-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

MAZA JIYA Hausa Novel

MAZA JIYA Hausa Novel

 Mazan jiya 4

littafe na hudu

part 1

typing...... Suleiman Zidane Kd.

.


Sai da sarki dujalu ya shafe sa.a shida cif yana baiwa hursiya lbrin sadauki shaddadu na birnin kufa, amma ba ta kosa ba da jin labarin har ya zamana cewa dare ya raba amma ko gyan gyadi bata fara ba. Shi kuwa sarki dujalu a wannan lokaci bakinsa ya gaji da surutu kawai so yake yayi shiru don ya huta.

Dama ga tsananin gajiyar yaki gami da tsamin jiki da radadin raunikan jikinsa sun dameshi. Kwatsam! Sai Hursiya taji sarki dujalu yai shiru ga barin zance..

Cikin tsanani damuwa ta dubeshi ta ce ya kai dan uwana ina dalilin yin shirunka? Ina mai rokonka bisa girman iyayenmu daka cigaaba da bani wannan lbr mai dadi domin ina son naji yadda karshensa zai kasamce kamar yadda na ji na JARUMI HANTARU.

Koda jin wannan batu sai sarki dujalu yayi doguwae hamma gami da ,murmushi sannan ya dubi hursiyya yace haba yake yar uwata ai idan kika ce na ci gaba da baki wannan lbr har sai na je karshensa ba kiyi min adalci ba sbda koda zamu kwna muna yi ba zai kare ba.

Zidane kenan.

Ki sani cewa duk a cikin labaran uku babu HIkAYA mai tsawonta tunda gashi dai har yanzu ba ta kammalu ba.

Kiyi hkri idan mun yi tsawon rai nan gaba bayan wanna yaki na karasa miki wannan labari. Lallai akwai bukatar na kwanta domin na sami isasshen hutu da bacci domin na sami kuzarin domin iya ci gaba da yaki. Idan gari ya waye.

Koda gama fadin hakan sai sarki dujalu ya kwanta akan shimfidarsa yaja mayafi ya lulluba.

Faruwar hakan ke da wuya kuwa sai barci ya sace shi....,

koda ganin hakan sai itama Hursiyya ta kwanta akan tara shimfidar taja mayafi kuma ta rintse idanu domin ta yi barci, amma sai barcin ya gagara sakamakon tunani da fargabar yadda makomar wannan gagarumin yaki zai kasance idan anci gaba dashi a gobe ba ta sami damar rintsawa ba sai da suba ta kusanto..

Sai da gari ya waye rana ta take amma sarki dujalu da yar uwarsa gimbiya Hursiyya ba su farka ba daga barci...

Zidane kd....

A wannan lokacin gaba dayan mutanen nasu da ke sansanin tuni sun farka daga barci an yi kalaci kuma an gama shirin ci gaba da yaki sahun aljanu dabam da na mutane..

A wannan lokacin manyan dakarun sarki dujalu matinu da ratiju sun tsaya a gaban rundunar tasu suna jiran fitowar sarki dujalu domin ya bayar da umarni....

Tsakanin rundunar sun sarki dujalu da ta su sarki Hamraz bai wucce taku dari biyu ba sbda dama dukkaninsu abakin kogin na bahar sufiyan suka yada sansani., kowanne bangare suna hango abokan gabarsu...

Lokacin da matinu ta hango abokan gaba sun gama nasu shirin tsaf kuma sarki maharaz sadauki inmal da sadauki hibru na tsaye agaban rudunar tasu sun zobo ido izuwa ga nasu matinu kawai jira suke suga sarki dujalu ya baiyana agaba,,.

Cikin tsananin damuwa matinu ya dubi dan uwansa ratiju yace ja ruga izuwa tantin sarki ko lpya..

Kafin matinu ta gama rufe bakinsa tuni ratiju yaruga izuwa can tanti sarki yake..

Yana isa ya dubi dakarun da suka

Kewaye tantin don tabbatar da tsaron yace kuyi min iso a wajen sarki.

Kafin daya daga cikinsu tace kala sai suka jiyo gyaran ,muryar sarki...

Nan take sarki dujalu ya fito daga cikin tantin a cikin gagarumar shigarsa ta yaki kuma fuskaraa cike da annuri ya dubi rantiju cikin murmushi yace ya kai babban jarumi ka kwnatar da hankalinka kayi sani cewa yau ba rana bace ta gaggawa domin kuwa a yau ne za ayi tata kare!

Ko dai muyi nasarar wannan yaki ko kuma mai abonka gabar mu su samu wata kila ayi ragas ina mai tabbar muku da cewa yakin da muka yi jiya share fage ne ko kuma wasan yara akan wanda za ayi yau.:

(TAB IJAM! DUK BAKAR GUMURZUN DA AKAYI KUNJI PA WAI WASAN YARA YAKI CEWA TO KUBIYO NI MUJI YAWANNAN NA YAU ZATA KASANCE KENAN TIN DA YACE WANCAN WASA YARAN NE SULEIMAN ZIDANE KD.)

Yaune maza zasu gane kurensu. Yau ne kasa da taiku zasu sha jini suyi gyatsa, kuma a yaune tarihin jarumta zai kafa kansa a bakin teku. Maza ka koma can bakin filin daga ka gayawa rundunarmu cewa gani nan tafe yanzu kuma ina zuwa za a fara wannan yaki.

A jirani zan gana da yar uwata Hursiyya.

Koda jin haka sai ratiju ya juya da sauri kuma ya falfala da matsanaicin gdu domin yaje ya isar da wannan sako.

Tafiyarsa ke da wuya sai sarki dujalu ya juya ya fuskanci yar uwarsa Hursiyya suka kurawa juna idanu.

Nan take duk biyun idanunsu suka ciko da kwlla.

Hawayen sarki dujalu ne ya fara zubowa sannan nata. Sarki dujalu ya sa hannu ya share hawayen nasa yace yake yar uwata kiyi sani cewa wannan hawayen nawa bai zubo ba sboda tunanin zamu rabu ba. Tabbas ni na san ba zan mutu ba a wannan yaki to amma taki rayuwar ce bani da tabbacin zata tsira.

Babu mamaki wannan gani da nake yi miki shi ne na karshe.

Hanya daya ce nake zaton zan iya tserar da rayuwarki wato nasa a dauke ki yanzy a mayar da ke cikin birninmu domin ciki gaba da tafiyar da mulkin kasata.

A hakan ma bani da tabbacin birnin nawa zai ci gaba da wanzuwa..

Koda sarki dujalu yazo nan a zancesa sai wani sabon hawaye yasake gangarowa daga cikin idanu Hursiyya ta dubeshi tace haba yakai dan uwana ashe har ka manta da bayanin da nayi ,maka kenan a jiya da daddare??

Nifa bazan iya rabuwa da kai ba a yanzu sai dai a ci gabada wannan yaki a gaban idanuna idan ma mutuwa zaka yi mu mutu tare domin muddin bana tare da kai ba zan taba samun sukuni da kwnaciyar hankali ba...

Koda jin hakan sai sarki dujalu ya juyawa Hursiya baya a lokacin da shima hawayen ya sake subuto masa ya ce ai kuwa sai dai kiyi hkr domin rabuwarmu a yanzu ta zama dole..

Yana gama fadin hakan yaka tafiya ya nufi inda sansanin dakarunsa suke..

Koda ganin hakan sai goimbiya Hursiyya ta yunkura da nufin ta bishi ta gudu kawai sa taji an sureta an yi sama da ita tamkar shaho ya dau shirwa.

Wata irin iska mai karfi taji tana busota a sama. Koda ta dga kanta sama sau ta ga ashe wani aljanu ne mai suna BARZARU ya dauketa wanda ya kasance babban hadimin sarki dujalu.

.

.

.

.

..

MAZAN JIYA 4

LITTAFE NA HUDU

PART 2

 suna BARZARU ya dauketa wanda ya kasance babban hadimin sarki dujalu.

Koda Hursiya taga barzaru ya juya da ita baya don barin sansanin yakin gaba daya sai ta kwlla ihu, ta fashe da matsanaicin kuka cikin sbda ta gane cewa dan uwanta sarki dujalu ya shammace ta ne ya sa a mayar da ita can gida domin ta tsira da ga masifar wannan yaki.


Haka dai Hursiya ta ci gaba da ihu tama rusa kukan bakin cikin har aljani barzaru ya luluka da ita a cikin gajimare suka kule aka daina hangosu..


*     *    *

ACAN Sansanin yaki kuwa lokacin da sarki dujalu ya iso filim dagar ya tsaya a tsakiyar matinu da ratiju sai aka fara kallon kallon tsakanin rudunar tasu da ta su sarki Maharaz.


Kowanne bangare yana da jinsin mutane da na aljanu dukkaninsu a cikin gaagarumar shigar yaki mai matukar kwarjini da ban tsoro.


Wasu aljanun ma ko kallomsu mutum yayi nan take yake iya samin tabin hankali mai dakakkiyar zuciya zai tsure da gudawa ya cika wandonsa da iska.


A dai dai wannan lokacin ne mulaifa ta matso gaban inmal ta tsaya tana mai rike da takobi..


Page 9


cikin tsananin mamaki inmal ta dubeta yace yake masoyiya mene ne yakawo ki nan filin yakin alhalin sarki ma yace ki yi zamanki a cikin tanti har izuwa karshen Yakin?


Sa.adda mulaifa taji wannan tambayan sai tayi murmushi tace ai idan har na zauna a cikin tanti na bar masoyina yana fafatawa anan filin daga kuma na bar mahaifina yana gwagwarmaya ban cika jinin sarauta ba kuma ban yiwa soyayya adalci ba.


Idan har a wannan yaki zaku mutu to ina fatan na mutu tare da ku.


Koda Gimbiya mulaifa tazo nan a zancenta sai sarkin yaki hibru ya taho gareta domin ya rarsheta ya mai da uta can baya inda tantin sarki yake amma sai sarki Maharaz ya sha gabansa yace ka kyaleta.


Ai yana da kyau ta nuna gadon gidansu.


Cikin alamun tsananin mamaki da fargaba Hibru ya dubi sarki Maharaz yace haba ya kai abkna akan wane dalili za ka bar yarka gda daya jal a duniya tayi wannan yaki mai tsananin hadari alhalin ko sarrafa takobi bata iyaba?


Kuma bata da wani sihirin tsafi da za ta iya kare kanta.


Ko kana so ne ta hallaka a banza?


Suleiman Zidane kd)


dajin wannan batu sai sarki Maharaz yayi murmushi gami da yar guntuwar dariya sannan ya ce abinda nakeso da kai ya kai abkna ka zuba ido kawai zaka sha mamaki.


Sannan ina son ka gane cewa muddin mulaifa tana tare da inmal babu abinda zai sameta.


Page 10


gama fadin hakan ke da wuya sai sarki Maharaz ya wucce gaban rundunar da kimanin tafiya taku goma sanan ya tsaya.


Koda ganin hakan sai shima sarki dujalu ya wucce gaban tasa rundunar da kimanin tafiya taku goma sannan ya tsaya..


Ya zamana cewa tsakaninsa da sarki Maharaz bai wucce taku arba.in ba amma sbda karfin sihirinsu kowannesu na iya jiyo numfashin dayan.


Nana fa suka fara yin kallon kallo na yan dakiku sannan sarki Maharaz yai ajiyar numfashi yace ya wanan sarki kayi sani cewa yakin da muka yi asarar 


Miliyoyin rayuka.


A yau kuwa idan muka cigaba zamu iya kawar da dukkkaninmu a karshe duk mu tashi a tutar babu zamana cewa babu wanda ya sami nasarar dauko TAKOBIN SAIFUL LUJARA da ke karkashen wannan teku na bahar sufiya dake gabanmu.


Wai shin me zai hana mu fito da wani tsarin dabam a wannan yaki wanda zai kawo karshen rigimar da ke tsakaninmu.


Abinda nake nufi shi ne mu ware jarumai uku uku daga cikin mu su yaki juna.


Idan nawa jaruman ne suka kashe naka sai ka hkr ka bar mini takokobin SAIFUL LUJARA. 


Idan kuma naka jarumai ne suka kashe nawa sai na hkr na bar maka.


Ba don komai na yi wannan tunanin ba sai domin mu rage asarar miliyoyin rayukan da za ayi anan gaba.


PAGE 11

Suleiman Zidane Kd)


SA,ADDA sarki Maharaz yazo nan a zancensa sai sarki dujalu ya tuntsure da mahaukaciyar dariya kolacin guda kuma ya turbure fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa yace ya kai maharaz na ji duk abinda kace kuma na aminta da shi.


Amma bisa sharadi guda biyu.


Sharadi nafarko shine jaruman uku uku da zasuyi wannan fafatawa ba zasu yi amfani da karfin sihiri ba kuma sai kowa ya rantse da abin bautarsa cewar ba zai yi yaudaraba sai dai ya yi amdani da tsagwaron karfensa da kwarewarsa ta yaki....


Sharadi na biyu shine babu wanda zai zabi abkin gwaminsa da kansa sai dai ayi kuria a rubuta sunanyen jarumai shida a jikin duwatsu a gwamutsasu a zubar a kasa kowa ya dauki dutsen daya dauka shine abkin gwaminsa.


Yayin da sarki dujalu yazo nan a zancensa sai sarki maharaz yai shiru yana tunani da nazari.


A wannan lokacin gaba dayan jamaar dake sansanin yakin hakalinsu ya dugunzuma ainun sbda sun san cewa  idan har aka bi wannan tsari wanda sarki dujalu yazo da shi dole ne ayi asarae manyan abban dogaro na kowanen bangare.


Bayan sarki Maharaz ya gama nazari da tunani sai ya  dubi sarki dujalu yace ina bukatar nayi shawara da mutanena....


Page 12


sarki dujalu yayi murmushi yace na baka har tsawon rabi sa a kaje jayi shawara bisa abinda zai fisheju jai da jama arka...


Koda gama fadin hakan sai sarki dujalu ya juya da baya ya koma cikin ayarin rundunarsa ya ja sadauki ratinu da Matinu gefe daya domin suma su yi shawara.


Sarki Maharazya durfafi inda su Hibru ke tsaye jikinsa a sanyaye fuskarsa cike da alamun tsananin damuwa.


Da isarsa garesu sai suka kebe suka zauna a gefe daya suka shiga tataunawa sarki Maharaz dubi Hibru sannan ya dubi inmal yace me kake gani dangane da shawarar da nazo da ita bisa rage yawan a sarar miliyoyin rayukan da za a yi nan gaba? 


Hibru da inmal suka junansu  suka sunkui da kansu kas sai ga mataimakin hibru ya taho gareshi barde KURSHAM.


Kursham ya zauna daf da sarki maharaz ya risuna cikin girmamawa yace ya Shugabana ka zo da shawara mai kyau amma kuma itace mafi hadari idan ka yi la.akari da sharuddan da sarki dujalu ya kafa.


Ka sani cewa kai kanka baka da wani abin dogaro wanda yafi karfin sihirin tsafi kuma gashi


An ce baza ayi amfani da tsafin ba sai dai mutun yayi amfani da tsagwaron karfin sihirin tsafi kuma gashi ai amfani da tsagwaron karfin dantsensa.


Page 13


lallai kuwa in dau hakan za ayi to babu kai a cikin wanna fafatawan da za ayi mutum uku uku koda jin haka sai sarki maharaz ya dakawa barde kursham tsawa yace wnann wacce irin maganar banza kake yi haka?


Ka sanin cewa yadda nake kishin jamaata da kasata bana kishin tawa rayuwar don haka lallai dani a cikin mutane ukun da zasu yi wannan fafatawa.


Kafin sarki maharaz ya gama rufe bakinsa tuni sarkin yaki Hibru ya taru numfashinsa a fusatace cikin daga murya yace dakata ya kai abkna ka yi sani cewa wani lokacin ran mutum daya yafi na mutane dubunanai muhimmaci.


Shin baka tunanin cewa idan aka kasheka a farko wanna yaki jama armu zasu sami karayar zuciya su kasa aiwatar da komai a wanna yaki?


Shin baka tunanin cewa kai bango ne babban a filin yaki wanda idan ya fadi bamu da kwnacin hankali a can gida da nan waje.


Kuma makiya zasu sami karfin guiwar daza su dada zage dantse akanmu domin ganin sun gagauta shafemu.


Abin nake so da kai shine ka amince mana mu uku nan ni Hibru da Inmal mu wakilceka a wannan Gumurzu da za ayi.


Koda jin haka sai sarki mahaza ya yunkura a fusace yace ba zan taba yarda ba ayi hakan ba.


Ai mutuwa tace maza ta dada kara muku fishi da kwarin guiwa a wannan filin daga kuci gaba da ragargaza abokan gaba har ku karar dasu..


Page 14

ZAN DAKATA ANAN SAI KUMA ALLAH YAKAI MU GOBE DASAFE KUYI HAKURI YAU BAN KAWO MUKU DA WURIBA AIKI NE SHIYA NAKU HAR KULLU SULEIMAN ZIDANE KD.

PAGE 


Home of Littafan Yaki  And Hausa Novels


KAYI LIKE ACIKIN BLUE DINAN DOMUN SHIGA PAGE DINMU.


COMMENT AND SHARE PLS......

MAZAN JIYA 4

Littafe na hudu

part 3

Typing. Suleiman Zidane kd.

Page 14

Da jin haka sai sarki yaki Hibru ya matso gaban sarki Maharaz ya kusanceshi ainu yadda har suna iya jin numfashin juna yace ya kai abkina ka sani cewa tsawon shekaru ina bauta a karkashinka kuma ina yi maka biyyya ban taba kin bin umarninka ba amma a yau baza ka bi umarnin naka ba kuma zan yi maka dole akan ka hakura da shiga wannan yaki idan kuma kaki to zan kashe kaina.

Koda gama fadin hakan sai hawaye ya zubiwa Hibru aL.amarin da ya karya zuciyar sarki maharaz kenan nan da nan shima idanunsa suka ciko da kwallah ya rugunme Hibru yana mai cewa hakika yau ka nuna mini cewa bani da wani masoyi da ya fika a doron kasa don haka na janye nawa nunfi.

Ku tafi ku ukun ku wakilceni a wannan yaki.

Zan ci gana da hangenku daga nan inda nake.

Ubangiji Durbuza ya baku nasara koda gama fadin hakan sai sarki maharaz ya janye jikinsa daga cikin na Hibru.

Shi ku,ma hibru sai yadubi inmal da barde kursham yayi musu inkiyar su bishi izuwa can filin daga.

Nan take kuwa suka bishi da sauri suka nufi can tsakiyar filin suka tsaya.

Suleiman zidane kd)

A sanna ne sarki dujalu Matinu da Ratiju ma suka tunkarosu.

Sai ga ya rage saura bai fi taku goma ba a tsakaninsu sannan suka tsaya aka yi mugun kallon kallo yan dakiku.

Page 15

nan take sarki dujalu yasa aka kawo tsakuwoyi guda shida masu dan fadi aka rubuta sunan kowannesu jikin tsakuwa guda sannan aka zuba tsakuwunyi duka shidan a cikin wani kurtu aka karkada suka hautsine a cikin sannan aka ajiye a kasa.

Sarki dujalu ya bushe da dariya mugunta kuma ta turbune fuska yace kowannemu daya bayan daya zai zura hannusa ya dauko tsakuwa guda a cikin kuttun nan.

Duk tsakuwar da mutum ya daulo to sunan wanda ke jikin tsakuwar shine abkin gwaminsa.

Suwaye zasu fara zabar tsakuwar mu ne ko kuma kune?

Sariki dujalu ya tambaya yana mai kallon fuskar inmal.

Inmal yayi dan guntun murmushi mai nuna dakewar zuciya da jarumta ya ce kune zaku fara zaba sanna mu.

Sarki dujalu ya bushe da dariya yace ai komai nisan jifa kasa zai fado.

Yaro yau zan kasan cewa dujalu murucin kan dutse ne bai fito ba sai da yashirya kuma zaku san cewa kun tabo tsulliyar dodo.

A yau ne zan karar da dukkanin wannan runduna taku sannan na shiga cikin karkashin kogin BAHAR SUFIYA na dauko TAKOBIN SAIFUL LUJARA daga nan naje na dauko MASHIN GALILLUL HARAS da HULAR LAMSARA wato na hada MAKAMAN da zan gagaru duniya gaba dayanta na zama sarkin ko ina da ina.

Page 16

ka sani cewa birninku shi ne na farkon wanda zanje na mallakeshi.

Waccan yarinyar kuwa Gimbiya Mulaifa wacce kake tsananin so zan masheta baiwa na wulakantata tamkar Akuya..

Suleiman Z kd.

Kafin sarki dujalu ya gama wannan furuci tuni zuciyar inmal ta kufulo jikinsa ya kama tsuma don haka sai ya daka masa tsawa yace karyarka ta sha karsha yakai wannan sarki.

Kayisani cewa nine mai yanka maka dukkan wannan burin naka kuma bani da wani buri wanda yafi ya zamana cewa kaine abkin gwamina ayanzu.

Idan kowa ya dauki tsakuwarsa domin na yi maka kisan Gilla!

Koda jin wnan batu sai sarki dujalu ya takarkare ya bushe da dariyar mugunta sannan yace ai ni da kai KAR TA SAN KAR ne tunda mun hada jiki ka ji.

Ni babban bakin cikina shine rashin ganin sarki Maharaz a cikin ku ukun nan.

Ko dayake na san bai isa ya shiga wannan gumurzu ba tunda shi jarimtakarsa ta karfin sihiri ce kawai...

Na so ya zama abkin gwamina na yi masa mugun kisa a gaban yarsa da sirikinsa domin na kunsa muku gagarumin bakin ciki.

Koda jin wanna batu sai Hibru da Inmal suka fusata ainun suka ji kamar su zare takubbansu su afkawa dujalu amma sai suka daure suka tsaya suna kallonsa kawai cikin hahara jikinsu na tsuma.

Page 17

suleiman zidane kd.

Nan take sarki dujalu ya dubi Matinu wanda ke tsye a hannun hagunsa yace.

Maza ka sa hannunka a cikin wannan kurtu ka zabo avkin yakinka.

Cikin hanzari Matinu ta cika umarnu ai kuwa yana dauko tsakuwar sai aka duba aka ga sunan sarkin taki barde kursham.

Matinu da kursham suka zubawa juna idanu suna yiwa kansu kallon raini sbda kowannensu gani yake zai iya gamawa da dayan a cikin kankanin lokaci.

ABIN DA SUKA MANTA SHINE SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARA!

sarki dujalu ya dubi su inmal yayi murmushin mugunta yace yanzu kuma kune zaku zaba ko mu?

Da jin haka sai inmal ya yunkura domin ya sanya hannunsa a cikin wannan kurtu amma sai Hibru

ANAN ZAN DAKATA SAI KUMA GOBE DA SAFE.

COMMENT SULEIMAN ZIDANE KD..

PAGE. HOME OF LITTAFAN YAKI AND HAUSA NOVELS....


Aslm yan uwa ga page dinnmu sai kayi kokari shiga domin samun Littafe Kala Kala cikin blue dinnan Na kasa..


Duniyar Masoya Litattafan yaki only


Home of Littafan Yaki  And Hausa Novels


Matan Arewa Special Group


Zauren Muslims

MAZAN JIYA 4

Littafe na hudu

part 4

Typing. Suleiman zidane kd

.

Hibru yai sauri ya sha gabansa yace dakata

ya kai dana ai nine yakamata na zaba yanzu

kuma da izinin ubangiji garzuba sarki dujalu

zan zabo a matsayin abkin gwamina.

Cikin alamun firgici da tsananin tsoro inmal

ya dubi Hibru yace haba ya kai abbana ina

kai ina tarar sarki dujalu alhalin ka sancewa

ya fika jarumtaka nesa ba kusa ba?

Page 18

ni kaina da nake da kuruciya a jikina na

tsorata da shi bare kai da yanzy girma ya

fara riskarka..

Yayin da yazo nan a zancensa sai Hibru ya

numfasa yace yakai dana ai ni burina ke nan

na kara da shi domin ya kasheni ba tare da

naga yadda zai kashe kaba.

Domin mutuwar tawa ta fiye mini sauki da

ganin taka.

Koda sarkin yaki Hibru yazo nan a zancensa

sai Inmal yaji ya kamu da tsananin kaunarsa

gami da matukar tausayinsa don haka bai

san saadda hawaye ya subuto masa ba.

NIMA KAINA ZIDANE SAI DA NA MATUKAR

TAUSAYA MASU:p)

hibru yai sauri ya kau da fuskarsa ga barin

kallon inmal don haka shima ya zubar da

hawayen kawai sai yaje inda wannan kuttu

mai tsakuwoyin yake ya zura hannunsa a

cikin ya dauko tsakuwa guda koda ya fiddo

tsakuwar aka duba sai aka ga sunan sarki

dujalu ne.

Nan fa sarki dujalu ya kamu da tsananin

farin ciki yayi kururuwar murna.

Shi kuwa inmal sai yakamu da tsananin

bakin ciki ya cigaba da zubar da hawaye

sbda ya sancewa lokacin rabuwarsa da

mahaifinsa tazo.

Bayan sarki dujalu ya gama kururwar murna

gami da dariyar faran ciki sai ya dubi Rijiju

sannan ya dubi inmal yace, ku kadai ne kuka

rage baku dauki tsakuwoyin kuba don haka

dole dai baku da sauyin abkin gwami don

haka ba sai kun sa hannun a cikin wannan

kuttaba.

Yanzu mu bi ka idar wanan fafatawa domin

a fara.

Page 19

Gama fadin hakan ke da wuya sai sarki

dujalu Matinu da Ratinu suka hada baki suka

yi rantsuwa da Girman Gunki da suke

bautawa cewar baza suyi amfani da karfin

tsafi ba ko yaudara a cikin wannan gumurzu

da za ayi face tsagwaron karfin dantsen su

da kwarewarsu ta yaki.

Koda gama fadin hakan sai suma su inmal

su ka hada baki suka yi irin rantsuwar da su

dujalu sukayi suna kammalawa ne Matinu da

Barde Kurshm na zare takubbansu suka

buda suna masu kallon juna cikin nazari

sannan kuma sai suka fara zagaya gama da

dan uwansa cikin kankanin lokaci.

Lokaci guda gaba dayansu suka yi kururuwa

uku ruga kan juna suka kacame da

azababben yki suna masu kaiwa junansu

sara da suka cikin tsananin zafin nama

juriya da jarumtaka kowannensu na kokarin

yiwa dayan farat daya.

Bisa mamaki sai aka ga duk suna amfani da

da salon fada iri daya kuma sai gashi sun

kasa cutar da juna.

Haka dai suka ci gaba da fafatawa har izuwa

tsawon dakika dari uku da tamanin amma

babu yanda ya sami nasarar koda

kwarzanar jikin dan uwansa.

Hatta kaifin takubbansu sai da ya fara

dusashewa sbda yawan goguwa da juna.

Page 20

da kansu suka ja da baya suka yi cirko cirko

suna haki kamar zakaru sbda gajiya gami da

mamakin yadda aka yi salon fadan

Nasu yazo iri daya.

A bangare sauran dakarun yaki kuwa

kowannen bangare sun zuba idanu ne suna

kallo cikin fargaba gami da zakuwar sin

ganin nasu ne ya sami nasara.

Bayan Matinu da barde Kursham sun samu

hutu na tsawon yan dakiku sai kowanensu

ya yar da takobin hannunsa.

Matinu ya zare wadansu gajerun adduna

guda biyu dake kuibin cinyoyinsa a cikin

kufe shi kuma Barde Kursham sai ya zare

wata sharbebiyar wuka wacce tsawonta bai

wuce kamu biyu ba amma tana da fadi gami

da tsananin kaifi sannan ya kuya ya dubi

jama,ar runfunarsa dake baya yana mai

daga hannu.

Nan take wani badakare ya rugo ya kawo

masa garkuwa ya riketa da hannun hagu.

.

Yana karba garkuwar sai ya fuskanci matinu

suka rugo da gudu izuwa kan juna.

Ya yin da yarage saura baifi taku hudu ba

sai kowannensu ya daka tsalle sama suka

kaiwa juna mugun hari.

Cikin sa.a Matinu ya dankarawa barde

kursham sara a kan kafada.

Shim kuma kursham ya sokeshi da wannan

wuka a tsakiyar kirjinsa har sai da wukar ta

bullo ta gadon bayansa.

Page 21

Suleiman zidane kd

Duk su biyun suka tsanfara uban ihu a

lokacin da jijiyar kafadar barde Kursgam ta

tsinke jini ya kama tsartuwa a sama.

Shi kuwa matinu jini ne ya kama bulbulowa

ta cikin ramin da wukar ta yi a kirjinsa

wanda inda za a tara yar kwatarniya sai ta

cika fal da jini.

Nan take du su biyun suka kama mata gun

gun a tsaye har sai dasuka sulale kasa suka

kama shure shure.

Idan suka yunkura kamar zasu iya mikewa

sai kaga sun sake bajewa.

A haka dai duk su biyun suka zama gawa.

Koda ganin wanan al mari sai kowane

bangare sukakamu da tsananin bakin ciki

sakamakon RAGAS da akayi.

Har sarki yaji ya yunkura zai tari sarki dujalu

sai shi sarki dujalu ya nole yace ai ni da kai

manyan giwaye ne mu bari mu ga yadda

fadan kananun giwaye zai kasance sannan

muyi namu a karshe...

ANAN ZANDAKATA SAI KUMA IN ALLAH

YAKAIAMU GOBE DA SAFE.

SULEIMAN ZIDANE KD.

PAGE HOME OF LITTAFAN YAKI AND HAUSA

NOVELSMAZAN JIYA 4

Littafe na hudu

Na abdul aziz sani.

part 5

Type suleiman zidane kd.

manyan giwaye ne mu bari mu ga yadda

fadan kananun giwaye zai kasance sannan

muyi namu a karshe...

Ba tare da gardamar komai ba Hibru ya ja da

baya ya dubi inmal.

Kawai sai inmal ya tunkari abkin gwaminsa

Ratiju ba tare da ya zare takobinsa ba.

Koda Ratiju ya ga inmal ya durfafoshi babu

makami sai ya cika da tsananin farin ciki

sbda tunanin cewa ya sami babbar da mar

da zai yi masa kwaf daya.

