masu ruwan bula da ratsin fari an rubuta adidas a

jikinsu,gsky yafi yan gidanmu kyau,maza da mata dogo

ne yana da dan fadin ga kwarjini gashin kanshi a

nannade ina tsammanin yana sanya mai ne akan ko

kuma haka gashin nashi yake?oho ban san dalili ba duk

sanda na ganshi sai gabana yayi wani mugun faduwa

bana raba daya biyu don ina jin tsoronshi ne,na iso daf

dasu kanshi a duke yana danna waya amma sai naji

yace ke in kin shiga kice Sa'a ko Bilki su kawo mana

butoci,to ba ma magana dasu Sa'a ko ince basa min

magana kuma ban ga mami ba sai naje dakinmu na

dauko butoci guda biyu na kai masu shi baya gun ina

zaton bayinshi na daki zaiyi sagir na tura sagir ya

kwaso mana butocin,wata rana asabar zan tafi

islamoya don yanzu bana jiran kowa a yan gidanmu dan

ba lokaci daya muke karatu dasu ba sai dai na biya wa

Amira mu tafi,sanye nake da hijab har kasa nasa safa

da nikab yayanmu na gani yana kulle dakinshi sanye

yake da gajeren wando da yar rigar nike kafarshi da

safa da takalmi but na kwallo da alama zai motsa jiki

ne,nazo zan wuce ya dan dubeni ina jin yana son ya

gane kowacece kamar na gaishe ahi sai kuma na fasa

ina zaton bai gane ni ba,na gota shi kadan sai ya juyo

yace ke gabana ya fadi dama cikin faduwar gaba

nike,na dawo kaina a kasa nace gani baiyi magana ba

ya gama rufe dakin ya matso gab da ni sannan yasa

hannu ya dage nikab din idona ya firfito don tsoro yace

ooh na dauka mami ce,ya cigaba da magana fuskarshi

a daure ke na lura sam baki gaida mutane ko?na dan

saci kallonshi fuskata yake kallo na kali kasa sannan

nace ina kwana?yace wuce bani so sai da na roka

kenan dubeta ,a raina nace masifaffe kar ka amsa din

na tafi abina.

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

Zama da Amira yasa yau da gobe nima na soma

karanta littafi kuma sai da na tambayi mama tace

amma na dinga karanta masu kyau kuma masu amfani

sannan in har zan karanta to ya zama bani da aiki ko

na makaranta ko na gida shi yasa ma nafi yin karatun

da daddare kasancewar bana fita ko ina ko samari

sunzo kirana mama bata matsa mani ba don tace in kr2

nake son nayi to na tsayar da hankalina gun

karatun.Yau monday muna hutun easter bani da wani

aiki duk na gama kwance nake bisa gadona ina karanta

wani littafi mai suna auren kisan wuta ina jin dadin lbr

banji sallamar mami ba sai dai naji an fisgw littafin

daga hannuna cikin sauri na tashi tana dariya tace kai

iman,ke dai kina krt nan baki jin komi,nace lbr ya

hadu,tace hala na soyayya ne?nace eh tace ai na sani

nace kin san me?ai ku ne kuke soyayya ni kin ganni da

saurayi ne?naci gaba da cewa wallahi ni banma yarda

akwai wata soyayya da kuke cewa ba,mami ta soma

dariya tace lallai yarinya da sauranki ke da kike karanta

littatafai ai ke zaki ba wani lbr yadda ake soyayya,nace

suma duk jinsu nake sai kiji an ce wai tana tuna shi

tana mafarkinahi,don Allah da gaske ne?mami tace aa

karya ne randa baku iya nutso a cikin soyayya ba ba

zan yi magana ta katse ni da cewa ke ni ba wannan ya

kawo ni ba an sa ranar su a anty Mariya wannan

Alhajin kin ganeahi?nace mai katon cikin nan?tace eh

shi ita kuma Hadiza wannan Sanusin mai jar motar

nan,nace na ganeahi wanda ya taba cewa na kirata,don

ya bata kudi ta bani shine ake cewa kar na kuma

gaishe da saurayinta,don mu duk wanda ya dafe mana

ya dafe mana kenan mami tayi dariya tace to shi. Yaya

a

Abubakr yana zuwa gidanmu haka yaya ibrahim

dukkansu suna min hidima sannan yaya Sulaiman

shima yana zuwa sai dukkansu sun daina shiga wurin

mama sai dai su gaishe ta waya,wani abin mamaki

kuma yaya Abubakar shi kadai yake zuwa haka ma

yaya Ibrahim din duk babu wanda ya taba min maganar

soyayya ina ganin take takensu kuma bana jin zan iya

amince ma dayansu.

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

Yaya Kabir ya gama bautar kasarshi ya dawo gida,to

shi dama muna shiri dashi rannan na fita da safe zani

shagon mal Sani dan sayan sabulu naga yaya Kabir

yana tahowa daga bakin kasuwa na jira ya iso nace kai

kam ka cika yawo daga ina? Na duba wani abokin bab

can da bashi da lfy nace ko Alhaji isa naji mami tana

maganar zuwa duboshi yace yea shi ne,muka jero

muna tfy har gida na tsaya daidai kofar dakinshi zai

bani kwanukan dana kawo mishi abinci da daddare ya

fito dasu kenan yayanmu shima ya fito daga dakinshi

cikin sauri na gaisheshi sau daya wato ina kwana yace

lafiya dama shi gaisuwarshi bata wuce haka in ma ka

kara to ba zai amsa ba na amshi na wuce sai naji

yayanmu na cewa kice mami tazo tayi mani shara kan

nayi magana sai yaya Kabir ya riga ni yace ai yaya

Abdulrahim dama wannan din kasa da kafi ganin daidai

dan ta kware yacw to gashi in kin gama ki rufe mani

dakin kiba brother key din,nasa hannu biyu na karba

gami da cewa a dawo lfy bai amsa ba yayi gaba,na dubi

yaya Kabir nace don Allah shi yayanmu baya amsa

gaisuwa ne?Kabir yace yayanmu kenan ai shi daban ne

duk yanda kika so ki san halinshi ba zaki iya ba mutum

ne mai ban alajabi na wuce ina dariya,na sanar da

mama aikin da yayanmu ya sani tace to na bar wankan

naje na gyara mishi dakin zatayi ma su jamila in na

dawo sai nayi nima nace to na shiga dakin yayanmu sai

yau na yima dakin kallon tsaf,leather sit ne kujerun shi

bakake ne masu girma setinau sai kayan wuta kafet da

labulaye jajaye dakin sai kamshi yak nan na soma da

bedroom din katuwar katifa irin wadda ba asa ta a gado

din nan ce sai hanga na kayan sakawa a saman hangar

akwatuna ne saiti biyu na dubi hangar rataye da kaya

jibge a kan katifar ma duk kaya ne dai dai ko ina

kwashe masu datti nayi a cikin wani dogon kwando irin

na zuba kayan na gyara uwar daki tsaf sannan na koma

falo shima nayi mishi aiki sosai na goge electronics din

komai yayi tsaf sannan na dauko turaren daki na feshe

ko ina na kulle dakin,na kaima kabir,wanan shine silar

fara sani aikinshi na zama mai gyara mishi daki har ya

zama dayan key din dakin ma a hannuna yake kullum

da safe sai na gyara nake tafy makaranta wata ranar

laraba na isa dakin da sauri dan in gyara na tura naga

dakin ya bude a raina nace yau yayanmu bai je training

bane?na shiga ban ganshi ba na cire hijabina na ninke

na ajiye a saman kujera kaina tsaye na shige uwar

dakin kayan barci ne a jikina doguwar riga da

wando,sam ban san yana bedroom ba na shige toilet na

gyara tsaf na fito bedroom din sai a lokacin na kula da

mutum kudundune cikin bargo nayi sauri na duba kan

gado dan na tabbatar yayanmu ne a kwance,ya

kudundune da sauri na juya zan fita sai naji yace zo

nan muryarshi irin ta marassa lfy nazo na dan duko

yacw ki dafa mani ruwan lipton nace to na fita zuwa

dakinmu mama na samu tacw har kin gama?nace ban

ma gyara ba don yana nan ne yace akawo mashi ruwan

lipton inaga bashi da lfy ne,mama tace ga wannan dibar

mashi a ciki na baban sagir ne da yasa na dafa mashi

dan yana fama da mura sai dai nasa kayan

kamshi,nace zaisha ai yana shan na gida kuma yana

sawa na diba na kaimashi na rusuna na bashi da kyar

ya mike ya zauna akan gadon ya amsa duk naji banji

dadi ba nace yayanmu baka da lfy ne?yace eh nace

sannu,haka na koma naci gaba da gyaran falon har na

gama na kara lekowa nace sannu na gama ko za'a

kawo maka wani abu ne?yace ki shiga ki sanar da

hajiyata sannan in ba zakiyi latti ba to ki dafa min

indomie nace to cikin mintuna da basu fi biyar ba na

dafa mishi hadaddiyar indomie na kai mishi....

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

Afalo na sameshi zaune kan doguwar kujera yana

sanye da singilet da gajeran wando naja dan karamin

table din glass din dake tsakar dakin na dora cooler fin

a kai na zuba mishi a cikin plste nasa cokali nace a

baka ruwa?ya girgiza kai a raina nace yau dai ba danne

dannen waya ba tare da ya dubeni yace kin fada ma

hajiyata din ne?nace bata bude kofa ba,yace bani waya

a cikin bedroom na shiga na wayar na kan katifarshi na

dauko na duba fuskar wayar gabana yayi wani

mummunan faduwa sakamakon ganin hoton anty mimi

a fuskar wayar na kai mishi sa帽an nace bari na gyara

cikin,na shiga na gyara na fito yana cin abinci yace

bani abinsha a fridge na bude coke na gwangwani na

dauko mishi dan ina yawan ganin gwangwanayen coke

din a cikin bolarshi na hado mishi da ruwan Cway na

aje na wuce ban wani karya ba shiryawa nayi kawai

nasha ruwan tea kadan don kar mama tayi min magana

na fito su mami sun jima da shiryawa shi yasa ma ban

tsaya saka safa ba,haj yaya mukayi karo da ita ta dawo

daga dakin yayanmu ta dubi bilkisu tace yayanku bashi

da lafiya ku shiga ku gaishe ahi keda saa da mami

sukace to sun shiga ni kuma na tsaya daga waje ko

yaya akayi ya ganni sai ji nayi yace ba zaki shigo bane

ke? Na shiga da sallama na ce sannu bai amsa mani ba

ya cigaba da cewa in kin dawo makaranta ki dafa mani

wani abu ,karfe nawa kuke dawowa?nace biyu yace to

zan je na ga likitane sai ki samar mani wani abu nace

nace me zaa dafa yace komai ma,muka fito su bilkisu

sai wai hararata suke yi ni ko tausayin halin da yake

ciki shi ya dameni ko a mota sam na kasa sakewa duk

tunanina yana can gunshi sai kuma abin da yafi tsaya

mani a rai hoton anty mimi dake cikin wayar yayanmu

tana sanye da jar riga kanta ba dankwali tana ta faman

murmushi duk sanda na tino sai gabana ya fadi a ranar

sukuku na yini ko yan ajinmu sai da suka tambayeni

nace banjin dadi haka a mota da muna dawowa na kifa

fuskata kan jakata ban da tunanin yanda yayanmu ya

yini da jiki bana tunanin komai har naga karfin halina

irin wannan daga hankali haka,mami ta dafa bayana

tace iman wai yau me yake damunki ne?nace banjin

dadi ne tace sannu na amsa muna isowa gida kowa na

kokarin leka dakin don naga an karo kofar saa ta

harareni tace neman suna shishigi babu kwarjini ban

kula ta ba na shige dakin da sallama yana kwance

sambal a kan 3sitter barci yake amma fuskarshi a sake

tamkar yana murmushi don ko idonshi biyu bai cika

faraa ba,wayarshi a ajiye kan kirjinshi ina mamakin irin

son da yake ma waya na dubi fuskarshi gsky yana da

kyau sosai cikinshi a dame tamkar baya cin abinci na

kuma duba sa amma shi dogo ne don kanshi a hannun

kujerar yake taga ba ma kafar shi ya dora amma duk da

haka kafar sai dai karfinashi ne ya haukan hannun

kujerar farin gajeren wando da yar tshirt itama fara

sune jikinshi,na juya da niyar in fita sai naji ance me

kike so?gabana ya yi mumunan faduwa nasa hannu na

dafe kirjina jakata ta fadi kasa na kuma kasa juyowa

jikina sai rawa yake yi nayi waje da gudu a firgice na

shiga daki Allah yasa mama bata falo don haka sai na

shige dakinmu,sai da na nutsu sannan na fito na shiga

dakin mama ta dubeni tace ya sauran yan uwanki suka

rigaki shigowa?nace yayanmu ne ya kirani yace na dafa

mashi abinci kuma yaki fada min wane zan dafa yace

wai kowanne na dafa,mama tace tunda bashi da lfy ne

to ki dafa mashi wake da alayyahu ki sa kayan ciki

akwai a fridge ki mishi hadi sosai yanda zai mishi dadin

ci nace to.Da yake tun a makaranta mukayi sallah sai

na shiga aiki kawai uku da kwata na kammala aikin sai

da na watsa ruwa sannan na aiki sagir ya gani ko kofar

dakin yayanmu bude take bayan ya duba ina sanye da

riga da siket na farin lesi na shiga da sallama shine ya

amsa gaba na na faduwa na shiga abinda na gani shine

ya tsorata ni,anty mimi zaune a gabanshi a kan kujera

shi kuma yana kwance tana rike da hannunshi bansan

dalili ba sai naji duk banji dadin ganin haka ba sannan

ga wani abu da ya tokare mani kirji wata tsawa da anty

mimi ta dakan ita ce kuma silar rudewa ba zaki ajiye

abin da ke hannunki bar nan ba?useless kawai kin wani

tsaya akan mutane,na ajiye kan table zan juya sai

sannan yayi magana yace baki zuba mani ba zaki

tafi,,Najuyo da sauri ban dubesu ba na dauki plate daya

da na kawo don haka na zuba mashi cokali ma daya na

kawo na sa mashi na tura table din gabanshi dan ya

tashi zaune,dakin ya dauki kamshin abinci yace ki kawo

wani cokali da plate din tace no ba zan ci ba barshi,na

bude fridge na fito mashi da coke da ruwa na ajiye

tunda na fito nake mamakin yayanmu iya kwanakin da

na dauka ina mishi aiki ban taba jin yace mani sannu

ba haka ban taba jin yace abincin nan ko dakin nan

baiyi daidai ba sam.Wasa wasa na zama baiwa,gyaran

daki nice girki nice aike yanzu duk inda naje sai ya

jirani na dawo sannan zai aiken abinda ke ban mamaki

bai taba nuna min yana jin dadin abinda nake mashi ba

sannan uwarshi da kannanshi sun kara sani a gaba wai

mun shanye mata da kabir ma ya kan sani nayi mashi

aiki amma ba kullum ba kwana biyu uku hakan ya kan

ce a share mashi daki kuma idan na dafa ma yayanmu

abinci shima ina zuba mashi to a cikin satin nan ya

soma aiki shima aikinshi ya ragu,

Kwanaki sun shura ana saura sati ukku bikin su Anty

Mariya mami take bani lbr komawar yayanmu in anyi

biki da kwana biyu nan duk naji ba dadi nace mata sai

ya dade zai dawo?tace a'a yace duk bayan wata shidda

zai dinga zuwa saboda zancen bikinshi da mami da

zaran ta gama HND dinta nace Allah ya kaimu.....

