-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

SARKIN SARAKAI Hausa Novel

SARKIN SARAKAI Hausa Novel

 SARKIN SARAKAI

Littafi Na Daya (1)

Complete 

.


Ina yima daukacin musulmai murnan zuwan Azumin watan Ramadan, Allah ya bamu Alkhairan cikinsa

.

Marubucin littafin

Abdul Aziz Sani M/Gini

AA Misau Ke Magana

.

Labari ya isowa AA Misau Cewa..

Suleiman zidane kd 

A WANI ZAMANI can baya mai tsawo da ya shude anyi wani mashahurin sarki a birnin misra mai suna SAHIBUL HAIRI

Shidai wannan sarki ba a tabayin talakan sarki ba kamarsa a duniya saboda yawan kyautarsa da taimakon talakawa

akarshe da talauci ya isheshi sai ya shirya ya tafi wajen wani boka AWANI DAJI WAI shi HAZARIL DALFUR 

a yammacin misra Daga cikin birnin misra zuwa wurin wannan boka tafiya ce ta s'a biyu kacal sarki Sahibul hairi

bai tafi wannan daji ba sai da dare ya raba kuma saida ya saci jiki yayi bad da kama ya tafi a kasa ba tare da ya hau doki ba ko rakumi

Bayan tafiyar sa'a biyu ne dai dai ya iso kofar gidan boka HADIMUL ASUR

Wanda aka ginashi da zallan itatuwa bisa kan wani godon dutse faffada mai tsawon gaske

lokacin da sarki Sahibul hairi yazo gaban dutsen sai ya tsaya yana tunanin hanyar da zaibi ya hau kan dutsen ba zato ba tsammani sai yaga boka Hadimul Asur ya bayyana a gabansa yana mai murmushi

hadimul asur yayi sujjada ga sarki Sahibul hairi yace Lale marhaban da SARKIN SARAKAI na duniya baki daya kaine sarkin da zaiyi arziki da daukakar da ba a taba yin kamar su ba nan gaba idan har ka sami nasarar samo abubuwan da zan gaya maka yanzu

muje zuwa cikin turakata domin mu zanta a tsanake kafin sarki sahibul hairi yace wani abu tuni boka Hadimun Asur ya dafa kafadarsa take suka bace bat sai gashi sun

bayyana a cikin turakar boka hadimul asur Wadda akayi mata ado da fatun manyan dabbobin dawa da kwarangwal din kawunansu

nan take hadimul asur ya yiwa sarki nuni da wata shimfida mai taushi shi kuwa sai yaje ya zauna a kai zamansa keda wuya saiga wata zabgegiyar budurwa ta fito daga cikin

wani daki dauke da tambulan na ruwan inibi da kofin zinare a hannu

tun da sarki sahibul hairi yazo duniya bai taba ganin budurwa mai kuruciya da kyau kamarta ba duk da cewa sarki sahibul hairi yayi alkawarin cewa ba zai taba yin aure ba saida yaji yayi sha awar wannan budurwa

budurwar tazo gaban sarki ta tsugunna sannan ta zuba ruwan inibi a cikin kofin zinare ta mikawa sarki ya karba kofin yana mai kura mata ido da murmushi

ita kuwa saita sunkuyar da kanta ta fice daga cikin turakar fitarta keda wuya sai sarki ya bude baki da nufin yayi magana amma sai boka hadimul asur yai masa nuni da yayi shiru

yace dashi wannan 'yata ce ita kadai gareni a duniya kuma babu abinda na ke so sama da ita ka bar batunta yanzu zamuyi shi nan gaba

ya kai wannan sarki mai daraja kayi sani cewa tuni na san abindake tafe dakai kuma kamar yadda na gaya maka cewa bukata zata biya idan harka sami nasarar samo abinda na umarceka da samowa

Sa'adda boka hadimul asur yazo nan a zancensa sai sarki ya dubeshi cikin kokwanto da mamaki yace yakai wannan boka hakika nayi mamakin jin yadda kake bayani tamkar kasan sirrin xuciyata

amma duk da haka ina so ka fada mini ainihin bukatar da nazo da ita gareka domin na kara samun natsuwa dakai

koda jin wannan batu sai boka hadimul Asur ya tuntsure da dariya sannan yace yakai wannan sarki na gani cewa kwanaki bakwai da suka shude

sarakai bakwai sun aiko maka da wasika A cikin wasikar sunyi bayanin cewa tunda ka zamo almajiri zasu rinka taimaka da sadaka domin kada ka dinga zubar da kimar sarakai a duniya kuma sunyi maka gorin baka da lafiya tunda baka da aure

lokacin da ka sami wannan sako saibakin ciki ya turnuke ka har ka shiga cikin turakarka kayita shara kuka a boye ba wanda ya sani bayan kayi kukanka ka gaji ne kayi rantsuwa da girman karagar mulkinka cewa 

saikafi dukkan sarakunan duniya mulki dukiya da mata to ka sani cewa idan har kana so ka sami wannan matsayi dolene ka nemo wadansu 'yan mata guda uku ka aura mace ta farko utace 'ya ga wata mace wadda duk duniya babu mai iliminta yanzu ita dai wannan mata tana jin yare guda dari ba daya haka kuma ta kasance malama a cikin addinai guda dari ba daya shekarunta dari ba daya cif-cif kuma ta boye kanta tare da 'yarta a inda babu wanda ya sani a halin yanzu in banda wannan 'ya tata duk duniya babu mai iliminta

mace ta biyu babu wanda yafi mahaifinta yawo a duniya mahaifinta bai mutuba saida ya ziyarci kasashe dari tara da casa'in da tara inda ya cika dubu da ya sami matsayin da kake son samu yanxu 'yar wannan mutum yanzu haka ta ziyarci kasashe dari takwas da sittin a cikin shekaru bayar kacal baisa taimakon wani Aljani waishi KALBURA a matsayin abin hawanta

wannan budurwa ta lashi takobin cewa saita ziyarci kasashe dubu dan cika burin mahaifinta wanda ajali ya hanashi cikawa duk kasar data ziyarta saita debo irin kasar da aka gina gidan farko a nahiyar idan ta kammala tara kasar guda dubu shine zata sami wannan daukakar

budurwata uku itace 'yaga wani mutum wanda yafi kowa sanin tarihin sarakunan duniya da mulkinsu itama wannan budurwa mahaifinta ya mutu kuma ta gajeshi A halin ynx itace kadai tasan adadin sarakan duniya da tarihin mulkinsu tun daga farko har karshe

wannan budurwa kwakwalwarta kamar littafi yake domin tarihin a rubuce yake a kanta zata iya baka lbrn shekara dari baya......

YAKAI WANNAN SARKI kayi sani cewa idan har kana son kafi dukkanin sarakunan duniya mulki dukiya dolene ka nemo wadannan yan mata uku ka auresu

sa adda boka Hadimun Asur yazo nan a zancensa sai yayi shiru ya kurawa sarki idanuwa kawai cikin tsananin damuwa sarki Sahibul hairi yace yanzu a ina zan ga wadannan yan mata kuma waye zai iya samo minsu

boka Hadimul Asur yace tambaya ta farko tafi karfina domin banida amsarta amma tambaya ta biyu itace a halin yanzu duk duniya babu wanda zai iya samo ma wadannan yan mata face wani jarumi saurayi kuma mafarauci wanda ake kira SADAUKI AWAISU

sadauki awaisu na zaune a can nahiyar kasar Hindu a cikin wani birni da ake kira HALRALI awaisu ya kasance matsafin gaske kuma yana da wani Aljani wanda ake kira SARMUDA

aljani sarmuda ya kasance matashi mai karfin gaske kuma a cuk cikin jama ar aljanun duniya babu kamar sa a fagen karfin gudu da sauri yayin tafiya a sararin sama Aljani KALBURA ne kadai ke iya yin rabin tafiyar sa a gudu

sadauki Awaisu bazai taba yarda ya samo maka wadannan 'yan mata uku ba face ka samo masa 'yarsa guda daya wata karamar yarinya yar shekara bakwai ALFILA 

WACCE aka saceta a shekaru uku da suka gabata babu irin neman da sadauki awaisu bai yiwa wannan ya tasa ba amma ya rasa inda take da yayi bincike a cikin tsafinsa sai ya gano cewa yarinyar na can hannun wani mashahurin bokan Aljanu ne a cikin wani gida dake tsakiyar tsibirin tekun BAHAR ZAILUS

sunan wannan boka SHAMZUBUL AZWAS ba komai bane yasa bokan ya sace Alfila ba sai don ya kwashe sirrikan tsafin dake jikinta guda dari tara domin shi yana da guda dari nasa da kansa idan ya hada da wannan sirrika zai zamo babu wani matsafi kamarsa a doron kasa 

Shamzubul Azwas ba zai iya kwashe wadannan sirrikan tsafin ba daga jikin Alfila har sai izuwa tsawon shekara biyar A halin yanzu saura shekara biyu kawai ya kammala debe sirrikan tsafin su kuwa sirrikan tsafin ainihinsu na Sadauki awaisu ne duk duniya babu mai irinsu face shi

bayan rasuwar mahaifiyar Alfila da shekara daya sadauki awaisu ya zuba wadannan sirrikan tsafi guda dari tara a cikin jikin Alfila domin burinsa a duniya shine ta gajeshi a fagen tsafi

lokacin da sadauki awaisu ya gano inda aka boye masa 'yarsa sai yayi shiri ya hau kan aljani Sarmula suka durfafi tsuburin bahar zallus daga birnin Hindu zuwa bahar zallus tafiyace ta shekara goma sha daya akan rakumi ko doki amma cikin wata uku aljani sarmuda ya isa can

koda suka sauka a kofar gidan boka shamzubul azwas sai suka iske cewa gidan an ginashi ne da zallan bakin karfe kuma bashi da kofa ko taga wacce za a iya bi a shiga cikinta kuma koda mutun ya shiga gidan ba zai iya kashe dakarun Aljanun dake ciki ba guda dubu dari wadanda suka kasance manyan zakwakuran mayaka masutaurin kai da dakakkiyar zuciya

nan da nan sadauki awaisu da aljani sarmuda sukayi ta kokarin shiga wannan gida ta hanyar amfani da karfin sihiri da kyar suka gano wata kofa guda daya wacce akayita da karfen lu u lu u nan take suka fara kokarin bude ta da karfin tsiya domin shiga

amma sai abu ya faskara saida suka kwana uku a wajan suna saran kofar da makamai iri iri amma kofar taki buduwa

tabbas inda kofar ta bude to sai sunsami nasarar shiga gidan kuma sai sun kashe dukkan dakarun ciki sun hallaka boka shamzubul azwas sannan su dauki Yarinya alfila

Yakai wannan sarki kayi sani cewa bincike ya nuna mini cewa akwai wani gatari guda daya a duniya wanda zai iya sare wannan kofa ta gidan boka shamzubul azwas shidai wannan gatari ya kasance mai girma da nauyin tsiya domin sai karti sittin sun taru suke iya daga shi sama kuma anyi shine da zallan lu'u lu'u bincike ya nuna mini cewa kaikadaine mutumin da zai iya sarrafa wannan gatari sbd sadaukantakarka tafi ta kowa a wannan zamani

A yanzu haka wannan gatari na can a ajiye a cikin fadar sarki BARUSA na birnin ASKANDARIYYA cikin mummunan tsaro Ainihin wannan gatari na sarkin farko ne na kasar don kowanne sarki zuwa yake ya tarar dashi a matsayin abin gado kai sbd ganin darajar gatarin ma har takai cewa mutanen kasar sun camfashi a matsayin indai yana nan ajiye a cikin gidan sarautarsu to har abada ba za a cisu da yaki ba bisa wannan dalili ne kullum dare da rana aka zuba dakaru dubu uku suke gadinsa

wadannan dakaru dubu uku sun kasance karfafa mayakan kwarai wadanda ake takama dasu a birnin Askandariyya yakai wannan sarki ya zama wajibi a gareka kayi shirin yaki ka tafi izuwa birnin domin ka dakko wannan gatari na sihiri ka dawo gareni sannan na kimtsaka ka tafi izuwa fadar boka shamzubul azwas don ka dauki Alfila yar sadauki awaisu idan ka daukota saikazo da ita nan mu ajiyeta har sai yaje ya samo mana wadannan yan mata uku wadanda sune bukataka zata biya

sa adda boka hadimul Asur yazo nan a zancensa sai sarki sahibul hairi yace to yanzu idan sadauki Awaisu yazo yaga 'yarsa baka tunanin cewa zai iya karbeta da karfin tsiya ba tare da ya biya muna bukatarmu ba?