Page 22

cikin hanzari Ratiju ya zare takobinsa ya

falfala da azababben gudu izuwa kan inmal

yana kwarara ihu mai tsananin firgitarwa

wanda ka iya tarwatsa gungu dakaru a filin

fama.

Ko gezau inmal bai yiba yaci gaba da

tunkarasa batare da yazare takobinsa ba

daga cikin kufeta.

Ai kuwa suna haduwa sai ratiju ya kawowa

inmal wani irin mugun wawan sara a wuya

da dukkan karfinsa cikin bakin zafin nama

inamal ya sunkuya domin ya kauce saran

amma dukk da haka sai da kaifin takobin

ratiju ya shaftare saman kunne inmal ya

yanke rabin gashin kansa sai ga jini na diga

daga kunnen inmla a yayin da aka sami yar

taraza a tsakaninsu.

Kofa inmal ya shafa kunnensa ya ji jini kuma

ya ga rabin gashin kansa a kas sai ya fusata

ainun zuciyarsa ta kama tarfafasa kamar

zata kone.

Shi kuwa ratiju sai ya kama dariyar keta da

murna yna ganin cewa idan aka sake

gamuwa fara daya zai gama fa inmal.

Batare da inmal ya zare takobin tasa ba sai

ya sake durfafar ratiju al.amarin da yai

matukar dugunzuma hankalin sarki Maharaz

ke nan.

Har Hibru ya fara kwalawa inma kira yana yi

masa tsawa akan ya zare takobinsa kafin su

hadu da ratiju.

Inmal yayi kamar bai ji umarunin Hibru ba ya

ci gaba da tunkarar ratiju a hakan.

Page 23

ita kuwa Gimbiya mulaifa wacce ke tsaye

acan gefe daya tana kallon abin da faruwa

tuni ta fara kuka tun sa,adda ta ga an

rutsure rabbin gashin kan inmal kuma anyi

masa rauni a kunne.

Sarki dujalu kuwa dariya yake ta kyalkyalawa

yana yiwa ratiju kirari gami da kara masa

kwarin guiwa.

Dama sadaiki ratiju ya fi Matinu karfin

dantse da zafin nama shi kansa sarki dujalu

idan suna yar gwajin jarumtaka shi da ratiju

sai yayi da gaske yake samun nasara akansa

don haka a yanzu yana kyautata zato cewa

ratiju zai iya hallaka inmal duk da cewa yayi

yaki da inmal ya ga irin tsananin tasa

jarumtakar.

Koda ratiju da inmal suka sake haduwa a

kari na biyu, sai ratiju ya kawowa inmak

muguwar suka a ciki.

Kawai sai inmal ya tare tsinin takobin da

tafin hannayensa biyu.

Nan fa ratiju ya fara danno takobin da

dukkan karfinsa domin ya huda cikin inmal.

Wohoho! Mai karfi sai allah ya isa! Nan fa

tsagwaron karfin dantse ya fara amfani sai

gashi duk su biyun kwanjin jikinsu ya

kumbura jijiyoyinsu suka tashi suka yi

burdin burdin.

A lokacin guda duk su biyun sai ga gumi na

karyi musu. Shi dai Ratiju ya kasa dannan

tsinin takobin ta shige izuwa cikin inmal.

Page 24

Shi kuma inmal ya kasa kautar

da takobin daga saitin cikinsa.

Tsawon komanin dakika dari da sittin suna

tsaye kikam a hakan kowannensu yana jin

jiki har kaifin takobin ta Ratiju ya fara

yankar tafin hannun inmal jimi ya fara diga.

Kwatsam! Sai inmal ya kwarara uban ihu ya

daga takobin da shi kansa ratiju sama yai

wurgi da su.

Tamkar an cilla hoge sama hakan ratiju da

takobin suka luluka sama suka watse a

saman.

Kafin ratiju ya fado kasa inmal ya daka tsalle

sama ya taresahi kawai sai ya kama kansa

da hannu biyu ya murde masa wuya.

Sai gashi inmal ya duro kasa bisa kan turba

rungume da gawar tatiju.

Nan take yi jifa da gawar tamkar tsummam,

ya mike tsaye yana mai karkade jurar jikinsa.

Ai kuwa su sarki Maharaz basu san saadda

suka kaure da shewar farinciki ba suka

kama yiwa inmal kirari gami da jinjina bisa

wannan gagarumar jarumtaka da yayi.

Shi kuwa sarki dujalu da jama.arsa kamewa

suka yi kamar gumaka sbda mamaki da

bakin ciki. Nan take hawaye takaici ya

zuvowa sarki dujalu sbda ya san cewa yayi

asarar babban mayakinsa wanda bashi da

kamarsa.

Bayan sarki dujalu ya gama alhinin mutuwar

ratuju izuwa tsawon yan dakiku sai ya tako

kafafunsa yazo tsakiyar filin dagar ya tsaya

sannan ya xare wadansu manyan takubba

guda biyu dake soke a gadon bayansa ya

fuskanci sarki yaki Hibru.

Adaidai wannan lokacin ne hankalin inmal

da na Sarki Maharaz ya dugunzuma ainun

suka ji kamar su rike Hibru su hanashi tarar

sarki dujalu.

Kawai sai suka ga shima Hibru ya zare nasa

takubban guda biyu ya yunkura zai tunkari

sarki dujalu.

A guje inmal yasha gaban Hibru ya dubeshi

cikin tsananin damuwa yace yakai abbana

ka bani dama na karbeka a wannan

gumurzu ni na fafata da sarki dujalu.

Koda jin wnan batu sai Hibru ya yi

murmushi yace yakai dana kayi sani cewa ai

bakin alkalami ya riga ta bushe.

Tun da har muka yi rantsuwa da girman

ubangikinmu Darbuza babu gudu kuma

babu ja da baya.

Kamar yadda na zuba ido ka yina ka

gumurzu har kasami nasara hakan kaima

zaka zuba ido ka kalli nawa.

MAZAN JIYA 4

Littafe na hudu

Na abdul aziz:

part 6

TYPING SULEIMAN ZIDANE KD:

YAU ne ranar da zan san iyakar jarumtakata kuma ka sani cewa ko kashe ni aka yi zan mutu ne a cikin alfharin kare kasata gami da martabar sarautar abkna aminina:

alfarma daya nake nema a wajenka; duk wuya duk rintsi karka bari gimbiya Mulaifa ta rasa rayuwarta kuma in dai kayi tsawon rai ka aureta ku koma birninmu ku karasa rayuwarku ta duniya:

koda gama fadin hakan sai Hibru ya juya ya kalli abkinsa sarki Maharaz wani kallo yayi masa mai kama dana bankwana a cikin murmushi mai dugunzua hankali:

Page 26:

Nan take sarki Maharaz ya ji hawaye ya zubo asa kua ya ji kamar ya ruga da gudu ya rike Hibru ya hanashi karo da sarki dujalu:

Nan take Hibru ya durfafi Sarki Dujalu shima sarki dujalu sai ya tunkaroshi kiwannensu ya taho a fusace acikin mugun nufi amma a hankali suke tahowa cikin nutsuwa ba tare da sauri ba;

sai da yarege saura baifi taku goa a tsakninsu ba sannan suka ruga da gudu izuwa kan juna suka ruguntsue da azababben yaki:

Wohoho! Maza maganin maza.

Hakika idan jarumtaka ta hadu da sadaukantaka gami da naci da tsantsar juriya dole ne gumurzun ya yi dadin kallo kuma ya zama abin tsaro:

anfara wannan bakin artabu tsakanin sarki dujalu da Hibru sai labri ya zaa sabo:

gaba dayan mutanen dake fili babu wanda hankalinsa bai dugunzuma ba fiye da ko yaushe sbo da ganin yadda jaruman biyu suke kaiwa junansu mugayen hare hare na musamman wanda babu mai iya yin irinsa face tshon hannu bangaren yaki:

duk dace wa sarki dujalu yafi Hibru tsauntsar karfin dantse amma sai gashi Hibru na iya kare hare harensa har ma yana mai da martanin shi kansa sarki dujalu yayi matukar mamkin yadda hakan ta kasance domin yayi zaton cewa suna fara gumurzu zai iya kuntatashi da karfin dantsensa cikin kankanin lokaci amma sai gashi labari ya sha bamban:

Page 27

Suleiman zidane kd

nan ta suka tashi hankalin kasa kura ta turnuke filin yakin dudufniyar kafafuwansu dakarar haduwar makamansu suka cika dodon kunne kaai cw mutum dubu ne suka gwamuse suke yakin:

Sai da suka shafe sa:a uku cur! Suna wannan dauki ba dadi tamkar jikinsu bana kashi da tsoka bane face na karfe zallah sannan suka gaji:

bisa dole kowannensu ya ha da baya suja yi cirko cirko kmar zakaru suna haki gami da kallon juna kuma kowannensu ya jike sharkaf da zufa kamar daga cikin kogin aka tsamosu;

Abin da ya daurewa kowannensu kai kuma ya basu haushi shine ganin yadda suka dade suna wannan gumurzu amma dayansu bai sami nasar koda kwarzanar jikin daya ba:

Su kansu taron rudunonin biyu dake kallon wannan gumurzu ji suka yi kamar da can ruwan masifa ake zubowa daga sama amma da jaruman sua daina yakin sai suka ji an dauke ruwan masifar:

Sai da sarki dujalu da Hibru suka shefe tsawon dakika dari biyar da arba:in suna haki da hararar juna kuma kowannensu na tunanin irin salon da ya kaata ya sauya domin ya sai nasara:

kamar hadin baki sai aka Ga duk su biyun sun taso da gudu a lokaci guda sun durfafi juna: gudu ne na bala i tamkar zasu tashi sama kuma kowannensu da dukkan karfinsa ya taho cikin mugun nufi:

maimakon su daka tsalle sama su yi mugun gamo a kasan kowanensu ya kaiwa dan uwansa mumunnan hari:

sai ga shi kowannensu ya wuce dan uwansa amma sai duk suka sulale kasa bisa guiwoyinsu suka kame kamar gumaka:

Al:amarin da ya razana kowa kenan a wajen gashi dai dukkanninsu sun rankwafar da kawunansu kas ama basa motsi tamka babu mai rai acikinsu:::

page 28

daga can sai aka ga jini na malalowa kasa daga jikin hannun daman sarki dujalu kuma yana rike da hannun:

shi kuwa Hibru sai aka ga jini na malalowa ta kuibin cikinsa:

jim kadan sai hannun daan na sarki dujalu ya gutsure ya fado kasa shima ya sulale kasa sumame:

shi kuwa Hibru sai ya bingire kasa ya kaa shure shuren mutuwa;

cikin tsananin dimauta sarki maharaz da inmal suka ruga izuwa kan Hibru:

tun daga nesa suka fara rasu ihu suka fashe da kuka:

a bangare sarki dujalu kuwa dakarunsa ne suka rugo da gudu suka daukeshi yana cikin halin suman suka ruga dashi izuwa can cikin sansaninsu:

lokacin da inmal da sarki Maharaz suka iso kan Hibru yana takakarin mutuwa sai suka durkusa a gabansa suka sake fashewa da matsanaicin kuka sbda sun lura da raunin dake kuibin cikin nasa sun ga yayi rami zururu babu yadda za ayi ya rayu:

hannun Hibru na karkarwa ya kamo hannun sarki Maharaz ya dora bisa kirjinsa suka kurawa juna idanu;:

Page 29

cikin matukar karfin hali Hibru ya dudi baki da kyar yace yakai abkna yau fa ranar rabuwarmu ta zo:

Tabbas mutuwa zan yi yanzu ba zan tashi ba:

ina alfahari da wannan mutuwa tawa domin na mutu ne a filin daga bisa kare kasata da mutuncika:

sannan ina alfahari da cewar na sarewa sarki dujalu hannun daya har ya bar duniya ba zai taba mantawa da niba na cusa masa bakin cikin da zai tafi da shi har kabarinsa:

koda Hibru yazo nan a znacesa sai sarki Maharaz ya tasoshi zauna ya rungumeshi yana mai fashewa da sabon kuku yace yakai masoyina babban amina saboda me zaka tafi kabarni a cikin wannan duniya wacce baya da dadin zama idan babu masoyi?

Ka sani cewa in banda yata ba mulaifa bani da kowa sai kai gashi zaka mutu a dai dai lokacin da zan samu duniya na yi aka sakayya bisa bautar da kayi mini a baya gai da nuna tsantsar so da kauna:

ai kuwa tun da har tafiya zaka yi nia ina mai rokin darbuza da ya gaggauta dauke....

Kafin sarki Maharaz ya gama rufe bakinsa sai HIBRU yarufe asa baki da tafin hannunsa yace idan kaima ka tafi waye zai ga auren yayanmu kenan? Ya kai masoyina komai RINTSI DA TSANANI Lallai ka rayu a wannan yaki koda kuwa bamu samu nasara mallakar Takobin Saiful Lujara ba:

burina kawai shine kai da inmal da gimbiya mulaifa ku koma gida a raye:

Saadda Hibru yazo nan a zncensa sai sarki maharaz yasake fashewa da kuka yace yakai masoyina kayi sani cewa bakin alkalami ya bushe domin kafin mu baro gida mai girma Darbuza ya tabbatar Mini dacewa mutum hudu ne kacal zasu tsira a wannan filin yaki kuma mutum biyu daga cikinmu:

kaga kenan a tsakanin ni inmal da mulaifa dole ne dayanmu ya mutu:

koda jin wannan batu Sai Hibru ta ci gaba da kakarin mutuwa da zafi;

page 30

Al amarin da ya dimauta su inmal kenan:

inmal yai sauri ya karbi Hibru daha hannu sarki maharaz ya rungumeshi a kirjinsa yana mai tsala ihun bakin ciki sa;adda hawaye ke ta kwararowa daga cikin idanunsa:

a sannan ne Hibru ya dan dawo cikin hakanlinsa ka dan ya dubi inmal yayi masa murmushi karfin hali yace yakai dana ka zamo mai juriya bisa rashina:

ina mai fari ciki kasancewar zan mutu akan tafin hannunka kamar yadda mahaifin ya mutu akan tafin hannuna kuma a filin yaki:

kaima ina maka fatan mutuwa irin ta manya mazaje a karshen rayuwarka:

ina fatan baza ka manta da wasiyyata ba akan masoyiyarka mulaifa:

a wannan lokaci mulaifa na can nesa da su kadan tana faman rusa kuka ta kasa karosowa inda suke:::

page 31

hibru ya juyar da kansa ya dubi inda mulaifa take tsaye a lokacin da idanunsa ke ganinta dishi dishi sannan ya waigo ya dubi inmal yayi masa kallon karshe:

a hakan idanunsa suka kafe yana yiwa inmal murmushi; kuma gaba dayan jikinsa ya sandare:

inmal bais san cewa Hibru ya mutu ba sai daya lura da cewa idanunsa sun daina kiftawa:

koda ya fahimci hakan sai ya tsandara uban ihu wanda ya firgita komai da kowa ke cikin dajin:

nan take shi da sarki maharaz suka kankame gawar hibru a jinsu suna masu fashewa da matsainincin kuka:

a sanna ne itaama gimbiya ta rugo sa gudu ta fada kan gawar Hibru ta tayasu kukan:

KAI ABIN MAMASU KADAN BA HATTANI ZIDANE SAI DANA TAYASU KUKA;()

* * *

Al amarin sarki dujalu kuwa lokacin da darunsa suka daukeshi da gudu suka tafi dashi izuwa cikin sansaninsu sai aka wuce da shi izuwa cikin tintinsa aka kwantar da shi akan shimfidarsa:

nan fa likitansa ya shiga aiki:

bayan ya tsaida jinin dake zuba a gundulmin hannunsa sai ya samasa magani sannan ya lulluceshi iya kirji da mayafi kowa ya fice daga cikin tanti aka bar sarki dujalu shi kadai har a sanna bai farfado daga dogon suman da yayi ba amma akwai alamar fitar numfashinsa kadan kadan:

sarki dujalu bai farfado ba sai bayan saa biyu sa rabi :

koda ya bude idanunsa ya tsinci kansa a cikin tantinsa a kwance sai ya cika da tsananin mamaki domin shi a zatonsa ya mutu a filin yaki:

sarki dujalu ya yunkura domin ya yaye mayafinsa da aka lullbeshi da hannunsa na dama kawai sai yaji kamar bashi da hannun gaba daya:

cikin tsananin firgici ya sa daya hannun nasa na hagu ya yaye mayafin take yayi arba da hannunsa na dama ya ga yazama gungulmi:

sarki dujalu ya takarkare ya kwarara mugun ihu mai tsananin karfi gami da amsa kuwwa izuwa cikin dajin gaba daya: kai hataa dabbobi da aljanun dake rayuwa a cikin karkashin teku bahar Sufuya sai da wannan ihu na sarki dujalu ya eazansu:

page 32

bayan yayi ihu kuma sai ya fashe dd matsanaici kukan vakin ciki domin wanan shine karo na farko da Taba yi masa rauni a filin yaki a iya tsawon rayuwarsa duk da cewar ya halarci yakukuwa sama da guda dari a rayuwarsa:::::::::::::::::::

ANAN ZAN DAKATA SAI IN ALLAH YAKAIMU GOBE DASAFE ZAMU CIGABA NAKU HAR KULLU SULEIMAN ZIDANE KD

WHATSAPP NUMBER

09064179602

MAZAN JIYA 4

Littafe na hudu

Part 7

Typing:  Suleiman zidane kd


kuma tunda uwarsa ta haifeshi bai taba zubar da hawayen takaici ba sai yau:


cikin wannan hali ne shugaban Dakarunsa na jinsin Aljanu wanda ake kira BARUZUL MADWAN yashigo cikin tantin ya zube kasa ya kwashi gaisuwa yace Ya shugabana yanzu mene ne abin yi tsakaninmu da su waye zai sami damar shiga cikin wannan kogi na Bahar Sufiya don dauko Takobin saiful Lujara tsakanin mu da su; tunda anyi yarjejeniya bisa cewar wadanda suka yi nasara a yakin mutum uku uku sune zasu dauko takobin kuma gashi yanzu kamar RAGAS akayi tunda kai suma kayi a filin yakin shi kuma Hibru mutuwa yayi:


Page 33


Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lulube sarki dujalu bisa jin cewar yasamin nasarar kashe Hibru amma kuma da ya dubi gundulmi hannunsa sai ya sake kamuwa da tsananin bakin ciki:


NIMA ZIDANE SAI NATAYI SHI BAKIN CIKI WANNAN ABU)


tsawon tan dakiku sarki dujalu yana tunani  bai baiwa aljani barzul madwan amsar tambayarsa ba sai daga can ya dago kai ya dubeshi yace ya kai shugaban dakarun aljanu kayi sani cewa a halin yanzu yarjejeniyar da ke tsakaninmu da su sarki maharaz ta rushe wannan yaki ya zama danye don haka za ayi hutu na tsawon kwna uku domin na baiwa avkan gabamu damar da zasu sami saukin dacin rashin da suka yina babban masoyinsu:


dalilina anan shine abin kunya ne a gareni na yakesu a lokacin da zukatansu ke cike da rauni:


lallai na fi son na yakesu a lokacin da suke cikin nutsuwarsu sbda haka yanzu kaje ka sa a rubuta takarda a kaiwa abkan gaba bisa wannan hukuci da nayanke:::


Page 34


Aljani barzul madwan ya risina yace angama ya shugabana:


kawwai sai ya bace bat! Daga cikin tanti tamkar bai taba wanzuwa ba a ciki::


*       *       *        *

bayan su sarki Maharaz sun kwashe gawarwakin dakarunsu mutum biyu da aka kashe; wato gawar sarki yaki Hibru data Barde Kursham sun koma cikin sansaninsu sai aka shiga gidimar binne gawar:


nan fa kowa da kowa ya kama kuka kamar ba za a daina ba:


babu wanda zai fi baka tausayi ma sama da sarki Maharaz domin har birgima ya kama ya a kasa sai da aka rirrikrshi aka shiga bashi baki sbda jiya yiya tsani kansa gwara ma ace shima ya mutu ya huta da bakin ciki:


Lokacin da aka sanya Hibru a cikin kabarinsa aka rufeshi sai inmal da sarki maharaz suka kwana akan kabarin suja cigaba da kuka ba sassauci:


akan kabarin suka kwna suna kukan har sai da alfirjir ya keto sannan aka zo aka kwashesi sumammu aka kaisu cikin tanti aka kwantar:


da kyar da sindin goshi gimbiya Mulaifa ta ceto rayuwarsu:


bayan sun dawo hayyancisu  ne aka kawo musu abin kalaci dama a jiya da daddare ma basu ci komai ba:


nan fa gardama ta karke a tsakaninsu da mulaifa suka ce ba zasu ciba:


Gimbiya Mulaifa ta zare wata karaar wuka mai tsananin kaifi da tsini ta saita cikintana kuka tace idan har baza ku cin abinci ba lallai zata kashe kanta:


nan fa suka kama cin abinci bisa dole har sai da suka koshi:


gama cin abinci nasu ke da wuya sai ga wani badakare  Mai suna GAIYABU ya shigo cikin tanti rike da wasika a hannunsa:

Gaiyabu ya zube kasa gaban sarki maharaz ya kwashe gaisuwa sannan ya mika masa wasikar:

nan take sarki maharaz ya warware wasikar ya karanta a fili kamar haka:::::::::::


PAGE 35


SAKO DAGA SARKI DUJALU:


ZUWA GA SARKI MAHARAZ BABBAN ABOKIN GABATA:

YAKAI WANNAN SARKI KAYI SANI CEWA ABINDA YA FARU TSAKANINMU DA KU BA KOMAI BANE FACE SHARAR FAGE: NA SANCEWA NA KUNSA MUKU GAGARUMIN BAKIN CIKI BISA NASARAR DA NA SAMU TA KASHE SARKI YAKINKA; KUMA BABBAN MASOYINKA HIBRU TO AMMA NIMA HIBRU YA TAFI YA BARNI DA TABON BAKIN CIKI DA HAR ABADA BA ZAN MANTA DASHI BA TUNDA YARABANI DA HANNUNA GUDA DAYA:

TABBAS NAYI JINJINA GA MAMACI HIBRU DOMIN SHI NE JARUMI NA FARKO WANDA YA TABA SAMUN DAMAR YI MIN RAUNI A FILIN DAGA KUMA NA YI ALKWARI KODA BAYAN WANNA YAKI NE ZAN ZIRYACI KABARIN HIBRU NA YI MASA JINJINA:


INA MAI SANAR DAKAI CEWA BISA GUMURZUN DA AKA YI A JIYA MU DAKU BABU WANI SAKAMAKO FACE RAGAS SABODA HAKA ZAMU CI GABA DA WANNAN YAKI NAN DA CIKAR KWANA UKU SBDA NAFI SON NAYI YAKIN DA KU A LOKACIN DA KUKE DA NATSUWA BA YANZU BA DA KUKE CIKIN DAMUWA DA ALHINI:


INA FATAN ZA KU KARBI WANNAN SHAWARA TAWA HANNU BIYU::


PAGE 36

SULEIMAN ZIDANE KD


Koda sarki maharaz ya zo nan a karatun wasikar sai yamike tsaye zumbur a fusace ya yayyaga wasikar sannan ya yunkura da nufin yafita waje ya sa a fara shirye shiryen yaki::::


cikin hanzari inmal ya sha gabansa yace ya shugabana ka tausasa zuciyarka ka dau hkr sau tari yanke hukunci a lokacin da rai ya fusata baya haifar da komai face nadama da asara:


muyi amfani da shawarar wanan abokin ga namu mujira izuw tsawon kwna ukun:


koda jin wanna batu sai sarki maharaz ya duci inmal cikin alamun tsananin damuwa yace yakai magajin sarkin yaki shin baka da tunanin cewa sarki dujalu so yake ya yaudaremu ya yi amfani dawann dama ya kawi mana harin sumamea cikin kwana ukun nan yadda zai iya murkusheu a cikin kankanin lokaci?


Inmal ya numfasa yace haba ya shugabana ai babu wani motsi wanda sarki da dakarunsa za suyi ba tare da mun gani ba tunda daga nan sasaninmu muna hangensu suna hangenmu:


PAGE 37

dare da ranan masu gadi suna lura:


ka kara hakuri ya shugabana  har ixuwa lokacin da wadannan kwanki zasu ciki::


ni ina ji a jikina cewar mune zamu sami nasarar dauko takobin Saiful Lujara a cikin wannan kogi:


koda inmal yazo nan a zancensa sai Gimbiya mulaifa mata dubeshi tace kayi amfani da shwarar inmla ya kai abbana domin ina gainin cewa itace zata fiye mana alheri:


koda gama fadin hakan mulaifa ta kama hannun inmal taja shi suka fice daga cikin tantin suka bar sarki maharaz a tsaye cikin tsananin da muwada takaici::::


WANNAN SHINE ABINDA YAFARU A CAN BAKIN KOGIN BAHAR SUFIYA BAYAN ANCI GABADA FAFATA YAKKI TSAKANIN RUDUNAR SARKI MAHARAZ DA RUNDUNAR SARKI DUJALU A KARO NA BIYU 2::::::::::::


*          *          *         *          *


AL:AMARIN Gimbiya Hursiya Kuwa; lokacin da aljani burzaru ya nufi can birnin da ira ta tabbatar da cewa an rabata  Da sarki kenan sai ta fashe da matsaininci kukana bakin ciki:


Page 38

zidane


bata gushe ba tana kukan hat aljni Barzaru ya sauketa a tsakiyar gidan sarautar tasu::


Koda bayi kunyangi barori da dakarun tsaro na gidan suka ganta sai duk suka zube kasa a gabnta suna kwasar gaisuwa ko kallomsu ba tayi ba sai ta juya a fusace tashige izuwaa can cikin gidan sarautar da sauri:


duk sa adda ta waigo bayanta sai ta ga aljani Barzaru nabiye da ita:


Al:amarin da yai matukar ba ta mamaki da tsoro kenan:


nan take ta gane cewa lallai sarki ne ya umarci barzaru da ya sa ido akanta don kada ta sulale ta koma can sansani yaki:


Nan fa Hursiya taji hankalinta ya dugunzuma ainun kuma ta kudurce a ranta cewar takowanne hali sai ta san yadda tayi ta subecewa barzaru takoma can sansanin yaki sbda gwara itama ta mutu a can da dai azo mata da labarin mutuwar sarki tunda bata da kowa a duniya sai shi:


kai tsaye Gimbiya Hursiyya ta wuce izuwa cikin turakarta:

tana shiga ciki ta mai da kofa tarufe bam da karfi cikin fishi sannan ta fada kam gadonta ta kwanta ruf da ciki ta fashe da sabon kuka:


Shi kuwa aljani barzaru a kofar turakar yaja ya tsaya kuma ya kame kamar gunki yana muzurai ko yaushe idanunsa na kallon gabas da yamma kudu da arewa don hada gimbiya Hursiya ta Shamaceshi ta fice ba tare da sani ba:


su kuwa fadawan sarki dujalu wadanda aka barwa jiran gari koda suka ji cewar  gimbiya Hursiya ta dawo daga sansanin yaki ita kadai?


Sai suka cika da tsananin mamaki suka dugungumo gaba daynasu syka zo ganin gimbiya:


koda suka aika da manzo a gareta bisa zuwansu sai ta aiko a gay musu cewa baza ta gana dakowa ba sai gobe da safe a fada:

Page 39

Al:amarin da yai matukar dugunzuma hakalinsu kenan suka rasa abinda ke musu dadi sabo sa su kawai so suke suji matsayin da ake ciki a can sansanin yaki:


Shin sarki Dujalu yana nan a raye ko kuwa ya mutu?


MASU IYA MAGANA SUN CE IDAN KAGA KARE YANA SHINSHINA TAKALMI TO SO YAKE ZAI DAUKA::::::


tunda gimbiya Hursiyya taji cewa yan majalisar sarki sun kagu da su yi magana da ita sai jikinta ya bata cewar so suke suci amanar sarki :


ma ana idan suka ji sarki ya mutu sai su yi sauri su nada wanda suke son ya gajeshi acikinsu batare da sun bata sarautar bakamar yadda yake aka ida:


page 40


koda aiyana hakan sai hankalin Hursiya ya sake dugunzuma ainun domin ta fahimci cewar lallai tana ciki  hadari domin idan ta fadawa yan majalisar gaskiya al amari cewar bata san abinda ya faru a filin yakin ba tunda bata gani da idanunta zasu zata karya take su dauka cewa lallai itama da kyar ta tsira kuma an kashe sarki da mukarrabansa:

ama da Hursiya ta tuna cewa ai tana tare da aljani Barzaru babban jarumi kuma sadauki mai watsa maza babbn hadimi sarki dujalu mai amana sai hankalinta ya dan kwanta sbda ta san cewa zai kareta daga dukkan wani mugun abu amma kuma sai ta fara tunasnin hanyar da zata bita koma can sansanin yakin domin zamanta a can zai fiye mata kwnciyar hankalii:::::::::::::::::::::


ANAN ZAN DAKA TA SAI KUMA GOBE 

TYPING SULEIMAN ZIDANE KD

GASKIYA BAKUSAN YI COMMENT..

