-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Kalaman soyayya Masu Sanyaya Zuciyar Masoya

Kalaman soyayya Masu Sanyaya Zuciyar Masoya

Kalaman soyayya Masu Sanyaya Zuciyar MasoyaSlm amincin Allah ya tabbata ga wannan kyakykyawan saurayi mai zazakar murya .muryar da take sa kunnuwan mai saurare cikin dausayin kauna ka zamo Abun so da muradin malaka ga duk idaniyar da tayi araba dakai.  Kai sarki ne mai cike da dogon zamani kyakykyawa son kowa kin  wanda ya rasa.

Masoyiyata, ina son ki fiye da yadda kike so na. Ina son kasancewa tare da ke domin kina farantawa zuciyata. Kallon ki kaɗai kan sanya in samu kuzari, duk wata kasala da lalaci in ji ta gushe. Ke ce farin cikina.

TAURARON ZUCIYATA.Kaine  mafi tsuma zuciya da nishad'i mafi 'karfin kore damuwar zuciyata basu kasance a tare da ni ba sai bayan da na had'u da kai. Kai ne ka zamo tauraron da hasken sa yayi sanadiyar raba zuciyata da ba'kin duhun da ta dad'e a ciki. Had'uwa da kai ya kawo canji mai yawa a cikin rayuwata. Ka huta lafiya. Ina Son Ka.

Na gaskata cewa tasirin dake boye a cikin muryarki  sinadari ne dake gusar da damuwa ga duk wanda ya saurareta Aduk lokacin da naji muryarki  inajin tamkar a wannan lokacin aka Halicci farin ciki.

kallon farko da nayi miki na fahimci cewa kina da baiwar da Duk wani da namiji zaiji yana soki.  baya ga haka ke kyakkyawace , na dade ina neman hanyar da xan furta maki soyayyata sai dai xuciyata tana jiye min wani abu, daxaki amince da syyyt da nayi farin ciki domin na dade ina fatan naga cewa mun xamo masoyan juna ni da ke, hakik babu wata makusa a gareki domin kinada kyawun da kowa zaiso yayi rayuwa dake.

Ina ma ace kin fahimci cewa *ina sanki,* Nasan Abune mai wuyar fahimta  *Gane so* Ba tare da an furta ba.  Na fahimci cewa Duk wani masoyi *marar lfy ne.* Amman tsanani rashin lfy shine kana son wani Amman ka kasa fada masa. *Son maso wani*  itace rashin lfy da tafi kowacce wahalar da gangar jiki.

A Ciki soyayya Akwai Adalci Da rukon Amana  Aduk lkc Da ka rabu da wanda yace yana sanka  Ba shakka ka karya Alkawari Kuma kaci Amana.

Kaso duk wanda yace yana sonka Idan har ba mugunta zakayi ba Wannan shine  Dokar soyayya. A kwai alajabi acikin rayuwar Wanda kake so da Wanda yake sonka. nutsuwar zuciya shine samun kyautatawa daga wajen wadda take so Yarda da juna shike sa a sami Aminci. A kullum burina shine samar da mafita ga masoya. Zaku iya aiko da sakon ku ta hanyar comment.

Kaso a soka yafi komai dadi a soyayya. Samun masoyin gaskiya akwai wahala a wannan lokaci. Fadi ra'ayinka game da So. Nidai game dani shine "So cutane dayake raunata gangar jiki" Maganin cutar shine " aure".

Babbar kyauta da muhimmanci a gareni shine samun ganin kyakykyawar fuskarki. burina shine naga bayyanar fitar murmushi akan kyakykyawar fuskarki. Kuma ace nine sanadin yinsa . Inaso ki fahimci cewa burina a koda yaushe ki kasance cikin farin ciki.

SINADARIN RAYUWATA SO shine abinda ya dunkule zuciyoyinmu wuri daya muka tsinci kanmu a cikin soyayya Ina fatan bazaki bari wani dan Adam ya shiga tsakaninmu ba Ina sonki Ke tamkar zinarece a cikin rayuwata Idan na rasaki zanyi rayuwar da babu armashi a cikinta***Ki rikemin amanar kanki

Bakowa Akeba Mallakar Xuciyah Va Sai Wanda Yasan Darajarta. Nakanji Dadi Idan Naga Ana soyayyah, Saidae Kash! Nakanji Tausayin Wanda Yarasa Mai Sonsa. Shin Ko Kunsan Radadin Dayake Tattare Da Quncin Ravuwa Da Masoyi? Haqiqa Soyayyar Gaskia Tanada Ampani, Kuma Kariqe Wanda Yace Yana Sonka Koda Da Wasa Ne, Domin Ita Kalmar So Daga Wasa Takan Iya Xama Gaskia. Kaxauna Dakowa Lapia Shine Wayewa. Qauyanchi Shine Rashin Sanin Darajar Mutane Da Kuma Wulaqantasu, Koda Kasanya Tupapin Xinare A Jikinka Idan Bakasan Darajar Mutane Ba To Wallahi Sunanka BAQAUYE.!!! dafatan xamu kula da masoyanmu.


TABBACIN SO Tabbas nasani cewa ban kasance farkoba ban kuma zamo karshan furta kalmar so agarekiba domin kuwa zuciya da marari ba'a hanata abinda take kauna wanda koda an haneta hakurinta bai wuce kaddaraba. Har a kullum bakina ya saba furta kalmar so agareki wanda ban taba canza batuna akan hakan domin baiyanarki ta kasance tamkar fitowar hasken rana a kowanne lokaci wanda ganina baya samuwa sai dashi hakan yasa nake kallanki a matsayin jagora wacce zuciya ta kasance mai yin alfahari sannan ta amintarwa kanta zabi mafi dacewa agareta.

7 Responses to "Kalaman soyayya Masu Sanyaya Zuciyar Masoya"