KODA jin wannan batu sai boka Hadimun asur ya tuntsure da dariya sannan yace ai kowa a gidansa sarki ne ina tabbatar maka da cewa indai kazo da Alfila cikin wannan gida nawa babu wanda ya isa ya tafi da ita face da yarda ta

da wannan kalmomi nake maka sallama dan haka sai ka tafi kayi shirin zuwa fadar sarki Barusa na birnin Askandariya don dauko gatarin sihiri zan kasance mai sauraronka a nan

kuma ina yi maka tuni da cewa shima wannan gatarin sihiri karka barshi a can fadar boka Shamzubul azwas lallai ka taho da shi nan gareni tare da yarinya Alfila

koda gama fadin wannan batu sai boka hadimul asur ya sake dafa kafadar sarki sahibul hairi nan take sarki sahibul hairi ya tsinci kansa a wajen gidan boka hadimul asur kuma a kasan dogon dutsen nan kawai sai sarki sahibul hairi ya juya ya tafi ya nufi cikin birnin misra yana mai tafiya da sauri don ya isa gida kafin fitowar Alfijir

kashe gari da sassafe sarki sahibul hairi ya tura aka kirawo masa dukkanin fadawaLabarai farko sunyi tsammanin cewa wani abu zai nema a hannunsu don haka sai wadannsu suka noke suka ki zuwa da wuri suna karyar fadin cewa suna nan tafe

koda ganin haka sai sarki ya fusata yace a gaya musu cewa duk wanda baizo ba a yanzu a bakacin ransa koda jin haka sai yan majalisar suka rude nan da nan suka iso fadar suna masu rawar jiki bayan sun hallara sai kowa ya nutsu yayi shiru baka jin motsin komai a dakin face sautin numfashi

daga can sai sarki sahibul hairi ya mike tsaye fuskarsa a murtuke babu alamar fara a Al amarin da ya kara firgita fadawan ke nan gaba daya suka sunkuyar da kawunansu kasa don gudun fushinsa sarki yace dasu

''yaku yan majalisa kuyi sani cewa raina ya baci bisa halaiyarku ta kina da guduna sbd halin da na shiga na babu wannan ya nuna min cewa babu soyayyar gaskiya a tsakanina daku kuma kuna tsoron kada ku talauce ne shiyasa kuke guduna? To ku sani cewa daga yau bana bukatarkomai daga hannun ku kuma nayi muku Alkawari cewa ba zan sake neman komai ba a wajenku

kuyi sani cewa ba wani abu bane yasa na taraku a nan ba sai don na gaya muku cewa zan tafi yaki izuwa birnin Askandariyya domin dauko gatarin nan na sihiri wanda suka baiwa kyakkyawan tsaro zanyi amfani da wannan gatari ne don kawo karshen wannan talauci da nake famda dashi kunga kuwa idan na rabu da talauci kuma kun huta da fargabar komai

kuyi sani cewa bayan na sami wannan gatarin kuma zan wuce izuwa tsibirin zallus inda boka shamzubul azwas yake domin na dauko wata karamar yarinya wacce ya saceta shekaru uku da suka gabata wadda ta kasance yaga babban matsafi sadauki Awasisu

a kalla zan sami shekara guda kafin na kammala wannan tafiya na dawo sabo da haka yanzu ina son ku zabi wanda zai rike mini kasa daga cikinku kafin na dawo koda jin haka sai gaba dayan suka kidime suka haukace nace kowa na cewa shine zai rike kasar shikuwa sarki sahibul hairi sai yai shiru ya zuba musu idanu kawai yana nazarinsu ya fuskanci cewa gaba dayansu babu abin yarda a gareshi

yayi da sarki yaga sun kaure da gardama sai ya daka musu tsawa nan take suka kame kamar gumaka kowa ya yi tsit sarki ya kira wani barde dake can kofar shigowa dakin da suke ciki barden ya rugo da gudu ya zube kasa gabansa sarki yace da barden maza kaje dakin ajiya ka debo mini akwatunan karfe iya adadin fadawan nan nawa

barden ya mike da sauri yace an gama ranka ya dade koda ficewar barden sai cikin yan majalisar nan ya duri ruwa domin a zatonda suke shi ne sarki zaisa su a cikin akwatunan ne ya kulle domin akwatunan sn kasance darma darma baisa wannan daliline jikinsu ya kama kyarma gaba daya kamar ace kyat su fita da gudu

barden ya dinga shigowa da akwatunan daya bayan daya yana saukewa da jerawa a waje guda har saida ya gama tara guda taran koda ya gama ajiye akwatunan sai sarki ya dubi yan majalisar yace gaba dayanku ku fita su rufe kofar kuma su tsaya a bakin kofar cikin rawar jiki suka bi umarni fitarsu keda wuya sai sarki ya dauki kwagirinsa na sarauta ya saka a cikin daya daga cikin akwatunan bayan ya bame akwatun saiya yiwa yan majalisar nan izini su shigo cikin hanzari suka shigo suka tsaitsaya a jere waje guda sarki ya dubesu a natse yace 

yaku yan majalisa kuyi sani cewa kwagirin sarautata na cikin daya daga cikin akwatunan nan guda tara daya bayan daya zakuzo ku zabi akwati dai dai ku budeta wanda ya dauko kwagirin sarautata shine zai rike mun kasata har na dawo daga doguwar tafiya

koda jin wannan batu sai gabadayansu hankalinsu ya dugunzuma wazirin Akiyanu ya dubi sarki sahibul hairi yace ya shugabana ni a tunanina bai kamata ayi haka ba ni da nake a matsayin wazirinka nine na dace na rike maka kasa

koda jin haka sai sarki ya yi murmushi yace na sani cewa ka dace ka wakilceni to amma fa ka sani cewa ban taba yin tafiya irin wannan ba kuma gaba dayanku babu wanda hankalina ya kwanta da shi don haka kawai sa'a naga mai rabo dole ne abi wannan tsari nawa....

KAFIN WAZIRI ya kara cewa wani abu tuni Sarki sahibul hairi ya dubi yan majalisar na farko ya umarceshi da yaje kan akwatunan ya zaba hannayensa na karkarwa sai ya tsaya ya kasa zabar akwatin da zai bude sai da sarki ya daka masa tsawa sannan yaje ya bude akwatin farko

aikuwa yana budewa sai yaga wayan babu komai ciki koda ganin haka sai kwalla ta ciko idanun dan majalisar ya fara kukan zuci don takaicin rashin samun nasara daya bayan daya suka rinka bude akwatunan har akazo kan mutum na tara shine wanda na kashe wanda ake kira AMINUL HAS

Aminul has ya kasance shine galadiman sarki kuma duk a cikin yan majalisar shine wanda baya gajiya da yiwa sarki hidima duk sa adda sarki ya aika masa da bukatar abinci ko sutura take yake aiko masa har saida takai cewa sarki sahibul hairi ya kure Aminul has ya talautar dashi duk ya siyar da kadarorinsa

wani lokacin ma idan aka turo da bukatar sarki sai yayi rance sannan ya aika wajan yaransa da suke tafiya fatauci a kawo masa kudi ya biya bashin gaba daya yan majalisar mutum takwas babu wanda ya sami nasarar dauko kwagirin sarautar kuma duk su takwas din babu wanda bai zub da hawaye ba da fargaba lokacin da ya zo bude akwatinshi

Shikuwa Aminul has cikin nutsuwa ba da fargabar komai ba ya zo ya bude akwatin ta karshe wadda ba a bude ba bisa mamaki sai shima yaga babu komai a cikin akwatin

yan majalisar suka dubi sarki sahibul hairi waziri Akiyanu yace ranka ya dade yazaka yaudaremu kace akwai kwagirinka a cikin daya daga cikin akwatunan nan alhali babu?

Koda jin haka sai sarki sahibul hairi ya bushe da dariya sannan yace hakika na yaudareku amma ba dan komai nayi hakaba sai don na gane wanda ke kaunata a tsakaninku gaba dayanku nan kun sani cewa wannan tafiya da zanyi mai hadarin gaske ce kuma na tabbata cewa duk kuna ganin cewa idan natafi ba zan dawo da raina ba don haka duk wanda ya hau kan karagata ya haukenan

gaba dayanku takwas din nan babu wanda baiyi kukan takaici ba a nan da fargabar rashin samun nasara face Galadima kuma a cikinku shi kadai ne bai gajiya da bukatata lallai yanzu na dad gamsuwa cewa Galadima masoyina neh na kwarai tunda baya harin kujerata

batun kwagirin sarautata kuwa hakika da farko na sanya shi a cikin akwatin tsakiya amma kafin ku shigo sai na sauya shawara na dauke abina sakamakon wannan hikimar da tazo cikin gaggawa koda gama fadin haka sai sarki sahibul hairi ya fiddo kwagirin sarautarsa daga cikin alkyabbarsa ya baiwa aminul has ya karba sannan yace dashi

daga yau kaine sarkin misra kafin na dawo daga tafiyata ko shakka babu zan dawo kuma na umarceka da kayi adalci a cikin harkokin mulki kamar yadda na sabayi

nan take sarki ya sallamesu gaba daya suka tafi cikin bakin ciki galadima ne kadai ya zamo a cikin dumbin farin ciki mara misaltuwa domin dama yana da wani babban buri a zuciyarsa wanda ba zai taba cika shiba face ya zama sarkin misra

bayan sarki ya sallami yan majalisa sai yasa aka shirya masa doki da guzuri amma sai bawan dake wannan aiki ya sanar dashi cewa guzurin fa ba zai isheshi ba har ya isa birnin Askandariyya

kafin bawan ya gama rufe bakinsa saiga manzo daga gidan Galadima janye da wata doguwar taguwa akan taguwar kuwa guzurin tafiya ne mai yawa ga sarki Sahibul hairi

yayinda sarki yaga wannan sako sai ya cika da tsananin farin ciki kuma yaji cewa kaunar Aminul has ta karu a zuciyarsa ainun nan take yayi alkawari a zuciyarsa cewa randa duk bukatarsa ta biya sai ya maishe da galadima waziri kuma zai bashi dukiya mai tarin yawa da bazasu iya cinyeta ba har zuwa karshen rayuwarsu

bayan an gama kimtsa taguwar sarki da guzurinsa sai ya umarci wani bakin bawa nasa mai suna HALUF daya shirya suyi wannan tafiya tare cikin murna da zumudi Haluf yaje ya kimtsa koda fitowarsa sai ya iske yayi shigar yaki mai tsananin kwarjini da ban tsoro gaba daya shigar bakaken kaya sarki yayi sannan ya sanya bakin sulke da bakaken takalma dogaye na fata iya gwuiwa hatta kufen takobinsa da garkuwarsa ma bakakene fuskarsa ya rufeta ruf da bakin rawani ba aganin komai face idanunsa nan take sarki da haluf suka fito daga cikin gida 

sarki ya hau taguwa shi kuwa bawa haluf yahau doki ba tare da bata lokaci ba suka kama hanya suka bar cikin birnin misra A wannan lokaci kuwa rana na gaf da faduwa domin gari ya soma duhu haka dai sarki da bawa haluf sukaci gaba da tafiya harsuka nausa cikin dokar daji

basu gusheba suna tafiya har saida sukaga duhu yayi sosai sannan suka yada zango a bakin wata bishiyar dabino cikin gaggawa bawa haluf ya kafawa sarki tanti sannan yayi masa shimfida a cikin tantin ya kunna masa fitila

koda gama wannan shiri sai ya mike tsaye da nufin ya fita daga cikin tantin sarki Sahibul hairi ya kira sunansa yana mai cewa 

Ina zaka ya Haluf??

Bawa haluf yace ya shugabana ai zan fita wajan tantin nanne natsaya don na tabbatar da tsaro kada wani mugun abu ya sumamemu....

Zan dakata anan saikuma Allah yakaimu gobe zamu cigaba

Admin AA Misau Ke Magana

Zidane kd 

SARKIN SARAKAI 1

PART B. 

TYPE AA. MISAU.

POST SULEIMAN ZIDANE KID. 