MAZAN JIYA 4

Littafe na hudu

part 8

Typing Suleiman zidane kd::


Kashe gari da safe bayan Gimbiya Hursiya ta gama kintsawa tayi kalaci sai ta caba ado sanna ta nufi fada fuskarta cike da annuri tana takawa dai dai tamkar taron  dawisu ta rinka tafiya cikin izza da jin kamshi:


da shigarta cikin fadar sai ta iske gaba dayan yan majalisar a zaune sun yi tsuru tsuru suna jira isowarta:


koda suka ga gimbiya a cikin fara ada nishadi sai hankalinsu ya dugunzuma ainun suka fara tunanin cewa lallai sarki dujalu ne yake samun nasara acan filin yakin:


Page 41


Dama bayan tafiyar sarki dujalu da rundunarsa ta yaki sai yan majalisar suja yi taro na sirri a tsakaninsu inda suka gaiyato wani amintaccen bokansu mai suna IRMAS BINI KAIBUR suka umarceshi daya yi musu bincike akan abinda zai faru a can bakin kogin Bahar sufiya:


Koda boka Irmas ya dauko madubin tsafinsa ya shafeshi da hannun hagu domin yaga abinsa zai faru sai nan take madubin tsafin yayi bindiga ya farfashe:

Al:amarin da yai matukar razana boka irmas da yan majalisar kenan suka firgita ainun:

Har yan majalisar sun yunkura zasu mike tsaye su fice da gudu dga cikin dakin tsaro sai boka irmas ya daka musu tsawa yace kowa ya zauna a inda yake in bahaka ba kuwa babu wanda zai koma gidansa a raye:

Koda jin hakan sai kowa ya koa inda yake ya zauna:

boka irmas yai gyaran murya sannan ya dubi gaba dayan yan majalisar yace yaku shuganbanina kuyi sani cewa babu wani matsafi a wannan nahiya mai karfin sihiri dayakai na sarki dujalu sbda haka ya boye duk abinda ke faruwa a cam bakin tekun bahar sufiya ga dukkan wani mahaluki dake cikin wannan nahiya:

bisa wannan dalili ne kuka ga madubin tsafina yai bindiga;

yanzu hanya daya ce zamu bi my iya ganewa idan sarki dujalu yana samun nasara a filin yaki ko baya samu:

Nan gaba a lokacin da yakin ya fara tsauri lallai akwai mutumin da zai dawo daga can filin yakin wandas ya kasance makusanci na sarki  ya hau kan karagar sarki ya zauna: to tabbas rudunarmu basu da saa kuma baza su dawo ba a raye::


idan kuwa yaki zama akan karagr sarki to tabbas sarki dujalu zai dawo gida a raye:


Kofa gimbiya Hursiya taga yan majalissar sun kura mata idanu sai hankalinta ya dugunzuma ta dada tabbatar da cewa lalai akwai wani mugun abu da ke ransu:

Awannan Lokaci aljani barzaru na biye da ita yana take mata bayan don tabbatar da tsaro amma babu mai ganinsa face gimbiy Harsiya kadai:


har Gimbiya hursiya ta nufi inda karagar sarki take da nufin ta zauna sai aljani barzaru yi sauri ta sha gabanta yayi mata nuni da jada taje ta zauna akan karagar:

page 42

batare da gardamar komai ba kuwa ta sauya wuri taje ta zauna akan kujerar da ta saba zama ko da yaushe a fadar kamar kullum:

koda ganin haka sai jikin yan majalisar ya yi sanyi gaba dayansu sai murna takoma ciki kuma hankain su ya dugunzuma sabo da burin da suke son cikawa tsawon shekara da shekaru ya rushe alhalin wannan ce kadai damar da suke da ita da zasu kawr da bakin zalunci da aka dade ana yi musu a nahiyar:


a  wanna lok  Icin fadar tacika makil da mutanen gari da duk inda mutum ya duba sai dai yaga kawunnan bil adama rututu ako ina bbu masakar sinke:


ba komai ne ya janyo wannan cikowa ba face mutane sun ji cewar gimbiya hursiya ce kadai ta dawo daga can baki kogin bahar safiya don haka kowa yana son yaji halin da yan uwansa ke ciki wadanda suka tafi yaki::


Page 43


bayan Gimbiya Hursiya ta zauna akan wannan kujera wadda ta saba zama akai sai aka buga  mata tamburan sarauta gami da bushin algaita don girmamawa a gareta bisa matsayinta na kanwar sarki:::


Ana gama buga tamburan ne gimbiya hursiya ta mike ta fuskacin jamaar gari tace ua ku jamaata ina mai sanar da ku cewar wannan yaki da muka fita mun fita akan saa da nasara domin kuwa na baro jamaarmu suna ragargazar jama ar sarki maharaz doin haka akwai cikakakiyar alama tacewar mune zamu ci wannan yki::


koda gimbiya Hursiya tazo nan a zncenta sai fadar ta rude da shewar mutane jama a su cika da dumbin farin ciki kuma suka sami kwanciyar hankali ba komai ne ke damub mutne ba facw tunanin yan uwansu wadanda aka tafi da su yakin suna ga nin cewa ba lallai bane su dawo ba amma jin cewar sune kesamu nasara a yakin sai suka sami nutsuwa sun san cewa da yawan  jama arsu za su dawo a raye::


haka gimbiya Hursiya ta cigaba da kwantar musu da hakalin jama a cikin  kalami na kara kwarin guiwar har suka sami cikakkiyar nutuswa da fahimta:

a sannan ne ta sallami kowa  a fadar ta watse kowa ya kama gabansa::::


*     *      *      * 

lokacin da yan majalisar suka fice daga cikin fadar sai suka kewaye daya bayan daya a sirrince suka hadu acan gidan waziri sarki dujalu wanda ake kira MAZARUB IBINI HALSHAM kuma basu taru ba sai da dare ya raba saada gari yayi tsit ba a jin sauti komai face kukan tsuntsaye da nakarnuka::::

::::::::

A cin wani babban falo na waxiri mazarub suka hadu: hatta barori da bayi na gidan a wannna rana tsaresu aka yi a wani daki dabam don kada su gazuwan yan majalisar ko su ji abinda zasu tatauna :

dakarun dake tsaron gidan ne kawai suke kai kawo wadanda suka kasance aminatattun waziri mazarub:::


bayan kowa ya gama hallara a cikin wannan falo sai aka janyo kofofi da tagogin falon aka rufee sannan wziri maharab yai gyaran murya ya kalli yan majalisar mutu tara shine cikon na goman wadanda gaba dayansu sun kasance dattijai babu dan kasa da shekara hamsin da biyar a cikinsu:

waziri marzub yace yaku yan majalisa kun sani cewa shekara da shekaru tun zamanin mahaifin sarki dujalu muke fama da kunci bakin ciki gami da takaici bisa irin mulkin zalunci da ake yi mana ::


babu sasauci ga basarke attajiri ko talakan gari:

Gaba daya kasashen dake wannan nahiya a karkashin ikon sarki dujalu suke sai abinda yace shi akeyi:

Yafi kowa dukiya karfi tsafi da karfin dantse amma dik da haka ya raina wanan baiwa daya samu kuma so yake ya mallaki duniya nan gaba danyata;;

Shin haka za mu cigaba da zuba ido muyi ta zama a matsayin bayinsa yayanmu da jikokinmu masu cigaba da yi masa bauta har abadan abidina::::::::::::::::


ANAN ZANDAKATA BAYAWA SAKAMAKON BANDA LAFIYA SOSAI ALLAH YASA MUDACE

MAZAN JIYA 4

Littafe na hudu

Part 9

typing::: Suleiman zidane

kusa ni fa cewa mune makasantansa amma

bai san darajarmu da kimanmuba:

to ko mutuwa yayi haka yar uwarsa

gombiya Hursiya zata ci gaba da azabtar

damu:

Tunda yanzu sarki dujalu yana can sassann

yakin da yafi kowanne yaki hadari a

rayuwarsa mun sami dsmar da zamu kawo

karshen bakin cikinmu::

Yanzu gashi yar uwarsa ta dawo tace wai

mune muke samun nasara a wanna yaki ta

yaya zamu iya tabbatar da cewa abin data

fadi gaskiya ne:

kumas ta ya ya zamu iya cimma burinmu mu

yar da kwallon mangwaro mu huta da

kuda?

Sa adda waziri mazarub yazo nan a

zancensa sai falon yayi tsit Tamkar mutuwa

ce ta gifta gaba dayan suka kama muzurai

suna kallon junansu aka rasa wanda zai ce

kala::

page 46

suleiman zidane:

daga can sai wani tsohon mafi shekaru a

cikinsu wanda ya kasancve dan wada

wanda tsawonsa bai wucce kamu shida ba

mai suna SADUSA ya mike tsaye yana mai

gyaran murya:

Nan fa kowa ya Uba masa idanu:

NIMA ZIDANE NA BISHI DANA MUJIYA:)::

sadusa yai murmushi sannan ya shafi dogon

gemunsa wanda ya sauko har kasan cikinsa

yace yaku yan uwana yan majalisa ku yi sani

cewa ga dade ina jiran zuwan wannan rana

har mana fidda tsammanin zuwanta ama sai

gashi tazo::

ina so ku sani cewa a duk fadin kasar nan

da nahiyar nan bani da wani makiyi wanda

yafi sarki dujalu::

domin a sanadinsa ne na rasa iyayena

iyalina da dukkan dangina:

A yanzu haka ni kadai ne na rage daga

cikoin zuri armu hakam ya samo asali ne

akan wani laifi da zuri armu tayi masa yasa

aka rinka kamosu daya bayan daya ana yi

musu yankan rago:::

A wannan lokaci ni bana wannan nahiyar na

bazama cikin duniya neman ilmin tsafi:

Ban dawo ba sai bayan sarki dujalu ya gama

kashe gaba dayan zuri ar tamu gidamu

mana iskeshi a kone kurmus ko tsinke guda

daya ban samu ba::::::

Page 47

a bakin wani makofcinmu na sami lbrin

abinda ya faru ga zuri ata gaba daya:

Nan take zuciyata ta kama tafarfasa kamar

zata kone sbda fishi::

Nan fa wannan makoci nawa ya shiga

rarrashina yana mai bani shawarar na

hanzarta na bar garin nan domin idan sarki

dujalu ya sami lbr cewa ina dsga cikin zuri

ar da suka yi masa wannan laifi tabbas

kashe ni zai yi::

A wannan lokaci ina ta faman rusa kukane

na bakin ciki amma ko danaji wananan

makofci nawa yace wai sarki zai sa a

kasheni:

Sai na bushe da dariyar takama na ce ai na

wuce wannan matsayi: Kai dai kawai ka

zuba ido ka sha kallo:

Ba komai ne yasana yarda da kaina ba sai

bisa tarin dumbin ilimin da na samo na tsafi

don haka ina ganin cewa zan iya kare kaina

daga dukkan masifa:

Nan take na mike tsaye na yiwa makobcin

nawa sallama sannan na bude jakata na

debo dukkan gurayena da layu na tsafi na

daddaurasu a jikina:

Bayan na kammala shiri sai na durfafi fadae

sarki dujalu kai tsaye ba tare da fargabar

komai ba:

Lokacin da na isa fadar sarki dujalu sai na

isketa a cike makil da fadawansa da

;mutanen gari ana tafiyar da harkokin

mulki::

Page 48

duk da cewar fadar cike take da dajaru a ko

ina masu kwarjini da banTsoro amma ni dai

ko gezau banyi ba na cigaba da tunkarar

inda karagar sarki take:;

Su kansu dakaru da zarar sun ganni sai ka

ga suna buda mini hanya ina wucewa:

koda sarki dujalu ya hangoni na durfafo

inda yake zaune sai ya kura mini ido kawai

yana sauraron isowata:

kafin mutum ya isa inda aka ajiye karagar

mulkin sarki dujalu akwai wadansu

dardumai guda uku da aka shimfida kala

uku:

fara baka da ja:

tunda sarki dujalu ya hau kan mulki aka

shimfida wadannan dardumai amma ba a

taba ganin ranar da wani mahaluki ya taba

isa inda dardumai farko take ba wato

wannan farar darduma ya take ba bare har

ya taka ta biyu da ta ukun komai matsayin

mutum komai jarumtakarsa da karfin

sihirinsa ma baya iya zuwa ya taka wannan

darduma ta farko::

Kawai sai na cigaba da tafiya ina durfafar

sarki dujalu:

A lokacin ne gaba dayan mutane dake fadar

suka cika da mamakina kuma suka zubo

mana idanu nida sarki dujalu domin su ga

abinda zai faru:

Saboda ba a taba ganin wanda yashigo fada

ba a haka babu iso kuma babu sallama

sannan kuma gashi ya durfafi inda sarki ke

zaune an rasa badakare daya da zai tsayar

dani::::

Haka dai na cigaba da tafiya har na sami

nasarar taka durduna ta farko:

Al:amarin da yai matukar baiwa kowa

mamki kenan:

Shi kansa sarki Dujalu sai da Gyara zama

Yana mai Al ajabina:

Na ci gaba da tafiya sai gashi na taka

darduma na biyu::

page 49

Suleiman zidane kd

Kawai sai aka ga sarki dujalu ya mike tsaye

ya zare takobinsa jikinsa ya kama tsuma har

fuskarsa yana yi gatsine:

Nima Sai na zare waya adda wacce ta fini

tsawo tana sheki gami da wani irin walwali

na tsafi::

Na cigaba da tafiya da nufin na taka

darduma ta uku wacce ta kasance ja:

Koda na iso karshen darduma ta biyu sai na

kasa daga kafata na cigaba da tafiya:

Nan fa na shiga karanta wadansu dalasimai

na tsafi domin na wuce gaba amma sai

nakasa;

koda ganin abinda ya faru sai sarki dujalu ya

bushe da dariyar farin ciki; lokacin guda

kumkuma ya turbune fuska ya dubeni yace

lale

marhaban da sadusa ibn zaiyar T@bbas ban

ga laifinka ba da kake kokarin kasheni

tunda nine na kashe iyalinka danginka da

duk zuri arka:

A rayuwarta ban taba zaton cewa akwai

mahalukin da ya sami sihirin tsafin dake daf

da nawa ba tabbas na san cewa kasha

bakar wahala kafin ka sami sihirin tsafin da

kake da shi a yanzu samun kmarka a doron

kasa a yanzu sai an sha wuya:

Bisa wannan dalilin ba zan kashe kaba duk

da cewar ya kamata na kasheka din sbda na

san cewa ka tsaneni fiye da yadda ka tsani

mutuwarka: zan kyaleka kuma daga yau ka

zama dan majalisata amma busa sharadi

guda daya;

Sharadin kuwa shine idan har kayi wani

yunkuri na cutar dani zan yi maka daurin rai

da rai a kurkuku inda zaka karasa sauran

rayuwarka ta duniya:::

Page 50

Sa adda tsoho sardusa yazo nan a lbrinsa sai

kowa yayi ajiyar zuciya a cikin falon:::::

ANAN ZAN DAKATA SAI KUMA IN ALLAH YAKAI

MU GOBE DA SAFE::

NAKU SULEIMAN ZIDANE KD KURINGA YI

COMMENT::::.

MAZAN JIYA 4

Littafe na hudu

Part 10

Typing: Suleiman Zidane Kd::

Sa adda tsoho sardusa yazo nan a lbrinsa

kowa yayi ajiyar zuciya a cikin falon sannan

sadusa ya cigaba da bayani yace yanzu

abinda ya kamata mu fara yi shine mu

tabbatar da gaskiyar lbrin da gimbiya

Hursiya tazo mana da shi:

SHIN gaskiya ne mu muke samun nasara?

Babu wata hanya da zamu iya sanin hakan

face mu tashi aljni mai tsananin karfin

gudun da zai iya zuwa bakin kogin Bahar

Sufiya koda a cikin kwana bakwai ne yaje ya

gano mana zahiri Al;amarin:

Idan har su sarki maharaz ne ke samun

nasara to tabbas akwai tuggun da zan iya

shiryawa mu yiwa sarki dujalu juyin mulki

yadda ba zai taba iya karba karagarsa bA:

Amma fa idan mune muke samun nasara a

filin yakin sai dai mu rungume kaddara mu

cigaba da zaman hkri har ixuwa sa;adda

ajali sarki dujalu zaizo: yanzu babbar

matsalar ita ce gaba dayan aljanun dake

wannan nahiryar tamu sarki dujalu ya tafi

da su wannan yaki saura matansu tsofaffi

da yaransu wadanda baza su iya wanan Aki

ba:

Sarauyin aljani mai tashen samartaka da

kafin gudu data be ya rage a yanxu kua ba

wani bane face aljani barzuri wanda

yadawo da Gimbiya Hursiya daga CAN bakin

Tekun Bahar sufiya:

Barzaru ya kasance amintaccen sarki dujalu

na gani kasheni don haka bazai taba yarda

yayi mana wannan aiki ba sai dai maya tona

mana asiri:

Ya zama wajibi nayi shiti da kaina na bar

wannan nahiya tamu na tafi nean aljanin

dazai yi ana wannan aiki a cikin gaggawa:

Page 51

SULEIMAN ZIDANE KD

sa adda sadusa yazo nan a zancensa sai

hankalin kowa ya kara dugunzuma domin

suna ganin cewa ai babu isasshen lokacin

da za ayi wannan aiki:

Cikin alamun tsananin damuwa waziri ya

dubi sadusa yace yanzu a cikin kwana nawa

kake ganin za ka iya zuwa kasamo aljanin

da zai yi mana wannan aiki?

Sadusa yai murmushi yace ku bani kwana

uku rak Ai Al mari ne na tsafi:

Koda jin haka sai farin ciki ya lullbe waziri da

sauran yan majalisar:

Nan take suka salami sadusa akan cewa za

su jira dawowarsa nan da cikar kwana uku:

Nan dai taro ya watse kowa ya sulale ya tafi

gidabsa cikin wannan dare:

* * *

AL AMARIN Gimbiya Hursiya kuwa; tun

sa;adda fada ta watse ta shige cikin gidan

sarautar sai ta wuce izuwa cikin turakarta ta

zauna a gefe gadonta ta shiga tunani mai

zurfi:

Page 52

A dai dai wanan lokaco ne wata kuyagarta

mai suna laziramat ta shigo cikin turakar

dauke da farantin shayi:

shi dai wannan shayi na ka:ida domin

kullum sai lazimat ta dauko butar shayin ta

tsiyaya a cikin wani dan karamin kofi na lu u

lu u ta kaiwa Gimbiya Hursiya:

Koda ta mikawa Gimbiya kofin shayin sai ga

ashe Gimbiya kuka take yi hawaye na ta

sartu kan kumatuwanta:

Al amarin da yai matukar dugunzuma

hankalin lazimat ke nan dubeta cikin

tsananin damuwa ba mai ajiye kofin shayin

akan faranti ta ce ya shugabata ki yafeni

idan nayi miki wani abu wanda ya bata miki

rai:

koda jin wannan batu saI Gimbiya Hursiya ta

sa hannu ta share hawayenta sannan tace

ya lazimat kiyi sanicewa a iya zamana dake

Tsawon shekaru baki taba yi mini wani abu

ba wanda ya bata min rai::

Wannan hawaye nawa dakika gayana zuba

bana komai bane face na tsananin bakin ciki

bisa karyar dana yiwa mutanen garin nan a

yau a fada:

Maganar gaskiya ban san abinda ya faru ba

a filin yaki domin ana daf da fara yakin ne

sarki shammaceni yasa aljani barzaru ya

sureni yai sama da ni kafin na ankara ya

luluka dani izuwa cikin gajimare:

Cikin abinda bai wucce kwanaki tara ba

muka iso nan gida;

Page 53

Ni yanzu babban abin bakin cikina shi ne

idan sarki ya mutu bana son na gajesgi

kuma yazama duniya babu wani mutum

dana shaku da shi sai shi;

Mene ne amfanin naci gaba da rayuwa a

duniya bani da masoyi?

Mulki daula da arziki duk shire ne a wannan

duniya idan babu masoyi:

Soyayya itace abar da take kawar da dukkan

takaici da bakin cikin rayuwa:

koda Gimmbiya Hursiya tazo nan a zanceta

sai kunyaga lazimat takamu datsananin

tausayinta har itama kwalla ya cika mata

idanu ta dubeta tace ya shugabata to yanzu

ke wanne irin hukunci kika yankewa

rayuwarki?

Hursiya ta ajiyar zuciya sannan tace ni yanzu

bana bukatar koai face na koma can bakin

kogin Bahar Sufiya domin naga yadda

karshen wannan yaki zai kasance idan har

sarki mutuwa zai yi to zanso na mutu tare

da shi amma bana son ace sarki ya mutu ni

nacigaba da sarauta anan sbda basan cewa

kamar yadda mutne ke kin sarki haka nima

zasukini:

Nasani cewa dan uwana Azzalumi ne

tsawon shekara da shekaru mutanen dake

nahiryar nan basa jin dadi mulkinmu tun

iyaye da kakani::

Page 54

kin sani cewa nima bana son irin wannan

mulki da sarki ke yiwa jamaa amma ban isa

na hanashe ba don haka ciwon ido sai hkri:

Ni ina ganin cewa zai fi kyau ni da sarki duk

mu mutu a wajen wannan yaki domin a

sami sabo shugabanci a wannan nahiya

mutane su huta da mulkin zalunci a sami na

sauyin rayuwa mai dadi:

Koda Hursiya tazo nan azancenta sai ta

fashe da kuka Al amarin da ya kara jefa

kunyaga lazimat cikin tsananin tsananin

tausayinta kenan ta rungumeta ta

na mai rarrashinta har tadaina kukan

sannan ta ja jikunta daga cikin na tata

debeta tace;

ya shugabata kiyi sani cewa a iyarayuwata

ta duniya ban taba zama da basarake mai

tunani da sani yakamata ba kamarki wanda

yake da jin kai gama son talakawansa tunda

gashi kin zabi ki mutu don kawai takawa su

sami rayuwa mai dadi:Ya shugabata kiyi

sani cewa rashinki a doron kasa ba karamar

asara ba ce domin samun mace mai kyau da

kyan hali irin naki sai an tona:

Ya kamata a ce kin sami saurayi kyakkyawa

kuma mai kyawun hali irin na ki domin

yazma abkin rayuwarki ku haifawa baya

abinda zasu amfanesu;

yayin da Gimbiya Hursiya taji wannan sai

murmushi ya subuce mata tace ai niban

yaba yin soyayya ba kiuma ban zaton zanyi

ta anan gaba har izuwa karshen rayuwata

ban san maye SO ba:

Tun ban taba kamani ba:

KAUNA kawai na sani irin wacce ke

tsakanina da dan uwana sarki dujalu da

kuma mutane ire irenku wadanda nayi sabo

da su sanadiyar zamantakewa;lokacin da

Gimbiya hursiya tazo nan a zanceta sai itaa

kuyanga lazimat

Tayi murmushi tace ya shugabata kada kiyi

kuri ko cika baki akan SOYAYYYA Domin

kuwa shI SO abu ne wanda baya sallama

bare ayi masa iso a duk yayin da yaga zuciya

yake nean shiga cikinta::

Karfin gudunsa ya wuce na iska ko guguwa

haka kuma DAFIN SO yafi na kibiya:

A duk sa:adda ya soki mutum to fa babu

wani magani da zai warka dashi face

kasancewa tare da masoyinsa::

Page 55

ANAN ZANDAKATA SAI KUMA IN ALLAH YA

NUNA MANA GOBE LPY ZAMU CIGABA :::::

ZIDANE COMMENT::::

,MAZAN JIYA 4

Littafe na hudu

Part 11

Typing:::: Suleiman zidane kd

PAGE Home of Littafan Yaki  And Hausa Novels

Dajin wannan batu sai Hursiya ta bushe da dariya sannan ta dauki wannan kofin shayi ta kurba sau uku tace daga yau mun kulla gasa nidake na ga wanda zai lashe gasar:

Ni Hursiya na cika miki baki cewar KIBIYAR SO ba ta isa ta huda jikina ba bare ta samini dafin da zan rasa maganinsa::

Duk ranar da kika lashe wnnan gasa in dai ina raye nayi  alkawari zan yantaki kuma zan baki dukiya mai yanwa gaske:


Koda jin wannan batu sai kuyanga lazimat ta kamu da tsananin farin ciki tace tabbas zamu bambance tsakanin aya da tsakuwa kuma lokacin ne zai raba wannan gardaa dake tsakaninmu Hursiya ta yi ajiyar dogon numfashi a lokacin data ajiye wannan kofin shayi sannan ta kurawa lazimat idanu tace yanzu wacce hanya kike ganin zan bina sami damar komawa sansanin yakin nan a cikin yan kwanaki kadan kafin yakin yakare?

Yayin da lazimat taji wannan tambaya sai hankalinta ya dugunzuma tayi shiru tana tunanun har izuwa tsawon wadansu yan dakiku kamar ba zatace komai ba:


Page 56

suleiman z kd


Daga can sai ta kawo gwauron numfashi ta aje sannan tace ya Shuganta akan bukatarki ta biya zan iya sallaa raina da jikina sbda kauna da aminci dake tsakaninmu don haka ki bani kwana biyu rak zan je na biwata hanya wucce nake gani cewa zata kaimu ga nasara::


Koda jin haka sai gimbiya Hursiya takamu da tsananin farin ciki nan take ta bude wata farar akwati ta debo dinare da yawa batare da sanin adadinsa  ba cikin tafin hannunta ta mikawa lazimat tace ungo wannan ki tafi da shi sbda nasan cewa yanzu aiki  wannan zamani babu wani wani aiki da yake tafiya ba tare da kudi ba:


Lazimat tacce haba ya shugabata ai wannan kudn yayi yawa:

Hursiya ta kada kai tace ai girman wannan aiki da nabaki yafi wannan dinare cikin turakar nan tawa duka:

Hadarinsa kuwa dai dai yake da mutum ya sayi ajalinsa inda zan baki dukiya cikin gidan sarautar nan gaba daya ban biyaki ladan wannan aiki ba:


Page 57


Ki tashi ki tafi na sallameki sai nan da kwana biyu ki dawo mini da jawabi mai dadi sai ki wakilta wata daga cikin sauran kuyangina ta cigaba da yin irin aikin da kika saba yimini::


Amma lallai ki sami mai amana wacce zata iya rike sirrina:

kunyanga lazimat ta risina cikin biyayya tace angama ya shugabata:::


WANNAN SHINE ABIN DA YAFARU A BIRNIN SARKI DUJALU BAYAN ALJANI BARZARU YA DAWO DA GIMBIYA HURSIYA DAGA BAKIN TEKUN BAHAR SUFIYA INDA AKE SHIRIN FAFATA YAKI TSAKANIN RUNDUNARSU DATA SARKI MAHARAZ:::

*     *     *


ACAN Sansanin yaki kuwa awana na ukun da akayi ana hutun yaki kullum inmal da sarki mahazar suna zaune a gaban kabarin sarki yaki Hibru suna kuka dare da rana:


Abinci a da kyar suke cin kadan idan Gimbiya Mulaifa ta matsa musu tana mai yi musu tuni da cewar idan fa basu ci abinci ba to fa bazasu sami damar cigaba da yakin ba tunda bazasu samu kuzari ba ajikinsu::


Wannan batu ne yasa suke daurewa su ci abinci kadan bayadda zasu koshi ba:


A ranar dare na biyu ne sarki maharaaz inmal da sauran manyan daraunsu na  Yaki suka zauna domin su tattauna akan yadda zasu bullowa wannan yaki a wannan karo na uku domin su sami nasara akan abokan gaba cikin kankanin lokaci:


Page 58


wani barde da ake kira shamal shine ya fara magana yana mai duban sarki maharaz yace ya shugabana shawara ta ta farko dazna bayar ita ce kamata yayi ana fara wannan yaki inmal tare da manyan jarimanmu masu jarumtakar gaske su yiwa sarki dujalu rubdugu domin a kashe shi da wurin tabbas idan muka sami nasarar kashe sarki dujalu mun karya logon abkan gabarmu tunda a bangaren dakarunu na aljanu karfinsu yazo daidai da na dakarun aljanun su:


koda jin wannan batu  sai sarki maharaz ya dubi kowa yace ya ku dirkokin birnina kun ji shawarar da shamal ya kawo:

Shin kun amince da ita ko kuwa akwai mai korafi aknta:@?


Gaba dayansu sai suka yi shiru aka rasa wannan da zaice kala; sai inmal ne yai gyaran murya sannan ya ce ai ko kadan wannan shawarar da shamal ya kawo ba zata yi tasiri ba:


dalilina na fadin haka shine  masu iya magana sunce MASO ABINKA YAFI KA DABARA: 

kada ku manta cewa shi kansa srki dujalu zai yi irin wannan tunanin da shamal yayi don haka dole ne ya san dabarar  da zaiyi yarufe wannan kofa: abu na biyu da nakeso da nake so ku gane shine:

Dakarun yakinsa suna da bakin naci fiye da namu dakaru:


Idan muka tattara hankalinu akan sarki dujalu kawai zasu sai damar daza suyiwa namu dakarun mumunar barna:


Page 59


kafin inmal ya gama rufe bakinsa tuni shamal ya tarin numfashinsa yace to wai shin kaanta ne cewar sarki dujalu ya zama masaki mai hannu daya:

wannan lalura da ta same shi zata rage masa karfin da zafin nama:


inmal ya girgiza kai ya ce ba haka bane ai kada mage ba yanka bane kuma ina so ka sancewa mazanjen kwarai suna yaki ne da zuciyarsu kafin jikinsu:


Ma ana taurin zuciyarsu da karfinta yafi na hannayensu sbda haka wannan rashin hannu daya na sarki dujalu ba zai rage shi da komai ba face ma ya kara masa kuzari da mugun nufi akanmu:


Sa adda inmal yazo nan a jawabinsa sai jikin kowa yayi sanyi aka yi shiru ana tunani :

Jim kadan sai wani bardw shi KIMARU ya numfasa yana mai duban sarki maharazz yace ya Shugabana wai shi mezai hana goben da dazar an busa kohon ci gaba da yakin nan ka shammaci abkan gaba ka hallakasu da karfin sihirinka?


Kafin kimaru yagama rufe bakinsa tuni sarki maharaz ya shara masa mari sbda karfin marin sai da kimaru ya tuntsure kasa ya mike zaune wuf, cikin firgici yana mai sunkui da kansa kas::


sauran dakarun kuwa duk sai suka firgita suka sunkuui da kawunansu kas don kada laifin wani ya shafesu::   


Page 60

zidane


Sarki maharaz yadubi kimaru a fusace yace shin kai kurma ne a lokacin da nayi rantsuwa da sunan mai girma darbuza cewar ba zan yi amfani da karfin sihiri ba tun a farkon wannan yaki bisa yarjejiniyar da ke tsakaninmu da sarki dujalu?