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

Baba shine yayi mana ankon bikin gaba daya ko da

yake kala biyar suka fitar shi kuma biyu yayi mana, ana

sauran kwana goma biki da misalin karfe uku na

yamma ina tsaye bakin kofar yayanmu ina sanye da

atamfa sai karamin hijabina mai less fari takalmina fari

yayanmu yace nazo zai aikeni kafin ya fito daga daki

sai ga wasu abokanshi suka min sallama na amsa

sannan na gaishesu suka amsa min gami da cewa mai

dakin yana nan?nace yana ciki suka ja fararen kujerun

roba da yayanmu ya zuba a gurin suka zauna,sai gashi

ya fito guna ya nufo da leda an rubuta SI super market

a jiki,yace ga wannan ki hau mashin ai kinsan gidan su

mimi ko?nace e yace to ki kaimata kuma ki yi sauri

yanzun nan,ga wannan ya miko mani dari biyar na fita

ba wai don nasan gidansu anty mimi ba bana dai iyayi

mashi musu ne,bansan dalili ba na dai san malali

suke,gidansu Amira na shiga sannan nace don Allah ta

kira mani mami da wayarta mami tace gata nan ma

zuwa gidansu Amiran dana soma mata bayanin cewa ta

min kwatancen gidan su Anty Mimi sai tace min me

zan je inyi?nace yayanmu ne ya aikeni,suka rakani su

da Amira don na hau mashin tayi ma mai mashin din

kwatancen inda zai saukeni muka tafi yanda Mami tayi

mani kwatance haka nabi bayan na sauka a mashin nan

da nana sai gani a gidansu anty mimi na shiga

kannanta na samu suna wasa a harabar gidan sune

suka yi min jagora har ciki nan na sami Haj Laura da

wata kawarta suna hira na gaishesu da farko bata

ganeni ba sai da na gaya mata daga inda nake sannan

ta murtuke fuska tace zauna nan na zauna.Ta daga

murya ta kwala ma Mimi kira kan Mimi ta fito sai

wannan kawar tata take tambayarta wannan yar gidan

wacece?maman tace yar gidan kishiyar hajiya ce

yar'uwata itama ta yatsuna baki tace ai har ta haifi yar

da takai girman haka?ko ba amaryasu ba?tace itama

mana amma ai wannan agola ce sai shegen kankanba

kan ta kuma cewa wani 脿bu sai ga Anty Mimi ta fito

tace gani Mumy, Hajiya ta dube ta sannan ta nuna

mata ni tace ga mai nemanki nan muna hada ido

gabana ya fadi tace meye kike nemana?nace yayanmu

ne ya aikoni tace yace me?na isa gunta nace gashi

yace na baki ta dubi kayan tace duk gidan ba zai aiko

kowa ba sai ke ko?shegu mayun asiri ni dai nayi shiru

na kasa magana,Haj laure dake zaune can gefe tace to

ko bata kayan ta maida mashi mana,tace tabdi ai shi

momy daban yake in har na bari aka maida kayan nan

ai sai nayi dana sani,ta fincike daga hannuna tace ai

zamu hadu ni dashi,a raina nace kamar zata iya mashi

wani abu,ina jinsu sai faman masifa suke nace ai sai

kuyi a raina,ina fitowa daga gidan na soma raba ido ko

zan ga mai mashin amma ban gani ba na soma tafiya

sai naji ihu ban juya ba naci gaba da tafy mai motar

yaja ya tsaya ya fito ya biyoni yace ke yan mata ina

magana,na juyo cikin dardar don ban taba tsayawa da

wani ba nace lfy?ya ce kalau in har ba zaki damu ba

ina son sanin sunanki nace don Allah mallam kayi

hakuri,nacigaba da tfy ganin yana ta bina gashi ban

sami mashin ba ko wane yazo sai ka ganshi da mutum

akai nace sunana Amira yace to ina ne gidanku nan dai

nayi mashi kwatancen gidansu Amira muka rabu dashi

lfy,da kyar na samu mai mashin na isa gida in da na

bar su yaya nan na samesu na dan rusuna nace na

kaimata yana sanarshi(wato danna waya)ba tare da ya

dubeni ba yace ki shiga daki ki dauki wata leda ke ma

kije kiyi amfani dashi nace to nagode kwarai,bai amsa

ba na mika mashi kudin hanuna nace ga canjin kai

kawai ya girgiza mani na nufi dakinshi,irin ledar da ya

aike ni da ita ce akan kujera don haka nasa hannu na

dauka na nufi cikin gida ni da mama muka duba less ne

me shegen kyau kala biyu sai wani yadi mai santsi

shima kala biyu takalmi da jakka kala biyu mama tace

kin gode,nace mama ki bani da na kamu dana su

Jamila sai na kaima yaya Sulaiman a tudun wada tace

sai dai gobe nace mata dama ai.

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

A ranar yaya Abubkr yazo da daddare kofar gida ya

tsaya ya aiko Kamal wai nazo,na fita muka gaisa muka

shiga hirar duniya can ya ce kanwata yau nazo da

alamurra masu girma nace to yace zancen na zama ne

na isa kofar dakin yayanmu ganin baya nan sai na

dauko kujerun shi na robana aje mana a kofar dakin

yaya kabir muka zauna ya dubeni yace lman nace

na'am yace ya kamata ace tuntuni kinsan inda nasa

gaba,nace kamar yaya kenan?yace yau dai na gaji ina

son in fadi maki cewar ina sonki kuma da aure ba da

wasa ba,nayi shiru don banyi wani mamaki ba don na

kula da hakan shima yaya Ibrahim kwana hudu kenan

da yazo min da irin wannan maganar,yace sister naji

kin yi shiru,nace to me zance?gasky yaya ni bazan

boye maka ba karatu zanyi har sai naga karshen

biro,ya tsura min ido sannan yace in har zaki yarda ki

aureni to ni kuma na miki alkawarin zan jira ki,na dan

bata fuska nace gsky kar katsaya jirana don ni sai nan

da shekara ashirin zanyi kai kuma kila a lokacin kace

na tsufa ko ni naga tsufanka,yace inda so ai tsufa ba

matsala bane nayi shiru ina tunani shi ma fa haka

mukayi dashi (wato yaya Ibrahim)sam wai jirana

zaiyi,yaya abubkr yaci gaba da matsa min nace yaya

mubar maganar nan in lokaci yayi sai ayi na sako

mashi wani zancen muna cikin hira yayanmu ya dawo a

motarshi na raya a raina cewa daga gidansu Mimi yake

sai kawai naji banji dadi ba kuma wancan abin dake

samani nauyin kirji ya taso,sau daya ya dubi inda muke

ya shige dakinshi sai naji ma duk hirar ta gunsheni

nace da yaya Abubkr zan shiga gida yayanmu ya dawo

kuma fada yake mana ya dubeni yayi shiru sannan

yace har yanzu bakida waya a hannunki ko?nace eh

amma mama tace ina gama secondary zata sai mani

ya juya gefenshi ya dauko wata leda yace min gashi

wannan ni na sai maki ba Baba bane bare mama tace

ki maida,nace to bari sai na fara fadi mata in ta yarda

sai na amsa yace dole sai na amsa ko ya kwana a

gidan nan,dole na amsa yana tfy na dauki kujerun

yayannu na nufi kofar dakinshi cikin sanda na ajiye zan

tafi naji yace wanene a nan?nace nice yace me kike

nema?nayi shiru sai gashi yazo bakin kofa fuskarshi a

murtuke yake magana wayace ki daukar min kujera?

nayi tsuru tsuru yace wannan shine na farko kuma

inason ya zama na karshe kar ki yarda ki kuma daukar

min kujera ko ni sa'anki ne?nace a'a na durkusa nace

yi hakuri bai min magana ba ya wuce daki ni kaina dari

dari nake bansan yanda zanyi da waya ba. Washe gari

nayi kuru da safe na nuna mata tace ke bakya jin

magana ko?nace miki sai kin kammala karatunki

sannan zaki ci gaba sai na sai maki waya amma kinje

kinsa Abubakr ya sai maki ko?to shi kenan,na soma

hawaye ina cewa wllh mama bani na sashi ba tace ki

maida mishi in yazo nace to har tara na safe ban daina

kukan wannan magana ba ni ba wai wayar da Mama

tace kar inyi amfani da ita bane ya dameni a'a sai dai

ganin da tayi tamkar na roka,tafe nake ina share kwalla

zanje gun mamansu Amira in amso ma mama kanunfari

zata yi ma su sagir kulin kamu yaya Kabir naci karo

dashi zai shigo gidan yace Iman me ya sameki?na

cigaba da kuka yana ta magana nayi shiru,yace nasan

su hajiyarmu ne ko?nan nayi magana nace basu bane

ni da mamanmu ne,yace duk yanda akayi kece kika

tabo ta nace wani ne ya saya mani waya shine take

ganin kamar na rokeshi ne,yace to ta kwace wayar ne?

nace nifa ba kwace wayar ne ya bani haushi ba,yace

na fahimceki kafin ya kara wata maganar sai ga

yayanmu sun nufo cikin gidan shi da Anty Mimi shima

ya ja birki yana ce ma yaya Kabir brother me ya

sameta?kabir ya soma yi mashi bayanin cewa bafa

wani abu bane wai yayanta ya bata waya shine maman

Sagir tace wai ta rokeshi ne,ya dan dubeni sannan ya

dubi yaya Kabir yace to yanzun ta kawo karanta ne?

yaya Kabir yace no na dai tambayeta ne shine take min

bayani,ya dubeni yace wannan marar kunya da ya

zauna mani a kujera shine yayanki?daka mani tsawa

yayi nace shine yace good gara da ta kwace wannaki

bashi da kunya bai iya gaida mutane ba sai aikin kallon

mutane don haka in ya kuma zuwa kice mishi ya tsaya

daga bakin gate sannan ki san kin maida mishi wayar

nan,a fusace ya yi cikin gida daga ni har yaya Kabir da

kallo muka bishi Kabir yace ki tafi inda aka aikeki,na

tafi ina mamakin wannan karfin hali wai (barawo da

sallam)

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

Ashe yana shiga gida dakinmu ya shiga dama shima

duk safiya yakan shiga falonmu ya gaida mama tamkar

yanda yake gaida mama tamkar yanda yake gaida

sauran matan babansa,bayan sun gaisa ne sai yake ce

mata maman Sagir mai ya sami yarinyar dakin nan na

ganta tana kuka? Sai mama tayi mishi bayani ta kara

da cewa nasan ba zata rokeshi ba na dai mata haka ne

don kar ta kuma karbar wani abu gunsa,yace hakan na

da kyau ta maida mashi zan sai mata waya bansan

bata da waya ba kuma sanda na dawo ban san tana

nan ba,mama tace ka barshi kawai yayansu nima zan

sai mata nafi son sai sun kammala krt don yan

satittuka ne suka rage masu su soma jarabawa yace

haka ne in ta gama ko ba na nan zan aiko mata da

waya,mama tayi godiya sannan ta kara da cewa ga

kuma dawainiyar kayan da ka sai mata jiya an gode,na

dawo na samu zai fita daga dakinmu na dan dube shi

harara ya watsa mani nayi sauri na dukar da kai,na

shige daki.

Sam ya manta da cewa tare da Mimi suke sai da ya

shiga dakin Haj yaya sannan ya ganta zaune tana cika

tana batsewa ya zauna a kan kafet din dakin

kasancewar mahaifiyarshi tana kan kujera ya gaisheta

ta amsa a ciki ciki sannan tace kai wai ba zakaji

magana ba ko?ya dubeta yace haj me ya faru?tace ai

kafi kowa sanin abinda ya faru don tsabar iskanci ku

taho da mimi amma ku taho amma sai ka bar ta anan

tana ta faman jiranka kuma kasan makaranta zata je

tace tun tara take da lectures yanxu goma da rabi a

ina kasa gaba?kafin yayi magana mimi tayi saurin cewa

wurin fa bakar yarinyar nan ya tsaya wai sun ganta

tana kuka suka firgice shida Kabir sai tambayarta

sukeyi ban.......tsawa ya daka mata ke shiga hankalinki

ni sa'anki ne?uban wa yace da zaki makaranta ki biyo

ta nan?me zan miki?karki sa ma bakinki kwado zaki

sha mamaki duk sanda ana min magana kika tsoma

baki ya nuna kofa da hannunsa yace see your way,fita

a nan ta mike jiki na rawa mama ki daina min fada a

gabanta kin manta ita ce matar da kika zaba mani na

aura?zata raina ni ne hajiya in kina min haka a gabanta

har tana sa baki dan raini,wllh taci albarkacinki ne da

sai na mata dukan tsiya,ya cigaba da cewa bata san

cewa ni saboda ke ni zan aure ta ba ba wai don tayi

mani ba?haj yaya tace tsaya tsaya ba na son cin fuska

ka manta ni da uwarta nono daya muka sha?bayan

haka ma mimi bata da makusa ubanta balarabe ne ka

kuma sani inma ilimi ne akan nema take gashi tana

sonka sosai amma kai sai faman goce goce kake yi shi

yasa na canza shawara kafin ka tafi sai an sa ranar

aurenku,ya dubi haj yace ki dai yi hakiri na dawo don

kar aje ana dagawa tace sam ban yarda ba yace to shi

kenan ta juya zancen dake cewa wacece take kuka ku

ka tsaya kai da Kabiru?yace waccan yarinyar da nake

aike ce,nan ta hau bala'i da masifa tace dama in banyi

da gaske ba sai Habiba ta shanye min yara yanda ta

shanye babanku kallonka kawai nake yi wannan

mummunar yarinyar yanzun itace abincinka gyaran

dakinka,aike yanzu itace tunda haka kafi so ai sai kayi

sauran ka ka soma kai shawara gun Habiba haka tayi

ta sababi yana bata hakuri har dai ta sauka,Niko tuni

nakai dinkinmu gun yaya Sulaiman nan da nan kuwa sai

ga kaya ya kawo,na rakoshi zai hau mashin nan mukayi

kicibis da yaya Kabir suka gaisa da yaya Sulaiman ga

mamakina sai naga yaya Kabir ya daure fuska ya

dubeni yace na lura baki jin magana ko Iman?me yaya

Abdulrahim yace maki?na dibe yaya kabir nace ai to

wannan ba yayan da ya bani waya bane wannan wani

ne bai saurareni ba yayi cikin gida muka fita ina ta

mamakin wannan abu da yaya Kabir yayi na dubi yaya

sulaiman da nufin nayi magana sai kawai shima naga

yayi fuskar shanu(wato ya hada rai)yace wannan kuma

wanene?nace yayanmu ne yace ni ba wani yayanku na

kula ke sam baki ma san halin da nike ciki ba ko?

gabana ya fadi nace me kake nufi?yace ina cikin

mayen sonki,na dade da yin nutso cikin kogin sonki don

Allh ki taimaka min da ganin wannan da ya wuce sonki

shima yake yi,nan take hankalina ya tashi na gudu nayi

cikin gida dakinmu na fada na kwanta a kan gado

rigingine nayi fuskata na kallon silin na soma tunani,

yaya Abubakar sona yake,yaya Ibrahim sona yake,yau

ga yaya sulaiman da wannan zancan har kuma yana

tunanin wai shima yaya Kabir sona yake, ban ganeba?

