-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

A ZATO NA Hausa Novel

A ZATO NA Hausa Novel

  *⋆☆A ZATO NA...!☆⋆* 




        *⋆©Jeedderh Lawals⋆*





                             *☆⋆01⋆☆*






              Assalamu Alaikum wa Rahmatullah. Muna kara godiya da taruwarku a wannan zaure mai albarka, ina fata Allah Yasa mu gama lafiya kamar yadda zamu fara lafiya. 


Littafin 'A Zato Na' mallakin wadda ta rubuta ne, ba'a yarda wani/wata su canza kowace irin suffa ta wannan littafi ba. 


Muna fata zaku rike mana alkawari, ku kuma rike mana amana. Allah Yasa mu dace. 

_Da sunan Allah Mai Rahma Mai jin Kai'_






'Kirr! Kirrr!!'...


Karan daya ziyarci kunnena kenan lokacin da na danna lambar wayar kawata Janan. Bata dauka nan take ba, sai da yayi kara kamar sau biyar. 

Kafin ta dauka hakurina ya gama karewa, saboda haka tana dagawa, ban bari ko sallama tayi ba na tare ta da; "wai dallah can malama me kika tsaya yi ne kin tsaida mutane?".


Tace "jeez girl, bi a hankali mana. Ina jiran Anty Raheemah ne ta dawo kafin in fita".


Na ja dan siririn tsaki, "kawai ki fito ki bar mata gidan a haka mana. Ba maigadi yana nan ba?". Janan tayi ajiyar zuciya, "kin fa san abinda ya faru last time da nayi haka. Tace an shiga an mata satar kudi da jewelries, kuma dole sai da Yaya Bilal ya biyata sannan aka zauna lafiya, bana son abu makamancin haka ya sake faruwa". Nace "sai kiyi ta zama ai ta mayar da ke maigadinta. Ni dai wallahi idan baki zo nan da mintuna goma ba ko? Sai dai mu hadu da ke acan kawai!". Ban jira ta kara cewa komi ba na kashe wayar na ajiye ta a gefena. 


Browsing naci gaba da yi da system dina, sai da nayi kamar minti goma sha biyar kafin na kashe na ajiyeta a mazauninta. Janan na sake dannawa kira, tana dauka tace "gani nan don Allah, sarkin gajen hakuri kawai!". Na tabe baki ba tare da na damu da abinda tace ba, nace "better. Idan kin iso ki kira ni kawai mu hadu a main entrance" tace "toh".


Gadona na dan gyara kafin ta iso. Zuwa lokacin da Janan ta kirani, na gama kimtsawa. Na dauki gyale na nada shi a kaina yadda ya zagaye rabin kirjina da bayana, na dauki wayar hannu, purse da flat din takalmi ruwan goro kalar veil dina da zanen flower da yake jikin doguwar rigar gown ta atamfa da na sa, na zura shi a kafata. Aylah, roommate dina na yiwa sallama na fita. 


A bakin hostel din Queen Amina dake cikin campus din ABU Zaria, na tsaya ina karewa wajen kallo cikin neman Janan. Ina kokarin kiranta a waya na hango ta acan inda ake parking motoci a gefen hostel din tana dago min hannu, murmushi na saki cike da murna da dokin ganinta na taka a nutse na tsallaka zuwa inda take. A tsakiyar wajen ta tareni, muka rungume juna cike da doki. Duk duniya, ita kadai ce naki jinta kamar wata yar uwata ta jini, kamar yadda nasan itama haka take a bangarenta. 


Na kalli iNext din da naga ta fito daga ciki ina daga mata gira, "Ya Almu ya sake sabuwar mota ne hala?". Ta girgiza kai tana murmushi, "ina Almu na yayi arzikin sayen irin wannan abun? Yaya Bilal ne". Na dan zare ido cikin mamaki, "Holy Wow!! Yaushe rabon da in ga Yaya Bilal? Har na manta wallahi. Yau dai Allah ya nufa zamu hadu kenan!". 

Tayi dariya da tasa dimples dinta suka lotsa, abinda yake burgeni da haliitar ta kenan. Tace "sosai ma. Allah ne yasa ban samu abin hawa da wuri ba, shine yace bari ya kaini tunda shima wajen FCE din yayi. Taho muje, muna kara makara". Na bi bayanta zuwa wajen motar. 


Janan ta bude gidan gaba, ni kuma na bude baya muka shiga a lokaci guda, bakina dauke da sallama. Sansanyan kamshin freshener na cytrus da mix din strawberry ya doki hancina hade da sansanyan sanyin AC daya dumame motar. Muna tsakiyar watan May ne, saboda haka ba karamin zafi muke sha ba a garin na Zaria. 


A nutse na gaishe da Yaya Bilal, ya juyo a kaikaice ya amsa tare da juyawa ya tashi motar muka bar wajen. Babu abinda na iya kararwa game dashi sai cewa faded jeans ne a jikinshi da T-shirt mai zanen zebra a jiki, sai sunglass da ya saka ya sakaya idanunshi.


A hankali yake tukin, tattausar kira'ar Sheikh Malam Minshawee tana tashi cikin suratul-Kahf, na jingina kaina da kujerar motar na lumshe idanuna, a can kasan zuciyata kuma ina bin kira'ar bi da bi. Yayin da a gefe guda, shi da Janan suke hira jifa-jifa. Har muka isa makarantar Kongo, inda zamu je, a bakin gate ya nemi waje yayi parking. Sai a baki-baki ma yayi parking din, saboda yadda wajen ya cika da mutane da ababen hawa. Muka mishi godiya muka fita, ya ja motar ya tafi, mu kuma muka tunkari gate din makarantar. 


Ranar babban Shehin malami, ' Dr. Bilal Philips' yake zuwa yin wa'azi. Saboda haka, you can only imagine yadda wajen zai cika da mutane wai don ma na mata ne zallah. Duk da mun zo kusan mintuna arba'in kafin a fara wa'azin, da kyar muka samu wajen zama muka zauna. 


Akan Matan da zasu shiga aljanna yayi wa'azin ranar. Kafin ya gama, jikin kowace diya mace dake wajen yayi sanyi saboda yadda ya dinga zano abubuwa da mu mata muke yi, muna tunanin ba wani abu bane, either ga junanmu ko ga mazaje da iyayenmu, alhalin abubuwan nan za su iya jagorantarmu zuwa wuta. Karfe sha biyu na rana aka gama wa'azin, saboda karancin abubuwan hawa da aka yi ranar, bamu samu mun koma cikin makaranta ba sai kusan karfe daya da rabi. 


A dakina muka sauka, Janan tayi sallar azuhur, kafin ta gama ni da bana yin sallah na gama dafa mana jollop spaghetti. Bayan mun gama cin abincin, kan gadon muka hau, na kunna mana film din Pick the Stars, wani Korean Film, muna kallo. Bamu jima da fara kallon ba, barci ya daukeni.



"Na'ilah!".

"Uhmn?" na amsa cikin barci. 


A hankali naji an kai tattausan hannu gefen fuskana an shafa cike da wani irin tenderness da yasa naji bugun zuciyata ya canza sosai. "I Love You, baby! So much!!".

Aka fadi a daidai saitin kunnena, cikin wata irin tattausar murya. A hankali na bude idanuna dake cike da barci, mutumin da ke zaune a gefen gadon da nake kwance, appears very blurry, bana iya ganinshi cikin rashin hasken dakin. 


"Na'ilah?" naji ya sake kirana cikin tattausar muryarshi, na saki murmushi a tausashe ina amsawa, "uhmmn??".


"Na'ilah!!". Wannan karon naji an kirani da karfi. A gigice na tashi zaune, kaina ya bugu da bango. Da sauri na dafe wajen na maida kaina kan pillow ina hararar Janan dake zaune a gefena, tana kallona cike da alamun tambaya.


Harara na jefa mata tun karfina, cikin tsiwa nace "dallah can Malama meye haka, zaki katse min barcina mai dadi?".

Ta daga kafada, "maganganu kike yi cikin barci. Abin naki ya dawo ne?".


Na kara komawa kan katifar na kwanta, "Wallahi kuwa Jan. Yaushe rabon ma da inyi irin mafarkannan? Har na manta. Sai yau". 

Janan tace "to sai ki kiyaye da addu'o'i dai. Is'haq yazo yana jirana a waje, bari in tafi".

Na duba naga yamma har tayi.


Na mike ina lalubar mayafi na, "muje in miki rakiya to!".


Ta tashi na rufa mata baya, dakin na rufe kasancewar abokiyar zama na bata dawo ba, muka sauka kasa ni da ita. 

Har parking lot na rakata inda Is'haq yake jiranta. Ta bude gidan baya ta shiga, na maida mata kofar na rufe ina daga mata hannu, a haka suka tafi. Sai da na tsaya anan kofar hostel din na sayi yoghurt babbar roba mai sanyi sannan na koma daki. 


Bayan na yi yan gyare-gyare da kimtse-kimtse na, arm chair na dauka na ajiye a gefen gadona na zauna, na dora laptop dina akan gadon na bude tare da cigaba da kallon da muka fara ni da Janan. 


Sai bayan magriba Aylah, roommate dina ta dawo. Har zuwa lokacin ina kan system dina, ta min sallama na amsa, a gajiye ta zauna a gefen gadonta. Sai da ta huta, sannan tayi sallah. Taci sauran spaghetti din da muka bari ni da Janan. 

Ni kam karfe bakwai tana yi, na kashe laptop din na mike. Kasa na sauka inda common room yake, na kalli serieses din da nake kallo a Zee World; Twist of Fate da King of two Hearts. Karfe tara na koma daki, ina zuwa shirin kwanciya barci nayi cikin riga da wando, na bi lafiyar katifa na kwanta. 


Hira muka fara da Aylah, tana bani labarin abinda ya faru a wajen bikin da taje ranar. Wai mutumin mace ta biyu ce zai aura, wadda ta kasance kawarsu ce. Shine a wajen lunch party, matarshi ta farko taje da tawagarta, aka yi rashin mutunci dai yadda ya kamata. 


"Dama duka yaushe ne Yayan su Afrah kawata zai sake aure, amaryar ta hadu da uwargidan a shagon saloon. Wallahi tsiyar da aka yi a wajen sai ta baki mamaki. Kaca-kaca suka yi wa juna. Bayan anyi auren kuma da sati biyu, ya dankarawa uwargidan nashi saki. Naji ance kusan watannninta biyu a gida, sai kwanannan ta koma".


Nayi ajiyar zuciya tare da girgiza kai. Abinda yawancin mata suke jin tsoro game da kishiya kenan, taje ta fitar dasu daga gidansu. Ko ta hana su zaman lafiya da miji. Ko ta zauna, haka zaka kare rayuwarka cikin tashin hankali, fargaba da takaici. 


Aylah ta cigaba da cewa, "ni wallahi gani nake babu wani aibu game da wata kishiya. Ba abokiyar zama bace? Menene a ciki? Idan dai ka kwantar da hankalinka, tsaf zaku yi zaman lafiya da ita wallahi!'.


Na kada idanu, "baki san komi ba game da kishiya Aylah. Kiyi shiru kawai. Ina tunanin duk danginki babu wadda take zaune da kishiya ko?".

Ta daga kafada, "Anty Hanifa ce kawai, kuma suna zaune da ita lafiya lau".


A hankali murmushi ya subuce min, "to wannan sa'a ce tayi ba karama ba, ina gaya miki. Wallahi da tayi rashin sa'a, gabadaya sai ta girgiza family dinku saboda sanabe".

Aylah ta girgiza kai, "naa. Bana tunanin haka. Kada dai kice min, baki son kishiya Na'ilah?!".


Murmushi kawai nayi, na gyara kwanciyata tare da mata sai da safe.



Dare ya tsala matuka, yayin da barci ya gagari idanuwana. Zuciyata tayi wani irin nauyi, ji nake kamar an dauki wani gungumemen dutse an dora min a kai, numfashi ma sai da naji ya fara gagarata. A hankali na janyo wayata da headphone na hada, na kamo kira'ar Sheikh Malam Ahmad Suleiman na kunna. Idanuwa na lumshe a hankali, ina bin kira'ar a cikin raina. 


To say that na tsani kishiya, is an understatement. 


I despise her! Na tsaneta with all my being.


Tunanin zama da kishiya kadai a cikin raina, yana sa jinin jikina tafasa, zuciyata zafi kamar ana diga ruwan dafaffiyar dalma. 


Allah Ya gani, bana son kishiya. Ina kuma da yakini a cikin raina, ko zan mutu tuzuruwa, sai dai hakan ta faru, amma ba zan taba zama da kishiya ba!!. 


And why not, you might ask?! 


A shekaru na bakwa a cikin rayuwata, na dandana zafin kaidi irin na kishiyar uwa, a wani unfortunate dare, da na kira 'bakin dare'. 


Ranar mahaifina yake sake aure, kyakkyawar bafulatanar mata, fara doguwa, tsayi wanda ta tafi gabadayanta ta mike, babu lankwasa ko duk'awa, har yau ina mamakin dalilin da yasa Baba ya aureta. 


Idan kyawune, mahaifiyata tana daya daga cikin kyawawan cikin danginsu, kasancewarta ruwa biyu, shuwa-arab da barbanci, yasa ta kasance mace daya tamkar dubu. Kyawu, ladabi, biyayya, iya girki, kwalliya, kada ma ayi maganar tsafta, don gani nake duk duniya, babu na biyun mahaifiyata a tsafta. 


Saboda haka, dalilin auren Babana da bafulatana Ramata, kazamiya mara kira, still remains a mystery, yet to be solved to me. 


Bana taba manta ranar da aka kawota gidanmu, ina ta murna an kawo min wadda zan kira Anty na. Masu kai amarya sun shigo da habaici, suka tafi da bakaken maganganu a bakinsu, duk mahaifiyata da abokanta yan dannar cinya suna jinsu, amma suka kauda kai kamar basu ji ba. Wannan abu ya bakanta musu rai.

Wata daga cikin kawayen Mama da ta kasa kau da kai, ta tanka musu. Ba bata lokaci suka hau zage-zage, kamar dama jira suke yi, ko kuma da guzirin zagin suka shigo. Da kyar aka ba Iya Lami hakuri, su kuma suka tafi. 


Bayan tafiyarsu babu jimawa, suma yan dannar cinyar suka mana sallama suka tafi, suna ta kara ba Mama na hakuri. Ni kam ina zaune muk'u a lokacin, ina jiran Mahaifina ya dawo. Bai dawo ba har barci ya daukeni. 


Can zuwa cikin dare, hayaniya ta tasheni. Ba wai kuma normal hayaniya ba, kukan mahaifiyata ne ya tasheni wanda nake jiyowa yana tashi daga can dakin Babanmu.

Kasancewar gidanmu dakuna hudu ne, biyu suna kallon biyu. Dakin Mama shi yake kallon na amarya da Baba. 


Daga tagar cikin dakin Mama na leka, ina hangen ta tsugune a gaban Baba. Matar da aka kai mishi a matsayin amaryarshi, a zaune a gefenshi kamar zata hau cinyarshi, tana ta wani firirita. Ban jiyo abinda suke cewa ba, daga karshe dai na ga Mama ta tashi ta fado daki da sauri. 


Babu bata lokaci ta hau lalubar mayafi, ta yafa nata, nima ta miko min nawa. Ina tambayarta 'Ina zamu je Mama?', amma saboda tsabar kuka da take yi, ta kasa amsa min. Hannuna kawai ta kama ta ja muka fita daga dakin.


A bakin kofa, mahaifina ne a tsaye, kamar wanda yake jiran ta fito. Muna fita, ya kamo hannuna ya rike. Har yau ina tuna maganganun daya fada mata clearly, 

"Kada ki kuskura kiyi tunanin zaki tafar min da diyata, yadda itama zaki je ki koya mata rashin kunya da rashin mutunci ko? To ba dani ba, yadda kika zo gidannan zikal, haka zaki tafi!".


Wani kukan ya sake barkewa daga bakin Mama, cikin rishin kuka, magana na fita da kyar, tace "haba Malam, ta yaya zaka ce in bar maka yarinya yar shekara bakwai a hannun wannan azzalumar mata ta ka?".

Ina tunanin hakan shi ya kara tunzira Baba, ya bude baki ya hau zazzagawa Mama masifa kamar wanda yake amayo kalmomin. Ban taba ganin tashin hankali irin na ranar ba. 


Tunda aka haifeni, ban taba ganin sa'insa tsakanin iyayena ba. Tun tasowata, iyakarsu kawai: 'Yana yi kaza, to. Yana kada kiyi kaza, to Malam'.  Ganin wannan abu a ranar nan, was a first. And definitely not a good one. 


Ina ji, ina gani, Mama tasa kafa ta bar gidan, Baba ya bita a baya ya rufo gidan. Bai ma kula da cewa ina kofar dakin Mahaifiyata daya gama ci wa mutunci a gabana ba, ya wuce dakinshi. Amaryarshi na tsaye a kofar daki tana jiranshi, yana shiga, aka maida kofar dakin aka rufe, ji kake garammmmm!!. 


A hankali naja kafafuna da suke rawa, na koma cikin daki. Kan gadon Mamata na hau, na kwanta. 

Karo na farko a rayuwata dana kwanta ba tare da na ji dumin mahaifiyata a jikina ba. Kullum sai na yi barci take tafiya dakin Baba. Sai dai kawai wani lokaci idan na tashi cikin dare, in ga bata nan. 


Daren ranar barci sai barawo.


Washegari tun da safe na tashi, al'adar gidanmu ce. Na share tsakar gida tsaf, na kunna wuta a murhu na dafa ruwan zafi, kasancewar lokacin sanyi ya fara shiga. Na je nayi wanka, na koma daki na shirya.


Shiru ina zaune, ina jiran a fito a dora abincin kari, ban ga motsin kowa ba. Ganin karfe takwas tana neman shigewa, yasa na dauki jakar Islamiya ta na fita. Sai da na saka makulii na rufe dakin Mama, sannan na yi sallama a kofar dakin Babana. 


Sai da aka dauki lokaci kafin aka amsa min, a hankali na tura kofar dakin na shiga. Baba yana zaune a gefen katifarshi, amaryarshi na kasa kusa dashi, tsabar kusanci har cinyarshi na gogar tata, nayi saurin yin kasa da idanuwana. 

Karin safe ne a gabansu, shayi, libgegen biridi, soyayyen kwai, da indomie. 


A nutse na gaidashi, ya amsa ciki-ciki. Ganin na ki gaida matarshi, yasa ya umarceni da in gaidata. Cikin tafasar zuciya na gaidata, ta amsa tana watso min wasu dogayen hakora marasa tsari, wai ita ala dole murmushi take yi. Bayan a hakikanin gaskiya, ko kare aka yiwa murmushinnan yasan cewa dole tasa aka kakaro shi. 


Bayan nan zamana nayi ina kallonsu suna karyawarsu a nutse, sai daya gaji da ganina sannan ya tambayeni lafiya? Na bude baki ni kuwa nace mishi ban karya ba. 

Ya yanko burodin gami da tsiyaya shayin daya sha hadi, yaje yanko kwai amarya tasa hannu ta kame, ta wani langabar da kai tana mishi magana kasa-kasa, ban san me tace mishi ba, na dai ga ya zare hannunshi ya miko min biredi da shayin, na sa hannu biyu na amsa. 


Waje na koma, na zauna na shanye. Na dauraye kofin. Daya daga cikin al'adar Mama kenan da na dauka, sam bata barin kwano mai datti. Hatta da cokali idan tayi amfani dashi, a take a wurin take wankeshi. 


Ban kara waiwayar Baba da Amaryarshi ba, na wuce makaranta abina.


Karfe sha daya na safe muke tashi daga Islamiya a lokacin, daga can na kan wuce gidan Kakannina, iyayen Mama. Malam Bako Kakana, babban malamin allo ne da yayi suna a ciki da wajen garin Gashua. Yana da tarin dalibai yara da manya da suka kasance a ciki da wajen garin Yobe baki daya. Kullum na tashi daga makaranta, wajenshi nake wucewa inje ya taya ni biya karatuna, ya kuma dora min nashi wanda muke yi, watarana acan nake tsayawa har lokacin komawarmu Islamiya da yamma yayi, bana komawa gida sai dai in koma makaranta daga can. 


Ranar ma can na wuce. Bayan munyi karatun, anan nake jin cewa wai ya je ya samu Babana akan maganarshi da Mama. Wai Baban yayi fir yace wai shi bai kori Mama daga gidan ba, ita taga damar tafiya, anan nasan cewa lallai sake aure ya kan sa mutum ya canza halaye. 

Ban taba jin Babana ya fadi abinda ba shi kenan ba, sai a lokacin. 


A daren ranar da dare Mama ta koma gida. Tun daga wannan ranar, ko in ce tun daga ranar da kafar Ramata ta taka doron kasar gidanmu, bamu sake samun farinciki da kwanciyar hankalin da muka samu kafin tazo ba, har yau dake motsi...




*******



Karan alarm din dana saka ne ya tashe ni daga barcin daya daukeni. Jiya barci ya daukeni ban cire headphone din dana saka a kunne na ba, ban san ma yadda aka yi na cire shi ba, na dai hango shi a kasan gadona. Na kai hannu kasan filona na zaro wayar, dusu-dusu nake ganin komi saboda barcin daya cika min ido. Naga karfe hudu da rabi. 

Na kan manta in cire alarm din da yake tashi na sallar asuba duk lokacin da nake fashin sallah. 


Kashe alarm din nayi, na koma na sake kwanciya. Sai karfe shida alarm dina na biyu ya sake bugawa. Nan na samu na mike da kyar ina layi. Cikin awa daya, nayi wanka na hada abin kari. Yeah, idan zaku kira indomie da bakin shayi breakfast, to abin kari.

Lokacin Aylah itama ta tashi. 


Babu wata kwalliya da na tsaya bata fuskata da ita, daga mai, hoda, da janbaki, bana kara komi. Sai a lokutan da basu cika faruwa bane nake saka jagira da kwalli. 


Na janyo stool gefen gadona na zauna na karya, ina gamawa na janyo uniform dina farare tas na saka. 

Dogon wando ne fari, da riga wadda ta kai har gwiwata, na daura farin dankwali a kaina bayan na cikuikuye dogon sassalkan bakin gashin kaina na daure da ribbon, sai na dauko karamar farar hijabi data tsaya a saman kirjina na saka.


Na dauki agogon hannu ruwan kasa mai haske na daura, a jikinta naga cewa bakwai da rabi ta kusa yi. Cikin sauri na dauki gyale mai yalwar fadi na yafa a jikina. Na dauki purse, wayar hannu da littafin da nake shigar da duk wasu bayanai na ilimin dana dauka a ranar da naje asibiti, cikin sauri na zura bakin toms a kafata, na yiwa abokiyar zamana sallama na fita har ina hadawa da dan gudu.


Ina zuwa, bus din da take daukanmu zuwa Kongo tana zuwa, don haka na bi jerin mutanen dake layi suna shiga ciki, bayan na biya kudin mota. 


Karfe takwas da yan mintuna na sauka a inda na saba sauka. Daga nan acaba na hau, zuwa cikin unguwar Gyallesu, wani karamin public health centre nake zuwa aikin TP na. Karfe takwas muke farawa mu gama karfe daya zuwa biyu. Kowa dai yasan yadda dalibai suke da son yin latti, musamman a irin wannan lokacin da kasan cewa babu wanda zai kulle maka aji, ko ya hana ka attendance. 


Duk da lattin da nayi, sai da na riga Janan isa. Ita wannan dama ba'a maganarta idan ana zancen latti, sam bata dana biyu. 


Karfe sha daya da rabi muka tashi. Muka fita daga wajen ni da ita a gajiye, kuma cikin sanyin jiki. Babu ranar banza da ba zaka je asibitin nan baka ga abinda zai tayar maka da hankali ba. 


Ranar an kai wata mata mai ciki asibitin. Kwanaki uku kenan da aka yi mata scanning, aka ga cewar dan cikinta ya rasu. Maimakon a yi inducing dinta, sai mijin ya ciccibeta suka koma gida. Wani abin karin haushi da ban takaici shine, mijin nata likita ne, duk da ba zan ce likitan ainihi ba tunda shago ne yake dashi babba da ake sayar da magunguna. 

Tun shakaranjiya take nakuda, bai kaita asibiti ba sai ya kira unguwar-zoma. Ana ta kai da kawo dai, har jiya bata samu ta haihu ba, shine yau da safe suka tarkata ta zuwa asibitin. Ana maganar a dauketa a kaita Shika, domin a mata tiyata a cire cikin, rai yayi halinsa.

Abin gwanin ban tausayi da takaici. Ga ta da yara kanana wadanda basu gama mallakar hankulan kansu ba. 


Har muka je inda muke hawa acaba, abinda muke tattaunawa kenan ni da Janan. 

Ta kalleni tana canza muryarta zuwa alamun roko, "don Allah sis, kizo muje gida mana. Sai ki koma da yamma, kinji?".


Na harareta, "tab! Allah Ya kyauta wallahi. Ni kin ma ga tafiyata!".

Nayi saurin sa hannu ina kiran daya daga cikin yan acaban da suka yi jerin gwano, suna jiran fasinjoji. 

Da sauri ta riko hannuna, "please, kinji? Don Allah!. Wallahi kwana biyun nan gidan babu dadi. Dama a wajen Yaya Bilal nake samu na dan ji sauki wasu lokutan, idan yana gida. To shima kwanannan sai a hankali. Tun jiya da yamma ya rikice, ko kallona baya yi wallahi. Yau da safe dana gaida shi, ko amsawa ma baiyi ba. Kuma ya hana ni yawo, balle inje wani wajen. Don Allah, muje ki dan debe min kewa, kinji?".


Gabadaya tausayin ta ya lullube ni. Wani irin bahagon zama suke yi da matar yayanta. Wani lokacin sai kayi kuskure kace irin zaman kishiyoyin nan ne da suke zabga dan banzan kishi suke yi. 

Ba tare dana sake tunani ba, na gyada mata kai. Tayi tsallen murna tare da rukunkume ni. 


Napep muka tara, bayan na ba dan acaban da muka kira hakuri. Unguwar PZ muka nufa, wadda bata da nisa da wajen da muke zuwa TP din. 


Gidan Yaya Bilal, inda Janan take zaune, babban gida ne sosai. Daga nesa idan ka hango shi zaka yi tunanin irin family house dinnan ne. Sai dai su biyu ne suke zaune, shi da kaninshi Jameel, sai kuma matansu. 

Kowacce tana da part dinta, masu fadi da nisa da kowannensu, ta yadda idan daya taga dama, zata kwashe watanni bata ga yar'uwarta ba. 


Sashen gidan Yaya Bilal ake fara tardawa idan aka shiga gidan. Shima can din ya kasu kusan parts uku, duk da sauran biyun duk a kulle suke, dayan ne Janan take zaune ita da Raheema matar Yaya Bilal. 

Shekaru biyu da suka wuce ne suka yi auren, basu ma cika da yin shekara biyu ba. Har yau Allah bai basu haihuwa ba. 


Abu ne da naji kus-kus suna tashi akan cewa wai, wai Yaya Bilal din baya haihuwa. Saboda matarshi ta farko ma, Ameerah, wadda suka kwashe shekaru kusan shida a tare, auren saurayi da budurwa, bata taba haihuwa ba itama. 


A hankali muka yi sallama cikin falon gidan, bamu ji motsin kowa ba, ko na TV babu, balle na mutane. Janan ta ja ni zuwa dakinta, ta koma kicin ta dauko mana ruwa da lemu. 


Ina zaune a gefen gadonta, na dinga jiyo karar sautin kida tana tashi. Na kalleta, tana tsaye a gaban wardrobe tana nema mana kaya masu saukin nauyi da zamu saka. 

Nace "wannan karar fa, daga ina take fitowa haka?".


Ta dan juyo ta kalleni, kafin ta maida kanta cikin closet din. "babu mamaki su Haleemo ne suke kallo!".


Na dafe baki, "wai dama yaran nan suna nan har yanzu?".

Tayi yar dariya, wadda take lullube da zallan takaici, "to dama ina zasu je? Ai suna nan a gidan nan, basu da ranar fita!".


Ta miko min Skirt dogo na wani yadi tare da riga, na amsa na fara zare kayan jikina, nace "to Allah Ya kara rufa mana asiri!".

Tace "ameen".


Ni tunda nake ganin gidan aure da cakudewar rayuwar aure, ban taba ganin irin wadda ta kama kafar ta gidan Yaya Bilal ba. 


An saba idan aka yi aure, akai amarya ita daya zikal dinta gidan miji. Sai dai ita wannan abun nata ya bambanta. Koda aka kai amarya, sai kannenta guda biyu suka samu waje suka share, suka mike kafafu a gidan. _Marry one, get two free kenan!._


Watanni bakwai da kai amarya, Babbar kawar amaryar ta kaso aurenta, itama taje tabi layin jerin yan'uwanta dake gidan kamar wadda bata da gidan zama. Yanzu dai su ukun duka suna zaune a karkashin kulawar Yaya Bilal ne. Amma yar kanwarsa daya tilo dake zaune dasu, sun kasa riketa balle su kula da ita. 


Kullum fata da buri nasu ta bar gidan, bin malamai, asiri, kissa da kisisina, babu wadda basa yi. Allah ne kadai yake kareta a gidan nan. 


Tana gama sallatar azuhur, ta ja ni muka shiga kicin domin mu nemi abinda zamu saka a cikinmu. Muna cikin girkin Yaya Bilal ya shigo kicin din, ya amsa gaisuwar da muka mishi a kaikaice. 

Ya kalli Janan yana wani cin magani, "ke ina Raheema take ne?".

A hankali kamar mai tsoron magana, tace "yanzu muma muka dawo, bamu sameta a gidan ba".

Bai kara cewa komi ba, ya fita daga kicin din. Ko me yake faruwa kuma yanzu? Na saba ganin kallon so da kulawa daga gareshi zuwa ga yar kanwar tashi, yau kuma naga wani abu daban. 

Na kalli Janan dake kokarin hadiye kwallar data cika mata ido, cike da tausayi. Haka Allah ya halicceta mai sanyin hali, da sanyin zuciya. 


Danwaken fulawa muka kwaba, daidai wanda zai dauki cikin mutum biyu. Duk kokarin da tayi na mu kara yawan fulawar, ki nayi. Saboda nasan saboda wannan lalatattun yaran take so muyi da yawa. Ni kuwa da in dafa abinci da hannuna, kattin banza su cinye, su goge hannu da tissue su kara mike kafa, karshe ni ce zan kwashe kwanukan da suka ci abincin ma, na gwammace in zauna da yunwa. 


Muna gamawa, muka juye shi a cikin kula tare da gyara kicin din tsaf, kamar babu abinda aka yi. Janan ta wuce mana da kular daki, ni kuma na dauki plates da vegetables din da muka yanka nima na fita dasu. 


A bakin kofar kicin muka ci karo da Salama, kanwar Anty Raheemah. Duk cikin kannenta babu wadda ta fita rashin da'a da rashin mutunci, shi yasa jininmu bai hadu ba, sam. 

Ta wani tsaya kerere, ta kama kugu tare da kara babakewa akan hanya. Ko tayi zaton zagayeta zanyi in wuce? Na saki wani murmushin mugunta. Lallai yarinya har yau baki gama sani na ba. 

Na tunkareta gadan-gadan. Da dai taga ina shirin bangajeta, sai taja baya. Na ja dan siririn tsaki a cikin raina, ina raya 'dama kin tsaya kin ga karshen wulakanci!'.


Ta wani daga murya, "ina namu abincin?".

Na kuwa tsaya cak, na juya na kalleta, "ban gane naku abincin ba? Kin daukeni aikatau din yi miki girki ne dama ban sani ba?".


Tayi gyatsine, "taya za ayi ki shigo har cikin gidan Yayata, kiyi girki sannan kuma ki k'i ajiye mana?".


Naji wata dariya na neman subuce min, nace "to sannu hamshakiya! Sarauniya mai girma!! Allah Ya bamu hakuri mu da bamu da gidan Yaya dake aure a gidan mutane, balle muje mu shimfida mulki a inda bai dace ba!. Girki ne, bamu yi daku ba. In kinyi zuciya, ga hanyar kicin nan, ki shiga ki girka wanda yafi wanda muka girka!".

Na juya na shige daki, tare da maida kofar dakin na rufe. Ina jin sautin maganganu da zage-zagen da take yi. Janan tace "ni dai wallahi da baki biye mata ba!".


Harara na jefa mata, "ai a haka suke samun damar taka ki kamar wata sakara. Ke dai da kika ga zaki iya, sai kije kiyi tayi. Ni kam, ba zan iya jure rashin kunya irin nasu ba wallahi!".


Kai kawai ta gyada, don tasan gardama dani ma bata baki ne. 




Karfe biyar na mata sallama zan koma makaranta. Zuwa lokacin babu kowa a cikin gidan, muna jin lokacin da suka fita. Daidai bayan tagar dakin Yaya Bilal, na hangi wani abu daya dauke min hankali. Da sauri na kalli Janan, "kai! Kinga kuwa na manta jotter na akan gado, don Allah taimaka ki dauko min ita mana, zan jira ki anan!".

Babu musu tace "to!".


Tana bada baya, nayi sauri na karasa wajen. Da sauri na duka tare da yin bismillah, na fara hak'a. Kamar yadda nayi zato, wasu kullin abubuwa naci karo dasu. Da sauri na ciresu, na maida kasar na rufe kamar yadda take.

Ina komawa inda Janan ta barni, sai gata ta dawo. "Ni fa ban ganta ba, ko dai a asibiti kika barta ne?".


Na daga mata hannun dama ta, "ashe tana hannuna, sha'afa nayi".

Ta kada idanu, "ke dai shiriritarki tayi yawa wallahi!".

Muka jera da ita har zuwa inda zan hau bus. Sai da taga na shiga, motar ta tashi, sannan ta juya tana daga min hannu, tare da jaddada min dana isa cikin makaranta, in kira ta.

Dariya kawai nayi na gyada mata kai, wani lokacin haka take, kamar wata overprotective Yaya, ko Uwa.









                         















    *☆⋆02⋆☆*






"Haba Sweety, ni sai ki dinga cewa wai bana sonki saboda Allah! Bayan kin san cewa duk duniya bani da kamar ki!".

Ya fada daga can daya bangaren na wayar, whinnying kamar wani karamin yaro. 


Na kada idanu sama, "To ai kai dinne sai ka dinga wasu irin maganganu da suke saka ni cikin shakku, Umar". I mean, ta ya mutumin da yake ikirarin saboda Allah yake sonka, kuma ya dinga kokarin dilmiya ka a duniyar 'sex chat?'. Kullum muka yi waya dashi, da kalar dirty maganganun da zai tare ni dasu, tun ina mishi alkunya, a tunanina zai fahimci zancen ya daina, har na fito baro-baro na fada mishi cewa bana son hakan, amma duk da haka bai fasa ba. Don haka nace mishi naga alamun cewa ba son gaskiya yake yi min ba, akwai abinda ya gani a jikina dai kawai. Nan ma yace ba haka bane, daga nan ya dan rage yin maganganun, note that 'ragewa' nace, ba dainawa ba. Ni kuma kullum ya dauko min maganar abinda nake ce mishi kenan. 


Yace "to naji, shikenan. Ni dama na kula da cewa ba wani sona kike yi ba, son da nake miki yafi yawa!".

Nayi murmushi kasa-kasa, da wata ce kam, zai iya samun damar cin galaba a kanta da irin wadannan maganganun har yayi amfani da wannan damar ya samu abinda yake bukata daga gareta, amma banda ni. A tsaye nake kyam! Akan duk wata kalma da na furta, ko abinda na kudurta a cikin raina. 


Nace "duk abinda kayi tunani hakan ne, Umar".

Ina jin dariyar daya saki mai sauti, wadda ta saka ni yin murmushi ba tare dana shirya ba. "Sweety na kenan! Shi yasa nake jin sonki kullum yana kara yaduwa a cikin sassan zuciyata wallahi. Amma yanzu Oga na ya shigo inda muke, zan kira ki anjima in shaa Allah, ok?". 


Na girgiza kai, "babu damuwa ai, sai anjiman".

Nan muka yi sallama da juna, bayan ya manna min sumba ta jikin wayar. Kai kawai na girgiza, speechless, muka ajiye wayoyinmu. 


Na sauke ajiyar zuciya tare da kurawa gadajen da patients suke kwanciya akai da suka kasance empty. Ban san lokacin dana dauka cikin tunani ba, sai da naji an dafa min kafada. Nayi firgigit! Na kalli gefen damana, Janan ce. 

Murmushi na saki ina harararta cikin wasa, "wato tsabar shahara, yau sai karfe tara ma kika zo ko?".


Tayi yar dariya, "to me yafi raina? Tunda an riga anzo anyi supervising dinmu, mun kuma yi presenting dinmu, ai babu abinda ya rage mana sai chilling. Yaya Bilal ne ma ya tsaida ni da jira, wai sai na jira shi ya karya sannan zai zo ya sauke ni. Kinsan na fada miki mun shirya dashi".

Na gyada kai ina wasa da kan wayata, "yeah, haka kika ce. Yanzu idan muka gama ina kika nufa ne?".


Tace "yo ni ina na sani? Watakila in tafi wajen Yaya Sa'a Funtua, ko kuma Kaduna wajen Umman mu. Ke fa?".

Na harareta, "har wani tambayana ma kike yi? Bayan kin riga kin san komi?".

Tace "to kizo muje wajen Umman mu mana kawai? Tunda dai ko kin je gidan ma ba wani jimawa zaki yi ba?".

Nace "lallai ma, watanninmu kusan shida a makaranta fa, ban leka gida ko da wasa ba, kuma kinsan idan muka dawo hutu ma ba wani hutu zamu samu ba, gwara inje dai kawai".

Ta kada kai gefe guda, "ai shikenan. In ka ki ji, ba zaka ki gani ba. Amma ai ba a goben zaki tafi ba dai ko?".

Nace "a'ah, sai ranar assabar in Allah Ya kaimu".


Kiran da daya daga cikin nurse din ta kwala mana, shine ya katse mana hirar da muke yi, muka tashi muka tafi wajen data kira mu. 


Ranar ma karfe daya muka tashi. Janan ta sake ja na zuwa gidan Yaya Bilal, wai in taya ta hada kayan tafiya. Yau mun ci nasarar samun Anty Raheemah a gida. Tana zaune a falo sun kure kida ita da kannenta, wasu suna rawa, wasu kuma a zaune kawai suna kallonsu. Muka musu sannu da gida, suka amsa a kaikaice. Bamu kula su ba muka wuce dakin Janan abinmu. 


Da yamma wajen karfe biyar, na mike ina rataya jakata. Janan ta shigo dakin hannunta rike da wasu ledoji biyu, tace "Yaya Bilal zai shiga Samaru yanzu, yace zai rage miki hanya".

Na zaro ido, "what? No!! Kada ma ya wahalar da kanshi wallahi, zan bi bus kamar yadda na saba".

Ta harareni, "jibe ta don Allah! To ya riga yace zai kaiki, yanzu haka yana jiranki ma a waje. Sauri yake yi, yau a gidan Anty Ameerah zai kwana, kuma dawowarshi daga Kaduna kenan, so yake yi yaje ya huta".


Na dafe kai, "to menene na wahalar dashi akan cewa ya wani sauke ni a school? Da kin barshi yaje ya huta abinshi".

Tace "sai kiyi kuma, tunda sabonki ne yin korafi. Yaya dai yana waje yana jiranki, idan kin tsaida shi, damuwar ki ce. Gashi Umma tace a kawo miki".


Ta miko min daya daga cikin ledojin hannunta, na leka kaina cikin ledar. Turare ne, kayan biscuits da chocolates har da yan kunne da takalmi mai kyau. Umman su Janan tana yi min wani kallo ne kamar yadda take kallon Janan. 'Diyarta, 'ya kuma mafi soyuwa a gareta. 

Duk wani abu da zata yiwa Janan, sai ta hada da ni. Ko ina nan, ko bana nan, ko ina sane, ko bana sane, zata bani da hannunta, ko ta bada a ajiye min. 

Shi yasa nake matukar girmama matar. Ko ba don alkhairin da take yi min ba, don yadda take daukata kamar diyarta. Idan nayi wani abu da bai dace ba, zata kira ni ta zaunar dani, ta bani duk wata shawara da uwa ta gari ya dace ta bawa diyarta, ta tsaya daram, akan kafafunta, wajen dora ni akan hanya, duk da cewa bamu hada ko digon gumi ni da ita ba. 

Ko a hakan kadai aka tsaya, wallahi ta gama min komi. Balle kuma ayi zancen irin alkhairanta a gareni. 


Duk abinda zata yiwa Janan, ba ta taba bambanta mu, sai dai ko kala da tsayi.


Na kalleta ina murmushi, "Madallah da wannan sako, lallai Umma ta gano ni. Bari in koma sai in latsa mata kira inyi godiya. Na gode kwarai".

Tayi dariya, "ai fa! Yanzu ke dai mu tafi, kada Yaya ya gaji da kira".

Kamar yana ji, sai ga kiranshi ya shigo wayar. Ta daga tana ce mishi gamu nan fitowa, ban san me yake ce mata ba, na dai ji tana cewa "minti daya!". Ta ja hannuna muka tafi. 

Sai da na leka ta dakin Anty Raheemah muka mata sallama, sannan muka fita ni da Janan. 


Yaya Bilal yana cikin motarshi a zaune, ya zuro kafarshi daya waje. Kyakkyawan takalmin D&G baki, budadde na fata yana ta sheki a kafar tashi. Na gaida shi kafin na zagaya ta daya gefen na shiga gefen mai zaman banza. 

Janan ta leko tana min Allah ya kiyaye, yayin da Yaya ya tashi motar muka fita daga gidan. 