WHAT'S APP 09064179602


KODA jin wannan batu sai boka Hadimun asur ya tuntsure da dariya sannan yace ai kowa a gidansa sarki ne ina tabbatar maka da cewa indai kazo da Alfila cikin wannan gida nawa babu wanda ya isa ya tafi da ita face da yarda ta

da wannan kalmomi nake maka sallama dan haka sai ka tafi kayi shirin zuwa fadar sarki Barusa na birnin Askandariya don dauko gatarin sihiri zan kasance mai sauraronka a nan

kuma ina yi maka tuni da cewa shima wannan gatarin sihiri karka barshi a can fadar boka Shamzubul azwas lallai ka taho da shi nan gareni tare da yarinya Alfila

koda gama fadin wannan batu sai boka hadimul asur ya sake dafa kafadar sarki sahibul hairi nan take sarki sahibul hairi ya tsinci kansa a wajen gidan boka hadimul asur kuma a kasan dogon dutsen nan kawai sai sarki sahibul hairi ya juya ya tafi ya nufi cikin birnin misra yana mai tafiya da sauri don ya isa gida kafin fitowar Alfijir

kashe gari da sassafe sarki sahibul hairi ya tura aka kirawo masa dukkanin fadawaLabarai farko sunyi tsammanin cewa wani abu zai nema a hannunsu don haka sai wadannsu suka noke suka ki zuwa da wuri suna karyar fadin cewa suna nan tafe

koda ganin haka sai sarki ya fusata yace a gaya musu cewa duk wanda baizo ba a yanzu a bakacin ransa koda jin haka sai yan majalisar suka rude nan da nan suka iso fadar suna masu rawar jiki bayan sun hallara sai kowa ya nutsu yayi shiru baka jin motsin komai a dakin face sautin numfashi

daga can sai sarki sahibul hairi ya mike tsaye fuskarsa a murtuke babu alamar fara a Al amarin da ya kara firgita fadawan ke nan gaba daya suka sunkuyar da kawunansu kasa don gudun fushinsa sarki yace dasu

''yaku yan majalisa kuyi sani cewa raina ya baci bisa halaiyarku ta kina da guduna sbd halin da na shiga na babu wannan ya nuna min cewa babu soyayyar gaskiya a tsakanina daku kuma kuna tsoron kada ku talauce ne shiyasa kuke guduna? To ku sani cewa daga yau bana bukatarkomai daga hannun ku kuma nayi muku Alkawari cewa ba zan sake neman komai ba a wajenku

kuyi sani cewa ba wani abu bane yasa na taraku a nan ba sai don na gaya muku cewa zan tafi yaki izuwa birnin Askandariyya domin dauko gatarin nan na sihiri wanda suka baiwa kyakkyawan tsaro zanyi amfani da wannan gatari ne don kawo karshen wannan talauci da nake famda dashi kunga kuwa idan na rabu da talauci kuma kun huta da fargabar komai

kuyi sani cewa bayan na sami wannan gatarin kuma zan wuce izuwa tsibirin zallus inda boka shamzubul azwas yake domin na dauko wata karamar yarinya wacce ya saceta shekaru uku da suka gabata wadda ta kasance yaga babban matsafi sadauki Awasisu

a kalla zan sami shekara guda kafin na kammala wannan tafiya na dawo sabo da haka yanzu ina son ku zabi wanda zai rike mini kasa daga cikinku kafin na dawo koda jin haka sai gaba dayan suka kidime suka haukace nace kowa na cewa shine zai rike kasar shikuwa sarki sahibul hairi sai yai shiru ya zuba musu idanu kawai yana nazarinsu ya fuskanci cewa gaba dayansu babu abin yarda a gareshi

yayi da sarki yaga sun kaure da gardama sai ya daka musu tsawa nan take suka kame kamar gumaka kowa ya yi tsit sarki ya kira wani barde dake can kofar shigowa dakin da suke ciki barden ya rugo da gudu ya zube kasa gabansa sarki yace da barden maza kaje dakin ajiya ka debo mini akwatunan karfe iya adadin fadawan nan nawa

barden ya mike da sauri yace an gama ranka ya dade koda ficewar barden sai cikin yan majalisar nan ya duri ruwa domin a zatonda suke shi ne sarki zaisa su a cikin akwatunan ne ya kulle domin akwatunan sn kasance darma darma baisa wannan daliline jikinsu ya kama kyarma gaba daya kamar ace kyat su fita da gudu

barden ya dinga shigowa da akwatunan daya bayan daya yana saukewa da jerawa a waje guda har saida ya gama tara guda taran koda ya gama ajiye akwatunan sai sarki ya dubi yan majalisar yace gaba dayanku ku fita su rufe kofar kuma su tsaya a bakin kofar cikin rawar jiki suka bi umarni fitarsu keda wuya sai sarki ya dauki kwagirinsa na sarauta ya saka a cikin daya daga cikin akwatunan bayan ya bame akwatun saiya yiwa yan majalisar nan izini su shigo cikin hanzari suka shigo suka tsaitsaya a jere waje guda sarki ya dubesu a natse yace 

yaku yan majalisa kuyi sani cewa kwagirin sarautata na cikin daya daga cikin akwatunan nan guda tara daya bayan daya zakuzo ku zabi akwati dai dai ku budeta wanda ya dauko kwagirin sarautata shine zai rike mun kasata har na dawo daga doguwar tafiya

koda jin wannan batu sai gabadayansu hankalinsu ya dugunzuma wazirin Akiyanu ya dubi sarki sahibul hairi yace ya shugabana ni a tunanina bai kamata ayi haka ba ni da nake a matsayin wazirinka nine na dace na rike maka kasa

koda jin haka sai sarki ya yi murmushi yace na sani cewa ka dace ka wakilceni to amma fa ka sani cewa ban taba yin tafiya irin wannan ba kuma gaba dayanku babu wanda hankalina ya kwanta da shi don haka kawai sa'a naga mai rabo dole ne abi wannan tsari nawa....


KAFIN WAZIRI ya kara cewa wani abu tuni Sarki sahibul hairi ya dubi yan majalisar na farko ya umarceshi da yaje kan akwatunan ya zaba hannayensa na karkarwa sai ya tsaya ya kasa zabar akwatin da zai bude sai da sarki ya daka masa tsawa sannan yaje ya bude akwatin farko

aikuwa yana budewa sai yaga wayan babu komai ciki koda ganin haka sai kwalla ta ciko idanun dan majalisar ya fara kukan zuci don takaicin rashin samun nasara daya bayan daya suka rinka bude akwatunan har akazo kan mutum na tara shine wanda na kashe wanda ake kira AMINUL HAS

Aminul has ya kasance shine galadiman sarki kuma duk a cikin yan majalisar shine wanda baya gajiya da yiwa sarki hidima duk sa adda sarki ya aika masa da bukatar abinci ko sutura take yake aiko masa har saida takai cewa sarki sahibul hairi ya kure Aminul has ya talautar dashi duk ya siyar da kadarorinsa

wani lokacin ma idan aka turo da bukatar sarki sai yayi rance sannan ya aika wajan yaransa da suke tafiya fatauci a kawo masa kudi ya biya bashin gaba daya yan majalisar mutum takwas babu wanda ya sami nasarar dauko kwagirin sarautar kuma duk su takwas din babu wanda bai zub da hawaye ba da fargaba lokacin da ya zo bude akwatinshi

Shikuwa Aminul has cikin nutsuwa ba da fargabar komai ba ya zo ya bude akwatin ta karshe wadda ba a bude ba bisa mamaki sai shima yaga babu komai a cikin akwatin

yan majalisar suka dubi sarki sahibul hairi waziri Akiyanu yace ranka ya dade yazaka yaudaremu kace akwai kwagirinka a cikin daya daga cikin akwatunan nan alhali babu?

Koda jin haka sai sarki sahibul hairi ya bushe da dariya sannan yace hakika na yaudareku amma ba dan komai nayi hakaba sai don na gane wanda ke kaunata a tsakaninku gaba dayanku nan kun sani cewa wannan tafiya da zanyi mai hadarin gaske ce kuma na tabbata cewa duk kuna ganin cewa idan natafi ba zan dawo da raina ba don haka duk wanda ya hau kan karagata ya haukenan

gaba dayanku takwas din nan babu wanda baiyi kukan takaici ba a nan da fargabar rashin samun nasara face Galadima kuma a cikinku shi kadai ne bai gajiya da bukatata lallai yanzu na dad gamsuwa cewa Galadima masoyina neh na kwarai tunda baya harin kujerata

batun kwagirin sarautata kuwa hakika da farko na sanya shi a cikin akwatin tsakiya amma kafin ku shigo sai na sauya shawara na dauke abina sakamakon wannan hikimar da tazo cikin gaggawa koda gama fadin haka sai sarki sahibul hairi ya fiddo kwagirin sarautarsa daga cikin alkyabbarsa ya baiwa aminul has ya karba sannan yace dashi

daga yau kaine sarkin misra kafin na dawo daga tafiyata ko shakka babu zan dawo kuma na umarceka da kayi adalci a cikin harkokin mulki kamar yadda na sabayi

nan take sarki ya sallamesu gaba daya suka tafi cikin bakin ciki galadima ne kadai ya zamo a cikin dumbin farin ciki mara misaltuwa domin dama yana da wani babban buri a zuciyarsa wanda ba zai taba cika shiba face ya zama sarkin misra

bayan sarki ya sallami yan majalisa sai yasa aka shirya masa doki da guzuri amma sai bawan dake wannan aiki ya sanar dashi cewa guzurin fa ba zai isheshi ba har ya isa birnin Askandariyya

kafin bawan ya gama rufe bakinsa saiga manzo daga gidan Galadima janye da wata doguwar taguwa akan taguwar kuwa guzurin tafiya ne mai yawa ga sarki Sahibul hairi

yayinda sarki yaga wannan sako sai ya cika da tsananin farin ciki kuma yaji cewa kaunar Aminul has ta karu a zuciyarsa ainun nan take yayi alkawari a zuciyarsa cewa randa duk bukatarsa ta biya sai ya maishe da galadima waziri kuma zai bashi dukiya mai tarin yawa da bazasu iya cinyeta ba har zuwa karshen rayuwarsu

bayan an gama kimtsa taguwar sarki da guzurinsa sai ya umarci wani bakin bawa nasa mai suna HALUF daya shirya suyi wannan tafiya tare cikin murna da zumudi Haluf yaje ya kimtsa koda fitowarsa sai ya iske yayi shigar yaki mai tsananin kwarjini da ban tsoro gaba daya shigar bakaken kaya sarki yayi sannan ya sanya bakin sulke da bakaken takalma dogaye na fata iya gwuiwa hatta kufen takobinsa da garkuwarsa ma bakakene fuskarsa ya rufeta ruf da bakin rawani ba aganin komai face idanunsa nan take sarki da haluf suka fito daga cikin gida 

sarki ya hau taguwa shi kuwa bawa haluf yahau doki ba tare da bata lokaci ba suka kama hanya suka bar cikin birnin misra A wannan lokaci kuwa rana na gaf da faduwa domin gari ya soma duhu haka dai sarki da bawa haluf sukaci gaba da tafiya harsuka nausa cikin dokar daji

basu gusheba suna tafiya har saida sukaga duhu yayi sosai sannan suka yada zango a bakin wata bishiyar dabino cikin gaggawa bawa haluf ya kafawa sarki tanti sannan yayi masa shimfida a cikin tantin ya kunna masa fitila

koda gama wannan shiri sai ya mike tsaye da nufin ya fita daga cikin tantin sarki Sahibul hairi ya kira sunansa yana mai cewa 

Ina zaka ya Haluf??

Bawa haluf yace ya shugabana ai zan fita wajan tantin nanne natsaya don na tabbatar da tsaro kada wani mugun abu ya sumamemu.......


Zan Cigaba Insha Allah

Zidane kd 

SARKIN SARAKAI

Littafi Na Daya (1)

Part C.

.

Marubucin littafin

Abdul Aziz Sani M/Gini

AA Misau Ke Magana

.

Labari ya isowa AA Misau Cewa..

.