na mike zumbur tamkar an tsunguleni nace da na shiga

uku ni Iman muddin Haj Yaya taji wannan lbr na ciji

yatsana na soma sintiri a tsakar dakin tabbas da zan so

yaya kabir ko ba komai yana dan yanayi da yayanmu

wata zuciyar tace min in yana yanayi da yayanmu shi

kenan sai ki soshi a matsayin da yayan naku ya taka a

zuciyarki?shin kina neman ma kanki rigima da

mahaifiyarki?menene laifin Abubakar da ba zaki soshi

ba?ya jima yana maki dawainiya dake in ba ki son shi

ga Ibrahim nan shima dan uwanki ne sannan in dama

za kuyu adalci to da Sulaiman kika zaba ki tuna shine

yake maki hidima ta fannin dinki tun kina karama har

yau dinnan shi ke maki dinki,

****hhh! Lallai yariya taki tasameki,duk cikin wayit

blood ne*****

ban san shigowar mama ba sai dai naji an girgiza ni

sannan nayi sauri na jiyo cikin tsoro naga tana kallona

tace iman me kike tunani haka?na shiga uku ni Habiba

na soma in ina,ina cewa ba komai ta girgiza kafaduna

da karfi cikin daga murya murya tace kinsan tsawon

lokacin dana dauka ina maki magana nan kuwa baki

sani ba,na jima a nan ina kallonki kina safa da marwa

tamkar wadda abin duniya ya dama,ta ja hannuna muka

zauna a bakin gado ta sanyaya murya tace Iman sanar

dani matsalarki don baki da wanda ya fini kuma na jaki

a jikina don irin wannan ranar wato don neman

shawara kar kiji komai sanar dani ta fada tana kallona

nayi shiru ina tunanin mama gaskiya dole ne ma na

sanar da ita sai dai ba zan gaya mata maganar kabir

ba, na dubi mama nace yayyena duka uku sune suka

sani shiga wannan tunani,tace kamar yaya?na dukar da

kaina kasa sannan nace yaya Abubakar da yaya

Ibrahim da kuma yaya Sulaiman kowanne yazo wai

yace yana sona,Mama tayi shiru kamar ruwa ya cita

tace ke me kika gani?ta cigaba da cewa Abubakar da

ne ga yayar mahaifinki cikinsu daya,Ibrahim kuma dan

kanin mahaifinki ne da suke uba daya shi ko Sulaiman

dan wana ne nima cikinmu daya sai ki fadi min wanda

kika zaba?nayi shiru tunani ya dawo sabo mama tace

ba tunani zakiyi ba sanar dani abinda kikace masu ke

kin amsa musu dukansu ne?nace aa duk hakuri na

basu,nace ni karatu zanyi amma tamkar sun hada baki

kowa sai yace zai jirani yaya Sulaiman ne ma ban

tsaya yi mishi magana ba,mama ta dafa ni sannan tace

yanzu gaya mani a cikinsu wa kikafi so?sai na baki

shawara nace gsky mama ni cikinsu bana son kowa,ta

mike tana fadin alhamdll gara hakan don dama ko da

dole sai na zabi daya ne,to nace gara Sulaiman yaron

na da mutunci,kuma naji ma ina fuskantarshi game da

ke ma na dade da gane cewa sonki yake nayi kwadayin

dama shi kadai ne yace yana sonki taci gaba da cewa

yanzu in naceki amince dashi sai ace don yaron

danuwana ne shi yasa don haka ki kwantar da

hankalinki kinga jarabawa na matsowa kar ki yarda na

kuma samunki kina wannan tunani ba yarda za ai ki

auri wanda bakiso ba mai matsa maki don karatu ma

zakiyi,haka mama tayi ta lallashina har dai na saki jiki

sai dai a raina maganar yaya Kabir itace a raina.

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

Tun ana saura kwana uku bikinsu anty mariya dangi

suka cika gidan,fannin Haj Shuwa da yanuwa Haj

Yaya,sai yan uwan Alh Mukhtar wato yan maska Aunty

Mimi ma a ranar tazo don ranar ne za'ayi

dayis,yayanmu ranar bai wuni gida ba sai yamma dama

ni banje masu wurin da suke yin lalle ba nida Amira

mukaje mukayi kitso sannan mukayo namu lallen a can

don dama mu ba ma saka mai a kanmu. Misalin karfe

biyar na yamma yayanmu ya aiko Kamal ya kira ni nazo

yace na kawo masa wani abu tabawa in akwai dan

yinwa yakeji na koma ba wani abin kirki sai na rana

kuma ya huce nasan ba zai ci ba,don haka sai na dafa

mashi indomie da kwai na kawo mishi natarar da Aunty

Mimi a dakin sai naji raina ya baci na ajiye zan juya

yace ke kizo ki zuba mani mana na dawo sai tace ka

barta sai na zuba maka ,bai dubeta ba yace min samin

mana kina kallona baki sanni bane?nayi kasa da kaina

sannan na zuba mishi na dauko mishi coke da ruwa

sannan na juya zan fita sai naji yace shiga bedroom ki

dauko wayarki tana nan a kan katifa,na dauko sannan

nayi mashi godiya,washe gari a command quest za'ayi

kowa ya shirya cikin anko nima na sanya nawa ankon

nayi kyau sosai na fito harabar gidanmu a nan ne ake

daukan yan matan tuni kowa ya tafi sai Amarya da

kawayenta wadannan kuma bana tunkare su ba itako

mami tuni dama tana can don sune masu shirya gurin

dasu bilkisu da sauran kawaye,ina tsaye na jingina da

bangon dakin yayanmu ina kallon kawayen amarya suna

ta kai da kawowa kowacce na rike da waya tamkar

masu gasarta nan na tuno da tawa mama tace na aje

sai mun gama zana jarabawa ina wannan tunanin naga

anty mimi sun fito itada yayanmu itama anko ne a

jikinta irin nawa tayi matukar kyau dama anty mimi ba

dai kyau ba gata fara yanda mami ke gaya mani

mahaifinta balarabe ne zamanin da Haj Laure

mahaifiyarta suke zuwa kano to jidda a can Allah ya

hadata da wani balarabe ta aura shekarunsu ko goma

ne da aure ya rasu lokacin Anty Mimi na shekara

shidda shine ta gudo da ita ba tare da sanin dangin

babanta ba,sannan ta sake aure shine ta haifi yaya uku

sanda naji wannan lbr a raina nace ashe jirgi daya ya

debomu ni da ita.....Ku ziyarci blog dinmu domin

karanta Littatafai masu nishadantarwa

Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347DOCUMENT CREATED BY

ZAHARADDEEN SHOMAR

WHATSAPP 08168575100


Tawa Tasameni 1-03

Posted by ANaM Dorayi on 02:31 AM, 29-Dec-15

Under: TAWA TASAMENI

__________NA HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

Garama ni ubana yana nan, haka danginshi, nayi nisa

cikin tunani na ji horn ba karewa na juya can wajen da

ake horn din bakin gate sai naga ashe su yayanmu ne

zasu tafi ban fahimci wai ni suke ma horn ba sai da anty

Mimi ta bude gaban mota tace ke na dubeta na dafa

kirjina nace ni?eh da Allah zo nan ana maki horn kinyi

banza da mutane, na nufi gunsu ina zuwa naga yayanmu

ya sako hannu ya bude baya yace shiga,gabana na

faduwa na shiga motar don nasan ba wanda ya taba

shigarta a yan gidanmu sai yaya Kabir na zauna sannan

na rufe sanyi da kamshi sune suka ziyarceni tamkar wata

munafuka haka na zauna a motar kaina a kasa, suko

suna ta labari bana jin dai muryar yayanmu sai ta anty

.Mun yi nisa sannan na dago idona sai kawai muka hada

ido da yayanmu ta madubi nayi sauri na sunkuyar da

kaina kasa har mukaje ban tanka ba,ban kuma daga

idona ba,sai da naji an tsaya sannan na dubi gurin yan

mata ne cike na buda zan fita sai naji yayanmu yace

karba,na juyo sai naga yana bani kudi ne sababbi yan

naira hamsin na amsa nace Allah ya saka da

alkhairi,anty Mimi ta shaka sosai da na kalli fuskarta ni

dai nayi ciki ko zan ga Mami, ana cikin hidima shalele

suka kira don haka gun ya cika da karan kidan police

band Sa'a tazo tace kije ana kira gabana yana faduwa

nace inji wa?ta harareni dole sai kinji? ki zo mana na

bita can baya mukaje ganin Anty Mimi da Amare da

kuma kawayensu yasa wata faduwar gaba ta sameni na

dai daure na isa wurin,Anty Mimi ta kai mani rankwashi

akai tace ina jakarki?nace tana gun Mami tace nawa

yayanmu ya baki?nace ban kirga ba nan ta shiga

zayyane masu wai wannan wace irin yarinyace,Anty

Hadiza tace ai wannan daga ita har uwarta annoba

ce,Anty Mimi ta cigaba da cewa kunga jiya a gabana ya

bata waya irin tawa ce sak koda ganin kwalin sannan yau

zamu taho nan ta zo ta rabe ya dauko mu tare kunji

biyu,cikon na uku kuma sai gashi ya raba mana kudi

kilan ma daidai ya raba tamkar wasu kishiyoy,nan suka

taru a kaina wannan ya kai mani bugu kowa dai na fadin

albarkacin bakinshi, Mami ta iso daidai lokacin da wasu

kawayen Anty Mimi suke cewa asiri tayi mishi daga

gani,in ba haka ba me zaiyi da wannan mummunar

yarinyar gara ma ki dauki mataki tun da wuri akan abin,

Mami tazo tana cewa Anty Mariya kuzo anguna sunzo fa

ana ta nemanku,kan suyi magana Anty Mimi tace Mami

muga jakar wannan jakar,sai sannan Mami ta ganni ina

kuka tace Iman menene?Bilki tace ba'a sani ba ke dai ki

bada jaka a kace Mami tace bazan bayar ba nace Mami

bata ta mika mata sai da suka kirga kudi daidai da nata

dubu ashirin da biyu ne dama ban kirga ba,saura sukace

kar ki bata ko sisi Mami tace wllh sai naga ya wa

yayanmu in har kika dauki kudin nan,Anty Mimi ta watso

kudin da jakar a jikina sannan tace ki jira abinda zai biyo

baya ta wuce sauran suka bi bayanta aka bar daga ni sai

Mami inata kuka,Mami ta kwashe tana tambayata abinda

ke faruwa na zayyane mata komai itama na kula ta dan

yi mamakin kudin da ya bani tace Iman yayanmu yana ji

dake fa nace Nami ku kula da wani abu daya yayanmu

nice nake mashi aiki,shiyasa yake mani alheri amma wai

suna zargin wai yana sona ne ni nasan ko mata sun kare

yayanmu ba zai taba cewa yan sona ba ke kinsani balle

yana da kamar Anty Mimi,Mami tace ai itama anty Mimin

ba wani kyau ne da ita ba uban gashi ne kamar jirgi ya

daso tasha kuma a tsaye take ba wani diri kirji kamar na

bera ba wasu nonuwan kirki nace to shi dai tayi mashi

Mami tace ke zo muje ba wani yi mashin da tayi kawai

saboda mamansu zai aure ta.

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

TAWA TA SAMENI,haka na fada ranar daurin auren anty

mariya ba wani abu yasa na fada ba sai ganin munsa

less iri daya da Anty Mimi wato wanda yayanmu ya bani

nasa daya daga ciki me ruwan lemun tsami takalmi da

jaka iri daya itama ni take kallo ta zauna kofar dakin

yayanmu a fararen kujerunshi ranta yayi matuka gun baci

naga ta yi cikin gida ni kuma sai na nufi gidan su

Amira,dama dazun ta aiko Faruq wai ta dawo dama jiya

ne ta tafi unguwar dosa gun kanwar mamansu da suka

dawo kwanan nan shine taje kwana,ta fito wanka na

sameta nan nake zayyane mata abin dake faruwa ta

dinga mamakin karfin halin irin na nasu Aunty Mimi dan

yayanmu ya min kyauta ta kara da cewa komai ya sai

maki ba zai biyaki ba irin dawainiyar da kike mishi ba

nace suna zargin fa wai sona yake yi,Amira tace haba

dai nasan ma ba zai fara ba domin kin......na katse

Amira nace ni ba ajinshi bane nasan da haka kuma ko

mata sun kare ba zai so ni ba Amira tace ba nufi na

kenan ba ina nufin matsalar dake tsakanin mahaifiyarki

da tasa ai yasan da wannan matsalar ba zaima ce yana

sonki ba.Nace ato su sai hauka suke yanzun nan na

hadu da anty Mimin shine ta ganni da kayan nan har

jakar to tayi cikin gida ban san me zai faru ba,dama

bikin nan sai yan tsegungumi sukeyi dangin Haj Yaya

naci gaba da cewa kinsan abin da ya faru ne da babansu

Mami ya tambayi Haj Yaya game da kayan da za'a siya

don yayanmu ya riga ya sai masu sai yace to suyi mashi

list din kudin sukayi mashi hauka to hauka mana wai fa

miliyan daya da rabi suka rubuta shiko ya kira mama tayi

mashi lissafin kayan dakin mata mata har da na jere da

na kicin duk ta sanar dashi naji ya bata kudi sukaje ita

da Anty Yagana suka sawo mashi komi don Mama cewa

tayi sai da tayi ciko suka kawo ya dinga sa mata albarka

itama ta bashi nata gudummuwar na zannuwan gado to

wannan abin shi yayi matukar tada hankalinsu Haj Yaya

da har sunce sam kayan nan bai masu ba shine baban

yace yayi in baiyi masu ba to su sai nasu da kudinsu

kafin Amira tayi magana sai ga Jamila kanwata da

kukanta wai ana fada da Mama nace mama da wa tace

Mama da mutane yan biki nace yau mun shiga uku ko

takalma bansa ba na nufi gida Amira ta biyoni,tun a

harabar gidan nake jin hayaniya yaya Kabir na gani ya

fito daga cikin gidan ranshi a bace da ganina ya nufoni

yace kar ki shiga zo nan,na soma kuka ina cewa ni dai

na shiga uku ya ja min hannu zo muje karki shiga,nace

ina kuka yaya Kabir barni naje naga Mama yace

Mamanki tana dakin Alhajinmu zo muje ya jani dakinshi

ya zaunar dani kan kujera sannan ya tsugunna gabana

yace kiyi shiru zan tambayeki ne,nayi shiru ina share

hawayena yace yaya Abdulrahim yace yana sonki? nace

aah yayi ajiyar zuciya sannan yace alhmdll yayi shiru

zuwa can yace a gaskiya Iman na dade ina sonki shiyasa

ma har yau na kasa kula duk wata ya mace da sunan so

na mike tsaye na ce Kabir tun ina ganinka da gashi kar

ka yarda na kuma jin wannan zancen kana ganin balain

da muke shiga kullum a gidan nan sannan zakace wai

kan sona ni dai ba ruwana,ya zaro mani ido gami da

tasowa kamar zai bugeni yace sai kin soni kuma ni da

ruwana ba abinda ya dameni da fadan iyayenmu,na mike

zan fita yace kar ki yarda ki fita su Haj Laure zasu dake

ki muddin kika shiga,jin maganar duka ni uwar yan tsoro

na dawo na zauna na sanyaya muryata nace sun doki

Mama ne?yace suna hauka ne?ita ko kulasu ma batayi

ba shine yar Alhajinmu da tazo daga maska tace ta

shuga dakin Alhajin tasa na mashi waya yanzun nan yana

zuwa shiyasa nace kar kije,na cigaba da kukana yaya

Kabir yana lallashina har nayi shiru ya dinga shigar

dakan shi a guna yana ce min in na yarda yasan

Akhajinsu zai tsaya man kuma zai nemi canjin gun aiki

mu bar kaduna haka ya yi ta cusa min raayi har na soma

yarda,sai dai ina tunanin mama ba zata amince ba na dai

yanke shawarar zan ci gaba da addua. wayar yaya kabir

tayi kara yace in dauka don nafi kusa da wayar,na dauka

sai naga sunan yayanmu sai na mika masa yace ya baki

dauka ba?nace yayanmu ne ban san mai yake ce mazhi

ba na dai ji yace gata nan sai na kuma jin yace dakina

sai gabana ya fadi,sai naji yace to gata nan zuwa,ya

dubeni yace alhaji yazo yana dakinshi an ce kije,nace

yayanmu na gurin ne?yace shi ne yayi min waya wai

Jamila tace nine na tare ki ina kike yanxu sai shine nace

gaki nan ki tafi ko na raka kine?nayi saurin cewa a'a don

kar agan mu tare,cikin dar dar na shiga gidan yan biki

sai ni suke kallo gashi ko takalmi babu a kafata na shiga

ciki nayi sallama a kofar falon Alhaji na shiga Alhaji na

kan wata kujera irin ta karfen nan ne dama nan ne gun

zamanshi sai Mama akan kujerar gefen damanshi dayan

gefen Haj Yayace sai Haj Shuwa kusa da ita Haj Kulu na

dakin sai yaya ta maska(wato yayar Alhj)yayanmu na

kan kafet kusa da kafar Alhaji nima na shiga na samu

guri kusa da Mamana na zauna a kan kafet.