Tafe muke a cikin motar, babu wanda yake furta uffan. Sai sautin wakar "earned it' ta weekend dake tashi a nutse. A hankali nake bin wakar, ba lallai ka sani ba sai idan ka kalli bakina sosai, inda zaka ga yana motsawa kawai ba tare da sauti ya fita ba. 


Idanuna suna ta tagar gefena suna kallon cikin garin Zaria. Na dinga jin alamun idanu a kaina, nasan cewa zargin hakan ne kawai nake yi a cikin raina. Da abin ya girmama, sai na juya a hankali cikin dabara, na kalli inda Yaya Bilal yake, idanunshi straight suna kallon gabanshi. Na girgiza kai, dama sai da nace zargine nake yi. 


A kofar Bitmas Bakery naga yayi parking motar. Ya kashe tare da fita daga motar yana muttering "excuse me!". Wanda ba don na juya a daidai lokacin idanuna sun sauka akan fuskarshi, na ga bakinshi ya motsa ba, ba zan ji mai yace ba. 

Na zaro wayata a cikin jaka ina dubawa don in rage kadaicin zama. 


Bayan kimanin mintuna biyar da fitarshi, naji an kwankwasa gilashin tagar motar, gefen inda nake zaune. 

Na daga kai, naga Umar a gefen a tsaye. 


Nayi murmushi tare da sauke gilashin kasa, "hey handsome, me kake yi anan?".

Shima yayi murmushin, "wai mun tsaya ne zamu sayi fruits fa, ina jiyowa kuma sai na ganki. Daga ina?".

Nace "daga gidansu Jan. Tare muke da Yaya Bilal, zai sauke ni a makaranta".


Ya gyada kai, "uhmmn... Ya shirye-shiryen tafiya gida? Jibi zaki tafi ko?". Nace "ehh!".


Yana nan a tsaye muna hira, Yaya Bilal ya dawo. Kwata-kwata ban ga wucewar shi ba, sai da ya bude motar ya shigo. Na kalli Umar ina murmushi, "handsome, bari mu wuce ko?".

Ya gyada kai, "Ok Sweety, zamu yi waya ko?".

Na jinjina kai, "in shaa Allah. See you!".

Har ya juya ya tafi, sai kuma ya juyo da sauri, "hey, bari in miko miki fruits".


Na daga baki da niyar cewa na gode, Yaya Bilal ya katse ni ta hanyar yiwa motar key. Ya kalli Umar, "ta gode, sauri muke". Da wannan yaja motar. Ina hango Umar ta cikin gilashi yana daga kafada. 


A main gate na kalleshi nace "Yaya ko zaka ajiye ni anan kawai, sai in karasa ciki?".

Yadda kasan bango, haka ya maida ni. Bai ma nuna alamun yaji abinda nace ba, sai ma ya karawa motar wuta ya shige ta cikin makarantar. 

A bakin hostel ya samu waje yayi parking din motar, na fara yunkurin bude kofar ina jera mishi godiya, 

"na gode Yaya, a gaida Anty Ameerah".


Sai da na fita, ina kokarin maida kofar in rufe, naga yana miko min leda mai dauke da tambarin Bitmas, na kalleshi fuskata dauke da alamun tambaya, kafin inyi magana ya riga ni, "karbi mana, kina bata min lokaci!".


Nasa hannu biyu na karba, nace "nagode, Allah Ya amfana". Yace "Ameen" a kaikaice, yawa motarshi wuta ya kara gaba. Ni kuma na shige cikin hostel. 


Sai bayan sallar magriba dana gama komi, na bude ledar. Bread ne da roll cake da suke yi a wajen guda biyu, da ice cream biyu shima. Na dauki daidaya na mikawa Ayla, tana ta min tsiya, wai "lallai yau Umar ya tuna damu!". Dariya kawai na mata na koma gefe ina cin nawa. Sai da na gama ci sannan na tashi na hau hada kayan tafiya gida. 

Bayan na gama, na turawa Baba sako akan cewa zan taho ranar Asabar, ya turo min kudin motar tafiya gida. 


Washegari muka je asibiti muka yi bankwana dasu. Daga nan muka yi bankwana da Janan, itama ranar Lahdi zata tafi Kaduna wajen Umma. Ni da ita kuma sai idan mun dawo hutu. 

Na dawo hostel na karasa shirya kayana, wadanda zan bari anan kuma na hade su waje daya tsaf na rufe da mayafai saboda kura. Na share waje na zauna ina jiran kudin mota. 






_*NA'ILAH!*_




Mahaifana su duka biyun, asalin yan garin Gashua ne. Mahaifina, Alhaji Al-Hassan Hannafi, cikakken haifaffen garin Gashua ne. Iyayenshi hausa/fulanin dake cikin garin ne, duk da cewa sun rasu tun ma kafin a haifeni, sai sauran dangi na nesa-nesa kawai. Yayin da mahaifiyata, Yana, ta kasance ruwa biyu. Mahaifinta Barebari ne, mahaifiyarta kuma Shuwa Arab. 

Kakana Bako Audu, shahararren malami ne, Kakata Fatima da muke kira da Fatsu, ta kasance mai sana'ar sake-saken kaya, a cewarta tun tana budurwa. 


Mahaifiyata ta kasance kyakkyawar mata, fara, doguwa, mai dogon hanci da dogon gashi da dara-daran idanu masu tsari. Babu abinda ta bari na Fatsu. Allah Ya hore mata hakuri, Kawaici da kawar da kai. Aurenta da mahaifina ya kawo yar matsala a tsakanin danginsu ta fannin mahaifiyarta, su a sonsu ta auri dan uwanta ta fannin uwa, ko Barebari, amma ta kafe. Sai kuma matsalar rashin aiki, don a lokacin da suka yi aure, ya gama kammala degree dinshi akan banking and finance, amma bai samu aiki ba. Jajircewar Bako ce kawai tasa aka yi auren, suma kuma dangin nata suka hakura. 


Bayan auren nasu da kadan, ya samu aiki da bankin GT, anan cikin Gashua din, ya fara zuwa aikinshi. 


Yaya Mudatthir shine 'Da na farko a wajen iyayenmu. Shekaru biyar cur ya bani. 

Yawancin rayuwar yarintata a gaban su Fatsu da Bako nayi ta. Ba kamar Ya Mudatthir daya dauko kamanni da suffofi da halayen Mama kamar tayi kaki ta tofar, ni babu abinda na dauko nata sai yanayin idanuwanta da kuma dogon sassalkan bakin gashinta. Bayan haka, gabadayana Bako Audu ce. Ina da tsayi na daidai-wa-daida, da zubin halitta mai daukar hankali. Shi yasa bana shiga mai fitar da surar jiki. Kalar fatata baka ce, wasu kuma su kan ce wankan tarwada. Ko ma dai wace iri ce, ina jin dadi da alfahari da kalar fatata. Kalata mai sheki ce, sannan fatata mai taushi ce. 


A halayen Mama kam, zan iya cewa tsafta da wasu halayen na dauko nata. Hakuri na kadan ne, sannan bana daukar wulakanci ko kadan, ko daga wajen waye kuwa. Bako ya kan ce shi duk cikin danginsu bai ga mai hali na ba, zafin kai, kafiya da taurin kai. Ina da rikakken ra'ayi, idan nace zan yi abu, to zanyi. Idan kuwa nace ba zan yi ba, mai canza min wannan magana kam sai ikon Allah. 


Munyi zama mai dadi da iyayenmu, a dan abinda zan iya tunawa na rayuwarmu da wanda Mama ko Ya Mudatthir suke bani labari, Babanmu ya so mu, mutum ne mai son iyalanshi da kuma kyautata musu. Duk da cewa bashi da wani hali na azo a gani, amma rayuwarmu Alhamdulillah, babu abinda muka nema muka rasa. 


Wannan kafin ya auro bakar ashana Ramata kenan. Lokacin da aka yi auren, Ya Mudatthir yana makarantar maza ta kwana a cikin Yobe. Ni kadai ce a cikin gidan, sai su Mama. 


Tunda aka yi auren wannan, muka nemi walwala da kwanciyar hankalinmu muka rasa. Muka nemi Babanmu, Mama ta nemi mijinta, duk muka rasa. Rayuwar gidan ta koma kadaran-kadahan, yau daci gobe b'auri. Babu wani armashi. Ance wai ba'a kure mai hakuri, amma ni na gani akan idanu na, ranar da aka kure hakurin Mama a gidan nan, ranar da ta daga baki tace hakurinta ya kare.

Ranar ce Baba yasa belt ya zane mu ni da ita a tsakiyar gidanshi, akan naman kaji. 

Ya kai mata nama ta soya, aka nemi naman a dakinta aka rasa. A cewarshi, satar nama take mishi idan ya kawo, dama kullum idan ya kai nama a soya sai ya ga babu wani bangare. 


Mama tace "haba Malam, in rasa abinda zan daukar maka a gida sai nama? Tunda muke zaune da kai, na taba daukar maka abu ba tare da saninka ba?".


Budar bakin amaryar Baba sai cewa tayi, "kenan kina nufin ni na dauki naman ko kuwa me?".

Mama tace "ni ban ce ba, amma haka bai taba faruwa tsakanina da mijina ba, sai da kika zo!".

Kawai ba sai mata ta dora hannu aka ba? Ta hau ihu, tana kururuwa, ita wallahi ba zata yarda ba, ance mata barauniya, zata bar wa Babanmu gida, sai yaci gaba da zama damu tunda yana zaune a gabanshi aka zageta bai ce komi ba. 

Daga nan sai saukar duka kawai Mama taji, nayi tsalle na rungumota. Bai damu ba, ya hada mu mu duka ya mana lilis, kuka ranar haka muka shiga daki muka sha, babu mai lallashi. 


Daga ranar dai bamu kara ganin nama a idanunmu ba, an haramta mana shi, duk wannan bai dameni ba, sai ganin an fiddo kwanon da Mama ta zuba naman da aka nema aka rasa daga dakin matar Baba, da tsakiyar ranar Allah Ta'ala. Babu kunya balle tsoron Allah. Wani karin abin haushi ma, da naje na yiwa Baba maganar, saboda Mama taki zuwa ta fada mishi, wai bata son wata rigimar ta sake tasowa, sai ya hau fadace-fadace, abinda na kira borin kunya. 


Daga ranar muka kullata da ita. Ban kara ganin idanunta da kwalli ba, ban sake kallon kanta da gashi ba, ban kara mata magana cike da ladabi ko girmamawa ba.



Shekaru shida da karin auren da Baba yayi, shekaru uku da muka rasa walwalarmu. Muka yi rashin da har yau bamu samu mun cike wannan gurbi ba. Mama ta rasu wajen haihuwa. Nakuda ta kamata, cikin dake jikinta yana wata takwas da yan satika a lokacin, haka ta rasu, bata kai ga haihuwar abinda yake cikin nata ba, Allah ya karbi ranta. Munyi kuka, kuka ba kadan ba, Allah kadai yasan tashin hankalin da muka shiga ciki a lokacin. 


Muna tsakiyar karbar ta'aziyar Mama, muna cikin wannan yanayi na jimami, tashin hankali da kunar zuciya, kwana biyu kenan da rasuwar mahaifiyata, har zuwa lokacin ina jin zafin rashinta kamar a lokacin ne hannunta ya silale daga cikin nawa, babu rai. Sai ga Ramata ta fito daga dakinta, taci kwalliya ta sha gyale sai zuba kamshi take yi, tana rike da hannun Aliyu dan data haifa dan kimanin shekaru biyu, Yayarshi Maryam mai kimanin shekaru biyar tana binta a baya. Babu wanda ta kalla a cikin yan karbar gaisuwa, ta tafi wajen bikin kanwarta. Da yake duk dai anan cikin unguwarmu suke dama, layi daya ne a tsakaninmu, muna iya jiyo sautin karar kidan da suka saka na biki kamar a tsakiyar gidanmu aka sa kayan. 

Har yau dake motsi, matar nan bata yi min gaisuwar rasuwar Mama ba. 

Har yau kuma, ina jin zafin hakan, sai dai idan ban kalleta ba. 


Ita ta gwada min cewa kishiya ba karamar masifa bace, kuma kishiya, ba mutuniyar arziki bace, shi kanshi kishin, ba abu bane mai dadi. Na fara neman tsari da kishi irin nata, a ganina bashi da amfani. Da wannan tunanin, na girma na tashi. 


Rayuwar dai gata nan sai godiyar Allah. Bayan yan gaisuwa sun watse, gida ya koma sai ni sai ita don Yaya ma ya koma makaranta saboda jarabawa, sai na kasa zama a gidan. Saboda haka na kwashi kayayyakina na koma wajen Fatsu. Na dauki lokaci mai tsayi a wajensu, kafin in koma gida.

Kafin in saba da sabuwar rayuwar wannan na jima. 


Da rayuwa nayi mai dadi, ruwan wanka sai an kai min bandaki, abinci sai an zo ance min in ci, makaranta sai an zo an ce min in tafi, kayan makaranta sai an wanke an goge min. Amma yanzu wadannan duk sun zama tsohon tarihi. Abinci sai na je na nema, an wulakanta ni kamar ba gidan uba na ba. Kai sai da ta kai ta kawo, sai kannenta sun je gidan sun ci abinci, sannan za'a bani sauran inci. 

Kullum ina hanyar gidan su Bako, cin abinci, kullum. Na fadawa Baba ya fi sau shurin masaki, ko maganar bai taba mata ba. Ni kuma na gaji. 


Idan nace ta bani abinci ta ki, sai in shiga har kuryar dakinta in zubo abina. Idan Baba ya dawo ta fada mishi, inyi kyar da idanu ince hana ni tayi, baya da yadda zai yi dani. 

Cikin haka Yaya ya dawo gida. Gabadaya taso ta maida mu yan aiki a tsakiyar gidannan. Kayan fitsari da kashin Aliyu da nata har ma dana Maryam haka zata libgo mana su tace mu wanke, Yaya ne yake zama yayi aikin wankin nan, watarana yana gamawa ma zata ce sai ya sake wai bai yi ba. Idan nace ya daina mata, sai yace wai ai bamu da yadda zamu yi, matsayin mahaifiyarmu take. Sai inyi tsaki in ce Allah ya kiyaye. Kuma fa kada ku ce hakan shi yake hana ta zage mu, ko kadan. Haka kawai zata hau zaginmu, watarana ma haka har sunan Mama zata kira ta kare mata zagi, a gabanmu kuma. 


Da naga ya matsa kuma ya ki saurarena, sai na kyale shi yake ta mata aikace-aikacen. Ni dai na ki. Koda ya koma makaranta, idan ma ta kawo kayan wankin sai in tsere abina, watarana ma fakat zan ce ba zan yi ba. Idan an gayawa Baba naki yin aiki, ince yankewa nayi, ko yatsa ta take ciwo, ko kuma wani abu dai. Na dai zame mata karfen kafa kiri-kiri kamar yadda nima ta zame min. Koda wasa ban bari ta juya ni ba. 


Wannan yana daya daga cikin manyan dalilan da yasa kullum nayi sallah sai na daga hannuna sama na roki Allah Ya kareni daga sharrin kishiya. Allah ya kiyaye ni da haduwa da ita a gidan aure. 


A cikin haka aka wa Baba kari da kuma canjin wajen aiki. Dama lokaci zuwa lokaci ana mishi canjin wajen ayyuka, amma kuma ba mai nisa bane. Wannan karon Katsina aka kaishi. Saboda haka muka fara shirin kaura zuwa Katsina. Yaya yana ajinshi na karshe lokacin a sakandire, don haka aka barshi a can. Ni kuwa da nake aji daya, aka min canjin makaranta zuwa Ulul-Albab.

Babu yadda banyi ba akan a barni a gaban su Bako, fir Baba ya ki. Ranar da za'a tafi din kam da kuka muka rabu. Da kyar aka tura ni cikin motar da Baba yayi shata ta kwashe mu zuwa Katsina. 


Mun dauki lokuta kafin mu saba da yanayin sabon garin da muka je. Musamman gari inda babu dangin Uwa balle na Uba kuma ko abokai, yana da wahalar sabo, amma a hakan dai muka zauna muka fara sabawa dasu din. Anan kusa da inda muka koma, wata Ummu-Kulsum, itama kimanin shekaru na ce, mun fara sabawa da ita da mutanen gidansu nake jin labarin itama a Ulul-Albab din take, nan na makale mata sosai. Nan da nan abota ta kullu a tsakaninmu. Ya zamana na gwammace in yini cur a gidansu maimakon inyi gidanmu, saboda idan ma na zauna a gidan me zanyi? Habaici ne nake sha da bakar magana, sai kace ni ce kishiyar ta ba diyar kishiyarta ba. 

Da na samu ma baba ya sai min form din islamiyar da Kulsum take zuwa shikenan, sai muka kara gamewa da ita. 


Suna kare hutunsu na bita muka tafi. Duk da ba wasu kayan azo a gani aka hada min ba, naji dadin dan abinda yayi din, ban raina ba. Allah Ya taimakeni term daya kadai nayi missing, dana maida hankalina kan karatuna sosai, tuni na wuce aji biyu. 


Mun koma gida hutu, na tarda amarya Alawiyya a gida. Abin ya bani mamaki, ko kadan ban ji labarin auren ba, wanda a yadda ake fada min, kusan watanta uku kenan a gidan. 

Kodayake, daga bakin wa ma zan ji labarin? Tunda aka kaini aka ajiye a makarantar, ban kara ganin kowa ba. Ni da visiting dama sai in su Inna - mahaifiyar Kulsum sun je, sannan nake ganin na gida. Ni da Baba dama sai dai in ina bukatar wani abu, in ari wayar wani malami in kira shi in fada mishi. A hakan ma sai ya dauki lokacin shi kafin ya turo abinda zai turo din, kudi ne ko kuma abin bukata. Watarana kuma sai dai ya ba su Inna su kawo min kam. 


Na sha shigewa bandaki in shaki kukana, ko kuma in haye can kan gadona in yi kukan. Abin yana da matukar cin rai da ban takaici, na rasa dalilin da yasa ni hakan take faruwa dani. A kaika makarantar kwana na wata da watanni amma ka rasa naka wanda zai leko ka ko da wasa? Rashin uwa ne ya janyo haka ko kuma rashin dangi? Saboda na tabbata cewa da a gaban su Bako nake, da lallai sai na ma gaji da ganin dangina. A hakan nake ta cijewa ina danne komi a cikin raina, har muka koma gida hutu. 


Amarya ko in ce bazawara Alawiyya ta shiga da rawar kai da jiji da kai, sai dai bai je ko'ina ba ya sauka. Saboda Ramata ba kanwar lasa bace ba. Zama a gabansu sai ya zama kamar zama da wasu kishiyoyi ne, suka sako ni a gaba. Ni abin yana bani mamaki, ban tsarewa kowa komi ba, amma ni kuma ace na tsare? Shima din taso taga tayi dani, taga dai daga ita har Ramata din na jefa su a kwandon shara, sai ta saddakar, ta koma kan Ramata din. 


Matsala ta farko a cikin wannan gida, ita ce rashin adalci. It was obvious Baba yafi son Ramata akan Alawiyya, zata iya yiwuwa so ne na tsakani da Allah, ko kuma wanda ta nemo a wajen malamai da yan tsibbu, koma dai wannene, amma kuma bai san ta yadda zai daidaita ko ya boye son nata ba domin samun adalci a cikin iyalansa, hakan yasa a kowane abu ne sai ya fifitata akan Alawiyya da 'ya'yansu. Ita da 'ya'yanta sun fi kowa kima da mutunci a idanun Baba. 


A hakan ma kuma bata bar Alawiyya din ta zauna ba, ta hana ta zama lafiya da mijinta, ta hana ta sana'a. Kudi duk yawansu idan ta tarki sana'a dasu, zasu kare ne kafin a je ko'ina. Wani abu ne da naji suna kira wai 'mai rariya', duk yawan kudin da zasu shiga hannun mutum to zasu koma kamar an cinna musu wuta, nan da nan zasu kare ka rasa ta inda suka shiga. Abubuwa ne da ni na sha gani da idanuna. Wani lokaci na tashi cikin dare zan yi sallah inji ana kurumtu ko a bayan dakin Baba ko na Alawiyya, watarana shara zan shiga yi a dakin Baba in ga kulli-kulli na magani ko dami na layu da dai tarkace a lungu da sako na dakin, sai dai in daukesu in shiga wajen su Inna in kona su. 

Bazamar da Alawiyya tayi wajen malaman Allah da Annabi domin neman kariya da kuma karyewar abubuwan dake kanta, itama ta fada cikin taskun bin malamai da yan tsibbun har ma da yan bori. Wannan masifa dana gani da idanu na, ta tsorata ni fiye da tunani na. 

Duk sallar duniya idan nayi, sai na roki Allah ya raba ni da zama da kishiya. Ya zamana tunanin zama da kishiya kadai kan sa inji kamar zuciyata zata rabe biyu. A zamanin budurcina, saurayi yana zuwa daya, tambaya daya ce: kana da ra'ayin zama da mata biyu nan gaba? Idan yace eh, to sai in ce Allah ya kiyaye hanya tun ma kafin tafiya tayi nisa. To da yake ma ba kula samarin nake yi ba, saboda a lokacin hankalina yana kan in gama sakandire da sakamako mai kyau, in samu in shiga jami'a. 


Allah Ya taimakeni sosai, gabadaya jarabobina na waec da neco suka yi matukar kyawu, sai dai kasancewar banyi jamb ba, -a cewar Baba in bari sai sakamakon jarabawar ya fita sannan-,  yasa da Baban su Kulsum ya tashi sai mata form din makarantar SBRS, kasancewar ita bata ci jamb ba, yasa na roke shi akan ya nusar da Baba nima ya sai min. Allah Ya taimaka ya siya min, muka samu admission muka tafi. 










  *☆⋆03⋆☆*







                  A SBRS muka hadu da Janan. Haduwa irin ta wajen registration, daga tambayar zuwa wajen signing, sai kuma muka ji cewa ai duk dakinmu daya, nan muka hade. Ita Janan wanda yake auren Yayarta shine ya mata hanyar zuwa can, a lokacin shine DG din makarantar ma. Amma da yake irin mutane ko in ce iyayen nan ne na da, bai barta ta zauna a gida ta huta ba, da kanta tayi komi na registration. 


Kasancewarmu a daki daya yasa zumuntarmu gaba daya tayi karfi. Yayarta, Anty Sa'a anan cikin makarantar suke zaune ita da maigidanta da 'ya'yansu, duk da cewa suna da gida a Zaria, amma bata taba zuwa can ta kwana ba, wani abu da Anty Sa'a din da maigidanta suka ce wai zai sa ta dinga slacking akan karatunta. 

Abotarmu tasa muka saba da danginsu sosai, har ma watarana Yayansu Bilal yazo ya daukar mana excuse, ya daukemu zuwa can gida Kaduna lokacin da aka yi bikinshi da Anty Ameerah. Yan'uwansu mutane ne masu mutunci kwarai, karimci da kyautatawa, jininmu ya hadu dasu sosai. Wannan shine ganina da Yaya Bilal na farko. 


Mun gama makarantar da sakamako mai kyau, amma ba wanda zai shigar damu jami'ar Ahmadu Bello ba. Da yake Remedial Studies ne muka yi, idan Allah ya taimakeka ka fitar da sakamakon da ake so, za'a baka gurbin karatu a jami'ar Ahmadu Bello, matakin karatu na aji biyu, to mu Allah bai kaddara zamu samu ba. Amma mun sake rubuta jamb, mun kuma samu sakamako mai kyau both a jamb da kuma post-utme. Cikin ikon Allah duk suka bamu course din da muke so, nursing. 


Nan muka koma gida muka fara shirin tafiya. Sai da muka tsaya aka yi bikin Kulsum. Kasancewar wanda zata aura ya dage akan yana bukatar ayi aurensu, yasa aka daura musu auren, da sharadin zata nemi gurbin karatu anan Umyuk, kuma zai barta tayi, yace ya amince. 

Bayan bikin, muka je muka yi registration. Na koma gida na kara kimtsawa na sati daya, na tafi makaranta. 


Mun shiga aji na uku muka hadu da Umar, ya raka kanwarshi registration lokacin. Shi NDA ta Kaduna yayi, ya samu ya gama, ya fara posting dinshi kenan muka hadu. Allah Ya taimake shi yana da hanya, shi yasa suka barshi a nan Zaria basu jefa shi waje mai nisa ba. 

Babu bata lokaci muka fara soyayya ni da shi. A duk tsayin rayuwata, wannan shine karo na farko da na tsaya nayi wata soyayya da wani da namiji, ban taba ba kaina wannan damar ba. 


Lokacin da ina gida da, na fara tsayawa da wasu. Sai dai, ban san dalili ba, duk wasu kalamai na so da zan ji sun fita daga bakinsu, sai inji ina karyata hakan. Wannan dalili yasa zancen ma baya yin nisa, ake watsewa. Daga karshe dai na fahimci cewa ban yarda da soyayyar bane. Duk lokacin da zan ji wani ya ambaci true love, to zan ce maka bata existing sai cikin littafan novels da fina-finai. Janan ta kan ce saboda ban samu wanda raina ya kwanta dashi bane, ko kuma ina jin tsoron commitment ne. Koma dai wannene, ban damu ba. 


Shi kanshi Umar din, lokacin dana fara amincewa dashi, ba so bane, it was more like burgewa ko kuma abokantaka. A lokacin I was in a desperate situation, you know irin lokutan nan da zaka ji kana bukatar wani a kusa da kai, bayan abokai da yan uwa of course, sai kuma ya kasance na samu duk wani abu da ake bukata a wajen namiji a tattare dashi Tattali,kulawa da saukin kai. Irin free-spirited mutanen nan ne, duk inda zaku zauna dashi, in shaa Allah zaka ji ya shiga ranka. Sai dai rawar kai da ba'a rasa samarin yanzu da ita, wanda shima sai da muka yi nisa da haduwa dashi sannan na fara karantar hakan, amma nasan cewa lokaci ne, zai daina, tunda ina matukar yin kokari wajen ganin cewa duk lokacin da yayi kokarin yi min maganar banza na dakatar dashi. Hakan yasa lokuta da dama zamu yi fada burum-burum dashi, daga baya dai zai sake dawowa mu shirya. 


Bayan wannan sai kuma daga baya da naji na zama very comfortable a tare dashi, ba kamar sauran samarin da nayi a baya ba. Ina jin shi kamar Janan, yadda zan zauna inyi hira da ita babu wani boye-boye, shima haka zan zauna inyi hira dashi. To ko bana son shi, a ganina wannan kadai ai zai ishi rayuwar aurenmu ko? Tunda mun fahimci juna sosai. Balle ma ina son shi. Duk da cewa maganar aurena dashi tana sa inji wani unsettling abu a cikina. Kodayake, har yau bai ma fara zancen auren namu ba, nafi tsammanin kila sai bayan mun gama karatu sannan, and I'm totally fine with that. 


Shekararmu ta farko a makaranta babu sauki, yanayin karatunsu mai zafi ne, duk da cewa mun yi wanda yaci uban wannan a SBRS, still, yana mana wahala. Ni a cikin hostel din makaranta na zauna. Yayin da Janan take zaune tare da matar Yaya Bilal anan cikin samaru. 


Yaya Bilal yana aiki da kamfanin jaridar daily trust ne. Kasancewar kamfanin yana Abuja ne, yasa yake tafiya can duk ranar lahdi da yamma ko litinin da safe, ya dawo ranar Juma'ah da yamma. Ban san dalilin da yasa bai tafi da amaryar shi ba, tunda naji Janan tace yana da gida acan Abujar. Ban kuma taba tambayarta ba koda wasa. Daga bakinta dai naji tace ashe ma gidan da suke zaune, mahaifin Ameerah ne ya sai musu gidan. Duk da abin ya daure min kai, ban tambayeta dalili ba shima. 


Na sha jin korafin bata jin dadin zama da matar Yaya, ban taba fahimtar dalili ba sai da watarana daya da muka je gidan. 

Muna cikin shirye-shiryen exams ne, Janan ta saba shigowa makarantar a ranakun weekends, muje library mu yi karatu. Ranar tana zuwa, Yaya Bilal ya kirata yana tambayar tana ina, ta fada mishi. Ba'a jima ba sai gashi yazo, ashe Anty Ameerah ce bata jin dadi, yace zai je ya dauko family doctor din su Ameerah din, muje mu tayata zama kafin ya dawo, a karo na barkatai, naji lamarin nasu ya daure min kai. Nan dai muka tarkata muka tafi. 


A kofar gidan ya ajiye mu ko ciki bai shiga ba, ya juya, mu kuma muka shiga ciki. Gidan nasu dan madaidaici, mai kyau. A kalla mun dauki fiye da mintuna goma sha biyar muna doka kararrawar sanar da zuwan bako gidan. Ina tunanin ba wanda yake cikin gidan ba, hatta da wanda yake makotaka dasu, yaji wannan bugu da muka dinga yi. Yadda Janan tayi, very calm and collected, babu alamun wata damuwa a tattare da ita, yasa na gane cewa wannan ba shine karo na farko da irin haka ta faru ba. 


Sai da aka kara kusan mintuna biyar sannan naji motsin taba kofa, aka bude kofar falau, cikin sanyin jiki duk muka shiga cikin falon. Ance wai shimfidar fuska tafi ta tabarma, duk da irin kayan alatun da suke cikin falon, hakan bai sa naji ni very welcomed ba a gidan. Ba'a bamu wajen zama ba, babu sannu da zuwa balle ga ruwan sha, haka aka barmu tsaye a tsakiyar falon dakin. Sai Janan ce ta min nuni da kujera, tace in zauna bari taje ta dauko min ruwa. Jiki a sanyaye na lalubi kujera na zauna, cikin nuna girmamawa na gaidata. Sai data gama shan kamshi sannan ta amsa, ya saukin jikin dana mata ma Allah bai bata ikon amsawa ba. Dama na gama shaka da ita, daga nan nima na maida kaina cikin wayata na cigaba da karatuna. A zuciyata kuma cike da mamakin wannan mata. Ita ba wata babba ba, saboda daga ganinta shekarun data bamu kadan ne, ita ba wata dangin sarauta ba balle ince ko jinin sarauta ne a jikinta, amma kice dole sai kin shimfida mulki? Duk da cewa yes, tana da kyawu Masha Allah, kuma daga yadda naji, mahaifinta mashahurin mai kudi ne, kila hakan ne yasa take dagawa. Na girgiza kai kawai. 

Ko kallon ruwan da Janan ta kawo min ban yi ba, Allah-Allah nake Yaya Bilal ya dawo, in narko wani excuse din in karawa bujena iska don ba zan iya zama a haka ba Allah ya sani. 


Muna zaune mu duka ukun, babu wanda yake cewa wani ci kanka, har rana ta daga sosai babu alamun Yaya. Gashi ko TV ba'a kunna ba a falon balle mu ce zata dauke mana hankali. Gabadaya naji na takura, ban iya dogon zama irin haka babu hira ko wani abu to discuss ba. Rawar kai na da tsokanata basa barina zama waje daya. 

Janan ce ta katse dogon shirun daya mamaye dakin ta hanyar tambayar ta, 'Anty ko za'a dora abinci yanzu ne?'.

Budar bakinta sai cewa tayi, 'daga gida za'a kawo mata abinci yau, bata son jin kamshin gas ko risho', da dai na samu na hana kaina daga kama baki in ce to?!, sai na bame bakina na kara tura kaina cikin wayata. 


Allah ya taimakemu Yaya ya zabi daidai wannan lokacin ya fado falon kamar an jefo shi daga sama. 

Tayi tsalle ta afka jikinshi, mu da muka dago da niyar yi mishi sannu da zuwa sai kasa muka yi da kanmu a rikice saboda ta'asar dake gudana. To ta'asa mana! Ba kullum bane kake ganin irin wannan 'intimate moment' a gabanka ba. Sai daya gama tsotse mata baki da fuska, sannan muka jiyo alamun tashin muryarsu kasa-kasa, hakuri ya dinga bata kan cewa bai samu ganin likitan nasu ba, kuma har gidanshi yaje, amma ko zata daure su tafi asibiti yanzu? Ta wani lankwashe murya kamar wata yarinya karama, tana cewa ai ita so tayi ya zauna kusa da ita kawai, bata wani bukatar likita. 

Nayi kokari na danne dariyar data kusa kamo ni, irin wadannan 'cheesy lines' din ai nayi zaton a films kadai suke amfani da novels, ba a ainihin rayuwarmu ba. 


Yaya ko kallon mu bai kara yi ba, ya dai jefo mana "ku zauna ku jira ni, ina zuwa!", bai jira jin ta bakinmu ba, ya ciccibi amaryarshi suka shige daki. Na kama baki na bi bayansu da kallo, a zuciyata ina kara tausayawa Janan. Idan har haka ake treating dinta a gidan Yayanta, Allah kadai yasan halin da take ciki gaskiya. 


Ta ja ni zuwa dakinta inda yake can cikin falon, can karshe kusa da wani karamin daki da suka mayar dashi kamar store. A gefen katifa duk muka zauna, na titsiyeta sai data bani labarin abinda yake faruwa a gidan, tun daga farko har karshe. 

Matar Yayanta irin matannan ne da idan Allah ya hada ka kishi dasu, taka ta kare. Babu boka babu malam, zasu dafa ka cikin ruwan sanyi ka kankare. Irin matannan ne masu dan banzan kissa. 

Tace a bayan idon Yaya Bilal, ita, Janan din da sauran dangin shi har ma da Ummansu, basu maraba da kayan wanki a wajenta, amma idan a gabanshi ne sai tayi ta tattalinsu tana ririta su. 


Ameerah irin sangartattun yaran masu kudin nan ne. A wannan shekarar ta gama karatunta. Bata aikin komi a gidan wannan sai zama, kallo da nanikewa miji. Tana da yan aiki kala-kala, don ma dai ba kwana suke yi a gidan ba. Da masu girki, masu sharar waje, masu wanki, har da masu gyaran daki, kuma duk mahaifinta yake biyansu. Tace yanzu haka garar da aka kawota da ita tana cike da store, ko alamun tabata ba ayi ba, saboda bata yin girki. Watarana ma daga gidansu takanas ake dafo abincin a kawo mata. Kai hatta da wutar amfani wannan ta gidan, mahaifinta ne yake biya. Yayan yayi magana game da hakan, amma mahaifanta suka nuna duk cikin son da suke yiwa diyarsu ne. 


Tunda Janan taje gidan, take gasa mata aya a tafin hannu cikin ruwan sanyi. Bata da bakin korafi saboda koda wasa bata bar hanyar da Yaya zai yi suspecting dinta ba. Spare makullin gidan da Yaya ya bata, ta amshe, kullum sai ta buga mata gida idan ta dawo daga makaranta, kuma sai ta wulakantata kafin ta bude mata gidan, store din abinci a kulle yake, wani lokacin sai dai ta saka kudinta ta sayi abinci. Idan Yaya baya gidan to ita da babu duk daya suke, duk kokarin Janan akan su daidaita abin yaci tura. Ita cewa ma tayi gwanda ace fada suke yi akan wannan zaman doya da manja din. 


Ita kuma tayi-tayi dashi akan ya bari ta koma wajen Anty Sa'a tunda suna Zaria yanzu, ko basa nan akwai kanwar mijinta da suke zaune tare a gidan sai ta zauna dasu, ko kuma ya kama mata gida a samaru, ko ma dai a ina ne, amma yayi fir ya ki. Ita kuma bata so ta takura mishi da maganar kada yace ko bata son zama da matar shi ne ko wani abu. 


Sai a ranar naji cewa ashe ba mahaifinsu daya da Yaya Bilal ba. Mahaifinsu Yayan ya jima da rasuwa, bayan nan ne ta auri wani mutum a Kaduna, shine mahaifin Janan din. Sai lokacin na fahimci komi, ina ta mamakin dalilin da yasa Ummarsu take zaune a Kaduna bayan duk danginsu suna Zaria, nayi zaton ko aikine ya kai baban su Janan din Kaduna. Amma nayi mamaki, koda wasa basu taba nuna mata banbanci ba, ita ko su Harira diyar kishiyar Umma, basu taba nuna mata wani ki ko kyama ba. 


Janan kuka take yi sosai lokacin da take bani labarin wannan, na rungumeta ina bata hakuri, don shine kadai abinda zan iya yi a lokacin, har ta gama kukan. Daga nan muka fito da littafanmu muka cigaba da karatu har aka kira sallah muka tashi muka yi, muka koma muka cigaba da karatunmu. Muna nan sai ga Anty Ameerah ta leko, tace muje mu debi abinci, Janan ta fita zata zubo mana abincin, sai gata ta dawo wai Yayan yace muje muci tare dasu. Tace haka yake, in dai yana gidan tare suke cin abinci. Na dauki hijabita na saka muka fita.

A falon sai na daga baki ina kallon ikon Allah, gabadaya mata ta rikide, ta koma kamar wata salihar kirki, kamar ba wannan matar da take amsa mana magana da dai-daya ba. 

Sai nan-nan take yi damu, abinci kamar zata zuba mana a baki yadda take ta turo mana plates na varieties din abinci gaban mu. Tsabar mamaki ma ni kasa yin magana nayi. Lallai an saka Janan a cikin tsaka mai wuya. Idan har haka take mata, to lallai kuwa babu wanda zai yarda da cewa idan an saka mata yatsa a baki zata ciza, sai dai idan har tayi hakan a gabanka. 


Muna gama cin abincin muka koma daki. Muna shiga na fara zuba magana, tsananin mamakin matar ya hana ni hada maganganu masu ma'ana ma, Janan sai gefe ta koma tana min dariya. Sai dana nutsu sannan na iya zama muka yi magana akan haka da ita. 


Sai bayan sallar la'asar can, sannan na mike ganin cewa Yaya bashi da niyar barin gidan. Janan tayi-tayi dani akan in tsaya Yaya ya fito, nace mata ina da abubuwan yi ne a hostel, dole ta kyaleni na tafi. 

Daga wannan rana ban kara taka kafata zuwa gidan Yaya Bilal ba har yau. 



Karatunmu yaci gaba da tafiya cikin nasara. Ni da Janan duk bamu dauki karatunmu da wasa ba, duk da bamu yin topping, amma dai Alhamdulillah, babu abinda ya taba dawo mana. 


Muna shekarar mu ta uku, Yaya ya sake yin wani auren, ya auro Anty Raheemah. Yadda ya rikice akan wannan auren, yasa na kara tsurewa da lamarin maza. Lokacin bikinsu da Anty Ameerah yadda yake ta rawar kai da zakewa, kai sai kayi zaton babu wata 'ya mace da zata sake yin daraja ko kuma a idonshi bayan ita, sai gashi tun ba aje ko'ina ba ya karo wani auren. 


Janan tace ba karamin rikici suka yi da matar Yayan ba, har ta kai ga cewa ya fita ya bar mata gida, inda abin ya yiwa Yaya ciwo matuka. Ya karasa gyara gidan gadonsu, dama can ya fara gyarawa zai kai Ameerah din, iyayenta suka hana.


An dai yi biki lafiya, despite tashe-tashen hankulan da aka sha, amarya ta tare a gidan mijinta, Janan ma tayi kaura can. 

Muna ta murna, a tunaninmu wannan zamu tafi da ita, tunda sa'ar mu ce ita, ashe yaudarar kanmu muke yi. 


Raheemah da kannenta irin 'ya'yan mace dinnan ne. Zaku yi mamaki idan kuka ji cewa suna da uba da yake raye, kuma auren iyayensu yana nan, amma suna zaune separately. Duniya da son abin duniya ya rufe musu ido daga su har uwarsu, mahaifinsu kuwa mutum ne mai wadatar zuciya da tsoron Allah. 

Tun yarintarsu, bin bokaye da malamai shine amsar tambayarsu da komi nasu. Kodayake, wanene a garin Zaria bai san da zaman Hajja Ladidi ba? Shi yasa tashin farko da naji wai Yaya zai auri daya daga cikin diyanta, abin ya bani mamaki kwarai. Sam ire-iren su ba irin wadanda yaya yake hulda dasu bane. 


Kannen Raheemah biyu da suka tare a gidan su suke kara rura wutar dake cikin gidan Yaya Bilal. Su duka biyun suna karatu a jami'ar Kongo. Saboda haka suka baro gidansu dake Hanwa, suka koma can saboda ya fi kusa da makaranta. Duk da a zahirin gaskiya ba hakan bane. Haleemo da Salama sune yan kanzagin ta, sune masu zuwa garuruwa da kauyuka amso mata magunguna wajen malamai da yan tsubbu yayin da take gida ta mike kafa. 


Sai da na yiwa Janan fatan dama a wajen Anty Ameerah ta zauna, tace mugun fata nake mata. A cewarta zama dasu Haleemo, duk da gallazawar da suke mata, yafi mata sau dubu akan zama da Ameerah. Don haka na kawo idanu na zuba mata. Don haka ban taba ganin laifinta ba don tana zuwa wajen Umma weekend ba duk karshen sati, watarana ma nima ina binta. 


To da yake ita rayuwa babu abinda hakuri baya maka, gashi yanzu har zamu shiga shekararmu ta karshe, ko ma in ce mun shiga. Duk da har yanzu dai babu abinda ya canza, sai ma karuwa da yake yi. Tun basa cin karfin Yaya akan Janan, har suka zo suka ci galaba a kanshi. Wasu lokutan haka zai birkice mata kamar ba Yayan nan nata mai son ta ba, sau tari sai dai ta kira ni tayi ta kuka, ni kam sai dai inyi ta bata hakuri. Rabin abubuwan da ake mata a gidan nan, ko Ummarsu bata sani ba, tunda duk cikin danginsu babu mai zuwa gidan balle yaga halin da take ciki. 