Duk da kasancewarsa ba tsohoba jama a sun dade suna mamakin dalilin da yasa yake dogara sanda a duk sa adda yake tafiya alhali bai tsufa ba har Abu hakim ya rasu babu wanda yasan dalilin da yasa yake amfani da wannan sandan Lokacinda cutar Ajali ta kama abu hakim a wannan lokaci tuni matarsa ta dade da rasuwa kuma ta bar masa ya guda daya wato shulaiba saboda aminci da kaunar dake tsakanin sarki sahibul hairi da abu hakim saiyasa aka kawo shi cikin gidan sarauta ya zamana cewa shi da kansa yake jinyarsa sannan kuma yasa aka dinga kula da shulaiba tamkar yar cikinsa bayan kamar wata hudu da faruwar haka sai ciow ya kara tsanani wani yammaci sarki sahibul hairi da shulaiba na zaune a gaban abu hakim sun zuba masa ido suna kwalla sbd ganin halinda yake ciki sai abu hakim ya dubi sarki sahibul hairi yayi murmushi sannan ya dubi shulaiba ya fashe da kuka koda ganin haka sai hankalin sarki sahibul hairi ya dugunzuma yace yakai aminin mahaifina shin zaka iya gaya min dalilin da yasa ka dubeni kayi murmushi amma da ka dubi shulaiba saika fashe da kuka sa adda abu hakim yaji wannan tambaya saiya gyada kai yana mai alamun cewa zai iya amsa tambayar cikin karfin hali ya bude baki yace yakai wannan sarki mai adalci zanso ka tashi kafaduna ka jingina bayana a wannan gado da nake kwance domin naji dadin sanardakai abinda zai amfani rayuwarka data yata nan gaba koda jin haka sai sarki sahibul hairi ya mike da sauri ya kama kafadun abu hakim ya tashe shi zaune ya jingina bayansa a jikin marikin gadon koda gama hakan sai abu hakim ya kira sunan shulaiba yace taho gareni yake yata shulaiba ta fada kan kirjinsa ya rungumeta a lokacinda duk su biyun suka fashe da kuka al amarinda ya sa sarki cikin tsananin tausayinsu kenan shima bai san sa adda ya fara kuka ba jim kadan sai abu hakim ya dubi shulaiba yace yake yata kiyi hakuri domin ciwonnan nawa bana tashi bane amma ki sani cewa ko a bayan raina baki da wani gata koda jin wannan batu sai mamaki ya kama sarki sahibul hairi yace haba yakai wannan aminin abbana saboda me kake irin wannan furuci alhali ina raye a matsayin sarkin misra Abu hakim ya dago kai ya dubi sarki sahibul hairi a lokacinda hawaye ya subuto masa yace yakai dan aminina ina mai bakin cikin sanar dakai cewa nan gaba awasu shekaru masu zuwa saikashiga cikin wani irin mummunan hali na rashi harta kai cewa ba zaka iya daukar nauyin kanka ba bare ka dauki nauyin wani dukda cewa kana matsayin sarki A wannan lokaci jama a zasu gujeka musamman fadawanka abokanka sauran sarakai zasu kyamaceka su dinga yi maka ba a da isgilanci ka kasance mai hakuri a duk matsayin da ka tsinci kanka kuma ka jajirce wajen neman mafita amanar da zan bar maka itace ga yata shulaiba lallai ka aurar da ita ga mafi soyuwa a ranka daga cikin fadawanka wanda ka tabbatar da cewa yana kaunarka dari bisa dari kuma lallai kada ka aurar da ita a lokacin da ta haura shekara tara a duniya ina nufin ka aurar da ita nan da shekara biyu. Sa adda abu hakim yazo nan a zancensa sai sarki ya cika da tsananin mamaki yace haba ya aminin abbana saboda me kace zanyi talauci alhalin ina da matsayin sarkin misra kuma taya za ayi kace na aurar da yarka a lokacinda take shekara tara alhalin ba a taba yin haka ba a garinnan? Abu hakim ya dubi sarki sahibul hairi yace shin ka yarda cewa kafin rasuwar mahaifinka bashi da abokin shawara wanda ya fini sarki yace gaskiya ne Abu hakim yace shin na taba baka shawara wacce ka bita kaga ba dai dai ba sarki yace A'a to abind anake so ka gane shine abinda na sani har abada ba zaka saniba face na sanar dakai abinda zan hango har abada ba zaka iya hangoshi ba abinda nake so aidakai shine ka kiyaye da duk abubuwanda na fada maka a baya kuma kayi aiki dasu idan kana so ka cimma nasara a rayuwarka lokacin da abu hakim yazo nan a zancensa sai ya janye shulaiba daga kan kirjinsa ya dubeta yace yake yata ki sani cewa nitalaka ne babu abinda zan bar miki na daga dukiya amma zan bar miki wadansu abubuwa guda biyu wadanda indai kina tare dasu har abada keda mijinki ba zakuyi talauci ba kuma babu wani tsautsayi da zai hau kanku wadannan abubuwa biyu ba komai bane face sandata da kuma takalmina nan take Abu hakim ya dauko takalminsa a karkashin gadonda yake kwance gami da sandarsa ya mikawa shulaiba ta karba sannan yace ki boye wadannan abubuwa biyu da kyau har zuwa ranar da kikaga mijinki ya sami babban matsayi a kasar nan to a sannan ne zaki dauki wannan sanda da takalmin ki bashi kuma ki umarceshi da yayi amfani dasu ko yaushe dare da rana koda kuwa yana kwance ne a kan gadonsa ina nufin kada ya kuskura yacire wannan takalmin daga kafarsa face zai shiga kewaye ita kuwa wannan sanda ko barci zaiyi ya ajiyeta a daf dashi lokacinda shulaiba tazo dai dai nan a tunaninta Sai aminul has ya girgiza kafadunta yace Wai shin wanne irin tunani kike yi ne haka??.

Aminul has ya girgizata yace tunanin me kikeyine haka kamar wacce ta farka daga bacci haka ta zabura koda tadawo cikin hayyacinta saita dubi Aminul has tace ka jirani Anan karka matsa ko ina zan shiga daki na fito nan take shulaiba ta juya ta nufi cikin dakinta shi kuwa sai yabita da kallo kawai jim kadan saiga shulaiba ta dawo rike da shohuwar takalmi a hannunta koda ta iso gaban Aminul has saita tsaya suka kurawa juna ido yana mai mamakin ganin tada wadannan tsofaffin abubuwa biyu shulaiba tayi murmushi mai taushi a gareshi tace yakai mijina shin kayi imani da kaunar da nake maka cewa ta cika dari bisa dari? Aminul has yace babu kokwanto ga hakan shulaiba tace idan har kayi imani da hakan toka rike wannan takalmi da wannan sanda daga yau ka kasance a tare dasu dare da rana ya zamana cewa babu abindake rabaka dasu hatta kwanciya bacci face idan zaka shiga kewaye tabbas idanka kiyaye da haka babu tsautsayin da zai sameka kodajin wannan batu sai aminul has ya kurawa wannan sanda da takalmi idanu kawai ya karbesu ya rungumesu a kirjinsa yana mai cewa hakika na gamsu cewa wadannan abubuwa biyu sun fito daga hannun wanda ba za a taba mantawa dashiba lallai zaki sameni mai kiyayewa da umarninki. Nan take aminul has ya cire takalmin dake kafarsa ya saka wannan tsofaffi sannan ya dogara wannan sanda ya nufi cikin turakarsa yana mai waigen shulaiba suna yiwa juna murmushi. Wannan shine abinda ya faru tsakanin aminul has da matarsa shulaiba bayan ya karbi rikon kasar misra daga hannun sarki sahibul hairi ++...

Al'amarin sarki sahibul hairi da bawa haluf kuwa tun da sarki ya kama barci a cikin tantinsa bai farka ba saida gari ya waye har rana ta iske koda budewar idanunsa sai yaji rurin gagarumar wuta a wajen tantinsa cikin sauri ya mike tsaye ya fita waje da hanzari yana mai zare takobinsa don tsammanin ko wadansu yan fashi ne suka kawo sumame da fitowarsa saiyaga ashe bawa haluf ne ya tara gawarwakin yan fashin da ya kashe jiya a waje daya ya kunna musu wuta, sarki sahibul hairi yayi murmushi sannan ya yafito bawa haluf da hannu cikin hanzari haluf ya rugo gareshi suka koma cikin tantin tare da shigarsa sai haluf yaga ashe har sarki ya fiddo abincin kalaci ya shirya shi bisa faranti. Sarki ya dubi haluf yace ina son muyi sauri mu gama kalaci domin muci gaba da tafiya ka san cewa a kalla nan gaba sai mun kwana talatin da bakwai kafin mu isa birnin Askandariyya ba tare da gardamar komai ba bawa haluf yabi umarni suka zauna tare suna masu fuskantar juna suna cikin cin abincin ne sarki sahibul hairi ya lura idanun bawa haluf yaga sunyi jawur kawai sai yayi murmushi yace yakai haluf kai kuwa menene ya hanaka yin barci jiya da daddare?. Koda jin wannan tambaya sai haluf yayi ajiyar zuciya yace ya shugabana hakika jiya naga bala'in da bantaba gani ba kuma naga jarumtaka a wajenka wacce inda zanje na bayar da labarinta baza a gasgata ni ba hakika ka cika sadauki uban sadaukai ka sani cewa ko a yanzu idan na runtse idanuna sai nayi ta ganin yadda ka dinga karya barayin jiya kana sawa suna sare kawunansu da soke juna. Yayinda sarki sahibul hairi yaji wannan batu saiya bushe da dariya yace yakai haluf hakika inda kana nan a lokacin da nayi wani yaki da mutanen birnin Rum da wata kila kwakwalwarka ta birkice ka sami tabin hankali A rayuwata ban taba yin yakin da na sha bakar wahala ba kamarsa domin saida na kwana na yini ina yaki ba tare da na sami damar hutawa ba daidai da dakika daya a wannan yakine na shiga tsakiyar abokan gaba mutum dubu dari uku ni kadai suka yanyameni suna kawo mini sara da suka nima ina maida martani A tsawon kwana da yinin ne nayi musu mummunar barna na kashe mutum dubu dari da talatin A wannan yaki gaba dayan dakaruna mutum dubu dari biyu da hamsin saida aka kashe su ni kadaine na rage Lokacinda abokan gaba sukaga inatayi musu barna amma sun kasa cimmani sai suka kara kaimi suna kokarin hallakani ta kowanne hali amma saina zame musu alakakai kaini kaina a wannan yaki saida na tausayawa abokan gaban saboda irin kisan gillar da nake musu. Wani lokacin idan na sari mutum saidai kaga gangar jikinta tsage gida biyu bari da bari duk inda nasa gaba sai daikaga sassan jikin bil'adama suna yawo a sararin sama gaba dayan jikina saida ya rine da jini ba a ganin komai sai idanuna tamkar anyi mini wanka a kogin jini babu abinda zai baka tausayi face ganin yawan gawarwakin a zube tuli a filin yakin tamkar yabanya a gona lokacin da muka kwana muka yini muna wannan yakin ya zamana cewa na kasa karar da abokan gaba sukuma sun kasa cimmani sai gajiya ta fara riskata a sannanne fa abokan gaba suka fara samun lagona har aka yi min sara uku a gadon bayana kuma aka sokeni a kwibin hagu na cikina nan fa jini ya fara zuba a jikina koda naga zan hallaka saina kwarara uban ihu wanda ya firgita gaba dayan abokan gabar suka jada baya suka tarwatse koda naga hanya ta samu saina ruga da gudu ina gudun ina saransu kafin abokan gaba su ankara nayi nisa 

suka jada baya suka tarwatse koda naga hanya ta samu saina ruga da gudu ina gudun ina saransu kafin abokan gaba su ankara nayi nisa.

Ai kuwa sai suka biyoni cikin matsanancin gudu amma na gaba yai gaba na baya sai labari lokacin da nake wannan gudu ina yinsane cikin takaici domin a rayuwata ban taba guduwa ba daga filin yaki yau gashi bala'i yakai har gudu ya zamadole a gareni inba haka ba kuwa na rasa rayuwata shidai wannan yaki muna yinsa ne a wani daji wanda ake kira BAHARUL SHARUL dajin na dauke da manyan tsaunuka da manyan koguna inda ruwa ke bulbulowa daga cikin duwatsu yana kwaranya yana gudu sa adda abokan gaba suka tasoni a gaba na ga babu matsera kawai saina durfafi wani katon tsauni wanda nidai a rayuwata ban taba ganin tsauni mai tsawonsa ba ina kyautata zaton cewa duk duniya babu tsauni mai fadi da tsawonsa nan fa naci gaba da gudu suna biye dani har muka isa can saman tsaunin muka kureshi koda na leqo kasan tsaunin na ga zurfinsa sai zuciyata ta bugu abokan gaba kuwa sai suka ja dinga a bayana suka fara kyakyata dariya don sun tabbatar da cewa duk wanda ya fada daaga saman wannan tsauni sunansa gawa. Nanfa na tsaya ina tunani a raina nace hakika idan ajalina ya tabbata a hannun abokan gaba an rusa mini tunkahona da darajata a idanun duniya kawai saina sake lekawa kasan tsaunin naga yadda ruwa ke kwarara kasa sanna na yanke hukuncin na daka tsalle na sallamo kasa ko dai na rayu ko na mutu kafin nayi hakan saina juya na dubi abokan gaba nayi murmushi nace idan akwai da namijin da ya isa a cikinku ya biyoni inda zan tafi' kafin abokan gaba suyi wani yunkuri na daka tsalle na sallamo izuwa kasan tsauni lokaci guda abokan gaba suka rugo izuwa karshen tsaunin suka yi cirko cirko suna masu lekowa kasa don suga irin mutuwar da zanyi saboda nisan dake tsakanin saman tsaunin da kasansa sai da dakika dari uku ta shude sannan na iso kasa cikin kogi saura kiris kuwa kaina ya fado kan wani dutse amma sai kafata ta bugi wani wuri a jikin tsaunin saina sauya wuri na nutse izuwa can karkashin kogi.

A wannan lokaci na suma bansan halinda nake cikiba kawai sai farkawa nayi na ganni a gabar kogi a can wani daji daban koda na tsinci kaina a raye sai murna ta kamani nan take na mike tsaye na tafi neman itatuwan da zan sarrafa na yiwa raunikan jikina magani saida na shafe kwana sittin ina tafiya a daji na kwana nan na tashi can sannan na koma gida wato birnin misra.

Sa adda sarki sahibul hairi yazo nan a labarinsa tuni sun gama cinye abincin dake gabansu haluf ya jinjina kai yace hakika ya shugabana ka cika jarumi uban jarumai ina ba don wasu dalilai ba da sainace idan akwai irinka goma a birnin misra da munci duniya da yaki. Koda jin haka sai sarki ya bushe da dariya ba tare da yace komaiba ya mike ya fita wajen tantin koda ganin haka sai bawa haluf ya mike da sauri ya harhada kayansu gaba daya sannan suka hau ababan hawansu suka nausa daji. Kamar yadda sarki sahibul hairi ya fada haka lamarin yakasance wato basu isa birnin askandariyya ba sai kwana talatin da bakwai har suka isa can din kuwa basu sake haduwa da yan fashi ba saidai muggan dabbobin dawa wadanda nan take sarki sahibul hairi keyi musu kisan farat daya.