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

Alhj na gaisar sannan yayi gyaran murya yace to gara ke

Murja(haj yaya)menene sanadin wannan fadan?na

tambayeki dazu kince sai an kira Iman gata tazo sai ki

fda muji ynxu,ta soma magana cikin sababi ni dai Alhj

kawai kayi mani tsakani da Habiba da kuma 'ya'yana in

kai ta gama da kai to ni da 'ya'yana li'ilafi,,tashanye min

yara basa cin girkin kowa sai na 'yarta sannan yanzu shi

wannan miskilin dana gani kamar zai zama namiji amma

ba haka bane ya tashi sai kashe mata kudi yakeyi harda

yi mata anko da matar da zai aura me hakan yake nufi?

na dai san rokonshi sukayi don haka ayi mana iyaka dasu

ba 'ya'yanta ba nawa,tun da ta soma bata tsaya ba kuma

ba a katse ta ba,jin tayi shiru sai na dago kai na dubi

kowa kowa dai ita yake kallo sannan na dubi yayanmu

wanda kanshi yake kasa Alhj yace to naji naki ke kuma

Habiba ya abin yake?Mama ta soma magana cikin sanyin

murya lafuzza masu kyau tace ni dai Alhaji a gefena ba

wani matsala yarinyar nan dai itace matsalar, da zaka

amince min da sai na dauketa na maidata wajen

kawunta don inda bata nan gidan da baza ta ga ma

'ya'yan Haj Yaya ba bare su sata aiki sannan muddin

tana nan gidan ba zan hanata aiki ma kowa ba har Hajiya

Yaya inda zata sata,amma kiyi hakuri Yaya zan maido

maki da dukkan abinda Abdulrahim ya sai ma Iman

sannan kuma sai kiyi mashi magana ya daina sata aiki a

zauna lfy,na dubi Mama hankalinta a kwance tayi

maganar sabanin Haj Yaya wadda ke cika tana batsewa.

Dakin yayi shiru sai can a

Alhj ya soma magana yace Murja! Haj Yaya tace na'am

da karfi tana karkada kafa yace ina son kisan cewa

'ya'yan nan nawa ne kuma wancan ma tawa ce don ni da

kaina na daukota ko uwarta bata san zan kawo ta sai dai

ta ganmu Allah yasan wannan don haka ba zaki raba min

kan 'ya'ya ba kinyi kadan,Habiba yarinya ce a kanki

amma tafiki hankali da tunani saboda haka kar ki yarda

ki amshi duk wani abu da yayi mata kuma aiki duk wanda

yayi niyyar sata kar ya fasa don haka na gama wannan

maganar sannan ki gargadi laure ta kiyayeni da wasa naji

ta taba Habiba ko Iman sai nasa an daureta gara ma ta

tabaki zaifi mata sauki,Haj Maska tace yayi daidai

hakan,Murja in ka girma to kasan ka girma don haka sai

ta soma kuka tana cewa dama namiji ba dan goyo bane

nan na dauki kudina na baka ko basu ne silar arzikin naka

ba?daban haka ai da har yanxu kana a fakirin ka dole ka

min sakamako da mun wulakanci ta nuna ni tace ke

kuma zakiga hukuncin da zan yanke a kanki muddin kika

kuma ko kallon min 'ya'yane na durkusa da sauri(don har

ta mike)nace don son Annabi(SAW) kiyi hakuri bankade

ni tayi waje sauran kishiyoyinta suka take mata baya,Alhj

ya bisu kallo sannan yace Allah sarki to Allah ya sa ku

gane,ya dubi yayanmu yace kaima kayi hakurin dai zan

baka cikin sanyin murya yace Alhj kaimin izinin na koma

england jibi,yace na maka amma yaushe zaka dawo?kar

kaje ka kuma zama yace nan da wata shida ne yace to

Allah ya kaimu ya fita na bishi da kallo.

Karya ne gane halin da fuskarshi take ciki wato laifinmu

yake gani ko na uwarshi,ban taba ganinshi cikin dogayen

kaya ba tunda yazo sai yau boyel ne baki amma kanshi

ba hula Alhaji ya dubeni yace Allah yayi maki albarka

Iman kiyi koyi da halin mahaifiyarki kinji?na daga kai ya

cigaba da cewa muddin kikayi halin uwarki to kin

dace,sannan mijin da zaki aura ma yadace,su Abdulrahim

da Kabir duk yayyanki ne duk abinda suka saki

kiyi,sannan in sun maki kyauta ki amsa kice kin gode

nace to Alhj na gode,na mike na fita dakinmu na wuce

kai tsaye kan gado na fada raina a cunkushe na rasa me

ke daga min hankali son da Kabir yace yana min ko

matakin da Haj Yay tace zata dauka a kaina ne?wata

zuciyar tace duk ba wannan bane tafy yayanku ce

wannan amsar da zuciya ta bani itace sanadiyar tashina

zaune saboda tashin hankali da naji ni a ciki na mike ina

safa da marwa nace a fili ban so akayi wannan rikicin ba

ba zanji dadi ba muddin yayanmu ya tafi kai zanje na

bashi hakuri in ya tafi na mutu,da sauri na dauki hijabina

na fita falo nan nayi turus ganin mama a falon tace ina

kuma zaki?karon farko da na soma yi mata karya nace

gidansu Amira tace me xakiyi?nace takalmina da gyalena

dauko tace ko bari zata aiko maki ko ki aika Jamila kar

ki fita ko ina ynxu zo nan kiji,na isa gunta na zauna tace

kin dai ga abinda ya faru ko?nace eh tace to ina son kiyi

taka tsan tsan da kowa a gidan nan banda yawan

shigewa duk wanda ya saki aiki to kiyi masa kamar

yadda kikaji Alhaji yace maki,nace to ta kuma duba na

tace yanaga kinyi wani sukuku dake?nace bani son

tashin hankali ne mama shiyasa tace kar ki damu aikin

shedan ne kuma ki cigaba da addua sannan daga ynxu

zan na tashin ki duk dare in tashi yin nafila sannan zaki

dinga yin azumin litinin da alhamis,sai mu dinga tare in

kuma an gama bikin nan zanje wurin kawunki na samo

mana addu'o'i na tsari mu dukufa,Allah ya ja mana

gaba,sauran maganganun da mama takeyi duk banji su

ba ina ta tunanin yanda zan ga yayanmu don nasan nice

na jawo wannan tashin hankalin gaisuwar da naji mama

ta na amsawa shine yasa na juyo Mami ce ta dubeni

tace ya dai?na mike muka shiga dakinmu kan gado muka

zube na dube ta nace ya dai tace ina gidan walima muna

shirya guri sai ga Sa'a wai ana fada da mamanku da su

Haj Laure har sunce sai sun zane ku?nayi tsaki nace kan

fa kaya ne kin gansu nan jikina yayanmu ya bani ashe

irin na Anty mimi ne shi kenan sai tashin hankali gashi

yanzu ma yace zai koma jibi,Mami tace ai dama bayan

biki da kwana biyu yace zai koma nace to ai gashi ba'a

gama bikin ba ni gani nake ma duk laifina ne hawaye

suka zubo mani akan kumatu Mami ta tsaya kallona baki

bude shi ne harda kuka?kuma ma ina wani laifinki anan?

nace nasa kayan tace to baya baki don kisa bane?shi

yayanmu in zai ma mutum kyauta ba ruwanshi da wani

nuna bambanci nace rakani na bashi hakuri,Mami tace

tab ai sai dai kije ke kadai yayanmu ba ya son ai ta

faman bashi hakuri musamman in yana cikin tashin

hankali gara makin zauna,ke menene naki na damuwa?