Shi kanshi Yaya din, yau da gobe ce tasa ya gane tana zaman gallazawa a gidanshi. Sai ma watarana da yazo ya tadda Sa'adiya wadda suke cewa Adi, kawar Raheemah din da take zaune a gidan, tana ta zagin Janan akan wai bata yi mopping din falo ba, ran Yaya ya baci matuka, ya tara su su duka ya ja musu kunne, kuma yace daga ranar duk wadda ta sake taba mishi kanwa a gidannan, sai ta bar mishi gida. Aikin gidan ma kuma daga ranar ya hana ta yi, ita ce dai taga dama taci gaba da yi, tunda kunnen kashi gareta. Duk yadda nayi da ita akan ta bari tunda yace ta bari din, kiyawa tayi. Don haka na zuba mata ido, ni dai nasan da ni ce, da zuwa yanzu su duka sun bar gidan. 


To rayuwar dai haka ake yinta, yau dadi, gobe madaci, gashi yanzu wasu abubuwan sun zama sai dai a tarihi. Nan da lokaci kadan ma, zata bar musu gidan. 






                                   *







        


     *☆⋆04⋆☆*






*                          ☆                       *



Har washegari Lahdi ina jiran Baba ya turo min kudin mota, amma shiru kake ji, kamar an shuka dusa. 

Na duba agogon dake daure a tsintsiyar hannuna, naga cewa karfe goma sha daya na safe ta wuce. Nayi kwafa. Wani text din na sake tura mishi. Sai can wajen karfe sha biyu da rabi naji karan shigowar text, na duba naga shine ya turo min kudin motar, nayi kokarin resisting takaicin daya tuko ni, zuciyata na tunatar dani gida za ni ba wani waje ba. 

Sai da nayi sallah sannan muka yi sallama da Aylah cike da kewa. Ina shirin fita kiran Umar ya shigo wayata, ya sanar dani yana waje yana jira na, don haka na ciccibi akwatuna na fita. 


Ya saka akwatin a bayan booth, ni kuma na bude gidan gaba na shiga. Ya shigo motar ya tashe ta. Sai daya tsaya a banki na ciri kudi, sannan muka tafi. Har tashar mota ya kaini. Sai daya biya min kudin mota, sannan ya min sallama. Na mishi godiya sosai. Allah ya taimakeni motar ta kusa cika, ba'a jima ba muka dauki hanyar Katsina. 




*



Karfe biyar na yamma a cikin garin Katsina ta mana. Motar tayi karan karshe a cikin tasha, a gajiye na fito daga motar ina mika. Na rataya jakata a kafada tare da daukar dan madaidaicin trolley din dana sako kayan da zan bukata na fita daga tasha din. Shatar adaidata nayi har unguwar Magama inda gidanmu yake. 


Madaidaicin gidane daidai masu rufin asiri. Na fita daga cikin adaidaita din bayan na biya shi kudin shi. Wasu daga cikin yaran gidan dake kofar gida suna wasa suka bazamo da gudu suna ihun min oyoyo, nayi dariya ina dukawa kasa yadda zasu ji dadin rungumeni sosai. Abbakar ya dauki trolley na, yayin da Auwal ya rike jakar hannuna, na kama hannun Mufeedah muka shiga gidan. 


Matan gidan suna zaune a tsakar gida, Anty Alawiyya na dura kunun aya da take yi na sayarwa a cikin gororin ruwa, Anty Ramata kuma tana kofar kicin a zaune, ina zaton ita take da girki yau. 

Duk suka saurara da abinda suke yi jin hayaniyar yara har muka shiga cikin gidan. Anty Alawiyya ce ta mike tana dan murmushi, "mutanen Zaria ne yau a garin? Ai bamu ji labarin zaki zo ba koda wasa!".

Nayi murmushin yake, dama a ina zasu ji? Na san koda wasa Baba ba zai fada musu ba. Ni kuwa dama ba waya muke yi dasu sosai ba, tunda na fara makaranta, babu wadda ta taba daga waya ta kira ni da sunan mu gaisa, sai nice idan naga an kwashi kwanaki nake kiransu haka nan dai, musamman ma don mu gaisa da yara. Kullum idan na dawo daga makaranta zancen daya, ne babu wani canji. 


Na sauke Mufeedah kasa tare da gaidasu daya bayan daya, suka amsa fuska babu yabo babu fallasa, na tabe baki tare da ciccibar akwatuna na tunkari dakin daya kasance nawa tunda muka dawo Katsina. 

Na ja nayi turus, sakamakon ganin kofar dakin a bude, abin ya bani mamaki. Na tabbata da zan tafi makaranta sai da na saka kwado na rufe kofar dakin, kuma ban bar dan makullin a gida ba. Babu wanda yayi tunanin yi min karin bayanin abinda yake faruwa, don haka na tura kofar dakin. 


Abu na farko daya fara min sallama shine tarin kayana da aka hade waje guda acan karshen lungu, akwatuna daya kan daya, kwalaye bisa kwalaye, yayin da ilahirin tsakiyar dakin yake shake da tarkacen kayan Maryam. Na juya na kalli Saudah yar autar Anty Ramata dake zaune a kofar dakin mamanta dake kusa da dakin da nake, nace mata "waye yake kwana a dakina?".

Tace "Anty Maryam ce, Mama tace ta koma dakinki tunda kullum a kulle yake kuma tayi girma da zama a dakinta".


Nayi kwafa ina kallon Uwarta ta, nace "shine saboda tsabar bani da muhimmanci babu wanda yayi tunanin sanar dani?". Duk suka yi tsuru su biyun. Na sake yin kwafa tare da shiga cikin dakin. Ko karewa dakin kallo ban yi ba naje na dauro alwala na dawo dakin nayi sallah. Sai dana gama sannan na kira Umar na sanar dashi sauka ta, yayi min sannu da zuwa. Bayan nan na kira Janan itama muka gaisa, tana dariya tace "bana miki wayo, ni tun safe ina gaban Ummana!". 

Nayi yar dariya, "ya miki kyau ai, Allah ne ma yasa motar tayi gudu sosai, kila da sai magriba zan iso ni kam".

Mun dan yi hira kadan da ita, har ta bani Umma muka gaisa, sannan muka yi sallama da ita. 


Tashi nayi na fara gyara kayana da aka wulakanta a dakin, ina maida su ainihin wajen da suke da. Kafin a kira sallar magriba na kammala gyarasu tas. Nayi sallah, na zauna akan abin sallar nayi karatu kamar yadda na saba har aka kira isha'i nayi, sannan naci gaba da gyara dakin. Na share shi nayi mopping, na dauko room freshener dana saba yin guzurinta na fesa a dakin. Nan da nan dakin ya fito tas dashi, ba kamar yadda na same shi dazu ba kamar bana mahaukata. 


Tun ina karatu naji alamun karan motar Baba alamun ya dawo gida. Kasancewar yau babu aiki nasan cewa daga shago yake. Zuwa yanzu nasan cewa ya ci abinci kuma ya huta, na dauki hijabina na fita zuwa dakinshi. Babu kowa a dakin na shi sai shi kadai. Na durkusa acan gefenshi na gaida shi, ya amsa. Da alamun yana cikin yanayi mai dadi, tunda har na zauna muka danyi hira dashi. Abinda sai lokaci zuwa lokaci yake faruwa. 

Ban san me yasa ba, ni da Baba sam bamu cika shiri ba. Amma nafi kyautata zaton rawar kaina ce ta janyo hakan, tunda ya sha fada ba sau daya ba, ba sau biyu ba. 

Sai da Ramata ta shigo dakin sannan na mishi sai da safe, na koma dakina, ko ince dakinmu. 


Ina komawa shirin barci na fara yi. Bayan nayi Sallar shafa'i da wutiri, na samu gefen katifa na zauna tare da dauko wayata dana ajiye a kasan filona. Ina cikin chatting Maryam ta shigo cikin dakin. 


Duk yan dakin Ramata, ita, Aliyu da Hareerah, da ita kadai muka fi dasawa. Sauran suna kan hudubar uwarsu na cewa 'yan uba, ba 'yan uwa bane! saboda haka bamu cika shiri dasu ba. Amma ita babu ruwanta ko kadan. 


Tayi murmushi tana kallona, "yanzu Hareerah take fada min cewa kin zo, ina ta mamaki".

Nayi yar dariya ina kallonta tana zame after dress din dake jikinta, riga top mai karamin hannu da wnadon bakin jeans suka bayyana a jikinta, dariyata ta koma daga gida mai nuna alamun tambaya, nace "daga ina kike, kuma wannan shigar fa?".


Ta kalli jikinta kafin ta kalleni, "kawata take bikin birthday, shine na leka wallahi".

Na girgiza kai, "birthday party kuma sai da irin wannan shiga Maryam? Me yasa?".

Tayi dariya, "Yaya Na'ilah ke da kike makarantar jami'a kin fa fini sanin irin wadannan abubuwan. Yanzu 'yanmata ai sai da swagger! Idan mutum ba so yake a dinga mishi kallon taro-uku-sisi ba!".


Cikin mamaki nake kallonta, "ban san daga ina kika dauko wannan kalar abu ba Maryam, amma hakan bai kama ce ki ba gaskiya. Ta ya kike zaton Mamanki zata dauki wannan maganar idan taji irin shigar da kike boyewa a cikin hijabi? Don daga ji nasan cewa wannan ba shine karonki na farko ba".


Tayi dariya tana watso min wani kallo irin 'are you kidding me' dinnan Tace "me Mama zata ce kuwa? In fada miki gaskiya ita ta bani shawarar in dinga sanya after dress idan zan fita, in naje can inda zan je sai in cire saboda kada wani idon sani ya ganni a haka... Amma meye na wani boyo? Zamaninmu ne fa!".

Tunda ta fara maganar bakina a hangame yake a bude, Subhanallah! Yaushe yaran gidanmu suka fara bin wannan hanyar ne? Nasan cewa tsakanin iyalan dama babu hadin kai da kaunar juna, saboda tun farko basu ga hakan daga wajen iyayensu ba, amma wannan wani babban al'amari ne, wanda nake ganin idan har aka bari ya girmama, akwai matsala. To amma, abinda uwa take supporting da dukkan karfinta, waye yake da karfin hana ta? 


Ta tunkari kofa zata fita tana furta, "bari in zo inyi sallah!".

Ina nan zaune ina ta saka da warwara ta dawo, ta shimfida abin sallah ta kalli gabas. Yadda take yin Sallar ma kadai abin zai baka mamaki. Kamar wadda bata taba taka ajin islamiya ba Raka'o'in data jero masu yawa yasa na fahimci cewa ba sallar isha'i kadai tayi ba. 


Sai dana bari ta gama duk abinda zata yi, har ta kwanta sannan na dubi inda take, nace "ni kuwa a wani matakin karatu kike yanzu a islamiya?", na dai san cewa yanzu tana ss2. 

Tayi dariya, "na kusa wata ma ni rabona da makarantar nan yanzu, yan ajinmu aka wa karin aji zuwa na yan sauka, ni kuma aka barni a ajin baya shi yasa na daina zuwa ma kwata-kwata".


Na tashi zaune sosai ina kallonta, sanin halin Maryam na saurin fahimta da ganewa yasa nafi jin dadin zama yi mata magana ko gyara akan wani abu, ba kamar Aliyu ba. Sau tari dan karamin gyara sai ya kaimu ga ya kalli tsakiyar idanuna ya zage tas kamar wanda yake jira dama. 


Nace "kin san fa yanzu kece babba a gidannan Maryam. Kuma duk abinda kika yi, kannenki da suke tasowa shi zasu dinga yi. Yanzu idan basu ga yayarsu na zuwa makaranta ba, ta ya kike tunanin zasu samu kwarin gwiwar zuwa makaranta? Kinga ke dai baki da bakin cewa su zo su tafi, tunda kema ba zuwa kike yi ba. Sannan dubi dai irin shigar da kika yi yanzu, ya Baba zai ji, kuma me kike zaton zai ce duk ranar da yaci karo da irin wannan abu da kike yi? Maryam, kinga ke diya macece, sannan yarinya, kada ki bari rudin duniya da abokai ya rude ki, ki saka kanki cikin rayuwar da tafi karfinki. Shiga irin wannan da kike yi ta nuna jiki, ki shiga cikin kawaye ana ta cakuda da maza, akan wane dalili? Ina kika baro tarbiyar gidanmu da kuma al'adarmu ta hausa/fulani?".


Tayi kasa da kanta a kunyace, "wallahi Yaya, Mama ce take cewa in dai ba za'a hada mu da yan ajinmu ba, sai dai in daina zuwa makarantar. Kuma ita take sawa inyi shigar. Ranar ma ana bikin Na'imah dana sanya hijabi sai ta hau fada, tana cewa wai ni ban waye ba!".


Na girgiza kai cike da jimami, iyayen yanzu yawanci su suke bada gudummawa wajen lalacewar tarbiyar yaranmu. Uwa ce wai zata dorawa diya akidar yafa gyale da saka suturun banza, ita zata sanya mata akidar bin kawaye da samarin banza, daga karshe kuma idan lamari yazo ya bace bakinta ne zai fi na kowa wajen ihun cewa an lalata mata tarbiyar yara, bayan kuma itace tayi contributing wajen lalacewar tata. 


Tsam na tashi na koma kusa da ita na zauna tare da dafa kafadarta, nace "idan tayi hakan ba laifi bane, tana so ne ki zama abar kallo, kamar tauraruwa. Sai dai, zaki iya zama fiye da hakan ma, ba kuma sai kin sabawa Ubangiji ba, kin gane?". Ta daga kai. 

Nace "good. Saboda haka gobe zamu je islamiyar taku, zan samu malaman naku muyi magana dasu. Sannan don Allah, shiga ta banza mai nuna jiki, ki daina yin ta. Ko ba don ke ba, ki duba kimar da Baba yake da ita a idanun mutane, balle ke kanki idan baki kame kanki a matsayinki na ya mace ba, Maryam zaki ga kin rasa girmamawar mutane, kin fahimce ni?". Nan ma ta gyada kai. 


Nayi murmushi cike da jindadi. Yanayin yadda jikinta yayi sanyi ya nuna min cewa taji, kuma ta dauki abinda nace. Na rungumota gefen kafadata ina kara yi mata bayanai da nasiha akan rayuwa. Daga karshe dai na janyo laptop dita na kunna mana kallo a ciki, babu TV a dakinmu sai na Baba dana matanshi, yawanci can muke zuwa muyi kallo. Ranar akan katifarta na kwana. 


Tunda Baba ya tashemu sallar asuba ban koma barci ba. Ina gama azkar din dana saba yi lokacin gari ya fara yin haske, na fita na share tsakar gida tas. Na hada kayan wanke-wanke nayi, na shiga kicin na kunna wuta tare da dora ruwa wanda yara zasu yi wanka dashi na kuma dora musu abincin da zasu tafi makaranta dashi. 

Har wajen karfe bakwai na safe ban ga motsin kowa a tsakiyar gidan ba. Matan sun riga da sun san dama ni nike ayyukan gidan, shi yasa daga ranar da nazo, har in bar gidan babu wadda take ayyukan gida. Duk da har yanzu Ramata bata sakar min ragamar ayyukanta ba, ranar girkinta ita take yin girkinta gabadaya, wanke-wanke da shara ne dai take bari na dasu. Hakan bai dameni ba. 


Yanzun ma ina kan zuzzubawa yara taliyar dana dafa musu a cikin kulolim makaranta, sai gata ta fito daga dakin Baba. Kicin din ta shigo, na gaidata ta amsa. Tukunyar ruwan zafi ta bude, ta zuba daidai wanda zata hadawa Baba shayi ta fita daga kicin din. 

Daya bayan daya yaran suka fara fitowa, na dauki kofi ina zuba zuzzuba musu. kowannensu yazo, sai ya duka ya gaida ni, ni kuma sai in mika mishi kofin shayi da biredi ya amsa ya tafi. 

Maryam da take tsaye a gefena tun dazu, tayi murmushi lokacin dana mikawa Auwal nashi kofin shayin bayan na shafa kanshi. 

Tace "shi yasa nake son ki zo gida wallahi, yaran nan sun fi behaving. Yanzu da ni ce da har yanzu ina nan ina ta faman su zo su amshi abincin, amma su ki".

Nayi dariya, "kin san yara sai da lallashi da lalama. Yadda nasan halinki na zafin kai dama, ta ina yara zasu dinga binki sau da kafa?".

Duk muka yi dariya ni da ita. Itama na zuba mata nata ta tafi ta karya. 

Ban fita daga kicin din ba sai da duk suka tafi, sannan nima na zuba nawa nan tafi daki na karya. 


Bayan na gama gyara kicin, wanda nasan idan ban gyara ba haka zan dawo in same shi. Musamman ma tunda yau da safe Ramata ta fita daga girki. Haka kuma Anty Alawiyya zata shiga tayi nata girkin ta barshi kaca-kaca. Na girgiza kai cike da takaicin halayen wannan matan. 

Dana gama da kicin daki na koma shima na gyara shi. Kai tsaye wanka na fada, na sanya riga da zani na atamfa, dinkin single da fitted riga. Sallama na wa mutanen gidan na shiga cikin unguwa. Daya baya daya na bi gidajen makota muna gaisawa, daga karshe na dire a gidan su Kulsum, a raina ina ayyana sai da yamma sannan zan je nata gidan, in yaso bayan magriba sai in dawo. 


Ina yin sallama a tsakar gida, na ja nayi turus ganin yar halas din a tsakiyar gida tana wa yarinyarta yar shekara uku, Muneerah wanka. 

Tana ganina tayi murmushi, "saukar yaushe?".

Nayi dariya ina zama a gefenta, "jiya da yamma wallahi. Me kike yiwa mutane a gida haka tunda safiyar Allah Ta'ala? Inna ina kwana?". Na gaida Inna data fito daga cikin madafi. Inna ta amsa tana min sannu da zuwa. 


Na kalli Kulsum, "ko dai awon ciki kika zo ne?".

Ta dan harareni, "wani irin awon ciki kuma ana zaman lafiya? Mu a gidannan ma muka kwana in fada miki!".

Jikina yayi sanyi da jin abinda tace, nace "kamar ya? Ban gane ba, wani abu ya faru ne?".

Inna tace "menene ma bai faru ba yar nan? Ai tafi wata daya a gida yanzu".

Naji zancen kamar wani saukar guduma a kaina, nace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un!".


Inna ta girgiza kai kawai, "ai ke dai abin ba'a cewa komi Na'ilah. Sai dai abinda Allah ya kaddara dama babu makawa sai ya faru, sai hakuri kawai".


Na fara cira idanu tsakanin Inna da Kulsum, Babu wanda ya sake yin magana a cikinmu har ta gama yiwa Muneerah wankan, ta tsaneta cikin zani. Muna zaune ta shiryata cikin kayanta, ta tura ta zuwa wajen Inna. Kallo kawai nake binta dashi. 

Tun can nasan cewa dama suna ta faman samun sabani da mijinta Mukhtar. Ko waccan zuwan da nayi dama, sai da suka sha dabi har sai da Iyaye suka shiga cikin maganar. Sai dai wannan karon, jikina yana bani cewa wannan yafi karfin fadan da suka saba yi. 


Tana gama hada kan kayan, na ja ta zuwa dakin da yake nata da. Tarin akwatunan dana gani da kuma kayan kwalliyar daki yasa naji jikina ya kara yin sanyi. Na zaunar da ita a gefen gado nima na zauna, tun kafin in daga baki ma in tambayeta ta riga ni, tace "rabuwa muka yi da Abban Muneerah!".


Na zare ido kamar zasu fado kasa, na kara yin wani salatin dai na sanar da Ubangiji. Ta girgiza kai, "Abban Muneerah ya rikice. Zama yaki ci yaki cinyewa. Ki duba lokacin da aka yi aurenmu, yazo ya hana ni karatu kiri-kiri, haka muka hakura ni dasu Baba. Yazo ya dinga gallaza min a zamanmu, wasu abubuwan ma kawai shiru nake yi. Tun ina kawo kara gida ana mishi fada, har aka daina. Abinci wannan haka ya dinga gagarata a gidanshi, ke kin san yawancin abubuwan dake faruwa. Sana'a na fara yi da kudina, amma haka zai zo ya cinye kudin kuma ya hana ni. Kwanan nan aka ba Inna kudin adashi, ta hada kan kudinnan ta sai min keken dinki, wallahi ko sati uku keken bai rufa ba ya dauke shi yaje ya sayar. Wai kudin toshi ya kai da kudin...". Kuka ya kwace mata anan. 

Na dafata ina lallashinta har tayi shiru. 


"Ashe wata ce ya hango a wajen aikinsu. Bai ma gaya min yana nemanta ba, sai a gari naji labari. Wata makociyata ta jiyo labarin take gaya min. Dana tuhume shi, kai tsaye ya amsa babu musu. Na tambayeshi dalili, sai cewa yayi saboda tana da ilimi, kuma ta fi ni hankali da natsuwa. Nace laifin waye to da bani da ilimin? Sai ya hau cewa ni ce sakara ai. Daga wannan rana gabadaya sai ya kara rikicewa, wallahi bamu kara samun zaman lafiya ba. A gabana zai kira ta a waya, su raba dare suna hira, tun ina kuka har na hakura na daina. Iyayenmu duk sun shiga cikin maganar, Kawu Bala da yaje akan maganar baki ji zagin kare dangin daya mishi ba, yace ina ruwanshi tunda ni matar shi ce? Bashi da ikon da zai hana shi yin abinda yaga dama. Ke magana taki ci taki cinyewa fa. Ranar nan kawai ina zaune da dare, sai gashi ya shigo gidan. Yace min an sanya aurenshi watanni biyu masu zuwa, nace mishi to Allah ya sanya alkhairi, yace ameen. Washegari wai sai ya sameni yace shi tafa bashi da wajen da zai saka amarya idan tazo, nace 'to Abban Mufeedah, ya kake so ayi kenan?', bai ce komi ba dai ya tafi. Haka muke ta zama dai, hatta yan uwanshi sai da suka fara shigowa suna zagina. Wai ni matsiyaciya ce, ban iya komi ba sai ci. Ita kuma wadda yake neman auren tana ta musu hidima. Abubuwa fa duk suka rikice. Yanzu kawai ranar nan ina zaune, sai gashi yazo da takarda ya miko min, wai ya sake ni saki biyu. Nace 'me na maka?', sai ya hau zage-zage da daga jijiyar wuya, wai shi dama can ya gaji da zama dani, yana ta hakuri da nine dama, kuma hakurinshi ya kai makura, in fita in bar mishi gidanshi kawai. Nace to shikenan, shine na tattara kayana na dawo gida abina!".


Cike da jimami nace "to Allah yasa hakan shine mafi alkhairi. Kuma babu wanda ya same shi game da maganar akan haka?".

Tace "ace mishi me Na'ilah? Last week aka daura mishi aure, har cikin gidannan yayi sallama ya kawowa Malam katin gayyata".

Na zare idanu, "ikon Allah! Wannan ai cin fuska ne!".

Tayi dan murmushi cike da takaici, "cin fuska kuma wani iri ne ban gani ba a wajen Mukhtar? Ai sai dai in karas kawai. Kuma yaje na barshi da Allah!".


Nayi saurin girgiza kai, "a'ah, kada ki ce haka mana. Ko babu komi mahaifin diyar ki ne, kuma akwai sauran igiyar aure a tsakaninku, idan Allah ya nufa sai ki ga kun komawa aurenku!".

Tace "da wa? Allah ya tsareni wallahi. Kinsan cewa sauran Kayankayan dakina da ba'a dauka ba, ya sayar dasu?".

Nace "me yake damun wannan mutumin ne haka?".

Tayi kwafa, "tijara mana! Su Malam zasu yi magana, nace su barshi. Wallahi na yafe mishi duniya da lahira, Tunda dai na samu aka rabu lafiya, to ni na godewa Allah".


Na janyo ta jikina na rungume cike da nuna lallashi, nace "to Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a gareku ku duka".

Tace "Ameen. Ni yanzu haka so nake in gama iddata, makaranta zan koma in cigaba da karatu na".

Nace "haka ne, Allah ya sanya albarka to. Allah kuma yasa hakan shine daidai".

Tace "Ameen. Ina Janan?".

Daga nan muka canza akalar hirar zuwa ta Janan. Sai ma dana kirata muka sha hira da ita. Ita kanta taji haushin abinda Mukhtar din yayi, ta ma so ta fi ni jin zafin abin. Sai data gama kumfar baki sannan kuma muka hau hira. 


A gidan na yini, muna daki muna ta maida bayanai, irin zaman da suka yi da tsohon mijinta, da yadda danginshi suka juya mata baya lokaci daya. Wasu abubuwan ma dai gwanin ban takaici. Tunda kwata-kwata wasu abubuwan kawai sai dai fa yayi su ya kawo wani excuse da bai hau ba ya dora. Kawai abin dai dama kamar yana neman hanyar fita ne, shi yasa. 


Da lokacin yin abinci yayi na shiga gida na dafa, na koma muka dora daga inda muka tsaya. 


Da yamma na raka Maryam islamiyarsu, na samu malamanta muka yi magana dasu. Korafinsu daya, rashin maida hankali da take yi. A sati bai fi taje makaranta sau biyu ba, idan tayi da yawa sau uku. Na musu alkawarin idan Allah ya yarda za'a mata magana, nan suka ce idan ma ta maida hankali zata iya bin yan ajin nasu, dama as a warning ne yasa aka yi mata hakan, ko zata hankalta. Nan dai na musu godiya tare da biyan kudin watanta da bata biya ba, tace Baba ya bata amma cinyewa nayi. Anan na barta ni kuma na koma gida. 



Kwana na shida a gida, komi yana tafiya yadda yakamata. Yawanci a gidan su Kulsum nake yini. Da safe idan na gama yin komi nawa zan shiga can. In taya ta aikin awara da dankali da take yi na saidawa da rana. In muka gama kuma mu hau aikin zobo shima da take yi ana kaiwa shaguna suna sai da mata. Haka dai nake juya rayuwar tawa. 




Na shigo gidan kenan da yamma, daidai kofar dakin Aliyu dake kusa da kofar gida naji motsi da hayaniya. Sautin kida yana ta tashi daga dakin nashi. Na girgiza kai, ban san me yake damun yaron ba, haka zai tara yaran unguwa sa'anninshi su yi ta hayaniya a daki. Basa komi sai jin kida da wake-wake. Bana tunanin yaje makaranta ma yau. 

Har na wuce ta kofar dakin, sai kuma na koma sakamakom hayaki da naga yana fita daga jikin labule da aka sakaye dakin dashi. Daga farko nayi tunanin ko girki ne yake yi a dakin, tunda wasu lokutan yana shiga cikin gidan ya kwashi garwashi yace zai dafa ruwan shayi. 

Sai dai abinda na gani ne yasa na yaye labulen dakin sosai. 

Shisha ce a tsakiyar dakin, sun sakata a tsakiya shi da abokanshi su uku suna zuka. 


Nace "Aliyu!! Meye haka kuke yi?".

Duk suka dago a tsorace suna kallona, sai dai idanun Aliyun kyar suke a kaina, babu ko dar a cikinsu. 

Na harari abokan nashi da suka yi cirko-cirko a zaune, nace "ku tashi ku fita". Babu musu suka mike sumi-sumi suka fita daga dakin. 

Na maida kallona ga Aliyun, nace "kai yanzu abinda kake yi dama a cikin dakin kenan kai da abokanka? Shi yasa kullum kuke shiga ku rufo daki a rasa abinda kuke yi?".


Ya mike tsaye yana wani muzurai, "to meye hadin mutum dani? Naga cewa dai rayuwata ce bata uban wani ba! Meye hadinki dani?".


Nace "ko banza naci darajar kasancewa yayarka Aliyu. Wannan sam ba dabi'ar data dace bace, ka rasa a inda ma zaka sha shisha sai a gidan mahaifinka?".

Caraf! Sai Ramata ta cafe maganar, "kinga kada ki sake cewa d'a na yana shaye-shaye. Gwanda ma shi an san abinda yake yi, kuma a gabanmu yake. Ke waya san wace tsiyar kike yi a can?".


Na kalleta idanuna har juyawa suke yi saboda yadda maganganunta suka dake ni, nace "ke kan ki kinsan cewa nafi karfin yin wannan rayuwar da kike ambatowa, kuma karya kike yi kice saboda bana gaban iyayena zanyi rayuwar da bata dace ba!".


Ai sai shima Aliyun ya hayyako min, "kada ki kuskura ki zagar min uwa fa!. Ba gaskiya ta fada ba? Ke har kina da bakin kirana dan shaye-shaye??".

Nace "Aliyu ka kiyaye ni, kada bakinka ya sake kuskuren ci min mutunci!".

Sai ya kara matsowa daf dani, "idan naki fa? Nace idan naki fa? Kashi zaki bani? Ke din banza! Ke har kin isa ki zauna kina gaya min kabli da ba'adi? Wallahi idan baki kiyaye ni ba sai in kwantar dake anan wajen!!".

Ramata tace "yayi daidai da na. Yanzu na tabbatar da cewa nice na haife ka! Ka cika da!!".


Inna data jiyo hayaniya da wata Assibi makociyar mu suka shigo, itace ta tari bakin Ramata din, tace "haba ke kuwa! Da girmanki zaki biyewa yara har ki goya mishi baya. Yanzu ko Na'ilah bata girmi Aliyu ba, ai tana da damar idan yayi abinda bai yi daidai ba ta kwabar mishi!".


Sai ta harari Innar, tace "yo meye a cikin shishar? Uban wa yace miki kayan shaye-shaye ne ita?".

Inna ta kama baki cike da mamakin zagin data yi. Assibi tace "amma kuma ai daga nan yara suke ganin hanyar shaye-shayen ko?".


Sai Ramata ta kara kumbura, ta karkace daurin dankwali ta kawo shi goshi ta kafe. "ni fa dama ina sane da duk munafurcin da kuke min a cikin unguwar wannan musamman ma ke!", ta nuna Inna. "Na'ilah tana zuwa gidanku kuna zagina da gulmata. To wallahi ta Allah ba taku ba! Kuma ni da 'ya'yana nan gani nan bari. Idan ma wani kulli ake musu don su lalace to wallahi sai dai dan wani ya lalace don ni naci dubu sai ceto! Kuma bari uban Na'ilar ya dawo, sai ya gaya min in uban wani ne ya haifar min diyana ko ni!!". Ta kama hannun Aliyu suka shige dakinta ta barmu anan a tsaye. 

Assibi tace "to kuwa Allah ya kyauta miki gaskiya lamarinki sai du'a'i!".

Tuni mutane har sun fara shigowa gidan jin hayaniya. Inna da Assibi ne suka kore su, bayan sun tafi suka lullube ni suna bani hakuri. Ban iya magana ba, na zame na shige daki. 


Ina shiga daki jikina ya shiga rawa, na zame gefe katifa na zauna. Ban iya rigima ba ko kadan. Sam bani son rigima. Barni da tsiwa dai da mita, da kuma rashin barin ko ta kwana. Abin ya min ciwo kwarai da gaske, kanina wanda na bashi shekarun da suka fi yatsun hannu, zai tsaga tsakiyar idanuna yaci mutuncina a gaban uwarshi. Kuma nasan cewa ya zage ni a bulis, nasan cewa ko na gayawa Baba babu abinda zai yi akai. 


Abubuwa irin wadannan ba yau ne suka fara faruwa ba, kuma kowane lokaci haka abin yake, ya zageni, kuma bani da bakin ramawa ko na kai korafi, sai dai in shige daki in shaki kuka. To na gama kukan. Nayi alkawarin in dai akan Aliyu da uwarshi ne, to na daina kuka. 


Wayata na janyo, banyi tunanin komi ba na dannawa Ya Mudatthir kira. Ina jin sautin muryarshi, naji na fashe da kuka. Take naji ya rikice, ya fara tambayata lafiya? Me ya faru? Duk yadda naso in daina kukan kasawa nayi, sai da nayi mai isa ta, sannan na fara zayyane mishi dukkan abinda ya faru tun daga farko har karshe. Nasan wasu abubuwan kawai yaji su ne ba don ya fahimta ba, saboda yadda muryata dama jikina suke rawa. 


Bai katse ni ba har na gama mishi bayanin, sai dana gama sannan ya fara jefo min tambayoyi. "ita babar tashi me tace ne?".

Nace "itama fada ta hau yi, tana cewa wai nace mishi dan shaye-shaye, kuma ni wallahi ban ce mishi haka ba. Kawai magana ce na mishi!".

Yace "na sani Na'ilah, nasan ba zaki ce mishi haka ba. Zan kira Baban anjima, yana nan aka yi?" 

Nace "a'ah, baya gida".

Yace "to shikenan. Kina son zuwa nan ne?".

Da sauri na hau daga kai kamar yana ganina, nace "ehh!". Yayi yar dariya, "to shikenan, zan turo miki kudin mota. Idan zaki iya tahowa gobe, sai ki taho. Idan kuma baki samu dama ba, sai ki bari sai jibi".

Nace "to Yaya, nagode. Allah ya kara girma".

Muka yi bankwana dashi na kashe wayar. 


Sau tari ina fata dama ace ni ce na samu damar da Yaya ya samu. Yana gaban danginmu lullube dasu hankalinshi kwance. Tun lokacin daya gama sakandire, Yobe ya koma yayi degree dinshi acan. Da Allah ya taimake shi ya samu aiki yana gama makaranta, sai ya zaune acan abinshi. Ni kam tsakanina dasu sai dai zuwa hutu, ko kuma idan wani daga cikinsu yazo, ko kuma wata sabga ta biki wanda Baba bai cika bari na naje ba. 


Duk da hakan akwai shakuwa da kusanci a tsakaninmu dashi sosai. Yana so na kuma yana tattalina. 


Ina gama sallar isha'i na hau hada kan kayana waje guda. Maryam da take kwance tana kallo ta kalleni, "wai garin zaki bari ne kike hada kaya?".

Nayi dan murmushi, "wallahi kuwa".


Ta tashi zaune, "ba dai akan rikicin dazu bane ba ko?". Tunda aka yi abin ma ni babu wanda ya tuntube ni da zancen, sai naji abin ya dawo min sabo. 

Na girgiza kai, "ko kadan. Dama ina son zuwa".

Tace "to shikenan. Ki dai kara hakuri don Allah. Mama ta daure mishi gindi da yawa wallahi, ni kaina rashin kunya yake min, bani da yadda zanyi dashi kuma".

Kai kawai na iya daga mata don bana ma son maganar tayi tsawo. 


Washegari tunda safe nayi wanka na shirya tsaf, na fito da akwatuna na ajiye a kofar daki nayi sallama a kofar dakin Baba. Sai da aka amsa min sannan na shiga. 

Yana zaune a kan kujera yana duba jarida, na durkusa a gefenshi na gaida shi ya amsa. Nace "Baba zan tafi Gashua!".


Nayi zaton ma zai yi magana akan zancenmu da Aliyu, ga mamakina bai ce komi ba, sai tambayata da yayi, "shi wanda yace kije din, ya baki kudin mota ko? Don bani da kudin da zan baki".

Na gyada kai, nace "ehh".

Yace "to madallah. Allah kiyaye". Daga haka ya maida kanshi ya cigaba da karatun shi. Na tashi na fita daga dakin. 


Sai dana bi su daki na musu bankwana, Maryam ta taya ni daukar akwatina muka fita. Na shiga gidan su Inna su ma na musu sallama. Kulsum da Maryam suka raka ni har bakin titi kasancewar babu ababen hawa tunda safiya ce sosai, na tari adaidaita sahu na hau muka tafi tasha. Motar Kano na hau, tana cika muka dauki hanya.















         *☆⋆05⋆☆*






Tunda muka isa Kano da misalin karfe goma na safe,  muka hau motar Gashua. Sai a tasha na samu yogurt mai sanyi da cake na ci. zuwa karfe sha daya muka dauki hanya. A Hadejia muka tsaya aka yi sallah tare da cin abinci, muka sake daukar hanya. Karfe biyar da yan mintuna muka shiga garin Gashua. 


Yaya Mudatthir da kanshi yaje ya dauko ni. Ya kalli yadda nayi wuki-wuki saboda gajiya yayi dariya, "Subhanallah!! Illo! (nick name din da yake kira na dashi), you look like a total mess!".

Nima nayi dariya, "Yaya tafiyar awanni fiye da bakwai a mota ai ba ta wasa bace ba!".

Ya gyada kai, "kwarai kuwa. Sannu da zuwa. Ya hanya?".

Nace "Alhamdulillah". Ya taya ni daukar akwatina ya dora akan mashin dinshi, nima na hau muka tafi. 


A gidan Bako ya ajiye ni, ko shiga bai yi ba yace min zai dawo bayan magriba, na mishi godiya. Ya juya ni kuma na shiga gidan wani almajiri ya biyo ni da akwatina. 

Inna Fatsu na gaban wuta tana tuka tuwo nayi sallama na shiga cikin gidan. Ta tashi tsaye tare da dago kanta sakamakon jin muryata a kanta. Kafin ta tantance ko ni ce ko ba ni bace ba, na saki jakar hannuna kasa na falla da gudu na fada jikinta. Allah ya taimaka ta dafe bango da sai na kaimu kasa gabadayanmu. 

Ta fara kokarin yakice ni tana mitar, "ban san ko sai yaushe bane zaki daina wannan shirmen naki ba Na'ilah. Ina ga dai sai ranar da Allah ya baki sa'a kika buga mu da kasa mu duka kika karya min kugu sannan zaki daina!".


Nayi dariya tare da daga kaina na kalleta, "Fatsu na, kin sake yin kyau wallahi. Me Malam yake baki kina ci ne?".

Ta girgiza kai, amma murmushine akan fuskarta, "tuwon dawa ne da miyar. Idan so kike yanzu in bada nikanta".

Nayi dariya, "Inna kin san wannan ba cima ta bace. Abu zaki bane mai sanyi da mai romo don na kwaso gajiya da yunwa".

Tace "ki fara shiga kiyi wanka, sai ki zo kici abinci".

Nace "haka za ayi". Na fada daki. 

Ita ta biyo ni da jakar hannuna dana yasar da akwatina tana mita. Dariya kawai na dinga mata. 

Idan ina gabansu ji na nake yi kamar wata karamar yarinya yar shekara goma. 


Da nayi wankan sai na dauro alwala kawai. Na shiga dakin Fatsu da aka mamaye da carpet mai laushi. Dakin irin tsarin nan ne na mutanen da, gadon karfe babba da kuma karami na katako, sai wardrobe babba, da kuma tarkace da ba'a raba tsofi dasu. Na zauna na shafa mai tare da lalubo kaya masu karancin nauyi na saka. Ina sakawa sai gata ta shigo dakin da plate da kula. 

Na mike kafa akan carpet din tare da amsar plate din, maltina ce mai sanyi har raba yake da ruwan sanyi, kular kuma soyayyar indomie ce a ciki. 

Tace "Yayanki yace kada ayi abinci dake, za'a dafo daga gidanshi a kawo miki".


Nayi murmushi cike da jindadi, "sai ni yar gatar Yaya da Anty Sailu".

Tayi dariya, "kwarai kuwa, dazu zuwanta biyu nan wai taga ko kin zo".

Nima nayi dariyar. Sailuba itace wadda Yaya Mudatthir ya aura. Wannan shekarar su ta biyo ne kenan. Auren dangi ne suka yi, diyar Iya Lami kanwar Mama ce. Da yake duk tare muka taso da ita da sauran diyan dangi sa'anninmu, kusan duk abokan juna ne mu. 

Na sa fork na fara cin indomie, taji maggi da dan taruhu, dama in dai Inna Fatsu ce bana jinta wajen girki. Ta iya hada abinci kala-kala, tun daga na da har na zamani. 

Sai dana kusa yin rabi sannan na daga kai na kalleta, "wai ni ina Malam yayi ne? Nayi zaton ma yana dakin soro ne".

Tace "ai Malam wajen jana'izah yaje, nasan kuma daga can zai wuce masallaci. Shi da gida sai bayan isha'i".

Nace "Allah sarki, waye ya rasu?".

Tace "wani abokinshi Malam Mati idan baki manta shi ba".

Nace "ina zan manta Malam Mati? Shi da nake kaiwa rubutuna idan nayi a allo ya wanke min kafin in iya?".

Inna tayi dariya, "Aikuwa shi ne. Rashin lafiya ce yayi wallahi, ya kusa share watanni biyu a aaibiti".

Nace "Allah ya jikanshi, Allah kuma yasa mutuwar hutu ce a gare shi. In shaa Allah idan na fita gobe kuwa zan je inyi gaisuwa".

Tace "yakamata dai".

Ina gama cin abincin aka fara kiran sallah. Na daukesu na fidda waje na koma daki nayi sallah. 


Ina gamawa naji wayata tana kara, na tashi a nutse na dauketa daga inda na ajiyeta, lokacin kiran har ya katse. Na duba naga Maryam ce. Murmushi nayi kafin na sake kiranta. Yana fara ringing ta dauka, "Yaya Na'ilah tun dazu nake kiranki baki dauka ba, hankalina har ya fara tashi wallahi!".

Nayi dariya, "ban jima da isowar bane, ina zuwa kuma wanka nayi. Ina ga lokacin kika kira. Na sauka lafiya, ina dakin Fatsu na ma idan abinda kika kira ki tambaya kenan".

Tace "shine dama. Ya hanya? Kin same su lafiya dai?".

Nace "lafiya lau kowa. Ya gidan?".

Mun danyi hira da ita ta fada min yadda su Muneerah da Auwal suka dinga cigiyata a gidan, ina ta dariya. Daga karshe dai muka yi sallama da ita akan cewa zan kira washegari ta hada ni da yaran. Bayan mun kashe wayar Baba na turawa text na sanar dashi na sauka lafiya duk da cewa nasan Yaya zai fada mishi. 

Kan abin sallah na koma na zauna gefen Fatsu da take lazumi nima na fara nawa har aka kira sallah. 


Sai bayan sallar isha'i sannan Malam ya shigo gidan. Na dauki kwanukan da aka zuba mishi abinci na tafi dakinshi. A bakin kofar dakin nayi sallama, daga can ciki na jiyo ya amsa cikin muryarshi mai cike da kamala da haiba. 