Lokacinda suka iso kofar birnin Askandariyya dare yayi tsaka har bawa haluf ya nufi kofar birnin da nufin yaje ya kwankwasa a bude masa sai sarki ya dakatar dashi yace saurara yakai haluf aini kadai zan shiga cikin birnin nan kuma indai na shiga ba zan tsaya ko ina ba har saina dangana da fadar sarki barusa naje har inda aka ajiye gatarin nan na lu'u lu'u na daukoshi ka sani yaki da daddare na matsoraci ne lallai gobe da safe ido na ganin ido zan shiga cikin wannan birni na nufi gidan sarautar gadan gadan duk wanda ya tsaya a gabana sai dai gawarsa abinda nake so dakai mu kwana nan kofar gari kuma idan gari ya waye ka jirani a nan har naje na dawo bayan cikar burina idan kuwa kayi kuskure ka biyoni lallai zaka rasa rayuwarka.

Koda gama wannan jawabi sai bawa haluf ya sauko daga kan dokinsa sannan yarike taguwar sarki shima ya sauka cikin hanzari ya daure ababan hawansu a jikin wani dutse ya kafa musu tanti suka shiga ciki suka kwanta suka kama aikin rago. Da Asubar fari sarki ya farka daga barci koda bude idansa yaga bawa haluf yanata barci har da munshari saiya mike ya kama yin damarar yaki ya kwaso makamansa ya shiryasu a jikinsa da ya gama wannan shiri sai ya rufe fuskarsa da wani rawani ya zamana cewa idanunsa kadai ake iya gani ba tare da ya tashi bawa haluf daga barci ba sai ya fita daga tantin yaje ya kwance taguwarsa ya haye kanta ya durfafi kofar birnin Askandariyya a lokacinda gari ya waye sosai rana ta fito. Koda ya iso daf da kofar birnin wacce akayita da bakin karfe sai yaja dunga ba tare da ya sauko daga kan taguwar ba ya zare takobinsa ya kwankwasa kofar da ita faruwar hakankeda wuya sai yaji an tambayeshi da kakkausar murya wanene nan yake kwankwasa mana kofa da sassafe haka? Hala kai bakone baka san ka'idar shigowa birnin mu ba.....

Koda budar bakin sarki sahibul hairi sai yace Ubankane yake kwankwasa kofar tun muna shaida juna ka bude kofar nan in kuwa ka kuskura na banke kofar na shigo sai mataccen dake kabari yafika kwanciyar hankali maimakon abi umarni a bude kofar sai aka kyalkyale da dariya Al amarinda ya fusata sarki kenan kawai ya sauko daga kan taguwar tasa yaja da baya kimanin taku Ashirin sannan ya rugo da gudu ya hada karfinsa gaba daya ya doki kofar garin da kwanjinsa take kofar ta fita fit! Shi da ita suka burma ciki kai kace giwace ta rugo ta bangaji kofar .wOHoHO :) Cikin hanzari sarki sahibul hairi ya mike tsaye sai yayi arba da wani murjejen kato a gabansa katon sanye da suulken yaki kuma ga wani shafcecen gatari a hannunsa amma duk jikinsa karkarwa yake ya kurawa sarki sahibul hairi idanu kawai cikin firgici kamar ace kyat ya fita da gudu sbd razana shidai wannan kato ba kowa bane face sarkin kofa sahibul hairi ya dubi katon yace, kai kuma waye kuma me kake jira dani ba tare da ka afko mini ba tunda ga makami a hannunka' cikin murma mai rawa katon yace nine sarkin kofar birnin Askandariyya yau shekarata arba'in ina gadin wannan kofa amma a tsawon wadannan shekaru ban taba ganin sadaukin mutum tamkarka ba ka sani cewa an taba kokarin balle wannan kofa da karfin giwaye biyu amma abu ya faskara yau gashi kai bil adama kai daya ka banketa anya kuwa kaiba aljan bane? Idan kai mutum ne wanene kai kuma menene yazo dakai wannan birni namu' sarki sahibul hairi yace nine sarki sahibul hairi na birnin misa kuma nazo wannan birni nakune don biyan wata bukata tawa, kayi mini jagora izuwa fadar sarkinku inba haka ba kuwa yanzun nan zaka bakunci barzahu, lokacinda sarki yazo nan a zancensa sai sarkin kofa yai ajiyar zuciya yace hakika biri yayi kama da mutum ni kam nasan cewa duk duniya babu wani sadauki da zai iya bangaje wannan kofa ta fadi face sarkin misra tuni labarinka yazo mana nan to amma ina mai shawartarka da ka janye duk irin bukatar dakazo da ita domin na tabbata cewa sarkinmu bazai yarda da ita ba na sani cewa kai jarumine uban jarumai amma kada ka manta cewa sarkin yawa yafi sarkin karfi kodajin haka sai sarki sahibul hairi ya dakawa sarkin kofa tsawa yace ai ragon maza shike tsoron yawan maza kabi umarnina ko kuma na tabbatar da alkawarina akanka sarkin kofa yace nikam bazanbi umarninkaba saidai nabi na sarkina domin idan na saba masa masifarda zan shiga saina gwammace Ajalina kafin sarki yace wani abu tuni sarkin kofa ya zare wani kaho ya busa faruwar hakan keda wuya saiga dakaru suna ta bullowa a guje tako ina duk sun zare makamai ashe tun dazu ma a lallabe suke suna ganin abinda ke faruwa tsakaninsu lokacinda sarki ya balla kofar birnin saida karar kofar ta cika birnin gaba daya amma da yawan jama a basuyi tsammanin cewa kofar birnin bace wasuma sun zata fashewar dutsen wuta ne kafin sarki ya ankara tuni sama da mutum dari uku sun kewaye shi rike da makamai tsirara sahibul hairi ya dubesu yai murmushi kawai saiya yunkura da nufin ya ratsa ta cikinsu yai gaba aikuwa sai suka rufar masa gaba daya da nufinsu daddatsashi suyi gunduwa gunduwa dashi hakika rashin sani yafi dare duhu inda wadannan dakaru sunsan abinda zai biyo baya da basuyi gangancin afkawa sarki sahibul hairi ba domin a cikin dakika dari da ashirin ya rugurguzasu tamkar an kwankwasa gilashi ya zamana cewa sarkin kofa ne kawai a tsaye kikam kamar gunki idanunsa sun zazzaro kamar zasu fado kasa gaba daya jikinsa rawa yake ya firgita fiye da dazu sa adda ya gaya balla kofar birnin ya fado ciki sahibul hairi ya dubi sarkin kofa yace maza ka gayawa sarkinku abinda ya faru yanzu kuma kace dashi idan ya bani abinda nazo nema zamu rabu lafiya idan kuma ya ki a yau dinnan zan baje wannan birni yadda ko a tarihi baza a tuna dakuba. Koda gama fadin haka sai sarkin kofa ya ruga inda dokinsa yake ya kwance ya haye sannan ya sukwaneshi izuwa cikin birnin Askandariyya shikuwa sarki sahibul hairi sai ya koma inda yabaro taguwarsa yahau sanna ya shigo cikin birnin ya kara gaba ++

A can fadar sarki barusa kuwa fadar ta cika makil da fadawa da talakawan gari domin a yaune sarki barusa ke walimar cikar shekaru talatin akan karagar mulki banda shagali babu abinda akeyi a fadar masu kida nayi masu rawa nayi abinci kuwa da abin shaye shaye gasu nan birjik babu adadi kowa abinda yake so shi yakeci kallo daya mutum zaiyiwa sarki barusa ya gane cewa a cikin tsananin farin ciki yake A wannan lokaci Barusa na zaune shirim kamar giwa a kan karagar mulki yanata kwankwadar giya sai rusa dariya yake yana kallon wadansu yan mata dake ta tikar rawa a gabansa yana annashawa. Ana cikin tsakiyar wannan haline akaga sarkin kofa ya shigo a guje yanata faman haki Al amarinda ya dugunzuma hankalin kowa kenan akayi tsit tamkar mutuwa ta gifta kowa kuma ya kame kamar babu mai rai a wajen ++ .......

Zan dakata anan saikuma Allah yakaimu gobe zamu cigaba

Admin AA Misau Ke Magana

Zidane kd 

SARKIN SARAKAI

Littafi Na Daya (1)

Part D.

.

Marubucin littafin

Abdul Aziz Sani M/Gini

AA Misau Ke Magana

.

Labari ya isowa AA Misau Cewa..

.

Ana cikin tsakiyar wannan haline akaga sarkin kofa ya shigo a guje yana ta faman haki Al amarinda ya dugunzuma hankalin kowa kenan akayi tsit kamar mutuwa ta gifta kowa ya kame kamar babu mai rai a wajen Da zuwan sarkin kofa saiya fadi gaban sarki yayi gaisuwa sannan yace ya shugabana kayi sani cewa yanzu haka jarumi uban jarumai ya shigo kasar nan ya banke kofar gari da karfin sadaukantakarsa kuma ya kashe dukkanin abokan aikina yana nan tafe izuwa nan fadarka don biyan wata bukata tasa ni kaina ya kyaleni ne kawai don nazo na isar da sako' cikin tsananin fushi sarki BARUSA ya dakawa sarkin fada tsawa wacce tasa dukkanin jamar wajan suka fadi kasa suka kwanta da ruf da ciki don tsananin razana sarki barusa ya kasance lafcecen katon mutum mai surar mutanen farko gashi dogo kuma gashi kakkaura duk jikinsa a murde yake ya tara jijiya da kwanji komai tsawon mutum sarki barusa na iya dora abinci a kansa yaci yana da jajayen idanuwa ababan tsoro yanada wawakeken hanci da katon baki a takaice dai idan ana batun muni to sarki BARUSA kurunkus ne! Sarki barusa ya nuna sarkin kofa da yatsa yace wai shin wanene jarumi uban jarumai harda ya isa ya banke kofar birnina ya kashe min dakaru har yace lallai sai ya shigo fadata bidar wani abu? Sarkin kofa yace Aiba wani fane face SARKI SAHIBUL HAIRI na birnin misra kodajin wannan batu sai sarki barusa ya mike tsaye ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya ita kanta dariyar abar tsoroce domin zata iya firgita mai ciki tayi bari :o zata iya sa mutum gudawa kuma zata iya zamo sanadin yin hijirar dukkanin tsuntsayen daji bayan sarki barusa yai dariya ya gaji saiya koma kan kujerarsa ya zauna su kuwa fadawanda gaba daya sun tsure sun dimauce tunda sukaji ance sarki sahibul hairine yazo wazirin sarki barusa wanda ake kira YARKUS ya matso daf da sarki yace ranka ya dade yanzu menene abinyi? Ka sani cewa sarki sahibul hairi ya shahara fagen jarumtaka da samun nasarar yaki shinefa mutuminda ya gagari rumawa da hindu shine wanda ya shiga har birnin farisa ya sare kan sarkinsu kuma shine sarkinda ba a taba cin kasarsa da yaki ba sai sau daya a yakin da suka gwaza da rumawa amma dukda cewa an kashe gaba daya dakarunsa saura shi kadai saida yayi musu mummunar barna kuma ya tsira da rayuwarsa lokacinda waziri yarkus yazo nan a zancensa sai sarki barusa ya sake bushewa da dariya a karo na biyu daga can kuma ya murtuke fuskarsa yace ya kai yarkus kayi sani cewa baka fini sanin ko waye sahibul hairi ba na sanshi kamar yadda na san kaina abinda nake so daku shine kowa ya nutsu ya koma mazauninsa idan sahibul hairi ya shigo nan ya iskemu muna harkokinmu kamar yadda muke yi dazu tamkar labarinsa bai riskemu ba ina son naji abinda ya zo nema a kasata sannan na san hukuncin da zan dauka akansa koda gama fadin haka saigaba daya jama ar dake fadar suka dawo cikin hayyacinsu aka ci gaba da sharholiya tamkar babu abinda ya faru jim kadan da faruwar haka saiga sarki sahibul hairi bisa taguwarsa ya shigo da ita har cikin fadar babu abinda zai baiwa mutum mamaki face ganin yadda ita kanta taguwar take tafiyar kasaita tamkar akan sahara shi kuwa sarki sahibul hairi na zaune a kanta cikin wannan shigata bakaken kaya fuskarsa arufe idanunsa kadai ake gani sbd tsabar kwarjinin sahibul hairi saida masu rawa da kida suka kasa cigaba da aikinsa fadawa da sauran jama ar gari kuwa saida kowa ya natsu ya kurawa sarki sahibul hairi idanu duk wanda ka duba saikaga bakinsa a bude tamkar shashasha. Taguwa taci gaba da tafiya har ta iso daf da karagar sarki barusa sannan ta tsaya cak aka fara kallon kallo a tsakanin sarakan biyu sarki barusa ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa dama tuniya kule saboda ganin jama arsa sun firgita da ganin sarki sahibul hairi.