kina ganin zaki iya hana shi ya tafi ne?nace bani na ja

komai ba,tace sannunki da kai ta mike zo muje gidan

walima nace ni kaina ma ciwo yake bazan sami zuwa ba

ta tafi na koma na kwanta na cigaba da kuka rurus,saidai

za'a a tsira ni ko da bindigane ba zan ce ga abinda nake

ma kuka ba sai da nayi ya ishe ni sannan ciwon kai ya

yomin sallama kafin wayewar gari nayi rigif ko sallar

asuba kasa yi nayi sai wurin bakwai na safe yinin ranar

nan haka nayi shi, misalin karfe uku Alhj ya shirya da

Yaya Abdulrahim yace Habiba danku zai wuce fa,kan

Mama tayi magana shima Yayan namu ya shigo ban san

lokacin da na mike ba ya zauna a kan kujera yana gaida

mama bayan ta amsa sannan ta ce ikon Allah tafiyar ta

tashi ne Abdulrahim?na dauka gobe ne?yace eh gobe ne

zanje lagos ne na kwana shida na safe jirginmu zai tashi

yanzu ma jirgin karfe biyar zanbi zuwa lagos din yana

magana niko bakinshi nake kallo da sauraron muryarshi

mai dadi tamkar ba namiji ba ne yake magana ba Mama

da Alhj suka shiga dakinta ya bisu da kallo sannan ya

juyo ya dubeni na dukar da kai gabana sai faduwa yake

yi,ga mamakina naji yace Amina nayi sauri na dago kai

baki bude ina dubanahi shima ya kafa min idanu na

sunkuyar da kai don ba zan iya cigaba da kallon kwayar

idonshi ba sai ina ganin wani abu yana fitowa daga idon

shi,yana shigowa nawa,murya kasa kasa yace zan tafi

kiyi mani addua kaina a kasa nace adawo lfy Allah ya

bada sa'a,a lebanshi naga ya amsa,Alhj ne ya fara fitowa

yana cewa Abdul walarka nace Mam zata baka?yace no

Maman Sagir kar ki damu ba sai kin bani komai ba Mama

ta fito da dambun nama dayawa tace to ka tafi da

dambun naman nan Iman tayishi shekaran jiya ya dubeni

sannan yace to zan amshi wannan sai naji wani sanyi a

raina suka fita nima na daga labulen dakinmu ina kallo

ga yan biki nan sai a dawo lfy suke mashi harda su Haj

Yaya dasu mama aka fita harabar gidan wajen ajiye

motoci nima na fito ina daga can baya ina kallonsa har

aka shigar mashi da jakunkunan shi cikin boot din

motarshi yaya Kabir ne zai jashi,ga wasu abokanshi

suma zasu shiga wata motar ya fito daga dakinshi har

ya sauya kayansa da jc jajaye masu ratsin fari dogon

wando da riga mai dogon hannu sai takalmin kwallo Anty

Mimi ma ta fito sai kuka takeyi haushinta ya kamani a

ganina nice yafi dacewa inyi kuka ba ita ba ko mai yasa

oho zai shiga mota kenan ya hango ni sai naga ya tsaya

yana kallona har Anty Mimi ma ta juyo taga wa yake

kallo?sai taga ni yake kallo sai naga ta kawar da kai niko

sai na kwantar da kaina a jikin bango sannan na daga

mashi hannu alamr bye bye sai ya shige mota suka tafi

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

Tun daga wannan rana ban kuma wani sukuni ko

walwala ba har mamakin kaina nakeyi kullum cikin

damuwa bana wani cin abincin kirki gashi kowa ya gane

halin da nake ciki a gida da makaranta sai dai kowa ya

tambayeni sai nace bani da lfy ne.Azumi da nafilflii

kullum cikinsu nake

,ranar da yayanmu yayi kwana biyar da tafy Mama taga

abin ya isheta bani magana sosai koda yaushe a kwance

ga jarabawa ta matso amma bana wani krt sati da lahdi

suka zo suka wuce amma banje islamiya ba wato

(sanawiyya),Ranar monday mama tace kar naje

makaranta na shirya muje Asibiti nace lfy ta kalau tace

na dai shirya muje kawai rimi clinic mukaje mama tayi

ma likita bayanin yanda nakeyi,likita ta barshi dani bayan

fitar mama sai likita ya dubeni yace sanar dani yadda

kikeji sai nace kasala nikeji sai kirjina da ke min nauyi

kuma bani son yawan surutu yadan gwaggwadani sannan

yace kina yawan tunani ko?nace eh yace to tunanin me

kikeyi?nace ba komai yace karya ne da na rasa ta cewa

sai na ce jarabawa ce nake tunani ba dan ya yarda ba

yace to shi kenan ki daina yawan tunani kisa Allah a

gaba ya rubuta mana magunguna muka tafi,haka nayi ta

shan magunguna amma tamkar ana zugani Mama ta

koma na gargajiya ni dai nawa shane a haka jarabawa ta

same ni mukayi ta nidai ban sa rai da zanci ba ranar da

muka gama ne a nata murna masu hoto nayi,niko sai

kallon mutane nake,Mami ta dafa ni tace ga wata yar

ajinku can tana nemanki nace ina take?ta nuna min ita

ashe Hauwa'u Aminu ce nan tamin korafin rashin sanin

gidanmu ita kuma ta bani no wayarta ni kuma nace mata

in na fara anfani da tawa sai taga tawa lambar,sai da

zamu bar harabar makarantar ne sannan naji duk kewar

makarantar ta ka mani.Abdulrahim zaune a kan kujera a

cikin falon Hotel din da yayi masauki, ko nace nan ne

dama club dinsu suka kama mashi tun farko,kanshi yana

jingine a bayan kujera, tebur ne dan karami cike da

kayan ciye ciye da shaye shaye amma sam ya kasa cin

komai tunanin yakeyi wayarshi tayi kara ya juyo ya dube

ta kamar kar ya dauka sai kuma ya dauka Mimi ce ta

kirashi bai san dalili ba sai yaji wani kunci a ranshi amma

sai ya daure ya dauka,tace yayanmu kana lfy?yace lfy

kalau,yake dinfa?tace ina nan lfy dama naga tunda ka

tafi baka kira ba ne,yau kwana shida kenan?yace ban

sami dama bane,tace to ina jiran kiranka,yace to kawai

ya kashe wayar juyawa yayi ya dubi abincinshi kusan

minti arbain kenan da kawo abincin amma ya kasa ci ya

kai hannu ya bude plate din abincin da yafi so yayi order

amma sam sai yaji kamshin abincin ma baya mishi dadi

kokadan a fili yayi magana yace yarinyar nan ta bata ni

da kalolin abincinta masu dadi,yayi shiru yana tunani tun

zuwan shi kasar nan bai wani ci abinci ba daga ruwan

lipton sai dambun naman nan,kwankwasa kofar akayi ya

bada izinin a shigo ne abokinshi ne shima dan kwallo ne

amma shi bature ne ya dubi Abdulrahim sannan yace

cikin turanci Maska naga baka shirya ba ne,wannan

karon baka so dawowa ba ne tunda ka dawo sam baka

da kuzari,me yasa?Abdulrahim ya mike yana fadin

tunanin gida nakeyi ya shige dakin barcinsa shima ya

shiryo cikin JC na training suka fita.A daran daya cika

kwana bakwai da zuwa yana zaune a harabar Hotel din

haske ne ya kewaye gurin kamar rana gabanshi

gwangwanin coke ne da dan karamin plate cike da

dambun nama sannan ya kai hannu ya dauki wayarshi ya

soma sana'ar wato danne danne wayarshi can yayi tsaki

ya kashe wayar ya mike,da ya kamata ya nufi gurin

abokanshi ne tunda ba dare ne yayi sosai ba kuma yasan

zasu sa ran zuwansa, amma sam sai yaji ba zai iya ba

saboda wani abu da ya taba zuciyasa sama ya nufa

dakinshi ya zauna a bakin gado sannan ya aje tarkaccen

hannunsa a kasa wayarshi ya rike sannan ya soma

sarrafata cikin kwarewa, Babanshi ya kira bayan ya

dauka sai yace Alhj ina yini?bayan sun gaisa sai yake

cema Alhj dama ya kira ne dan ya amshi lambar wayan

Maman sagir domin yana da lambar kowa a gidan itace

bai da ita,Alhj yace gata nan ma Habibar ku gaisa,bayan

sun gaisa ne sannan ya bukaci lambarta ba tare da wani

tunani ba ta bashi,ya jima yana tunanin dalilin karbar no

kafin daga karshe ya gane sai dai wani tunaninshi abin

zai zamar mashi abin kunya da nunawa cikin

abokai,muddin suka san halin da yake ciki,nan a dalilin

wata kankanuwar yarinya wacce da yayi auren wuri

tabbas zai haifi kamarta.Kwance yake akan gadonshi

amma sai sautin daddadar muryar yarinyar yake dawo

mashi ya tuno ranar da bashi da lfy duk gidan ba wanda

ya kula dashi tamkar ita muryarta ya tuna sannu

yayanmu za ai maka wani abu ne?ya sake tuno yanda ya

kara tsorata ta ranar da ta daukan mashi kujera tabbas

in tana cikin tsoro tana matukar burgeshi yayi magana a

fili inda yace nayi missing din ganin tsoranki.

(Lallai Iman kinga takanki, mudai daganan sai muce!

Allah yakyauta)

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

Ya cigaba da juyi a kan gado ba komai ke dawainiya

dashi ba sai begen yarinyar da yake gani abin kunya ne

ace ya sota ya tuna da mimi yarinya mai kyau jinin

larabawa sai dai shi baya jinta a ranshi yanda yake jin

wannan yar mitsilar yarinyar zai auri Mimi ne kawai don

bin umarnin mahaifiyarshi kuma ya san duk inda suka

shiga ba zai ji kunyar nunata ba a matsayin matarshi

shekarunta ashirin da biyar shi kanshi shekara biyar ya

bata bugu da kari gashi ta soma zurfi a karatunta,amma

in yace wannan yarinyar zai aur脿 shima yasan rigima zai

jawo,yanda mahaifiyarshi ta tsane su wata zuciyar ta ce

mashi ga yaran nan da rashin kunya tana jin kace kana

sonta to raini ya shiga tsakaninku gara ma Mimi hadaku

akayi kuma kasan ta mutu kanka don haka baza ta maka

wani rawar kai ba,"A dawo lfy Allah ya bada sa'a" ya

kuma tuno muryata da yaji na karshe sannan lokacin da

ta rakube a jikin bango tana mashi bye bye ya dawo

mishi tausayinta yaji lokacin kuma jikinshi na bashi kamar

itama tana jin yanda yake ji a ranta,zaune ya mike yana

magana shi kadai tamkar wanda ya tabu yana fadin

Amina kiyi hakuri bani da sh脿'awar auran mata biyu ki

bari in runtsa ya kuma fadawa kan gado.Niko yanzu na

zama kurma bana magana sosai ban kuma cika son

magana ba sai dai maganar su Amira ce ke damuna da

suka ce wai ina ciki mayen soyayya na dai ki sanar dasu

wanda nake so,inko har zancensu gsky ne to na debo da

zafi don ko in har yanda zuciyata ke mani game da

yayanmu so ne to ko shakka babu gara na rufa ma kaina

asiri nayi shiru da bakina don nasan ko yaji ubana zaici

don nasan ni ba ajinshi bace,me kamar Anty Mimi?

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

kammala karatuna shi ya ba samari damar damuna

tamakar anbi su an gaya musu musamman ma yaya

Kabir shine yasani wannan ya sani wancan,su yaya ma

suna zuwa,ban manta wata rana yaya Kabir ya aiko Sagir

dinmu ya kirani na fito na sameshi a daki kan kujera na

zauna fuskata na kallon wani katon hoton yayanmu

sanye yake da JC kore da fari irin na yan wasan Nigeria

hannunshi a kan kirjinshi daga gani lokacin suna taken

Nigeria ne aka dauke shi,muka gaisa da yaya Kabir ya

soma yi min zancen soyayya niko hankalina ba ya tare

dashi, yayanmu kawai nake kallo da kyaun da Allah yayi

mashi ba abinda ya birgeni irin shedar sallah daya fito

mishi a saman goshinshi yayi baki tamkar ya diga ina

cikin wannan tunanin ne naji yaya Kabir na min magana

da karfi nayi ajiyar zuciya sannan na dube shi nace ka

gama?zan shiga gida yace na tambayeki baki bani amsa

ba nace ni ban wani jika ba na mike nayi waje yana

kirana na fito kirana naji anyi daga bakin gate ko ban

juya ba nasan yaya Abubakr ne dogon tsaki naja sannan

naje ina zuwa na hau shi da masifa shima kallona naga

ya tsaya yi,ina cewa nace ni ba aure zanyi ba amma kun

dameni don Allah ku rabu dani ko dole ne?na juyo abina

wani abin haushi ina shiga falonmu sai ga yaya Suleiman

zaune suna hira da Mama...(hhhhhhhhha.yarinya taki

tasameki.)

dakin kwananmu na wuce nayi kwanciyata naki fitowa

ban fi minti goma ba mama ta shigo ta dubeni tace

Sulaiman ya dade yana jiranki wai me kika tsaya yi wurin

Kabir din?nace ya aike nine bayan na dawo kuma sai na

gamu da da yaya Abubkr na cigaba da cewa gsky ni dai

mama ki samu su yaya Abubkr kiyi musu magana nifa ba

aure zanyi ba su rabu dani mana,mama tace aike ma yan

uwanki ne kuma nasan in ki sanar dasu zasu kyaleki

sannan suna ganin girmana sosai bazan iya tunkararsu

da wannan zancen ba, nace haka fa shekaran jiya yaya

Ibrahim yazo wai har yana takama zaije ya samu babana

kuma ko ina so ko bani so shi zai bashi ni mama tace to

bisimilla ai ga kinan taci gaba da cewa don haka ma ni

koda auren ne cikinsu gara Abubakr din nace ni dai

dukkansu har yaya Sulaiman din hakuri zaiyi dani dan

bana son auren zumuncin nan mama ta fita tana cewa

dai gashi can ku gaisa,na dauki hijabina na fito falo

fuskata a daure muka gaisa yace to Iman gani dai na

kuma dawowa duk da kin sanar dani krt zakiyi shine na

yanke shawara ki yarda a daura mana aure ni kuma zan

yarje maki kiyi krt har kiga karshen biro nace mu bar

zancen nan, ina Nana?yace Nana tana nan jiya aka sa

ranarta goron ne ma na kawo ma Mama nace lallai Nana

yanxu itama auren zatayi?yace shine mutuncin duk wata

'ya mace nace to Allah yasa alkhair ni zan shiga na

kwanta ka gaida min da su baba uwa kace da Nana inna

jiran zuwanta, yace amsata fa? ko zaki yi min waya don

Mama tace kin soma amfani da wayarki nace jiya na

soma sai dai ni bata dameni ba don haka ko lambar ban

rike ba in Nana tazo taje maka da lambar yace ai bazaki

min ko flashn bane tunda kinsan tawa nace to na maka

na shige daki ina jinshi yana fadin barakiya?

Sannu a hankali zuciya da gangar jiki suka tsananta da

so kauna da kuma begen wanda bazasu samu ba sannan

ni naki yarda da cewa sonshi nake ban yarda da nayi

nutso a kogin sayayya ba sai da na samu kaina da rashin

barci,sannan na kama karatun littatafai na

soyayya,kallace kallace da basu dameni ba yanzun nakan

zauna nayi duk saurayin da aka nuno sai naga bai kai

yayanmu komai ba ni fa gani nake ba wani namiji wanda

ya amsa sunan namiji in ba yayanmu ba,yauma kwance

nake akan gado yar karamar Rediyon da nike yin karatu

ce na manna a kunnena kaset na wakar fim din kugiya

na sa wakar na ratsani Idona a lumshe sai nakejin kamar

nice nakeyin wakar, duka naji an dada min da sauri na

tashi ganin Amira da Mami shine yasa nayi ajiyar zuciya

nace kin dau alhakina Amira ta cire wayar kunnena sai

ta dauke Radion ta sa a kunnenta dajin wakar sai naga

ta cire da sauri tace Mami ji wannan kaset din Mami ta

sa taji sai naga sun dubi juna sukayi dariya nace wai

menene?suka zauna suna cewa zancenmu gasky ne

nace kamar yaya zancenku gsky ne?Amira ta dauke

fuska tace Iman mun gamsu nace me na muku?Mami

tace akwai abinda yake damunki amma kin kasa sanar

damu,Amira ta amshe damu ne da munhau gaya maki

nayi shiru ina tunanin me zan ce masu can dai nace

Amira,Mami kunsan yayyena Abubkr,Ibrahim da

Sulaiman?suka ce sosai ma kuwa nace dukansu sunce

suna sona ni kuma bani son ko daya sannan yaya Kabir

shima yace wai sona yake na mike tsaye don girmama

maganar da zanyi na cigaba da cewa ni kuma zuciyata

da gangar jikina sun nutse a son wanda bai san inayi ba

kuma koda ya sani ba zai soni ba don yana da wacce ta

fini kyau da ilimi da kuma shekaru,hawaye suka soma

zubo min na juyo da sauri na rike kafadun Mami da

karfiina cewa ku bani shawara kawayena ku taimaka min

da maganin da zan daina sonshi don kukan ku da zaku

san ko wanene da kunce lallai zuciyata tayi wauta,suka

kamani suka zaunar dani tsakiyarsu suka yi shiru dakin

ya yi tsit daga ajiyar zuciata da nakeyi sai karan fanka

can Amira tace a ina yake?kuma yaya sunanshi?nace

kuyi hakuri wata rana zan gaya muku don ba anan yake

ba Mami tace dakin gaya mana ai da mun san yanda

zamu bullowa abin nace no ko zan mutu bazan taba

tunkarar wani da namiji da sunansa ba yanzu ku bani

shawara yaya zanyi na daina tunaninshi suka yi shiru

can Mami tace rokon Allah zakiyi muma zamu taya ki

nace sai dai mukara don kullum yi nake amma ba sauki

sai dai abinda ya karu nan dai suka lallashe ni gami da

bani shawarwari.

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

Haka naci gaba da rayuwa cikin kunci,wata safiya misalin

karfe takwas Mama tana dakin Alhaji ta kai masa abin

kari ni kuma ina ta faman gyaran dakinmu na gama na

koma dakin Mama ina cikin aiki naji wayar Mama tana

ringin na dauka sai ga lambobin rakwacam na dauka

nace Assalamu alaikum sai naji ance

Wa'alaikummussalam,jin muryar da ta amsa nan da nan

na gane yayanmu ne farin ciki da na ji baya misaltuwa

ina wannan tunanin ne naji yace Naman Sagir ina yini?

nace ba ita bace ni ce Mama tana dakin Alhaji yace ok!

nace ina kwana?yace lafiya amma mu nan rana ce kuna

lfy?nace lfy lau yace to kice da Maman Sagir ina gaishe

ta dama don mu gaisa ne na kira kafin nace to har ya

kashe ranar nayi walwala har yamma don jin muryar abin

sona.

ShareDOCUMENT CREATED BY

ZAHARADDEEN SHOMAR

WHATSAPP 08168575100

Tawa Tasameni1-04

Posted by ANaM Dorayi on 10:13 PM, 30-Dec-15

__________ NA HALIMA ABDULLAHI K/MASHI__

Lokacin da zai tfy nan ko ince da zaya koma ina cikin

wannan tunani sai naji yace kin gama?dama na gama sai

nace e yace to gashi na isa na dan rage tsawo yace

wannan ya turo mani akwati naki ne sannan daya kuma

zaki kaima Mimi nata nace to nagode Allah ya kara

daukaka duk da bai amsa ba nasan yaji dadin adduar,na

dau akwatin nayi cikin gida Allah yasa ba kowa a tsakar

gidan ni da mama muka bude muna ganin kaya nayi

mamakin kayan domin suna da yawa bayan haka kuma

zasuyi tsada english ne kala bakwai sai jakunkuna da

takalma sai rigunan barci masu kyau sai wani zobe cikin

akwatinsa mai kyallin gaske,na dauka ina dubawa zobe

ne na zinari mai nauyi akwai stone mai kalar ruwa gargar

tamkar kankara in ka kura ma stone din ido zaka ga an

rubuta A guda biyu daya kan daya nace la mama duba ki

gani harda farkon sunana tace kin gode sai dai fa in har

irin na 'yan uwanshi ne to ba zaki sa su ba na dan bata

rai sannan nace bama iri daya bane na tashi na soma

gwadawa duk wanda nasa sai su zauna min tamkar a

jikina aka kerasu,da yamma ina zaune a daki ni dai bani

son zuwa aiken yayanmu domin na tsani ganin Mimi

nasan ma wulankanci zasu min Sagir ne yace yayanmu

na kirana dama a shirye nake ina son inga ko ya manta

ne in share in ya tambayeni daga baya sai nace na

manta ne nima haka na tashi na tafi dakin mama na

sanar da ita tace sai na dawo,su hudu na samu na

gaishesu suka amsa dayan cikinsu yace Maska wannan

ma sister ka ce?yace ban sani ba ya wani daka min

tsawa yace shiga ciki ki dauko jaka adidas kizo ki wuce

kin wani tsaya kina kallon mutane na shige

dakinbarcinshi da sauri ya juya gun abokanshi yana ce

mishi dj bana son aboida kuke min baku san yaran nan

da raini ba sai taga kamar sa'aninta ne mu wani yace to

Nasir fa da zai auri Mami kanwarka?yayanmu yace ai

yaga zai iya ne sannan nace mishi kar ya yarda ya kawo

min karanta raina shi ga manyan babys a gari yazo zai

nace gun wadannan yaran,jikina yayi sanyi na sabi jaka

na fito ya dubeni yace kikai mata saura ki dade na fito

ba tare da ya bani kudin mashin ba, gidansu Amira na

shiga bayan mun gaisa da mamansu tace min tana cikin

dakinta na shiga tace daga ina haka?nace ina zani zaki

ce ta ce to sai ina?na zauna bakin gado na ajiye jakar a

kasa na dubeta na nace don Allah zaki raka ni?tace ina?