Na yaye labulen dakin na shiga, yana ganina ya hau sakin murmushi "Masha Allah, amaryar tawa ta karaso kenan?".

Nayi yar dariya tare da zama a gefen shi, "ni ai nayi fushi, tunda kaki zuwa tarya na!".


Yayi yar dariya, "to, ki ce wannan karon da yan rigimun kika zo kenan?".

Inna data shigo dakin hannunta dauke da kofin ruwa tace "kamar kuwa ka sani!".


Na zauna a gefenshi tare da ajiye kwanukan a gabanshi. A nutse na gaida shi ya amsa tare da tambayata mutanen gida, na amsa tare da mishi ta'aziya. 

Inna ta gama zuba mishi tuwon. Ya wanke hannunshi tare da yin bismillah ya fara cin tuwon. Ya kalleni, "yau ba za'a taya ni cin abincin bane?".

Inna tace "yau dai kai kadai zaka ci abincinka. Girkin matar Yayanta take jira".


Tana rufe baki sai ga sallamar Yayan a tsakar gida. Na tashi da sauri na fita tsakar gidan. Wani dan ihu nayi na dafe Sailuba dake gefen Yayan. Ya girgiza kai kawai ya shige dakin Malam ko tunanin yi mana magana bai yi ba, don yasan in muka hadu sai a hankali. 

Sai da muka gama murnar ganin juna sannan muka shiga ta gaida su Malam. 

Na dauki kwandon da suka shigo dashi na ja ta muka koma dakin Inna. Da yake da wuta kar a garin, na kara mana gudun fanka. 

Farfesun busasshen kifi ne ta kawo min da chips din doya. Na zuba iya wanda zai ishe mu na ciccibi sauran na kaiwa su Inna. 

Dakin na koma muka dasa dandalin hira ni da ita, bamu san dare yayi ba sai da Yaya ya leko yace mata ta tashi su tafi. Na raka su har kofar gidan muka yi sallama dasu. 


Dakin Fatsu na koma nayi shirin kwanciya barci na. Ina zaune Fatsu itama tayi nata shirin ta tafi dakin Malam. Wutar dakin na kashe tare da sakaya dakin, na kara ware iskan fanka na fada kan karamin gado na kwanta. 

Sai dana kira Janan muka gaisa na fada mata ina Gashua sannan na dannawa Umar kira. 

Yana dauka ya tare ni da, "haba Sweety na, ina kika shiga ne tun safe nake nemanki?".


Nayi murmushi, "hello to you too, and yes, lafiya lau na wuni!".

Ina jin sautim dariyar daya saki, "Lols.. Da gaske nake fa. Har na fara shirya kayan tahowa Kt gobe idan baki amsa kira na dama".

Nayi murmushi, "lallai ma, yanzu kawai sai ka taho Katsina?".

Yace "ai ba kawai bane, ina lafiya bugun zuciyata bata daga kira na?".

Nace "ba kin daga wayarka nayi ba, ina tunanin matsalar netwok ne. Kasan ina Gashua fa!".

Yace "hope komi lafiya?".


Dadina da Umar kenan, kulawarshi a gareni na matukar tafiya dani. Nace "lafiya lau fa, kawai nazo ganinsu ne!".

Yace "good. Shine kuma sai yanzu kike fada min ko?".

Nayi dariya sosai, rigimar Umar watarana tafi karfin mai rai. 

Mun dauki kusan mintuna goma muna sa'insa akan ban fada mishi ba, daga baya dai ya saki zancen muka shiga wani kan yanayin aikinshi. 

Sai dana fara jero hamma sannan muka yi sallama dashi, "goodnight dear, dream of me fa! Zan kira ki gobe ki bani labarin kalar mafarkin da kika yi". Abinda yace kenan kafin ya kashe wayar. 

Nayi murmushi kawai tare da ajiye wayar a gefen gado. Nayi addu'ar kwanciya barci tare da jan abin rufa zuwa jikina tare da rufe idanuna. 




*




Funkasu muka ci a matsayin abincin kari. Ina gamawa nayi wanka na shirya na tafi gidan Yaya. Naci sa'a yana gida bai kai ga fita ba. Yana aiki ne da wani research institute. Na gaida shi ya amsa. Sailuba ta fito daga daki tana murmushi, "yanzu nake cewa ya kira ki kizo ki ci abinci".

Na kalli inda take nuna min, kuloli ne a shirye akan ledar cin abinci. Na shafa cikina, "abincin nan sai dai ko anjima don yanzu dai kam cikina a cike yake".

Tace "to ai shikenan".


Yaya ya mike zai wuce, na mishi Allah kiyaye, ita kuma ta bishi zata mishi rakiya. Yace "kada dai a yi nisa Na'ilah, na san ki da yawo. Duk ranar da kika zo haka zaki ja matata ku shiga gari sai na nemo ku".

Nace "Yaya sau daya ne fa ka taba nemo mu".

Yace "oho dai. Idan dai kuka dade, babu fita gobe!". 

Nayi dariya "matar ka zaka ja wa kunne kuma wannan, ita ce mai son yawo bani ba".

Yace "ni dai na fada muku!". Daga haka ya fita. 


Ina zaune a inda suka barni ina wasa da kan wayata ta dawo, tace "bari in shirya sai mu fita ko? Abincin sai mu tafi dashi gidan Yaseerah mu ci".

Na gyada kai, "haka za ayi".

Ta shige can kuryar daki ni kuma na cigaba da danne-danne na har ta fito sanye da riga da zani na atamfa, hannunta rike da jaka da hijabi. Na bita da kallo kafin inyi sequeling na fara tsalle akan kujera, "ke matar Yaya sai kice kin kusa sauke mana baby!".


Tayi sauri ta ja rigarta kasa tana hararata kasa-kasa, "ni kada ki min ihu anan. Don mayuntaka har kin hango abinda ko wata uku bai rufa ba!".

Na daga mata gira ina dariya, "haba mata, kada kiyi underestimating dina ta wannan fannin!".

Ta shafa cikin tana dan murmushi, "ku dai taya mu da addu'a dai kawai, Allah yasa mai tsayawa ne".

Murmushin tsokanar kan fuskata ya dusashe, sau biyu tana yin barin ciki, likitoci sun ce mahaifarta bata da karfin da zata dauki ciki ne, saboda haka aka mata daurin mahaifa. 

Na dafa kafadarta ina murmushi  reassuringly, nace "da yardar Allah babu abinda zai faru, zaki haifo mana babynmu lafiya lau, in samu takwara!".

Hakan yasa ta saki dariya a tausashe, ni kuma nayi murmushi, tace "muje, Yaseerah har ta fara danno min flashing".

Nayi dariya tare da ciccibar kwandon da ta saka abincin data ajiye mana, muka fita. 


Yaseerah diyar Baba Adama kanwar Mama ce. Su hudu ne a wajen su Bako duka mata, Inna Talatu ita ce ta farko, tana aure a Damaturu, sai Mama na, Iya Lami da Adama, su duka suna nan Gashua ne. Yaseerah, ni, Sailuba, Ma'u kanwar Sailuba da Lawisa kanwar Yaseerah duk tare muka taso dasu, kusan duk sa'annin juna ne mu. Yaseerah a shekara daya aka aurar dasu ita da Sailuba. Yanzu har tana da yar diyarta Hafsat. 


Gidan Yaseerah muka fara zuwa, a shirye muka sameta tsaf tana jiranmu. Bayan mun gaisa da yin yar hirar yaushe gamo, muka ci abinci, daga nan muka fita. 

Gidan  Iya Lami dake nan unguwar su Yaseerah muka fara shiga muka gaidata. Daga can muka biya gidan Marigayi Malam Mati muka yi gaisuwa. 

Yinin ranar dai a haka muka gama shi. Shiga nan fita can, sai wajen karfe biyar muka koma gidan Sailuba. 


Yaseerah da Ma'u suka koma gidanta, ni na tsaya wajen Sailuba. Sai da na taya ta tayi girkin abincin dare, sannan na mata sallama na tafi, lokacin har an gama sallar magriba. 

Nayi sallama na shiga dakin Fatsu. Tana zaune akan abin sallah tana lazumi a tsakiyar daki, ta bini da kallo lokacin da nake ajiye hijabin dana cire akan gado. 


Tace "wato Na'ilah kina nan da yawon nan naki ko? Yanzu saboda Allah ace kin fita tunda sanyin safiya amma sai yanzu zamu ganki? Saboda kin raina mu ne ko me? Idan a gaban mahaifinki kike kina wannan yawace-yawacen ne na babu gaira babu dalili?".

Nace "haba Fatsu, ya zaki ce wai ina yawo? Ziyarar yan'uwa ce fa nayi, zumunci. Kuma a gida yawon me zanyi? Bani da kowa acan sai nan din dai, kin san haka".

Tace "ai sai kiyi tayi, tunda bakinki bai iya bada hakuri ba balle ya iya amsa laifin da yayi!".


Na koma gefenta na zauna ina yar dariya, "to naji Fatsu na, Allah ya baki hakuri, na tuba na bi Allah na bi ki. In Allah ya yarda gobe babu inda zan je, a kugunki zan wuni. Kinji dadi?".

Ta dan harareni cikin wasa, gefe daya kuma tana kokarin danne murmushin da take yi, tace "Allah yasa, kullum ke dama maganar ki daya, amma baki cikawa!".

Nace "in Allah ya yarda wannan karon da gaske nake, I'll be all yours gobe!".



Kamar yadda nayi alkawari, washegari a gidan na yini, ko nan da kofar gida ban leka ba. Da yake ba wasu ayyuka muka yi a gidan ba, na shiga dakin Malam na fiddo kayan ciki gabadaya na sharo dakin tas, na maida na sake mishi wani sabon shirin. 

Da yamma bayan nayi wanka, na dauko littafaina da textbooks dana taho dasu ina bita. Nasan cewa nan da sati daya ne zasu fara zancen mu koma makaranta. Bana bari koda wasa in shantake a gida idan naje hutu, ina da lokuta na musamman da nake warewa, lokaci zuwa lokaci na kan dauko littafaina inyi bita musamman akan courses din da zamu yi a semester ta gaba ko kuma wadda muke cikin yi. 


Da dare bayan isha'i muna zaune akan tabarma a tsakar gida. Bura-busko muka ci, (tuwon biski/tuwon tsakin masara ko na gero), wannan karon na masara ne muka yi, da miyar kuka da man shanu. Kamshin tuwon ma kadai ya isa yasa yawun mutum tsinkewa balle dadin da yayi. Malam yayi baki, tare suka ci abincin shi da bakin a dakin soro inda ya saba ajiye baki na nesa. 

Bayan mun gama cin abincin, na koma na zauna ina taya Fatsu hade kayan sakar da tayi da zare, kasancewar babu wutar lantarki, hasken farin wata ne tar ya mamaye kafatanin tsakiyar gidan, sai kuma hasken wutar candle dana kunna daya kara taimakawa wajen kara haskake wajen. 

Ita tana gaban murhu tana zubawa almajirai abinci. Malam ya dauki nauyin ciyar da kananan almajirai wadanda karfinsu bai gama kaiwa ba. Yanzu ya daina karbar almajirai na nesa ma, sai wadanda suke cikin Yobe kawai, kuma garinsu bai yi nisa ba.

Manyan tsofin almajiranshi kuwa tuni ya yaye su, wasu sun koma garuruwansu. Yayin da wasu suna nan cikin Gashua, wasu sunyi aure, wasu suna sana'o'insu, su da garuruwansu sai dai ziyara. 

Da ta gama zuba musu, ta dawo gefena ta zauna muka cigaba da yin aikin tare.


Wani almajiri yayi sallama ya shigo, duk muka amsa mishi. Ya durkusa a gefen Fatsu, yace "wai ance ana sallama da Na'ilah a waje!".

Nayi kasake da zare a hannu ina kallon yaron baki a dage, wa na sani da zai yi sallama dani a garin Gashua ne? Inna ce ta tambayeshi inji wa? Yace "yace wai ace Magaji ne".

Sai lokacin naji na sauke ajiyar zuciyar da ban san dalilinta ba, nace "kace mishi ina zuwa".


Bayan fitarshi Fatsu ta kalleni cikin yin kasa da idanu, murya cike da gargadi tace "kinsan dai Yayanki ba zai ji dadin wannan magana ba ko?".

Na kada idanu, "gaisawa ce fa kawai ba wani abu ba. Beside, babu wata magana a tsakanina da Magaji sai zumunci kawai da girmama juna".

Tace "ai shikenan!". Hijabina na saka na fita. 


Magaji kusan zan iya cewa abokin Yaya ne, duk da dai ba aboki bane na kut-da-kut, they were more like classmates. Shekaru kusan uku da suka wuce ya nuna yana da sha'awar aurena, tun ma kafin mu hadu da Umar. Na sanar dashi ban shirya yin wani relationship ba a lokacin, yace ya yarda zai jira ni. Ni dai na fito fili na sanar dashi cewa bani da ra'ayin yin wata alaka data wuce ta mutunci dashi, yace babu laifi, ya amince. Amma lokaci zuwa lokaci ya kan yi min tuni, ko kuma nuna alamun har yanzu fa yana so na, ni kam sai dai in banzatar da maganar kawai. 


Yanzu ma gaisawa kawai muka yi, ya sanar dani dama wucewa yazo yi, da yake jiya ya ga wucewar mu ta kofar shagon dinkinshi, shine yace bari yazo ya min barka da zuwa. 

Muna tsaye anan Yaya yazo wucewa, na dan duka ina gaida shi, hararar daya daka min kadai tasa naji diyan cikina suna kadawa. Ya ba Magaji hannu suka gaisa yana ta wani basarwa, ya shige cikin gida. 

Yana bada baya Magaji ya dube ni yana dan yin murmushi, "to ranki ya dade, bari in koma shago, sai wani lokaci kuma".

Na gyada kai, "to Magaji, na gode". Na shige ciki, shi kuma ya wuce. 


Ina yin sallama a gidan, Yaya ya taro ni da fada, "wato Na'ilah kunnen kashi ne dake ko? Sau nawa ina fada miki na hana ki tsayawa da Magajin wannan?".

Nace "ni fa Yaya babu abinda yake tsakaninmu dashi sai mutunci kawai, zuwa ne yayi mu gaisa fa ba wani abu ba!".

Murya cikin fada yace "koma menene, na fada miki na hana. Kuma wannan shine gargadi na karshe da zan miki akan wannan maganar, idan na kara ganinki dashi a tsaye, kinsan hakan ba zai miki dadi ba. Kina ji na?!". Ya shura kafa ya bar gidan tun kafin in ce mishi wani abu.

Na turo baki ina satar kallon Fatsu da take sakar ta kamar bata san abinda yake faruwa ba. Na kara turo baki na wuce daki ina dira kafa.


Washegari a Damaturu na wuni gidan Inna Talatu. Da yamma Hafiz, babban danta namiji ya biyo ni muka dawo gida. Sana'o'in shi yake yi a garin Gashua da sauran kananun garuruwa da kauyuka dake makwaftaka da Gashua. 



*



Kwanaki bakwai nayi a Gashua ina shan hutu na. Da za'a tambayeni menene ainihin ma'anar hutu? To ni zan ce hutu a gaban Fatsu da Yaya ne hutu. 

Nan kadai ne zan yi rayuwata yadda naga dama ba tare da an juya ni ba. Babu abinda yake burgeni da zama a Gashua sai gani na tare, kuma lullube da dangi, duk inda na juya sune. Babu ranar banza da wani nawa ba zai yi sallama ya shigo gidan Bako ba, ko kuma ni ban je naga wani nawa ba. Wannan kadai, ni abin dadi ne a gareni. Ina son dangina, musamman fannin Mama. 


Dangin Babana da yake suna da rufin asirinsu daidai misali, kuma da yake babu wasu na kusa, daga diyan kawunnai sai kannen kakanni. Idan kaje gidajensu sai su yi ta wani daga hanci suna shan mur, ko suna zaton rokonsu kaje yi ne? Shi yasa wasu lokutan idan naje Gashua bai fi in leka su sau daya ba, sai dai ko idan biki ake yi ko wata hidimar. 


Yau kauyen Alkali muka je ni da Sailuba. akwai wata kanwar Babana, from another father da take aure acan, sunanta Fatima amma Juma ake ce mata. Duk cikin dangin Baba ita kadai ce mai kirki da kuma zumunci. Yawanci idan harka a gidanmu ta tashi, musamman idan su Anty suka haihu, ita kam tana zuwa. Haka idan nazo Gashua, watarana har takanas take yi tazo nan mu gaisa. Shi yasa nima bana zuwa ba tare dana leka ta ba.


Kayan dana kai wa diyanta, yawancinsu wadanda suka min kadan ne na kai musu, sai mazan dana shiga kasuwa na samo musu, tayi ta godiya yadda kasan harshenta zai fadi kasa. 

Yini guda muka musu, musamman da yake yau kasuwar garin take ci, muka shiga mu da Hanne babbar diyarta da take kai tallar nono. Rana ta dan fara alamun faduwa lokacin da muka yi sallama dasu zamu tafi, suka ciko mu da tsarabar kayan kauye cike taf da buhu. 


Kasancewar Fatsu ta min fadan jimawa a unguwa yasa ko gidan Sailu ban shiga ba na wuce gida. 

Bako yana kofar gida yana alwalar sallar magriba, na durkusa na gaida shi, kai kawai ya gyada min, na mike na shige gida. A gidan ma itama Fatsu alwalar na tarar tana yi, na shiga daki na ajiye kayan hannuna na fito nima na daura alwalar. 


Tun wajen karfe tara na kwanta saboda gajiya da nayi saboda mun sha yawo a garin Alkali yau. Har barci ya fara dauka ta na jiyo muryar Yaya a kofar dakin Fatsu suna magana shi da ita, Fatsu take cewa "aikuwa ta dade da kwanciya, idan ba sa'a ba ta riga tayi barci zuwa yanzu".

Yace "to gashi ki ajiye mata, nima a hanya na sayo shi, kin santa da son kifi soyayye".

Ai jin an ambaci kifi sai nayi wukit, na hantsalo daga kan gado. Kawai sai gani na suka yi a gabansu. Fatsu ta dafe baki, "kai wannan 'ya, Allah ya kyauta miki ke kam. Nayi zaton kinyi barci?".


Na ja ledar dana gani a gabanta ina murmushi, nace "na dai fara, amma bai yi nauyi ba. Yaya ya hanya?".

Yayi dariya, "lafiya lau Na'ilah.. Bari in karasa gida ni". Muka mishi sai da safe ni da Fatsu, ya tafi ni kuma na tashi na shiga daki na dauko yaji na koma na zauna. Kifin na bare, ina cire mana kayar ina dangwala shi da yaji ina ci, Fatsu kam haka nan taci shi. Ganin Malam bai shigo ba yasa na kai mishi nashi daki. 

Ruwa na kora mai sanyi na koma daki na kwanta. 


Wayata ta fara haske wanda yake nuna min ajiyayyen sako da ban daga ba, nayi unlocking wayar ina dubawa. Umar ne da Janan. Shi yana tambayar yadda na wuni, ita kuma tana tambayar ko naji komawa makaranta nan da kwanaki hudu? Na maida mata amsar na sani, shi ma Umar din na maida mishi reply din. 

Na koma kan gadon na kwanta, zuciyata cike da tunanin Umar din. Kwana biyu bamu yi waya dashi ba, ko musayar sako, to da yake ma sau tari haka muke kasancewa yasa ban cika damuwa ba. 

A hankali tunanin nawa ya gangaro kaina, jibi nake so in koma gida saboda in fara shirye-shiryen komawa makaranta. Kasancewar shekarar karshe zamu shiga, nasan projects da sauransu ba zasu bari in kara samun hutu mai tsayi kamar wannan ba. 


Tuni kewar su Fatsu ta fara lullubeni. Nayi fatan ace na hado duk wasu kaya da zan bukata daga gida, da bari zanyi kawai in wuce daga nan tunda dama na saba yin hakan. Amma yanzu babu damar yin hakan, su ma nasan kila tsakanina dasu sai dai ko in Yaya yaje Kano ko Kaduna, ya biya ta wajena. Amma na kudirta idan muka samu hutun sallah wannan karon anan zan yi shi. Da wadannan tunanikan barci ya daukeni.


Washegari na shiga yin sallama da mutanen garin Gashua, wasu dangin ma sai a ranar na leka su kasancewar Mama na Allah ya albarkace su da dangi Masha Allah. 

Ranar da zan tafi kam ban ma fara shirin tafiya ba sai dana karya. Sai wajen karfe tara sannan na mike, tuni kayana sun nabba'a a bayan mashin din Yaya. Bayan akwatina, akwai jakar Ghana madaidaiciya shake da tarkacen tsaraba da aka hada min wadanda zan koma makaranta dasu, dangin busasshen kifi, cukwi. Akwai wani abu da Iya Lami take yi wai shi 'mitimis', da nikakkiyar danyar gyada ake yi da sugar, sai a yanka in cubes kamar dai tuwon madara. Shima sai data cika min katuwar leda dashi. Haka dai abin yake kasancewa a duk lokacin da naje Gashua. 

Kaunar da mutanen nan suke nuna min is so overwhelming da take saka ni zubar da hawaye a lokuta da dama. Ko yanzu da Yaya ya raka ni tasha, ya biya min kudin mota tare da damka min wasu a hannu in case zan bukace su, ga kuma hannuna rike da plastic rubber da Sailu ta soya chips din dankali da sauce din kwai ta bashi ya kawo min, hawayen nake sharewa, ya dafa kaina yana murmushi fondly, cike kuma da tsokana, yace "daina hawayen mana. Bansan wanda ya shagwaba ki da yawa ba Illo, har sai yaushe ne zaki girma ke kam?". 


Nayi murmushi ina share hawayen, yana tsaye na shige mota, da yake karama ce ba bus ba, tuni ta cika. Yaya yana tsaye yana daga min hannu muka fita daga cikin tasha din. A mota na rubuta text na turawa Janan da Umar don su san da tahowata, na maida kaina jikin kujera na kwantar. 



*



Wasu masallatai har sun gama sallame sallar isha'i lokacin dana yi sallama tsakar gidanmu. Motar Baba tana fake a nan bayan dakin su Aliyu inda ya saba ajiye ta, hakan ya sanar dani yana gida. Babu kowa a tsakar gidan, don haka na ja akwatina na shiga daki. 


Maryam dake kan abin sallah, tayi tsalle daga jin muryata ta dafe jikina tana ihun oyoyo, ina tunanin jin ihunta ne ya janyo hankalin su Auwal, sai gasu sun fado dakin da gudu su ma suna nasu ihun murnar. Nayi dariya tare da zama daram a kasa sakamakon jin suna neman kayar dani a kasa. Sai da suka gama ihun murnar, na bude jakata na ciro cakuletin eclairs na damkawa kowannensu a hannu, sannan duk suka watse. 


Na tashi na shiga bandaki na dauro alwala. Kasancewar an fara yin ruwa, iska mai sanyi yake kadawa sakamakon ruwa da aka yi da rana. 

Sai da nayi sallah sannan na dauki wayata na sanar da su Yaya da Fatsu karasowa ta gida lafiya. 

Na fita na leka dakin su Anty duk na musu sannu da gida. Nasan cewa in ba lekawa nayi ba, babu wadda zata damu da ko furta min kalmar sannu da hanya ne. Zamu iya haduwa dasu a tsakar gida ma gobe su nuna kamar dama can ina gidan. 


Ina gamawa dasu ban bata lokaci ba na nemi makwancin barci, ina yada kai akan katifa kuwa, barci yayi awon gaba dani. 















   *☆⋆06⋆☆*






"Ni dai yanzu haka maganar da ake yi babu kudi a hannuna Na'ilah, duka-duka shekaranjiya na biyawa yara kudin school fees su ma, ga kuma sauran hidimar gida dake kaina, ta ina kike zaton zan lalubo naira kusan dubu arba'in cikin kwana biyu?".


Na kifta idanuna kamar wanda abu ya fada cikin idanun, tunda ya fara maganar kallonshi kawai nake yi babu ko kiftawa saboda jin maganganun da suka fita daga bakinshi, sai dana hadiyi yawu na jika makoshina da naji ya bushe, nace "amma Baba tun da nazo dama na fada maka, kuma yanzu idan ban biya kudin akan lokaci ba, ba zan taba samun accomodation ba!".


Ya kalleni a kaikaice, "to yanzu ya kike so inyi ne? Tunda nace miki bani da kudi a hannuna, ta ina kike tunanin zan je in lalubo su?".

Ramata dake gefenshi ta kalleshi tana wata kwarkwasa, "kasan akwai kudin anko na dake kanka ko? Kuma bikin satin sama ne".

Ban san lokacin dana jefa mata harara ba, aka yi sa'a ta kalloni muka hada ido, da sauri ta janye kanta daga kallona, nayi kwafa, can kasan zuciyata ina raya 'kin kyautawa kanki!'.


Baba yace "to bari mu jira zuwa ranar laraba mu ga yadda hali zai yi". Daga wannan magana sai ya dauke kanshi gabadaya daga inda nake, clearly dismissing me, na mike gwiwa a salube na fita daga dakin. 



Gefen katifa na laluba na zauna, Allah ya so ni Maryam bata gidan, wai ta tafi suna gidan kawarta, shigar banzar dai dana mata magana akai, ita tayi. Binta da kallo kawai nayi lokacin da naga ta fito sanye da riga da siket na atamfa, an musu wani irin dinki na cin mutunci. Siket din ya matseta tsam, kamar in tayi nishi mai karfi zai yage, rigar ma haka, ga wani dan iskan 'show me your back' shima da aka yi, tayi daurin dankwali mai nadin doughnut a goshi, ga gyalen nan kamar matacin koko saboda shara-shara da yayi ta dora a wuya. Ban ma yi tunanin yi mata magana ba, har yanzu fushin abinda Aliyu yayi min kamar sabo yake a cikin raina, ban shirya shiga wani bacin rai makamancin haka ba so soon kuma. Koma dai menene tayi, Allah ya gani, nayi iyaka bakin kokari na. Magana akan shigar banza irin haka ba tun yau nake yiwa Maryam ita ba, tun kafin ta fara kirgan dangi muke haka. Sai kuma ta nuna ta fahimta, taji maganata, daga baya sai uwar ta kara zuga ta dai, sai ta koma cikin ruwa tsamo-tsamo. 

Allah yasa for now dai, ita kadai ce budurwa mai tasawa a gidan, sauran duk suna kan hanya, ina kuma fata kafin su gama yin hankalin kansu, su dauki irin dabi'arta, zata daina. 


Rashin Maryam a dakin shi ya bani damar jingina da bango, na tsunduma cikin tunani mai zurfi. Yakamata ace na saba da abinda Baba yake yi min, sai dai, kamar yadda ba'a taba sabo da wahala, haka ma ba'a sabo da bacin rai. Musamman idan wanda yake haddasa maka hakan ya kasance majibanci, kuma majingini a gareka, wanda kake ganin zaka iya rab'a a duk lokacin da komi ya yaye maka baya, kuma ya tallafa maka. Sai dai no, ko kadan ba hakan take ba. 

Lokacin da zamu tafi registration dinmu na farko, haka Baba yayi min wannan delaying din. Sanadiyar haka na rasa accomodation a cikin hostel, wata kawarmu da muka yi sbrs da ita, ita tayi squatting dina. Believe me when I say, it wasn't fun at all. Ban taba raina kaina ba sai a wannan lokacin, ban taba jin dadin rayuwar gidanmu ba, in fact, ni zan iya dukan kirji in ce rayuwar makaranta ta fiye min rayuwar gidanmu, amma a wancan lokacin sai dana fara rethinking wannan tunani. Sai dana gwammace rayuwar gidanmu sau dari akan wannan rayuwar. At least a can, ina da wajen da zan kira dakina, sannan duk lokacin da dare yayi, a gida nasan cewa ina da wajen da zan kwantar da hakarkarina, amma ban da nan.

Haka taci gaba da faruwa, for once, ban taba biyan makaranta akan kari ba, kullum, kuma kodayaushe, sai na kara kwanaki ko satika, duk da cewa kowani lokaci nakan fadawa Baba da wuri yadda zai tanadi kudin, but no, kodayaushe akwai uzirin da zai ratso ya shiga ta cikin kudinnan. Ban sani ba, daga gareshi ne ko daga matanshi, ko kuwa in ce matar shi? Allah ne masani. 


Yaya Mudatthir, Allah ya albarkaci rayuwar shi. Da ba don shi ba kam, ban san yadda karatuna zai kasance ba. Idan Allah ya taimaka yana da kudi, shi yake daukar jigilar registration dina, daga baya in Baba ya turo, in tura mishi, duk da a yawancin lokuta ya kan dawo min dasu ko kuma yace in barsu, sai dai in maida mishi rabi ko ya dawo min da rabi. 

Ko last year, Allah ne yasa Yaya Jameel, yayan Janan, da yake lecturer ne a cikin makarantar, ya bata daki, Yaya ya hanata zama, ni kuma ta bar min shi.


Da tunanika iri-iri na kwanta. Sau tari sai inji gabadaya karatun ya fita a cikin raina, inji kawai gwanda in hakura dashi, in huta da bakinciki da takaicin da nake kwasa daga wajen Baba. Sai dai wasu lokutan, sai in ga daurewar tafi. Musamman idan naga cewa shine kadai gatana a yanzu. Karatun shi zai tallafa min, in tsaya akan kafafuna ba tare dana jingina da wani ba. Idan nayi hakuri, na dan lokaci ne. Komi wucewa zai yi, ya zama tarihi, kamar bai taba faruwa ba. At least, abinda nake fata kenan. 



                                       *



Washegari da dare, mun zagaya nan bayan gidanmu ni da Kulsum dubo wata Hassana wadda muka yi aji daya da ita a makarantar Islamiya. A hanyarmu ta dawowa, muna tattaunawa game da matsalolin da ita Kulsum din take fuskanta daga tsohon mijinta.

Ya fara mata zarya akan cewa yana so ya amshi Muneerah daga wajenta, ita kuma tace gaskiya bata son bashi ita. 


Ni kaina shawarar dana bata kenan. Nace idan da yadda zasu yi akan haka, gaskiya suyi, ya bar mata diyarta ta tarbiyantar da ita a gabanta. Tunda ma ba maganar aurenta bace ta taso, ko iddah bata gama ba, balle yace ta wannan dalili yake son karbar ta. 

Wahalhalun dana sha a hannun kishiyar uwa, shi nake guje mata. Duk da cewa ni rashin mahaifiya ne ya jawo min, ita tata mahaifiyar tana raye. Kuma tana ji tana gani, haka za'a fi karfinta akan diyarta. Bana fata ko makiyina ya dandani kwatankwacin abinda na dandana. Abinda na dinga tunani a cikin raina kenan, ban furta mata hakan ba amma. 

Koda kasancewarta kawata, ko ma ince aminiya, tarihin gidanmu, da irin zaman da nayi da mutanen gidan, dama wanda nake yi, ba duka ta sani ba. Ta dai san wanda kunnenta ya jiye mata, kuma idanunta suka gane mata, shikenan. A tunanina, tado abinda ya wuce, yake kuma sosa ran mutum, duk ba solution bane. Hakan babu abinda zai haifar sai ma wani karin bacin rai, hakan zai sa ka kullaci mutane a cikin ranka, kila dan mutuncinta da kake gani nasu ya zube. Babu abinda zai sa, kuma babu abinda zai hana. 


Daidai bayan gidanmu, na hangi wata yarinya Lubah, yar dakin Ramata ce. Anan cikin unguwar take, duk wata gulma da tsegumi daya taba gidanmu, daga gidansu yarinyar yake fara fita. 

A durkushe na ganta, kamar tana tona kasa ko kuma wasa take yi? Sai waiwaye take yi da kalle-kalle, kamar dai wadda take tsoron wani ya ganta. Na dan yamutsa fuska in suspicion, kamar zan karasa in ga abinda take yi, sai kuma naga hakan ba hurumina bane, tunda ba shiga harkarta ko ta mutanen gidansu nake yi ba. Muka wuce ta. 


A tsakar gidan su Kulsum muka zube ni da ita akan tabarma, muka cigaba da tattaunawa. Mun yanke shawarar zata je ta samu Kawunta tayi mishi bayani, zai je ya samu iyayen Mukhtar din sai suyi mishi magana. A cewar Inna, hakan zai fi kawai, in yaso idan ta tashi yin aure, ko kuma Muneerah din ta fara mallakar hankalin kanta, sai ta koma din. Tunda dai duk inda za aje a dawo, gidan mahaifin nata dai nan ne mutuncinta. Da wannan na musu sai da safe na wuce gida. 






Washegari Laraba, nayi sa'ar samun Baba kafin ya tafi wajen aiki. Na gaida shi, ya amsa yana kora shayin da Alawiyya ta hada mishi, yayin da Ramata take gefenshi zaune a hakimce. Yadda nayi zaune a gabanshi, nasan cewa yasan dalilin yin hakan, amma ya basar dani. 

Ban yi fushi ba, na kaskantar da murya, nace "Baba zancen registration dina?".


Daga farko shiru yayi kamar ba zai yi magana ba, can kuma yayi gyaran murya, yace "kudin nan naki fa sai dai kiyi hakuri sai zuwa satin da zai kama. Ranar litinin zan biyawa kaninki kudin waec da neco, abubuwan zasu yi min yawa!".


Wani abu daya kusa bani dariya shine, jarabawar waec da neco zata iya jira har nan da watanni biyar zuwa shida masu zuwa, tunda dai ba'a fara zancen yin ta ba balle akai ga saka deadline din wadanda basu biya ba zasu rubuta jarabawar ba da sauransu. Naso in tunatar dashi hakan idan ma mantawa yayi, yadda naga ya zubo min ido ne yana jira yaji ta bakina, Ramata ma da Alawiyya sun zubo min nasu suna jira inyi magana, kila dalilin haka Baban ma yayi fushi, satin samar ma yazo yace bashi da kudi, yasa na hadiye duk takaicina da kududun daya makale min a makoshi, nace "to babu laifi, Allah ya hore!". Na tashi na kara gaba. Banyi kuskuren ganin yadda suka bini da kallo baki a dage ba. 


Magana ta gaskiya ita ce, na gaji da takaicin da suke guma min. Daga Baban har su. A kullum, kuma a kodayaushe, hidimar kansu data 'ya'yansu ita ce ta farko a idanunsu, koda tawa matsalar tafi bukatar agajin gaggawa, haka za ayi shagulatin bangaro da ni da lamarina, har sai an biya musu nasu bukatun. Idan kuma nayi magana, sai cibi ya zama kari. All tables will turn, and bets will be off. Sai laifi ya dawo kaina, ace na cika bakin ciki, su ce bana son cigaban su ko na 'ya'yansu, su ce bani da godiyar Allah, daga karshe kuma su zo suyi sanadin wannan abin ba za'a yi shi ba kenan. Idan ma anyi, to a kurarren lokaci ne. 

Saboda haka naga, meye amfanin yin maganar? Babu abinda hakan zai karas dani sai bacin rai. Meye kuma amfanin sanya maganar a cikin raina, again, sakamakon hakan dai bacin rai ne. Don haka nayi wurgi da maganar cikin kwandon shara, naci gaba da harkokina cikin kwanciyar hankali. 


Sai dai Baban yana fita, sai ga Ramata ta fiddo dankareren Swiss lace daga daki, ta fito tsakar gida tana ba danta Aliyu da bai je makaranta ba, labarin jiya Baba ya bata kudin, dubu ashirin da biyu ta sayo, ya kara mata da dubu uku kudin dinki. Tace yayi maza-maza yazo ya kai mata shi wajen telanta ya watsa mata dinki na rashin mutunci, na shiga taron manya. 

Nasan duk don inji haushi take yin hakan, sakonta kuma ya shigeni yadda yakamata, naji haushin. Sai dai wannan karon ma maimakon magana, sai na kada kaina na shige daki. Ai sai ina wajen sannan zata yi tunanin tsokano ni ko? Sai dai ga yadda na ga fuskar Alawiyya, to ta shaka da yawa. Nasan a cike take dam, kiris take jira ta fashe. Nasan kuma da Baba ya dawo zata tare shi da maganar, idan Allah ya taimaketa, ya dorata a kanshi itama ya siyo mata lace din ko ya bata kudin yace ta dinka. Wanda kuma da kyar ne, hakan sau daya yake faruwa a gidanmu a shekara. 


A tunanina, idan mutum ya sai wa matarshi wani abu, itama dayar tana da hakkin ya sai mata irinshi, ko kuma ya bata adadin kudin daya batar wajen sayen abin? But no, banda gidanmu. Ban taba ganin haka ba, koda wasa. 

Yawanci idan abu makamancin haka ya faru, sai dai hakan ya kare ga fada kawai. Ita Alawiyya bata hakura, kullum aka yi haka sai ta bukaci itama a bata nata kason, lokuta daidaiku ne Baban yake bata, basu fi a daga hannu a kirga su ba. 

Wani lokacin tausayinta dana 'ya'yanta yana cika raina, amma nafi tausayawa Ramata dana 'ya'yanta. 



Wunin ranar haka nayi shi smoothly. Da yamma ina kicin ina tuka tuwom dare, Maryam ta fado kicin din da sauri, wayata dana bata tayi kallo tana ringing a hannunta, ta miko min. Na duba naga mai kiran Janan ce, da sauri na daga ina murmushi. 

"Hi...", na furta a hankali, da niyar gaisuwa. 

Tace "hii yourself, yaushe kike da niyar dawowa makaranta ne? Ni fa har na dawo Zaria".

Na zaro ido cike da mamaki, "wow, lallai kina kaunar Zaria da yawa. Ni yanzu haka ban san ranar dawowata ba".


Tayi dariya, "bana son shakiyanci wallahi, meye abin so a Zariar ne? Kinsan da maganar council exams dinmu ana tunanin kamar upper week fa za'a yi. Kinsan wasu lecturers har sun fara shiga aji kuwa?".

Na dafe kai, "damn! Subhanallah! Daga dawowa?".

Ta sake yin dariya, "exactly abinda na fada Saboda haka ki fara tattara naki-ya-naki, ki ciccibo kanki ki taho wallahi. Gobe in shaa Allah zan shiga in ga yadda ake ciki".


Nayi shiru ina kallon wutar da take ci bal-bal a cikin murhu, da kyar na samu muryata, "ina tunanin kuwa sai dai inyi karatuna a gida. Ni da Zaria maybe sai upper week din".

Tuni naji ta rikice, "ban gane ba, mai ya faru ne? Baki da lafiya ne? Ko wani ne a gida bashi da lafiya?".

Nace "sam ba haka bane, ke da kika san banyi registration ba?".

Tace "sai aka yi yaya?"

Banyi mamaki ba, nasan hakan zata fada, nace "sai bani da wajen zama. A kanki zan zauna in na dawo ba'a riga an bani daki ba?".


Tace "ko baki zauna a kaina ba, kin zauna a dakina. Ki zo sai ki zauna dani kafin ki biya!".

God!, wai komai ma sai nayi guessing dinshi daidai? Shima nasan abinda zata fada kenan, nace "nop... Nagode, amma zan jira a gida har sai na kammala komi sannan".


Shiru ya biyo baya, again, nasan fada ne zai biyo baya, illa kuwa, 

"wai Na'ilah, ni ce baki son zama dani ko kuwa me? Kada ki manta, last time ma abinda kika min kenan, hutun kirsemeti wannan na kwana hudu da aka bamu kin zuwa kika yi muyi a gidan Yaya, kika zauna ke kadai a daki kamar mayya. Yanzu ma kuma kina fada min wai zaki zauna a gida, baki son zama dani ne?" 


Na kai hannu ina sosa bayan wuyana, ni dama nasan za'a rina. Nace "kamar ya bani son zama dake, ya ma zaki ce haka?".

Wannan karon muryarta ta fara dagawa cikin alamun fada, tace "haka ne mana! Kada ki manta, duk lokacin dana miki tayin kizo mu zauna, ko wani abu makamancin haka, sai ki hau kame-kame kina wani kawo excuses. Me kike so in zata, idan ba haka ba?".


Na girgiza kaina kamar ina gabanta, "wallahi ba haka bane Janan, ba haka bane. Kin san yadda muke sarai da matar Yaya da kuma kannenta, bana son harkar da zan je gidan mutane in zauna, wata magana da bata dace ba tazo ta fara fita. Ko kuma rashin hakurina yasa in zo inyi abinda zai janyo mana matsala, shine kawai".


Da alama maimakon maganar ta sanyayar mata da rai, sai ma ta kara tunzurata, tace "to akansu zaki zauna ne da zasu yi korafi? Idan kinzo din duka kwana nawa ne zaki yi ki wuce hostel abinki? Ba lallai kullum sai kun hadu dasu ba!".

Nace "duk da haka Janan, gaskiya kiyi hakuri kawai. Zan kara turzawa dai in gani, tunda jarabawa ce kawai, zanyi karatuna a gida, sauran lectures idan na dawo I'll catch up with you".

Dan siririn tsaki taja, "ai sai kije kiyi tayi, sarkin kafiyar kai. Ba'a tana nuna miki gabas ki bi, sai dai kiyi yamma!". Ta katse wayar tana gunguni. Murmushi na saki a hankali ina girhiza kai, Janan kenan!. 


Sai dai ba'a yi mintuna talatin ba, sai gashi ta sake kirana. Na daga da sauri, sai dai tun kafin inyi magana ta riga ni, "to Yaya dai yace ki hado kan kayanki ki taho gobe!". Kafin ince komi ta sake kashe wayar, na bi wayar da kallo baki a dage.


Dawowar Maryam yasa na mika mata wayar, na cigaba da tukin tuwona cike da sake-sake. Wani bangaren na zuciyata yana fada min inje, wani kuma yana ce min a'ah. Na farko ni dai ban taba zuwa gidansu na kwana ba, na biyu ga yar tsamar da muke yi da kanwar matarshi nasan da kyar ne idan watarana, duk kawar da kaina, na biye mata mun raba hali ba, sannan ni fa bana son zuwa gidan mutane haka kawai in zaune musu. Ni duk wani abu da zai sa in zama uncomfortable bana son shi ko kadan. 