Tsawon yan dakiku fadar tayi shiru kamar ba mai rai a cikinta daga can sai sarki sahibul hairi ya risina kadan ga sarki barusa yace tsakanin sarki da sarki akwai girmamawa yakai mai birnin Askandariyya kayi sani cewa ban shigo kasarka da nufin cin zarafinka ba ko zalunci ba zan la anta kowa ba face wanda yaso la antani ina hadaka da girma da arziki ka bani abu guda daya rak na tafi dashi idan kayi haka nayi alkawarin ba zan cutar da ko kazar garinnan ba idan kuma kaki nayi alkawari saina karar da dukkanin dakarunka na biya bukatata koda kuwa a sanadin hakan zan baje gidajenku su zamo turbaya koda jin wannan batu sai sarki barusa ya bushe da dariya sannan ya hade fuska yace yakai mai birnin misra ka fadi abinda kake bukata daga gareni na baka domin ina da labarin cewa fatara da talauci sun isheka idan na abinci ne zan sa a baka wanda zakaci kaida jama arka na shekara goma idan kuma sutura ce kake so zan baka wacce zata kaika shekara arba in kana sawa kullum sa adda sarki sahibul hairi yaji wannan batu sai ya murtuke fuskarsa yace ai ba bara nazo yi wajenka ba abinda nake bukata a wajenka ba komai bane face gatarin lu'u lu'u wanda kuke bautawa .

Koda jin wannan batu sai sarki barusa ya sake bushewa da dariya a karo na hudu sannan ya mike tsaye ya dubi sahibul hairi cikin murmushi yace ai wannan abune mai sauki kabi waccen hanyar zaka isa dakin da gatarin yake saika dauko cikin salama kazo kayi tafiyarka' ba tare da tsayawa yin wani nazari ko tunani ba kawai sarki sahibul hairi yabi wannan hanya wadda sarki barusa ya nuna masa koda ya kusa isa wata kofa sai kasa ta dare ya rufta cikin wani dakin kasa mai tsananin zurfi yana fadawa sai kasar ta hade ta rufe ruf tamkar bata taba darewa ba sarki barusa ya tuntsure da dariya yace lallai wannan ya cika mahaukaci to inbanda mahaukaci wane ne abokin gabarsa zai nuna masa hanya yabi? Tabbas yakai kansa izuwa mahallakarsa sa adda sauran fadawa da jama ar gari sukaji haka sai suma suka kama kyalkyala dariya suna cewa tabbas sarki sahibul hairi ya cika mahaukaci.

WANNAN SHINE ABINDA YA FARU A FADAR SARKI BARUSA ++.

AL AMARIN SARKI SAHIBUL HAIRI kuwa lokacinda kasa ta dare ya fada kasanta sai yaji ya fadi cikin wani faffadan daki mai tsananin zurfi fadowarsa keda wuya yaji ana tayin wani irin gurnani mai ban tsoro kasancewar dakin akwai duhun gaske baiga abubuwanda ke gurnanin ba.

Bazato ba tsammani sai dakin ya haske fayau yaga abubuwan dake gurnanin ba komai bane face wadansu rikakkun zakuna wadanda a kalla adadinsu yakai guda dubu dukkaninsu a kwance suke sunyi wa dakin kawanya ma ana a tsakiyarsu sarki sahibul hairi yafado koda zakunan nan sukayi arba dashi sai suka fara zazzago harshe suna tamde baki alamar cewa sun jima suna fama da yunwar abinci kawai suke nema tunda sahibul hairi yazo duniya bai taba ganin zakuna masu girma da tamkar wadannan dukda dakakkiyar zuciya ta mazan jiya saida hankalinsa ya dugunzuma yasan cewa lallai yau ya gamu da gamonsa sai abinda hali yayi kamar hadin baki sai zakuna suka daka tsalle lokaci guda gaba dayansu suka yi kan sarki sahibul hairi suka tumurmusheshi da nufin su cinyeshi sahibul hairi ya yunkura da dukkanin karfinsa ya watsar dasu sai gashi sun tarwatse a sama suna buguwa da garun dakin kafin su sake kawo masa farmaki tuni ya zare takubba biyu a jikinsa hagu da dama ya hausu da sara duk zakin da ya sara sai yaji kamar dutse ne saidai kaji wani irin sauti ya tashi kall.

Al amarinda ya dugunzuma hankalinsa kenan ya tabbatar da cewa lallai maganar sarki barusa ta tabbata cewa ya kawo kansa izuwa mahallakarsa nanfa zakunan nan suka kara kaimi wajen daka tsalle suna kai masa hari suna kokarin ya kusarsa da kokarin cinyeshi inba don sahibul hairi ya kasance mai tsananin zafin nama da sadaukantaka ba da tuni sun gama dashi amma dukda hakan saida suka fara karkarce jikinsa da faratan hannunsu kafin ya ankara tuni jini ya fara zuba a jikinsa koda ya fuskanci cewa zai hallaka ba da dadewa ba in akaci gaba da wannan gumurzu sai yayi jifa da takkubban hannunsa sannan ya takarkare ya kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa ihune ya sa zakunan sukaja da baya sukayi cirko cirko ihun yaci gaba da amsa kuwwa har sarki barusa da jama arsa dake zaune a can fada saida suka jiyo ihun amma sai sukayi zaton cewa wahala ce tasa sahibul hairi yake wannan ihu don haka sai suka kama kyalkyala dariyar mugunta lokacinda zakunan nan suka firgice da jin wannan ihu na sahibul hairi sai aka fara kallon kallo tsakaninsa dasu tamkar sunji tsoro bazasu sake afka masa ba daga can sai suka sake daka tsalle gaba dayansu sukayi masa rubdugu wohoho! A sannan ne fa tsagwaron karfi da jarumtaka sukayi ranarsu domin sahibul hairi wanzuwa yayi tamkar shaidani a tsakiyar zakunan nan duk wanda ya nausa sai dai kaga yai sama ya fado kasa kafin ya mike sai yasa kafa ya tatsile kansa take zakaga kan zakin ya dagwargwaje tamkar an kwankwatsa shida dutse wani lokacin idan ya naushi zaki a gadon baya saidai kaji bass! Wato ya karya masa kashi nan fa zakunan nan suka ringa bajewa a kasa suna zama gawa koda sahibul hairi yaga ya samo lagon zakunan saiya kara kaimi a kansu yaci gaba da ragargazarsu da karfin damtse cikin zafin nama da juriya da jarumtaka kai saida takai cewa yana kama kawunansu yana murde musu wuya da karfin tsiya saidai kaga yayi jifa da gawar zaki. Hakika karfi jarine domin inda sarki bai kasance sadaukin gaskeba da tuni zakunan sun zamo sanadiyar Ajalinsa duk da cewar ya samo lagon zakunan ba su fasa yi masa rauni ba domin kartar jikinsa suke da farata nan da nan jikin nasa yai fata fata tamkar da kaifin takobi ake saransa saboda zafin yankan da suke masa ne ya dinga kwarara ihu yana ci gaba da kakkarya gabban jikinsu. Saida aka shafe kusan rabin sa'a ana wannan dauki ba dadi sannan ya samu ya kashe gaba dayan zakunan nan aikuwa yana gamawa dasu ya yanke jiki ya fadi a lokacinda jiri da jini ke dibarsa, dama tun lokacinda aka fara wannan gumurzu su sarki barusa na jiyo ihunsu da gurnanin zakunan amma daga bisani sai sukaji shiru ba ihun sarki bana zakuna 

Dama tun lokacin da aka fara wannan gumurzu tsakanin sahibul Haiti da zakunan su sarku barusa Na jiyo ihunsu da gurnaninsu amma daga bisani sukaji shuru ma ana babu ihun sahibul Haiti kuma babu Na zakunan Al,amarinda ya baiwa sarki barusa mamaki kenan kawai sai ya dubi wadansu dakaru dubu uku tace maza kuje cikin wannan dakin Kasan su gano masa abindake faruwa shinn zakunann nan sunn kashee sarki sahibul hairii ko kuwa shine yakarkashesu. Yayinda dakaru sukaji wannan umarni Na sarki barusa sai hankalinsu ya dugunnzuma suka tsaya suka yi charko charko suna kallon junansu aka rasa Wanda zai wuce gaba Ba wani dalili bane yasa wadannann dakaru suka kasa zuwa wqnnan daki ba sai saboda bala,in dake cikinsa Shidai wannan wuri an tanadeshine musamman son hallaka iron mutanan da aka yankewa hukunncin kisa hakika sarrki barusaa karyaa yayiwa sahibull hairi cewaa a wannan bangareen gatarinn sihirinn yakee A cikin wannan gidaan kasa India sarki sahibul hairii ya fadaa akwai dakuna gomaa sha biyuu a cikinn kowanne dakinwl akwaii masifa iri dabann masifar dakina farko ta bata kai wacce take dakii nabiyu baa wadda ke dakin Na uku tafi ta daki nabiyu Wato dai abin bi dabi be har zuwa dakin karshe wato Na gomaa sha biyu Idan mutun ya kuskura ya fada daki Na farkoo toga babu wata hanya da zaibi ya fito dolene sai yabi ta cikin ragowar dakunaa goma sha dayann Lokacinda sarkibarusa yaga dakarunsa sunnoke sun kasa lafiya cikin wannan wuri sai ya tuntsure da dariyar far in ciki yace lallai kun Sani cewa ba a Shigaa wannan wuri a fito a rayee Ko shakka babu wannan makiyi namu tuni yanzu ya hallaka,, Koda fadawa da jama at gari sukaji wannan batu sai suka bushe da dariya nan take aka cigaba da shagali tamkarr babu wata miskila data task ++. +++. ++. ++

