-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Ramos da Varane da Camavinga da Coman da Messi, Ronaldo da Griezmann

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Ramos da Varane da Camavinga da Coman da Messi, Ronaldo da Griezmann

Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Ramos da Varane da Camavinga da Coman da Messi, Ronaldo da GriezmannƊan wasan Sifaniya mai shekara 35 Sergio Ramos, zai duba lafiyarsa a Paris a yau Talata gabanin komawa Paris St-Germain bayan bankwana da Real Madrid. (ESPN)

Ɗan wasan Sifaniya mai shekara 35 Sergio Ramos, zai duba lafiyarsa a Paris a yau Talata gabanin komawa Paris St-Germain bayan bankwana da Real Madrid. (ESPN)

Manchester United ta shirya kashe £50m domin sayen ɗan wasan Real Madrid Raphael Varane, da £25m kan ɗan wasan Rennes Eduardo Camavinga, mai shekara 18, yayin da take ci gaba da kashe kuɗaɗe domin yin zubin sabbin ƴan wasa. (Marca via Mail)

Shugaban Bayern Munich Oliver Kahn ya jajirce wajen ci gaba da rike dan wasan Faransa Kingsley Coman a ƙungiyar duk da zawarci da Liverpool ke nuna wa kan dan wasan mai shekara 25. (Mirror)

Paris St-Germain ta bai wa Lionel Messi kwantiragi bayan karewar wa'adin yarjejeniyarsa da Barcelona a makon da ya gabata. Ɗan wasan mai shekara 34 ya taimaka wa ƙasarsa wajen kai wa wasan dab da na karshe a Copa America duk da cewa yana cikin rashin tabbas a kungiyarsa.(Mail)

0 Response to "Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Ramos da Varane da Camavinga da Coman da Messi, Ronaldo da Griezmann"

Post a Comment