Na gama tuwon na gyara kicin din tsaf, wanke-wanke na barshi sai gobe don dare ya riga yayi. Kulolin dana zubawa Baba nashi, na cicciba na tafi zan kai dakin Alawiyya da take yin girki. A gefen gado na sameta a zaune dafe da gefen cikinta, na ajiye kayan a kasa, na kalleta cikin kulawa nace "Anty baki jin dadi ne?".


Ta dago ta kalleni, fuskarta na yamutsewa cikin nuna jin ciwo, tace "babu komi, cikina ne yake dan juyawa, amma zan sha magani".

Sai dai jikina ya bani ba wannan bane, zata iya yiwuwa ciwon cikin ne, amma ba na shan magani bane. Jikina yana bani wani abu ne daban. Kai kawai na gyada mata, na mata fatan Allah ya bata lafiya na fita daga dakin. 


Ina yarinya kimanin shekaru takwas, na fara ganin haka. It was weird. Wani lokacin kalar idanun mutum ce zata canza, wani lokacin hayakine zan ga yana fita daga waje ko jikin mutum, wani lokaci kuma jikina ne kawai zan ji ya bani. Wanda aka yiwa sammu, ko wanda yayi sammun, da wajen da aka binne ko aka kona abinda aka yin, cikin ikon Allah duk ina iya gani. 

Mama Allah jikan rai, farkon abin tace iska ne, Malam Bako yace ba lallai sai shafar aljanu bane yake kawo hakan, Iko ne kawai da wata hikima ta Ubangiji ba wani abu ba. 

Koma dai menene, ina godewa Allah. Zaman Mama da Ramata na sha ganin ire-iren abubuwan nan. Wasu lokutan a bandaki, daidai wajen tsuguno, sai dai in ciro layoyi, wasu lokutan kofar dakin Mama, watarana na Baba, sai dai in daukesu kawai in kaiwa Malam. Ko Mama watarana bana fadawa balle ta sani. A yanzu haka, bayan su Malam da Yaya, babu wanda yasan da hakan. 


Ina shirin kwanciya, Janan ta sake kirana, a sanyaye na daga. Tace "har kin gama shirin ko?".

Ni sai ma ta bani dariya, nace "wani irin shiri kuma kike magana a kai?".

Tace "dawowa mana".

Sai dana dan yi shiru kafin na fara magana, "look Janan...." 

Tayi saurin katseni, "a ganina ko yankar namanki za'a dinga yi, hakan ba zai hana ki k'i zuwa ki zauna dani ba. Haba Na'ilah, ba fa cewa aka yi zaman har abada ba zaki yi, duka satika nawa ne, zasu kai biyu? Ki zo mu zauna muyi shirin exams dinmu, mu fara fuskantar projects da suke tunkaro mu. Kin san idan kika zauna a gida babu abinda zaki iya yi, na riga na yiwa Yaya magana, ya kuma ce babu matsala zaki iya zama, to me kike jira kuma? Matar Yaya da kannenta duk ba matsala bace, ba fa a gidan zaki dinga wuni ba!".


Na kada kai gefe guda, ta wani bangaren haka ne, it's for my own good. Don haka na daga baki nace "to zan sanar da Baba, amma sai ranar Lahdi zan taho".

Ihun murnar data saki shi ya sake bani dariya, na girgiza kaina kawai. Tace "ko ke fa? Sai ki fara shirin tahowa".

Nace "in Allah ya yarda", muka yi sallama da ita, na kashe wayar. 


Koda na fadawa Baba, haka yace "Allah ya kaimu kawai". Babu tambayar yadda mutanen gidan suke, ko yadda ita yarinyar take, kawai to yace. Na koma daki na fara hada kan kayana. Wanki na fara yi. 


Rana ta fara yi lokacin da naji wani irin gurnani mai kama da kuka yana fitowa daga dakin Anty Alawiyya. Da sauri na saki kayan da nake wankewa na fada dakin, kwance rub da ciki a tsakiyar dakin, itace dafe da cikinta tana ihun kuka. Na tallabota jikina ina tambayar lafiya? Amma ta kasa magana. Yadda take yi har numfashinta yana alamun daukewa, yasa naji wani irin tausayinta ya lullubeni. Na tashi na dauki kofi na debo ruwa, nazo na dinga mata tofi a ciki. Ayoyin tsari da kariya na karanto na tofe mata a ciki, na tallabo kanta na dura mata ruwan, wani yana zubewa a kasa haka nan na dura mata, sauran ruwan da tayi kuma na shafe mata cikinta dashi. 

Mintunanmu kusan arba'in a haka, sannan ciwon ya fara lafawa. Ta fara zufa kamar wadda ake kwarawa ruwa. Na tashi na kara mata iskan fanka. Data dan dawo cikin hankalinta na taimaka mata ta koma kan gado ta kwanta, ni kuma na fita. Duk wannan abin da ake yi, Ramata tana tsakar gida a zaune tana jin rediyo abinta. Nayi kwafa kawai lokacin da muka hada ido da ita. 


Duhu yana fara yi, na salube jiki na fita daga gidan. Inda naga Lubah jiya naje na duka ina haskawa da fitila har na hangi inda nake nema, hannu kawai nasa ina tona wajen kasancewar kasa ce a wajen. Hannuna ya fara cin karo da wasu irin duwatsu da ban taba gani ba, wasu irin kala su ba bakake ba, kuma ba jajaye ba. Sai dana ciro kusan guda biyar, sai kuma naga wata tsohuwar wuka, gashin dabba kamar na Tunkiya dankare da wukar gaba da baya. Nayi bismillah na daukesu na nade su gabadaya na maida kasar wajen na rufe kamar babu abinda ya faru, na shige gidansu Inna.


A gaban Inna na zubesu ina mata bayani, ta hau tafa hannuwa tana salati. Tace "ai wannan sai dai a kona, kai Allah ya kiyashe mu da rashin tsoron Allah irin na mutane. Allah kadai yasan mugun abin da yake kunshe da wannan abu!".

Nace "duwatsun fa? Ya za muyi dasu? Tunda ba lallai su kone ba?".

Tace "to sai dai a nunawa Malam ya gani, sai muji abinda zai ce!". Anan take muka kona wutar, wata irin kalar wuta data dinga fita daga jiki, ga wani irin wari kamar na bunsuru da take fitarwa, haka dai muna tsaye suka gama konewa kurmus. Wukar Inna ta dauka ta hada da duwatsun nan. Sai dana yi sallah sannan na koma cikin gida. 



A haka dai na lallaba zuwa ranar Lahdi. Karfe goma na safe ina cikin tasha, bayan nayi sallama da mutanen gida. 




      *☆⋆07⋆☆*







Muna shigowa Zaria, kiran Umar ya shigo cikin wayata kamar ya sani. Kamar ma babu network a inda muke, saboda bana jin shi ta bangaren da yake, na gaya mishi bana jin shi amma idan na karasa gida zan kira shi, na kashe wayar. 


Muna shiga tasha mota ta samu waje tayi parking. Na biyo jerin wadanda suke fitowa, na dauki akwatina da jakata. Fita nayi daga tashar ina wurga idanuna ta tsallaken titin domin hango abin hawan da zan kira. Kamar wanda yake jira, ina fita, Umar yana tsayawa a gabana. Yayi murmushi lokacin da yake fitowa daga motarshi, nima na maida mishi martanin murmushin. Ya tsaya a gabana yana kallona, "welcome sweetie!".

Na saki dariya a hankali ina kallonshi cikin girgiza kai, "is this suppose to be a surprise welcome?".

Yayi murmushi, yace "ko kadan, na kira ki in fada miki na fito daukar ki sai baki ji na... Maza ki shigo mu wuce kada ki zube min anan saboda gajiya!". Ya karasa fadar haka yana bude min kofar gidan gaba. 


Na silala jikina cikin motar ina murmushi, "tafiyar merely awa hudu ba zata gajiyar dani haka ba, Umar".

Ya maida murfin motar ya rufe tare da ciccibar akwatina da jakata yasa a bayan booth, ya zagayo ya shiga yayi wa motar key, sai a lokacin ya juyo ya kalleni, "sai ina?". 

Nace "gidan su Janan". Yayi jim, kafin ya juyo ya kalleni, fuskarshi na nuna alamun tambaya, cike kuma da mamaki. Na ajiye ajiyar zuciya, cikin alamun bayani nace "a can zan zauna zuwa lokacin da zan samu wajen zama".

Yace "shine baki fada min da wuri ba? Da baki je wajen Mommy kin zauna ba?!".


Na daga baki ina kallonshi kamar wani wanda ya fitar da sabon kai, ya kyalkyale da dariya yana dukan sitiyari, "just kidding!".

Kai kawai na iya girgizawa. Abin ma sai ya bani dariya. Kawai sai aga budurwa taje gidan su saurayi zama, babu aure kuma babu komi. A can kasan zuciyata ina tunanin ai ko da ace Mommynsu da sauran kannenshi suna so na, ba zan iya wannan danyen aikin ba. Har yau bamu gama clicking waje daya da yan'uwanshi ba, ban san dalili ba. Amma na fi danganta hakan a rashin sanin juna sosai da muka yi. 


Ya juya baya yana lalube cikin wata leda har ya ciro gwangwanin maltina ya miko min, na amsa, sanyinta na ratsa hannuna. Na fasa na kafa a kai na daddaka, na ajiye numfashi in bliss, "God! Kamar kasan abinda nake bukata kenan!".

Yayi murmushi kawai tare da jan motar muka tafi. 


A kofar gate din gidan Yaya Bilal yayi parking din motar tare da kashewa. A kofar gidan, Halima da Salama kannen Anty Raheemah ne zaune a karkashin inuwar babbar bishiyar mangwaro kofar gidan, da alamu hira ce suke yi ko kuma shan iska kawai. 


Na bude murfin motar na zura kafata waje na fita daga ciki, shima Umar din ya fito, duk suka bi mu da kallo. Na gyara zaman gyalena a kafadata ina kallonshi nace, "na gode Umar, bari in karasa ciki".

Yayi murmushi, "it's my pleasure!"

Zagayawa yayi ta baya ya bude booth ya ciro min kayana dake ciki, ya sake bude bayan motar ya fito da shopping bag ya miko min, na daga baki zan yi magana yayi saurin katseni, "snacks ne kawai da drinks ba wani abu".

Nasa hannu biyu na karba ina mishi godiya, ya girgiza kai, "kila zuwa anjima idan na gama abubuwan da nake yi da wuri, zan biyo".

Nace "Allah ya kaimu anjiman".

Daga haka ya sake zagayawa ya shige cikin motarshi ya ja ya bar wajen. Na dauki akwatina a hannu daya, dayan kuma na dauki daya jakar da ledar da Umar ya kawo min na tunkari gidan. Strangely, naji bugun zuciyata ya canza, na danganta hakan da nervousness.


Haleemo ta kalleni tana murmushi, "ashe yau kike tafe? Sannu da zuwa, ya hanya?".

Na dan saki tight murmushi, gajiyar dana kwaso tana kara lullubeni, nace "lafiya kalau, sannunku". Na gaishe su gabadaya, a lokaci daya. Duk suka amsa min, na wuce cikin gidan. 


Duk cikin kannen Anty Raheemah, har ma ita Rahimar, Haleemo ta fi su sanyin hali, shiru-shiru, da kuma rashin rawar kai. Shi yasa tamu tafi zuwa daya da ita. Har wani lokacin idan naje gidan mu kan dan hiranta da ita. Salama kam, tsabar tsiwarta da rashin mutunci yasa ranar farko da muka fara haduwa da ita muka kusa yin baram-baram. Bata da kirki ko kadan, zata iya tsaga tsakiyar idanun mutum, ko ma wanene shi ta yanka mishi rashin mutunci ta kara gaba. To kada kuma Adi taji labari, ita ta damesu ta shanye. 

Ni dai fatana daya, in samu in gama dan zaman da zanyi dasu lafiya ba tare da wani rikici ba. Shi yasa na taho da kudiri, kuma da burin kai zuciyata nesa, kauda kai daga lamarinsu koda zasu taka ni ne, da kuma maida komi ba komi ba. A takaice dai, naci damarar ba banza ajiyarsu. 


Ina bi ta kofar gidan, maigadin gidan, Ahmad. Dan matashine, kuma buzu, ya fito daga dan dakinshi da sauri yana min oyoyo. Murmushi nayi a gajiye na amsa, ya karbi akwatin hannuna da jakar ya biyo ni a baya har sashen Yaya Bilal din. 

Na buga kofar falon gidan, jin alamun kofar a bude take yasa na tura kofar na shiga bayan na cire takalmina anan dan corridor din da suka tanada musamman saboda ajiye takalma. 

Ahmad ya ajiye min kayana na sake dauka na shiga babban falon nasu bakina dauke da sallama. Raheemah da kawarta Adi na zaune suna kallo, gefensu gwangwanayen lemuka ne da plates wanda nake tunanin suka gama cin abinci daga ciki. 


Babu wadda Allah ya bata ikon amsa min sallamar da nayi, sai kallo da dukansu suka fara bi na dashi, dani da kayan hannuna. Duk kokarin da nayi, sai da naji zuciyata ta fara rawa. Wani bangare mai rauni na zuciyata ya fara raya min over and over, zuwana nan gidan was a bad idea. Yana kara gaya min dalilai da dama, masu nuni da cewa gaskiya yake fada min. 

Bisa wadannan dalilai dama wasu, yasa naji na fara tantamar anya ba zan juya inda na fito ba kuwa? Musamman tunda Janan bata riga ta san da zuwa na ba, zan iya ce mata wani uziri ne ya taso na gaggawa da yasa na koma gida, ko rashin lafiya, ko...!


Daidai lokacin da kofar dakin Janan din ya bude, ta fito daga ciki. Muna hada ido da ita, ta saki murmushin daya haskake mata fuska baki daya. Ban san dalili ba, naji wani kwarin gwiwa ya shige ni, wani over confidence dana rasa daga inda yake. Da sassarfarta ta karaso wajena, bata yi wata-wata ba, ta janyo ni ta rungume. 

Sai data gama murnar ganina sannan ta sake ni, ta ja baya tana kare min kallo tun daga sama har kasa. "ke hutun nan dadi ya miki sosai fa da alama... Taho muje daga ciki dai, kiyi sallah ki huta!".


Ta kama akwatin hannuna ta fara ja. A hankali na maida kallona ga su Rahima da har lokacin, idanunsu na kanmu kurr. Yadda suka yi yasa na fara tunanin anya sun san da zuwan bakuwar da zata zaune musu a gida na yan kwanaki kuwa? Nayi kokari na danne uneasiness din da naji a jikina, ko ma dai menene, tsakanina da Allah bana son wani abu yaje ya zo, a dinga cewa ta dalilina hakan ya faru.

Don haka na dage tun karfina na kakalo murmushin da ni kaina nasan cewa sun san na yake ne, gajiyar da nayi ta kara worsening abin. Nace "Anty Rahima, Adi, sannunku da gida!".

Adi ta amsa da 'lafiya lau', yayin da Rahimar ta dauke kanta daga gareni ta maida kan Janan. 


Cewa tayi wai, "wannan fa?".

Nayi kwafa a boye, wani 'wannan fa!' sai kace wata shara ko kayan wanki, yadda kasan bata taba ganina ba. 

Janan da bata kula da rainin wayon da tambayar tazo dashi ba, ko kuwa ta fahimta fuskewa kawai tayi? Cikin murmushi tace "Anty kawata ce fa, Na'ilah. Yaya ya fada miki zata zauna damu kafin ta samu wajen zama a cikin hostel".


Antyn ta sake waiwayowa ta kalleni, fuska a murtuke, bakinta a tsuke, wanda ba karamin kokari nayi wajen danne dariyar data kamo ni ba sanadiyar ganin expression dinnan ba. Tace "zama damu ko ke?".

Janan din ta danyi turus! Kafin ta sake yin murmushi ta cigaba da jan akwatin zuwa dakinta tana furta "muje". Ban kara waiwayarsu ba na bi bayanta. 

Sai dai ko daga inda nake, ina iya jiyo sautin muryarta da maganganun da take yi da dan karfi, obviously yadda zamu jiyota sosai, "shima 'Baby' da dan banzan kwashe-kwashe. Kawai babu dangin iya balle na Baba ka wani kwaso mana yarinyar da baka sani ba, ka ajiye mana a gida. Ko da wanne yake so mutane su ji? Da wannan yar rainin wayon kanwar tashi ko kuwa da wata bare kuma?", tayi shiru tare da yin kwafa, "wai wani kafin ta samu daki! Ko kuma kwadayi ba!!. A dai zo a zauna din, aga idan wata tsiya za'a b'anb'ara daga jikinmu....".

Sauran maganar ta mutu lokacin da muka shige dakin Janan muka maida kofar muka rufe. 


Janan ta dubeni fuskarta cike da damuwa, "don Allah kiyi hakuri da abinda tace!".

Na daga kafada cikin nuna alamun rashin damuwa, duk da cewa kawai don kada ta damu ne na fadi hakan, amma fa maganar kwadayin nan ta taba raina sosai, nace "menene abin jin haushi a maganganunta? Babu komi wallahi. Bari inyi sallah".

Tace "to", a lokaci daya kuma tana fita daga dakin. Ni kuma na fada bandakinta. 


Ina gama sallah, ta hau turo min plates da bowls na abubuwa. Na kallesu ina kwashewa da dariya, nace "baiwar Allah ina kike so in kai wadannan abubuwan? Ba dai cikina ba ko?".

Itama tayi dariyar, "na san ki da rashin son cin abinci idan zaki yi tafiya, na tabbata rabonki da abinci tun karin safe".

Nayi shiru ban amsa ba saboda haka ne, shima karin safen da nayi shayi ne kawai, babu abinda na hada dashi. Daga shi sai maltina din wajen Umar. Hakan ya tuna min da ledar daya hado ni da ita. 


Na tashi na nade abin sallar, na koma gefenta na zauna bayan na dauko ledar. Lemuka ne kala-kala was ciki, wasu juices wasu kuma fruit juices sai su tarkacen doughnuts da cupcakes. Tare muka ci abincin da ita muka gama, bayan mun gama ta fita da kwanukan abincin, yayin da na ciro wayata daga cikin jaka na hau kiran yan gida ina sanar dasu na sauka lafiya. 


Wajen karfe takwas saura bayan mun gama yin sallah, Umar ya kira ni ya sanar dani yana kofar gida. Na dauki gyalena dana rataye a jikin hanger ina kokarin yafawa, ko hoda ban kara ba balle janbaki. Ni kwata-kwata bana ganin amfanin yin wannan kwalliyar ta dare idan za'a fita hira, koda yake dama ta yaya za ayi in gani tunda dama can kwalliyar ba damuna tayi ba?. 

Janan dake kwance ruf-da-ciki akan katifarta tana chatting ta kalleni lokacin da nake shirin fita, tace "kada dai ki wuce karfe tara da rabi, idan kuma ya shigo daga ciki, ku koma daga waje duk da nasan cewa ba lallai Ahmad ya bude mishi gate ba, sai dai idan baya nan".


Nayi yar dariya ina kallonta, "kada dai kice min kuna da curfew a gidannan?!".

Tace "Yaya ne yasa wallahi. Samarin su Salama suke shiga da fita babu kakkautawa a gidannan, ko ina kuma shigo dasu suke yi har cikin falon nan, shine ya kafa wannan doka".

Na gyada kai, "yayi kokari gaskiya, da haka ake yi a wasu wajajen ai da an samu zaman lafiya kuwa". Tayi yar dariya, "kin ci sa'a ma Yayan baya nan, da sai kin amsa tambayoyi daga wajenshi kamar kina rubuta jarabawar jamb kafin ki fita yanzu".

Na kama baki cike da mamaki, gefe daya kuma ina jinjina kokarin Yayan, a ganina hakan da yayi hanya ce mafi sauki ta sanin halin da kannenshi da samarinsu suke ciki. Na dai mata sallama na fita. 


A kofar gate muka yi clashing da Haleemo ita kuma zata shigo, ta ja da baya tana daga waje alamun ta bani waje in fara fita, na danyi murmushi appreciatingly na raba ta gefenta na fita. Ta kalli gefen gidan inda Umar yayi parking din motarshi, tace "saurayinki ne ya dawo?".

Mamakin tambayar ta kama ni, amma sai na fuske nayi yar dariya kawai ina gyada mata kai, tace "kinyi sa'a abinki ke kam!". Ta shige gida, na bita da kallo baki a bude slightly, ko meye hadinta da zancen soyayyata, sa'a ko rashinta? Na daga kafada tare da tsallakawa daya gefen. 


Da kanshi ya bude min murfin motar, na shiga ciki bakina dauke da sallama. Barin murfin motar nayi a bude, ban maida shi na rufe ba. Ya amsa min sallamar, scowling, na kula baya son hakan ko kadan, ya sha fadin hakan ma ba sau daya ba sau biyu ba. Kunnen uwar shegu kawai nake yi dashi. 

Mun fara hira dashi game da makarantarmu da wajen aikinshi. Ya fada min anyi posting dinshi zuwa Kaduna, satin sama zai shirya ya tafi. Na mishi addu'ar Allah ya taimaka. Daga nan hirar ta koma ta masoya, ya fara amayo kalmomin soyayya. Jinsu kawai nake yi suna shiga suna fita cikin kunnena. Ban sani ba, ko akwai ranar da zanji wani yace yana so na, in yarda da hakan? Inji zuciyata ta mamaye da haske da farinciki sanadiyar jin haka? Nayi nisa cikin tunanina, totally zoned out. Wani abu daya zame min jiki da zarar naji mutum ya fara amayo kalmomin nan, ban san lokacin da hakan take faruwa ba, kawai sai dai in tsince ni nayi nisa a duniyar tunani, I couldn't help it. 

Umar ya murza yatsunshi biyu a fuskata, sautin da suka yi ne yasa na dawo daga tunanin dana shiga. Na kalleshi sosai, kallona yake yi, nace "me kace?".


Fuskarshi ta nuna alamun damuwa da kulawa, yace "Sweetie, ban san sau nawa kike so in fada miki cewa bana jin dadin abinnan da kike yi ba. Sau tari sai in ganki kinyi nisa cikin tunani, hakan yana kona min rai. Don Allah ki fada min, idan wata damuwa ce take damunki, ki fada min inyi miki maganinta!".

Na girgiza kai, ina mishi murmushi a sanyaye, "babu abinda yake damuna Umar, kaima kasan cewa da da akwai zan fada maka ne".

Ya juya kai, "abinda kike cewa kenan kullum, babu canji. Har zuwa yaushe ne don Allah? Sai inga kamar baki jin dadin kasancewa da nine".


Na kalleshi cike da mamaki, "meya sa ka yin wannan tunanin? Ni fa na fada maka babu abinda yake damuna, idan akwai zan fada maka wallahi, kaima ka sani".

Ya rausayar da kai, "to ai shikenan sweetie, yadda kika ce". Shiru ya ratsa wajen, kafin naga ya bude dashboard ya ciro wani kwali. Yanayin tsayin kwalin yasa nayi zargin waya ce a ciki. 

Ya miko min, bakinshi dauke da murmushi kamar zai tsaga bakin. Yace "dazu na ganta a shago, sabuwar shigowa ce, ban yi tunanin kowa ba sai ke lokacin dana ganta".


Na sanya hannu na karba tare da budewa, sabuwar wayar Samsung ce sai sheki take yi. Duk da bai fada min kudin wayar ba, nasan ba karamin kudi zata yi ba.

Cikin alamun tambaya nace "amma me yasa? Ina da waya, ka tuna?".

Murmushin fuskarshi ya bace, "na sani mana, shi yasa ma na sai miki. Na kula da taki ta ma fara fading fa, kai gabadaya ma ta tsufa".

Na kai yatsa daya na shafo saman hancina, wani abu da nake yi unconsciously idan magana bata karbu a wajena ba, ko kuma idan maganganun mutum were so bored. Niyyata in tambayeshi sai me don wayata ta fara tsufa? Naga dai ina amfani da ita lafiya lau, kamar dai yadda sauran masu latest wayoyi suke yi. Sannan wayata lafiyayyiya ce, bata bani wata matsala balle yace saboda matsalar ta ne. 

Sai dai nayi shiru kawai, nasan cewa idan na daga baki nayi magana hakan zai kaimu ga yin sa'in'sa, hakan kuma ba dadi zai mana ba. Don haka nace mishi "to nagode kwarai, Allah ya amfana. Amma zaka amshi tsohuwar tawa wayar ne ko?".


Yayi wani irin murmushi, idanunshi na karade fuskata da kallo, "ko kadan sweetie na, amma zaki iya bani dan kiss, a matsayin tukuici na".

Na daga kai na kalli tsakiyar idanunshi, babu alamun wasa ko kadan, alamunshi sun nuna da gaske yake. Duk da haka, sai na maida abin wasa, nayi yar dariya kawai, "dadina da kai ka cika ban dariya wallahi Umar... Bari in koma daga cikin gida don lokacin da aka dibar min ya kusa cika!"..


Ban jira ya bani amsa ba, na yunkura da niyar fita daga motar. Kawai ji nayi murfin motar ya koma ya rufe, tare da wani karamin kara alamun an sa motar a lock. Na kai hannu da niyar bude motar, sai dai naji gam, kamar yadda nayi zato ya rufe ni. 


Na juya ina kallonshi, fuskata a dinke tsam babu alamun wasa balle yayi tunanin kawo min maganar shirme, nace "meye haka? Bude min kofa in fita don Allah".

Ya gyara zamanshi sosai, "a'ah, magana zamu yi dake sosai. Na kula duk lokacin dana fara furta miki abinda yake cikin raina, sai ki banzatar da maganar ki maidata wasa, an fada miki ni dan wasan kwaikwayon ban dariya ne? Ni fa in fada miki gaskiya na gaji haka nan Na'ilah! Na gaji! You are officially my girlfriend!! Yakamata ace zuwa yanzu mun wuce kan wannan maganar, ba tun yau ba yakamata ace wannan maganar a tsakaninmu ta wuce, ace mun wuce wannan matakin. Nima fa mutum ne. Nima ina so ace ina taba ki, ace zuwa yanzu jikinki ya riga ya saba da nawa, amma kullum sai ma kara janye jikinki da kike yi daga nawa, to na gaji, yau sai dai ayi ta ta kare tsakanina dake!!".


Tsananin mamakinshi ya dankarar dani a zaune, na kasa motsi. Bakina nake motsawa ina so inyi magana, in maida mishi martani ko yaya ne, amma kamar ansa zare da allura an dinke min shi, na kasa buda shi. 

Ganin haka yasa ya cigaba da magana babu kakkautawa, "meye bana miki? Meye bana baki?? Idan ma abinda nake miki ne bai isarki, kema kinsan ai ba sai kin zauna kina wani shan kwana ba, ki fito ki fada min mana ki ga idan ban baki ba yanzu take! Meye na roki ki min? It's just a kiss fa! Meye a cikinshi?".


Sai lokacin naji bakina ya motsa, saboda tsananin bacin ran da maganganunshi suka haifar min yasa naji jikina yana wani irin rawa, nace "sau nawa kake so mu yi wannan maganar da kai? Jikina ba jikim banza bane da zan sakar maka shi kawai saboda kana yi min hidima. Na fada maka ina bukatar abubuwan da kake yi min ne? Na taba daga baki na tambayi wani abu a wajenka? Ko kuma na taba furta maka ina bukatar irin rayuwar da kake son yi? Kawai saboda kai kana ganin irin wannan rayuwar itace wayewa, ni a ganina ba hakan bane. Ba zan taba yin rayuwar zubda mutunci ba, ba zan taba zubar da mutunci da kimata ta ya mace ba akan mata'ul hayat, abubuwan da zasu kare cikin dan kankanin lokaci, saboda haka ka bude min kofa in fita!".

Cikin saurin magana da bacin rai nake maganganun, nasan da kyar ne idan ya fahimci duk abinda na fada. 


Ya sauke ajiyar zuciya, "come on Na'ilah! Ni fa ban ce ki bani kanki ko wani abu ba, kawai kananun abubuwa nan da can ne fa, what's the harm in it? At least ki dan dinga appreciating dina mana!".


Na galla mishi harara, "kai a wajenka ba komi bane, saboda shaidan ya riga ya rufe maka idanu, amma ni a wajena it's a big deal. Kada ka manta, mun taba yin wannan maganar da kai, na fada maka idan kasan wani abu kake bukata daga wajena yafi mana sauki mu yanke alakarmu, don babu abinda zan iya maka. Ba zaka taba taking advantage dina ba Umar, ba zaka taba yin amfani da kayan banza ka yaudare ni ba wallahi, in Allah ya yarda nafi karfin haka. Don haka ka bude min kofa in fita tun muna shaidar juna ni da kai wallahi. Kuma ga wayar ka nan, bana so, kai bana so in kara ganinka ma!!".


Na hau kici-kicin bude kofa da sauri kamar wadda ta fita daga cikin hayyacinta. Ina ji yana kiran sunana amma nayi banza dashi. Ban tantance ba naji saukar hannunshi yana dafe min hannu, banyi wata-wata ba na wancakalar da hannun nashi can gefe. Bai daddara ba dai ya sake dafa kafadata, wannan karon dana kama hannunshi, twisting nayi da karfina duk da nasan ba lallai yaji zafin hakan ba, duba da yanayin aikinshi. 

Cikin tsananin bacin rai da tunda muke dashi bai taba ganin kwatankwacinsa ba, daga murya da tsawa nace "kada ka sake taba ni!! Kada ka sake kuskuren taba ni!! Kuma wallahi ka cuce ni da kayi tunanin zaka iya saya na da kyale-kyalin banza, in shaa Allahu sai Allah ya saka min. Ka bude min kofa nace!!".

Tsananin ihun da nayi ni kaina ya bani mamaki balle shi. Ina jin hakan ne yasa bai ma san lokacin da hannunshi ya danna madannar ba, ina jin na taba murfin ya bude, na fita daga motar da sauri. Ko sakan biyu ba ayi ba naji shima ya fito, ya hau auna min kira. Babu ko waiwaye, na shige gida da sauri. 


Jikina rawa yake, hannu, kafa, baki, kai, komi nawa rawa yake yi. A daidai parking space dinsu na tsaya, na dafa wani pole ina haki kamar wadda tasha tseren rai da rayuwa. Kodayake kusan hakan ne. 

Tunanina daya a lokacin, da ace yaki bude kofar fa? Me zai faru da yaki bude kofar? Me zai faru idan bai daina taba ni ba? Me zai faru idan wajen da muke babu mutanen da zasu ji ihuna idan ina ihun neman taimako? Tambayoyin suka yiwa zuciyata yawa. Ban san lokacin da gwiwoyina suka saki ba, na zube akan gwiwata a wajen. Allah kadai yasan iya lokacin dana dauka a wajen, ban ma san a wani hali nake ciki ba. Kai ban ma san ina hawaye ba sai da naji lema da alamun gishirin hawaye akan lebena sannan na ankara. Sai kuma vibrating din da wayata take tayi babu kakkautawa. Na daga na ga sunan Umar yana rawa a jiki, tsaki na ja nayi declining, yana katsewa wani kiran ya sake shigowa. Wayar na dauka gabadayanta na kashe. 


Na mike na kakkabe jikina tare da share hawayena. Sai dana tabbatar da na dawo cikin nutsuwata sannan na wuce cikin gida. Su duka suna falon suna kallo banda Janan, na musu sannu na wuce ba tare dana jira naji sun amsa min ko basu amsa ba.


Janan tana tsaye a tsakiyar daki da waya a kunnenta, ina shiga ta sauke wayar, "yanzu fa nake kiran wayarki, sai kuma naji ta kashe".

Na kalli wayar kafin na kalleta, "kashe ta nayi".

Ina tunanin bata kula da yanayin da nake ciki ba sai a lokacin, da sauri ta matso wajena, fuskarta dauke da alamun damuwa, "lafiyarki lau? Me ya faru??".

Na girgiza mata kai, "babu komi fa!".

Ban jira amsarta ba na yaye gyalena na rataye na shige bandaki. Alwala na dauro na fito. 


Janan ta bini da kallo har na shimfida abin sallah, bata ce komi ba. Har na gama shafa'i da wutiri, na fara shirin saka kayan barci. Tasan ko ta dameni ma babu abinda zan iya gaya mata, sai ma karin bacin rai da hakan zai haifar min, don haka taja bakinta tayi shiru, tasan duk lokacin dana sauka don kaina, zan fada mata. Babu boye-boye a tsakanina da ita. 

Instead sai tace "idan kin gama kafin mu kwanta, ki zo in danyi briefing dinki akan abubuwan da muka yi wannan satin".

Kai kawai na iya gyada mata. Dana gama shiryawan, naje gefenta na zauna, ta dauko littafinta ta bude ta fara min bayani. 

Zuwa lokacin da muka gama, na dan fara saukowa daga fushin, haka ma zafin zuciyata ya dan lafa, amma duk da haka abin yana makale a cikin raina. 

Kai har lokacin dana kai ga kwantar da jikina akan katifar Janan da niyar inyi barci, abin yana makale a cikin raina. Nasan cewa shi da fita har abada. 
















      *☆⋆08⋆☆*






Da azumi muka tashi washegari, bayan munyi sahur, wanda ni ruwa kawai na iya sha, muka yi nafiloli har aka kira sallah, muka yi. 

Janan ta tashi zata fita bayan gari ya fara yin haske kadan, lokacin na gama azkar dina kenan. Na dubeta cike da alamun tambaya, tace "breakfast zan je in hada, kiyi wanka kafin in fito".

A zato na ko haka dokar gidan take, don haka naga bai kamata in barsu suyi aikin su kadai ba. Na tashi na saka karamar hijabi akan kayan barcina, duk da ba masu fitar da jiki bane, kuma Janan tace Yaya a gidan Anty Ameerah ya kwana, still ba zan dauki chances ba. Sai dai ina zuwa kitchen din nayi turus, ganin Janan ita kadai a tsakiyar madaidaicin kicin dinsu tana kokarin dora tukunya akan gas. Na shiga ina karewa kicin din kallo, "ina sauran?".


Da sauri ta juyo ta kalli inda nake, ina tunanin bata tsammaneni a wajen ba shi yasa taji abin unexpected, "su wa fa?". Ta tambaya lokacin da take kokarin zuba mai a cikin tukunyar. 

Na kada idanuwa, "ina nufin sauran wadanda kuke zaune a gidan dasu, ba zasu fito kuyi aikin tare bane?".

Ta danyi murmushi cikin girgiza kai, "ni kadai nake aikin dama can!".


Na zaro ido, "say what??!". Ta kwashe da dariya, na harareta, "wannan ba abin dariya bane Jan, this is serious! Ta ya za ace gardawan banza suna kwance sun saki baki da hanci suna barci, ke kuma zaki dage ki girka musu abinci? Wow! Ko da kike cewa suna sakar miki aikin gida, ban yi zaton har da wannan ba ai".

Tayi yar dariyarta a sanyaye, "ni ban ga abin daga jijiyar wuya a cikin wannan lamari ba. Na riga na saba ne, har ya zame min jiki wallahi. Sannan yawanci kafin Yaya ya wuce Abuja yana biyowa ta nan yayi karin safe, shi yasa nake tashi in hada, sai kuma abin ya zame min jiki."


Duk bayanan da take yi sai lokacin ta dago ta kalleni, ganin yadda nake kallonta kamar wata tababbiya yasa ta sake sakin wata dariyar, "da gaske ba wani abu bane, ni wallahi ban damu ba. Besides, su suke yin abincinsu da rana, wanda sai na ga dama nake ci".

Nace "ai shikenan, me zan taya ki dashi ne?".

Ta jefo min peeler, na cafe, tace "fara da dankalin can mu gani".

Na fara fereye dankalin yayin da taci gaba da soya kayan miya da tayi grating. 


Cikin dan lokaci kankani na gama firar, muna yi muna hira jifa-jifa, duk da dai shiru yafi yawa. Na kunna stove tare da dora frying pan da mai a ciki, yana yin zafi na fara zuba dankalin da na yanka a tsaitsaye, bayan na zuba maggi da dan gishiri, wata dabarar soya chips da Fatsu ta koya min. 


Muna gamawa ta dauko kula da flask, ta zubawa Yaya nashi da kunun gyada, fari tas dashi yana ta kamshi, ta kai falo ta ajiye. 

Muna cikin maida kayayyakin da muka yi amfani dashi bayan mun wanke, muka jiyo karan bude gate. Janan ta leka ta tagar kicin din da take fuskantar gate, ta jiyo ta kalleni "Yaya ne!". 

Na ajiye frying pan a inda yake na juya ina kallonta, "bari in shiga wanka kawai, bakwai ta kusa yi", kai kawai ta gyada min saboda hankalinta yana kan sauran kunun gyadar da take juyewa a cikin wani babban silver flask. Na fita daga kicin din. 


Ina shiga daki na hada kayan da zan bukata na fada toilet. Bandakinta babba ne, yana da fadin shi daidai misali da kuma kayan amfani na zamani. Nayi amfani da sabulunta na 'Vix' mai kamshin sandalwood nayi wanka. Ban tsaya bata lokaci ba don nasan bamu da cikakken lokaci. 

Ina gama wankan nayi amfani da karamin towel na kafe jikina. A cikin bandakin na zura doguwar rigar material ruwan kasa mai laushi, kafin na fita. 


Janan tana gefen katifarta daure da towel, waya a hannu, da alamun jirana take yi. Ta daga kai ta kalleni lokacin da taji na maida kofar bandakin na rufe. 

"wai fada kuka yi ne ke da Umar?".

Naji wata irin faduwar gaba lokacin da naji ta ambaci sunanshi. Tunda na tashi da safe nake ta gujewa tunaninshi a cikin raina. Na hana kaina sakat, da naji sunanshi ko fuskarshi na shirin fado min a cikin raina sai inyi saurin sako wani abun daban. 

Na daka fuska ina zama akan kujerar dake gaban dressing mirror dinta, "me kika gani?".


Cike da tuhuma tace, "ban sanar dake bane kawai, amma tun jiya da dare yake kiran wayata da turo texts, sai daina dagawa nayi. Yanzu ma tun dazu yake kira, yace in baki hakuri".

Nayi kwafa kawai ban amsa mata ba, ta tashi tsaye tazo ta dafa kafadata, "ki daure ki daga kiranshi don Allah, baki san abinda yake son ya fada miki ba. Nayi zaton kun wuce matakin irin wannan fadan ke dashi?".

Na harareta ta cikin madubin, "bamu wuce ba, kuma ma in Allah ya yarda wannan shine karo na karshe da zamu yi fada dashi, we are done Jan!".


Fuskarta bata nuna komi ba, babu mamaki, farinciki ko akasinsa, sai kai kawai data gyada, tace "bari inyi wankan nima, amma ki dai daure ki bude wayarki, ko ba don shi ba saboda mutane masu nemanki. Yaya Mudan ma ya kirani lokacin da kina wanka, shima dai ya nemi wayarki a kashe".

Sai lokacin naji nayi murmushi, nace "wato har yanzu dai Mudan dinnan yana nan ko? Kinsan Yaya ya tsani sunan nan".

Tayi dariya, "ramawa kura aniyarta kenan!". Daga haka ta shige bandaki. Nayi dariya kawai naci gaba da shirina. 


Zuwa lokacin dana gama hada komi da zan bukata, Janan ta fito daga wanka itama ta fara shiri. Da wayarta nayi amfani na kira Yaya, yana jin ni ce ya fara zuba min korafin ina na shiga? Excuse din dana bashi shine 'wayar ce babu caji tun jiya'.

Yace "su Malam ne nima suka dameni da kira tun safiyar yau, wai suna ta kiran wayarki su ji in kin sauka lafiya kuma a kashe, shine hankalinsu ya tashi!".


Ni gabadaya na ma manta ban kira su ba a jiyan. Na manta yadda suke ne, musamman idan zanyi tafiya, hankalinsu baya kwanciya sai sunji muryata na tabbatar musu da saukata lafiya sannan.

Nace "afuwan, ka basu hakuri don Allah. Wallahi mantawa nayi ban kira su ba, idan nayi caji zuwa anjima zan kira su".

Yace "to shikenan, Antynki tana gaishe ki", daga nan inda yake ina jiyo sautin muryarta tana kiran sunana, nayi murmushi nace "a gaishe ta itama, sai anjima". Na kashe wayar tare da ajiyeta a gefena. 


Ina zaune har Janan ta gama shirinta, ta dauki jaka tana zuba jotters da handouts dake tsakiyar dakin a yashe inda muka barsu jiya da muka gama karatu. Na mike nima ina kara gyara kayan jikina. Muna gamawa muka fita daga dakin, ina kallo tasa key ta rufe dakin ta maida key din cikin jakarta. 

Har yanzu falon babu kowa, gabadaya gidan ma shiru kake ji kamar babu masu rai. 

Sai da muka fita daga gidan muka dauki hanyar da zata sada mu da babban titi inda zamu hau bus, tace "Yaya sauri yake yi, shi yasa bai tsaya kun gaisa ba, ya bar sakon gaisuwa dai".

Nayi murmushi, "babu damuwa, idan ya dawo zamu gaisa ai in da rabo".


Ta zage zip din bayan jakarta ta ciro dubu biyar, sababbi kar ta miko min, na amsa ina kallonta fuskata cike da alamun tambaya, nace "me zanyi dasu?".

Ta daga kafada, "Yaya yace a baki!".

Na zaro ido, "what?...," a lokaci daya kuma ina mika mata kudin, "A'ah, gaskiya ba zan amsa ba, this is way too much!".

Ta harareni, "sai ki bari in yazo ki maida mishi da hannunki. Kafin kuma ki fara wani tunani, wannan ba wani abu bane. Kamar kudin albashi ne daya saba bamu gabadayanmu har su Haleemo, saboda hidimar makaranta da sauransu, kin gane?".