Al amarin sarki sahibul haiiri kuwa lokacinda yaga ya kashe zakunan nan gudaa dubu saiya fadii kasa yana haki saboda tsananin gajiyaa Visa dole ya yanke hukuncin ya tsaya yayi jinyar jikinsa kafinnan kafin ya tunkari daki Na gabaa tunda dai baisan masifar dazai iske ba a cikinta nan take ya kwance wata karamar jakaa dake kugunsa ya fiddo wani Baron magani ya shashahafa a jikinsa sannan ya kwanta a cikin gawarwakin zakunan nan son ya huta Faruwar hakan keda wuya sai bacci ya saceshi bai saniba aikuwa bai farka ba sai da rana ta fadi kodaya bude idonsa ya tsinci Kansas cikin gawarwakin zakuna kuma ya fuskancii cewaa ya Dade yana wannan bacci sai ransa ya baci domin yaso ace duk bala inda zaiyi ya dauko Gagarin sihirin a cikin abinda vai wuce ss a biyarba har yabarr kasar Askandariyya Nan take kuma sahibul haiiri yaji yanajin yunwa gashi kuma bai taho da jakar guzuri ba ya barta a can bayan gari wajan bawa haluf nanfa hankalinsa ya tashi SBD yasan cewa Indaii yacigaba da Shiva dakunan wannan gida a haka zai jya rasa rayuwarsa tunda gajiya da yunwa a jikinsa babu kuzarinda zai iya yin yaki Yana cikin wannan haline dabara ta fado masa nan take ya farke cikin zakuna ya fiddo kayan cikinsu yakama cinsu danye bataree da gashiba tunda babu wutarda zaigasa run yana yamutsa fuska SBD rashin jin dadin naman a bakinsa harma yajiyasaba da rashin dadin Bai gusheba yanacin naman harsaida yaji ya koshi sannan ya mike tsaye yasake daukar takubbansa guda biyu nan ya banke kofar dakina biyu da kafarsa ya kunnna kai ciki Da shigarsa sarki sahibul haiiri cikin dakinn Na biyu sai yayi arba da wadansu irin zagba zabgan maridai wadanda girmansu ya wuce kima da tunanin bill adama kowanne daga cikin su ya ninka sarki barusa a tsawo sai biyu hakama fadinsu da kaurinsu Dukda cewa sarki sahibul haiiri Nada dakakkiyar zuciya saida ya tsorata ainun da ganin wadannan maridai Dan ko a labaran dayasha ji baitaba jincewa akwai maridai kalan suba Wadannan maridai dai su dubu ne cif kuma kowannensu Na rike da zabgegiyar makamai guda Inda za a ajiye makamin mutum daga daga cikinsu makamin ba zai dauuku ba face antara karti majiya karfii mutum arba in Sudai wadannan maridai suna da mummunar siffa maiban tsoro tamkar dodanni kallon daga zakayiwa kirar jikinsu kasan cewa karfafane domin duk naman jikinsu a cure take tamkar an shirya mulmulallen diwatsu gashi sun Tara many an damatsa jijiyoyin kwanji hakika idan aka Tara irinsu goma zasu iya yakar babban birni suciahida yaki a cikin Rabin ss a Yayinda sarki sahibul hairi yai arba da wadannan maridai sai zuciyarsa ta karaya ya juya d baya da nufin ya koma wajan da ya fito wato dakina farko aikuwa saidaya daga cikin maridan ya zuro zungureren hannunsa ya cafkoshi yai samaa dashi ya fyada da kasa Saboda tsananon radadi da zugi saida sahibul hairi yatakarkare yaji kamar an karya Massa duk kasusuwan dake bayansaa don haka saiya kasa tashi Maridin ya daga wani faskeken gatari Dame hannunsa ya dankarawa sahibul haiiri Sara a cikii aikuwa koda gatarin ya dira akan cikin sahibul haiiri saiya kakkarye amma karfinn saran yasa cikinsa ya kulle yaji kamar zai suma Kosa faruwar haka sai mamaki ya kama maridannan gaba dayansuu saboda ganin yadda karfin gatarinsu yake yasiri a cikin duk wani .wahaluki amma yau gashi bill adama yaki yayi tasiri a jikinsa harma ya zauna lafiya bayan a tarihin Gagarin ba a taba saran wani abuba Wanda ya kasa rabewa gida biyu Aikuwa sai maridannan suka taso Masa gaba dayansu shikuma yahau maridannan da Sara da suka sukuwa suka dinga kai masaaa cafka yana gocewa Babban abinda yatayarwa da sahibul haiiri hankali shine gashidai yana saransu jikinsu nadarewa yana zubar da jini amma ko kadan basa gezau kai wani lokacima harr caka musu adduna yake a cikinsu amma da ya zaree saikaga sun cigaba sa yaki saboda taurin rai da naci iron nasu Al,amarin da ya dugunzuma hankalinsa kenan ya tabbatar da cewa indai akaci gaba da wannan gumurzu a haka izuwa wani lokaci mai tsawo zai iya gajiya su sami damar hallakashi Su kansu maridan sunsan cewa yau sun hadu da shahararren bill adama domin tinda suka wanzu a wannan wuri ba a taba jeho musu mutun ya gagaresu hallakawa a cikin dakika sittin yau gashi sun shade kusan Rabin sa a suna artabu da mutum daga kacal alhali sunsha ragargaza mutane dubu cikin kankanin lokaci Ana cikin wannan dauki ba dadi ne sahibul haiiri ya sari daga daga cikin maridan a tsakiyar kai kawai sai yaga wannan maridin ya sulale kasa ya zama gawa koda ganin haka sai murna ta kama sahibul haiiri don yagano lagonsu nan fa ya wanzu yana saransu aka suna faduwa kasa matattu Yayinda .maridan su kaga yanayi musu wannan barna suma sai suka kara kaimi wajen kokarin hallakashi maimakon koka Inda suke su cafkeshi sai suka fara kaimasa Sara da suka da bugu da naushi A wannan lokaci nefa yakin ya sauya salo domin idan suka sameshi da

Naushi saikaga kamar an cillashi daga cikin kibiya Saidai kaga yaje ya manne da jikin garu akwai lokacinda babban cikin maridan yayiwa sarki wawan naushi a ciki saiyaga sahibul haiiri a sama ya manne da rufin dakin yana aman jini amma SBD juriya irin namaza bai yarda sun cafkeahi ba sai yaci gaba da saransu aka sukaci haba da mutuwa .......

YAYINDA maridannan sukaga suna dada cigaba da mutuwa sai suka rude kuma suka firgice suka rinka kaiwa sahibul hairi mummunan sara da suka shikuwa ya wanzu yana mai zilliya da goce goce a tsakaninsu a hakanne fa suka rike kashe kansu basu saniba saida aka shafe sa a uku ana wannan dauki ba dadi sannan gaba daya maridannan suka kare wato dai suka zama gawa shikuwa sahibul hairi saiya bingire kasa a sume saboda tsananin jigata wannan shine abinda ya shiga cikin fadar sarki barusa don daukar gatarin sihiri ++

Al amarin bawa haluf kuwa lokacinda ya farka daga barci sai ya nemi ubangidansa bai ganshiba kuma baiga taguwarsa ba saiya tabbatar da cewa aikin gama ya gama wato tuni sarki sahibul hairi ya shiga cikin birnin Askandariyya nanfa hankalin sahibul hairi ya dugunzuma ya rasa abinda ke masa dadi kawai saiya zauna yana shawarwari a cikin zuciyarsa abu na farko dai shine bai san halinda sarki sahibul hairi ke ciki ba a yanzu, zata iya yiwuwa ya hallaka kuma ko yana fafatawa da cikin garin haluf ya san irinsu sarki sahibul hairi basa faduwa da wuri sai dubunnan mazaje sun fadi abin tambayar a nan shine shin har yanzu ana nan ana fafatawar ko kuwa an gama? Haluf ya tuna cewa idan fa yace zai bi sahun maigidansa kuma aka gane cewa tafiyarsu daya shima sunansa gawa nan fa hankalinsaya kara dugunzuma musamman da ya tuna cewa shifa bakin fata ne duk inda ya shiga a cikin birnin Askandariyya ansan cewa shi bawa ne donhaka kamashi za ayi kawai acigaba da bautar dashi haluf na nan zaune cikin tunanin mafita kawai sai ya hango wadansu dakaru bisa dawakai kimanin su dari uku bisa dawakai a tafe suna kewaye wani keken doki cikin firgici bawa haluf ya mike tsaye zumbur jikinsa na karkarwa yana tunanin ya gudu ko ya tsaya shidai yasan cewa wancan ayari sun hangoshi don haka ma inyace zai gudu ai bashi da mafita don zasu iya kure masa gudu bisa wannan daliline haluf ya rungumi kaddara ya tsaya cak a waje daya yana jiran karasowar ayarin inyaso kome zai faru ya faru lokacinda ayarin ya iso daf da haluf sai sukaja tunga suka tsaya cak a gabansa kawai saiyaga an bude labulen keken dokin nan take wata kyakkyawar mace ta leko da fuskarta waje sukayi arba kallo daya haluf yayiwa matar yasan cewa mai sarautace saboda irin tufafin dake jikinta da kuma sarka, da awarwaron dake jikinta matar ta kurawa bawa haluf idanu tana mai murmushi a gareshi tace yakai wannan bakin fata yaya akayi kazo wannan gari namu kuma menene dalilin da yasa ka tsaya a nan baka shiga garin ba ka sani cewa a cikin birninmu gaba daya babu bakin fata koda guda daya kasancewar mijina ya tsaneku ni kuma a duniya babu abinda nake sha awa sama da na ajiye bawa baki ina kallonsa yana min hidima sa adda bawa haluf yaji wannan tambaya saiya risina cikin biyayya yace yake wannan ma abociyar kyau kiyi sani cewa a shirye nake na baki amsar tambayoyin da kikamin amma sai idan kin yi alkawari cewa zaki shigar dani cikin birninku a boye kuma cikin sirri ba tare da sarkinku ya sani ba kuma zaki boyeni har izuwa lokacinda zan kammala abinda ya kawoni kasarku yayin da taji wannan batu saita bushe da dariya tace karka damu duk zanyi maka yadda kake so yanzu saika sanar dani sunanka bawa haluf yayi murmushi yace sunana haluf ibn bilal' kyakkyawar ta maida masa da murmushi tace nikuma sunana gimbiya SHUKURA ni ce matar sarki barusa guda daya jal a duniya koda gama fadin haka saita kira shugaban dakarun dake jagorantar wannan tafiya wani zabgegen kato mai kirar sadaukai wai shi jamhas tace dashi yakai jamhas kasan bukatata wadda na dade a kan nemanta don cikar burin rayuwata wannan bakin bawa shine zai zamo sanadin cikar burina abinda nake so dakai shine ka sanar da gaba daya jama ar dake cikin wannan ayari namu cewa duk abinda suka gani ya faru a yanzu tsakanina da wannan bawa suyi shiru da bakinsu su bar komai a cikin sirri idan kuwa sirrina ya fasu gaba dayansu zasu zama gawa jamhas yayi murmushi yace an gama ya shugabata nan take yabi dakarun gaba daya ya sanar dasu sakon gimbiya sannan ya koma izuwa wajen barorinta mata suma ya sanar dasu sa adda ya komo ga gimbiya saita sake dubansa tace kuje da haluf izuwa keken dokin barorina mata ka umarcesu da suyi masa shiga irin tamu ta mata kuma su sa masa suturar mata koda haluf yaji haka sai hankalinsa ya tashi yace a ransa yanzu shi za a mayar mace aikuwa ba za a iya batar da kamanninsa ba koda anyi masa siffar mata mutum mai natsuwa da kula zai iya ganeshi har haluf yayi nufin yaki yarda da wannan sirri sai kuma ya hakura domin bashi da wani zabi wanda yafi yabi umarnin shukura ba tare da wani bata lokaci ba jamhas yakai haluf izuwa cikin keken dokin nan ya sanar dasu bukatar gimbiya nan take sukabi umarni suka kama aiki lokacinda barori mata suka kammala aikinsu sai suka dauko babban madubi suka sa a gaban haluf ya kalli kansa a ciki nanfa haluf ya cika da tsananin mamaki domin shi kansa bai gane kansa ba dukda kasancewarsa bakin fata saiya zamo farar fata kuma ya juye......

Zan dakata anan saikuma Allah yakaimu gobe zamu cigaba

Admin AA Misau Ke Magana

Zidane kd 

SARKIN SARAKAI

Littafi Na Daya (1)

Part E.

.

Marubucin littafin

Abdul Aziz Sani M/Gini

AA Misau Ke Magana

.

Labari ya isowa AA Misau Cewa..

.

DUK DA kasancewarsa bakin fata saiyaga ya zamo farar fata kuma ya juye zuwa kyakkyawar budurwa hatta gashin kansa anmaidashi dogo.

kuma baki sidik mai kyalli kirjinsa ya cika fam irin na mata ita kanta rigar da aka sanya masa irinta sarakaice abar a tsaya a kalla haluf ya dubi kansa da kyau sai yace a ransa lallai ashe inda mace aka yoni da na kasance daya daga cikin kyawawan duniya koda kuwa an barni a matsayin bakar fata koda aka kammala sauyawa haluf kamanni daga da namiji izuwa ya mace sai jamhas ya tafi dashi izuwa keken dokin gimbiye shukura tunkafin su karasa gareta ta zubo musu idanu tana murmushi gami da yiwa haluf wani irin kallo mai cike da alamomin tambaya bisa dole ya tsargu cewa lallai wannan mace nada wata babbar manufa a kansa ba tare da ya bata lokaci ba gimbiya shukura ta umarci haluf daya shiga cikin keken dokinta haluf ya waiga gaba da baya yaga gaba daya jama ar ayarin shi suke kallo cikin tsananin mamaki kawai saiya shiga cikin keken dokin ya zauna a gefe daya suna fuskantar juna shida shukura koda isowarsu bakin kofa sai suka iske kofar a balle a kasa makera na ta aikin kokarin gyarata don mayar da ita inda take koda ganin haka sai gimbiya tabada umarnin a tsaya a gaban sarkin kofa A lokacin da sarkin kofa da wadansu sababbin abokan aikinsa suka risina ga gimbiya suna masu yi mata barka da zuwa gimbiya shukura ta dubi sarkin kofa tace menene kuma ya faru naga kofar birnin nan a balle shin giwace tayi mana wannan barnar? Sarkin kofa ya risina yace ranki ya dade ai wannan ba aikin giwa bane wani shahararren mayakine waishi sarki sahibul hairi yazo don ya rabamu da gatarin mu na sihiri yanzu haka ya zama gawa domin sarki ya jefashi cikin gidan masifa na karkashin kasa dake fada koda jin wannan batu sai hankalin bawa haluf ya tashi bai san sa adda gumi ya tsatstsafo masa ba nan da nan fuskarsa ta cika da alamomin tashin hankali yayinda gimbiya shukura ta dubi fuskar haluf ta lura da sabon yanayin daya shiga sai kawai tayi murmushi tayi umarnin aci gaba da tafiya nan take kuwa aka kara nausawa cikin birnin askandariyya lokacinda su gimbiya shukura suka iso fada sai suka iske an gama walimar da ake yi har sarki ya mike ya shiga gida jama a sun fara watsewa kowa na kama gabansa koda aka ga zuwan gimbiya sai aka rabe aka bata hanya kuma ana kwasar gaisuwa gaba daya dawakai suka iso wajen tsayuwarsu aka tsaida su sannan su gimbiya da bakuwarta suka fara gitowa daga cikin keken doki amma bakuwar tasha lullubi ba a iya gane ko wacece nan dai su gimbiya suka shige izuwa cikin gidan sarautar kuyanginta da barorinta na take mata baya su kuwa su jamhas sai suka watse koya ya tafi izuwa nasa gidan A ka ida duk sa adda gimbiya shukura tayi tafiya ta dawo saita aikawa da sarki cewar ta dawo yana jin haka zai tako da kafarsa yazo har turakarta su zauna ta bashi labarin abubuwan da suka faru yayin tafiyarta da dawowarta in banda irin wannan lokaci sarki barusa baya zuwa bangaren gimbiya shukura A wannan karon kuwa sai al amarin ya sauya domin tana shiga cikin turakarta bata zauna hutawa ba sai kawai ta tafi izuwa bangaren da kanta amma kafin ta tafi ta umarci kuyangi dasu yiwa bawa haluf wanka su cire masa tufafin da aka sa masa na mata a takaice dai adawo masa da siffarsa ta dai dai kamar yadda yake a matsayinsa na da namiji sarki barusa ya kishingide a cikin turakarsa cikin nishadi yana hutawa kawai sai yaga gimbiya shukura ta taho gareshi cikin tsananin mamaki ya mike tsaye ya tareta cikin tsananin farin ciki suna annashawa gaba dayansu A duniya babu abinda sarki barusa keso sama da gimbiya shukura don haka ko kadan baya son abinda zai bata mata rai komai kankantarsa sarki barusa ya dubi gimbiya shukura cikin murmushi yace yake abarkaunata yau kuma menene dalilinda ta hanaki turo a sanar dani dawowarki domin na taho turakarki mu zauna kamar yadda muka saba? Koda jin wannan tambaya saita maida masa martanin murmushin tace yakai rabin raina rabin jikina kayi sani cewa ba komai bane ya haddasa hakan ba face tsabar farin ciki domin wannan karon nazo ma ka da labari mai dadi ka sani cewa a wannan tafiya da nayi na ziyarci wani mashahurin boka wanda ya bani magani yace indai na sha wannan magani lallai zan samu ciki dakai na haihu a cikin shekara guda koda barusa yaji haka saiya cika da farin ciki ya sake kankame shukura a kirjinsa yana dariyar murna yau shekara goma sha biyar kenan da yin auran gmbiya shukura da sarki barusa amma basu taba samun haihuwa ba bayan shekara daya da yin auransu sukaga basu samu juna biyu ba sai hankalinsu ya dugunzuma suka bazama neman magani amma ba a dace ba saboda ganin yadda barusa ya damu matuka da neman haihuwa saita bashi shawarar ya sake yin wani auren ya gani domin babu mamaki matsalar daga gareta ne da farko da barusa yaki yarda da wannan shawara sbd sonda yake mata amma data matsa saiya amince saida sarki barusa ya auri mata goma sha daya lokaci guda amma da aka shekara yaga babu haihuwa duk ya koresu ya rungumi kaddara.......