To ka sani cewa ni da sarki dujalu babu wandazai yi amfani da karfin sihiri har  a gama wanna yaki tunda shima yayi rantsuwa da ubangijinu kamar yadda nayi:


yanzu dai na fuskaci cewa gaba daynku babu, Wanda yake da wata dabara ko sabuwar hikima wacce zamu yi amfani da ita don ganin mun saminasara r wannan yaki::


Abin da nakeso da ku kawa shine kowa yaje yayi shirin tunkarar wanannan yaki gobe idan aka fara yakin kowa yayi iya kokirinsa lallai sa a tana ga mai rabo walau garemu kukuma garesu::


koda gama wannan jawabi sai sarki maharaz ya mike tsaye ya tafi izuwa cikin tantinsa:

a sannan ne su bardw kimaru a suka tashi suka tafi izuwa nasu tantunan aka bar sadauki inmal a zaune shi kadai a lokacin da yada cikin kogin tunani:

A wannan lokaci wata irin iska mai sanyi ke kadawa:


inmal na cikin wannan tunanin ne yaji an taba kafadarsa ta baya:;


Cikin dan alamun razana inmal ya waiga da sauri don a zatonsa aljanu ne keson tabashi::


Page 61


koda ya yi arba da wanda ke tsaye abayansa sai ya cika da mamaki:::


PAGE Home of Littafan Yaki  And Hausa Novels


ANAN ZAN DAKATA SAIKUMA IN ALLAH YA KAIMU GOBE NAKU S ZIDANE KD:::


COMMENT:::::::::::, ,


MAZAN JIYA 4

Littafe na hudu

part 12

Typing: Suleiman zidane kd::


koda ya yi arba da wanda ke tsaye abayansa sai ya cika da mamaki:::


:ba wani bane face Gimbiya mulaifa:

Mulaifa da inmal suka yiwa juna murmushi sannan ta zauna a kusa da shi suka dubi gabas ba tare dayansu yace kala ba har izuwa tsawo yan dakiku:


Inmal ne ya katse shirun yace menene ya hanaki yin barci har izuwa tsawon wannan dare?


Mulaifa ta sake yin murmushi a karo n biyu sannan tace abinda ya hanaku yin barci kai da abbana shi ne ya hanani:


Ya kai abin kaunata kayi sani cewa bamu taba tsintar kanmu a cikin halin bakin ciki irin na wannan lokaci ba sakamakon mutuwar mahafinka::


Sannan kuma  bamu san yadda karshen wannan yaki zai kasance ba:


Ni babban abin ma daya dugunxuma hankalina shine naga mahaifina jikinsa yayi sanyi gaba daya akwai alamar cewa bashi da sauran  kuzari da sa ran samun nasara a wannan yaki:


Koda jin wannan batu sai inmal yayi ajiyar zuciya ya ce ni kaina jikina yayi sanyi ba don komai ba sai sbda ina ginincewa karshen wannan yaki ba zai yi kyau ba: 

Za a yi asarar miliyoyin rayuka ko dai ayi ragas ko kuma ayi kare jini biri jini:


Ni babban abinda yake damuna guda biyu ne:

Abu na farki shine na tsaya nayi tunani na gano cewa damu da su sarki dujalu duk muna yin wannan yaki ne sbda son zuciya kawai kowanne bangare suna son su mallaki kayan yakin MAZAN JIYA don kawai su mulki duniya:


Wannan duk al:amarin ne na zalunci:

Ni ka zan fi son su mallaki kayan Yakin MAZAN JIYA don kawai su mulki duniya:


Page 62


wannan duk al amarin ne na zalunci: 

Ni ka zan fison na mallaki wadannan kayan yaki na MAZAN JIYA don kawai na bar abin tarihi na jarumtaka wanda baza ataba mantawa dani ba:


Abu na biyu da yake damuna shi ne zuciyata tana rawa akan allolin da ake bautawa a wadannan nahiyoyo namu sbda na fuskanci cewar suna yin karya: 


Sau tari sukan fadi wani abun suce zai faru amma kuma sai aga sabanin haka:


An ya kuwa ba kya ganin cewa akwai wani ubangijin wanda yafi dukkanninsu wanda shine ne mafi karfi da daukaka?


Koda jin wannan tamabaya sai mulaifa tayi ajiyar zuciya sannan tace hakika duk abinda ka fada gaskiya ne kuma duk mai hankali dole ne yayi tunani akan hakan:


To amma abinda nake so naki daga gareka shi ne shin kana da wata hujja ne mai karfi wacce tasa ka fadin hakan?

Inmal yayi shiru yana mai daga kansa sama cikin alamun tunani sannan yace akwai wani lokaci a baya da marigayi mahaifina ya gaya mini cewa akwai wani ADDINI da ake kira ADDININ MUSULUNCI: YA tabbatar mini da cewa bai taba ganin mai karfinsa ba kuma yaji ajikinsa cewar shine addinin gaskiya sbda abinda ma abotansa suka sa a gaban koda jin wannan batu saijikin Gimbiya mulaifa yai sanyi tayi shiru har izuwa tsawon yan dakiku sannan tadubi inmal

Inmal tace ni kaina yanzu naji a a cikin raina na gamsu da wannan addini domin ka karbi addininin mu sami taimakon ubangijinsa bisa wannan gagarumin yaki dake gabanmu:


Inmal ya ja dogon numfashi yace hakika maganarki dutse ce amma tunda babu damar hakan sai mu rungumi kaddara:


Ta shi muje mu kwana domin kuwa dare ya raba sosai:

Yana da kyau mu sami barci a wannan dare sbda gagarumin aikin dake gabanmu a gobe::

mulaifa ta mike tsaye tace zanje dai na kwanta amma tun nayi barci ba zan iya ba tunda ina cikin fargaba da zullumi bisa abinda ka iya faruwa gobe:


Hatta kai da sarki duk nasan cewa baza ku iya rintsawa ba a wannan dare::

inmal yayi murmushi karfin hali yace hakika maganarki gaskiyace::


Page 64


koda gama fadin haka sai ya kama gannun mulaifa yaja ta izuwa ga tantin sarki:::

Koda suka iso kafar tanti sai ta dubeshi tace inason na karar da wannan dare tare dakai gaba dayansa tund babu mamaki daga yau ba zamu sake samun damar jin muryar juna ba da ganin fuskokinmu::


Koda jin haka sai inmal ya girgiza kai ya ce ai duk wuya duk dadi komai RINTSI DA TSANANI ina san ran cewa bazamu rabu ba kumma muna tare:::::


ki sani cewa mahafinki ya gaya mini cewa bisa binciken da yayi a hallarar tsafinsa lallai mutum hudu zasu tsira da rayuwarsu a wannan sansanin yaki:

Kuma mutum biyu daga bangare abkan gabarmu ne ragowar mutum biyu kuma daga namu ban garen:


Ina ji a jikina cewar kina daya daga cikin mutane biyun :

koda inmal yazo nan a zancensa sai idnsa suka ciko da kwallah har hawaye yazubo masa :

Al amarin da ya dugunzuma hankali mulaifa kenan ta rungume inmal tana mai cewa yakai abin kaunata ina dalilin zubar wannan hawaye naka?


Inmal yace ba komai ne yasani wannan kuka ba face tunanin cewa zan iya rasa babban masoyina na biyu a wannan yaki wanda na tabbatar da cewa yana sona kamar yadda mahafina marigayi yake sona:::


Page 65


Dajin wannan batu sai hawauye yazuvowa wa mulaifat tace Tabbas na san ba

wani kake nufi ba face mahaifina::

Koda jin haka sai inmal ya dada kankame

mulaifa a kirjinta yana mai sake fashewa da

sabon kuka: itama ta tayashi da kukan::::

A haka dai suka karasa cikin tantin na ta

suka zauna suka cigaba da hira maimakon

su kwnta su yi barci basu gushe ba suna

hira har sai da Alfijir ya keto a sannan ne

mai sacewa ya sacesu basu sani ba suka

kama gyangyandi:::

Sai da gari ya waye sosai har rana ta hudo

bayan kowanne bangare na mayanka sun

kimtsa sannan aka yiyo gayya aka taho filin

daga:: azuvowa wa mulaifat tace Tabbas na san ba wani kake nufi ba face mahaifina::


Koda jin haka sai inmal ya dada kankame mulaifa a kirjinta yana mai sake fashewa da sabon kuka: itama ta tayashi da kukan::::


A haka dai suka karasa cikin tantin na ta suka zauna suka cigaba da hira maimakon su kwnta su yi barci basu gushe ba suna hira har sai da Alfijir ya keto a sannan ne mai sacewa ya sacesu basu sani ba suka kama gyangyandi:::


Sai da gari ya waye sosai har rana ta hudo bayan kowanne bangare na mayanka sun kimtsa sannan aka yiyo gayya aka taho filin daga::

MAZAN JIYA 4

littafe na hudu

Na Abdul Aziz sani madakin Gini.

Page. Home of Littafan Yaki  And Hausa Novels

Part 13

Typing::: Suleiman Zidane 

Whatsapp 09064179602

sun kimtsa sannan aka yiyo gayya aka taho filin daga::


*  *     *


sarki dujalu akan gaba tare da zakwakuran dakarunsa cikin  gagarumar shigar yaki mai tsananin kwarjini fiye da wadda suka yi a yakin daya gabata:


*  *  *

 A bangaren su sarki maharaz kuwa inmal ne akan gaba shima tare da nasu zakwakuran mayakan ababan dogaro:


A kowanne bangaree kuma a sararin samaniya aljanu ne ke shawagi rike da muggan makai na KARE DANGI::

Kawai jira suke a basu umarni su afkawa abkan gaba::

***

Page 66

Sarki maharaz ma sai gashi akan gaba kusa da inmal rike da takobi da garkuwa:

Al amarin da yai matukar baiwa inmal mamaki ke nan kuma ya firgitashi ya dubi sarki maharaz cikin tsananin damuwa yace Ya Shugabana mene ne ya kawoka nan gaba alhalinka san cewa kai ba gawurtaccen ma yaki bane kuma gashi ba za ayi amfani da karfin sihiri ba a wannan yaki face tsagwaron karfin dantse kwarewa da sanin makama:


Sa adda sarki maharaz ya ji wannan tambaya ta inmal sai yayi guntun murmushi cikin yake yace ya kai dana kayi sani cewa ni yanzu komai na duniya yafita daga raina koda mun sami nasarar wannan yaki kuma mun sami nasarar dauko Takobin SAIFUL LUJARA bani da sauran bukatar na mulki duniyar tunda abkan jin dadin mulkin nawa bbu shi a lokacin da burin nawa ya cika na mallaki kayan yakin maxan jiya a sannan ne zan biya abkina Hibru wahalar bautar daya yi mini da kua hkrin da yayi dani na tsawon shekaru ina wulakantashi da rashin jansa a jikina::


ina so kasani cewa yau ne ranar farki da zanyi yaki a cikin fishin da ban taba yi ba sbda haka lallao zan baka mamaki a wannan yaki ::


Zan yi gagarumar jarumtaka irin wacce ban taba yi ba kuma zan ragargaji abkan gaba da yawan gaske::


Page 67

suleiman zidane kd


Sa adda sarki maharaz ke wannan jawabi sai ya hango gimbiya mulaifa a can bayan mayakansa a tsaye bisa kan wani dutse mai tudu tana hango abin da ke faruwa:

koda ganinta sai idanun sarki maharaz suka ciko da kwallah ya dubi innal yace yakai dana kayi sani cewa a bayan wannan yaki ne uwa da uba a waken mulaifa sbda haka na damka amanarta agareka:


Ina mai farin ciki daya zamana cewa yata ta kamu da tsaananin kaunarka ko ba komai na san cewa ba zan mutu na barta a matsayin marainiya ba mara kowa ko masoyi ba na san tana da kai:

*   *  *

A dai dai wannan lokaci ne sarki dujalu ya zare takobinsa da hannunsa na hagu daya dungulmin nasa na dama kuwa na boye acikin rigar da ke jikinsa::


yana zare takobin tasa kuwa sai yadubi inmal ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa mai amsa kuwwa hari sai da kasa takama girgiza kamar zata tsage komai ya rufta cikinta sannan yace ya kai da mai kamar ubansa kayi sani cewa yakin da zamu yi yau ba irin wanda muka yi bane a karon farko kuma ba irin na karo na biyu bane:


Yanzu zamu kaure ne da yaki kwanmu da kwaekatarmu:

Ma ana mu cakude mutanenmu da aljaninmu kuma ba yaro ba babba babu tsoho ko tsohuwa bare mace ko namiki:


babu sani kuma bbu sabo Zamu yi ta yi har sai mai nisan kwana a cikinmu ya tsira da rayuwarsa: 

Amma bisa sharadin nan dai na farko wato babu batun amfani da karfin sihiri sai tsagwaron karfin dantse:


Kafin inmal ko sarki maharaz daya daga cikinsu ya budi baki yace wani abu tuni sarki dujalu yayi nuni da takobinsa izuwa ga rundunar su sarki maharaz::


Page 68


Wohoho! Ai kuwa nan take gaba dayan dakarunsa mutane da aljanu suka kama zare makaman:

Karar zare makaman ta cika dodon kunne da dajin gaba daya tamkar ana aiki  da dukkan makerun duniya:

Ai kuwa suma rundunar tasu sarki maharaz sai suka zazzarenasu makaman:

A lokacin guda kowannen bangare suka rugo da gudu suna ihu da kururuwa domin a gwamutse:


Wohoho Inda ace mutum na tsaye a gefe daya yana kallon wannan sansanin yaki daga nesa kadan to da nan take zai tsure da gudawa sbda tsananin tsoro da fargabar abinda zai faru::


NIMA ZIDANE BADAN NAKASAN CE JARUMI BA DA TINI NA CIKA WANDO NA DA ISKA)


kai hatta kasa sai mutum ya tausaya mata sbda girgiza ta kama yi kamar zata rufta da duk abinda ke samanra sbda tsabar dudufniyar kafafuwan bil adama dana aljanu sararin samaniya kuwa sai yauo bakikkinri sbda ha yakin bala in dake fita daga cikin bakunan aljanu gami da sautin ihunsu mai haddasa tsawa da walkiya ai kuwa rundunonin biyu na haduwa aka ruguntsu me da masifaffen bala in yaki wanda yafi gaban bayani mai bayani: fasaltawar mai basira ko labarin mai labari kawai sai dai abinda ido ya iya tantancewa:

tartsatsin wuta ya tinka fallatsi a sararin sama yana zuvowa kasa yana haddasa gobara:


page 69

zidan ke magana:::


KAICO! WANDA BAI SAN YAKI DA MASIFA BA SHINE YAKE FATAN SU:


A wannan rana duniyar gaba dayanta sai da ta yi girgiza tamkar zata nutse i zuwa cikin karkashin kasa:

Duk wani abudaya kasance mai rai walau mutum aljan dabba tsuntsu ko kwaro sai daya firgice yayi nadamar zuwn wannnan rana:

Nan fa filin yakin ya ruguntsume gami da hautsinewa da dumulmulewa aka shiga cin kasuwar daukar rayuka:

jini kuwa daya soma fallatsi da malala gami da tsartuwa a sama da kasa sai da kalar bishiyoyi mutane da aljanu suka koma jajaye suka rine da jini babu kyan gani:

Sai da takai ta kawo cewa aljanu nasa shaida yan uwansu aljanu mutane basa gane yan  uwansu mutane; banda sara da suka babu abinda ake ji: 

Sassan jikin bil ada;a kuwa suka rinka shawagi a sararin sama suna zubowa kasa tamkar ruwan samansu akeyi::

*  *   *

Wohoho! JARUMTAKA KYAUTA DAGA ALLAH:

WANDA DUK ALLAH YABASHI SADAUKANTAKA GAMI DA JURIYA DA NACI TO FA SAI DAI AZUBA MASA NA MUJIYA KO KUA AYI MASA ALLAH YA ISA!

DOMIN YAZAMA ALAKAKAI KO KUMA ACE KADANGAREN BAKIN TULUA KARSHI A KAR TULU A BARSHI YAYI BARNA::


Page 70

zidane kd:


duk inda sarki dujalu da jarui inmal suka sa gabansu sai dai kaga mazaje na zubowa kasa tamkar ana sassabe a gona:


Sai da aka shafe sa a bakwai ana asarar miliyoyin rayuka amma duk bala in da ake yi inmal da sarki dujalu suna ta laluben juna amma sun kasa haduwa sbda bala in yaki gami da cakudewarsa:::::: 


Al amarin sarki maharaz Kuwa a wannan rana yayi shammace kuma yayi matukar bada mamaki domin shima sai yazamo gagarumin FASA TARO mai TARWATSA MAZA:

domin duk inda ya durfafa sai dai kaga ana zubewa tamkar ana karkada bishiyar busassun ganyaye:

Takobinsa ma gaba daya rinewa tayi tazama jajawur kamar yadda dukkkanin jikinsa yayi: Kai a wannan rana zufar jini ceta lullube fuskokin mutane aljanu har sai sun goge jinin dake fuskokinsu sanan suke iya gani: 


kai sbda tsananin bala i da masifar wannan yaki sai gaba dayan nahiyar da ake wannan mugun yaki sai da tayi bakikkirin tayi duhi dundum Tartsatsin wutar da ke tashi sakamakon haduwar makaan yaki kawai ya rinka haskawa har ake iya gane juna:

Ana cikin wannan bakin gumurzu ne sarki maharaz ya ga wani bakon jarumi a cikin jama arsa yana ta ragargaza abkan gaba: 

Jarumin ya rufe fuskarsa da jakinsa gaba daya yaddda an kasa shida namiji ne ma ko mace: Yana rike  da takubba guda biyu kuma shima duk inda sarki maharaz ya dauke kafarsa anan yake sa tasa:


Page 71

 Duk sa adda aka kai wa sarki maharaz wani mummunan hari sai kaga wannan bakom jarumi ya kareshi:


Babu abinda ya daurewa sarki maharaz kai face tsananin zafin naman jarumin jarui da tsananin jarumtakarsa tamkar ta inmal:


Burin sarki maharaz shi ne yaga fuskar wannan bakon jarumi amma abu ya gagara:

Ai kuwa shima inmal sai ya hango wannan bakon jarumi koda yaga irin gagarumin aikin da yake yi gami da kare rayuwar sarki maharaz sai ya cika da dumbin farin ciki: 

ya sami dadin kwarin guiwa da kuzari ya ci gaba da tagargazar maza:


KAICO MUTUWA RIGAR KOW:

        BALA I BA A SA MAKA RANA:

MUGUN JI DA MUGUN GANI BA SHI DA DADI:

       TSAUTSAYI DA ASARA BASA JIN BIRKI IN SUKA TAHO TAMKAR KUMALLO SUKE BABU MAI IYA TSAIDA SU::::


ANAN ZAN DAKATA SAI KUMA IN ALLAH YAKAI MU GOBE ZAMU CIGABA::

DAN ALLAH KURINGA COMMENT YANA KARA MANA KWARIN GUIWA WAJE YI MUKU TYPING MAI YAWA::

PAGE:Home of Littafan Yaki  And Hausa Novels

WhatsApp 09064179602

MAZAN JIYA 4

Littafe na Hudu

Part 14

Typing: Suleiman zidane kd:

KAICO MUTUWA RIGAR KOW:

BALA I BA A SA MAKA RANA:

MUGUN JI DA MUGUN GANI BA SHI DA DADI:

TSAUTSAYI DA ASARA BASA JIN BIRKI IN SUKA

TAHO TAMKAR KUMALLO SUKE BABU MAI IYA

TSAIDA SU::::

* * *

Haka dai aka cigaba da wannan yaki wanda

tun daga farko kafuwar duniya kawo i

yanzu ba a taba yin makamancinsa ba

domin sai da aka kwana tara gami da sa a

tara ana zubar da mazaje da aljanu da

mutane a kas a sannan ne tsananin gajiya

da nadama ta sa kowane bangare yayi

janyewar dole aka ja da baya domin

makogwaron kowa ya bushe sbda tsananin

kishirwa:

Hanji cikin kuwa ya kananade ya daure sbda

yunwa:

Shin kasan ruwan Kogin BAHAR SUFIYA

wanda ya rine ya zama jini tafarfasa yake

sbda masifar tartsatsin wutar dake zbowa

cikinsa:

Page 72

Da Zarar mutum ya tsoma hannunsa a ciki

domin ya debo ruwan jinin ya sha ya kawar

da kishirwa sai kaga nan take hannun nasa

ya kone tamkar a cikin wuta ya tsomashi::

** *

Lokacin da kowanen bangare ya ja da baya

aka dai na sara da suka sai gaba dayan

duhun da ya mamaye sama da kasa yayaye

tamkar da can a cikin bakin dare ake gari ya

waye:

A sannan ne idanun kowa suka bude sosai

aka ga irin mummunar asaran rayukan da

akayi:

Da zazar mutum ko aljan ya dubi kas sai

yaga ashe kowa akan gawarwaki yake

tamkar da gawar aka yi kasar wajen duka

sai dai kaga gawa kan gawa; lodi ajan lodi

har tana tsiri tana ruguzowa kasa:

A sannan ne mazaje suka kama mugun haki

kamar ransu zai fita daga cikin gangar

jikinsu aka fara kallon kallo aka fara iya

shaida juna:

sai gashi sarki dujalu da jarumi inmal sun yi

arba da junansu ashe ma tazarar da ke

gsakaninsu bata wuce taku goma ba amma

wani iko na allah duk tsawon kwanakin da

suka shude ana wannan bakim artabu ko

sau daya basu hadu ba sun yi gaba da gaba:

A dai dai wannan lokaci ne bakon jarumin

cikin rundunar su sarki maharaz ma ya cire

hular karfen da ke kansa sai ga dogon gashi

na mace mai tsananin baki da sheki ya zubo

kasa:

BA WATA BACE FACE GIMBIYA MULAIFA!

Page 73

Al amarin da yai matukar girgiza kowa

kenan a filin yakin aka cika da dumbin

mamaki:

Sarki maharaz dake tsaye a can gefe daya

yana ta faman haki baisan saadda ya saki

takobinsa ba ta fadi kasa ba sbda tsananin

mamakin ganin cewa ashe yarsa ce gimbiya

mulaifa bakuwar jarumar da tayi ta

ragargazar abkn gaba::

Abinda yai matukar daure masa kai shine

yaushe mulaifa ta koyi yaki haka har ta

kuma tasami wannan gagarumar

jarumtakar amma bai sani ba?

Koda sarki dujalu ya hango sarki maharaz

sai ya yunkura da nufin ya ruga izuwa

gareshi domin ya gagauta hallakashi ya

kunsawa jarumi inmal bakin ciki a karo na

biyu:

KwatsaM! Ba zato b tsammani sai aka ji an

busa kahon tsai da yaki daga kowannen

bangare::

Cikin tsaninin bakin ciki sarki dujalu ya mai

da takobinsa cikin kufe sannan yadubi a

dadin gawarwakin jama arsa na mutane da

aljanu ya kwantantasu da nasu sarki

maharaz sai ya ga kusan kunnen doki ne

amma kuma a kaso goma na kowannen

bangare An karaar da kaso bakwai bakwai:

Al amarin da yai matukar dugunzuma

hankalinsa keanan ya tabbatar da cewa lallai

RAGAS aka dada yi a cikin wannan yaki::

Page 74

Kawai sai sarki dujalu ya durfafi inda sarki

maharaz ke tsaye:

Har inmal ya yunkura zai tareshi sbda

tunanin ko cutar da maharaz zai yi:

sai sarki maharaz ya dagawa inmal hannu

yana mai yi masa nuni da ya dakata:

inmal ya vi umarni ya tsaya a inda yake har

sai da sarki dujalu ya iso daf da inda sarki

maharaz yake tsaye yadda har suna iya jin

numfashi juna sannan yace yakai babban

abkin gabata kayi sani ce wa hakika ka

shammaceni ainun domin ban taba zaton

cewa kai da yarka kuna da gagarumae

jarumtaka haka ba:

To amma ka sani cewa idan aka dawo filin

daga zamuyi karo ne na karshe:

Na rantse da darajar abin bautata ba zaku

tsallake masifataba:::

Da wannan hannunawa guda daya sai na

dada kunsa muku bkin cikin da bazai taba

shafewa ba a cikin kundin tarihin

rayuwarku::

Lokacin da sarki dujalu ya yazo nan

azancesa sai sarki maharaz ya bushe da

dariya lokaci guda kuma

ta turbune fuska ya dakawa sarki dujalu

tsawo ya ce yakai babban abkin gabata kayi

sani cewa mulki da daukaka ba banza bane:

Duk dan sarki dole ya gaji jarumtaka domin

ba a yin mulki a banza:

na dade ina boye jarumtakata kuma ina

tandinta sbda zuwan irin wannan rana: ina

mai tabbatar maka dacewa koda zaka cusa

mana wanna bakin cikin a karo na biyu kaar

yadda ka kunsa mana na farko ka rabau da

babban masoyinmu sarki yaki Hibru to kai a

kwa sai mun kunsa maka bakin cikin da zai

bibiyeka har izuwa karshen rayuwarka:

Page 75

zidane kd:

Koda gama fadin hakan sai sarki maharaz ya

juya ya nufin sansannsu gaba dayan sauran

jama arsa wadanda suka yi saura mutane da

aljanu sai suka bi bayansa sai jarumi inmal

da mulaifa suka tsaya ana kallon kallo

tsakaninsu da sarki dujalu a lokacin da suma

jama ar sarki dujalu suka juya suka nufi

sansaninsu:

tsirarun dakaru na kowannen bangare ne

suka tsaya suna tatara gawarwakin yan

uwansu suna tarasu a waje guda domin

akonesu sbda yawnsu yafi karfin ace za a

binne::

Sai da ka shafe kusan dakika dari da ashirin

ana kallon kallo gami da harara tsakanin

sarki dujalu da su inmal sannan mulaifa ta

zo ta kama hannun inmal ta janyeshi suka

tafi izuwa nasu sansannin suna waigen

sarki dujalu:

Har sai da su inamal suka bacewa dujalu

dagani sannan shima ya juya a fusace ya

nufi nasu sansanin

* * =

bayan kowa ya huta hankalo ya dawo jiki:

wato kawar da yunwa da kishirwa:

MULAIFA da inmal na zaune a cikin tanti

suna hutawa har izuwa tsawon lokaci

daynsu bai ce uffan ba sai inmal yayi gyaran

murya yana mai dubeta yace yake abar

kaunata;

kiyi sani cewa a yau ya da uba sun yi

matukar shammatata kuma sun bani

mamaki:

ashe keda sarki kuna da gagarumar

jarumtaka haka amma ban taba sani ba? To

wau shin dama kuna karbar horon yaki ne a

boye batare da kowa yasani ba???

Page 76

ANAN ZAN DAKATA SAI KUMA IN ALLAH YAKAI

MU GOBE NAKU HAR KULLU SULEIMAN ZIDANE

KD:::

0906417602

whatsapp:::

MAZAN JIYA

Littafe na hudu

Part 15

Typing: Suleiman zidane kd:

Page Home of Littafan Yaki  And Hausa Novels


To wau shin  dama kuna karbar horon yaki ne a boye batare da kowa yasani ba???


Page 76 

:::


Koda jin wannan tamb&ya sai gimbiya mulaifa tayi dariya sannan tace ni kaina ban taba sani cewa mahaifina yana da irin wannan gagarumar jarumtakar ba:


Amma tawa jarumtakar na sameta ne daga wajen wanda ya ko ya maka::

Koda jin wannan batu sai inmal ya sake mamaki ya dubi mulaifa cikin alamun rashin yarsa da batunta yace haba masoyiyata ya ya zaki min da wani zance na rainin hankali? Yaushe mahaifina ya kooya miki yaki amma ko sau daya ba taba gani ba alhalin ke boyeki ma ake yi a cikin gidan sarauta babu wanda ya isa ya je kusa dake?


Sa adda mulaifa taji wannan batu sai ta bushe da dariya sanan tace yakai abin kauna kayi sani cewa mahaifinka bashi da iyaka a cikin gidanmu face daki guda daya wato dakin da maigirma darbuza yake: 


Ba zan taba mancewa da ranar da mahaifika ya fara koya mini yaki na:


Abun ya faru ne a wani yammaci ina zaune a cikin farfajiyar turakata a cikin lambu ina shakatawa cikin nishadi ina kallom furaanni da kananan tsutsaye wadanda aka killace acikin kanannan kejina suna ta dan tsattsage tsattsagesu a ciki abin gwanin ban sha awa kasancewar su kyawawan tsutsaye masu launin jiki kala kala:::


Page 77


kwatsam Ina cikin wannan hali sai na hango marigayi shi kadai ya durfafo cikin lambun::


Nan take na mike tsaye da sauri na ruga gareshi ina mai risinawa cikin biyayya da nufin na duka na gaishe shi amma sai yai sauri ya kama kafaduna ya tasheni tsaye yace haba ranki yadade a ina kika taba ganin  ubangida ya dukawa bawansa?


Koda naji wannan tambaya sai na dubeshi a cikin mamaki nace ya kai abkin abbana hakika kabani mamaki domin ban taba zaton cewa wannan kalma zatafito ba daga bakimka duk da cewae nasan a  halin yanzu mahaifina baya girmamaka kuma baya  janka a jikinsa na san cewa kana da babban matsayi a wajensa wanda yakasance boyayyen al amarin:

Dajin wannan batu sai shima marigayi ya cika da tsananin mamaki ya dubeni yace dani mahaifinki ya taba baki balarin matsauina ne wajensa???