Na karkata hankalina gabadaya na maida kanta, "duk sati yake baku 5k, kawai saboda hidimar makaranta?".

Ta gyada kai tana kallona, irin ba wani big deal bane a wajenta. 

Nayi yar dariya, "Woah, dole a makale a gida aki tafiya, kuma dole ace kwadayi nazo yi ba wani abu ba. Maganar gaskiya though, ba zan iya amsar kudin nan ba gaskiya, kiyi hakuri ki amsa".


Ta fara huro hanci alamun na fara bata haushi, "sai kiyi kuma tunda kin saba, ni na gaya miki sako aka bani na baki, in kinga dama kada kiyi amfani dasu, ki jira har sai Yaya ya dawo sai ki maida mishi ki gani idan amsa zai yi!".

Na dan dakata da tafiyar da nake yi, "meye abin fushi kuma anan Jan?".

Tace "ke din ce ai idan ba gani kika yi ana miki wuta ba, baki cika fahimtar abu ba".

Nace "to naji, na karba, kuma na gode, Allah ya saka da alkahiri".

Ta harareni cikin wasa, "abinda yakamata ki ce tun dazu kenan, ba ki tsaya neman magana ba!".

Nayi dariya kawai jin abinda tace. Muka cigaba da takawa har muka fita bakin titi. Shatar keke-napep kawai muka yi saboda lokaci daya fara kurewa. 


Allah ya taimaka muka isa akan lokaci. Kasancewar duk practicals ne muka yi, kuma abubuwa basu fara yin nisa ba, yasa bamu jima ba muka taho gida. Karfe biyu ma bata karasa ba muka dawo. 

Wannan karon ma napep muka hau. Muna sauka, wata hadaddiyar Range Rover tana shiga gidan. Muka bita a baya muma muka shiga gidan. Ganin ta gangara can bangaren Yaya Jameel, yasa na kalli Janan, "Anty Sarah ta sake mota kenan?".

Tace "da alama, ko kuma ta gidansu ce. Tunda ko yau da safe motar bata nan".


Wadda muke maganar a kanta ta bude gidan gaba ta fito. Matar Yaya Jameel ce. Saratu da muke kira, ko ince ake kira da Sarah, cikakkiyar yar gayu ce, wadda tasan fashion, kodayake kamar akan abinda naji ance tayi karatu kenan, ko kuma dai wani abu mai kama da hakan. Daga yanayin yadda take shigarta, takunta da gudanar da al'amuran rayuwarta, zaka tabbatar da cewa wayayyiyar mace ce, wadda ilimin boko ya ratsa ta. Gidansu gabadayansu yan boko ne. Kai ita kanta a kasar Germany naji ance taje ta hado degree dinta. Matsalarta daya, rashin shiga mutane. Zaku iya kwashe sati cikakke baku hadu da junanku ba, ni da yake dama ba zuwa gidan nake yi sosai ba, zan iya cewa na kwashe watanni fiye da biyar ban ganta ba. 


Muka karasa wajen da take, daidai lokacin da diyarsu mai kimanin shekaru biyar, Ruqayyah wadda suke kira Mimah, ta fito daga daya gefen mai zaman banza dauke da jakarta da lunch box. 

A lokaci daya muka gaidata ni da Janan, ta amsa tana kama hannun Mimah da take kokarin isowa gareme, jininmu ya hadu da ita sosai. Halin mahaifiyarta na shiga part dinta ta rufe ta kuma hanata fitowa yasa bamu haduwa da ita sosai, sai lokaci zuwa lokaci.

Tana gamawa amsawa ta latsa key tasa motarta a lock, taja hannun diyarta suka tafi. 


Duk da haka sai da Mimah ta juyo tana daga mana hannu, mu duka muka daga mata hannun muna murmushi har suka shige part dinsu, ta rufo. Ni da Janan muka kalli juna muka sake yin murmushi, kafin muma muka shige nasu part din. 


Adi, da Haleemo suna kicin lokacin da muka shiga, Raheemah kuma tana zaune tana sana'ar kallo, ban san ina Salama ta shiga ba tunda bamu ganta ba. Mu dai muka musu sannu, muka shige daki ba tare da mun damu da kallon banza da aka bimu dashi ba. 


Bayan la'asar muka fita waje ni da Janan muka sayo fruits a bakin titi. Muka zo muka hada fruits salad da kayan shan ruwa. Muna cikin soya yam balls, Salama ta shigo kicin din. Babu wanda ta yiwa ko sannu a cikinmu, ta dauki plate kawai sai ganin tana zuba yam balls din a plate din muka yi. Ta debi iya wanda zata dauka, ta fita daga kicin din. Duk kallo muka bita dashi har ta fita. Maimakon abin ya bani haushi, sai ya ma bani dariya. Na girgiza kai kawai, a zuciyata ina furta 'Allah ya kyauta!'. 


Sai bayan mun sha ruwa sannan na kunna wayata. Messages, missed calls, voice mails, messages din whatsapp da voice notes babu iyaka daga Umar, duk abu daya yake tambaya, 'don Allah in daga wayata', na harari wayar tawa kamar shine a gabana, in daga wayata in ce mishi me?! 












     *☆⋆09⋆☆*






Har washegari Umar bai daina kiran wayata ba, nima kuma ban daga ba. Zuwa lokacin missed calls dinshi sun fi a kirga. 

Da safe ina browsing din wasu procedures a wayata lokacin da nake jiran Jan ta fito daga wanka, don na rigata shiryawa. Wata bakuwar lamba ta min sallama ta whatsapp. Daga farko nayi zaton ko Umar ne, sai dana bi ta cikin description dinshi sannan naga kwata-kwata komi nashi bai yi shige da na Umar ba. Na farko dai Umar daya zauna ya zubo miki layi biyu a rubuce, ya gwammace kuyi awa biyu akan waya kuna hira. Shi yasa yanzun haka voice notes dinshi ne suka cika min waya. 

Kamar wanda yake jira, ina amsawa ana maido da amsar ya nake? Fatan na tashi lafiya?.

Nace lafiya lau, ko wanene yake magana? 

Sai aka turo, 'ba lallai ki sanni ba gaskiya, amma ni na sanki farin sani. Ba tun yau ba nake ta so in miki magana, sai yau Allah ya yarda. Sunana Muhammad'. 


Na rubuta, 'to Malam Muhammad ko zaka iya sanar dani inda ka sanni? Don bana tunanin nasan wani Muhammad anan inda nake'. 

Yace 'in shaa Allah zaki sanni nan ba da jimawa ba, na miki wannan alkawarin. Magana ta gaskiya yanzu bana gari shi yasa, amma da zarar na shigo zan zo in same ki, nasan lokacin kuna shika'.


Na daga gira cikin mamaki, ta alama mutumin nan ya sanni fiye da yadda nayi tsammani. Nace 'ta yaya aka yi kasan haka?', ina tura mishi amsar Jan tana fitowa daga bandaki, na kashe datar na sauka daga kan WhatsApp din ina kallonta. Zama tayi ta gama shirinta a nutse. Tana gamawa muka ci pancake da muka yi da ruwan shayi, da muka gama muka dauki sauran da muka yi muka kai kicin muka wuce. 



*


Yau sai yamma likis muka dawo daga asibitin. Da yake yau a bakin titi muka sauka, akan kafafunmu muka gangaro zuwa gidan Yaya. 

A kofar gidan, Umar ne tsaye ya jingina da motar shi. Na danyi turus da ganinshi, gabana yana faduwa, kafin na dake muka cigaba da tafiya. 

Da sauri ya tari gabanmu, "Na'ilah, sweetie, don Allah ki dakata, don Allah ki saurareni, wallahi na tuba, don Allah....".


Jan ta kalleni, yadda na hade fuska kamar naga wani dan aiken mutuwata, yasa ta fara raba idanu tsakanina da Umar. Yaci gaba da zuba magiya yayin da na zagaya ta gefenshi na tunkari kofar gidan gadan-gadan. Janan ta riko hannuna, na juya ina kallonta, tace "meye haka Na'ilah? Ban san ki da wulakanta mutane ba sam".

Nace "kiyi shiru Janan, baki san abinda ya faru ba, don haka kada kiyi kokarin shiga cikin wannan fadan".

Umar yayi tsulum da bakinshi, "don Allah ki saurareni Sweetie, please...".


Na kare mishi kallo, duk da kokarin dannewa da nake yi, da nuna kamar ban damu ba, amma nayi kewar shi. Kwana daya da yini daya kacal, amma nayi kewarshi. 

Na kalli Jan data tsaya tana kallonmu, nace "ki wuce abinki kawai, zan shigo in same ki". Babu musu ta shige cikin gidan ta barmu a tsaye. 

Na harde hannu a kirji ina kallonshi, "me? Yanzu kuma mai kake bukata ne? Kana so mu kebe wani waje ne ko kuma ka kama mana daki ne a hotel?".


Ya dafe kai, "Subhanallah, haba Na'ilah me ya kawo wannan maganar kuma? Kuskure ne nasan dana riga na tafka shi, amma ina neman afuwarki don Allah. Wallahi ban san abinda ya hau kaina ba, ok, na sani. Gajen hakuri ne irin nawa, amma wallahi na gane kuskurena, ba zan kara ba, don Allah ki bani dama Na'ilah, na miki alkawarin hakan ba zata sake faruwa ba".

Naji zuciyata ta fara yin sanyi da jin hakan, nace "how sure are you? Ta yaya zaka tabbatar da cewa nan gaba ba zaka sake tare ni a cikin mota, trying to touch me inappropriate ba?".


Ya hau girgiza kai da sauri, "I assure you hakan ba zata sake faruwa ba, na miki alkawarin ba zan kara taba ki ba tare da izinin ki ba har auren mu!".

Nace "idan kuma hakan ya sake faruwa fa?". 

Yayi shiru yana kallona, nace "magana daya ce Umar, idan abu makamancin haka ya sake faruwa, we are over! Dama kasan hakan ta taba faruwa, yazo ya sake faruwa yanzu, to babu na uku. Idan kuma muka rabu, mun rabu kenan, ka yarda?".

Ya gyada kai, "it's not as if zan sake maimaitawa, but yeah, na yarda. Fushin ki ba abu bane da zan yi marmarin sake gani ba koda wasa. Yanzu dai kin yafe min?".

Nayi jim ina tunani, na yafe mishi? Ya riga yayi convincing dina, kuma yayi alkawarin hakan ba zata kara faruwa ba, saboda haka meye aibun yafe mishi a ciki? Don haka na gyada kaina, ya saki murmushi a tausashe wanda ya sanya ni sakin murmushin nima, "oh thank God! Wallahi baki ji yadda na damu ba, God, I miss you wallahi".

Nayi murmushi kawai, yayin da naji wani sanyi yana kwaranya a cikin raina. Ban sani ba, na yafe mishi din da nayi ne, ko kuma na dawowa gareni da yayi bane. Kafin in sake daga baki inyi magana, muka ji kiran sallah, ya kalleni yana murmushi, "bari in wuce masallaci to, zan kira ki zuwa anjima".

Na gyada mishi kai tare da shigewa gida. 


Bayan mun ci abincin dare a dakin Janan, ta zauna a gefen katifa suna waya da Al-Mustapha saurayinta, ni kuma na shiga whatsapp chatting. Sakon mutumin nan na dazu shine abinda na fara gani, ni na ma manta dashi. 

Amsar tambayar dazu dana mishi da safe ce ya turo min, "kamar yadda na fada miki, na san ki farin sani. Kuma ina matukar kula da lamuran wadanda suke very special a gareni, don haka ba wani abin mamaki bane".


Na maida mishi da amsar 'haba? Ta yaya aka yi na zama very special a gare ka?'.

Babu jimawa sai ga reply ya shigo, 'oh, you are very very special in fact! Idan nace zan miki bayani zamu jima a haka, to cut it short, ina jin ki a cikin raina fiye da yadda kike tsammani'. 

Haka kawai na tsinci kaina da darawa. Wani abu game da mutumin is very fascinating, yet so familiar. A karo na kusan biyar tunda muka fara chatting dashi yanzu, da naji a jikina duk yadda za ayi mutumin nan ya sanni fiye da sani na, kuma nima ko yaya ne na san shi. Sai dai duk hakan bai dameni ba, yadda naji hira dashi ta dauke min hankali, shine abinda ya bani mamaki ya kuma daure min kai a lokaci guda. It's a first. 


Mintunanmu talatin kacal muna hira ta hanyar musayar rubutattun kalmomi, sai gani kwance rigingine a tsakiyar daki, ina kallon fankar dakin dake juyawa, waya a hannu ina ta faman rubutu, yayin da lokaci zuwa lokaci sautin dariya zai fito daga baki na, walau na sani ko ban sani ba. Hakan ya kan sa Jan, da har lokacin tana kan waya, zata juyo ta kalleni cikin alamun tambaya, amma bata tambayeni ba. 


Zuwa lokacin da yayi min sallama akan wani aiki da zai tafi yayi, ba ni kaina ba, hatta zuciyata da gangar jikina naji sun aminta da mutumin. Wanda hakan a karan kanshi ma abin tambaya ne, na farko ban san mutumin ba, babu abinda na sani dangane dashi sai sunanshi, yana aiki da wani kamfani da yake sarrafa takardu, shikenan. Dana tambayeshi yana da mata? Sai yace ba ga ki nan ba? Hakan yasa naji sautin bugun zuciyata kamar zai tsaga tsakiyar kirjina zuciyar ta fito. 

Tsakanina da Allah ban so muka yi sallama dashi ba, na tabbata idan zamu kwana muna chatting dashi ba zan taba damuwa ba a cikin raina, kai a takaice ma zan so hakan ba kadan ba. Muka yi musayar sai da safe, ya tafi bayan ya turo min 'sleep tight!', ya Allah, ban taba jin dadin ganin kalmomin nan daga kowa ba a rayuwata sai a yau din nan. 

Yana sauka naji gabadaya chatting din ya fita daga raina, don haka nima na sauka. 

Na lalubo jakata na ciro littafai daga ciki na fara karatu da bibiyar practicals din da muka yi yau. 


Sai wajen karfe goma Jan ta gama tata hirar da Almunta, (yadda take kiranshi). Ta juyo ta kalleni tana murmushin tsokana, "fadan masoya hutu, wato saboda kun shirya shine kike wannan glowing?".

Nayi murmushi kafin na jefa mata harara, "ni kada ki min sharri wallahi".

Tace "wani sharri? Ga abu nan a fuskarki, kin kuwa ga yadda kike ta zuba murmushi sanda kuke chatting dinnan? Har wani dariya kike yi, irin soyayya tayi dadi dinnan!".


Na danyi frowning ina kallonta, a hankali nace "ba da Umar nayi chatting ba dazu".

Ta hangame baki cikin mamaki, "wasa kike yi ko? I mean, idan ba Umar ba, waye to? Yanzu da kika fadi haka sai na tuna Umar baya dogon chatting, wanene muka samu??". Ta karasa fada tana daga min gira cikin alamun tsokana. 

Na jefeta da littafin hannuna, ta cafe tana dariya, "fada min mana!".

Na mike ina tattara kayan dana baza a wajen na maida su cikin jaka. Bandaki na fada kai tsaye na barta tana ihun, "ko shekara zaki yi a ciki sai kin fito kin fada min wanene yarinya!". Dariya kawai na saki mai sauti. Nasan kafin in fito ta manta da zancen. 


Har mun kashe wutar daki bayan mun kwanta, Janan ta kira sunana, na amsa a dan gajiye da kuma barci daya fara cin idanuwana, tace "wai me ya hada ki da Umar ne da?".

Nayi sighing a hankali, "abinda ya faru ya riga ya faru Jan, mun riga mun shirya dashi, that's all that matters. Tone-tonen abinda ya riga ya faru, babu abinda zai mana, don haka ki manta da maganar".

Tace "of course sugar, baki da matsala dani".

Kaunarta naji tana kara ratsa zuciyata, fahimtarta da goyon bayanta a kullum suna kara sa inji ta can cikin zuciya da ruhina. A hankali nace "nagode Jan".

Ina jin sautin murmushin data saki cikin duhun dakin, "sai da safe Na'ilah!".

Nima na maida mata martanin murmushin duk da nasan ba lallai ta gani ba, nace "sai da safe Jan!". Na juya barin damana, tare da rufe idanuna. 


Daren ranar mafarkai nayi masu yawa, da yawa daga cikinsu sun kunshi wani mutum da yake ta nanata kalmar, "ke ce Matata!," kamar waka. 




-Afuwan, in shaa Allah gobe zan turo mai yawa, wannan dinma aradun Allah da kyar hannuna da idanuna suka bada hadin kai nayi typing dinsa. Thank you all. 









#F.W.A




[17/03 9:34 PM] Jiddah Lawal: 🌟 *⋆☆A ZATO NA...!☆⋆* 🌟



        *⋆©Jeedderh Lawals⋆*





                             *☆⋆14⋆☆*






Halin dana sameta a ciki ya sanyayar min da jiki, gabadayanta ta fita daga hayyacinta don ma sun ce wai a hakan ma tayi dama. Yayan da Anty Sarah kadai na tarar a asibitin, a cewarsu wai Raheemah bata jima da barin asibitin ba. Na zauna a gefen gadon tare da shafa gefen fuskarta cike da tausayi, har ta dan fada, gashi yanayin numfashinta bai gama daidaituwa ba har yanzu. 

Muna zaune a hakan har rana tayi, Yaya yake ta shiga da fita daga ofishin likita zuwa inda aka kwantar da ita din. An samu tayi barci, bayan anyi mata allura har aka samu numfashinta ya daidaita. 


Da lokacin tafiya masallaci yayi, Yaya ya tafi akan cewa zai turo Raheemah tazo ta zauna damu, sai dai har aka fito daga masallacin, har muma muka yi tamu sallar bamu ga alamunta. 

Lokacin daya dawo ina kan sallaya a zaune, Anty Sarah kuma tana zaune akan farar kujera tana jan carbi, ya ajiye ledar take away a gefen gadon, yace "ga abinci kuci, likitan yace zamu iya tafiya gida da ita idan ta tashi".

Anty Sarah tace ta koshi, nima nace na koshi da yake cikina a cike yake. 


Karan text daya shigo wayata ne yasa na maida hankalina ga wayar, na duba naga daga Muhammad ne. "Hey baby!", abinda ya turo kenan. Na kara maimaita text din cikin mamakin kalmomin, motsin da Jan ta fara yi ne yasa na wancakalar da wayar gefe na nufeta da sauri. Yaya ya taimaka mata ta zauna akan gadon,  gabadayanmu sannu muke jera mata tana amsawa a hankali. 


Yaya ya dauko madarar ruwa ya fasa tare da mika mata, ta amsa ta sha kamar rabi ta maida mishi sauran, yace "har kin koshi?", ta gyada mishi kai. 

Anty Sarah tace "dama ba lallai ta iya cin abinci yanzu ba".

Yaya ya umarcemu da mu hada kan kayanmu, ya miko gyalen Janan na yafa mata. Da taimakona ta sauko daga kan gadon, ina tallabe da ita a jikina muka fita daga asibitin zuwa wajen da Yaya yayi parking din motarshi. Ya bude mana gidan baya duk muka shige ciki. Bayan ya gama clearing din komi a asibitin, yazo ya shiga motar ya tayar muka tafi.


Yaya Bilal ya kashe motar a ainihin inda suke ajiye motocinsu, farko-farkon shiga gidan, daga nan tafiya ce zaka yi kadan daga bangaren damar ka da zata sadaka da wani zagayayyen karamin garden, grass carpet ne shimfide a wajen, wajen yana da fadi sai kuma bishiyoyin mangwaro, gwaiba, gwanda, ayaba, da sauran kayan marmari dai. Daga gefen garden dinne aka shimfida doguwar hanya da interlocks, kanana masu kyau, itace zata sadaka zuwa bangaren Yaya Bilal. Wadda kuma tayi barin hagu itace zata sada ka da bangaren su Anty Sarah. 


Kan Janan yana kan kafadata, wani barcin ne yake kokarin daukarta. A hankali na tasheta, muka fito daga motar. Anty Sarah ta mana fatan Allah sauwake, ta wuce sashenta muna mata godiya. Rabin jikin Janan yana jikina, na tallabota muka wuce saboda har yanzu jikinta babu karfi sosai. Yaya Bilal yana binmu a baya hannu rike da makullin motarshi da kuma ledar take away din da yayi. 


Gabadaya mutanen gidan suna falo, wannan karon a zaune suke kawai suna hira sabanin kallo da suka saba yi a yawancin lokuta. Raheemah ce ta fara ankara da shigarmu falon, ta mike tana zuba sannu da zuwa cikin alamun borin kunya, kannenta suma suka mike, "ah.., har kun dawo ashe? Yanzu muke cewa mu tashi mu koma fa! Sannunku, ya jikin?".

Muka amsa musu ciki-ciki, Yaya ya umarce ni da in taimaka mata Janan zuwa dakinta, don haka na gewaye su muka wuce zuwa dakinta. Bansan Yayan yana bayanmu ba sai dana ji karan sake bude kofa bayan na maida na rufe. 

Na kwantar da ita akan katifarta, na ja abin rufa na rufa mata daga kafafunta zuwa rabin jikinta, tuni barci yayi awon gaba da ita. Yaya ya miko min ledar hannunshi, yace "ki samu ki zauna kici abinci haka nan, ki zauna ki huta kema".


Na karbi ledar, kaina a kasa, wata irin kunyarshi naji ta lullube ni wanda na rasa dalilin hakan. Nace "to, nagode, Allah ya amfana".

Ya girgiza kai a hankali, wani irin kallo a cikin kwayar idanuwanshi da suka sanya naji jikina ya dauki wata irin kyarma, ikon Allah! Ko dai bani da lafiya ne nima?! Yace "ni ne da godiya Na'ilah! You've no idea how grateful I am right now!".


Subhanallah!! Me ke shirin faruwa da ni ne? Jin fitar sunana daga bakinshi ya haifar min da jin wani irin abu a cikin raina, shin ko mai yasa hakan? Hakan bai taba faruwa dani ba! Sannan muryar Yaya Bilal, yau naji tana min kama da wata murya hallau, matsalar na kasa tunawa ko a ina ne na ji muryar. 

Ban san lokacin daya juya ya bar dakin ba, sai karar rufe kofa naji. 

Na bude ledar na fito da take away din ciki, guda biyu ne da lemukan fanta suma guda biyu, don haka na dauki daya na ajiye, dayan kuma na barsu a cikin ledar na fita domin in mikawa Anty Sarah nata. 


A falo Yaya Bilal ne a tsaye kikam, kamar wani tsohon soja. Su kuma suna lafe akan kujeru kamar wadanda aka kama sun nannagawa sarki garinsu karya. Daga yanayin fuskar shi da take a cune da yadda bakinshi yake kumfa, zaka san cewa fada yake musu, fada kuma bana wasa ba. Tunda nake dashi ban taba ganin fadan shi ba sai yau. Janan tana yawan cewa Yaya Bilal yana da fada, duk da cewa baka sanin fadanshi sai ka mugun tabo shi sannan, to da alamun yau dai an tabo shi. 


Ni dai na kada kai na fita. Yau kofar gidan na Anty Sarah a bude take, abin mamaki, na tura kofar na shiga. Tana kicin. Yanayin gidanta da ka shiga kicin zaka fara tararwa, sai falo da kuma bedrooms. Ta dago ta kalleni lokacin dana shiga, nace "kofar a bude take, shi yasa na shigo kai tsaye".

Tace "babu komi, ina tsammanin Mimah ne yanzu shi yasa, ya aka yi?".

Na mika mata ledar hannuna, "dama abincin da Yaya ya kai ne na kawo miki".

Murmushi naga tayi wanda ya bani mamaki, tace "da kin barshi wallahi kun ci, kin ga abinci ma nake shirin dorawa yanzu".

Nace "a'ah wallahi, ai guda biyu ne ya kawo".

Tace "to shikenan, na gode. Ya Janan din?". Nace "ta koma barci", daga haka na juya na fita daga gidan. 


Har na koma can, Yaya fada yake yi, "... In fada muku gaskiya ba zan dauki wannan cin mutuncin ba! An fada muku ita yar aiki ce? Ko kuma bata san ciwon kanta ba? Waye bai san tana da asthma ba, da zaku barta tayi aikin da zai tado mata shi?!". Ya dire maganar yana sauke numfashi cikin bacin rai. 


Raheemah ce ta samu ta iya magana duk cikinsu, "kayi hakuri, hakan ba zata kara faruwa ba. Ita ce tace zata yi ai...".


Tun ma kafin ta karasa ya katseta, "ke kuma saboda rashin hankali sai kuka barta ko? Na fa san abinnan ba tun yau yake faruwa ba, ina sane, iyaka gudun ruwanku ne kawai nake so in gani. Wallahi Tallahi, kunji rantsuwar da nayi, ba zan yi kaffara ba! Idan makamancin haka ya sake faruwa, gabadayanku sai kun bar min gidana. Kuma daga yau, duk wadda take son yin girki, ta shiga ta girka abinda zata ci ban yi mata iyaka da komi na gidannan ba, amma kun gama cin abincin Janan. Ba zata kara muku girki ba, haka ko tsinke ta tsince a gidannan da sunan shara ko gyara Allah zamanku a gidan nan ya kare! Kun dai ji na fada muku!!". Ya wuce dakinshi fuuuu! Kamar kububuwa tare da maida kofar dakin ya gamtso kamar tashin duniya. Mu kuwa duk muka bi bayanshi da kallo baki a dage. 


Maimakon hakan ya dan zame musu darasi, su dan saduda koda na dan lokaci ne, inaa. Tunzura su ma yayi. 

Adi ce ta fara jan tsaki, "mtswww, aikin banza! Yo mun taba matseta muka ce dole sai ta mana girki ko aiki? Kashi zamu bata idan bata mana aikin bane? Har da za'a zauna ana zagin mutane akan wata banzar bazara, gidan banza dana wofi! An fada musu mu bamu da gidan iyaye ne da za'a zo ana zaginmu ana mana gori?".


Salama ta cafe maganar, "ke ma dai kya fada. Aikin banza dana wofi, da dai ace bamu da gidan uba ne da sai muji haushi, to mun gode Allah muna da gidan uba, kuma ba a inda ba'a son zamanmu muke zaune ba! An fada mishi mu mabaratan abinci ne??".


Raheemah kuma tana ta kokarin sanya su suyi shiru a dan tsorace, "don Allah kuyi shiru mana!", ko kuma tace "don Allah kuyi a hankali kada ya jiyo ku ya sake fitowa!". Na girgiza kai kawai, wato shi dai mai rai ba'a taba iya mishi. Allah ya kyauta. 

Na barsu anan na koma daki. Har yanzu Janan barci take yi. Na duba cikin kayanta na ciro doguwar rigar leshi mara nauyi, na dauki kayan na shiga bandaki na sanya na fito, na sake zama a gabanta. 


Har bayan sallar la'asar bata tashi ba, bayan nayi sallah na zauna naci abincin da Yaya ya kawo mana, na maida sauran na rufe dana koshi. Ina nan a zaune naji karan buga kofa, na tashi na bude. Ga mamakina Anty Sarah ce a tsaye da kwando a hannunta, na mata sannu tare da bata hanya ta shiga cikin dakin. Tace "har yanzu bata tashi ba?".

Nace "wallahi har yanzu, kila an hada mata da allurar barci ne". Ta gyada kai idanunta akan Janan din, "Allah ya bata lafiya". Nace "ameen".


Ta min nuni da kwandon data ajiye, tace "ga wannan idan ta tashi sai taci, ba yawa". 

Nace "Allah ya saka da alkhairi". Ta amsa tare da tashi ta fita, na bi bayanta na maida kofar dakin zan rufe. Su Raheemah suna falon a zaune har yanzu, ta wuce ta gabansu. Ina tunanin basu cika shiri dasu ba, kila ma hakan ce ta goge mu, ko kuwa wani abu daban? Naga kwana biyu kamar ta dan sassauto. 


Sai wajen karfe biyar sannan ta farka, jikinta ya dan yi karfi ba kamar dazu ba. Na taimaka mata zuwa bandaki tayi wanka da ruwa mai dumi. Bayan ta fito na zuba mata abinda Anty Sarah ta kawo, wani irin abu ne tayi da kifi ban ma san sunanshi ba, kamar ta soya kifin, kamar kuma dahuwar ruwa ce, ga veggies da abin yasha sai tashin kamshi yake yi kuwa. Na zuba mata ta samu ta dan ci, tayi sallar azuhur da la'asar da aka yi tana barci. Na ballo magungunanta da aka rubuto mata ta sha, ta zauna a gefen katifa ta dauki wayarta da tun dazu sai gajiya nayi na sakata a silent saboda yadda ake kira. 


Ummah ta fara kira, taje umara kamar shekaranjiya naji Janan tace ta tafi. Bayan sun gaisa ta tabbatar mata da lafiyarta lau yanzu, ta miko min wayar muka gaisa da ita. Bayan munyi sallama ne ta amshi wayar ta kira Ya Almu. Ni kuma na dauki wayata ina game. 


Bayan sallar magriba Yaya Bilal ya sake shigo mana da abinci, chips ne da sauce da gasasshiyar kaza, nan ma sake zama yayi ya zuba mata dogon sharhi akan aikin gida, ya fada ya kara maimaitawa, daga wannan rana kada ta kuskura ta sake cewa zata yi kowani irin aiki ne in dai na gidan ne. 


Ashe wai gyaran gida ne suke yi saboda matsowar azumi, wanda ake tsammanin ranar litinin ko talata za'a tashi dashi. Ita ta fara dauko maganar ayi aikin tun daga farko ranar Alhamis bayan ta koma gida, shine sun shiga can cikin gidan, wani daki da suka maida dakin tarkace kawai, zasu gyara shi da niyar da azumi za'a dinga taruwa acan ana sallar tarawihi, suna fara aikin suka fara zamewa daya bayan daya har suka barta, wannan kura data shaka ita ce fa ta tado mata asthma. Allah ne ya taimaka da asubahin washegarin yau, Yaya Bilal daya dawo jiya da dare, ya leka dakin kasancewar bai samu ya ganta ba daya dawo, shine fa ya sameta a cikin mawuyacin hali. Da Allah kadai yasan abinda zai faru. 


Bayan mun ci kaza da chips munyi nak, kwanciya muka yi tun wajen karfe taran dare don ba karamar gajiya muka yi ba daga ni har ita. 

Ta kalleni lokacin da nake ta faman buga keyboard din wayata ina turawa Muhammad sako, tun wayar da muka yi da safe bamu yi wata ba har yanzu, haka tun text din daya tura min lokacin da muna asibiti bai sake tura wani ba, nima ban sake tura mishi ba saboda ban samu kaina ba sai yanzu. Bayan na tura mishi ne, idanuna suka sauka akan conversation dina da muka sha yi da Umar, rabon da in ga text dinshi a wayata kusan sati biyu kenan, haka ma kira. Tun ni ina yi da tura text, har na gaji na hakura kawai na koma gefe ina jiran ya sake waiwayata. 


Janan ta dafa goshina, tace "ke ma fa kamar baki da lafiya, jikinki zafi sosai".

Na kai bayan hannu na ina dafa wuyana, "lafiya ta lau Jan, ina tunanin yanayin nan ne, ko kuma mura. Kin san yadda murata take".

Muna hira kadan-kadan da ita dai har barci ya kwashe mu. 



*



Washegari ma haka Anty Sarah ta kawo wa Janan abin kari, bayan fitarta muka koma gefe ni da Janan muna gulmar kirkin da tayi kwanannan.

"Allah da gaske dama can tana da kirkinta, kafin zuwan Anty Raheemah kenan. Tana zuwa kwata-kwata sai ta hau kulle kanta a gidanta, ina tunanin jinin su ne bai zo daya ba". Cewar Janan tana shan romon naman kan sa data kai mana. 


Ni kam na kasa cin komi, sai sandwich daya na samu naci wanda tayi filling da sauce din kwai da sardines na gwangwani, ga cucumber a ciki, shima rabi, sai shayin dana hado mana da nake ta kurba. Tashi nayi bakina salam babu dadi, ga wani shafal da nake jina kamar babu laka a jikina ko kuma idan aka hure ni zan fadi, gefen kaina bugawa yake yi tun karfinshi idan nayi dan motsi, jiya da zazzabi na kwana a jikina, ga wani jiri da nake ji idan na tashi, daurewa kawai nake yi muna hira da Janan, amma Allah kadai yasan yadda kaina yake sarawa. Ita kam jikinta da kwari tubarkallah, kamar ba ita bace tasha jinyar nan jiya ba. Da safe su Raheemah sun leko sun mata sannu da jiki suka kara gaba. Kamar ma unguwa muka fita, don mu kadai muka yini a gidan, sai bayan isha'i suka dawo. 


Janan ce ta takura akan sai mun fita bakin titi mun sayo tangerine da mango. 

Nace "wai ke ma ga Ahmad nan, ki tura shi mana?".

Tace "ke zaki fita kiyi gadin gidan ko? Yadda Yaya zai dawo ya tadda baya nan ya tsige ni da raina ko?".

Nace "to yanzu kina tunanin idan ya dawo yaga bamu nan, ba zai tsige ki da ran naki ba dai?".

Tayi dariya, "sis, ki taso kawai mu fita, babu abinda zai faru. Ni fa bana jin dadin jikina wallahi, ai nayi kokari, kusan awanni na arba'in da takwas fa ba tare dana taka waje ba!".


Na jefa mata harara, "da can kuma da kike fin sati ma ba tare da kin fita ba fa?".

Tace "wannan ai ya banbanta, don Allah taso mu tafi kada mu bata lokaci har Yaya ya dawo".


Duk da ban so ba, haka nan na tashi na bi bayanta muka fita. Har yanzu ina jin jikina ba daidai ba, duk da dai tunda nasha paracetamol da yammar nan, zazzabin ya sauka, amma har yanzu ina jin jirin kadan-kadan da kuma ciwon kai. 


Can bakin titi muka fita, muka yi siyo duk abubuwan da idanunmu suka dora ido a kansu. Niki-niki haka muka juya gida hannuwa cike da ledoji. A hankali muke tafe akan titin, yanayin unguwarsu kamar G.R.A haka take, da rana ma baka cika ganin mutane suna shawagi ba balle da dare. Yanzu ma sai jifa-jifa muke ganin mutane, sai kuwa ababen hawa da suke ta wucewa. Wasu na fita wasu na shiga.

 

Gab da zamu shiga gidan naji nayi turus, sakamakon wata mota dana hango can gaba kadan da gidan. Idan da ba don wata sticker dake bayan motar ba, an rubuta 'born to fight', da cewa zanyi ba ita bace. Sai dai wannan babu tantama motar Umar ce, amma me zai kawo shi nan yanzu? Janan tana tambayata lafiya? Amma hankalina baya wajenta, wayata nake kokarin cirowa. A tunanina kila ya kira ni ban ji kiran ba, yanzu haka ma kila ni yake jira ko wani abu. Amma babu kiran Umar a wayata babu alamunshi. 


Na kalli Janan ina nuna mata motar, da yake akwai hasken da kwayayen dake kofar gidajen unguwar suke badawa, take ta gane motar, tace "kai! Kamar motar Umar dinki fa!".

Babu ko tantama nace "motar shi ce, amma me yake yi anan? Ko kirana fa bai yi ba!".

Tace "ko dai bashi bane?". Da sauri na hau girgiza mata kai, gabadaya na rasa akan abinda ya kamata inyi tunani a lokacin. Haka kawai naji jikina ya dauki wata irin rawa, ba kuma zazzabin da nake ji bane ya haddasa ta ba. 


Ba tare da tunanin komi ba, naji na fara daga kafa ta zuwa wajen motar. Duk taku daya, rawar jikina karuwa take yi, haka bugun zuciyata yake ninkuwa. 


Ban san tunanin me nake yi ba dana tunkari motar gadan gadan ba, amma ban shiryawa ganin abinda idanu na suka gane min ba. Ban shirya ba!. 


Umar ne kamar yadda nayi zato, zaune a gaban motar, sai dai ba shi kadai bane kamar yadda nayi zato. Tare suke da ba wata ba illa Haleemo. A zaunen ma zama na rashin da'a, saboda kusancinsu kamar a kan cinyarshi take zaune saboda irin zaman da suka yi. Ba wannan kadai ba, daidai lokacin da wata mota ta danno cikin layin a sukwane, haskenta ya dallare gaban motar, daidai lokacin da bakinsu ya hade da kiss. Hannuwanshi na yawo a wuyanta da bayanta. 


Naji kamar an katse duk wata magudanar jini a jikina, ban san lokacin da kayan hannuna suka zube ba. Innalillahi, me idanuna suke gani ne haka??! Da sauri na kauda kaina don bazan iya kallon irin wannan badala dake afkuwa a gabana ba. 


Tunanin farko daya dirar min, shine in kwashe kayana da suka zube a kasa in wuce gida, tunda dai sam basu san da kalar wainar da muke soyawa ba, sai kuma naga inaa! Don haka kafin ma in sake tunanin yin wani abu, naji kafafuna sun daukeni zuwa wajen motar. Na tsaya a daidai wajen da direba yake zama na bubbuga. 


Sai da aka dauki lokaci kafin aka yi kasa da tinted glass din da aka saka aka rufe motar, Umar ya zuro kanshi waje. Yadda idanunshi suka waro cikin gigita yasa naji wata irin tsanar shi ta cika min rai, me yasa zai yi min haka?? 


Da sauri ya fito daga cikin motar yana wani kame-kame, "hh-hheyyy... Sweetie. M-me kike yi... anan?!", ya tambaya cikin rawar murya. 


Na daure, na cije, na tattaro duk wani kwarin gwiwa daya rage min, nace "oh, wai zamu wuce ne sai naga kamar motarka, nace bari in tabbatar. Ashe kai dinne. Mai kake yi anan? Nayi tunanin kana Kaduna??".


Ya fara shafa bayan wuyanshi yana wuri-wuri da ido, "wannan? Ai dazu na dawo, tunda na tafi ban dawo ba sai yau! Ai ayyuka ne suka yi yawa! Kusan satina daya ban daga wayata ba saboda aiki!! Yanzu.... Yanzu ma wani abokina ne anan unguwar nazo gani, ai ban ma gane layin gidan su kawarki bane saboda duhu. Me ma kike yi anan unguwar? Nayi zaton kina Shika??!".


Ji nayi na gama sauraren kame-kamen da yake yi, rainin wayon yayi yawa. Banyi wata-wata ba na daga hannu na watsa mishi tafi...











#F.W.A

[17/03 9:37 PM] Jiddah Lawal: 🌟 *⋆☆A ZATO NA...!☆⋆* 🌟



        *⋆©Jeedderh Lawals⋆*





                             *☆⋆10⋆☆*






A gabadayan tarihin rayuwata, ban taba, ko a cikin mafarki kuwa, tunanin akwai wata rana da zata zo da zan kwanta in kuma tashi da tunanin abu daya a cikin raina ba, musamman idan abinnan ya kasance d'a namiji. Amma yau sai gani na tashi cike da tunanin wannan bawan Allah da ko sunan shi ban sani ba. Har nayi wanka, na shirya, muka karya, muka dauki hanyar asibiti, tunaninshi ne a cikin raina. Daidai da sakan daya bai bar cikin raina ba. 

Muna kan hanya, text message dinshi ya shigo cikin wayata. Na zaro wayar daga cikin jaka na daga, kawai cewa yayi, 

*'salam, just wanted to say hi... Ban sani ba ko kinyi tunanina tunda kika tashi, ni dai nayi. Anyway, have a nice day!.'*

Ji na nayi kamar wadda aka wa kyautar kujerar makkah. Garin bai ma gama wayewa ba, amma wannnan text din kadai made my day already. 

Na shiga cikin contacts dina nayi saving number da, 'Mysterious'.  Wannnan a karan kanshi abin tambaya ne ga wadanda suka sanni farin sani, domin haka kawai bana saving lambar mutane a cikin wayata, musamman wanda na sani na rana daya kacal, abu ne mai matukar wahalar yarda a wajensu. 


Yau ma da wuri muka dawo gida. Yau gidan babu kowa, muka dauki makullin gidan a wajen da suka saba ajiyewa muka bude muka shiga. Bayan sallar la'asar muka shiga kicin ni da Jan, muna cikin girki sai ga Haleemo ta fado kicin din, bamu ma ji lokacin data shigo gidan ba. Ta mana sannu muka amsa, tace "don Allah wayar wa take da sauran canji a cikinku ta taimaka min inyi kira?".

Jan tace ta baro wayarta a daki, ni kuma da wayata take saman cupboard muna sauraren kida da ita, na dauka na bata. Tayi godiya ta amsa ta fita. 


Janan ta kalleni bayan fitarta, "da alama kuna shiri da Haleemon nan".

Nace "tafi sauran yan uwanta kirki da rashin rawar kai shi yasa".

"uhmmm, don dai kawai ba a gabanki take yin abubuwa bane, amma kada ki bari shiru-shirunta ya kwashe ki wallahi, duk ta fisu rashin mutunci".

Na kalli kofar da tabi ta fita cike da mamaki, "amma kuma yanayinta sam bai yi kama da irin nasu ba".


Tace "dama idan mutum bashi da mutunci, rubuta shi yake yi a goshi ne? Ai ba tambari gare su ba, lokacin da suka buga miki shi ne zaki ji kamar kiyi kuka". Na kyalkyale da dariya. 

Ta girgiza kai, "wato dariya ma na baki? Zaki yi bayani ne yarinya!".


Haleemo ta dawo kicin din, ta miko min wayar tana murmushi, "yauwa, nagode Na'ilah". Na jinjina mata kai ina dan murmushi kawai, na karbi wayar na maida na ajiye. 

Ta leka kanta cikin tukunyar da muke girki da ita, "sai kamshi mai dadi yake tashi, me kuke dafawa ne?".