TUN daga wannan rana shukura ta cigaba da yin tafiye tafiye izuwa kasa kasa da ziyarar manyan bokayen duniya akan neman masalaha ranar da taje wajen wani mashahurin boka waishi KUMATU saiya yi bincike ya gano cewa matsalar haihuwarna tare da sarki barusa har abada bazai taba haihuwa ba ita kuma gimbiya shukura bazaata taba samun juna biyu ba face ta kwanta da namiji saurayi wanda shekarunsa basu kai talatinba wanda bai taba tarawa da ya mace ba kuma doleneya kasance bakin fata lokacinda gimbiya shukura taji wannan batu saita kamu da tsananin bakin ciki ta fashe da kuka saida ta dade tana kuka sannan tayi shiru ta dago kai tana mai duban boka kumatu hawaye na zuba a idonta.yace yakai wannan boka ina sonka sanar dani yadda zan gane saurayi mai wadannan suffofi duk sa ar da na hadu dashi boka kumatu yace duk ranar da kika hadu da wannan saurayi kina yin arba dashi zakiji ya kwanta miki a rai ma ana nan take zakiji sonsa to lallai in kikaji haka sine kadai saurayinda zaki tara dashi ki samu haihuwa in kuwa ba hakaba harki mutu ba ke ba samun da gimbiya shukura bata da wani buri wanda yafi ta haifi danda zai gaji mijinta wato sarki barusa domin ta san cewa duk ranar da sarki barusa ya fadi ya mutu dolene ta bar gidan sarautar domin wanine daban daga cikin fadawansa zai karbi mulkin bayan gimbiya shukura da sarki barusa sun gama murnar wanann labari datazo dashi sai tayi masa sallama akan cewa zata tafi dakinta ta kwanta domin ta huta gajiyar tafiya ba tare da gardamar komaiba yayi mata izinin tafiya, lokacinda gimbiya shukura ta iso cikin falon turakarta ta iske bawa haluf a zaune an caba masa ado kyawunsa yakara baiyana kururu a baiyane saita kamu da matukar sha awarsa kai tsaye ta nufo inda yake da zuwa saita yunkura da nufin ta rungumeshi cikin tsananin tsoro ya zame jikinsa ya mike tsaye ya koma can gefe daya ya dubeta cikin biyayya yace haba ya shugabata shin kin mantane cewar ke matar sarki ce sokike a tsireni idan aka kamani da laifin yin wani abu dake? Sa adda taji wannan batu saita kyalkyale da dariya sannan tace yakai wannan ma abocin kyau da kwarjini ka saki jikinka ka sani cewa duk abinda zamuyi a nan babu mai ganinmu yanzu dai kafin wani abu ya wakana a tsakaninmu ina son ka amsa min tambayoyin nan guda biyu da nayi maka tun farkon haduwarmu' kodajin haka sai haluf ya kirkiri karya ya shara mata yace ai shi bawane ya gudo daga hannun ubangidansa da ga can wata kasa da ake kira SHUBUR kuma ba komai bane ya sa ya gudo ba sai don tsananin aikin wahalar da ake sa shiyi kullum lokacinda ya gama wannan jawabi sai gimbiya shukura ta dubeshi ta kyallkyale da dariya tace haba dan samari ka dubeni da kyau kai kasan cewa ni ba yarinya bace karama kuma ina da kaifin tunani da lura ai fatar jikinta mutum ya duba ya san cewa a dduk inda kake baka shan waahala tun da dai ba zaka gaya min gaskiya ba ni yanzu zan sanar dakai ko kai waye . Yakai haluf ka sani cewa tundazu da muka dawo gida kafin naje ga mijina saida na shiga cikin wani daki na na sihiri inda nake tafiyar da harkokin sihirina yi bincikena na gano cewa kazo wannan birni namu ne tare da maigidanka sarki sahibul hairi na birnin misra domin ya rabamu da gatarinmu na sihiri sbd da wannan gatari ne kadai zai iya balle kofar gidan boka SHAMZUBUL AZWAS wanda ke can tsuburin tekun bahar zallus domin ya dauko karamar yarinya Alfila wadda ta kasance yace ga wani gagarumin sadauki waishi Awaisu yakai haluf kayi sani cewa nima na dade ina neman wannan yarinya alfila na rasa yadda zanyi na sameta saboda na kwashe sirrikan tsafin dake jikinta na dawo dasu jikina don cika burina na biyu a duniya burina na farko shine na haifi da wanda zai gaji sarautar birnin Askandariyya bincike ya nuna mini cewa kaine kadai namijin da zan kwanta dashi na samu haihuwa don haka ina bukatar hadin kanka ayanzu sa adda shukura tazo nan a zancenta saitaga hawaye na zuba a idanun bawa haluf al amarinda ya matukar bata mamaki kenan ta dubeshi tace kai kuwa menene dalilin zubarda wannan hawaye a idanunka? Haluf yace aini yanzu bani da sauran buri a duniya face mutuwa tunda babban masoyina mutumin da nafi shakuwa dashi fiye da kowa babu shi wato sahibul hairi naji dazu sarkin kofa yana bayanin cewa an jefa shi cikin dakin masifa na karkashin kasa ya hallaka bisa wannan dalili nake ganin cewa rayuwata bata da sauran amfani don haka kashe kaina zanyi koda gama fadin haka sai bawa haluf ya sa hannu cikin rigarsa ya dauko wata zuka ya daga sama da nufin ya caka a cikinsa aman sai gimbiya shukura tadubi hannunsa da kwayar idanta take wata irin iska mai karfi ta rike hannun haluf ya kasa cakawa kawai saiji yayi an fisge waukar daga hannunsa anyi jifa da ita can gefe cikin tsananin firgici da mamaki haluf ya zauna kasa dirshan yana mai kallon gimbiya shukura ita kuwa saitayi murmushi ta tako kafafunta tazo daf dashi ta tsugunna suka fuskanci juna tace.


KUMA TAKUN KARSHE.

GIMBIYA SHUKURA tacigaba da cewa aibazan bari ka mutu ba face na cika burina dakai ka kwantar da hankalinka ka sani cewa maigidanka sarki sahibul hairii na nan a raye bai mutuba.

Yanzun nan zan nuna maka zahiri ka gani, gama fadin haka keda wuya saitayi nuni da dan yatsanta guda izuwa jikin bango take wani irin haske ya fito daga cikin dan yatsanta ya dira a jikin bangon saiga hoton sahibul hairi kwance a sume cikin dakin nan na maridai a tsakiyar gawarwakin maridan A lokacinne ya farfado daga dogon suman da yayi ya mike ya zauna da kyar yana ta faman haki kamar zai mutu.

Ko ina a jikinsa rauni ne yai kaca kaca da jini gimbiya shukura ta dubi bawa haluf tace kaga halin da maigidanka ke ciki akwai dakuna goma sha biyu kowanne dakina dauke da masifa iri iri masifunda suke dakunan gaba sun ninka na baya yanzu ya wuce dakuna biyu saura goma a gabansa. Idan har ya wuce ta cikin ragowar dakunan goma yana raye yaci jarrabawata, don haka zan taimaka masa mu sace gatarin sihiri tare mu tafi izuwa gidan boka shamzubul Azwas dan dauko yarinya Alfila. Abinda nake soka gane shine zamu hada karfi da karfe ne domin nida shi kowa ya biya bukatarsa amma duk wannan zata farune idan ka bani hadin kai ka sadu dani yanzu' 'lokacinda haluf yaji wannan batu sai hankalinsa ya tashi fiye da ko yaushe ya rasa abinda zaice kawai saiya kurawa gimbiya shukura idanu yana mai al ajabin al amarinta . Wannan shine abinda ya faru tsakanin gimbiya shukura da bawa haluf bayan ta sa an sauya masa kamanni an shigar dashi ckin birnin askandariyya ba tareda sanin sarki barusaba ++ ++

Al'amarin jarumi uban jarumai kuwa wato sahibul hairi lokacinda ya farfado daga suman da yayi ya tsinci kansa cikin tsakiyar gawarwakin maridannan guda dubu yaga har yanzu gashi yana numfashi bai mutuba sai ya cika da mamaki kuma ya shiga tunanin zuci yace a ransa. '' wannan fa shine mataki na fardo da zanbi don biyan burina Amma gashi bani da tabbacin zan kai gaci yaushene zan samu nasarar daukar gatarin sihiri a cikin wannan gidan sarautar sannan na tafi gidan boka shamzubul azwas don dauko yarinya alfila na tabbata cewa masifar dake can fadar boka shamzubul azwas ta ninka wacce ke nan sau dubu idan ma na sami nasarar dauko Alfila yay tafiyarmu zata kasance nida sadauki Awaisu don neman wadannan 'yan matan uku wadanda zan Aura na cika burina na duniya......

Shin zamu sami nasarar ganin yan matan kuwa Alhalin babu wanda yasan a inda suke? Koda sarki sahibul hairi yazonan a tunaninsa sai yaji nadama tazo masa bisa gagarumin aikin daya daukowa kansa nan take zuciyarsa ta karaya ya fara aiyanawa a ransa cewa lallai a cikin wannan tafarki zai rasa rayuwarsa, gwarama ace ya rungumi kaddara ya zauna da talaucinsa har ajalinsa ya riskeshi... ¤ + + + + + + + ¤

SHIN BAWA HALUF ZAI AMINCE YA BIYAWA GIMBIYA SHUKURA BUKATARTA? .

SHIN SARKI SAHIBUL HAIRI ZAI IYA SHALLAKE MASIFUN DAKE CIKIN RAGOWAR WADANNAN DAKUNA GUDA GOMA? .

INA LABARIN GALADIMA AMINUL HAS WANDA SARKI SAHIBUL HAIRI YABAR MASA RIKON KASA, KUMA YA KASANCE A CIKIN TASHIN HANKALIN MAHASSADA .

marubucin yace mu hadu a SARKIN SARAKAI kashi na biyu donjin ci gaban wannan kasaitaccen labari. anan Nake cewa mu hadu a cikin littafi na biyu domin jin yadda zata kasance a wannan kasaitaccen labari 

Admin

AA Misau Ke Magana

Domin samun wasu sabbin littafe mu 08161272634


0 Response to "SARKIN SARAKAI Hausa Novel"

Post a Comment