nace malali gidansu Anty Mimi tace to jeki ki gaya ma

mamanmu sai na shirya kafin ki dawo nace to amma fa

kece zaki biya mana kudin mashin tace wane irin ni zan

biya nace to bai bani kudin mashin ba gashi har yana

cewa inyi sauri ni kuma ban fito da ko sisi ba na fito gun

mamansu na sanar da ita tace sai mun dawo muka fito

muka hau mashin sai malali

Yanda na zata hakan ce ta faru domin da Mamnsu wato

Haj Laure ta ganmu haka ta hau zaginmu wai mu juya da

kayan ba'a so inshi ba zai kawo ba to ya bari,Anty Mimin

itace ta hana tace mu kawo Amira tace ki barshi mana

sai mu maida Anty Mimi tace ke bani son rashin kunya

Amira tace ba rashin kunya bane ance ne mu juya dashi

na dubi Amira nace don Allah ki rufa mani asiri Amira ta

jani zamu juya Anty mimi ta biyomu ta fisge jakar ta juya

ni dariya ma abin ya bani,muna jiran mai mashin wani

yazo da mota a gabanmu ya tsaya ya dube mu yace

kuzo muje yanmata ina za'a kaiku?kafin nayi magana

Amira tace unguwar rimi na dubi Amira nace kina hauka

ne?tace zauna nan in ba zaki ba sai dai kiyi ta zama

anan yace magana fa nakeyi nace ku shigo muje nima

can na nufa,nace nidai ba zan shiga wannan motar ba

Amira ta bude baya ta shige sannan tace ai kina da

kudin mashin ko?nan na tuna bani da ko sisi nayi

tsaki,saurayi mai mota yace yar kanwata shigo mana jan

ajinki ya burgeni kuma na yaba,na dubi Amira ta wani

kame tamkar motar kanin babanta nace bani naira dari

tace nace maki bani da kudi ko?in zaki shiga ki shigo

dole,dole na shiga motar nima bayan na shiga yace yi

hakuri kanwata dan dawo nan mana na koma don

surutun ya soma isata yaja muka tafi,sannu a hankali

yake jan motar sunana ya tambaya nace mashi Amira,

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

Amira da take baya ashe taji tace yar iska sunanta Iman

yace yauwa mai sona fada min gsky Amira ta cigaba da

cewa xan kaika har gidansu yanda tace maka haka takeyi

ma samari tace sunanta Amira kuma ta yi masu

kwatancen gidanmu ina jinsu ban kuma magana ba sai

su keta faman labarinsu,muna zuwa kofar gidanmu ya

faka a daidai lokacin yayanmu yayo ma abokanshi rakiya

kallon motar ya tsaya yi da sauri na bude na fito daga

motar ido hudu mukayi da yayanmu nan da nan fuskarshi

ta sauya yayi murtuk tamkar bai taba dariya ba koda dai

dama ban taba ganin dariyar tashi ba,a hankali yake

tahowa har inda muke nayi zaton zai mare ni ne sai

naga ya wuce ya isa gun motar daidai kofar dreba ya

kwankasa gilashin motar,ina zaton Amira da bata fito ba

ita ce tace masa yayanmu ne sai naga ya fito daga cikin

motar da sauri sannan ya mikawa yayanmu hannu gami

da sallama,yayanmu nokewa yayi yaki bashi hannu sai

dai ya amsa sallamr a ciki ya dubeni yace menene

dalilinki na shiga motarshi?nayi shiru shi kuma saurayin

mai motar sai cewa yayi yallabai ai ina sonta ne kuma

banzo da wasa ba,sai ya kara daure fuska sannan yace

ita me tace maka?yace bamu yi magana ba

tukunna,yayanmu yayi mishi wani kallon wulaknci sannan

yace kar na kuma ganinka a gidan nan ka fahimceni?

yarinyar nan krt zatayi ku ne masu hure ma yaran

mutane kunne suki krt bani bukatar sake ganinka

understand?so kama gabanka ya juyo ya kalleni wata

uwar harara ya sakar mani ba zaki wuce a nan ba? Da

gudu nayi cikin gida.

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

Tara daidai na dare na gama shirin kwanciya kamal ya

shigo ya dubeni ke Iman yayanmu yace kikai mashi

tea,ban tsaya dogon turanci ba na fito falo dakin mama

na shiga ko zan samu ta dafa ma Alhj bata cikin dakin na

fito falo kan tebir naga ples din shayi na duba naga

akwai a ciki yar butar shayi na dauka na zuba na dora

kan tiranshi na hada da kofunan na fita sam na manta

ban sanya hijabi ba rigar bacci ne a jikina mai hawa biyu

sai hular hijabi nayi sallama da kyar ya amsa na dan

dube ahi fuskarshi a daure cikin tsoro na shiga zaune

yake kan kujera mai zaman mutum biyu ya dora kafarshi

suna kan teburin tsakar dakin irin dan karamin nan na

rage tsahona na ce gashi ya zuba min harara na ajiye da

sauri na zan fita sai naji yace ke zo nan na daqo ya

dubeni yace zauna na zauna kan kafet cikin hankali ya

sauke kafafuna daga kan tebur din ya zauna da

kyau,Amina naji ya kira sunana a hankali yar naji cikin

jikina gashi ya iya fadar sunan a gajiye na dubeshi

sannan na amsa yace na lura dake kina shaawar ganin

bacin raina ko? (hhahhh su yaynmu anyi nisa) na girgiza

kai alamar aa yace haka ne mana(a raina nace to me

nayi maka?) Yaci gaba in ba haka ba so nawa zance miki

bani son kina kula samari ko kema auren kike so?nace

aah yace kar ki damu in ma auran kike so to sanar dani

don akwai wani da yayi mani maganar yana sonki,gabana

yayi mugun faduwa a raina nace ni kai nake so ya kara

tausasa murya yace in har kina so ya kara tausasa

murya yace in har kina so ki kwantar min da hankali to ki

tsaya kiyi karatunki kar ki damu da su mami basu san

matsalolin da ke cikin auran ba,kinga kema karamar

yarinya ce baki san komai game da aure ba undaerstand

me?na gyada kai alamar eh yace to yi min alkawari da

bakinki cewa ba zaki kula kowanne da namiji ba ko bana

garin ko bana kasar har sai na dawo na bada izini ba

tare da wani tunani ba nace nayi alkawari ba zan kula

kowa ba ko ba kanan yace promise nima nace promise

yace good ya saki fuska tashi kije ki kwanta na mike sai

da naje kofar fita na juyo shima ni yaje kallo ga

mamakina sai naga ya min murmushi mai tsayawa a rai

na saki labulen na tafi zuciyata na dauke da murmushin

da yayi min,haka na kwanta ina juya maganganun da yayi

min musamman in da yake cewa in har kina so ki

kwantar min da hankali to ki daina sauraron samari me

yake nufi?wata zuciyar tace min abokinshi mana haka

nayi ta juyi har barci ya daukeni

Washegari da safe ina shirin tfy comp Jamila da Sagir

suka shigo da gudu suna rige rigen fada min kiran yaya

Kabir na daka musu tsawa nace kai ba makaranta zaku

je ba?suka ce ai mun fita sai yayanmu yace kizo nace

yayanmu babba?suka ce a'a Kabir,na dan yi tsaki sannan

nace kuce gani nan,sagir yace anty kizo muje yace in

kika zo muje yace in kinzo zai bamu naira 100 nace ku

bace min da gani a nan suka fita sai da na gama sannan

nayi wa mama salla.a sannan na fita,na dauka ya tafi

gun aikinshi sai na ganshi a kofar dakinshi sai faman

duban agogo yake yi na isa gurin shi fuskata babu

walwala nace ina kwana?bai amsa ba sai dubana yake

yana murmushi yace da raina ya baci domin kin shanya

ni amma yanzu kin wanke min zuciyata na dubeshi nace

kamar yaya?kinyi dressing irin nawa,na dubi kayan

jikinshi kampala green nima haka sai naji tamkar na

koma na cire ya dube ni zo muje na saukeki nace ka

barshi yace duk da nayi latti sai na kaiki,dole na shiga

muna shirin fita yayanmu ya shigo shi da wasu

abokanshi cikin kayan training duk da kaninshi ne sai da

gabana ya fadi yako tsira mana ido sai ya tsaida motar

ya dubeni yace kin mani shara?na dubeshi yayi wani

kicin kicin nace a'a yace to fita ki min bai saurari amsata

ba yayi gaba na dubi yaya Kabir nace to kaji fa abinda

yace,yaya Kabir yace don Allah ki rabu dashi bari mu

tafi,nace wai ba haka a tsakaninmu haushi ya kama yaya

Kabir yace toko dai yana sonki ne?nace kaji ka da wata

magana kaima kasan ko mata sun kare yayanmu ba zai

soni ba yace saboda me kikace haka?nace ni nasan bani

da kyau kuma gani baka yayi murmushi sannan yace

ganinki kenan kina abubuwa masu fizgar hankali so ni dai

yanzun ki yarda na fito sai a hada da nasu Mami,haushi

yasa na bude motar na fito shima yayanmu na sameshi

ya cika dam ina shiga ya dube ni duban wulakanci yace

me kika tsaya yi a gunshi?nace ba komai ya nuna ni

yace look ba zaki min yawo da hankali ba bani son na

kara ganin kin shiga motar Kabir kina jina?ya daka min

tsawa nace to,ya fita na shiga gyaran daki ina mamakin

wannan ikon Allah..

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

Ina cikin goge TV ya shigo yana waya ya zauna kan

kujera yanda naji yana amsa wayar ne yasa naji duk

bakin ciki ya kamani ko bai fada ba nasan da Mimi yake

magana har yana cewa karki damu nima kin manne cikin

raina kuma ki saurareni in anjima da sauri na shiga

bedroom dinshi har lokacin wayar yakeyi ranar da takaici

na yini wata zuciyar tace min kina kishin banza kina

wahala bai san ma kinayi ba

Kwana biyu ni dasu yaya Abubkr da duk wani mai son

ganina in dai saurayi ne sai dai a waya ranar juma'a ina

zaune da yamma tsautsayin jin takaici ne yasa nace da

mama bari in shiga gun Amira ina isa daidai dakin

yayanmu shi kuma yana fitowa tare da abokinshi sun kai

su bakwai daya ne naji yana cewa ango ango to Maska

wata nawa aka sa yayanmu ne naji ya amsa da cewa

sati biyu suka sa da sauri na juyo cikin sa'a muka hada

ido shima sai naga yayi wani iri tamkar bai so naji

zancan ba wani abu mai nauyi naji ya tokare min wuyana

kirjina kuma ya hau zugi da kyar nake janyo numfashina

kokari nayi naci gaba da tfy amma bana ganin gabana

sosai jirin da naji ya soma dibana shi yasa na juyo na

koma gida ikon Allah nema ya kaini kofar dakinmu a nan

na zube ban kuma sanin in da kaina yake ba na dai

farfado na gani a gadon asibiti Mama tana zaune a kan

kujera tana rike da hannu na wanda aka sa min karin

ruwa ta min sannu na amsa da kyar a hankali na soma

tuno abubuwan da suka faru shi kenan yayanmu ya zama

na Anty Mimi ko shakka babu yana mutuwar sonta,na

tuno wata rana ina shara a dakin yaynmu har na gama

zan fita yace nazo nan na juya na koma nace gani yace

baki sa turaren daki ba nace na mance ne,na shiga

bedroom din shi idona ya sauka akan wani kyakyawan

frame kamar kaida in dai zan shiga uwardakin yayanmu

to ba abinda nake fara kallo sai wannan frame din yana

da kyau ga dauakar hankali gashi saitin kofa da ka shigo

shi zaka fara gani,na manta batun turaren daki na tsaya

duban frame rubutun jiki yan kanana shi yasa ban taba

karantawa ba amma lokacin sai na hangi rubutun saman

kamar hausa akayi nayi mamaki frame mai kyau da

shegiyar tsada irin wannan amma da hausa na ce kai yau

sai na dauko shi na karanta duk da wane yare ne na

duba dakin ko naga abinda zan taka don yayi sama sosai

ba wani abu mai tsawo sai tebur karami kuma na glass

ne na jawo shi a hankali na taka daya ke nima ina da

tsawo na dauko,tabbas da hausa akayi rubutun a saman

an rubuta:

Zinariyata Zuciyata ta jima tana begenta daga lokacin da

idanuna suka fara ganinta,na tsunduma a sonta duk

karancin shekarunta duk sanda na dubi idanunta sanyi

kasala sha'awa suna gajiyar dani bare in naji kamshinta,a

lokacin da nayi nisa da ganinta sai barci ya kaurace ma

idanuna sai tunaninta bana jin dadin wani girki sai nata

Allah ka azurtani da aurenta domin na samu ni'imarta

har ka azurtani da 'ya'ya masu albarka daga gareta

(A)amin.

jikina yayi sanyi sai dai abin daya bani mamaki shine

yanda (A)a cikin (A)tamkar irin na zoben da yayanmu ya

bani a cikin kayan tsaraba nace kai kilan ma ba (A)guda

biyu ba ne wani tambarin ne na wani camfanin a can

England din,na dubi fulawoyin dake jikin frame din da

tsuntsaye masu ban sha'awa ina cikin juya shi ina cewa

nasan Mimi yake nufi,shine Mami tace min baya sonta

ashe ma ya jima yana sonta gashi yace tun tana

karama,ina cikin tunani naji yayanmu daga falo yace baki

ga turaran bane?nan jikina ya soma rawa ina kokarin

maida wa ne tsautsayi yasa na goce,frame din ya fado

sai kan tebur din glass ji kake tats,jikina ya hau bari na

soma tsuma tamkar mazari,na dauki frame din baiyi

komai ba teburin ne ya fashe naga an daga labule da

sauri na dubi kofar yayanmu ne tsaye nayi duba zuwa ga

fuskarshi ya wani daure fuska me ya kai ki gurin frame

kina ganin sirrina ko?hawaye ya soma zarya a kan

kumatuna nace a'a zan goge ne yayi kura ya daka mani

tsawa yi min shiru kuma sai kin biya dukkan abinda kika

fasa min,na durkusa kan gwiwoyina na soma cewa don

Allah kayi hakuri yace ai zaneki zanyi yanzun nan

muryata tana rawa nace please yayanmu ya dubeni cikin

wani yanayi mai wuyar fahimta sannan yace gyara min

wirin ki wuce,ban san kan kwalba nasa gwiwata ba sai da

na gama gyra dakin sannan naji zafi na duba.kamshin

turaren da naji shi ya dawo dani cikin hayyacina ko ba'a

fada ba nasan yayanmu ne ya shigo Asibitin nan ban

gama tunani ba ya kwankwasa kofa ya shigo dama fuska

ta kofa take kallo don haka yana shigo dani muka soma

hada ido sai naga tamkar an kara mashi wani kyau....