Nace "shinkafa ce da miya". Tayi murmushi, "ki ce yau dadi zamu ci? Amma nasan sai zuwa dare don yanzu kaya zan dauka, wajen kamun bikin wata cousin dinmu zamu je".

Ni da Jan dai "humm!" kawai muka ce mata, ta fita daga kicin din. Bayan ta dauko kayan ma, sai data biya ta mana sallama sannan ta wuce. Mu dai muka samu muka gama girkin. Muka zuba musu a cikin manyan kuloli, mu kuma muka dauki namu muka wuce daki. 


Da dare Umar yazo, mun jima dashi a gefen gidan muna hira dashi, fir naki shiga motarshi. Ko yanzu ma hirar da muka yi dashi cikin dari-dari muka yi ta. Tun yana korafi har ya koma magiya, ya dawo ban hakuri. Nace mishi yayi hakuri, amma na kasa sakin jiki dashi, a haka dai muka yi sallama. 


                                  *



Ranar assabar yini muka yi a daki. Yaya ya dawo daga Abuja, amma da yake a gidan Anty Ameerah ya sauka, kawai dai ya biyo ne muka gaisa. Ina bandaki lokacin daya dawo a jiyan da yamma, har ya tafi bamu gaisa ba. Naji Jan tana cewa sai yau da yamma zai dawo nan. 


Tunda muka tashi wajen karfe goma na safe, brush kawai muka yi muka fita falo. Da alama mutanen gidan suna daki don babu kowa, muka shiga kicin da niyar dora abinda zamu karya dashi. Ga kaya nan baje a kicin din, da alamu anyi amfani da kayan ne amma ba'a wanke ba. Abinda suke mana kenan tunda nazo gidan, kodayake nafi kyautata zaton sun riga sun saba yin hakan ne tun ma kafin in zo gidan. Idan suka yi amfani da abu, anan zasu watsar dashi sai dai mu mu gyara. Hatta da su plates din da suka ci abinci, yawanci anan tsakiyar falo suke barinsu sai idan mun je gyara sannan zamu dauke shi. 


Yanzu ma tattara su kawai muka yi, bayan mun dama kunun tsamiya, Janan ta soya mana kosai muka shiga daki muka ci.

Muna cikin ci muka ji anyi knocking a kofar dakin, muka kalli juna ni da Jan, kafin ta tashi ta bude kofar. Ina ji ta fara cewa "Yaya ina wuni?", nayi sauri na lalubi hijabi na dora a saman kaina, nima na tashi lallaba na raba ta gefenta na durkusa nima na gaishe shi. Ya amsa hankalinshi akanta. 

Dadina da halin Yaya kenan, yana da kulawa, sai dai yana da kame kai matuka. Bai cika sakarwa Janan fuska ba, amma kuma ta acts dinshi kadai zaka san da cewa yana matukar son ta, kuma yana kulawa da ita matuka. 


Ya kara zuro kanshi cikin dakin yana shinshinawa, "meye haka kuka ci yake neman tado min yunwata?".

Janan tayi dariya, ni kuma na sunke kai a cikin hijabi ina dan murmushi. Tace "kosai ne muka yi, ko zubo maka zanyi?".

Idanunshi suka dan bude sosai, kamar alamun hope ko dai wani abu mai kama da haka, "kun girka da ni ne dama?".

Tace "mun dai yi da dan yawa ne saboda munyi tunanin zamu iya cinyewa saboda yunwa sai kuma muka yi saura."

Yayi yar dariya, "watarana zarinki zai janyo miki yin kibar da baki so. Ni dai tunda Allah ya taimakeni ya tsaga da rabona, ki zubo ki kawo min ina falo. Dama ban karya ba wallahi.... Mutanen gidan basu tashi bane?," ya tambaya yana juyawa yana kallon falon kamar mai duba wani abu. 

Janan tace "bari in kawo maka kunun", ba tare data amsa mishi tambayarshi ta karshe ba. Ya juya ya fita yayin da ta bi bayanshi ta dawo da plate da kofi a hannunta, ta zuba mishi ta cicciba ta fita. Ina jiyo sautin tashin muryarsu, suna hira, don haka na janyo wayata na jingina da bango na tsokano My mysterious Man, kamar yadda sunan nashi ya koma yanzu cikin wayata. 


Cikin yan kwanakin nan, mun kulla wata irin abota mai karfi dashi. Bai taba kirana a waya ba, kullum daga text sai ta chats kawai muke hira dashi, duk da cewa Allah kadai yasan yadda nake iya cijewa rashin jin muryarshi da ban taba yi ba, ban taba kokarin gwada kiranshi ba. Amma ina kwadaituwa da hakan. Ina yawan tunano yadda muryarshi zata kasance, yadda shi a karan kanshi zai kasance in person. I really want to see him. Amma dai na daure, ina jira in ga iya gudun ruwanshi. 


Har Janan ta dawo, ina kan waya ina chatting dina. Ina jinta tana korafin watarana sai ta dauke wayata, ko kuma ta goge whatsapp da duk chats dina, sai dai kasancewar hankalina yayi nisa ko jin abinda take cewa bana yi sosai. Sai da aka kira sallah muka hakura. 


Bayan azuhur, zaune muke a tsakiyar dakin, nayi matashin kai da cinyar Jan din tana warware min kalbar da tayi min. Saboda tsananin santsin kaina da tsayi, ban cika yin kitso ba. Idan ma nayi, baya daukar kwana uku yake warwarewa da kanshi. Jan take zaunawa ta min kalba, watarana sai ta sanya rubber bands kanana a karshen kowane kitso sannan yake dan yin kwanaki biyar zuwa sati. Shi yasa ban cika yin kitson bama sam. 


Littafin 'Always a Fighter' nake karanta mana a fili, lokaci zuwa lokaci zan saurara mu dan dara idan na karanta abin dariya, ko kuma mu dan tattauna akan wani abu daya ratso. 

Muna cikin haka sai b'ammm!! Karan turo kofa kamar za'a balleta, gabadayanmu sai da muka zabura muka tashi zaune a firgice. 


Mimah ta afko dakin a sukwane, kai tsaye bayan labule ta shige ta kame kamar wadda mutuwarta ta biyota. Cikin mamaki nace "Mimah lafiya? Ke da wa?".

Kafin ta amsa, an sake turo kofar dakin dai an shigo, muka maida hankalinmu ga kofar gabadayanmu. Anty Sarah ta fado dakin, tana karewa dakin kallo, da alamu Mimah ta biyo. 

Sai data karewa dakin kallo tsaf, sannan ta jiyo tana amsa mana gaisuwar da muke mata, ta kara da, "Mimah bata shigo nan bane?".


Muka kalli juna ni da Janan, ni ce na fara cewa "a'ah, bamu ganta ba". Daga haka ta juya ta bar dakin. Tana bada baya muka hade kawuna ni da Janan muka kwashe da dariya, tace "baki da kirki wallahi, mutum da diyarshi?".

Nayi dariya nace "kika san ko laifi tayi zata bata kashi? Sannan yarinyar nan tana bukatar fresh air da hasken rana, na tabbata rabonta da waje tunda aka dawo da ita daga makaranta jiya", na maida hankalina wajen inda Mimah ta boye, "Mimah fito, ta tafi".


Ba musu ta fito daga bayan labulen, da gudunta tazo ta haye kan cinyata, na shafa kanta ina murmushi, "meye na gudowa daga gida, laifi kika wa Mommy hala?".

Ta girgiza kai tana dariya, "naa, naki zuwa ta min wanka ne wai zamu raka daddy unguwa, ni kuma Uncle nake so, yace zai kaini wajen granny".

Muka yi dariyar yadda take maganar ni da Jan, na kamo kumatunta ina ja cikin wasa, "uhhhh Mimah, soooo adorable. Amma yi hakuri ki tafi kafin Mommy tayi fushi, ki bari idan kun dawo daga unguwar, sai Uncle din yazo ya kai ki".


Yadda ta dago da sauri, idanuwanta manya, farare tas cike da murna yasa naji zuciyata tayi rashin dadi akan turbar da zan dorata tunda nasan ba lallai hakan ta faru ba, tace "da gaske?".

Na daga mata kai da sauri, "hmm, ni da Janan ma zamu biyo ku muje tare". Tayi tsalle daga jikina ta dire cike da murna, "yay!!".

Gabadaya ni da Janan muka saki dariya, nace "to maza ki tafi kafin ta sake dawowa nan, ki kawo mana tsaraba fa". Ta fita daga dakin da gudu, ni da Janan muka bita da kallo muna murmushi har ta fita, sannan muka cigaba da tsifar da muke yi. 



*


Washegari tun da safe, ina jin ko karfe tara bata yi ba, muna kwance muna barcinmu, muka jiyo ana ihun murna daga falo, hakan ya tashe mu babu shiri duk muka tashi zaune muna sosa idanu. 

Su Haleemo ne suke ihun 'oyoyo, Mommynmu!', a raina na girgiza kai cike da mamaki. Zuwan suruka gidan surukai tun da safiyar Allah Ta'ala? Ban taba jin haka ba. 

Janan ta fara shiga ta wanke baki da fuskarta ta fito, nima na bi bayanta. Bayan mun dan fito more presentable, muka fita falon. Babu kowa, amma muna jin tashin hayaniyarsu daga can dakin Raheemah da yake kusa dana Yaya. 

Janan ta ja ni muka leka muka gaidata. Daga ganinta kasan kaga mahaifiyarsu, saboda kama da suke yi da ita gabadayansu, kamar tayi kaki ta tofar. Kallo daya zaka mata kasan cewa ka ga wayayyiyar mace, wadda duniya ta bude mata ido, wayewar kan har tayi yawa. Tun daga kan daurin dankwalin da tayi na yan duniya, da shigar da tayi, hakan yasa na daina mamakin irin shigar dasu Salama suke yi idan zasu fita, daga gani babu tambaya kasan gani suka yi ana yi. Duk da kasancewarta fara, har ma da 'ya'yan nata, amma daga ganin farinta kasan cewa an kara dana kanti. 

Ta amsa mana gaisuwarmu tana yatsina kamar taga kashi, tuni naji matar ta fita daga raina. Tun ma kafin a sallamemu, muka sallami kanmu don bamu ga fuskar zama ba a wajen. Muka dafa abinda zamu dafa muka koma daki abinmu. 


Yinin ranar nan cur, haka suka wuni a gidannan suna hayaniya da iface-iface kamar kananun yara. Da rana suka zage suka shiga kicin, kada ku sha mamaki idan kuka ji nace muku har uwar, suka dafa abinci, aka soya nama, su kaji, drinks. Muna daki aka kira mu aka ce muje mu ci abinci, muka fita. Ganinsu gabadaya a zaune suna cin abincin yasa muma muka dosana muka zauna, muka zuba namu muna ci, hankalinmu yana kan talabijin da take ta faman aiki. 


Mu muka tattara kan kayan muka je muka wanke, suna rarrashe a tsakiyar carpet din dakin suna hira. Ba wai kuma normal hira ba, a'ah, hira ta gulma da abubuwan da basu dace ba. Su ambaci wannan matar, su kwashe mata albarka ita da iyalanta, su kira waccan, itama dai su mata nasu kalar yankar kaunar. 

Bayan la'asar aka sayo musu tsire suka baje a tsakiyar falo suna ci, bayan nan suka kure gidan da kidan Ladi mai Kidan Kwarya, suka sha casun su kamar su kadai ne a duniyar. 


Tunda garin ya waye bamu ga giccin Yaya a gidan ba, amma naji dadin haka. I mean, ta yaya zai kalli surukar shi tana irin wadannan abubuwan? Bana tunanin zai kara kallonta da mutunci. Sai dai again, ban sani ko hakan ta saba faruwa dama can ba. 


Sai yamma likis sannan ta fito da shirin tafiya, dan siririn gyalenta a kafada kamar wata budurwa. Lokacin muna kicin muna dafa abincin dare, suka shigo kicin din. Da yake kicin dinsu hade yake da store, suka shige ciki. Babu kunya babu tsoron Allah suka dinga jidar mata kaya, kifin gwangwani, naman gwangwani, madarar gwangwani, kai tulin kaya kamar wani provision store ne suka shiga. Sai da suka cika mata leda shake da kaya, sannan ta bar gidan. 

Kai kawai nake girgizawa, ina gyadawa cike da tsananin mamaki daya daure min jijiyoyin da suke sarrafa magana a jikina. Nayi tur da wannan rayuwa, ko wa ya fada musu rayuwar auren hauka ce, kuma abin wasa ce? Da har uwa zata dinga zuwa gidan diyarta, tayi bushashar da taga dama, ta kwashi kaya ba tare da izinin mai shi ba ta kara gaba kamar wani abin wasa? Ita daya kamata ta musu gyara, idan taga sun dauko hanya irin wannan ta tsawatar musu, amma ita ce take dora su akan wannan hanyar? Lallai suna bukatar gyara kwarai a cikin lamarinsu. 










#F.W.A

[17/03 9:37 PM] Jiddah Lawal: 🌟 *⋆☆A ZATO NA...!☆⋆* 🌟



        *⋆©Jeedderh Lawals⋆*





                             *☆⋆11⋆☆*





Kafin yinin ranar Lahdin nan ya kare, gabadaya naji na gama takura da zama a gidan. Na riga na saba da hayaniyar hostel, can hayaniya ce mai cike da nishadi, ko ta tsakanin roommates, classmates, ko abokai. Na riga na saba da rashin shirun can, duk lokacin da naga damar fita, zan dauki hijabi ne in fita kawai, ba kamar gidan Yaya ba. Nan da kofar gida sai ka nemi izini kamar wata matar aure, hayaniya kuma daga ta zage-zage sai ta gulmace-gulmace, don haka ji na nake yi kamar wata fursuna. 


Zuwa ranar laraba da Baba ya turo min kudin registration dina, ji na dinga yi kamar wadda take yawo a sararin samaniya don murna. Dungurungum na ki shiga aji na tafi banki na biya kudin makaranta. Aka bani rasiti na tafi ofishin hall admin dake cikin hostel din yanmata na asibitin koyarwa na Shika na kai mata. Bayan ta dudduba files da sauransu dai, tayi assuring dina zuwa ranar Juma'ah zasu bani dakin saboda sai sun bincika wanda bai cika ba. Nayi mata godiya tare da mata sallama, aji daya na samu ranar, daga haka muka wuce gida. 


Washegari ranar Alhamis data kasance ranar public holiday, bamu tashi daga barci da wuri ba, muna ta warware gajiyar da muka kwasa cikin wannan satin don lectures dinmu sun fara yin zafi yanzu. 

Can da rana, Janan ta fita zata raka wata kawarta da take can cikin unguwar bakin titi. Ina zaune a falo, su Haleemo, Raheemah da Adi na zaune suma suna kallo, aikin da suka saba yi kenan. Yayin da nake wasa da wayata. Babu wanda yake magana a cikinmu sai su da suke hirarsu jifa-jifa. Abinda yake takura ni kenan. Na tsani zama kusa da mutanen da ba zamu yi hira dasu ba, meye amfanin zama a waje dayan to idan ba za ayi hira ba?.


Aka fara kwada sallama daga can waje, duk muka kalli kofar muna jiran a shigo, duk cikinsu babu wanda yayi kokarin tashi. Na mike na fita wajen, ina bude kofar na ci karo da Ummah tsaye. Nayi tsalle na fada jikinta, tayi yar dariyarta mai cike da haiba ta dora hannunta a bayana tana shafawa. 

Cikin tsananin murnar ganinta nake gaidata, ta amsa fuskarta na bayyana murmushi sosai. Tace "Na'ilah, idonki kenan ko?".

Na sadda kaina kasa a kunyace, rabon da inje Kaduna har na manta, sai dai a waya kawai muke gaisawa, to yanzun ma a wayar mun kwana biyu, nace "Ummah kiyi hakuri don Allah, kin san al'amuran makaranta ne suka yi yawa wallahi".

Tace "ba wani nan, ke dai kawai kice zumuncinki yayi karanci ne!".

Na fara girgiza mata kai da sauri, "Allah da gaske fa Umma...", sai lokacin na tuna a kofar falo fa muke tsaye. Da sauri na matsa gefe daga cikin falon ina cewa, "Ummah shigo don Allah".


Ta shigo ciki tare da cire takalminta, fararen kafafunta da suka sha lalle jawur gwanin sha'awa suka bayyana. Muna shirin wucewa, Janan ta fado falon. Tana ganin wadda take gabanta ta tsaya cak, "Ummah na?". Sai kuma tayi tsalle ta dafe ta, na matsa gefe ina kallonsu cikin burgewa. 

Hannunta ta kama ta fara ja kamar wata karamar yarinya, ni kuma na bi bayansu. A falo babu kowa haka muka tarar dashi kamar ba yanzu-yanzu na bar mutane suna kallo ba. Ga kuma talabijin din tana aikin yi. Gabadayanmu sai da muka dan dakata, sannan Janan ta wa Ummah jagora zuwa dakinta. Ummah tace "ni fa ba zama zanyi ba, yanzun nan zan koma Kaduna direba yana jirana a waje".

Ta turo baki cikin shagwaba, "amma dai kin tsaya ko ruwa ne ki sha ko? Sannan ku gaisa da mutanen gidan".

Ummah tace "suna nan ne? Naji gidan shiru".

Tace "ina zasu je? Yanzun nan da suke kallo anan falo fa, kila sun gaji da zaman ne suka koma daki". Ummah ta lalubi kujerar roba daya da take dakin ta zauna akai, Janan ta fita da sauri zata dauko mata ruwa. Gefen katifa na zauna, Ummah tana tambayata karatu da kuma yanayin damina daya fara shigowa, nace lafiya lau. 

Babu jimawa Janan ta dawo dakin hannunta dauke da gorar ruwa mai sanyi, Ummah tana sha ko rabi bata yi ba ta mike tsaye, muma duk muka mike. 


Janan tana turo baki ta kamo hannunta ta rike, "yanzu Ummah na maimakon ki jira sai yamma tayi sannan ki tafi?".

Umma tayi dariya tana rungumota jikinta, "Janan kenan, nasan idan kika ji na shigo Zaria ban leko nan ba ba zaki taba bari in samu lafiya bane shi yasa yanzun ma nazo".

Ta kara turo baki, "ni ai dama nasan kin daina so na yanzu shi yasa!".

Ni da Ummah duk muka dara, tace "yanzu idan na daina sonki wa zan so Janan??". Bata amsa ba sai baki data kara turowa. 


A kofar dakin Raheemah muka tsaya, Janan ta tura kofar, amma gam, a kulle. Tasa hannu ta dan kwankwasa, nan ma shiru, babu ko alamun motsin mutane. Da ace ba kofar fita daya bace a gidan, duk inda zaka je dole sai kabi ta babbar kofar falo, da sai ince ko ta wata hanyar suka bi suka fita daga gidan. Amma suna zaune fa a falon tazo, daga zuwa bude mata kofa ta shigo har sun bace kamar masu tafiya akan iska? Shin hakan yana nufin da gangan suka buya kenan??.


Ummah ta kallemu tana dan murmushinta na manya, duk da haka zaka karanci damuwa da rashin jin dadi a cikin idanunta. Tace "da alamu ko barci suke yi, kada ku tashe su. Bari kawai in tafi, watarana idan na dawo in Allah ya yarda sai mu gaisa din".

Janan ta daga baki zata yi magana, nayi saurin girgiza mata kai alamun kada tace komi, nasan ce mata zata yi bai ci ace sunyi barci ba yanzu, hakan kuma shi zai ba Ummah damar sanin da gangan suka shige daki suka rufe mata kofa duk da dai ina zargin da kyar idan bata harbo jirgin ba. Janan ta kama bakinta ta datse, muka saka Ummah a tsakiya muka fita. 


Sashen Yaya Jameel ta tsaya, nan kuma sai da muka kwashe kwararan mintuna uku muna buga kofa, har mun fara tunanin kila basa gidan ko kuma barcin rana suke yi, mun fara tunanin mu juya kawai, sannan muka ji alamun ana taba kofar alamun za'a bude. Anty Sarah ta bude kofar tare da dan fitowa waje, alamun bata da niyar barin wanda yake buga mata kofar ya shiga ciki. 

Sai dai tana ganin Ummah, ta fara fara'a da nan-nan da ita, "su Ummah ne? Ku shigo daga ciki mana! Sannu da zuwa Ummah, sannu, ya hanya?...", ta fara jera mata sannu har ta zauna akan kujera. Ko zama bata yi ba ta fada kicin dinsu da sauri. 

Ni da Janan kam falon kawai muke bi da kallo, da alama ta canza kayan daki akan wadanda muka sani da. Wannan wasu irin saitin royal kujeru ne purple da gold, gaskiya sunyi kyau ba karya. Ga kamshi da sanyi mai ni'ima da yake tashi, irin mai warware gajiyar nan. Dama can Anty Sarah ba daga nan ba indai ta fannin tsabta ne, babu na biyunta. 


Ta fito daga kicin din hannu niki-niki da tarin kayan motsa baki akan wani katon tray, ta ajiye a gaban Ummah ta hau zuzzuba mata. Sai bayan data zuba mata komi sannan ta zauna a kasa a gefenta tana gaidata cike da girmamawa, Ummahn ta amsa. 

Tace "ai kuwa yanzu suka fita shi da Mimah".

Ummah tace "ehh, na hadu dasu a babban gida (main house dinsu), Hajiya babba ce bata ji dadi ba kwana biyu dama shine nazo na dubata kuma sai nace bari in biyo a gaisa, kwana biyu".

Anty Sarah ta sadda kanta kasa tana dan murmushi, "wallahi kuwa Ummah, muna ta cewa zamu leka ku, bamu samu dama bane". Daga ji kasan ta fada ne kawai, amma duk da haka dai tafi wadda ta rufe kofar dakinta ma gabadaya. 


Ummah tace "dama haka ne, bari mu wuce mu". Tace "Ummahn tun yanzu? Ba zaki bari mu sauke abinci ba, yanzu aka dora".

Ummah tace "Allah ya amfana, amma nagode". Ta mike, da sauri Anty Sarah ta koma kicin din, sai gata ta dawo da leda a hannunta, ta juye duk snacks din data kai a ciki, ta mikawa Janan. Daga nan muka mata sallama, ta biyo bayanmu har bakin kofa, ta wa Ummah Allah ya tsare hanya, ta maida kofarta ta gamtse. Ni da Janan duk kai muka jinjina kawai, muka takewa Ummah sawu har inda direban daya kawota yake jiranta. 

Janan ta bude mata gidan baya ta shiga, ta dora mata ledar wajen Anty Sarah akan cinyarta. 


Kafin direba ya ja motar su tafi ta kalleni, "yata Na'ilah, yakamata ki daure watarana ki zo mana weekend mana?".

Na yi murmushi a dan kunyace, "in Allah ya yarda Ummah, zamu zo".

Ta gyada kai, "to madallah, a maida hankali kan karatu dai. Allah yayi muku albarka". Duk muka amsa da 'ameen'. Direban yaja suka tafi. Sai da Ahmad maigadi ya maida kofar ya rufe bayan sun fita daga gidan sannan muka juya. Har muka shiga cikin falon babu wanda ya furta uffan a cikinmu. 


Muna shiga falon muka ci karo da Adi da Raheemah a zaune abinsu, suna kallo. Wato da gaske dai suna sane suka gudu daki? Haushin abin ya cika ni, naji kamar in rufe su da duka su duka. Duk da ba ni suka wa abin ba, amma zafin da naji sai naji kamar ni ce naje gidan Yaya, matarshi ta rufe kofar dakinta don kada mu gaisa. 

Duk da yadda naso danne zuciyata, hakan bai hana tsakin da nake ta dannewa ya fito ba. Daidai lokacin da zamu wuce su. 


Adi ta wani tashi a fusace ta rike kugu, "ke malama waye kike ja wa tsaki a cikin dakin nan? Kin ga sa'an ki anan?".

Na tafi zan zagayeta ni da Janan, tayi saurin kamo wuyan hijabina ta janyo ni, na dawo muna fuskantar juna ni da ita ido da ido, tayi kasa-kasa da nata idanun cikin masifa, "wato yarinyar nan naga alamun wuyanki yayi kauri da yawa irin zama a gidan mutane yayi miki dadin nan. Ke har kin isa in dinga miki magana ki maida ni yar iska?".


Na kalli tsakiyar idanunta, ina kara nuna mata nima ba kirkin nan gare ni ba fa, nace "ai banyi zaton dani kike ba ganin cewa ni din ba yar iska bace. Maganar kiba kuwa da kike cewa nayi, gwanda ni ina girmama wadanda nayi kibar ta dalilinsu, ke kuma me kike yi?".

Ta fara hura hanci, dama gasu tubarkallah kamar kofofin wando, tana daga murya, "kan abu ta kazar abun nan!! (ta kawo zagi ta narka). Lallai yarinya kin daukowa kanki ruwan dafa kanki!. Ni zaki daga wannan tsantsaman bakin naki ki zaga kamar wata sa'ar wasanki? To wallahi na rantse da Allah yau ko ni ko ke a gidannan, sai naga wanda ya daure miki gindi!!".


Wani abin ban dariya shine, gabadayanta bata wuce sa'ar mu ba, abinda nafi tunani kenan tunda ko a tsayi ma na fita. Na kyalkyale da dariya, ina watsa mata wani kallon kaskanci tun daga sama har kasa, duk iskancinta sai data rusuna. Ina shirin maida mata amsa daidai da ita, Janan tayi saurin kama hannuna taja ni. 

Adi ta fara ihu, "idan ba tsoro ba ki tsaya mana ki gani?! Wallahi da sai na nada miki na jaki, yadda ko uwar data kawo ki duniya ba zata gane ki ba!!".


Janan dai ta samu ta ja ni daki, ta maida kofar dakin ta rufe, amma duk da haka bamu fasa jiyo zage-zagen da Adi take yi ba, har Salama data fito itama ta sanya baki itama tana nata kalar zagin da gori. Wai anzo musu gida an zaune, an ki tafiya saboda sanyin AC da naman kaza, ni abin ya ma so ya bani dariya. 

Na tsaya a tsakiyar dakin ina ajiye ajiyar zuciya daya bayan daya da sauri-sauri. Ta kalleni, "haba Na'ilah! Sau nawa nake fada miki ki daina biyewa wadannan mutanen? Kin san cewa ba ajinki bane ki zauna kuna sa'insa dasu ba ko?".

Na harareta cike da fushi, "wai sai ki dinga magana kamar baki wajen lokacin da take sauke min kwandon zagi da dibar albarka!".


Tace "ko ma menene dai, rashin tankawar yafi tankawar dai. Meye alfanun musayar kalamai, meye a cikin hakan?".

Na watsa hannuwa sama frustrated, "koma dai menene. Allah ne ya rufa mata asiri bata kai ga daga hannunta a kaina ba, da wallahi sai na baje shegiya yau a gidannan!!".

Janan ta girgiza kai kawai, ta fada bandaki tana furta "Allah ya shiryeki ke kam!". Nace "ameen", cike da izgilanci. 


Sai dana huce sannan na zauna a gefen katifa. Sakon text din mysterious daya shigo wayata a lokacin ne ya kara sauko da zuciyata kasa sosai. Na hau karanta sakon ina kara maimaitawa kamar mai harda, daga karshen sakon nashi ya rubuta *'talk to you soon babe!',*

Shin hakan yana nufin mun kusa yin waya dashi? Nayi tsalle na sake dira akan katifa ina dan ihun murna, Janan da fitowarta daga bandaki kenan ta kalleni baki a dage, "ke kuma lafiyarki lau kuwa? Yanzu-yanzu kina fushi, yanzu kuma kina ihun murna again?".

Na harareta cike da wasa, fuskata na dauke da murmushi. 



Washegari Juma'ah, muka shiga asibiti. Muna fita ajin karfe goma na yiwa ofishin hall admin tsinke. Nan ta bani lambar daki da teller, sai dana fara zuwa bank na biya kudin sannan na sake dawowa wajenta nayi clearance. Dakin mu uku ne, ka'ida mutane biyu ne a kowane daki, amma kasancewar wannan karon muna da yawa shi yasa suka maida shi uku per room. Ni duk bayanan da take yi ba jinta nake yi ba, ban damu ko mu hudu ko biyar zamu zauna ba, bukatata kawai in samu dakin. 

Tana miko min makullin dakin, na karba na mata godiya na bar ofis din. 

Dakin na fara zuwa na gani, wadanda suke zaune a dakin basa nan lokacin. Na sanya key na bude dakin, na kare mishi kallo sannan na maida dakin na rufe na koma class. 


Lokacin period ta biyu ya ma kusa cika, don haka na samu wasu seats da aka tanada a gaban classes na zauna ina jiran su fito. Kafin su fito na ciro wayata na turawa Yaya text din abinda ya faru. Babu jimawa ya turo min da sakon taya murna da tambayar yaushe zan koma cikin hostel din gabadaya? Nace mishi sai ranar Lahdi, nasan duk abinda zanyi Janan ba zata bari in koma gobe asabar ba. 

Ina nan har suka fito, na tari Janan a hanya muka dauki hanyar barin asibitin kasancewar mun gama da ranar. A hanyar nake fada mata yadda muka yi da hall admin da kuma ranar da zan koma hostel din. Daga ganin yadda ta turo baki nasan bata yi na'am da maganar ba, don haka na canza maganar kawai zuwa wata. 


Yau ma kamar yawancin ranaku, gidan babu kowa muka same shi. Muka tura kofar dakin Janan muka shiga, kayan jikinmu muka fara ragewa muka dauro alwala muka zo muka tada sallah. 


Da yamma wajen karfe hudu da rabi muna tsakiyar falo a kwance muna kallon 'Baaghi' a tashar Zee World. Meat pie din da Anty Sarah ta miko mana ne daga dawowarmu muke ci da lemun fanta na pineapple a kusa damu. 

Gardama muke akan tsakanin jarumi Tiger Shroff da Hrithik Roshan wa yafi wani iya rawa?.


"ina fada miki Hrithik shine oga, ni gani nake duk duniya babu kamar shi ma. Kin san dai idan fannin rawa ne, babu wanda zai iya gwada mishi ko wanene kuwa, kada ma ayi zancen physique, halitta, kyawu, and his eyes! Ya Allah, how I love his eyes!!". Na fada dreamily ina kara zooming hoton shi dake cikin wayata ina kara nuna mata idanunshi da suka fito sosai a daukar da aka mishi. 


Janan ta kada idanu sama, "nasan da haka, amma ki duba, Hrithik ya fara tsufa yanzu, Tiger shine jarumi mai tasowa yanzu, sannan idan halitta ce, shima fa Tiger ba baya bane, ga iya lankwasa jiki da acting".


Na mike zaune sosai, sautin muryata ya fara yin sama, "ni fa komi zaki ce, babu abinda zai canza min tunanina, Hrithik ne nawa. Sannan wa yace miki Hrithik ya tsufa? As in kin kuwa ga yadda yarintar shi take kara fitowa yanzu?".

Ta daga baki kenan zata musa, sai ga sautin, "idan kun gama musun naku, zaku iya taimaka min da wadannan kayan?".


Da sauri muka daga kai zuwa inda muka ji sautin maganar. Yaya Bilal ne tsaye a tsakiyar falon ya nade hannu a kirji. Sanye yake da suits ash color, ya sanya tie baki mai ratsin ash color akan white linen shirt din daya sa a kasan suit din. Cikin yan sakannin dana yi ina kare mishi kallo, naji ina raya 'wannan shine ainihin misalin wanda yarintar shi take kara fita kullum', a cikin zuciyata. 

Da sauri duk muka tashi muna mishi sannu da zuwa. Ya amsa mana yana dan murmushi, "wato maimakon ku zauna kuna debate ko quiz akan karatu, sai ku zauna kuna gardama akan mazajen mutane ko? In anyi magana kuma sai ku ce duk duniya kun fi kowa yin karatu ko?".


Janan tace "wallahi Yaya ba haka bane, yanzun ma hira ce kawai, arashi ne aka yi kai kuma kazo a daidai lokacin".

Yace "whatever, kuzo ku taya ni dauko kaya a waje". Ya juya ya fita, muma muka bi bayanshi. Doguwar riga baka kirar kasar Saudiya ce a jikina, dama gyalenta yana kan kujera don haka na dauke shi na dora shi a saman kaina. 

Kayane zube a kofar falon, kayan miya ne, vegetables, su doya da irish potato. Ahmad yake ta daukosu daga cikin mota yana ajiyewa a kofar falo, bakin kofar falon nan ne iyakar da Yaya ya musu. Ba'a barinsu su wuce nan. 

Muka fara daukar kayan zuwa kicin sai da muka gama gabadaya. Yaya ya zauna akan kujera a falo yana cire takalmin kafarshi, Na dauko ruwa mai dan sanyi a cikin firjin na dora akan karamin tray na roba da cup, na kai gabanshi na ajiye. 

Janan ce ta tsiyaya ruwan ta mika mishi ya karba yana furta "thank you".


Sai daya kusa shanye ruwan gorar gabadaya, ya ajiye kofin ya koma jikin kujerar ya jingina. Ya cewa Janan "gabadaya kayan can ku raba su uku, kashi daya ku mika gidan Jameel, dayan ku zuba su a cikin wani abun za'a kaiwa Ameerah, sauran ku ajiye su na nan ne". Muka ce "to".

Yace "ina Raheemah ne?", muka kalli juna ni da Janan, itace tace "bata nan!".

Ya karkata kanshi gefe daya kamar cikin mamaki, yace "ina taje?". A lokaci daya muka ce "bamu sani ba!".

Yayi shiru kamar cikin tunani kafin ya girgiza kanshi a hankali, ya tashi tsaye, "shikenan, kuje". Muka wuce kicin abinmu. 


Muna gama aikin daya sanya mu, muka dora girkin dare. Sai gab da magriba sannan suka dawo gidan. Raheemah ce ta leko kicin din, muka mata sannu da zuwa, ko amsawa bata yi ba ta fara jero mana tambayar "yaushe baby ya dawo? Ya tambayi inda nake?".

Janan ce ta amsa mata, ni kam juyawa nayi ina juya miyar da muke yi, tace "tun dazu dai, kuma ya tambayeki muka ce kin fita".


Taja wani dan siririn tsaki ta juya ta fita, muna jiyota ita da Adi a falo tana tambayarta me zata ce mishi idan ya tambayeta inda taje? Adin tana cewa "meye na wani rikicewa don ya dawo baki nan? Kawai ki fuske ki ce mishi wajen Momcy kika je mana!".

Raheemah din tayi ajiyar zuciya, "baki san abinda muke ciki bane kwanannan, a saman ruwa muke dashi wallahi!".

Adin taja tsaki tana cewa "sai kiyi kuma, na tabbata ko tambayarki ma ba zai yi ba". Daga haka suka shige daki. 



*



Washegari na hade kan kayana tsaf waje guda, nayi wanki da guga da sauransu. Ranar Lahdi Yaya ya bada mota da yamma, Is'haq direban gidan wanda yake musu aikace-aikace ya kaimu hostel ni da Janan. Sai ranar muka hadu da roommates dina, daya musulma ce yaren Ibira, sunanta Murjanatu, dayar kuma Esther Christian ce. Janan ta taya ni hade kan kayana waje guda muka shirya su, daga nan ta min sallama ta tafi. Na rakata har waje ta hau bus ta tafi, sannan nima na juya na koma hostel. 









#F.W.A

[17/03 9:38 PM] Jiddah Lawal: 🌟 *⋆☆A ZATO NA...!☆⋆* 🌟



        *⋆©Jeedderh Lawals⋆*





                             *☆⋆12⋆☆*



 



"Ok, spill the beans, me yake faruwa dake ne?".

Janan ta tambayeni. Fitowarmu daga labour ward kenan da yammacin ranar Laraba, mun tsaya a wani karamin gidan cin abinci dake nan mini market din asibitin. Na fasa lemun Dudu na jefa abin zuka a ciki ina kallonta cike da alamun tambaya, "ban gane ba, me yake faruwa dani?".

Tace "na fahimci tun shekaranjiya kamar jikinki a sanyaye yake, wani lokacin ana miki magana amma ba kya ji, ko kinji sai in ga kamar ba kya wajen saboda kinyi nisa a cikin tunani. Wani abu yana damunki ne? Ko kuma baki da lafiya ne? Kin gaji da zaman hostel dinne?".


Nayi murmushi jin tambayarta ta karshe, na girgiza mata kai, "ko daya, kawai dai...", ta dago kanta da sauri tana kallona cikin sauraren jin mai zan ce. 

Na kawo ajiyar zuciya na sauke tare da girgiza kai, "na kasa fahimta ne ni kaina wallahi, kwana biyun nan sai in ga kamar Umar yana min kauce-kauce, amma ban tabbatar ba".

Ta kalleni a nutse bayan ta taune egg roll din data kai baki ta hadiye, ta kora da lemun la Casera. Tace "me yasa kika ce haka? Ko kuma ince me kika gani?".


Nace "na farko kusan sati daya kenan rabon da in kira Umar ya daga, daga farko ya fara biyo baya, ya cikani da maganganu marasa kan gado akan wai aiki ne yayi yawa, to yanzu yau kwana uku kenan rabon daya daga kirana ko kuma ya kirani ma. Sannan baya maido min da replying din message idan na mishi. Ke duk chats dinshi babu inda ban bishi na mishi magana ba, amma a banza, na fara damuwa".

Tace "haba, kada ki wahalar da kanki a banza mana, kamar yadda yace, zata iya yiwuwa aiki ne ya sako shi a gaba!".

Nace "shine kuma zai kasa daga wayata balle messages dina? Gaskiya sai dai wani abu daban, amma ba wannan ba. Ko lokacin da suka yi posting dinsu, abubuwa ai sun fi haka tsanani, amma a hakan yake samun lokaci ya amsa kirana har ma yazo ya ganni, balle yanzu".

Ta gyada kai, "haka ne kuma. Amma ki kara bashi lokaci dai, baki san abinda yake faruwa dashi ba, zata iya yiwuwa wani abun ne daban".

"to shikenan!". Na fada ina karasa juye sauran lemun daya rage a bakina, na jefa robar cikin kwandon ajiye shara na kalli Jan data gama jefa nata itama, nace "muje muyi sallah a hostel ko? Karfe hudu yanzu zata yi, kuma kinsan hudu da rabi ya kamata mu koma".


Duk muka mike muna daukar jikkunanmu, muka dauki hanyar hostel. Hostel dinsu yana da nisa da ainihin cikin asibitin, tafiyar kusan mintuna goma sha biyar ce. Muna isa alwala kawai muka yi, muka yi sallah, muka koma ward din da aka kaimu wannan satin. 

Muna zaune a reception, Janan tana rubuce-rubuce, ni kuma ina gyara wasu files. Karan shigowar kira a wayata ya katse mu, abu na farko daya fara fado min rai kawai shine Umar. Na rarumo wayar da sauri, a raina ina raya kalar dibar albarkar da zan mishi. Sai dai duk wasu alwasai na sai suka koma can bayan zuciyata, sakamakon ganin mai kiran ba Umar bane, Maryam ce. 


Na dan matsa can gefe kadan saboda hayaniyar mutane na daga kiran, maimakon muryar Maryam sai naji ta Aliyu. Babu kunya wai gaisheni yake yi, "Yaya Na'ilah ina yini?".

Mamaki ya kama ni, tunda na dawo babu wanda ya neme ni a gidan, daga iyayen har 'ya'yan. Kiran Aliyu a yanzu yana nufin abu daya ne,

Na daure na amsa da "lafiya lau Aliyu, ya kuke?". Ya amsa da lafiya lau, tare da fara kame-kamen tambayar ya karatu na da sauransu dai. Daga karshe dai ya dire a ainihin dalilin da yasa yayi kiran daga farko. 


"Kati zaki turo min, subscription dina ya kusa yayi expire!". Wani lokaci sai in dinga mamakin ko ajiye ni yayi a matsayin personal bank account dinshi, da zai dinga cirar kudi a duk lokacin da yaga dama? 

Sai dai Allah bai halicceni da riko ba, sannan bana rikon mutum inyi amfani da hakan idan yana bukatar abu a wajena in wulakanta shi. Bugu da kari ina son 'yan'uwana, ina kuma iyaka bakin kokarina wajen ganin na kyautata musu, na hidimta musu, matukar ina dashi ina musu iyaka bakin kokarina. Ba yabon kai ba, ina hana kaina ko cikina in ciyar da nasu cikin ko wata bukata tasu. 

Su sun san da haka, ina zaton shi yasa suke amfani da wannan damar suna taka ni yadda suke so. 


Nace mishi "har katin nawa kake so kuma?".

Yace "na dubu daya da dari biyar ma ya isa". 

Na girgiza kai, ni kaina wannan watan ban yi subscribtion ba, kodayake Allah ne yasa Janan ta mana ni da ita. Nace "zan turo maka zuwa anjima, yanzu muna cikin ward sai mun fita".

Yace "babu damuwa, Maryam ma na bidar katin dari biyar". Babu ko godiya ko karin bayani, ya maidawa Maryam wayarta sai itace ta min godiya sosai. Daga nan muka kashe wayar. 


Saboda haka muna fita daga ward din da misalin karfe shida na yamma, na tsaya a kasan ginin na sayi kati na tura musu. Zan yiwa Janan rakiya kamar yadda na saba yi mata, tace "yau dai an hutar dake, ga Almu na can yazo daukata".

Na kalleta ina daga mata gira cikin tsokana, "shi yasa tun dazu baki yaki rufuwa, masoyin usul yazo gida!".

Janan ta kai min duka a hannu tana yar dariya, "ni bana son sharri irin naki fa!".


A haka muka karasa jikin motar Almun Jan, silver Matrix 56 ce, daga ganinta ko dai sabuwar yayi ce ko kuma sabuwa ce dal, yadda take ta sheki da walwali. Yana ganinmu yayi kasa da gilashin motar yana murmushin shi da kullum baya barin kan fuskarshi. 