Da jin haka sai na girgiza kaina nace ko kadan bai taba gayamin ba amma naga tarihin duk alakar da ke tsakaninku ne acikin kundin tarihin rayuwarsa wanda ya boyeshi acikin wata akwattu da ke karkashin gadonsa na barci::


Duk duniya babu wnda ya isa ya iya bude wannan akwati sbda an kulleta ne da karfin wadansu dalasimai na tsafi guda saba in da daya:


Page 78

zidane kd::


Dole sai mutm ya hadasu sannan zata budu::


Tun ina da shekara shida a duniya nake jin sarki yana karanta wadannan dalasimai na tsafi kullum da tsakiyar dare a cikin turakarsa kuma baya daga murya a duk sa adda zai karantasu sai dai na jiyoshi kamar yana yiwa wani rada::


Tun a sannan na ke labewa na kara kunnenaa ina sauraron abin da yake fada amma ban sami ikon haddace kalmoin ba sai a ranar nan da kayi laifi aka bankareka a saa aka yi maka wannan mummunana hukunci::

A ranar ne na bude akwatin sarki naga tarihirin  A ranar ne na bude akwatin sarki naga tarihin alakarsa da mahafinka kuma naga wani babban sirri wanda bazan iya gaya makashi yanzuba saidai a bayan wannan yaki idan muna raye::


lokacin da Gimbiya mulaifa tazo nan a zancenta sai jarumi inmal ya cika da tsananin mamaki yai shuru yana mai kallonta cikin mamaki:::


kada ganin haka sai tayi masa murmushi sannan ta kwanta yana mai dora kanra akan cinyanta domin ta dada huta gajiyar yaki::


WANNAN SHINE ABIN DA YA FARU A SANSANIN YAKI NA BAKIN TEKUN BAHAR SUFIYA BAYAN AN FAFATA KAZAMIN MASIFAFFEN YAKI A KARO NA UKU::


*     *      ¥


A CaN Birnin sarki dujalu kuwa karshe gari  da sassafe tun kafin alfirjir ya keto boka sadusa yayi shirin tafiya wata nahiyar dabam domin neman aljanin da zai aika can bakin kogin bahar sufiya a matsayin dan leken a sirin wanda zai gano musu halin da ake ciki:::


boka sadusa yanada matar aure guda daya wata kyakkyawar mace wadda ake kiraa Hunaisa sai kuma da Guda daya wani karamin yaro dan kimanin shekara bakwai 7 wanda ya kasance kyakkyawa kuma allah ya hore masa basira hikima da sauran fahimtar al amari har da hasashen abin da ka iya faruwa a gaba:::


Page 79:


Allah ya jarrabi boka sadusa da matukar son wannan da nasu mai suna HALYAL kuma sun shaku matuka yadda ko kadan basa son rabuwa da juna dai dai da kwana daya:


Wani abin mamaki shi ne babu yadda boka sadusa bai yi ba akan ya koyawa halyal ilimin tsafi amma ko kadan shi Halyal bashi da ra ayin ya gaji ubansa a wannan bangare::


Shi dai Halyal bashi da wani buri a rayuwarsa wanda yafi ya halarci yaki koda sau daya ne a rayuwarsa amma sadusa ya hanashi:


babu irin rokin da Halyal bai yiwa Sadusa ba akan ya kyaleshi ya tafi izuwa bakin kogon bahar sufiya domin ya gawannan gagarumin yaki wanda yayi Hasashen akana cewar yaki ne wanda ba a taba yin kamarsa ba a duniya kuma ba a zaton za ayi anan babban burin Halyal shine ya ga jarumtaka a fili yadda maza ke dakawa maza gumba a hannu kuma shima yana son anan gaba ya zama gawurtaccen jarumi wanda zai shahara a duniy ammma da yake ra ayinsa ya sha bamban da na mahafinsa bai taba samun damar koyon yaki ba sannan kuma ko kadan bashi da wata jarumtaka ko sadaukantaka a jikinsa al aarin da yasan asa bakin ciki da takaici kenan a cikin zuciyarsa::


Page 80


bayan sadusa ya gama shiri tsaf Ya sanya tufafinsa kua ya dauko jakar guzurinsa sai ya shiga cikin turakar matarsa Hunaisa domin ya yi musu sallaa: 

ita kadau a zuane tana kalaci::


Cikin mamaki ya dubeta yace ina Halyal yake?


Koda jin wannan tamabaya sai itaa ta dubeshi cikin mamaki tace ai yau halya ya rigani tashi ma:

Tun dazu yai wanka ya kitsa har ya dauki jakarsa ta tafiya don ya shaida mini cewa xakuyi wannan tambaya:


Koda jin haka sai boka sadusa ya murtuke fuska ya ce aa ni bamuyi haka da shi ba kuma ba zan yarda nayi wannan tafiyar mai hadari ba da shi:

wai shin ma yanzu ina Halyal din yake??


Hunaisa ta ce yana can kofar gida ya jiranka:


Ni dai ina rokinka da girman tsofafinka ka amince masa kuyi wannan tafiya .....


ANan ZAdakata saikuma gobe 

page dinmu Home of Littafan Yaki  And Hausa Novels

MAZAN JIYA 4

Littafe na hudu:

Part 16

Typing:: suleiman zidane kd::

Page.. Home of Littafan Yaki  And Hausa Novels


Matan Arewa Special Group


Zauren Muslims

Ni dai ina rokinka da girman tsofafinka ka amince masa kuyi wannan tafiya:::


Tare domin kuwa ya kwallafa ransa gaba daya akanta sbda yana gani cewa wannan ce kadai damar da yake da ita da zaije sansanin yaki yaga yadda ake zubar da jarumtaka tunda ka gaya mana cewa zaka tafi neman aljanin da zaka tura bakin tekun bahar sufiya ne::


Page 81:


Sa adda Hunaisa tazo nan a zancenta sai hankali boka sadusa ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe kuma yaji ya kamu da tausayin Halyal amma da ta tuna irin mugun hadarin dake cikin wannan tafiya sai zuciyarsa ta bushe kuma ta kekashe ga barin jin tausayin::


Sadusa ya dubi Husnaila yace ki yi hkri ya ke matata ba zan biyawa Halyal bukatarsa ba domin yin hakan dai dai yake da na turashi izuwa FARAUTAR AJALINSA sakamakon hadarin dake cikin wannan tafiya: kin fi kowa sannin halina idan na yi magana bana sauya ra ayi::

Da wannan furuci nake yi miki sallama sai na dawo:

Ina sa ran zansamu aljanin dazan tafi nema a cikin kwana uku amma ban sani ba ko aljanin zai tafi tare dani ne izuwa can kogin bahar sufiya ko kuma shi kadai zai tafi::


Duk dai halin da nake ciki zn aiko miki da wasika ta hannun tsuntsuna:: 


ko da gama fadin haka sai boka sadusa ya juya ya fice daga cikin turakar a lokacin da Hunaila ta biyo bayansa da sauri idanunta cike da kwalla

wahaye na shirin zubowa sbd tausayin danta halyal bisa bakin cikin da zai shiga idan aka ki tafiya dashi::


Hayal na zaune a gindin wata bishiya dake kofar gidansu ga jakarsa ta guzyri rataye a kafadarsa:


Page 82

zidane kd:


Yana wasa da tarin wadansu  tsakuwoyi da ke gabansa sai kawai ya hango mahaifinsa da mahaifinyarsa sun fito daga cikin gida sauri::


Koda halyal yayi arba da fuskar mahaifinsa ya ga ko kadan babu annuri a cikinta sai hankalinsa ya dugunzuma kuma jikinsa ya bashi cewar lallai mahaifin nasa bazai amince yayi wannan tafiya ba dashi ba::


Ya yin da sadusa ya matso daf da halyal sai halyal ya mike tsaye cikin sanyin jiki gami da karayar zuciya:::

Koda sadusa ya yi kwallah a cikin idanun halyal sai nan take shima yakamu da tausayinsa halyal ya dubeshi cikin yanayin damuwa yace ya kai dana na sani cewa a yau ne ranar da kake da damar cika babban burinka na duniya  amma kada kamanta cewa ni da mahaifiyarka muna sonka fiye da komai a cikin wanan duniya don haka lallai bama son abinda zai rabau da kai tunda kai kadai ne  damu:

Taya  yaya kake tsammmanin cewa nida kaina zandaukeka na tafi da kai izuwa hallaka?

Ina so ka sani cewa a halin yanzu zan yi wannan tafiya ne izuwa wata nahiyar dabam wacce ban san sirrin dazukantaba kuma ban san irin mugayen abubuwn da zan riska ba a cikinta kafin na sami aljanin da nake nema: Bubu mamaki mana rasa rayuwata a wanan tafarki ka ga kenan idan na tafi tare da kai mahaifiyarka zata yi rashi biyu:

Babu miji kua babu da yaya kake zaton rayuwarta za ta kasance idan babu mu a doron kasa??


Lokacin da boka sadusa yazo nan azancensa jikin halyal yayi sanyi 


Ainun ta sunkui da kansa kamar ya hakura daga can kuma sai ya dago kai ya dubeshi ya ce Yakai abbana shin ka manta ne cewar ka taba gayamini cewar bisa binciken da kayi a hallarar tsafinka ajali ba zau taba riskar daya daga cikinmu ba a wani wuri face a gida??


Ashe kenan duk irin gararin da zamu shiga zamu dawo gida a raye?

Page 83


Lokacin da boka sadusa ya jin wannan batu sai ya sunkuo da kansa kas cikin alamun kunya yai shiru yace komai ba har izuwa tsawon yan dakiku sai daga can kuma ya dago kai ya dubi halyal lokacin da kwalla ta ciko a cikin kwayar idanunsa ya ce ya kai dana hakika duk abinda ka fadi gaskiya ne to amma kuma ai bana son mu dawo gida a cikin muugun hali rashin lpyar da zata zama sanadin ajalinmuka hkri bazan iya yin wannan tafiya ba tare da kai:

koda jin haka sai halyal ya durkushe kasa yana mai fashewa da kuka:

al amarin daya kara jefa sadusa da Hunaisa cikin tsananin tausayinsa kenan:

nan dai sadusa ya kama kadadun halyal ya tasoshi tsaye ya sumbaci goshinsa sannan ya rungumeshi a kirjinsa duk su biyun suka fashe da kuka a lokacin guda::


Page 84


Koda ganin haka sai itama hunaisa ta rugo garesu ta kankamesu su ukun ta tayasu kukan sadusa ya janye jikinsa daga cikin nasu ya tafi yana waigensu hawaye na zuba  daga idaanunsa::


Al amarin daya kara dugunzuma hankali halyal da Hunaisa kenan suka ci gaba da  matsanaicin kuka suna hangen sadusa har sau da ya bace musu da gani::


Nan fa Halyal da Hunaisa suka cigaba da kuka suna kankame juna kamar bazasu daina ba har izuwa tsawon kusan dakika daru biyu da sitttib::::


Kwatsam! Ba zato ba tsammani sai suka jiyo takun sawu a yayin da kawunansu ke kallon kasa cikin sauri suka dago domin su ga wanda ke zuwa:

Kawai sau suka ga ashe sadusa ne ya dawo kuma ya tunkarosu hannanyesa a bude hawaye yana shatata bisa kumatunsa::


Cikin tsananin farin ciki Halyal ya ruga izuwa gareshi ya dada kan kirjinsa suka rungume juna suna masu kyalkyala dariya:::


TO INIMA ZIDANE SAI NATAYASU KYALKYALA DARIYAR:::))


*    *    *


 

tunda suka fara tafiya daga cikin gari halyal yafara ganin abubuwan al ajabi bisa yanayin tafiyar tasu domin da zarar sun yi tafiya t kamar taku goma  sai yaga sun shafe nisan zira i dari nan da nan suka fice daga cikin gari suka nausa cikin daji::


Page 85


Ai kuwa suna shiga daji yaji sadusa ya kama hannunsa ya rike nan fa ya jashi da gudu suka falfala::


*      *     *


Wannan karo sai halyal ya sako cike da tsananin mamaki fiye da farko domin yanzu tafiyar sa a guda ce suke shafewa a cikin dakika sittin kacal sai dai kawai yaga suna gifta dazuzzuka a cikin matsananincin gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya::

Amma da ya tuna cewar duk wannan lamari  al amari ne na tsafi sai kawai yayi murmushi yace a zuciyarsa kowa da kiwon da ya karbeshi:::


Haka dai sadusa da halyal suka cigaba da gudu a cikin daji babu sassauci:

Tun safe suka fara wannan gudu amma har sai da rana ta fadi sannan suka tsaya cak::

A farkon wani daji mai yanayi iri dabam da na sauran dukkan dazuzzukan Da suka wuce a baya:


Adai dai wanna lokacin ne ji tsananin gajiya da kishirwa ta riskesy: ba shiri suka durkushe kasa bisa guiwoyinsu suka kama haki sannan kowannensu ya bude butar ruwansa ya kwankwada::


koda suka dawo cikin hayyacinsu sosai sai suka kama kallon wannan daji da suka tsinci kansu a cikinsa::

DAJI NE mai dauke da wandansu irin dogayen bishiyoyi masu tsananin tsawo da ba a iya ganin karshensu kuma ganyayen bishiyoyin masu fadi ne sosai don haka su karawa dajin duhu ya zama abin tsaro::


Page 87:

zidane kenan::


sannan kua akwai wadansu irin duwatsu a dajin masu wani irin sufofki na ban tsaro::

wani dutsen sai kaga yana kama da mutum wani kamar aljan wasu kuma da dabbobi suke kama:


   kai komai dakewar zuciyar mutum idan ya tsinci kansa a cikin wannan daji sai ya razana musaman idan ya ji irin tsananin shirun dak cikin dajin::


mutu baya jin sautin komai hatta na tsuntsaye kuwa aa da zarar mutum ya taka ganyeye bishiyoyin dajin wadanda suka fado kasa suka bushe rumus sai kaji karar ta cika dajin gaba daya hara da amsa kuwwa::


nan take halyal yakamu da tsananin tsaro gaba dayan jikinsa ya kama tsuma bai san sa adda ya dada kankame jikin sadusa ba::

Koda ganin haka sai sadusa yai murmushi yace saki jikinka ya kai dana kayi sani cewa inkana tare dani babu wani tsautsayi da zai sameka ka sani cewa tun shigo wata sabuwar nahiyar ne wacce ba tamu ba::


Yanzu kamata yayi mu nemi wuri mai kariya inda zamu yadda zango tunda duhu ya soma sannan  sai nayi mana bincike na gano ko akwai abinda muka zo nema a cikin wannan daji::


Page 87


koda gama fadin hakan sai suka mike tsaye  suka kara nausawa cikin suna ketawa ta cikin surkuki duhuwoyi ciyayi da sako sako:

Ai kuwa sai da suka shafe lokaci mai dan tsawo suna neman wani kogon dutse da zasu iya shiga cikinsa su fake sakamakon hadarin da yake barazanar zubar da ruwa a ko yaushe tunda har an fara walkoya gami da tsawa mai ban tsoro wacce duk sa adda aka yita sai dai kaga halyal na dada kankame hannun sadusa::


Abinda ya dada daure masu kai shine duk tsawin wannan lokaci da suka shafe suna yawo a cikin dahi ko kadangare basu gani ba kuma basu hadu da wani mugun abu ba::


shi kansa sadusa sai daya tambayi kansa a ckin zuciyarsa yace:::


TO WAI SHIN MENENE YA HANA DABBOBI DA KWARI RAYUWA A CIKIN WANNAN DAJI???


suna cikin wannan dube dube ne suka hango wani katon kogon dutse a gabansu cikin hanzari suka ruga izuwa bakin kogon a lokacin da aka fara yayyafi kua aka ci gbada tsala wakiya da tsawa::


da isarsu bakin kogon dutse sai suka tsaya sadusa ta yi nuni da hannunsa izuwa cikin kogon take wani irin haske na tsafi ya haskake cikin kogon gaba dayansu kofa suka yi arba da aabin da ke cikin kogon sai suka cika da tsananin mamaki::::


Page 88

zidane kd kenan::


ba komai suka gani ba face wata yar karama aljanar duniya:

kAya ne na alatu a cikin kogin tamkar turakar wani hamshikin basarake:

An shimfida dardua ta alfarma ai dan karen laushe ta rufe kasankogon gaba daya mai launin shudi:::

A gefe daya  Mutum ce kamarka:

koda kyakkyawar yarinyar Da suka wuce a baya:


Adai dai wanna lokacin ne ji tsananin gajiya da kishirwa ta riskesy: ba shiri suka durkushe kasa bisa guiwoyinsu suka kama haki sannan kowannensu ya bude butar ruwansa ya kwankwada::


koda suka dawo cikin hayyacinsu sosai sai suka kama kallon wannan daji da suka tsinci kansu a cikinsa::

DAJI NE mai dauke da wandansu irin dogayen bishiyoyi masu tsananin tsawo da ba a iya ganin karshensu kuma ganyayen bishiyoyin masu fadi ne sosai don haka su karawa dajin duhu ya zama abin tsaro::


Page 87:

zidane kenan::


sannan kua akwai wadansu irin duwatsu a dajin masu wani irin sufofki na ban tsaro::

wani dutsen sai kaga yana kama da mutum wani kamar aljan wasu kuma da dabbobi suke kama:


   kai komai dakewar zuciyar mutum idan ya tsinci kansa a cikin wannan daji sai ya razana musaman idan ya ji irin tsananin shirun dak cikin dajin::


mutu baya jin sautin komai hatta na tsuntsaye kuwa aa da zarar mutum ya taka ganyeye bishiyoyin dajin wadanda suka fado kasa suka bushe rumus sai kaji karar ta cika dajin gaba daya hara da amsa kuwwa::


nan take halyal yakamu da tsananin tsaro gaba dayan jikinsa ya kama tsuma bai san sa adda ya dada kankame jikin sadusa ba::

Koda ganin haka sai sadusa yai murmushi yace saki jikinka ya kai dana kayi sani cewa inkana tare dani babu wani tsautsayi da zai sameka ka sani cewa tun shigo wata sabuwar nahiyar ne wacce ba tamu ba::


Yanzu kamata yayi mu nemi wuri mai kariya inda zamu yadda zango tunda duhu ya soma sannan  sai nayi mana bincike na gano ko akwai abinda muka zo nema a cikin wannan daji::


Page 87


koda gama fadin hakan sai suka mike tsaye  suka kara nausawa cikin suna ketawa ta cikin surkuki duhuwoyi ciyayi da sako sako:

Ai kuwa sai da suka shafe lokaci mai dan tsawo suna neman wani kogon dutse da zasu iya shiga cikinsa su fake sakamakon hadarin da yake barazanar zubar da ruwa a ko yaushe tunda har an fara walkoya gami da tsawa mai ban tsoro wacce duk sa adda aka yita sai dai kaga halyal na dada kankame hannun sadusa::


Abinda ya dada daure masu kai shine duk tsawin wannan lokaci da suka shafe suna yawo a cikin dahi ko kadangare basu gani ba kuma basu hadu da wani mugun abu ba::


shi kansa sadusa sai daya tambayi kansa a ckin zuciyarsa yace:::


TO WAI SHIN MENENE YA HANA DABBOBI DA KWARI RAYUWA A CIKIN WANNAN DAJI???


suna cikin wannan dube dube ne suka hango wani katon kogon dutse a gabansu cikin hanzari suka ruga izuwa bakin kogon a lokacin da aka fara yayyafi kua aka ci gbada tsala wakiya da tsawa::


da isarsu bakin kogon dutse sai suka tsaya sadusa ta yi nuni da hannunsa izuwa cikin kogon take wani irin haske na tsafi ya haskake cikin kogon gaba dayansu kofa suka yi arba da aabin da ke cikin kogon sai suka cika da tsananin mamaki::::


Page 88

zidane kd kenan::


ba komai suka gani ba face wata yar karama aljanar duniya:

kAya ne na alatu a cikin kogin tamkar turakar wani hamshikin basarake:

An shimfida dardua ta alfarma ai dan karen laushe ta rufe kasankogon gaba daya mai launin shudi:::

A gefe daya  nan a zncenta sai ta fashe da kuka al amarin dayai matukar baiwa su sadusa mamaki kena har suka ji sun kamu da tsananin tausayinta::


daga can sau sadusa ya dubeta ya daka mata tsawa yace yake wannan ma abokiyar keji: shin yanzu zaki iya iya gaya mana ko wane ne ya ajiyayeki a wannan kogon dutse wanda muka ji kin kirashin da shugaban azzalumai na duniya??


Page 91

koda jin haka sai wannan kyakkyawa ta cikin keji tayi a jiyar zuciya tace sanin wanda ya ajiyeni  acikin wanna kogo dai dai yake da sanin ranar ajalin mutum domin yakasance GUGUWAR ANNOBA kuma GOBARA DAGA KOGI wacce ba da magani:


Sunan wanda ya ajiyeni anan shine ALJANI AUGATUL AGUWANU:


koda jin wannan batu sai boka sadusa ya mike zubur! Cikin firgici da tsananin tsoro ya kama hannun halyal domin su fice daga cikin kogon:

karar takun sawun aljani raugatul aguwanu tasa suka koma cikin kogon dutse da sauri suka shige cikin karkashin wanna makeken gado na aljanin raugatul aguwanu:

Takun sawun na Raugatul aguwanu tamkar giwaye neke tserun gudu a cikin dajin har maya haddasa girgizar kasa::


Kai tsaye aljani raugatul aguwanu yashigo cikin kogon nasa tya zauna kan gefen wanna gado nasa:::::::::::::


ANAN ZANDAKATA SAI KUMA IN ALLAH YAKAIMU GOBE ZANMU CIGABA NA KU HAR KULLU SULEIMAN ZIDANE KD::

PAGE DINMU:: Home of Littafan Yaki  And Hausa Novels


Matan Arewa Special Group


Zauren Muslims


Matan Arewa Special Group


Zauren Muslims

MAZAN JIYA 4

Littafe na hudu

Part 17

Typing:: Suleiman zidane kd:

Page: Home of Littafan Yaki  And Hausa Novels


Matan Arewa Special Group


Zauren Muslims

Kai tsaye aljani raugatul aguwanu yashigo cikin kogon nasa tya zauna kan gefen wanna gado nasa:::::::::::::

Saboda nauyinsa sai da gadon ya lotsa kasa har su sadusa suka ji kamar wani katon dutse ne ke shirin dannesu ya kakkarya musu kasusuwan gadon baya::


Koda kyakkyawar yarinyar nan tacikin keji ta ga haka sai ta dubi Raugatul Aguwanu ta bushe da dariya tace haba ya shugabana yau kuma wahalar farautar ce tasa ka manta ka fara zama akan teburinka kaci yayan itatuwa?


Koda jin haka sai aljani Raugatul Aguwanu ya bushe da dariyar farin ciki:

Kasancewar kyakkyawar yarinyar bata taba yi masa magana mai dadi ba a tsawon shekaru da ya ajiyeta a cikin wanan kogon sai yau::


Page 92


Cikin hanzari ya mike tsayee ya nufi inda kujerarsa ta zama take wadda ke karkashin wammam babban zagayayyen tebur::


Kafin ya isa kan kujerar tuni sadusa da Halyal sun fito daga karkashin gadon sun ruga izuwa bayan tarin dukiyar zinare sun buya::


A Dai Dai wannan lokaci ne Raugatul Aguwanu ya zauna akan kujerar: 

ai kuwa sai ya shaki kamshi bil adama a cikin kogon fiye da yadda ya saba shaka a kullum ya tabbatar da cewa yasami baki:

Nan fa ya kama waige waige da dube dube cikinn kogon:

Koda su sadusa suka ga haka sai suka binne kansu a cikin wannan duniya ta zinare tamkar basu taba wanzuwa ba a wajen::


Hakan ta faru ne da taimakon karfin sihirin tsafi sadusa::

Aljani Raugatul Aguwanu ya mike tsaye ya kama dube dube ya shiga nan ya fita can: ya bankada ko ina amma bai ga bil adama ba alhalin kuma yaji kamshinsu::


Page 93


koda ya dago kai suka hada ido da wanna kyakkyawar yarinya ta cikin keji sai ta sunkui dakanta kas: Abinka mara gaskiya ko a ruwa sai ya yi jibi sai jikinta ya kama tsuma::


A fusace Raugatul Aguwanu ya durfafo kejin da take cikin ya dubeta ya daka mata tsawa yace ke tsohuwar munafuka  tabbas kin san da shigowar baki wannnan kogo nawa amma sbda munafunci da cin mana irin naku na mata shine kika yi shiru baki gaya mini ba::

To ki sani cewa idan har baki gaya ini inda suka buya ba a cikin wannan kogo yanzu nan zan fito dake daga cikin kejin nan na yayyagaki filla filla na watsar: Ai daa na ajiyeki ne anan kawai don ki debe mini kewa kasancewar babu wata hallita a cikin wannan daji sai ni kadai::


koda jin wannan batu sai kyakkyawar ta bushe d dariya lokaci guda kua ta fashe da kuka sannan ta kalleshi tace ai daa na dade ina rokonka akan ka kasheni na huta da takai ci da bakin cikin rayuwar da ka jefani cikin amma kaki ka rabani da iyayena dangina da kasarmu ka baroni da cikin jinsin mutane yan uwana ka kawoni nan cikin wannan daji inda ko kwaro babu bare wani dan tsuntsu wanda zai rinka jin sautin kukansa ina jin dd cewar akwai mai rai a kusa dani::

Tun inayarinya karaa ka sato ni ka kawoni nan kuma ka tsafanceni ka sani a cikin wanna keji na zama kamar ya tsuntsuwa alhalin na kasance bil adama::


Page 94

zidane kd:


Ka cuceni cutar da bani da halin daukar fansa face na ga ranar da Zakayi mutuwar wulakanci :

Tabbas a duniya ba a taba samun azzalumai kamar ka ba: 

Ina mai rokonka da ka hanzarta kasheni domin na huta da wnn bakin zalunci naka::

 Sa adda kyakkyawar yarinyar ta cikin keji ta zo nan a zancenta sai aljani Raugatul Aguwanu ya kara fusata ainun yace aikuwa yanzu nan zan ida mugun nufina akanki::


Kawai sai ya kai hannu ya suro kejin danufin yabude ya daukota daga cikin amma sai yaji an ce dakata ya kai Shugaban azzalumai na duniya::


Cikin hanzari da mamaki Raugatul Aguwanu ya juyo da baya: take yayi arba da boka sadusa da dansa Halyal tsaye a bayansa::


Raugatul aguwanu ya kurawa boka sadusa idanu cikin tsananin mamaki har izuwa tsawon yan dakiku yana nazarinsa sanna yace ya kai wannan ha tsabibin boka kai kuwa ya ya aka yi ka shigo cikin wannan daji har ka iso nan cikin makwanci na batare dani ji motsin shigowarku ba? Kune bil adama na biyu da suka taba shigowa cikin wannan daji har suka rayu a tsawon sama da nisan sa a guda sbda karfin shirina gami da azababben karfin dantse na:::

wannan daji da kuka shigo shine dajin da ake yiwa lakabi da DARUL HUSHUSHUL MAUT wato gidan daba ashiga kuma ba a fita:


KUNJIPA IRIN WANI MASIFAFFAN DAJI;

SULEIMAN ZIDANE KD::)


tunda nazo na tare a wannan daji yazama nawa ni kadai domin na kori dukkan aljanu dabbobi da tsuntsaye gami da dukkan kwarin dake cikinsa:


Page 95


fatake da matafiya kuwa hatta na jinsin aljanu haka suka hkra da giftawa ta saman wanna daji domin koda tsautsayi suka zo wucewar kamawa suke 

da wuta su kone saidai tokarsu tazubo kasa:

kai kuwa wane irin karfin tsafi ne da kai hka wanda har yafi nawa ka ketare duk masifun da na zuva a wwannan daji?


Lokacin da boka sadusa yaji wannan tambaya sai yayi murmushi cikin izza sannan ya durfafo inda wannan tebur yake ya zauna kuma ya dauku tuffa guda daya yakama ci tamkar a cikin turakarsa yake sannan ya yafuto aljani Raugatul Aguwanu da hannu yana mai kiransa:


Ba tare da gardamar komai ba Raugatul Aguwanu ya ajiye wannan keji wanda yake hannunsa sannan ya taho wajen sadusa ya zauna akan tasa kujerar suka fuskaci juna:::

A wannan lokaci zuciyar sadusa ta kama dukan uku uku  domin a cikin matukar tsorace yake kawai dai banza ce ta kori wofi::


A iya tunanin aljani Raugatul Aguwanu boka sadusa ya fishi karfin sihirin tsafi tunda har ya iya shigowa wannan daji na darul hushushul mautt lapiya:


Abinda ya manta shine a yau ya sha afa cewar tunda sassafe ya cire dukkan tsaron da yasa wa dajin sakamakon wani dogon nazari da yayi a halwar tsafi don bincike akan yanayin da duniya kw ciki:

Har yagama binciken nasa ya tafi dajin dake gaban nasayin farauta bai mai da sihirin tsaron ba a dajin na darul Hushushul maut:


Page 96

Tun da boka sadusa yazo duniya bai taba ganin aljanin mai girma kirar karfi kutuciyar samartaka da tsananin muni ba kamar Raugatul Aguwanu don haka a cikin tsananin firgice yake da shi sbda ya san cewa ko yaya yayi wani dan kuskure wanda Raugatul Aguwanu ya gano cewa ya fishi karfin sihitin take zai halaka Su shi da halyal:


Bayan sun fuskanci juna sai sadusa yace ya kai wannan sarki jaruan aljanu na duniya ka yi sani cewa musaman nazo wannan daji na darul Hushushul maut domin na gana dakai::


Tabas na san wani gagarumin al amari wanna kai baka sani ba::


Koda jin wannan batu sai aljani Raugatul Aguwanu ya gyara zama ya tattara hankalinsa a waje daya kuma ya nutsu sosai yana mai  sauraron boka sadusa::


11:27am, Thu 12-07-2018::


Suleiman zidane kd

:


Sadusa yai gyaran murya sannan yace shin kana da lbrin gagarumin yakin da ake fafatawa yanzu hakan a can bakon kogin Bahar Sufiya?

Koda jin wanna batu sai aljani Raugatul Aguwanu yasake gyara zama yace kwarai kuwa na san da batun wannan yaki wanda ake yi tsakan Sarki dujalu da sarki maharaz:


Page 97


In banda abinka waye yake shiga fadan manya?

Ai dujalu da maharaz sun fi kowa karin sihirin tsafi a wanna duniya kaf:


Shi ya sa kagani na rabe a waje daya na dawo nan cikin daji na hakura da rayuwa acikin mutane da yan uwana aljanu::

Koda jin haka sai boka Sadusa ya kyalkyle da dariya al amarin da yai matukar baiwa aljani Raugatul Aguwanu mamaki kenan::


Awannan lokaci Halyal da kyakkyawar yarinya ta cikin keji kuwa a ckin matukar tsoro suke domin gani suke cewar idan tusa ta karewa bodari hallaka zaiyi::

Su kansu sun fahimci cewar sadusa dai yan dabaru yake yi domin su kubuta:


Cikin alamun dadin mamaki Raugatul Aguwanuyace yakai wannna hatsabibin bola ina dalilin wannan dariya taka?