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

Na lumshe ido sai naji wasu hawaye sun zubo min ina

jinshi suna gaisawa da mama ya tambayeta jikina tace

da sauki ban ma san har na kwana ba sai da naji yace

tun jiya bata tashi ba?mama tace dazun nan ta farka ina

mata magana banji ta amsa ba nayi mata sannu ta amsa

bata kuma magana ba sai hawaye da ke zuba daga

idonta shiru yayi na dan lokaci sannan yace bari inga

likitan mama tace yanzun nan babanku ya tafi gurinshi

tun jiya ma yace ciwon zuciya ne yake son kamata ni na

rasa mai yarinyar nan ta nema ta rasa da har ta sa

kanta cikin tunani,muryar yayanmu naji cikin sanyin shin

nan yace ai maman Sagir cututtuka sunyi yawa ba sai

mutum yana wani tunani ba Allah dai ya sauwake ya

juya zai fita sai ga a

Alhj ya turo kofa yayanmu ya matsa Alhj ya shigo yana

ma mama bayani sun tabbatar da zuciyata na son ta

harbu sannan yace su tuhumeni ko akwai wanda takeso

ne ko abinda ya shafi haka yayanmu yace Alhj bari nima

na ganshi likitan sukace to lokacin Alhj yasa an tashe ni

zaune ni kaina nasan na rame sosai cikin kwana daya

yayanmu ya dubeni yace sorry Iman na dubeshi yaune na

fara jin ya kirani da Iman na daga kai alamar

amsawa,yace maman Sagir me taci?mama tace bata ci

komi ba yanzu ne dai zan hada mata to amma tace sai

tayi sallah tukunna,ya dubeni zaki iya yin sallar ne?nace

eh tare da taimakon mama nayi alwala muna fitowa daga

bayi yayanmu yayi mana sallama yace da daddare zai

dawo haka na cigaba da jinya har tsawon kwana uku

kullum yan dubiya suna zuwa,Amira da Mami nan suke

yini haka yayanmu da yaya Kabir nan sau uku suke zuwa

sai dai duk lokacin da yayanmu yaga yaya Kabir

haushinshi yake ji, gudun fadan alhj yasa kishiyoyin

mama suka zo sau daya kuma basu kawo mana abinci

sai dai anty Yagana da maman su Amira kayan ciye ciye

kam yayanmu ya kashe kudi har Anty Mimi ya kawo ta

gaisheni nasan dai dole tazo ba don son ranta ba,niko

ban ma ji wani dadin zuwanta ba don ma kadan ya rage

ciwona ya dawo musamman ma da naga sun sa anko

yellow kampala sun man kyau sai dai kishi da ya sani

gaba,ban san yanda akayi su yaya Abubkr sukaji ba sai

dai ganinsu nayi yaya Ibrahim ne yake ce min babana

yana nan zuwa,yace a gaisheni naji dadi har ina

tambayarshi yaushe zaizo?yace kilan yau ko gobe nace

kilan a sallame ni yau ai a ranar aka sallameni kafin sati

na dan girgije,yan skull dinmu na comp ma sun zo duba

ni randa na cika kwana goma ranar na koma zuwa

makaranta lokacin saura kwana hudu bikin yayanmu su

Mimi duk sun damu da bikin sai rawar kai suke yi har

Mami na cewa da ban warke ba bikin ba zai mata dadi

ba sannan suna son kudi gun yayanmu nice ma zan

amsar musu nace ke Mami ki rabu dani ba wani kudin da

zan tambaya a raina nace in baku san dan dole zan

zauna a garin nan ayi biki ina nan ba da ba dan mama ba

zata yarda ba da naje tudun wada gidan kawuna sai

angama sai na dawoa dare yayanmu ya aiko nazo lokacin

ina zaune a falo ni da mama tana nuna min memo data

buga da sunansu au Jamila da Sagir sai agogon bango

suma guda dari wai in bashi ince ni na buga na dauki

guda daya ina dubawa hotunansu ne sunyi kyau sosai na

hadiye wani abu da yazo min wuya na dubi mama nace

sunyi kyau amma kin sha kudi tace yaya za'ayi ai yana

da mutunci sosai Abdulrahim na ce umm waya baki

hoton su?tace gun Kabir na amsa na rike hawayen idona

lokacin da naga sunana a matsayin wacce ta buga kafin

nace wani abu ne jamila ta shigo anty Iman kizo inji

yayanmu na danyi tsaki nace kice kaina na min ciwo ba

zan iya zuwa ba a raina nace ba zanzo ba tunda ka

kama matarka a hannu kasata aikin,Mama ta dubeni kije

mana Iman kije mishi da agogunan nace banjin dadi ne

mama tace daure na mike na ciccibe kwalin agogunan na

ce bari na kai wannan sai na kuma zuwa na dauki dayan

da kyar nakai dakin nayi sallama na shiga yana zaune da

kaya a gabanshi fuskarshi babu walwala ya dago kai ya

dube ni yaya kai din na dan lumshe ido sannna nace da

sauki na kula tun da nayi rashin lfy sam baya son yimin

tsawa ko fada ya dubi kwalin dake gabana yace menene

wannan?mYaya gudummuwata kenan a ba jama'a. Ina

zuwa na koma na dauko dayan kwalin na samehi yana

duba wa ya dubeni yace amma sunyi kyau mun gode,na

danyi yake nace um ya turo min kayan gabanshi yace ga

naki kayan bikin harda ankon,nace ai Baba yayi mana

ankon,yace duk da haka ki dauka ina son ki kaima telanki

da yake maki dinki don ya iya sosai nace yaya Sulaiman

ne ya ma samu aiki yanzu bai cika zaman shagon ba sai

dai yaranshi,yace to kikai inda za'ayi maki mai

kyau,takalman ki jakunkuna sai yau za'a kawo anjima

kadan gidan Nasir na manta su nace na gode ya kuma

duban hannuna ke bakiyi lallen bane?nace eh yace kiyi

gobe zanzo na kaiki saloon mamaki ya kamani nace ko

dai yana zaton da Amaryar yake magana ne?ni da ban

taba shiga motar shi ba,na boye mamakina nace ai bana

sa relaxer kitso nakeyi yace to kiyi kitson kinji ni?nace

to.kaya ne kala shida less biyu super biyu sai material

daya sai shadda,shaddar din kakkiya ce ta sha aiki riga

da zani sitayal din ya hadu ga shaddar mai tsada,turare

kala uku masu kyau da mayukan shafawa sai sarka da

'yan kunne,Mama ta dubeni tace oh ni Habiba wannan

hidima tayi yawa, shida ke cikin biki kayan nan Iman

ba'a karbe su duka ba bani wayata gata can a chargy,na

dauko mata shi ta kira tana mishi korafin yawan kayan

bansan me ya ce mata ba naga tayi murmushi tace ai

kanwarka ce kowane ai ta maka kabiyata kenan?can

kuma tace to shi kenan an gode Allah yasa ayi wannan

biki lfy ya kuma bada zaman lfy.Washe gari na shirya sai

tudun wada na kai dinkunan a can nayo kitsona da lallen

filawa mai ratsin ja,gidansu Amira na biya tace min

zakije Arabian day din ne yau?nace Mami tay min

magana amma da kyar in zani kinsan bana shiri da

Amaryar,

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

Amira tace indai ba zakije ba nima ba zani ba dama

domin ke zani nace to bari in zani zan maki waya ba

karfe hudu bane?na duba lokaci a wayata karfe biyu da

minti arbain nace bari na shiga gida dama dinki nakai

tudun wada,Amira ta dubeni tace name kuma ba kinyi

anko ba?nace jiya yayanmu yace ga nawa ankon dana

duba sai naga ba anko bane ya dai minne ne kala shida

harda takalma yau da safe ya bani takalman kala

uku,Amira tace gsky jininku ya hadu,sanda baki da

lafiyannan kar ki ga yanda ya damu ba dan munsan

yanayin rayuwar shi kenan yin alkhairi ba damin zargi ko

sonki yake na kai mata duka nace me zukekiyar mace

kamar Mimi me zaiyi dani?Amira tace Iman kina da kyau

amma sihirtacce ne sai na kusa dake komai sonki ko

kuma yasan kyau zai gane kiga Mimi mai mata kallon

gane muni zai ga muninta don tana da goshi da

kuma....na katse ta mu bar zancan nima ai in an kura

min ido za'a ga muni nawa,Amira tace Allah baza'a gani

ba sannan ne ma za'a ga kyaun ki nace um bari na shiga

gida. A gurin Arabian day kowa yayi kyau Amarya cikin

jallabiya baka da dan hijabi tana zaune a gun da aka

tanadar mata muka shigo nima sanye nake cikin

Jallabiya mai hawa biyu baka da ja hijabina da takalmina

jajaye ne, Hijabin dan karami iya wuya su mami da Anty

Mariya da kawayenau sai kai kawo suke ni kam guri

guda na kame mai kyamarar sai daukata yake tamkar

nice Amarya,ga masu Hotuna,Amira tace kai Iman kin

tafi da imanin masu hoton nan sai ke suke dauka kafi n

inyi magana Bilkisu tazo tace kai bafa wannan bace

Amaryar ba kun ganta tayi maku kama da Amare?nan

suka juya suna daukar ko ina haka taro ya tashi lfy ba

tashin hankali,washe gari sister day da safe yayanmu ya

aiko nazo dakinshi na same shi ya dubeni me kike

yanzu?nace ba komai yace to abokaina ne na england

yau zasu iso ina sonki shirya masu abinci kaloli masu

dadi don gidan Nasir zan saukesu kamar nawa ake

bukata?ko muje kasuwar tare in yaso sai ki duba

abubuwan da zakiyi amfani dasu gaba daya a wajen

girkin?nace to bari na sanar da mama yace shima bari

yayi wanka,cikin riga da wando na material ruwan

madara da filawoyi jajaye dan hijabina dan karami sai

takalmi sai abinda ya kamata na siya da kulolin girkin da

zan masu har da na sha ina tsaye jikin motarshi ya fito

daki sai da ya shiga su Sa'a da Bikisu da Maryam

kanwar anty Mimi dukkansu ni suka tsura ma ido na

shige mukayi gaba,ba wani hira muka yi ba ya dai sa

wakar tashi dakusan duk kullum sai naji ta a dakinshi tun

ina jin haushin wakar har yanzu nima ina sonta kuma

nama sai album din wakokin mata celine dion ina

wakokin don sanyin muryarta,wayata ta soma kidan kuch

kuch hota hai na kai hannu zan dauka sai naga yayanmu

ya dafa wayar ya dauka ya duba sunan Amira ya gani sai

ya mika min nayi ajiyar zuciya sannan na amsa

hello,Amira yaya dai?tace kina ina ne?nace muna hanyar

kasuwa ne menene?tace na sha kina gida ne na

shigo,nace bana gida in na dawo zan shigo gidan muyi

aikin abincin baki tace to sai kin dawo.

Sayayya mai yawa mukayi komai nace biyu sai yace na

dau uku,gidansu Amira ya saukeni ta fito muka kwashe

kayan,mun shirya abinci kala kala dana sha a sabbabin

kulolin da muka siya muka shirya muna gamawa muka yi

wanka na shiga kenan don nasa kaya yayanmu ya kira ni

nazo yace kun gama?nace eh yace to ga musa dryva nan

ya kaiki gidan Nasir ni kuma zamuje mu dibo su sauran

minti biyar su shigo KD daga Lagos nace to,banyi wani

shafe shafe ba nasa atamfa charas babba riga da siket

ne dinkin shot play sai karamin gyale muka jera abincin

nace Amira tazo muje tace aah ba ruwana da wannan

yayan naku zai iya kado ni,nayi dariya nace shi

kenan,nayi kusan minti talatin da zuwa sannan suka iso

cikin harshen turanci suke magana nima na gaishesu

cikin yaren nasara,Nasir yace ko inyiwa Mami waya ne

tazo ta taya yarinyar ne?ya harareshi yace ban ce ba

nikuma bayan sun zauna na gabatar masu da kayan ciye

ciye da shaye shaye na gida dana company,wani shima

bakin fata ne duk sanda na dubeshi sai mun hada ido

dashi haushinsa ya kamani can kuma wani daga cikinsu

yace Maska wannan itace Amaryar?yace a'a ita kanwata

ce sai yace to zaka bani kanwarka?don tana da kalar

asalin yan Nigeria yayanmu ya daure yace baya son

wannan maganar bakin fatar dake kallona yace Maska ni

zaka ba wannan mai kyaun din,don bana neman wata

kasani,y hiayanmu bai kuma magana ba ya dubi Nasir

yace bari na kaita gida na dawo,ya dubeni tashi muje na

dube su nayi musu sallama, a mota yace in zaki fita ki

daina shafe shafen nan na dubeahi nace ban shafa komi

ba sai hoda,yace duk inda kikaje sai ance mun ana sonki

ni kuma krt nake son kiyi ni dai nayi shiru yace kin tuna

alkawarin da kikayi min ko?nace eh yace to kar ki yarda

ki yi wasa da cika alkawari kin jini?nace e.A kurarren

lokaci muka isa gun Sisters day Angoma bai zoba na

tambayi Mami tace min yayi ma Amarya waya yana tare

da baki muka zauna,nanma ba laifi bikin yayi kyau ranar

ne akayi sa lalle banje ba, washe gari lunching a

hamdala hotel za'ayi sanye nake cikin dogayen riga na

shiga dakin yaynmu dan amsa kkranshi yace zauna na

zauna a kasan carpet ya dubeni yace yau wane kayan

zakisa,nace anko zamu sa yace to kar kisashi kisa sky

blue din less din nan,na gama kanki ba tare da wani

tunani ba na zame dan kwalin kaina kananan kitso ne

2step mai zigzag,yace to rufe ki shirya sosai ya dubi

dakinshi yace ga kayana nan dukkan abinda kike so ki

dauka na baki ki dauka nayi shiru na sunkuyar da kaina

ya taso ya tsugunna gabana Aminatu ya kira ni a hankali

cikin sanyin nan nashi na dube shi nidai da zance frame

din nan nake so amma sai nayi shiru ya kuma kiran

sunana na dube shi yace kina son Fridge?nace a'a TV

fa?nace a'a,Radio fa?nace a'a yace to me kike so?na

dubi hotonshi yana sanye da farin JC mai ratsin ja yayi

tsalle zai kama kwallo ina balain son hoton ya dube ni

shi kike so?na kada kai alamar eh bayan shi fa?nace ba

komai ya mike ya ciro min hoton ya hado da wani shima

mai kyau cikin jan JC kan kujera ya zauna sannan ya

kama hannuna gabana ya fadi naji wani yarr a jikina ya

rike yatsuna da zoben nan yake jiki wanda ya kawo min

tsaraba kar ki rabu da wannan zoben komin wuya kinji?

kasa magana nayi,yace wannan lallan ya min kyau waya

miki?kafin na bashi amsa sai akayi sallama gami da

shigowa gaba daya tsoro ya kamani da na juya naga

Anty Mimi itama tsoron ne da mamaki a kan fuskarta na

dubi yayanmu shi ko namijin duniya ko a jikinshi ya saki

hannuna yace Mimi lfy na ganki yanzu?ta juya da gudu

tana kuka yace me aka mata oho,yayi tambaya ya ba

kansa amsa na mike da hotuna sai nayi gidan su Amira

ban koma cikin gida ba ita ko Anty Mimi dakin Haj Yaya

ta nufa da kukanta da komai,ta sanar da hajiyan komai

haj yaya ta cika tamkar zata fashe ta dubi mimi tace

kince yana rike da hannunta?Mimi tace sai kallon juna

suke yi,haj yay tace lallai ma yaron nan jiya fa haka su

Bilkisu suka ce min sun ga ya shiga mota da ita banyi

maganin abun ba bari in kirashi,ta soma daddana waya

tana fadin kannanshi bai taba sa su a motarshi ba sai

wannan bakar mummunar yarinyar,ta soma magana kazo

yanzun nan ta kashe wayar taci gaba da fadin sun

asirceshi shima kamar babanshi na shiga uku ni Murja

tsakanina da Habiba Allah ya isa ban yafe mata

ba,yayanmu yayi sallama ya shiga dakin tana zaune kan

kujera sai cika takeyi ya ballama Mimi harara sannan ya

shiga ya zauna,duban wulakanci ta mishi sannnan tace

yanzu kai saboda Allah me ke tsakaninka da yarinyar nan

Iman yar karama da ita shine ta ke juyaka ta shanye ka

nan gaba ma kila kace aurenta ma zakayi ko?ya

sunkuyar da kai kasa bai amsa mata ba tace jiya ina

kukaje?yace Haj waya kawo maki wadannan kananan

surutan ne?nifa mutunci ne tsakanina da yarinyar nan

tana hidima dani sosai don Allah haj ki daina jin zancan

mutane yarinyar nan ita da uwarta suna da kirki kum....ta

katse shi an baka kaci a cikin abinci ba dole kace haka

ba na gaya ma ka koyaya ni zan mummunan saba maka

ta nuna Mimi wannan ita menene laifinta?da zaka sasu a

kasuwa sai kowa ya riga zabar Mimi kuma zanyi

maganin agola a gidan nan wayarta tayi kara ta dauka ta

duba ka dai ji na gaya maka ga babanku nan ma ya

dawo shi ne yake kira bari naje,ta dube shi sai ka bata

hakuri ai,tana fita ya galla ma Mimi harara sannan yace

ke ma zan yi maganinki bakina hada ni da uwata ba ya

mike ya zo kusa da ita wllh wllh in kika kuma hada ni da

ita sai na fasa auran nan ke ko an daura sai na sakeki

akan Iman,

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

Yayi waje ya barta cikin mamaki da tsoro koda haj yaya

ta dawo bata sanar da ita yanda suka yi ba ta dai ce ya

bata hakuri ya tafi haj yaya tace ai nasan zai rabu da

yarinyar nan sai ma kin shiga gidanshi Mimi tace haj ce

min yayi fa in anyi bikinmu da sati biyu zai tafi england

ya barni dama yaje dani don akwai masu mata a can,haj

yaya tace gsky haka za'ayi sai dai za'a yi fama kafin ya

yarda na ma huta hankalina ma ya kwanta baya kusa

bare in ta fargaba kar yace yana son yar iskar 'yar can

shima Kabiru zuwa zanyi na matsa mishi yayi auran

tunda yana aikinshi dama jira nake yayanshi yayi tukunna

cikin farin ciki Mimi ta fita ta san da haj yaya ta mishi

magana shi kenan zai yarda su tafi tare.

Da yamma na dawo daga gidansu Amira in da ta nuna

min gwaggwaro ba tace don Allah kisa yammata kowa

zai sa mu uku iri daya ?ami ta sai mana kalar namu

daban ne ma nace to in ya shiga da kayana zansa danni

ba anko zan sa ba tace me zaki sa?nace kayan gun

yayanmu,a falonmu su hajiyar maska ce da sauran

dangin alhj wadanda suka zo biki na rusuna na gaishe su

sannan na shiga dakinmu sai da naci abinci sama sama

sannan nayi wanka ina gaban madubi ina shafe shafe

waya tayi kara na dauka ga mamakina sai naga lambar

yayanmu ina da lambar amma bai taba kirana ba nima ko

da wasa ban kirashi ba nasa kunnena ban ce komai ba

inaji yace hello?sannan yace kina jina?a kasalance nace

umm da wani abu nake ji yana fita daga wayar zuwa

cikin kunnena yana raba ma jikina qani sako ne mai

wuyar fassara yace me kike yi yanzun?na samu kaina da

rike murya nace mashi ina shafa mai ne yace to kiyi

kwaliya da kyau amma kar ki kula ko wanne saurayi

kinjini?nace eh dukkanmu muka yi shiru bai kashe wayar

ba nima haka can yace to sai mun hadu a can ya kashe

na rungume wayar a kirjina ina jin tamkar shi na

rungume,soyayya kenan ban taba tunanin akwai ranar da

zata zo na shiga irin wannan halin ba sai gashi yanzu ina

ta nutso cikin kogin son wanda bai ma san inayi ba,Allah

kenan shi ne mai iya sanya fari ya koma baki.Kwaliya

sosai nayi tamkar ni ce amarya nasa lesa din da ya

umarceni nasa ya shiga da gwagwaron sai takalmi da

jaka su ma kalan gwagwaron ne ni kaina dana dubi

madubi sai da naji tsoro don kyan da nayi wayar Mami

na kira tace min tana can hotel din na kira Amira tace

min tana mota ne taga an gama kwashe mutane shine

taga kabir ta tambayeshi ni shine yace kamar ya ganni a

can ace mata ina gida ko fitowa banyi ba na mike na cire

gwagwaron na rike na fito falo dankwalin na rufa kaina

nayiwa mama sallama tace kai kin ko yi kyau,iman yau

dai ba zancan hijabi kenan?nayi murmushi na fita ina isa

harabar ajiye motoci duk an gama kwashe mutane sai

kawayen amarya na nufi waje da nufin in hau mashin sai

ga yaynmu shi da Nasir da wani abokinshi ya dubeni

yana daga cikin yayi min alamar in tsaya da ido na ko

tsaya ya fito ya kirani gefe yace kin ganki kuwa?kinyi

kyau fa nace nagode yace to ya baki tafi ba?nace ai

yanzun na fito shine naga an watse sai kawayen Amarya

yace kina da kudin liki ne?nace ina dasu amma ba

sababbi bane yace ok bari mu shiga ki amsa na bishi

abokanshi na zaune a falonshi ya shige uwar dakinshi jim

kadan yace Iman na ce na'am yace zo na shiga da

sallam ya amsa sannan yace shigo mana kin tsaya nan

kudi na gani a kan katifarshi ga yan ashirin ga yan

hamsin har zuwa dari biyar,ya dubeni dauka wanda

kikeso na sa hannu zan dauki ashirin ya dafe hannuna

sannan yace ki dau wannan yan dari biyu ne,ya samin a

tafin hannuna na gode na fada ina kallon idonshi,Man din

akwai sirrin kyau mai birgewa muka fito falo ismail ya

dubeni yace kai maska wannnan yarinyar ko dai kai kake

ma kanka farauta ne? Sai naga yayi kicin kicin da fuska

ya harari Ismail yace ku kun cika yarda girma ban da

yarda girma menene na cewa inayi ma kaina farauta?

bani son haka,jikina yayi sanyi zan fita yayanmu ki jirani

zan sa akaiki

Ina tsaye a bakin gate yazo ya dubeni menene kike bata

ranki?na dubeshi ba komai ya juya ya kira musa musa

direba yazo yace ina zaka na ganka da key a hannu?yace

haj ce ta aikeni gidan haj laure,yace to ka kai Iman gurin

party nan hotel yace to can na sami su Mami da kowa

yana ta hidimominsa inata neman Amira sai can ita ce

ma taganni muka zauna kujerun gaba na ce uwar sauri

shine kika wani taho Amira tace kar kiga laifina yayanku

Kabir shi yace min kina nan,nace don ni ce zan shirya

gun ba?dole na riga kowa zuwa yana sani don dai ya

dauke ki ne ta ce anji ki min shiru mu bar zancan.Biyar

saura ango da amarya suka zo less dina na gida irinshi

amarya tasa nace gara da na sa wannan din na dubi

ango sanye yake da wata dakakiyar shadda ruwan

sararin samaniya tamkar less din jikina ina cikin mamaki

Amira tace kunyi anko ke da ango sanya gwagwaron ki

nasa na gyara cikin raina nace kila ma don muyi anko ne

yasa yace nasa,mai gabatarwa ya fito yana kiran

kawayen Amarya bayan bude taro da addua suma

abokan ango an kirasu yawanci duk turawa ne,sai

kadan,Nasir da Mami aka hadashi tako sha harara gurin

ango can aka kira sunana Iman idris zata ba amarya

shawara ba don na iya turanci ba da nasha kunya

Amarya ta cika don haushi niko duk na tsargu Amira

tace don Allah tashi kije mana nace Amira bansan me

zance ba dadai tun a gida ne aka sanar dani da na

rubuta ana ta kiran suna na na dubi yayanmu yamin kar

da ido fuskarshi ba walwala na mike daidai lokacinda mai

gabatarwa yace ko bata nan ne?Iman Idris a hankali

nake tafiya har naje kan abinda aka tanada don hawan

mai magana da sallama na soma sannan nayi wa Annabi

salati kafin na soma bata shawara akan zaman aure na

kawo ayoyi da hadisai wadanda sukayi magana akan

zaman auren da hakkokin auran kansu.

Dana gama na sha tafi gun mutane na koma na zauna

haka akayi ta gabatar da komai har zuwa sanda zasu

ciyar da juna don kar in gani na dauko wayata ina ta

danne danne zuciyata kuwa sai zugi takeyi,can na mike

zan fita Amira tace ina zaki je gashi shalele na ta waka

yanxun za a soma rawa dole na tsaya suna shiga

yayanmu a tsaye yake baya rawa amma Amarya har da

juyi nace wawiya ba kunya ba jan aji nice na fara liki ina

ta zuba musu kudi cikin dauriya yayanmu ya juyo ya fara

zuba min na juya zan fita ya rike min riga amma ba

wanda zai kula don ta gefe ya rike ya dan matso kusa da

kunnena kar ki fita yanzun ki min rawa din dan ban iya

rawa ba nima ai ban iyaba Amarya ranta ya baci ta

dubeni ashe ita ta kula da abin da mukeyi guri ya kaure

liki wasu sun sha nice amaryar ne?ko ra'ayi ne?oho sai

ni suke ma liki gudun rikici yasa na fita abina na koma

na zauna,Amira tace yar gori a ina kika sami kudi kike

bari dasu?nace shi ya bani dubu ashirin kuma na like

musu abinsu Amira tace duka?nace a'a Mami ta iso

gunmu taja hannuna zo muje ki dan taka nace bana

rawa fa ta dubi Amira tace duk yanda suke da yayanmu

wai bazata yi rawa a bakinshi ba Amira tace ai ta basu

shawara yanda zasu zauna da juna,Mami tace yauwa na

tuna dazun me yace miki da naga ya wani karkato dai da

kunnank?nace ba zan fada ba Amira tace ashe kin lura

kema?sunyi kyau tamkar itace amaryar nace kun cika

sharri Mami tace to zamuje kiga hitunanku da masu hoto

sukayi suna ta saidawa a waje mu uku muka fita wajen

hall din gsky mami ga hotunanmu nan nida yayanmu

wani tare mukayi wani ni kadai wani shi kadai an barbaza

wanda yafi birgeni wanda mukayi da yayanmu ya dan

karkato yana min magana fuskarshi a sake ni kuma ina

murmushi fuskata tayi fayau idanuwana sunyi haske

kitsona ya zuba a kafaduna Duk masu daukar hoton nan

sai da na bisu na saye hotunanmu sannan muka koma

ciki nace kije kunnan gidado tace a ina zaki ganshi ta

fita kiran,ni kadai na zauna can ji an min sallama cikin

hausa da bata goge ba yace na zauna?nace zauna mana

ya zauna nadan dube ahi kamar na so na gane fuskarshi

yace baki ganeni ba?nace ban ganeka ba yace abokin

Maska da muka zo daga England nace ok na ganeka,yaci

gaba da cewa ina sonki amma Maska yace krt zakiyi?

nace haka ne yace toh zan jiraki mana nace kayi hakuri

dan zan dade ban gama ba,koyaushe zan jiraki,muna

cikin hirar ne can idona ya kai Ango da Amarya harara

ya sakar min na dauke kaina daga duban gunshi a raina

nace kai gara kai ka kama taka naci gaba da hirata jim

kadan wayata tayi kara na duba sai naga lambar

yayanmu da sauri na dubi gurin da yake bashi nan sai na

dauka nace hello ya katseni ki sameni a wajen hall din

nan gurin wayoyin nan ta kofar baya na fita da sauri can

bayan wasu furanni na ganshi na isa cikin fargaba ya

dubeni fuskarahi ba annuri yace me gayen nan yace

miki?nayi shiru ba zaki gaya min ba?ya daka min tsawa

jikina yana rawa nace yace ne yana sona,da sauri ya

dubeni sonki?.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta

Littatafai masu nishadantarwa

Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

Na gyada kai alamar eh yace oh my God bana sanar

dashi krt zakiyi ba?to naji me ke kikace mishi?nace nima

haka nace mishi ya dunkule hannunshi ya naushi dayan

hannun sannan ya dinga kai kawo a filin gun mamakin

shiga damuwar dayayi na tsaya yi a raina nace ya bar

amaryarshi yana yin abin da bai dameahi ba,kamar ya

san tunanin da nakeyi sai naji ya dawo gabana daf dani

yasa hannuwanshi ya rike kafaduna yace kar kiga na

shiga wannan halin kiyi tunanin inayin shishigi ne a cikin

abinda bai shafeni ba,no yin karatunki shine kwanciyar

hankalina kuma muddin na yarda wannan dan iskan ya

soma cusa maki ra'ayin sonshi to zai min illa domin

nasan Adam ba sanin yau ba yana da sa'a a rayuwarshi

zai yi wuya ya nemi abu bai samu ba tamkar ni yake,so

bazan yarda da huldarku ba,nayi shiru ina tunanin

wannan iko na yayanmu tunda yace tamkar shi yake sai

ma naji ya burgeni na dubi yayanmu nace to in dai zai

bari na gama karatuna why not na aureshi in kasan yana

da hali mai.....kafin na karasa sai saukar mari naji cikin

firgici na dube shi shima ni yake kallo ranshi a

bace,hawaye ya zubo min a kan fuskata yace kina hauka

ne?kike kiran wani ya aureki?sai kuma naga yayi shiru ya

juya min baya,Aminatu yaja sunan kafin na amsa sai ya

juyo da sauri ya zo guna ba zato sai gani nayi ya

rungume ni tsam tsam a jikinshi gabana yana faduwa

jikina na kyarma amma na kasa kwacewa ,nama kasa

kokarin kwacewar gwaggwarona kaina ya fadi gashina ya

bayyana a waje kitsona ya sauka a kan kafaduna ni kam

tamkar an jona ni a lantarki haka nake jina,cikin sanyin

murya yake magana,Amina bana son ki saurari Adams

zaiyi ma rayuwata illah nafi son sai kin gama karatu ne

kafin ayi maganar auranki,ki fahimceni ba ina nufin

hanaki aure bane a'a ina son kiyi krt ne,wani haushi naji

ya kamani domin a lokacin nayi zaton zai ce min yana

sona ne,yanda naga yayi mugun shiga damuwa sannan

ya kamani ya wani rungume yana faman ajiyar zuciya

tamkar jinjirin daya kwana uku ba tare da ya sha nonon

uwarshi ba ina fama da sonshi tamkar na mutu shi kuma

ya nan yayi aurenshi sannan ya zo ya wani rungumeni

yana min maganar banza nasoma kici kicin kwacewa ya

girgiza ni yace come on my sister ki.....kafin ya karasa

maganar da zaiyi sai jin salati mukayi akanmu,cikin

tsananin tsoro na juya su dayawa daga cikinsu akwai

kannanshi da Amarya da Haj Laure uwar Amarya da

wasu daga cikin danginsu,duk tsoro ya kamani,Amarya

tasa kuka na dubeshi shi kuma ko ajikinshi duban su ma

yake yi na tattare zani zan gudu sai naji ya sa hannu ya

riko ni.......Masha Allahu Alhamdulillah, mun Kammala

littafi na daya Mu hadu a littafi na biyu

jinjina agareki HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu

nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com

Kokuma ku kasance taredamu a facebook

https://mbasic.facebook.com/HAUSA-

Novels-389304544597988/?

_e_pi_=7%2CPAGE_ID10%2C737012347

Share

DOCUMENT CREATED BY

ZAHARADEEN SHOMAR

WHATSAPP ,,08168575100

0 Response to "Tawa Tasameni Hausa Novel"

Post a Comment