Sadusa ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa sannan yace ai nan dajin da ka  kadawo tamakar kayi gudun gara ne ka tarar da zago:

to tsaya kaji idan aka gama wannan yaki duk wanda yasami nasara tsakanin sarki dujalu da sarki maharaz shine zai mallaki kayan yakin MAZAN JIYA wannan duk kuwa ya mallaki Takobin SAIFUL LUJARA MASHIN GALILUL HARAS da HULAR LAMSARA sai ya mallaki kowa da komai na cikin wannan duniya kaga kenan kai kanka sai kazama bawansa wannan daji naka na darul Hushushul maut sai ya zama wajen shan iskasa::


Kai kuwa nasani cewa a dunia babu abinda ka tsana sama da kayi bauta a karkashin wani ka fi son rayuwarka ta kare acikin cin gashin kanka ko ba haka bane?


Page 98


koda boka sadusa yazo nan a zancesa sai hankalin aljani Raugatul Aguwanu ya dugunzuma ainun fiye da koyaushe a rayuwarsa sbda ko kada bai taba tunanin faruwar wannan al amari ba:


nan take halyal da kyakkyawar ta cije keji suka ji sun sami nutsuwa da kwanciyar hankali bisa jin wanna bayani da sadusa ya yiwa aljani Raugatul Aguwanu musamman da suka gayadda jinkisa yai sanyi kuma hankalinsa ya tsahi::


Tsawon yan dakiku Raugatul Aguwanu yana nazari tunani har maya mike tsaye yakama kai kawo yana ciza ya tsa::


daga bisani sai ya koma kan kujerarsa ya zauna kusa da sadusa ya dubeshi ya ce yakai wannan yakadarin boka kayi sani cewa hakika kazo mini da babban al amari wanda yafi gaban tunaniba da hangena don haka  sai nayi bincike na tabbatar da gaskiyarsa::


To wai shin idan har abindaka fada min gaskiyane to yaya zan iya kubuta kena

n:

Ni dai kam da dai na zauna a karkashin wani mulkeni gwara na kashe kaina domin ban ga anfani wannan tsananin karfin dantsen nawa gai da karfin sihirina wanda na shafe sama da shekaru arba in ina yawon nemansa a cikin duniya::

Sadusa ya gyada kai yace tabbas kayi gaskiya:

Amma ina mai tabbatar maka dacewa ni ina da mafita a gareka amma sai bayan ka gama bincikenka kaga gaskiyar wannan al amari sannan zan gaya maka mafitar kuma bisa wani sharadi::


Koda jin haka sai aljani Raugatul Aguwanu ya kyalkyale da dariya sanna yace hakika yai na gamu da sarkin wayo:

Ti amma fa kasani ramin karya kurarre ne idan har duk abinda kazo mini dashi ba gaskiya bane asirinka zai tonu::


idan kuwa asirinka ya tonu da kai da wancan kyakkyawan dan naka sai nayi muku mugun kisan gilla irin wanda ba taba yiwa wani mahaluki ba a doron kasa:::


kafin Aljani Raugatul Aguwanu ya gaa rufe bakinsa tuni boka sadusa ya dakamasa tsawa yana mai cewa kai matsoracin aljani wanda yakasa fita filin daga inda manya mazaje ke fafatawaa:


ina mai horonka da ka iya bakinka ka saisaita lafazinka a gareni in ba haka ba kuwa yanzu nan zan fusata na koneka kua na kone gaba dayan wannan daji dakake matukar kauna kamar yadda uwa keson danta::

Dajin wannan jawabi sai Raugatul Aguwanu ya dan tsorata don haka sao ya sunkui da kansa kas cikin alamun girmamawa yace kayi mini uzuri ya kai takadarin boka ka sani fa ni haka halina yake bana son raini::

:::::::::::::::::

Page 100

:::::::::::::::::

ANAN ZAN DAKATA SAI IN KUMA ALLLAH YAKAIMU GOBE DASAFE ZAN MU DAURA DAGA INDA MUKA DAKATA SAI DAI KUMA HAZANRI BA GUDUBA A GASKIYA MUTANAN WANNA PAGE DIN BAKUSAN YI COMMENT SOSAI INWANI PAGE NAYI POST SAI INRIGA GANIN COMMENT FIYE DANAKU KUMA DAN KUPA NAKE WANNAN TYPING::

BADAWANI PAGE BA:::

SHIYASA NAKE PARA MUKU POST KAFIN WANI GROUPP:

NA GODE DUK WANNA DA BAI SAMU DAMAN KARANTA WANI PART A CIKIN WANNA LITTAFE ZAN IYA GAYAMIN TA COMMENT DOMIN IN TURO MAI NA KU HARKULLU SULEIMAN ZIDANE KD:::

PAGE DINMU::: Home of Littafan Yaki  And Hausa Novels


Matan Arewa Special Group


Zauren Muslims


KASHIGA CIKIN BLUE DINNA NASAMA::::::::::BYYEEEEEE:

MAZAN JIYA 4

Littafe na hudu

Part 18

Typing:: Suleiman zidane kd::

Page Home of Littafan Yaki  And Hausa Novels


Matan Arewa Special Group


Zauren Muslims

Dajin wannan jawabi sai Raugatul Aguwanu ya dan tsorata don haka sao ya sunkui da kansa kas cikin alamun girmamawa yace kayi mini uzuri ya kai takadarin boka ka sani fa ni haka halina yake bana son raini::

:::::::::::::::::

Page 100

:::::::::::::::::


YANzu dai ni a koshe nake zan sha giya domin na kwanta na yi barci sosai sai dare ya tsala sannan zan tashi nayi bincike a Hallarar tsafina bisa wannna sabon al amarin daka zo mini da shi::

Abinda nake bukata da ku shine ya yin dana fara barci bana bukatar naji matsin komai ko yaya yakee domin idan har na farka bana iya komawa barci::

Kai idan da hali ma ku fita daga waje kuje ku yawata a cikin dajin nan har izuwa lokacin da zan tashi daga barcina::

ina mai tabbatar muku da cewa akwai abbuwan al ajabi da yawa a cikin daji nan wadanda zasu debe muku kewa izuwa lokacin tashina daga barci:

Koda jin wannan batu sai sadusa yayi murmushi sannan yace ka san ance da dan gari akan ci gari:

Me zai hana fito da wannan kyakyawar yarinya daga cikin keji domin tayi mana jagora a cikin wannan daji tunda ta fimu saninsa?


Sa adda aljani Raugatul Aguwanu yaji wannan bukata ta sadusa sai yai shiru ya juya al amarin a cikin zuciyarsa kuma ya kurawa sadusa idanun cikin alamun Rashin Yarda daga can sai yace Menene tabbacin cewa ba yaudarata za kuyi ba ku gudu da Gimbiya SHALBIRAT?

Kai sani cewa da raina babu wani abu na biyu da nakeso sama da ita:


Page 101

sadusa yai murmushi yace Ai inda don ita na zo wannan daji da baza kazo ka riskemu ba a cikin kogonka tunda ina da karfin sihirin da zan iya saceta:

Raugatul Aguwanu ya gyada kai cikin alamun nuna gamsuwa amma a can karkashin zuciyarsa Dari dari yake yi:::


Kawai sai yayi kuru ya sa danyatsansa guda ya bude kejin da gimbiya Shalbirat ke ciki:

Shabiyat ta taka dan yatsan Raugatul Aguwanu cikin tsananin farin ciki mara  misaltuwa sbd tsawon shekaru goma sha bakwan da ta yi a wannan daji na Darul Hushushul maut a cikin kejin ta yisu bata taba fitowa ba waje:::


A sannan ne Raugatul Aguwanu ya sauke tafin hannunsa kasa ta dir: 

Sai gata yar motsitsiya a gaban sadusa tamkar dan karamin bera::

Duk wannan abu dake faruwa Halyal na tsaye a can gefe daya ya kurawa Shalbiyat idanu yana mai matukar al Ajabi bisa ganin tsananin kyawunta wanda yake ganin cewa ko Gimbiya Hursiya kanwar sarki dujalu Albarka::

Lokacin da Shalbirat ta duro kasa daga kan tafin hannun Raugatul Aguwanu sai ta kaa raawa da tsalle doin murna kuma ta fasge da kukan farin ciki:


Page 102


A sannan ne aljani Raugatul Aguwanu ya dubi sadusa yace Ga masoyiyata Gimbiya Shalbirat na fito da ita kua na damkata amana a hannunka:

ka tafi da ita izuwa cikin daji ku yawata daga nan har izuwa wayewar gari:


Koda gama fadin hakan sai aljanin Raugatul Aguwanu ya nufi inda aka ajiye wani katon tulu wanda sbd girmansa da nauyinsa kato arba in bazasu iya rabashi da kasa ba ama shi da yan yatsu biyu ya daga tulun:

Ashe tulun cike yake da ruwan gida kawai sa 

i ya kafa bakin tulun a bakinsa ya kama sha kwal kwal karar tafiyar ruwan giyar a cikin cikinsa tamkar ruwan tekune ya balle yana shatata izuwa cikin teku::

Raugatul Aguwanu bai sauke tulun giyar kasaba sai da yaji babu sauran digo daya na ruwan giya sannan ya ajiyeshi a kas ya tafi izuwa kan wannan katon gado nasa na alfarma yana layi yakife kasa:


ko dakika goma bayi ba ya kama wani irin gagarumin Munshari:::


koda ganin faruwar hakan sai gimbiya shalbirat ta yunkura a fusace ta zare wata wukar sihiri ta aljani Raugatul Aguwanu dake kugunsa daga sama da nufin ta caka masa ita a kirjinsa sai boka sadusa yai wuf ya rike hannunta sanan ya karbe wukar ya mai da ira cikin kufenta da ke jikin Raugatul Aguwanu Sadusa yayiwa Shalbirat da Halyal nuni da suyi shiru kuma kada suyi wani kyakkyawar motsi:

Nan take yajasu suka fice daga cikin kogon gaba daya: 

Sai da suka yi nisa da inda kogon dutsen yake inda basa iya hangoshi sannan suka zauna domin su dan huta:

za;ansu ke da wuya sai Shalbirat ta fashe da matsanincin kuka::


Al amarin da yai matukar dugunzuma hankalin su Halyat kenan suka shiga rarrashinta suna tamyarta dalilin kukan nata:

Da kyar suka shawo kanta ta daina kukan sannan tace ba komai ne yasa kuka ga ina wannan kuka ba face tsananin bakin cikin kun hanani kashe aljani Raugatul Aguwanu domin ya salwantar da rayuwata kuma ya kunsa min bakin cikin da Har na mutu babu wata fansa da za ta kankareshi:

Page 103


kuyi sani cewa ni ce ya guda  daya a wajen mahaina sarki sharyalu na Birnin taukib:

babu irin kalar gatan da ban gani ba a duniya kuma a nahiyar damuke babu wani sarki mai karfin mulki da tarin dukiya irin ta mahaifina:


Mahaifin nawa bashi da kowa a duniya face wata kanwaesa mai suna JUZAIRAT ta ri ga mahaifina yin aure da shekara shida amma bata taba samun haihuwa ba har mahaifina yazo ya yi auren ka haifeni:


Al amarin da yajefa juzairat cikin tsananin bakin ciki kenan sbda bata da wani buri wanda ya fi ta haifi dan da zai gaje sarauta::::


Page 104

Suleiman zidane kd::


babu irin asirin da juzairat ba tayiwa mahaifiyata ba akan kada tasamu ciki gami da kulle kulle da makirce makirce na zahiri amma duk butaka bata biya ba::


Kai sai da takai ta kawo juzairat tana nuna kiyayyerta ga samun juna biyun mahaifiyata a filin har  maifina ya fahimta amma bai taba nuna mata damuwarsa ba sbd tsananin son da yake mata:

Lokacin da na isa shekara ba kwai a duniya lavarin tsananin kyawuna ya bazi ko ina a nahiyar ya zamana cewa tun a sannan ya yan sarakai da yan mayan attajirai sun fara zuwa neman aurena sai hankalin juzairat ya dugunzuma ainun kuma ta tsaneni fiye da komai:


A wannan lokaci tsufa ya fara riskar mahaifina kuma gashi kullum yana cikin fama da lalura ta rashin lafiya iri iri:

gaba daya likitocin mahaifina sun kasa gane abinda ke damunsa don haka suka daina bashi magani aka rinka kiran bokaye kowa yana yin iya bakin kokarinsa amma babu sauki::

A wannan lokacin na shaku da mahaifina ainun fiye da yadda na shaku da mahaiyata domin dare    Darana bana yarda na nisanra dashi sau tari sai bayan nayi barci akan kirjinsa sannan mahaifiyata take zuwa ta daukeni ta tafi dani izuwa kan gadonta ta shimfideni::


Page 105

Wani dare wanda shine daren mummunan bakin ciki a Tarihin rayuwata wato daren da ba zan taba mancewa dashi ba:


Ina kwance akan gado MAHaifina muna ta wasa dariya sai ciwo ya taso asa har ya mike zaune da kyar ya zama tari har da aman jini::

Al amarin da ya dugunzuma hankalina kenan na fara kuka kuma na yunkura da nufin  naje na kirawo mahaifiyata amma sai mahaifina ya yi wuf ya riko hannuna a lokacin da shima ya kama zubar da hawaye::


Cikin karfin hali yadubeni yace yake yata kiyi sani cewa bakin alkalami ya riga ya bushe mutuwa zanyi kuma yanzu nan ba dadewa ba:


Koda jin wanna batu sai na cika da tsananin mamaki na kasa tambayarsa dalilin da yasa ya fadi haka:

      

     Mahaifi nawa ya kankameni a kirjinsa ya fashe da matsananincin kuka har izuwa lokaci mai tsawo::


Daga can sai ya janyeni daga jikinsa muka fuskacin juna yace yake yata ki saurara da kyau kiji abinda zan gaya miki::


Kinga wannan rashin lapiya da na dade a kwance ina fama da ita ba wani bane yasa mini ita ba face yar uwata juzairat::


koda jin wanna batu sai idanuna suka zazzaro jikina ya kama tsuma sbd tsananin mamaki da tsoro:::


Page 106


mahaifina yacigaba da cewa juzairat tayi mini asiri ne ta hanyar amfani da wani azzaluin aljani wai shi Raugatul Aguwanu::

Duk mutumin da wannan aljani ya shafa har abada ba zai warke ba daga cuta sai dai ajali::

aljani Raugatul Aguwanu bai amince zai yi wannan mummunan aiki ba sai bisa sharadin cewa za a mallaka masa ke kyauta domin kyawunki:


ina tabbatar miki da cewa nan da cikar sa a uku zan mutum kuma junaizar da aljani Raugatul Aguwanu suna nan suna jiran cikar wannan lokaci domin juzairat ta sami damar hawa karagata ta mulki shi kuma aljani Raugatul Aguwanu ya sami damar daukeki ya tafi dake izuwa can wani sihirtaccen daji wanda baya shiguwa inda zai tsareki:

Na san zakiyi mamaki bisa yadda akayi nasan duk wannan al amari to na sani ne ta hanyar wanin shahararren bokon boka wanda yazo ya dubani::


Hatta lokacin da juzairat  ta gana da aljani Raugatul Aguwanu sai da yanuna mini a cikin madubin tsafinsa kuma ya tabbatar mini da cewar bakin alkalami ya bushe babu wani magani da zai iya bani na sha na warke daga wannan ciwo::


Koda na ji haka sai na fashe da kuka na dubi bokan nace yakai wannan boka kayi sani cewa ina yin wannan kuka ne ba don zan mutum ba ko don bakin cikin abinda yar uwata taui mini kawai inayi ne sbda zan mutu na bar yata gimbiya shalbirat::


Page 107


Ina mai rokanka da ka bani taimkon da zan iya kunbutar da rayuwar  yata da mahaifiyata a bayan raina koda kuwa zasu gudu sukama wata nahiyar su cigaba da sabuwar rayuwa::


koda nazo nan a zancena sai boka yakamu da tsananin tausayina Har hawaye ya zubo masa sannan ya dora hannunsa a cikin aljihu ya dauko wani lailayayen dutse ya miko mini na karba sannan yace ka boye wannan dutse sai nan da  Kwanaki casa in: a daren kwana na casa in dinne zaka mutu a lokacin dare ya raba tsakiya:


Lallai kafin cikar wannan lokaci ka damkawa yarka wannan dutse dana baka yanzu sannan ka umarceta da taje ta janye mahaifuarta a cikin wannan dare su sulale daga cikin birnin nana:

idan har wannan dutse yana hannin yarka shalbirat kuwa tana tare da mahairyarta babu wani tsautsayi da zai samesu har sun fice daga wannan nahiya:

koda bokan yazo nan a jawaabinsa sai na kamu da tsananin farinciki:

duk da cewar a kwance nake cikin jin radadin ciwo sai dana yunkura na mike zaune da kyar na kama yi masa gdya:


kafin na kirawo hadimina nasa a baiwa bokan lada tuni ya bace bat:

Ya nanemeshi sama da kasa ya rasa:


Nan take na boye wannan farin dutse a cikin aljihun wandona bantaba yarda ani ya ganshi ba duk dacewar ina cikin halim cuta::


Page 108

daga wannan rana kullum sai yar uwata Juzairat tazo turakata ta zauna sai ta sani a gaba ta na ta kuka tana nuna matukar bakin cikina bisa lalura da nake ciki:::::::::::


ANAN ZAN DAKATA SAI KUMA IN ALLAH YAKAIMU GOBE DASAFE ZAMU DAURAN DAGA INDA MUKA TSAYA:

NAKU HAR KULLUM SULEIMAN ZIDANE KD:::

FIRS ADMIN NA PAGE:: Home of Littafan Yaki  And Hausa Novels


Matan Arewa Special Group


Zauren Muslims

MAZAN JIYA 4

Littafe na hudu

Part 19

Typing:: Suleiman zidane kd:

daga wannan rana kullum sai yar uwata Juzairat tazo turakata ta zauna sai ta sani a gaba ta na ta kuka tana nuna matukar bakin cikina bisa lalura da nake ciki:::::::::::


Dai dai rana daya ban taba nuna mata cewa nasan kaidin data kulla mini ba:

Sai dai kawai idan na kalleta na zubar da hawaye takaici:

ba komai ne yasa nake zubar da hawayen takaici ba face nayi matukar mamaki bisa yadda wacce nake kauna fiye da komai a duniya ita ce take son ganin mutuwata:


Har izuwa wannan lokacin da nasan cewa ita ce ta samini wannan ciwo ban ji na tsaneta  cikin zuciyata ba sbda tun muna yara kanana na taso da tsananin sonta:


A dalilinta nayi yake yake ba adadi:

Na bata da abkaina sarakai wadanda suka kasance aminena sbda sun nemi aurenta basu samuba:

hakan ta faru ne sbda na bata damar tazabawa kanta miji: Muna yara juzairat ta taba taka dan aljani suka shafeta:

A kokarin samo mata magani sai dana bar gida na shekara hudu a cikn daji har na kusan rasa rayuwata domin da na dawo gida sai da na shekara guda akwance ina jinya::


kuma an bata maganin da nakawo take ta warke daga cutar mutuwarrabin jiki::


Yau gashi an wayi gari Juzairat suk ta manta da wannan wahalar da na sha a dalilinta wai ita ce ma take neman rayuwata sbda kawai kwadayin mulki kuma har takeson ta sabauta iyalina:


Page 109

yake yata yanzu zan baki wanan fari dutsen wanda boka ya bani:

Da zarar kin karbeshi sai ki ruga izuwa dakin mahaifiyarki ki labarta ma duk abinda na gaya miki yanzu domin ku gudu:


     Koda gama fadin hakan sai sarki ya zura hannunsa acikin aljihun wando ya dauko wannan farin dutsen ya miko mini:


HANNUNAna karkarwa  kuma ina kuka na karbi dutsen sannan na fada kan kirjinsa na kankameshi ina mai sake fashe wa da matsaicin kuka ina cewa ba zan iya rabuwa da kai ba ya kai abbana gwara na tsaya aljani ya kamani ya kaini inda bazan sake ganin komai da kowa ba har izuwa ranar ajalina tunda dai kaima mutuwa zakayi::


koda jin haka sai hankalina ya dungunzuma ya shiga rarrashina yana bani baki: 


sai da na shafe sa a biyu ina kankame da shi ina kuka da kyar ya shawo kaina na amince na sauka daga kan kadon rike da wannan farun dutsen na sihiri a hannuna ina waugensa ina zubar da hawaye shima yana daga mini hannun hawaye na kwararowa daga cikin idanunsa:


INA ZIDANE RANAR SAI DANAYI HAWAYE SOSAI::


Haka dai na daure na fice daga cikin turakar na ruga izuwa turakar mahaifiyata a cikin wannan dare:

  Duk inda na gifta a cikin gidan sai naga dakaru suna bina da kallo cikin mamaki::


Page 110

Haka dai na cigaba da gudu har na isa cikin turkar mahaifiyata na kunnan kai izuwa cikin turakarta:


Ina shiga sai na iske mahaifiyar tawa zaune a gefen gado idanunta cike da hawaye kuma ko kadan babu alamar tayi barci a kwayar idanunta:


Al amarin da yai matukar bani mamaki kenan na karasa gareta jikina a sanyaye:

HAR NA BUDI baki zan yi mata bayanin abinda ke tafe dani sai ta rigani tace duk abin da ya faru yanzu tsakaninki da m Amahaiki naji kua na ganin domin ina labe a kofar dakin ina kallonku baku sani ba::


Yake yata kiyi sani cewa zuciyarta ta karaya domin nasan cewa abi ne mawuyaci mu tsira daga sharrin Juzairat:


  Ni kam na zabi na mutu tare da mijina yau a cikin wannan dare nan da cikar sa a guda inyaso ke ki tserar da kanki::


koda jin wannan batu sai na fada kan kirjin mahaifiyata na fashe da sabon kuka ina mai cewa ai kuwa sai dai nima na tsaya na mutu tare da ku din da dai na tafi wata nahiyar daban na zauna inda ban ssan kowa ba ba a sannani ba inda babu uwa kuma babu uba:

Hakika rayuwar da babu masoyi ai ba ta da wani amfani a doron kasa::::::::


Page 110

koda mahaifiyata taji wannan batu sai ta mike tsaye zumbur cikin firgici ta sureni da gudu muka fito daga cikin turkarta:

Nan fa ta direni kasa ta kamo hannuna ta jani muka cigaba da gudu muka nudi kofar fita daga cikin gidan sarautar gaba daya:


Har a sannan ina rike da wannan farin mulmullen dutse na sihiri wanda mahaifina ya bani:


muka cikin gudun ne muka jiyo alamar wata irin gagarumar iska ta biyomu a baya tana kokarin cafkomu amma ta kasa:


Sai da ya rage saura bai fi taku biyar ba tsakaninmu da bakin kofar wacce tuni masu gadi sun firgice sun budeta suma sun cika wandunansu da iska sun yi waje:

Kawai sai muka ji wani irin gurnani mai tsananin ban tsoro a bayanmu:

page 111

Cikin tsananin firgita ni da mahaifiyata muka waiga baya ai kuwa sai muka yi arba da aljani Raugatul Aguwanu:


Nan takemuka razana ainun:

Faruwar hakan ce tasa nayi tuntube na fadu kasa:

ina faduwa sai wannan dutse dake tafin hannuna ya subuce ya gangare kasa can gabana:


kafin na mike ba ruga inda dutsen yake sai kawai naji an figeni anyi sama dani ana  ta kyalkyala wata dariya mugunta:

Abinda idanuna kawai suka iya hangowa sa adda na kallo kasa shine: Haukacewar mahaifiyata tana ihu tana cisge gashin kanta kuma tana sambatu:


Page112

Daga nan sai jinayi an lulaka dani izuwa can kololuwar samaniya a sannan ne jiri ya debeni:

Lokacin fa na farka na bude idanuna sai na tsinci kaina a cikin wannan dan karamin keji da ke rataye a saman kogon aljani RAUGATUL AGAWANU:


a firgice na mike tsaye na kama kai kawo cikin kejin: a sanan ne na gane cewa an asirceni na zama yar mitsitsiya:

Nan take na kwarara uban ihu kuma na fashe da matsanaicin kuka:


lokacin da Gimbiya Shalbirat ta zonan a Labarinta sai hawaye ya zubo mata ta dubi sadusa Halyal tace wannan shine labarina don haka ni na sancewa anan dajin zan gama rayuwata tunda ba zaku iya kubutar dani ba daga hannun wanan azzalumin aljani kuma ko dama kin kubutar dani bani da sauran sha awar cigaba da rayuwa tuda bani da sauran masoyi a doron kasa:


Koda jin wannan batu sai tausayin shalbirat takama boka sadusa da dansa halyal har idanun su suka ciko da kwallah:


kawai sai halyal ya dube shalbiyat yace yake wannan ma abociyar  kyawu kayi sani cewa baki databbacin cewa mahaifiyarki tana raye ko ta mutu?

 

Saboda haka bai kamata ki  cire sha awar ci gaba da rayiwa b a doron kasa:


Page 11 3:

Suleiman zidane kd:


bayan haka ina mai tabbatar miki dacewa mahaifina da muke tare da shi a yanzu zai iya kubutar dake daga hannun wannan aljani kua na yi miki alkwari komai dadewa sai na rakaki har izuwa birninku kin sadu da mahaifiyarki muddin tana raye:


Haka kuma indai juzairat na nan a raye sai kin dauki fansa akanta:


Sa adda Gimbiya Shalbiraat taji wannan bau sai ta girgiza kai tace wannan albishir naka daidai yake da tatsuniya a cikin kunnena ko kumma na kirashi da mafaarki da va zai taba zama gaskiya ba:


Koda jin haka sai boka sadusa yayi dariya sannan ya dubi shalbirat yace ke yarinya abinda dana yafada miki gaskiyane amma bari na fara nuna miki karfin aikina tun daga yanzu::


Gama fadin hakan ke da wuya sai sadusa ya karanta wadansu dalasiman tsafi guda bakwai ya tofa akan tafin hannunsa na hagu sannan ya dafa kan shalbirat::

Nan take Shalbirat ta dawo cikakkiyar surarta ta budurwa mai tsananin kyauwun diri da sura maimakon yadda ta kasance a da yar mitsitsiya:


Shi kansa sadusa sai daya dimauce bisa ganin tsananin kyawun nata:


Yayin da shalbirat taga ta dawo izuwa chakkiyar surarta ta mutum sai ta cika da tsananin farin ciki ta kama kyakyal dariya kamar bazata daina ba::


Page 114:


sai daga can ta nutsu ta dubi  boka sadusa ta durkusa har kasa bisa guiwoyinta takama yi masa gdya shi kuma sai ya kama kafadunta ya yasheta tsaye suka fuskacin juna yana mai yi mata murmushi yace wannan taimako dana yi miki ba komai bane face taimakon kaina domin kema akwai muhimmiyar rawa da zaki taka nan gaba bisa bukatar da ta fito damu daga birninmu::


A gobe ne zan rabaki da wannnan daji kuma idan mun isa can bakin kogin bahar sufiya za ki rabu da wannan azzalumin aljani har abada:


yanzu sai kuzo mu cigaba da yawatawa a cikin wannan daji har izuwa lokacin da aljani Raugatul Aguwanu ya bukata:


Koda gama fadin haka sai boka sadusa ya kunna kai izuwa cikin dajin cikin sauri shalbirat ta kama hannun Halyal suka taja shi suka bi bayan boka sadusa::


Haka dai su boka sadusa suka yi ta yawo a cikin dajin Darul HusHushul Maut; Shalbirat ta wucce gaba tana yi musu jagora har suna mamaki yadda ta lakanci hanyoyin dajin:


Ai kuwa sai suka yi ta ganin  abubuwan al ajabi wanda basu taba tsamamanin zasu gani ba: 


Abinda suka gani kuwa shi ne gaba daya bishiyoyin dajin na yan yan itatuwa ne iri iri sannan kuma bishiyoyin da ruwa ke zuba daga cikinsu mai haske da dadin dandano:


Page 115


 gaba daya dajin  a cikin ni ima yake kuma kowanne wuri irin tasa ni imar dabam data gaba:


Duk inda mutum ya shiga ba zai ji zafi ba kuma ba zai ji sanyi ba sannan a duk inda zaka kwanta wata irin ciyawa ce a lullbe mai tsananin laushi kuma hankalo kwance mutum zai yi kwanciyarsa babu tunanin wani kwaro zai cijeshi ko kuma wata muguwar dabba zata kawo masa hari::


Nan take sadusa Halyal da shabirat suka tsinko yayan itatuwa kala kala masu dadi suka sami wuri suka zauna suka kama ci suna hira har sai da suka koshi sannan suka mike suka cigaba da yawo abinsu:


Shalbirat  Dai a wannan rana ji ta yi taamkar an tsamota daga cikin gagarumar wuta an sanyata a cikin ruwan sanyi sbd farin ciki::


Haka dai suka wanzu suna yawo har suka gaji suka kwanta suka kama barci:


Al amarin aljani Raugatul Aguwanu kuwa tunda ya sha wannan giya yayi tatul kama barci bai farka ba sai da dare ya raba:


A firgice ya farka zuciyarsa na dukan uku uku:


Cikin hanzari ya mike tsaye ya dauko madubinsa na tsafi ya shafeshi:


Nan take yaga Hoton Shalbirat Sadusa da Halyal a cikin dajin a kwance suna ta shara barci::


koda yaga Shalbirat a cikin cikakkiyar surarta:

ta mutum sai ya razana ainun ya kuma tabbatar da cewa lallai boka sadusa ya cika hatsabibi domin shi a tunaninsa baza a taba samun bokan da zai iya karya wannan asirin ba:


Page 116

Nan dai zuciyarsa ta kama sake saketana mai gaya masa cewa:


AI KAWAI YANZU TUNDA SU BOKA SADUSA BARCI SUKEYI YAJE YA KASHESU YA DAUKE SHALBIRAT YA SAKE MAI DA ITA YAR MITSITSIYA YA SATA A CKIN KEJINTA:


wata zuciyar kuma sai ta ce da shi::


TO IDAN KUMA KA KASHE WANNAN BOKA WAYE ZAI TSERAR DA KAI DAGA SHARRIN SARKI DA ZAI MALLAKI KAYAN YAKIN MAZAN JIYA?


TABBAS IDAN KA BIYEWA SON ZUCIYARKA ZAKA YI CIN DARE DAYA NE KUMBURIN CIKI:


ZAI FI KYAU KA TSAYA KA GA IYA KOKARIN DA WANNAN HATSABIBIN BOKA ZAI YI MAKA:


haka dai aljani Raugatul Aguwanu yayi ta wasi wasi acikin zuciyarsa har dai daga karshe ya yanke shawarar ya jira abinda zai faru a gaba:


Kashe gari da sassafe su boka sadusa suka farka daga barci kawai sai suka ga aljani Raugatul Aguwanu

zaune a can gefe daya ya zura masu idanu:

koda suka tashi zaune sai Raugatul Aguwanu ya risina ga boka sadusa yai gaisuwa sannan ya dubi shalbirat ya sake duban sadusa yace ya shugabana anya kuwa bakayi mini gaggawa ba?


Ai ina ganin cewa bai kamata ka ai da shalbirat izuwa ainahin siffata ba tun yanzu tunda ban gamsu da cewar za ka iya warware mini matsalata ba::


Page 117

zidane kd::


koda jin wannan batu sai boka sadusa ya murtuke  fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa ya dakawa Raugatul Aguwanu harara yace shin kaine ka fini sani abinda yafi dacewa muyi ko kuwa nine?


Raugatul Aguwanu ya sunkui da kansa kas ya ce ka gafarceni ya shugabana mantawa nayi::


boka sadusa yai murmushi yace yanzu nake son ka daukemu mu ukun nan domin mu tafi izuwa can sansani yaki wato can baki kogin bahar sufiya :


   koda jin haka sai idanun Raugatul Aguwanu suka zazzaro ya kamu da tsananin tsoro yace haba ya shugabana ya ya zaka ce na kaimu izuwa inda ajali yake?


Ina mai tabbar maka dacewa masifar da ke bakin kogin bahar sufiya a yanzu babu kamarta a ko ina a cikin duniya::


koda jin haka sai boka sadusa yayi murmushi sannan yace ai ba wai ina nufin muje har inda ake yakin bane zaka sauke mu ne acan bayan kogin bahar sufiya nesa da inda ake fafata yakin sannan kaje kayi mana leken asiri bisa abinda ke faruwa::


abinfa nake bukata kawai shine nagane bangaren da suke samun nasara:

Da zarar na gano hakan akwai a sihirin da zanyi daga inda muke mu dauko Takobin SAIFUL LUJA RA a karkashin kogin ba tare da su sarki dujalu sun sani ba mu bace daga wajen::


kaga kenan sun sha wahalar banza kuma sun kashe junansu a banza wato kura da shan bugu gardi da kwashe kudi::


koda boka sadusa yazo nan a zancesa sai aljani Raugatul Aguwanu ya kura masa idanu cikin 

alamun rashin yarda yai shiru yana tunani da nazari::

Page 118

daga can sai ya ce kai boka nifa ina ganin cewa kazo mini da zance na rainin hakali:

Yaza ai kace zaka iya dauko takobin saiful lujara da karfin sihirinka alhalin wadanda suka fika karfin sihirin nesa ba kusaba sarki dujalu da sarki maharaz tuntuni sun kasa daukota?


Koda ma dayansu ya sami nasarar wannan yaki sai ya sha bakar wahala kafin yagano inda takobin take acikin karkashin tekun:

Kai ni ga yadda mana sami tarihi cewa aka yi tsaron dake inda takobin take yafi gaban hasashen mai hasashe sai dai abinda ido ya gani kawai::::::::::


ANAN ZANDAKATA SAI KUMA IN ALLAH YAKAI MU GOBE ZAMU CIGABA:

NAKU HARKULLLU SULEIMAN ZIDANE KD::: KUYI COMMENT::MUNASON HAKAN:::::

Page din mu....

gawadan da basu karanta farko littafe ba kuzi yarci wannan page Mai suna Duniyar masoya littafan yaki only..

πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

Aslm yan uwa ga page dinnmu sai kayi kokari shiga domin samun Littafe Kala Kala cikin blue dinnan Na kasa..


Duniyar Masoya Litattafan yaki only


Home of Littafan Yaki  And Hausa Novels


Matan Arewa Special Group


Zauren Muslims

MAZAN JIYA 4

littafe na hudu 4

part 20

typing: suleiman zidane kd:

::

Koda ma dayansu ya sami nasarar wannan yaki sai ya sha bakar wahala kafin yagano inda takobin take acikin karkashin tekun:

Kai ni ga yadda mana sami tarihi cewa aka yi tsaron dake inda takobin take yafi gaban hasashen mai hasashe sai dai abinda ido ya gani kawai::::::::::


koda jin wannan batu sai boka sadusa ya murtuke fuskarsa yace to shikeanan idan har baka aminta da abin danake gaya maka ba sai ka yankewa kanka hukunci :

kofa dai yanzu my yaki juna ni dakai wandaya kashe dayan yayi abinda yaso: ko kuma murabu salin alin kowa ya kama gabansa:

amma kasani dace idan muka rabu salin alin har abada ka rabuda Gimbiya Shalbirat kenan baza kasake mallakarta ba:


lokacin da boka sadusa yazo nan a zancesa sai hankali aljani Raugatul Aguwanu

ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe yarasa abinda ke masa dadi a duniya:

nan fa ya kasa zaune ko tsaye ya rinka kai kawo :

daga can sai ya dubi sadusa yace ka bani sa a uku na koma can kogona nayi bincike:

Page 119

da tunani tukkunna:

sadusa yai murmushi yace jeka nabaka tsawon sa a biyar ma:

nan take aljani Raugatul Aguwanu

 ya bace bat tamkar kiftawar ido:


A Sannan ne shalbirat ta dubi boka sadusa cikin alamun tsoro tace yakai abul halyal anya kuwa kana ganin cewa Raugatul Aguwanu zai amince ya daukemu yakaimu bakin kogin bahar sufiya?


To wai shin ma meye hikimarka ta zuwanmu can din alhalin kasan cewa sansani ne na mutuwa?

Sadusa yai ajiyar zuciya sannan yace kiyi hakuri yake wannan yar sarki:

Ki tuna cewa mu bamu baki labarin mu ba kamar yadda kika ban mu naki sakamakon cewar babi isashen lokaci na yin haka:

Page 120

zidane kd:


Ni dai kawai abinda na sani shine sau tari sai ka tari aradu da ka sannan kake fita daga cikin wata masifar:

akwai abin da ya baromu da kasarmu kuma bukatarmu ba zata biya ba face mun dangana da bakin tekun bahar Sufiya inda ake yin wannan yakin:

kuma ki rungumi kaddara har izuwa sa adda zamuje can dinko bakomai dai gwara ki mutu acan sansanin yakin da dai ki mutu a hannun wannan azzalumai alajni:

kodajin wannan batu sai shalbirat ta jinjina kai tayi shiru bata kara cewa komai ba::

* *  *:

BIRNIN SARKI DUJALU:


ACAN gidan sarautar sarki dujalu kuwa tundaga ranar da kunyaga lazimat ta tafi neman hanyar da Gimbiya Hursiya zata sami damar komawa sansanin yaki a cikin kwanki kadan bata dawo ba har kwanaki biyu da aka dirba mata suka cika:


A dare kwana na biyun ne hankalin Gimbiya Hursiya ya dugunzuma ainun ta kasa zaune ko tsaye:

fara zubar da hawaye domin ta saddakar da cewar har abada baza ta sake ganin dan uwanta ba sarki dujalu ba:


Page 121

babu abinda yake kara fusatata facw a duk sa adda ta leka wajen turakarta ta cikin taga sai ta hango aljani barzaru yana shawagi a saman turakae yana kewayeta don tabbatar da tsaro wato dai ta san cewa gadinta yake yi babu yadda za ayi wani ya iya zuwa yatafi da ita batare da yagani ba:


Gimbiya Hursiya na cikin wannan hali ne ta jiyo alamar takun sawu an nufo kofar turakar

Ta kawai sai ta zuba idanu akan kofar shigowar:


abinda ta sani shine koma wanane ya taho in dai bai kasance daya daga cikin kuyangitaba ko bayinta aljani barzaru ba zai barshi ya shigo ba:

Ashe ba wani bane ya durfafo turakar ta ba face kuyanga lazimat rike da wani jan fure mai kamshin gaske fisa faranti:

yayin daya rage bai fi saura taku biyar ba tsakanin kuyaga lazimat da kofar turakar gimbiya sai kawai taga aljani barzaru ya fado juf a gabanta;

ko Gezau batayi ba ta dubeshi a fusace yace meye haka zaka sha gabana alhalin kasanni na sanka ko kuwa ni bakuwa ce  a gidannan?


Aljani barzaru ya daka mata tsawa wacce tasa hanjin cikinta ya kada hannunta yakama karkaewa har farantin dake hannunta ya fadi kasa tayi sauri daukeshi:

Barzaru yadubi wannan fure dake kab faranti da kyau sannan ya dubi kwayar idanun lazimat ko zai ga alamun rashin gaskiya a tare da ita sanna ya ce: ke tsohuwar makira: ni fa ban yarda dake ba ina kyautata zaton cewa akwai wani kullin boye da kuke shiryawa ke da gimbiya:

page 122

shin baku san cewa ina lura da dukkan motsi ku ba? Yau kwanaki biyu kenan rabonki da turakar gimbiya alhalin kullum kuna tare baku taba rabuwa ba sai sa adda sarki ya tafi da gimbiya bakin tekun bahar sufiya: lallai akwai alamar cewa ta turaki ne kiyi mata aikin ne don haka ban yarda da wannan furen da kika kawo mata ba:

bani shi na koneshi:


Har aljani Barzaru ya yunkura zai dauke fure sai ya jiyo muryar gimbiya Hursiya tana mai daka masa tsawa; ba shiri ya janye hannunsa: nan take Hursiya ta dako kofar turakarta ta fito waje cikin tsananin fusata ta dubi aljani barzaru tace au sbda samun dama shine zaka wuce gona da iri a cikin aikin naka na gadinna?

Shin ka manta ne cewar tun ina yarinya karama babu abinda nakeso sama da jan fure?


Ka sani cewa labari ne yazo mini cewa an sami sabon samfarin jan fure a can birnin zandal shi ne na aikata taje ta siyo mini shi kuma ka san cewa dole ne mutum ya shafe kwana biyu kafin yake birnin zandal ya dawo ::

ka dubi wannan fure da kyau kaga ni zaka ga cewa yasha bamban da irin sauran janjayen furen da ake kawomini:

page 123

suleiman zidane kd:

Koda jin haka sai aljani barzaru ya kurawa wannan fure idanu nan take kuwa ya ga lallai fure ne dabam domin bai kasance ja zallah ba akwai ratsin ruwan dorawa a jikinsa:


koda ganin hakan sai ya zube kasa a gaban Gimbiya ya kama tuba;

ko kallinsa Gimbiya batayi ba ta kama hannin kuyanga lazimat taja izuwa cikin turakar suka rufe kofa suka kulle:

A sannan ne aljani barzaru ya mike tsaye ta bude fuka fukansa yai sama yana mai cigaba da shawagi yana kewaya saman turakar ta gimbiya don tabbatar da tsaro:


ABINDA BAI SANI BA SHINE AN KULLE KOFA DA BARAWO KUMA BAWANI BANE BARAWON FACE WANNAN JAN FURE WANDA KUYAGA LAZIMAT TA SHIGA DA SHI CIKIN TURAKAR GIMBIYA:

Lokacin da Gimbiya Hursiya ta ja kuyanga lazimat izuwa cikin turakarta sai suka shige har can cikin daki barcinta:

Suna shiga sai lazimat ta rufe dakin gami da tagogi sannan ta fiddo wani turare wuta na tsafi daga cikinAljihun rigarta:

take turarren wuta ya kunna kansa hakinsa ya cika dakin gaba daya tamkar hazo ne ya shigo dakin:

faruwar hakan ke da wuya sai wannan jan fure da ke kan faranti wanda lazimat taxo dashi ya rikide ya zama wani dan wadan aljani mai kwalelen kai wanda tsawonsa bai wucce kamu biyu ba:

page 124

Zidane kd:


tunda gimbiya Hursiya ta zo duniya bata taba ganin mitsitsin wada kamar saba sai kace yar tsana:

yana da kwala kwala idanu kamar na mujiya hancinsa kuwa wakakeke ne kamar na a zura kwai a ciki:

yana da dan mitstsin baki tamkar kwallon dabino bazai iya shigewa ba:

kafafuwansa kuwa yan dugul dugul ne kaman na agawagi:

koda bayyaynar wannan aljani sai gimbiya Hursiya ta fadawa kainun taja da baya cikin sauri tana mai fadawa kan gadonta kamar za ta kwalla ihu:

cikin tsananin razana ta dubi kuyanga lazimat tace sabda me zaki jeki nemo mini wannan aljani n mai ban tsoro haka?


Koda jin ewannan tambaya sai kuyanga lazimata tayi murmushi sannan tace ya shugabata wannan aljani ba mai cutarwa bane kawai dai halittarsa ce haka:


nantake dan wadan yadaka tsalee daga fartanti dayake ya dure kasa daf da gadon Gimbiya yai sujadda agareta yace sunana boka RADIYAL IBN ZAILUR: INA zaune a can nahiyar da ke kudanci taku ne sako ya riskeni cewar kina neman wanda zai kaiki can sansanin yaki na teku bahar sufiya shiyasa na taso da kaina nazo domin na biya  miki wannan bukata amma bisa sharadi guda:??


ANAN ZANDAKATA SAI KUMA IN ALLAH YAKAIMU GOBE DASAFE DAFATAN ZAN IMIN AFUWA NAKWANA BIYU DA AKAJENI SHIRU::COMMENT:::

MAZAN JIYA 4

Littafe na Hudu 

Part 21

Typing: Suleiman zidane kd:

in baku manta ba mun tsaya:

INA zaune a can nahiyar da ke kudanci taku ne sako ya riskeni cewar kina neman wanda zai kaiki can sansanin yaki na teku bahar sufiya shiyasa na taso da kaina nazo domin na biya  miki wannan bukata amma bisa sharadi guda:??

Cigaba:

Page 125

Koda jin wannan jawabi sai Gimbiya Hursiya ta tashi zaune tana ;mai gyara zama sannan ta dubi boka Radiyan ciki murmushi tace ina sauraronka ya kai wannan babban boka:

Radiyan yayi gyaran murya sannan yace a halin yanzu nayi bincike na gano cewa a duk fadin duniya babu wani aljani dazai iya zuwa bakin kogin bahar sufiya a cikin yan kwanaki kadan kafin a gaa gagarumin yaki da ake fafatawa acan face aljani daya wanda ake kira da suna Raugatul aguwanu wanda ke zaune a cn dajin darul Hushshul maut:

Dajin ne wanda sama da shekaru bakwai baya mutane aljanu dabbobi da tsuntsaye da kwari suka daina shiga ko wanzuwa a cikinsa amma a halin yanzu wani takadarin boka dake nan garin mai suna sadusa ya karya kofin da ke dajin ya shiga har ya sadu da aljani Raugatul aguwanu zai daukeshi a gobe su tafi izuwa bakin kogin na bahar sufiya:

zan iya kaiki can dajin Darul Hishushul maut a yau dinnan acikin abinda wuce sa a biyar ba kuma zamy shiga ne a sirrance ba tare da mun bari su aljani Raugatul aguwanu sun ganmu ba ko suji motsinmu ba:

Nida ke zamu shiga cikin kunnen aljani Raugatul aguwanu ne muyi zamanmu a ciki a lokacin da yake barci: 

Ba zai taba sanin da zamanmu ba a cikin kunnen nasa muddin zamu jure yi masa susar kunne domin a duniya babu abinda yake sa shi yamanta da koai face susar kunne:

Page 126

zidane kd::

A haka za a tadi dau izuwa bakin tekun bahar sufiya ba a sani ba:


Sharadin dake tsakanina dake shi ne ba zan yarda na kaiki inda aljani Raugatul aguwanu yake ba face kinyi alkawari cewar idan dan uwakinki sarki dujalu ya sami nasarar cin yaki kuma ya dauko takobin Saiful Lujara zaki sa ya maisheni daya daga cikin manya fadawansa na hannun dama:

lokacin da boka radinya yazo nan a jawabinsa sai hankalin gimbiya Hursiya ya dugunzuma tayi shiru tana tunani da nazari al amarin ta rasa abinda zatace:

daga can sai ta dago kai ta dubi boka radiyan tace yakai wannan boka kayi sani cewa ina da wadansu yan tambayoyi a gareka kafi na aminta dakai:

da farko dai ina son kaga mini dalilin da yasa boka sadusa yaje ya hada kai da aljani Raugatul aguwanu domin yaje sansanin yaki?

Tambaya ta biyu itace ta ya kake tunanin zaka iya fitae dani daga cikin gidan sarautae nan har ka kaini dajin darul hushushul maut alhalin aljani barzaru na shawagi a saan turakata yana gadina?


Tambaya ta uku wacce itace ta karshe yaza ayi muyiwa aljani Raugatul aguwanu susa a kunnensa ba tare da yagane cewa akwai baki hallitu a cikin kunnen nasaba?


Page 127

zidane kd:

Sa adda boka radiyan yaji wanna tambaya sai ya bushe da dariya lokaci guda kuma ya hade rai ya ce yake wannan yar saki kiyi sani cewa hakika aiki sai mai shi:

Dangane da tambayarki ta farko am . Sarta itace fadawan dan uwanki suna son su gaje karagar mulkinsa idan har yazamana cewa bai sami nasarar yaki ba a bakin tekun bahar sufiya domin su ke suga halin da ake cikin a sansanin yaki ne boka sadusa ya nemi hadin kan aljani Raugatul aguwanu tunda shi kadaine xai iya zuwa can din:

dangane da tambayarki ta biyu kuwa itace sa adda na shigo gidan nan ba tare da aljani barzaru ya ganni ba taha kema zaki fita :

sai tambayarki ta uku wacce itace ta karshe amsarta itace duk jikin aljani Raugatul aguwanu babu inda yafi girma da nauyi sama da kunnunwansa guda biyu don haka idan muka shiga cikinsu tamkar a dauki yar karamar tsakuwa ne a jefa cikin RIJIYA GABA DUBU:


bazai ji sa adda zamu shigaba kuma dazarar mun fara yimasa susa zai sami cikakkiyar nutsuwa da zai yi azabbaben gudu a sararin samaniya har mu isa bakin kogin bahr sufiya cikin sa o i kadan:


Yanzu dai kin shirya zamu tafi cikin murna Gimbiya Hursiya tace aini bani da wani shiri sai naka:


page 128:

kafin ta gaa rufe bakinta tuni boka radiya yayi nuni da hannunsa na hagu gareta:

lokacin guda shi da ita suka rikide suka zama wannan jan fure guda daya kawai sau kuyanga lazimat ta sunkuya ta dauki wannan fure ta dorashi akan farantin ta fita daga cikin turakar gimbiya Hursiya rike da faranti:


Tana fitawa sai taga aljani barzaru tsullu agabanta fuskarsa a murtuke babu alamar annuri nan take ya daka mata tsaya ta firgita ainun har ta saki fitsari a tsaye bata sani ba:


hunnunta yakama karkawa farantin dake hannunta ya rinka jujjuyawa kamar zata sakeshi ya fadi::


aljani barzaru yadubi wannan jan fure da ke hannunta sannan ya dubeta cikin alamun rashin yarda yace ina ma anar fitowa da wannan jan fure yanzu alhalin dazu nan kika shiga dashi?

Kuyanga lazimat ta budi baki muryata na rawa tace ai gimbiya ce tace batason wannan kalar sai dai mai dashi na canjo da irin wanda aka saba kawo mata:

page 129:

barzaru ya ce tome yasa kuke gudanar da wannan al amari yanzu a cikin wannan dare maimakon ku zarta dashi da safe?

Lazimat tace ai ka sani cewa yanzu duk abinda gimbiya takeso shi takeyi tunda sarki baya nan:

Duk umarnin da ta bayar shi akebi a gidannan :

kodajin haka sai alajni barzaru ya gyada kai yace Tabbas kiyi gaskiya amma dai ni yanzu ban zan amince da keba facce mun koma tare dake cikin turakar gimbiya na ganta  da idanuna:

koda jin wannan batu sai hankalin kiuyanga lazimat ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe alamomin tsoro da rashin gaskiya suka bayyana kururu akan fuskarta:

koda ganin haka sai aljani barzaru ya tukuda keyarta suka koma cikin turakar gimbiya suka wuce kai tsaye izuwa cikin dakin barcinta:


zidane kd::

WHATSAPP 09064179602


koda suka tura kofar sai suka ui arba da gimbiya hursiya kwance akan gadonta tana ta shara barci:

al amarin da yai matukar daurewa aljani barzaru kai kenan yacika da tsananin mamaki:

ita kuwa kuyanga lazimat sai ta sami nutsuwa takama murmushi;

Nan take suka juyo da baya kafin su fice daga cikin dakin tuni gimbiya hursiya wacce ke kwance a kan gado tanaBarci ta rikide ta zama ha yaki yashige cikin wannan jan fure dake hannun lazimat ba tare da aljani barzaru ya lura ba:

PAGE 130

ZIDANE KD:


WANNAN SHINE ABINDA YAFARU A BIRNIN SARKI DUJALU BAYAN GIMBIYA HURSIYA TA SAMI HANYAR DA ZATA SAKE KOMAWA CAN SANSANIN YAKI DOMIN TA SADUWA DA DAN UWANTA SARKI DUJALU

:

*   * *

ACAN sansanin yaki kuwa ba a sake fitowa filin daga ba sai bayan cikar kwanaki uku:

Da sassafe kowane bangare suka fito alaui sahu sahu ana fuskantar huna aka baiwa tekun bahar sufiya baya:::


NIMA SULEIMAN ZIDANE SAI NABAWA TEKUN BAHAR SUFIYA BAYA:


DOMIN SAMUN LITTAFAN YAKI NA SOYAYYA E:BOOK KAI HAR DAMA AUDIO MP3 ZAKA IYA MANA MAGANA TA WATSAPP TA WANNAN NUMBER KAMAN HAKA 09064179602:

TURAMAKA KUMA MUSAKA A GROUP DINMU NA WHATSAPP:

NAKU HAR KULLU SULEIMAN ZIDANE KD NAKE CEWA ALLAH YANUNA MANA GOBE LAPIYA ::::

MAZAN JIYA 4

Littafe Na Hudu

Part 23

Na abdul aziz Sani:

Typing: Suleiman Zidane Kd:


:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::

Da sassafe kowane bangare suka fito alaui sahu sahu ana fuskantar huna aka baiwa tekun bahar sufiya baya:::

wannan karon sai gashi su magaba daya dakarun aljanu ma sun sauko kasa bisa turba fuskanci junansu:

Rundunar sarki maharaz na kallon gabas su kuma rudunar sarki dujalu sun bawa yamma baya kowa sai muzurai yake:

Gurnani da hucin dakarun aljanu kadai ya isa ya firgita mutu ya tsure da gudawa bare kuma idan yaga tsananin yawansu da kwarjininsu:

Abangare bil adama kuwa dakarun kowane bangaren sun yi sabuwar shiga Yaki fiye da wadda suka yi a karon farko da karu na biyu a Yakin kuma kowacce runduna ta fito ne a fusace da nufin ayi ta ta kare a yau wadanfa ke da sa a su sami nasara:

Page: 131

Batare da shakkar komai ba Jarumi Inmal ya fuskacin wani babban jarumi mayaki na sarki dujalu wanda yafi kowa kokari a wancan karo na biyu da aka fafata:

Sarki ya dubi inmal a wulakance cikin raini sannan ya dubi sarki Maharaz ya bushe da mahaukaciyar dariya yace yau zan kashe da a gaban ubansa:

Sannan nayiwa uban mugun kisan gilla irin wanda ba a taba yiwa wani mahaluki ba:

Kafin sarki dujalu ya gama rufe bakinsa tuni jarumi inmal yatari numfashinsa cikin daga murya ya daka masa tsawa yace kai tsohon azzalumi karyarka ta sha karya:

Na rantse da kaunar da nake yiwa mahaifina marigayi yau sai na kasheka da Hannuna kamar yadda ka kashe min mahaifina domin na rushe mugun nufinka na son ka mallaki kayan yakin MAZAN JIYA domin ka cigaba da mulki zalunci a doron kasa:


koda jin haka sai dujalu ya sake tuntsurewa da dariyar mugunta a karo nabiyu sannan yace ai shi kenan inda babu kasa anan ake gardamar kokawa kuma ga filo ga mai doki sai akasa tseren mugani:

Yau fa ba gudu ba ja da baya: 

Ba za a busa kahon tsaida yaki ba har sai dole bangare guda ya sami nasarar murkushe daya bangare a yau babu batun mutum da mutu ko aljani da aljan babu batun da tsafi ko babu tsafi: Duk abin mutu yake takama dashi to yayi amfani da shi tunda yau ne karo na karshe:

Page 132

Suleiman zidane kd:

whatsapp 09064179602:

Dajin wannan wajabi sai sarki maharaz ya yi murmushi murna yace abin nema yasamu tunda matar falke ta haifi jaki: Tunda ka zaba hakan nima na amince muje zuwa mahaukaci ya hau kura:

Nan take wani Shirgegen aljani mai siffan batoyi daga bangaren dakarun Sarki Dujalu ya daga wani narkeken kaho ya busa karar  bushin kahon ta cika dajin gaba daya amsa kuwa har ruwan tekun yakaa tamba tambal kamar zai yi ambaliya ya cinye duk abinda ke wajen:;

KAI HATTA NI ZIDANE SAI DA NA TOSHEN KUNNUWA NA SABDA TSABAGEN KARAR DA YA ADDA BINI::

koda mayaka suka ji sautin wannan kaho sai aka zabura aka ruga dagu daga kowawane bangare::


Wahoho ! Karar sawayen Mutane da aljanu cika kunnuwa sbda dudufniya kuma ya haddasa  karamar girgizar kasa:

Ihun mazaje kuwa da karajin aljanu ya  haifar da rudewar duk wata hallita dake dajin gaba daya rudewar duk wata hallitar dake dajin gaba daya har da wacce take cikin karkashin tekun bahar sufiya:

Page 133

lokacin da rundunoni biyu suka gwamutse kuwa sai aka ruguntsume da azababben yaki na gaban tashin hankali; domin nan take kasuwar diban rayuka ta kama ci:

sai dai kaga aljani ya daga kafa ya talitse bil adama hamsin a lokacin guda:

WANNAN WANA KALAR BALA KI NE ZIDANE KD:

Koda sarki maharaz da sarki dujalu suka ga anfara asarar rayunka bil ada;a daga kowane bangare sai kowannensu ya fara amfani da karfin sihirinsa na kone aljanun abokan gaba:

Waiyo! Nan fa gaba dayan  aljanun da ke sansanin suka raina jarumtakarsu gami da karfin sihirinsu domin duk ya tashi a banza sai dai kaga aljani ya kama da wuta yana ihu yana gudu domin ya fada cikin tekun bahar sufiya amma kafin ya kai bakin tekun tuni ya kone kurmus Hatta kasusuwan jakinsa sai sun ruburbushe sun zama toka:

Babu abinda zai baiwa mutum tausayi face yanayin mutuwar da suke yi domin da farko dai sai sun fara kumbura sun yi suntum Ya yin da wutar ta fara cin jikinsu sannan sai kaga idanunwansu suna bullutsowa su fado kasa daga nan kua sai cikin ya fashe kayan cikinsu su zubo:

da sun fara kokarin gudu kuwa sai kaga sassan jikinsu na guntulewa yana faduwa kasa a haka har sai sun narke gaba dayan su zama toka::

Page 134

zidane kd:

Sai da aka shafe sa a bakwai ana wannan bakin gumurzu suma mutane suna nasu yakin:

kuma kowanen bangare suna asarar rayuka:

Duk inda jarumi inmal ya kutsa a cikin rudunar sarki dujalu ta bil adama sai dai kaga mazaje na zubewa kasa ramkar ana sassabe a gona   sbda inmal ya fito da wanannan yaki ne a fusace da takobi biyu yake amfani don haka nan da nan jikinsa gaba daya ya rune da jini:

Koda sa a bakwai ta cika sai ya zamana cewa gaba dayan  dakarun aljanun sun kare babu ko guda daya a wajen:

Don haka sai aka daiana jin karajinsu: hakan cetasa kowanne bangare suka janye aka ja da baya akayi cirko cirko ana haki da kallon juna:

A sannan ne kowane bangare ya gano irin mummunar barnar da akayi masa:

Su kansu dakarun bil adama na kowane banagare an kashe kimanin kaso saba in daga ciki dari::

Tarin gawarwakin da ke zube a kasa kuwa wasu kan wasu har suna tisra a sama gar ya ninka na wancan karon:

koda sarki dujalu ya dubi gaba day gawarwakin dake zube a kasa kuwa wasu kan wasu har suna tsira a sama har ya ninka na wancan karo;

koda sarki dujalu ya dubi gaba dayan gawarwakin da ke kwance a kas kuma ya dubi ragowar dakarun bil adaman da suka rage a tsaye ya fahimce cewar RAGAS ake yi a wannan yaki: sai rabsa ya baci zuciyarsa taka ma tafarfasa kaan zata kone:

Page 135:

zidane kd:

kawai sai ya takarkare ya kwarara uban ihu sannan ya wangame bakinsa wata irin gagarumar guguwa ta rinka fitowa daga cikin bakinsa ta durfafo inda abkan gaba suke zata hallakasu gaba daya:

koda sarki maharaz yaga wannan guguwa ta durfafo rundunarsa sai shia ya wangame bakinsa irin wannan guguwa ta rinka fita da gudu taje ta tare guguwar dujalu:

Ai kuwa suna haduwa sai suka haifar da tsawa tartsatsin wuta gai da walkiDa kumma girgizar kasa:

tsawon yan dakiku ana cikin wannan masifa gami da tashin hankalo amma an rasa wanda zai iya cutar da wani:

Al amarin daya fusata sarki maharaz da sarki dujalu kenan suka ci gaba da jarraba sirrinkan tsafin su kenan har sai da kowannen yayi amfani da sihiri guda dari da tara da casa in da tara; a Lokacin be duk su biyun suka jigata ainun kuma suka jike sharkaf da gumi suka zube kasa a cikin matukar galabaice suna numfashi sama sama:

kamar ransu zai fita:

A wannan lokaci jama ar kowannensu sun yi cirko cirko suna kallon abin al ajabi: baan sarki dujalu da sark maharaz sun dawo cikin hayyacinsu sai suka mike tsaye a tare kamar hadin baki suka tako kafafuwansu suka durfafi juna:

Page 137

Cikin Alamun tsoro inmal ya yunkura zai kaiwa sarki maharaz dauki don gudun kada dujalu ya cutar da shi kawai yaji anrukoshi ta baya yana waigawa ya ga ashe Gimbiya mulaifa ce kawai  sai ta dubeshi tace kwantar da hankalinka ya masoyina sarki dujalu ba zai iya cutar da mahaifina ba sbda karfinsu yazo daya kuma kasani cewa babu yaudara ko ha inci a wannan yaki bisa alkawarin da aka dauka da farko  sai gaskiya da gaskiya: 

kai ga ke nan ko yar kashi zasu gwada kafin ya cutar da shi zamu iya kai masa dauki a sake ruguntsumewa da yakin gaba  daya: kuma ni ina ganin cewa tunda yanzu sarki dujalu yasami nakasa hannu daya gareshi sarki zai iya saun galaba akansa:

inmal ya girguza kansa yace bahaka  bane duk yadda kike zato sarki dujalu ya wucce nan wannan rashin hannun dayan da yayi ba zai rage masa komai ba face a yakara masa tsananin  kafin zuciya da taurin domin ya gaya dauki fansa:

Ni yanzu kawai abinda nake tsoro shi ne rashin sanin mutane hudun da aka ce sune kadai zasu rayu a wannan Yaki; ni kaina bana sa kaina a cikin wadanda zasu tsiran:

Page 

137

koda jin haka sai mulaifa ta girgiza ka tace idan har kayi imani da cewa akawi wani addini wanda yafi dukkan addininmu gaskiya to bai kamata yanzu karinka amfani da abinda tsafinmu ko tsafin sarki dujalu ya fadi ba:

Ka yi sani cewa tun da ka bani labarin ma abota addinin MUSULUNCI sai tunanina ya sauya akan komai kuma naji cewar na gamsu da addini don haka kaia yanzu ina sonka sauya tunaninka daga kan komai ya koma ya izuwa ga yarda da wannan sabon addini na Musulunci:

Sa adda jarumi inmal yaji wannan batu sai yayi ajiyar zuciyar sannan yace hakika kin yi Gaskiya ya masoyiyyata tabbas yanzu bani da tabbacin abin da zai faru a karshen wannan yaki:

Yanzu dai bari muzuba ido muga abinda zai faru a tsakanin manya Giwayen biyu:

Gama fadin hakan ke da wuya sarki maharaz da sarki dujalu suka hada yazamana cewa tazarar da ke tsakaninsu bata wucce ta ku uku ba:

sarki dujalu ya dubi maharaz ya kyalkyale da dariya ai kuwa shima sarki maharaz ya bushe da dariyar suka zama kamar wadanda suka sami tabin hankali: 

lokacin guda kuma suka tsuke bakunansu koda ya murtuke fuska sannan dujalu ya dubeshi yace Hakika nayi maka jinjina yakai abkin gaba:

domin haka akeson namijin kwarai ya zamo mai taurin rai da rashin Karayar zuciya:

gashi dai  fiye da rabin dakarunmu na yaki sun shude amma baka sare ba kuma gashi na kashe babban amininka abokinka kuma masoyinka na kwaria wanda ya kasance dirka birninka amma ba ka razana ba:

to fa ka sani cewa yanzy ne zan a rufe babin wannan yaki tunda ni da kai duk mun yi amfani da karfin sihirinmu har guda daru tara da casa in da tara saura guda dai dai yarage mana kuma kasani idan mukayi amfani da cikon na dubun dayan mu bai sami nasara ba shi  ne har abada tsafinmu ya daina tasiri::::


ANAN ZANDAKATA SAI KUMA GOBE IN ALLAH YAKAIMU :SULEIMAN ZIDANE KD:

DOMIN SAMUN LITTAFAN YAKI NA SOYAYYA E:BOOK KAI HAR DAMA AUDIO MP3 ZAKA IYA MANA MAGANA TA WATSAPP TA WANNAN NUMBER KAMAN HAKA 09064179602:

TURAMAKA KUMA MUSAKA A GROUP DINMU NA WHATSAPP:

NAKU HAR KULLU SULEIMAN ZIDANE KD NAKE CEWA ALLAH YANUNA MANA GOBE LAPIYA ::::

Pls kuringa comment inbakwayi zan dana post gaskiya nafara gajiya

MAZAN JIYA 4

Littafe Na Hudu

Part 24

Na abdul aziz Sani:

Typing: Suleiman Zidane Kd:


:::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::::

sihirinmu har guda daru tara da casa in da tara saura guda dai dai yarage mana kuma kasani idan mukayi amfani da cikon na dubun dayan mu bai sami nasara ba shi  ne har abada tsafinmu ya daina tasiri::::

Sa adda sarki maharaz yaji wannan  batu sai ya bushe dariya al amarin da yai matukar baiwa sarki dujalu mamaki kenan:

Maharaz ya dubi dujalu a fusace yace ai ni ban ga amfanin sihirin tsafi ba a wajenmu yanzu tunda gashi yanzu dayanu bai cinye wannan Yaki ba sbd haka in ka shirya ga cikon sihirin tsafi nan na dubu gareka:

Kafin sarki dujalu ya budi baki yace wani abu tuni sarki maharaz yayi nuni da Hannunsa izuwa kan dujalu:


Nan take wata irin farar wuta ta tafi izuwa kansa zata koneshi:

bisa dole ba don a son ransa ba yana kuka da ihu gami da takaici sarki dujalu ya tare wannan farar wuta da nasa tafin hannun sai gashi shima tasa farar wuta ta taho da gudu ta tari ta Sarki maharaz:

Wutar biyu na haduwa sai suka yi bindiga tamkar dutsen wuta ne ya fashe har sai da dajin gaba daya ya yi girgiza:

Sarki dujalu da Sarki maharaz kuwa sai gani aka yi sun sulale kasa sumammu:

A guje kowane bangare suka je suka dauko sarkinsu Sai da aka yayyafawa su sarki maharaz ruwa sannan suka farfado:

Koda kowannensu ya bude idanu sai suka mike tsaye zumbur a fusace: Nan take kowannensu ya zare takobinsa ya daga ta sama:

Page 139:

cikin hadin baki kowanensy ta kwarara uban ihu yana mai ba da umarnin a afkawa abkan gaba:

Nan take kuwa kowacce runduna ta zare makamanta aka ruga da azababben gudu cikin mugun nufi ana ihu da kururuwa:

Ana haduwa a tsakiya sai aka gwamutse kuma aka ruguntume da masifaffen yaki:

karar karafa ta cika dodon kunne aka shiga gididdibar sassan jiki jii ya rinka fallatsi da fauntsama asama yana yiwa mutane da kasa ado:

Ihun mazaje ya yawaita bisa sa kuwa sai sarki dujalu da inmal suka yi karo da juna:

Sarki maharaz da babban sadaukin nan na dakarun dujalu ma suka yi karo;


NIKUMA ZIDANE SAI NAYI KARO DA WADANDA BASU SAN YI MANA COMMMENT:

PAGE 139

Nan fa aka kacame da azababben yaki ya zamana cewa jaruman hudu suna kaiwa junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta :


CAIKO HAKIKA MASU KARIN MAGANA SUYI GASKIYA DA SUKA CE TASHIN HANKALI BA A SAMASA RANA KUMA WANDA BAI SAN YAKI BA SHI NE YAKE CEWA ALLAH YA KAWOSHI DOMIN MASIFARSA TA WACCE TUNANIN MAI TUNANI:


IN BA YAKI BA MENENE YAKE KAWO FATARA DA TALAUCI FARAT DAYA?

YAKI NE YAKE HADDASA YUNWA DA KISHIRWA KUMA SHI NE YAKE HADDASA CUTUTTAKA MARASA ADADI:

YAKI NE YAKE KONE ALBARKATUN KASA KUMA YA GURBATAR DA RUWAN SHA:

Kai jama;a wanan rana ita kanta masifa sai da tasan cewa ta jangwalo masifa domin sai da maza suka raina kansu domin sun san cewa suna karo da maza yan uwansu:

anfara wannan yaki Gumurzu tsakanin sarki dujalu da jarumi inmal duk su biyun suka gano cewa shayi ruwa ne ba abinci mai nauyi ba domin karfin yazo daya duk da cewa kuwa Sarki dujalu da hannun daya yake yakin amma sai gashi yazamewa inmal alakakai:

Shi dai sarki dujalu yana amfani da kwarewarsa gami da sanin makama kuma da tsohon kashi:

Page 141

zidane kd:

Shi kuwa inmal yana amfani ne da tsananin juriyarsa da nacinsa inbadon hakan ba datuni ssarki dujalu ya gama da shi::

Gashi dai karfin dantsensu yazo  daua gami da zafin namansu domin kowanensu yana iya kare harin kowa kuma yamai da martani to amma dai kowanensu hankalinsa a tashe yake domin sun san cewa idan aka jima anan wannan gumurzu a haaka komai zai iya faruwa:

Irin wannan matsala da Sarki dujalu da inmal suka fuskanta ce ta sami sarki maharaz da sadauki Himalu na bangare sarki dujalu don haka tsanani yakai tsanani tura takai tura kowa ya kuntata mafita kawai ake nema ta kowanen hali::


WANNAN SHINE ABINDA YAFARU A BAKIN TEKUN BAHAR SUFIYA A LOKACIN DA YAKIN KARSHE YA KACAME TSAKANIN RUDUNAR SARKI DUJALU DA RUNDUNAR SARKI MAHARAZ DUK SABODA KAYAN YAKIN MAZAN JIYA WADANDA SUKE KARKASHIN KOGIN BAHAR SUFIYA KUMA BABU WANDA YA SAN A INDA KAYAN YAKIN SUKE FACE WADANSU MUGAYEN AZZALUMAN ALJANU MASU TSANANIN KARFIN DANTSE MAZAUNA KARKASHIN TEKUN WA DANDA SUNE MASU GADINSU:

ADADIN ALJANUN YA NINKA ADADIN DAKARUN DA SUKA YI YAKIN A BAKIN TEKUN SAU ARBA;IN DON HAKA SUN ZUBA IDO SUGA WANNAN ZAI IYA SHIGOWA CIKIN KARKASHIN TEKUN YA HALLAKASU GABA DAYANSU YA IYA DAUKAR TAKOBIN SAIFUL LUJARA:

Page 141


zidane kd:


page 142

ANAN ZANDAKATA SAIKUMA IN ALLAH YA NUNA MANA GOBE KUYI HKR BAYAWA YAU DAN ALLAH COMMENT:::::

DOMIN SAMUN LITTAFAN YAKI NA SOYAYYA E:BOOK KAI HAR DAMA AUDIO MP3 ZAKA IYA MANA MAGANA TA WATSAPP TA WANNAN NUMBER KAMAN HAKA 09064179602:

TURAMAKA KUMA MUSAKA A GROUP DINMU NA WHATSAPP:

NAKU HAR KULLU SULEIMAN ZIDANE KD NAKE CEWA ALLAH YANUNA MANA GOBE LAPIYA ::::

MAzAN JIYa 4

Littafe na hudu


Part ::25

Typing:: Suleiman zidane kd:

whatsapp 09064179602:

::::::::::::::


DON HAKA SUN ZUBA IDO SUGA WANNAN ZAI IYA SHIGOWA CIKIN KARKASHIN TEKUN YA HALLAKASU GABA DAYANSU YA IYA DAUKAR TAKOBIN SAIFUL LUJARA:

Page 141


zidane kd:


page 142

::::::::::::::::::::::::::::::::


Acan dajin darul Hushushul maut kuwa aljani Raugatul Aguwanu Ya shafe sama da sa a tara yana bincike a cikin madubin tsafinsa domin ya tabbatar da gaskiyar al amarin da su boka sadusa suka zo masa da shi amma sai ya kasa ganin komai::


A karshe ma daya matsa bincike sai madubin tsafin nasa yayi bindiga ya tarwatse: Al amarin da matukar firgitashi ke nan ya sake sallamawa boka sadusa;


Da sassafe su boka sadusa suka farka daga barci a cikin wannan kogo na aljani Raugatul Aguwanu:


suna bude idanuwansu suka ga aljani Raugatul Aguwanu a zaune yagama shirin tafiya yana sanye da bakin sulke na yaki irin nasu na aljanu sannan yana rike da wani dogon mashi gami da garkuwa: 

 A wannan lokaci idan mutum ya kalli ajani Raugatul Aguwanu sai yayi zaton cewa shi kadai zai iya yakar duniyar gaba dayanta sbda tsananin  girmansa da kwarjinsa:

Nan take Raugatul Aguwanu ya dubi boka sadusa yace na gama dukkan binciken da zan yi kuma na gamsu da duk abinda kazo mini da shi sbda haka yanzu ni nagama shirin wannan tafiya ku kawai  nake jira:

Page 144:

Tabbas da na zauna yaki yazo yacini har gida gwara naje na tari yakin:


koda jin wannan batu sai boka sadusa ya kyalkyale da dariya mugunta sannan yace ai kuwa kayi wa kanka riga kafi domin da cin dare daya kumburin ciki gwara dayawa tunda a dade anayi sai gaskiya:

batare da bata wani lokaci ba su boka sadusa suka shiga harhada kayayyakinsu:

Suna cikwannan hali ne aljani Raugatul Aguwanu ya kyalara ido ya kalli Gimbiya Shalbirat ya ganta a cikin ainahin siffarta ta mutum nan take yaji ya kamu da tsananin sonta fiye da ko yaushe sannan sai takaici ya rufeshi ya fara tunani zuci yana mai aiyanawa aransa cewa idan fa yayyi wasa wannan karon shi kenan an rabashi da shalbirat:

Nan take ya dubi boka sadusa a fusace ya ce yakai wannan takadarin bok shin mun yi yarjejeniyane da kai akan cewa zaka fiddo Gimbiya shalbirat daga cikin kejin dana sata har ka dawo mata da ainahin siffarta?

Sadusa yadakawa Raugatul Aguwanu tsawa yace tsakanin ni da kai wanene yafi sanin abinda yadace?

Kada kasake yi mini shisshigi a cikin aiki domin duk abin da kaga nayi shi ne daidai kuma kauce masa zai janyo rugujewar dukka shirinmu::


Page 145

zidane kd:

koda jin wannan batu sai jikin aljani Raugatul Aguwanu yai sanyi ya sunkui da kansa kas sanna yace toni zan fita waje dommin na sami damar bude fuka fukaina gaba daya zan kwanta a kasa na rankwafa da zarar kunfito sai ku hau kaina ku zauna ni kuma na tashi daku sama mu kama tafiya:

ina mai tabbatar muku dacewa zan kaimu bakin tekun bahar sufiya a cikin abinda bai wuce sa a hudu ba amma fa bisa sharadi guda :

cikin mamaki boka sadusa yace wannen irin sharadi kenan?

Raugatul Aguwanu yace ai dama tunDa farko baku yi dani cewa cikin sansanin yaki zan kai ku ba: lallai zan sauka ne a can bayan sansanin nesa da shi inda ba za a hangomu ba sai dai mu hangosu:


koda jin wannan batu sai boka sadusa ya bushe da dariya yace haba ya kai Raugatul Aguwanu yaya kana matsayin sarkin sadaukai na aljanun duniya amma ka dinga jin tsoro?

Raugatul Aguwanu yace ai komai isar aljani a wannan zamani dole ne yaji tsoron sarki dujalu da sarki maharaz sbd sun kure sun kai kololuwa a matakin karfe na sihirin tsafi:

sadusa yace to shi kenan naji mazza kaje wajen ka jirau gamu nan fitowa::


page 146

Nan take Raugatul Aguwanu ya fice daga cikin kogo dutsen yana ai waigen gibiya shalbirat cikin wani irin kallo mai nuna tsantsar kaunarsa a gareta ita kuwa sai ta galla masa harara tana ai da masa martanin kallon na tsananin kiyayya yadda inda za a danne mata shi zata iya sa wuka ta yankashi  musamman idan ta tuno da yankan kaunar da yai mata ya rabata da kasarsu da iyayenta ya ajiyeta acikin keji kamar tuntsuwar tsawon shekaru goma sha tara:::

DA fitowar aljani Raugatul Aguwanu daga cikin kogon dutsen sai ya tsaya a tsakiyar babban filin dake gaban kogon ya rankwafa kasa yana mai bude fuka ffukansa cikin nishadi:


Girman fuka funkansa guda daya ya isa ya yiwa mutu dubu daya rumfa su tsira daga zafi rana da saukar uwan sama:

A dai dai wannna lokaci ne aljanin Raugatul Aguwanu yaji wata irin iska ai dan karen sanyi da dadi ta busa har izuwa cikin kunnensa nan take  ya lumshe idanu ya kama gyangyandi ::


Ashe wannan iska mai dadi da sanyi ba iska bace daga allah iska ce ta tsafi kuma bawani bane ya busata face aljani Radiyan wanda ya dauko Gimbiya Hursiya daga can birnin sarki dujalu  domin ya mayar da ita can sansanin yaki:

A wannan lokacin aljani Radiyan da Gimbiya Hursiya na can labe a cikin duhuwar bishiyoyi suna hango abinda ke faruwa ga aljani Raugatul Aguwanu:

koda suka gaya kama gyangyadi sai suka fito da sauri daga maboyarsu suka ruga da gudu izuwa inda yake:

Da zuwa suka daka tsalle suka hau kan farsa suka cigaba da gudu a knsa har suka hau kan kafadarsa sannan suka daka tsalle suka fada cikin kunnensa na hagu:

Nan fa suka ji kamar a cikin RIJIYA GABA DUBU aka jefasu::

sai da suka shafe rabin saa suna ta fadwa can cikin kunnen sannan suka iso karshen mai tsananin duhu:

Page 147

zidane kd::

sai da boka Radiyn ya haskake cikin kunnen da hasken wata sandar tasafi sannan suka iya ganin junansu::


Nan fa Gimbiya Hursiya ta dubi gabas da yamma kudu da area kuma yadubi sama dakasa ta gaba kamar a cikin gidan sarautarsu aka sata sbda tsanani girman cikin kunnen::


Raugatul Aguwanuna na cikin yin wanna gyangyandi ne yaji kuma ana sosa masa kunnen: 

sbda tsananin dadi da yaji sai ya dada rufe idanunwansa yayi lamo kamar bashi da rai ko kadan  ma bai yi tunanin abinda ke sosa masa kunnen ba::

a zotonsa waannan iskar mai busowa da karfi ce tke shiga cikin kunnen nasa::

Page 148

Yana cikin wannan hali ne yaji an daka masa tsawa:

A firgice ya bude idaninsa ya mike zaune saiyag  

a she su boka sadusa ne tsaye a gabansa: 

sadusa ya dubeshi yace yaya kai da zamuyi doguwar tafiya tare da kai yanzu kuma zaka buge da gyan gyadi?

Raugatul Aguwanu yace ai dole ne na yi barci: shin baka jin daddadar iskar da take kadawa bane?


Sadusa yayi tsaki sannan yace kaidai ka cika shirirta da shirme::

to ai sai ka yi shiru gamu mun fito tafiya zamuyi:

nan take aljani Raugatul Aguwanu ya dada rankwafawa kasa boka sadusa Halyal Da Gimbiya Shalbirat suka hau kan gadon bayansa suka zauna:


zamansu ke da wuya sau ya bude fuka fukansa ya luluka da su izuwa can kololuwar sama ya kama tsala gudu yana keta giza gizai tamkar gudun taurariwa mai wutsiya::


A Dai dai wannan lokaci ne aljani Raugatul Aguwanu yaji dan motsi a cikin kunnensa har  ya daga dan yatsansa guda zai cusa a cikin kunnen yaji an fara masa susa::


Page 149

zidane kd::

Dan karen dadi daya ji ne yasa ya fasa sanya dan yatsan nasa ya saki jikinsa cikin kwanciyar hankali ya cigaba da tsala gudu:

a Wannna lokacin gimbiya Shalbirat ta kamu da tsananin farin ciki takama murmushi: 

boka sadusa ya dubeya cikin mamaki yace kekuwa menene ya saki farin ciki haka har kike ta murmushi da yake baki?

Shalbirat tace gaba ai dolene na kasance a cikin farin ciki tunda rabona da gannin fili haka ba a cikin keji ba yau shekara goma sha tara kenan:


Da jin haka sai tausayi ya kama sadusa da Halyal har idanunsu suka ciko da kwallah:


A cikin kunnen aljani Raugatul Aguwanu kuwa boka radiyan ya dubi Gimbiya Hursiya ya ce bari na karasa miki Labarin da dan uwanki sarki dujalu bai karasa miki ba hakan zai debe miki kewa kafin mu karasa bakin kogin bahar sufiya:


Cikin tsananin mamaki Hursiya ta dubi boka Radiyan ba tare da ta iya furta masa komai ba:

boka Radinyan yayi murmushi yace kada ki yi mamaki akan lamarina domin na wucce dukkan tunaninki na san abinda baki sani ba zaki gasgata hakan idan kiyi la akari da abubuwan da suka  faru tsakaninmu tunda haduwarmu kawo izuwa yanzu da muke cikin kunnen aljani Raugatul Aguwanu::


page 150


gimbiya Hursiya ta gyada kai kawai cikin tana sauraron boka Radiyan::

Shi kuma ya cigaba da dora mata Labarin Kamar Haka:::::


*    *     *


LOKACIN da jarumi Shadaddu ya cigaba da tafiya bisa wannan tsutsun tafi ga Mashin Galilul HarAs daure a Gadon bayansa kuma gashi a cikin gagarumar shigar yakin sai tsuntsun ya vigaba da keta giza gizai a sararin samaniya ba kakkautawa:::


NIMA SULEIMAN ZIDANE GOBE ZAN CIGABA DA KAWO MUKU BAKAUKKATAWA AMMA IDAN KUNA COMMENT:::

WANNAN KENAN ::

WHATSAPP 09064179602::

DOMIN SAMUN LITTAFAN YAKI NA SOYAYYA E:BOOK KAI HAR DAMA AUDIO MP3 ZAKA IYA MANA MAGANA TA WATSAPP TA WANNAN NUMBER KAMAN HAKA 09064179602:

TURAMAKA KUMA MUSAKA A GROUP DINMU NA WHATSAPP:

NAKU HAR KULLU SULEIMAN ZIDANE KD NAKE CEWA ALLAH YANUNA MANA GOBE LAPIYA :::Aslm yan uwa ga page dinnmu sai kayi kokari shiga domin samun Littafe Kala Kala cikin blue dinnan Na kasa..


Duniyar Masoya Litattafan yaki only


Home of Littafan Yaki  And Hausa Novels


Matan Arewa Special Group


Zauren Muslims

MAzAN JIYa 4

Littafe na hudu


Part ::26

Typing:: Suleiman zidane kd:

whatsapp 09064179602:

::::::::::::::


LOKACIN da jarumi Shadaddu ya cigaba da tafiya bisa wannan tsutsun tafi ga Mashin Galilul HarAs daure a Gadon bayansa kuma gashi a cikin gagarumar shigar yakin sai tsuntsun ya vigaba da keta giza gizai a sararin samaniya ba kakkautawa:::


Sai da suka shafe sa biyar da rabi suna tafiya sannan tsuntsun ya sauko kasa kasa da kansa ashe wani babban birnin suka tunkaro a gabansu:


koda ya rage bai fi zira i goa ba tsakaninsa da birnin sai tsutsun ya sauko kasa:

Shadaddu ya sauko daaga kan tsutsun:

saukarsa ke da wuya sai tsuntsun ya rikede ya zama dan karai kua ya tashi ya dira a kafadar Shadaddu:

Faruwar hakan ke da wuya sai shadaddu ya kunna kai izuwa kofar wannan birni ba tare da shakkar komai ba::


Page 151


da isarsa bakin kofar garin ya iske masu gadi wadansu dakaru samudawan karti kimanin su arba in a tsaitsaye cikin shigar Yaki:

Ko kallonsu shaddadu bai yi ba ya nufi bakin kofar garin wacce take a rufe: 

suma dakarun sai suka yi kamar basu ganshi ba domin ko kallonsa basuyi ba::

Shima sai yaki yi musu magana yaje ya kwankwasa kofar domin ya bude masa duk da cewa yaga daya daga cikin masu gadin a zaune daf da bakin kofar bisa wata kujera rike da kuba:

Shadaddu ya kwnkwakasa kofar har sau uku amma shiru ba a bude kofar ba:

kawai sai yaji masu gadin sun kama yi masa dariya::

Daya daga cikinsu ya dubeshi ya ce yakai wannan sakaran bako shin baka da da a ne ko kuwa ba a koya maka ladabi bane a gidanku? Idan haka Halayyarka take a can garinku to mu nan ba haka halayayarka take  a can garinku to mu nan ba haka bane:

Amma idan kai kurma ne sai kagaya mana:


Kawai sai Shaddadu Ya kalli mai maganar yai masa murumshi ba tare da ya maida masa da martanin maganar ba::

Kawai sai ya ja da baya kadan ya daga kafarsa ya doki kofar garin wacce t kasance mai kauri da nauyi gaske ta zallar bakin karfe:

Nan take kofar ta Jijjige fada ciki::


Page 152

Suleiman Zidane Kd:


Al amarin da yai matukar Firgita dakarun ke nan Suka zazzare mnakamansu amma kuma sai suka kasa afkawa shadaddu sakamakon ganin wannan gagarumar jarumtaka da yayi:


Shadaddu ya waigo yadubi dakarun yayi musu murmushi a karo na biyu sannan ya juya ya shige izuwa cikin birnin:

Nan fa dakarun nan suka kama duru duru suka rasa abinda zasu yi tsakanin subi wannan bakon saurayi su yakeshi ko kuma su kai rahotonsa izuwa ga sarauniyarsu?

Nan dai suka yanke shawarar daya daga cikinsu ya ruga izuwa fada ya kai labari:

Nan take kuwa aka bi wannna shawara:

Lokacin da Shadaddu ya kunnan kai izuwa cikin wannan birnin sai ya zama abin kallo duk inda ya ratsa sai ya ga mutane har fitowa suke daga cikin gidajensu suna binsa  a baya musamman mata domin dimaucewa suka rinka yi;


Abin da yai matukar baiwa shadaddu damamaki kenan domin shi bai ga abin kallo ba a tare da shi:


ABINDA SHADADDU BAI FAHIMTA BA SHI NE TSANANIN KYAWUNSA DA KWARJININSA NE YASA AKE KALLONSA:

koda yaga kallon da ake yi masa yayi  yawa ku� Ma jama a dada karuwa suke ana binsa sai ya juya ya kwarara uban ihu yayi kamar zai zare takobinsa:

Page 153

Nan fa jama a suka tarwatse cikin firgita suka kama gudu:

Kafin cikar dakika biyar babu kowa akan hanyar:


Shadaddu yai dariya yace ashe ma du matsoratane a garin:


kawai sai ya cigaba da tafiya: burinsa kawai shine yaga kasuwa ko inda ake siyar da abinci domin yyunwa ta fara damunsa gashi bai taho da wani abinci ba  a cikin jakar guzurinsa sai taarin dirhami mai yawan gaske:

Haka dai ya cigaba da tafiya yana kutsawa ta cikin lunguna da sako sako na garin amma kuma bai ga mutane sun daina kallonsa ba sai dai basa biyoshi a baya sakamakon ganin rashin annuri akab fusarsa kai da gani ka san cewa mutane suna shakkarsa sbda ganin irin kirarsa ta manyan sadaukai::

Yana cikin dube dube be ya hango gida wanda aka rubutu a jikin saman kofarsa kamar haka GIDAN ABINCI:

koda ganin wannan rubutu sai murna ta kama Shaddadu ya kunna kai izuwa cikin gidan::

TO INIMA SAI NA BI BAYANSA ZIDANE KD::

yana shiga ya iske mutane da yawa acikin zazzaune bisa kujeru a karkashin tebura suna cin abinci kala kala:

lokacin guda kowa ya dago kai ya kalleshi sannan aka kawar  da kai aka cigaba da cin abincin babu wnda ya sake dubansa::


Page 153


Al amarin da ya daurewa Shadaddu kai shine gaba dayan mutanen dake cikin gidan abinci mazas ne kuma karti majiya karfi ababan kwatance:

mace guda daya ce jal a cikin gidan kua itace mai bayar da abinci a can gefe daya bisa wani dogon tebur mai dauke da tukwanen abinci kianin guda goa::


Shadaddu yasake yin nazarin kartin dake cikin gidan yaga kowannensu yana da siffa irin ta ma yaki duk dacewar babu makamai  a jikinsu ::

nantake jikin shaddadu ya bashin cewa akwai tuggun da ake son shirya masa amma sai ya basar ya nuna baya tunanin komai:


 kai tsaye ya nufi inda mai bayar da abinci take::

da zuwa sai ya bude jakarsa ya dauko dirhami goma ya ajiye a  gabanta sannan yace nuna mata irin kalar abinci da yakeso::


KAI KUYI HAKURI WLH YAUSAI AHANKALI NE SHIYASA:::

WHATSAPP 09064179602::

DOMIN SAMUN LITTAFAN YAKI NA SOYAYYA E:BOOK KAI HAR DAMA AUDIO MP3 ZAKA IYA MANA MAGANA TA WATSAPP TA WANNAN NUMBER KAMAN HAKA 09064179602:

TURAMAKA KUMA MUSAKA A GROUP DINMU NA WHATSAPP:

NAKU HAR KULLU SULEIMAN ZIDANE KD NAKE CEWA ALLAH YANUNA MANA GOBE LAPIYA :::INKAKARANTA KAYI SHARE IZUWA WASU GROUP PLS::�

0 Response to "MAZA JIYA Hausa Novel"

Post a Comment