Al-Mustafa kyakkyawan namiji ne, fari, dogo, mai dan jiki. Yana da kirki, haka gabadayan yan'uwanshi suke, wadanda muka sani kenan. Mazauna garin Kaduna, a takaice ma a unguwar NDC unguwar kaji, unguwar su Ummah ainihin gidansu yake. Yayi degree dinshi anan Jami'ar Kongo, yanzu haka lauya ne mai zaman kanshi anan Kaduna din. Soyayyarsu da Janan ta samo asaline tun daga zamanin da take sakandire, suka kulla soyayyarsu mai tsafta, gashi har yanzu suna tare, kuma ana son juna. Ba shi kadai ba, hatta da yawancin yan gidansu sun sanni, na sansu saboda yawan zuwa Kaduna da nake yi, kuma muna yawan zuwa can gidan ko kuma su kannenshi su zo mana. Daga ganinsu kuma Janan ba zata samu matsalar zama dasu ba, saboda suna da kirki da sanin yakamata. 


Na gaishe shi a nutse, har ya hada da yar tsokanar daya saba min idan muka hadu, muna ta dariya. Daga karshe dai Janan ta shiga gaban motarshi ya tasheta yana kallona, "to Na'ilar Janan di ta, in shaa Allah a yau dinnan zan wuce Kaduna, sai dai in ce sai Allah yayi mana dawowa kuma".

Na gyada kai ina dan murmushi, "haka ne, to Allah ya tsare hanya. A gaida mutanen gida".

Yayi murmushi, "in ce musu me? Wadda ta guje su shekara da shekaru babu waiwaye tana gaida su?". Ya fada cike da tsokana. 

Nayi dariya sosai, "ni wannan korafe-korafe naku dai, in Allah ya yarda hutunmu na gaba zan samu inje Kadunar nan dai, ko kwana biyu ne in muku hakanan".

Yace "inaa, ai rike ki zamu yi sai kin karas da hutunki sannan zamu sake ki".

Na girgiza kai ina murmushi, nace "to ai shikenan, yadda kuka ce haka za ayi. Ku gaida gida". Na musu sallama na wuce don nasan idan na tsaya zamu iya kaiwa har magariba anan muna hira, abin kamar a jinin shi yake, idan kuna hira dashi sam baka sanin lokaci yayi, kafin ka ankara sai dai kaji ka kwashe awanni dashi kuna hira. Ko kuwa yanayin aikinsa ne?. 


Har na karasa hostel ban ji daga Maryam ko Aliyu ba, hakan yana nufin katinan sun shiga kenan. Idan naji kiran waya ko please call me bayan na tura kati, hakan yana nufin nayi kuskuren lamba kenan, dana tura kuma zan ji su dif, sai kuma bukatar hakan ta sake tasowa. Maryam ce ma ke kokarin kira lokaci zuwa lokaci haka nan a gaisa. 


Akan katifa dana nade ta da zanin gado yellow mai dauke da kwalliyar Malam buda min littafi da wasu kyawawan furanni na zube, da uniform dina da komi har takalmin toms baki da yake kafata. Dakin babu kowa, da alamu basu dawo ba ko kuma sun shiga makotan dakunanmu. Yau ba karamar gajiya muka nada ba, yadda majinyata suka dinga karakaina a ward din da aka tura mu yasa bamu samu mun zauna ba ko da wasa. Na lumshe idanuna a hankali, ina jin gajiyar jikina na neman rinjayata barci ya daukeni. Da sauri na tashi zaune. 

Kayan jikina na hau cirewa, na rataye su a jikin kusa dake jikin bango, na daura zanin atamfa tare da dora wata T-shirt baka akai, hula na dora akaina na fita tare da kulle dakin. Can kasa na sauka, da yake a sama muke. Sai dana tsaya a tap na debi ruwa, na daura alwala sannan na ciccibi bokitin ruwana na koma sama. 


Murjanatu na tarar a dakin, na mata sannu kawai. Ita kadai take hadamu da ita tunda nazo dakin, wani irin girman kai ne da ita, tunda ta ganta da wata akwalar 406 data fara cin duniya, gani take yi kamar ita din wata shegiya ce. Ni kuma naga meye abin dagawa akan haka? Akwai masu motoci da suka ninka nata a kyau da tsada da ake zaman lafiya dasu a cikin hostel din, wadanda iyayensu suka fita kudi ma. Ni fa ganina nake daidai da uban kowa, yadda kake sanya sutura mai tsada kayi kyau, haka nake saka mara tsada inyi kyau, har ma a kasa banbance mu. Abinda zaka fini kawai in damu, shine yawan maki, a test, assignment, exam ko result, wannan shine kawai. Itama don ta ita ne da bamu gaisa ba, sai dai ni ba'a zaman gaba dani. Ko sannu sai ta hada mu da kai, in yaso zabi ya rage naka, ko ka amsa, ko kar ka amsa, matsalarka ce, ni dai na fita hakkinka. Esther ce muka fi mutunci da ita dama. 


Kafin a kira sallah na dora jollop din macaroni, ana kiran sallah na rage wutar karamin gas din dana saya na tada sallah ta. Murjanatu tana zaune a gefen wayarta tana hira da saurayinta har na gama sallah ta na zuba abinci, tunda nazo dakin na kula sallah bata dameta ba ko kadan. Yau da asubahi dana tasheta sallah, cewa tayi period take yi. Sai da rana ta fito gade-gade, tana kallonta suna kallon juna, wai ta kalli gabas ta tada sallah. Na girgiza kai kawai dana tuno abin. 

Tayin abincin na mata ta girgiza kai kawai taci gaba da wayarta, nima na girgiza nawa kan na saka cokali na fara ci. Ko loma uku banyi ba Esther ta shigo dakin, nan ta dauko nata cokalin muka zauna muka ci muka yi nak, har da kari. Na sauka kasa na wanke plate din, na sake dauro alwala na dawo sama. 


Kan sallaya na koma na zauna ina lazumi har aka kira sallar isha'i nayi. Karfe takwas saura na dauki dan karamin littafin da nake daukar bayanai idan mun shiga ward, textbook akan matsalar da mata ke fuskanta yayin da suke dauke da juna biyu, sai kuma biro da pencil na sauka kasa. Common room naje na zauna, ba jimawa aka fara hasko diramar da nake zuwa kallo kullum. Ko bayan an gama anan na zauna can wani lungu inda babu hayaniya sosai, na cigaba da bita da karatuna har karfe goma tayi. Na mike na koma daki. 

Yanzu kuma Murjanatu ce bata dakin, babu mamaki daya daga cikin samarinta ne yazo. 


A rayuwar makaranta, musamman wadanda suke zaune a cikin hostel, babu abinda idanunka ba zasu jiye maka ba. Babu tabara, rashin kunya da banzatar da kai da ba zaka gani ba. 


Kai ne iyayenka suka taso ka tun daga wani gari, suka kawo ka wani, domin me? Domin fa kayi karatu ne, idan kuma kayi kai zai yiwa amfani ba wani ba. Amma sai kazo, ka biyewa kawaye da samarin banza ayi ta bushasha da dibar albarka, har ma ka manta da abinda ya kawo ka. Ka ci amanar kanka, ka ci ta iyayenka, ka kuma yaudari kanka. Tunda daga karshe dai, su wadanda ka rike din, zasu zo su maka tawaye, kawaye da suka zuga ka su yaye maka baya su koma gefenka suna maka dariya, samarin banza da suka daure maka gindi su samu wasu da suka fi ka, su kyaleka. A lokacin ne kuma idanu zasu raina fata, an barka da carry overs in ma kayi rashin sa'a da spilling, daga nan idan shaidan ya maka huduba, ka koma bin lecturers domin gyara takardu. Idan kuma hakan bata samu ba, a barka da hamma, kayi babun badinihu, baka ga tsuntsu baka ga tarko, sai zare idanu. Lokacin ne kuma zaka yi dana sani. 


Yanzu ita Murjanatu da muke magana a kanta, yar spilling ce. Kamata yayi ace yanzu ta gama nata aikin tana internship kamar yadda sauran yan ajinsu da suka gabata suke yi yanzu haka anan Shika din, amma gata nan. 

Yanzu haka har nayi shirin kwanciya barci na kwanta, bata dawo dakin ba. Sai wajen karfe goma sha biyu da rabi na dare sannan ta turo kofar dakin ta shigo. Ina kallonta ta cikin dusu-dusun hasken dakin ta kwanta akan katifarta. A raina na nema mata shiriya da ita da sauran masu hali irin nata, Allah ya nuna musu hanya madaidaiciya. 











#F.W.A

[17/03 9:38 PM] Jiddah Lawal: 🌟 *⋆☆A ZATO NA...!☆⋆* 🌟



        *⋆©Jeedderh Lawals⋆*





                             *☆⋆13⋆☆*







"Assalamu Alaikum wa Rahmatullah wa Barakatuhu, ina fata kin wayi gari cikin koshin lafiya ya ke ma'abociyar haske dake haskaka fadin zuciyata bakidayanta!".

Kamilalliya, kuma tattausar muryar ta fada, cikin wani irin huskinesa da sexiness da... da... abubuwa da dama.

Jin muryar kadai ya haifar min jin wasu abubuwa, wadanda nafi fahimta a cikinsu shine faduwar babu gaira babu dalili da gabana yake yi, sai kuma wata irin kasala, sauran na kasa fahimtar ko meye kuma. 


Karfe tara na safiyar ranar asabar, sai dana kusa tuntsirawa kasa lokacin da vibrating din da wayata tayi ya tashe ni daga daddadan barci da nake yi. Sai dai ba wannan bane yasa nayi suman zaune ba, ko kuwa kwance zan ce? Sunan wanda yake kiran ne da yake tsalle yana rawa akan screen din wayata ya kusa sumar dani. Mamakin ya wuce misali, haka fargabar ta wuce misali, nayi zaton mafarki nake yi, hakan ne yasa na kurawa wayar idanu tana ta ringing, wakar Chainsmokers da cold play ta 'something just like this' tayi-tayi har ta katse. Ba'a dauki wani lokaci ba aka sake kira, nan ma dai naci gaba da kallon wayar. Sai a karo na uku ne na samu kuzarin kifta idanuna, sannan na daga wayar na kara a kunne. 


Muryar data fara dakar kunnena rendered me speechless, na kasa magana. Na tabbata a lokacin da za'a dauki abin gwajin bugun zuciya, za aji zuciyata tana gudun fanfalaki. 

Na sha ayyana yadda muryar wannan bawan Allah zata kasance, har mafarki na sha yi. Amma muryarshi da naji yanzu, ban taba tunanota ba, ban taba mafarkinta ba, ban taba jin mai kama da ita ba. 

Na hadiye yawu mukut! Da kyar na iya warto murya da natsuwata da suka fara shawagi a saman kaina suna kokarin dagula min lissafi. 

Cikin rawar murya dana rasa dalilinta, na amsa. Zata iya yiwuwa saboda yadda muryarshi ta sanya zuciyata tsalle ne, ko kuma saboda yadda muryar tashi ta sanyayar min da jiki ne, zata kuma iya yiwuwa saboda yadda abin yazo min a bazata ne, za kuma ta iya yiwuwa duka abubuwan ne. 


Yace "wow, Masha Allah, ban taba tunanin muryarki zata kasance haka ba, lallai tsarki ya tabbata ga Ubangijin daya tsara ki, ya baki murya wadda zata iya shagaltar da mutum ga yin abu, shin ko ya zaki kasance a fili?".

Sai naji kunyar maganganunshi sun kama ni, don haka na buge da gaida shi. Ya amsa, ya kara dorawa da, "To daga farko dai sunana Muhammad M.B, ni bahaushe ne sannan ina aiki a Abuja, ban sani ba ko malamar ta ganeni?".

Nayi yar dariya, "na gane ka mana, Mr. Mysterious!".


Ya saki wata irin tattausar dariya data sa na kara narkewa akan katifata, jin muryarshi nake kamar ana min busar sarewa a kunne, yace "da gaske nayi zaton sai na zauna dogon bayani, shi yasa tunda gari ya waye nake ta hardar abinda zan fada miki, ki ce da ban wahalar da kaina ba?".

Na gyada kai ina dariya kamar wata sakara, "gaskiya kam, da ka kira tun da wuri".

Yace "yadda zan katse miki barci? Yanzu ma naji kamar daga barci kika tashi, sorry, na katse miki barci. Na kasa daurewa ne wallahi. Ina fata banyi laifin komi ba?".


Na girgiza kai kamar yana kallona, "ko kadan baka yi laifi ba, zan ma iya cewa kayi daidai!".

Ina jin ajiyar zuciyar daya sauke, "good. Don ba zan so ace daga wayar farko ba na fara yin laifi ba gaskiya". Duk muka yi dariya. 

Daga nan duk muka yi shiru, baka jin sautin komi sai karar dake fita daga cikin wayar kawai. Zuwa can yayi gyaran murya, yace "to Malama Na'ilah, kamar yadda nasan cewa kin san dalilin da yasa na tunkareki tun farko har ya kawo ga wayar da muke yi yanzu, magana ce ta so. Wadda nake so, kuma nake fatan idan Allah ya yarda ya amince, zata kaimu ga aure na sunnah. Magana ta gaskiya ban fito da wasa ba, kuma nayi niyar dana bayyana a gareki, muka samu fahimtar juna ni da ke, ba zanyi sanya ba zan fara zancen aurenmu, in samu in killace ki a dakina kafin kwado ya min kafa, me kika ce?".


Daga jin sautin muryarshi da yadda yake fitar da haruffa daya bayan daya, kasan cewa kaji mutum wanda yasan ciwon kanshi, wanda yasan me yake yi, ya kuma san yadda duniya take ci. Naji ya kara shiga raina. Nan nayi mishi bayanin cewa yanzu dai karatu nake yi, sannan kuma akwai wanda muke tare dashi a halin yanzu dai, ban boye mishi komi ba, na fada mishi komi da komi. Shi kuma ya burgeni daya saurareni tunda na fara magana har na gama bai katse ni ba. Hakan ya kara min wata martabar shi a cikin idanuna. 


Sai dana gama, ya nisa yace "naji dadi kwarai da baki boye min komi ba game dake, sannan maganar karatu a wajena ba matsala bace, koda ace baki fara ba, zan iya daukar nauyinki har ki gama, balle kuma duka-duka Allah na tuba menene ya rage a cikin karatun naku yanzu? Sauran kadan ne. Zancen wanda kuke tare kuma, wannan ai lokaci ne zai nuna mana ko ke din ta wacece. Illa iyaka, mutum ya zage damtse, ya shiga filin dagar neman ki sai aga wanda yake da nasara!".

Nayi dariya sosai da maganganunshi, da alamu Allah ya hore mishi iya sarrafa maganganu matuka. Shima ya biye min muka yi ta kyakyatawa kamar wasu kananun yara. Sai dana nutsa sannan nace mishi, "to Allah dai yayi mana zabin mafi alkhairi".

Ina dire aya ya cafe da; "in shaa Allahu ma kece alkhairin", ko yawu bai bari na gama hadiyawa ba. 

Nace "to Allah ya yarda".

Yace "ameen... Tunda yanzu mun yi wannan magana, ina fata mun fahimci juna ni dake? Kina da wata tambaya da kike son yi game dani?".

Nace "na fahimci komi, tambaya kuma bana tunanin a yanzu akwai ta, amma idan ina da ita nan gaba, zan yi maka".


Yace "zaki iya yi a koda yaushe, tunda yanzu na ji muryarki, ina tabbatar miki da cewa sai kin gaji da ganin kira na a wayarki, don zan so ace kullum cikin sauararen muryarki nake!".

A zuci so nayi in ce, "ai nima hakan take", amma a fili sai nayi dan murmushi kawai. 


Yace "yanzu dai bari in barki ki karya, nasan baki karya ba kika fara waya da ni. Bayan kin gama cin abincin zan kira ki mu dora daga inda muka tsaya, ki huta lafiya Baby na!". Daga haka ya tafi. 


Na bi wayar da kallo kamar shine a gabana, ina nanata kalmar 'baby na!' a cikin kaina kamar wata bakuwar kalma da ban taba jin kamarta ba sai yanzu. Gabadaya sai naji cikina ya cika, bana marmarin komi. Don haka na koma kan katifa na kwanta ina kara maimaita hirarmu da Malam Muhammad M.B a cikin zuciyata kamar wani shirin film da yake matukar kayatar dani, ina zabga murmushi kamar wadda ta fara zarewa.

Amma dan saurara, wani hanzari ba gudu ba., me yasa muryarshi take min kama da wani wanda na sani? Ban tabbatar ko waye ba, amma naji kamar na taba jin muryar nan, inda na taba ji dinne na kasa tunawa. 


Ban san iya lokacin dana dauka a cikin wannan hali ba na tsananin bege, sai dana ji an daka min duka a cinya. Nayi firgigit! Na mike zaune ina sosa wajen. Esther dake gefen katifata a zaune dangargar ta kalleni tana murmushi, "Babe, tunanin meye kike yi ne haka? Hala oganki ne?. Ta fada cikin harshen turanci kamar yadda ta saba magana dashi. 


Nace mata "nothing o...".

Tace "na lie... Kada kiyi tunanin ban ga yadda kike ta murmushi ba kina dariya lokacin dana zo fita". Na zaro ido ina kallonta, da gaske har fita tayi ta dawo ban sani ba?.

Ta kyalkyale da dariya ta dauki wata bakar leda da ban kula da ita ba, ta miko min, "dama kina ta soyewa ta ina zaki ji motsin mutane bayan kinyi nisa a duniyar da daga ke sai shi? Na tabbata za'a iya ciccibarki a lokacin baki ma sani ba!".

Harara kawai na jefa mata cikin murmushi. Na daga ledar, kamshin masa ne ya fara bugo ni tun ma kafin in ga masar. Sai a lokacin na tuna da cewa jiya da dare kafin mu kwanta na fada mata idan zata je siyan masar yau da safe ta tashe ni koda ina barci ne, don marmarin cin ta nake yi sosai. 


Nayi murmushi ina kallonta, "nagode kwarai Esther, ta nawa ce kika sayo?".

Tace "ban san ko ta nawa kike bukata ba, sai na sayo ta dari biyu".

Nace "tayi, nagode fa".

Tace "babu damuwa!".

Tashi nayi na dauki purse dita na bude na bata kudinta, na kara mata godiya, sannan na sauka kasa naje nayi brush na koma dakin. Bowl na dauka karama ta plastic na juye miyar da aka daure a cikin leda, na fara cin masar. 


Ina cikin ci ne na dauki waya na kira Janan, finally, abinda muke ta jira, mysterious dina dai ya kira waya. Nan muka sha ihun murnarmu da maida yadda aka yi. Wani labarin ma ai sai ta shigo ranar Monday sannan za ayi shi baki da baki. 

Yinin ranar wannan gabadayanshi, Allah ne kadai yasan farincikin dana yini dashi, wata irin far'ah dana rasa dalilinta, nishadi dana rasa dalilinshi. God, I'm so whipped, totally!!. 


Yini aka yi ana ruwa duk da ba mai karfi bane, amma yanzu da nake kudundune cikin bargo a dakina da dare, sanyin da ruwan saman ya haddasa da kuma kamshin ruwa da jikakkiyar kasa da yake tashi, da kuma tsananin taushin muryar Mysterious dake ratsawa ta cikin dodon kunnena a daidai wannan lokacin, sai naji babu wata damuwa a raina. Babu kowa, kuma babu komi a wannan lokacin sai ni sai shi kawai. And nothing matters!. 



Tuni mun riga mun sabarwa junanmu jin muryar junanmu a kowace rana. Muryar dayanmu zamu tashi da ita, texts zasu mana rakiya duk inda zamu je a yinin ranar, haka kuma zamu ji muryar juna kafin mu kwanta da dare. 

Da asuba tun ma kafin alarm dina ya buga, Muhammad zai kira ni ta waya, nan kira kawai zai yi in tashi, to idan na gama ne zamu yi wayar minti biyar zuwa goma, sai muyi sallama. In shiga wanka in shirya, in karya, in fita. Kafin in karasa ward ya turo min text mai cike da kalamai dadada da zasu sa in yini ina kallon wayata cikin murmushi, ina kara karanta shi over and over, sai in tura mishi amsa. Kafin yamma ta fadi at least zamu yi musayar messages sau uku ko fi, sannan da dare dole ne sai ya kira ni kafin in kwanta barci, watarana ma muna cikin hirar barci zai daukeni sai dai ya kashe wayar in yaji shiru. 


Ni kaina nasan cewa na canza, kamar wani abu yayi snapping a jikina ne. Duk wasu makamai da katangu dana sa a jikina, daya bayan daya Muhammad ya bisu ya sassare, kamar basu taba wanzuwa ba. 

Wani abu ne da bai taba faruwa dani a tarihin rayuwata, da shekaruna dai-daya har ashirin da hudu a duniya ba. Ban kuma taba zaton zai farun ba. Amma yanzu daya faru, sai nake jin ina zargi da tuhumar kaina, me yasa tun farko ban bar kaina nima naji dadin wannan abu ba? Na dinga takura kaina, ina matsawa kaina? Kodayake, komi yana da lokaci, kuma kamar yadda Janan take yawan cewa, _'idan lokacin ki kamu da so yayi, baki da yadda zaki yi, kina so ko ba kya so, zaki fada tarkon ko, kin sani ko baki sani ba!'._

To yanzun ma ina tunanin abinda ya faru kenan, lokaci na ne yayi. Na kamu da soyayya, soyayyar Muhammad mai zurfi. Zurfin da ya kai naji ina so inyi kugi da karaji, wanda duk duniya da mutanen cikinta zasu ji cewa ina cikin zazzafar kaunar mutumin da ban taba sakawa a cikin idanuna ba!. 



                               *   *   *




"Kyawunta ace wannan azumi da zai zo, wani mutumin kirkin zai zo ya dauki dubu ko hamsin ce ya baka, ya hada ka da buhun masara, gero, sukari ko rabin buhu ne! Kai ai da kakar ka ta yanke sa'a!! Sai ka nemi inuwa mai ni'ima kawai ka fuske, ka yini tun safe har dare a kwance Malam, babu ruwanka!!".

Wani kwandastan mota da muka hayo daga asibitin Shika zuwa kasuwar Samaru yake cewa. Duk cikin motar aka saka dariya. 


Wani mutum daga baya yace "wannan duk mafarki ne kake yi, wanda baya zama gaskiya. Abu mai yawa da zaka samu daga hannun manyan nan shine kwanon masara ko gero, ba'a hada maka guda biyu ma. Sai ka samu wani mai tsoron Allah shine zai kawo wata lalatacciyar dari biyu ya dora maka yace kayi nika. Ai yanzu wannan alherin a tsakanin masu kudi kawai ake yi, ka dauka ka kai gidan mai kudi, shima idan ya tashi yin nashi sai ya maido maka. Su kuma talakawa sai suje su nemo da karfinsu".


Wani ya cafe zancen, "ai sai dai kawai Allah ya kara rufa mana asiri. Wata irin rayuwa ake yi ta danniya da rashin tsoron Allah, mai shi ya dannewa mara shi, masu kudin namu kuma basa taimakon talakawanmu. Kowa kanshi ya sani ba wani abu ba, Allah dai yasa mu dace!". Duk muka amsa da ameen.

Har motar ta tsaya a bakin kasuwar, da yawanmu muka fita daga ciki, wasu suna ta tururuwar shiga, da alamu ranar da ake zabgawa yau ta gama dakar su. 


Ni da Janan muka tsallaka titi muka shiga kasuwar. Kasancewar Azumi yana ta gabatowa, ana tunanin nan da kwanaki biyar masu zuwa ma za'a tashi dashi. Shi yasa nace bari in shiga kasuwa in dan yi sayayya da sauran kudin da nake dasu kafin in cinye su. 

Mun shiga mun danyi saye-sayen mu, muka fito hannu riki-riki da kaya. A bakin titi muka tsaya, Jan zata tsallaka ta hau bus zuwa PZ ni kuma in matsa gaba in hau wadda zata maida ni asibiti. Kallon motoci, masu mashina, kekuna da ma masu tafiya akan kafafu da keken guragu nake yi suna ta karakaina, kowa harkar dake gabanshi ce ta dame shi. 


Janan ta fara daddabata da sauri, nayi saurin juyawa na kalleta, wata mota da take wucewa ta gabanmu wadda dan banzan go-slow din da ake yi ya saketa, nace "lafiya?".

Tace "waccan motar bata miki kama data Umar ba?".

Na kara bin motar da kallo wadda zuwa yanzu ta bace min, yanzu da tayi maganar sai naga irin tashi ce, amma kuma garin Zaria mai fadi, ba lallai ace shi kadai yake da irin wannan motar ba. Ko yanzu da zamu baro asibiti naga wata nurse ta fita a cikin irin motar tashi, wadda har kala bata banbanta su ba. Balle kuma wannan motar dana hango kamar mata da miji ne a ciki? Sannan bugu da kari, Umar yana Kaduna ba Zaria ba. 


Dana juyewa Janan wannan bayanai, sai ta gyada kai, tace "haka ne, mantawa nayi". Muka samu ababen hawan suka ragu a lokacin, ta tsallaka da sauri tana min bye-bye, sannan ne nima na juya na shiga bus. 




Ranar Juma'ah da wuri na fita zuwa cikin asibiti, kasancewar da wuri na tashi. Ranar tun daga cikin hostel muka fara waya da Muhammad har na shiga cikin ward, sannan muka yi sallama dashi akan cewa zai kira ni kafin ya tafi masallaci. 


Har karfe goma na safe babu Janan babu alamunta, hankalina yana bakin kofa, da naji alamun za'a shigo sai inyi sauri in kalli kofar cikin tsammanin itace, sai in ga wani daban. Ganin karfe goma tana shirin wucewa yasa na lalubo wayata daga cikin aljihun wandon uniform dina na kirata cikin faduwar gaba. Hakan bai taba faruwa da Janan ba. Duk son makararta, Janan bata yin fashi, don haka ne naji na damu. 


Wayarta tayi ta kara tana katsewa, a karo na kusan uku ne ta daga. Da sauri na fara jero mata tambayoyi, "wai ya ne har yanzu baki zo bane? Baki tashi da wuri bane ko kuma yau kinyi shawarar kin zuwa ne?!"..

Daga farko shiru aka yi, kafin daga baya inji muryar da ba ta Janan ba tace "uhmm, Janan din bata ji dadi bane".


Naji gabana ya fadi, nayi salati na sanar da Ubangiji, nace "lafiya, me ya sameta? Waye kuma?".

Mai maganar yace "Asthma dinta ne ta tashi, sannan Bilal ne". Na kalli wayar cike da mamaki, kwata-kwata muryar bata yi kama da tashi ba, a takaice ma dai muryar bata yi kama data mace ba balle namiji. Amma sai nafi kyautata hakan a matsayin sharrin network kawai. 


Nace "Subhanallah! Kuna gida ne?".

Yace "a'ah, muna asibitin Delicate dake bayan gidanmu, kin san shi?".

Nace "ehh, gani nan zuwa". Na kashe wayar da sauri na maida ta aljihu. 


Kayana na dauka a gaggauce, na tunkari office din matron din ward din. Na kwankwasa ta min izinin shiga. A gaggauce na mata bayanin abinda ake ciki, nan tace in tafi kawai babu komi, har ma ta kara da 'ki dubata. Sai ranar Monday idan jikin nata ya warware', na mata godiya na fita a sukwane kamar wadda zata tashi sama. 

Wata irin wahalalliyar asthma gareta, bata cika tashi ba, amma duk ranar data tashi sai ta jikatar da ita. Shi yasa naji hankalina ya kasa kwanciya, ko tunanin komawa hostel in canza kayan jikina banyi ba. Allah ya taimaka na samu abin hawa da sauri kasancewar ranar Juma'ah ce, kowa yana kokarin ya je inda zai je kafin lokacin masallaci yayi. 





~Phewwwwww!!!!!



[18/03 11:24 PM] Jiddah Lawal: 🌟 *⋆☆A ZATO NA...!☆⋆* 🌟



        *⋆©Jeedderh Lawals⋆*





                             *☆⋆15⋆☆*






Ba shi kadai ba, ni kaina nayi mamakin marin dana mishi, amma banyi nadamar hakan ba.

Ya dafe kuncinshi yana kallona cikin zare ido, "sweetie....!".


Cikin tsananin tsiwa da balbalin masifa nace "idan ka sake kirana da wannan sunan, Allah ya isa ban yafe maka ba Umar!!".

Yayi sararo a tsaye da baki a bude, ya rasa abin cewa. Nace "dama abinda kake yi kenan? Nayi tunanin cewa abubuwan da kake nuna min kawai kana yi ne saboda desperation, ashe halinka ne?". Munafikin sai yayi shiru kai a kasa yana muzurai. Daidai lokacin Haleemo ta fito daga cikin motar, kai a kasa babu kunya babu tsoron Allah tana nukutu. 


Na kalleta, wani tsabar takaici yana cina, ji nike kamar in kamata in hadata da bango ko motar, amma na cije don nasan shaidan ne yake so ya zuga ni. Na nunata da yatsa, "akan wannan abin ne ka yaudare ni? Akan wannan abin ka share ni tsawon watanni, ina bibiyarka kana yazga ni kamar wata mara aikin yi? Ba ni kuka cuta ba wallahi, kan ku kuka zalunta. Kuma ni babu abinda zan ce muku, babu kuma mummunar addu'ar da zanyi muku. Sai dai ku sani, za ku gani da idanunku, Allah ya kara muku dankon kauna!". Daga haka na juya da sauri na wuce, babu wanda ya iya cewa uffan a cikinsu. Janan data tsaya ta tsince kayan da suka zube, ta biyo bayana da sauri, jerawa muka yi muna tafiya ba tare da dayanmu ya cewa daya ci kanki ba. 


Muna shiga daki naji jikina ya dauki wata irin rawa, ba shiri na lalubi kujera na zauna. Na kai hannuwana duka biyu na dafe kaina ina girgizawa, dama abinda yake faruwa kenan, ni ina gefe guda na hangame baki ban san abinda ke wakana ba? Lallai, idan kana raye zaka sha kallo. Kallo ba na wasa ba kuwa. 


Janan ta zauna a kasa tana fuskantata, babu wanda ya iya magana a cikinmu, har muka dauki lokaci mai tsayi a hakan. Can na daga baki, a hankali nace "me yasa? Saboda bana son shi ne ko me?".

Janan ta dafa kafafuna da nake ta jijjigawa, cikin tausasshiyar murya tace "ko kadan, kawai son zuciya ne da rashin godiyar Allah. Kiyi hakuri, ban san hakan zata faru ba".


Na kura mata rikitattun idanuna da nasan sun rine da jan bacin rai, nace "me kike nufi?".

Tace "kamar sati biyu da suka wuce, na taba ganin hoton Umar din a wayar Haleemo, sai nake tambayarta a ina ta san shi, sai tace min abokin saurayinta ne. Ni kuma sai na share maganar. Ranar nan da nace miki kamar Umar, ni na tabbata na gan su su biyun, nasan banyi kuskure ba. Dana nuna miki kika musa sai naga babu amfanin fitowa gar da gar in fada miki, tunda ban tabbatar da alakar dake tsakaninsu ba... Don Allah kiyi hakuri!".


Na girgiza mata kai, "ki daina bada hakuri akan laifin da ba ke kika aikata shi ba Jan. Haushina daya, daya bari son zuciya ya rinjaye shi har ya iya juya min baya, amma kanshi ya yiwa ba wani ba. Na kuma gode Allah da yasa na ga hakan da idanuna, basu dinke ni a baibai ba. Da muka zo muka yi aure a haka, inyi yaya?".


Janan snorted, na bita da kallo cikin mamaki, tace "wai ke don Allah kina tunanin Umar yana da sha'awar kuyi aure?".

Na bita da kallo mai dauke da alamar tambaya, amma dai duk da haka na amsa mata, nace "ehh mana, me kike tunani ne, daukar lokacin da muka yi a tare a banza zata tashi ba tare da munyi aure ba?".

Tace "abinda nafi zargi kenan!", zanyi magana tayi gaggawar katseni, "ki duba fa, ba fa yau kuke tare dashi ba, amma bai taba tado miki maganar aure ba. Idan ma kin tado sai ya hau miki kame-kame, baki taba zargin ko baya son auren bane?".


Nayi shiru cikin tunani, ban taba yin wannan tunanin ba. Nafi kyautata zaton ko rashin maganar aure da baya min, baya so ne in hada karatuna da aure, yafi so sai na gama sannan ya fara maganar, don haka ban taba kawo zargin wani abu ba. Don haka na girgiza kaina kawai. 


Tace "ko ma menene, ki godewa Allah daya nuna miki hakan tun kafin zance yayi nisa. Samari irin su Umar su kan yi iyaka bakin kokarinsu wajen ganin sun cimma burinsu akan macen data burge su. Ina tunanin dalilin daya tsayar dashi kenan, ko kuma sun yi tsubbace-tsubbacen da suka saba sun shawo kanshi".


Na girgiza kai, "babu boka babu malam a cikin wannan lamari, ina tabbatar miki Umar a cikin hankalinshi yake".

A nutse na warware mata dalilin daya haddasa fadan da muka yi dashi last time, har ma wasu fadan da muka yi akan matsala irin wannan, wanda bata taba jin hakan ba sai yanzu. 


Ta kama baki cike da tu'ajjibi, tace "kin gani ko? wato da yaga cewa ta bangarenki babu sa'a, shine ita kuma data kai kanta yace bari ya biye mata. Kila a dabararshi idan ya gama da ita sai ya dawo kanki? Ko kuma wani shiri gare shi na daban?".


Nayi shiru kawai ina kara juya lamarin a cikin raina. Har yanzu kaina bai gama yayewa ba, mamakin abin bai sakeni ba. Dama ana haka a duniyarmu? Kina sane, kana sane, ku take sanin, ku yaudari kanku ku yaudari wasu? Ina jin labarin snatching da dama, mafi yawa a labarai ko a gidajen radio ko a fina-finai, ban taba zaton yana faruwa da gaske ba, sai gashi yau ya faru a gaban idona, a kaina kuma. 


Duk yadda naso in jurewa abin, kasawa nayi. Ji na nayi kawai hawaye na bin fuskata. Janan take ta bubbuga bayana tana bani kalamai masu kwantar da hankali, har naji zuciyata ta dan yi sanyi, amma nasan cewa na dan lokaci ne. 


A hankali na mike, jiri yana kwasata, na shiga bayi. Tsaye nayi a gaban babbar mirror dake manne a bangon bandakin ina karewa kaina kallo. Idanuwa sunyi luhu-luhu, sun kuma yi jawur, daga ganina babu tambaya kasan kuka na gama shaka. Ko yanzun ma wasu hawayen ne suka ciko min idanu. Me na yiwa Umar a duniya dana cancanki wannan yaudarar daga gareshi? Ko kuwa Haleemo zan ce? Shin wai, ta yaya ma har suka hadu suka kulla wannan cin amana? Tun yaushe kuma?? 


Wato dai kaji tsoron dan Adam. Kuma kaji tsoron mutane masu halin shiru-shiru, sai yanzu nake gane gaskiyar Jan da tace halinta yafi na sauran muni. Lallai na ga misali akan kaina. 

Na ciza lebena na kasa ina danne kwallar data ciko min ido. Ba zan kara zubda hawaye akan su ba, they are not worth it!. Na wanke fuskata kawai na daura alwala na fita. Katifa kawai na hau na kwanta, na ji wayata tana kara da vibrating, ina dagawa naga Umar ne yake kiran. Na jinjina kai kawai cikin rashin abin cewa, lallai rashin ta ido irin ta dan mutum tayi yawa. Wayar na dauka kawai na kashe nayi jifa da ita can bayan katifar, na sake komawa na kwanta. 

Janan duk yadda taso ta ja ni da hira, kasawa nayi. Haka nan ta hakura tayi shiru. Har barci ya dauketa idanuna biyu, ina ta saka da warwara har barcin ya daukeni nima. 



Washegari haka na tashi da matsanancin zazzabi da ciwon kai a jikina. Da kyar na iya yin sallar asuba, na koma na kara kwanciya na kawo bargo mai nauyi na rufawa jikina, amma hakan bai hana ni rawar sanyi ba. Har wajen karfe takwas na safe ina cikin wannan hali. 

Janan tana zaune a gefena tana kallona cike da alamun damuwa rubuce a fuskarta, tun da asubahin take bin kaina akan in shirya mu tafi asibiti, amma na ki tashi. Yanzun ma abinda take ta fama dani kenan, "don Allah ki tashi Na'ilah, jikin ki kara rikicewa yake yi". Ta fada cikin alamun lallashi da kuma roko, kai kawai na girgiza mata alamun a'ah, na kara jan bargo na rufa. 


Ta kura min idanu, akwai alamun takaici da kurar da ita da nake yi rubuce baro-baro akan fuskarta. Tace "shikenan, kiyi duk abinda kika ga dama, an fada miki na damu ne?".


Ta ga dai bani da alamun motsawa, sai ta kara matsowa kusa dani, cikin sanyin murya, cike kuma da nuna tausayi tace "haba Na'ilah! Ke da nake ganinki da hankalinki da komi, amma ki kasa yarda da abinda Allah ya tsaro miki? Akan namiji! Haba Na'ilah!! Akan namiji zaki zauna ki kashe kanki? In fada miki gaskiya? A banza zaki kashe kanki idan ma haka ne, mantawa zai yi dake, dama can bai daukeki a bakin komi ba. Yanzu haka ma kila ya riga da ya manta dake, kila yanzu haka suna can suna kwasar soyayyarsu babu abinda ya dame su yayin da ke kina nan kin saka bakin cikinsu a cikin ranki, kina nema ki kashe kanki a banza!".


Na samu na girgiza kaina da kyar, murya na fita da kyar, ina ganinta dishi-dishi, nace "ba akan Umar bane!".

Ta fusata, "to akan waye idan ba shi ba? Ke karamar yarinya ce da za a dinga bin kanki akan rashin lafiyarki wai? Idan kina so in yarda ki taso mu tafi asibiti yanzun nan!".

Nace "mura ce kawai ba wani abu ba, zuwa anjima zai sauka, ki daina damuwa".

Ta hau girgiza kai, "wannan kafar kai taki ban san irinta ba wallahi, Allah ya kyauta miki!".

Na lumshe idanuna kawai saboda yadda nake jin sunyi min nauyi. Janan kuma ta saka ni a gaba tana kallo. Wani wahalallen barci ya daukeni kenan, naji alamun taba kofa alamun an fita. Ba'a jima ba aka sake bude kofar aka dawo. 


Jin tashin murya ba daya a dakin ba yasa na bude idanuna da kyar. 

Yaya Bilal ya kalleni fuska babu yabo ba fallasa, sai dai can cikin kwayar idanunshi, akwai wata kwantacciyar damuwa dana tabbatar ba rashin lafiya ta bace ta haifar da ita ba. Wannan, ko kuma dai idanuna ne suke min gizo kawai. 


Ya dauke kallonshi daga kaina ya maida kan Janan dake tsaye a gefenshi, "me ya sameta?".

Tace "zazzabi ne da ciwon kai, tun jiya da dare, amma bata son mu je asibiti. Kuma zazzabin karuwa ma yake yi maimakon ya ragu".

Ya sake maida kallonshi kaina, duk da halin da nake ciki kasa daukar kallon shi nayi. Wasu irin sakonni ne suke fita daga cikin idanun nashi, bana tunanin shi kanshi ya san suna fita. Ga... Dan saurara! Wasu irin sakonni nake nufi? Anya kaina bai fara motsi ba kuwa? Ni wacece din shi da zan ce yana turo min sakonni ta idanunshi? Wow! Dama naji ance zafin zazzabi yana sa mutum ya dinga sambatu kila ma har da ganin hallucinations. Babu mamaki abinda nake gani kenan nima yanzu. 


Maganar da Yaya yake yi ce ta dawo dani daga rants din da nake zabgawa a cikin kaina, yace "bari in kira Dr. Zubair in gani, Allah yasa yana kusa". Ya juya ya fita daga dakin wayarshi a hannu yana dannawa. Janan kuma ta dawo gefena ta zauna, hannu ta kai tana daga goshina zuwa wuyana, ni kaina nasan ba karamin zafi jikina ya dauka ba, har wani tiririn zafi nake ji a jikina. 


Ba ayi cikakkun mintuna goma da fitar Yaya ba sai gashi ya dawo. Yace "bismillah dakta, shigo".


Janan ta tashi da sauri ta dauki gyale ta dora akan kayan barcinta. Ni kuwa dama kayan barcin dana saka doguwar rigar cotton ce mai dan gajeren hannu wanda ya tsaya min a damtsen hannu. 


Yaya ya fara shigowa dakin, wanda nake zaton shine likitan daya kira ya biyo bayanshi. Ya ajiye dan karamin akwatin daya shigo dashi, ya bude ya fara ciro abubuwan gwaji da sauransu. Yana fiddo komi ya fara aikinshi. 

Cikin awa daya sai gani manne da drip a hannu, da tulin magungunan malaria, har ma da typhoid.











#F.W.A

[19/03 11:03 PM] Jiddah Lawal: 🌟 *⋆☆A ZATO NA...!☆⋆* 🌟



        *⋆©Jeedderh Lawals⋆*





                             *☆⋆16⋆☆*






Ana sa min ruwan barci mai nauyi ya daukeni. Lokacin dana motsa har an cire ruwan, da alamun rana tayi sosai ko kuma ma lokacin azzuhur yayi saboda Janan dana hango akan abin sallah.

Jikina yayi karfi sosai fiye da lokacin dana tashi dazu da safe, na lallaba na tashi zaune. Cikin ikon Allah babu jirin da nake ji da kuma ciwon kan. Janan da taji motsina ta juyo, murmushi ta saki a hankali, "har kin tashi?". Na gyada mata kai. 


Ta tashi ta matso inda nake, "sannu, zaki iya tashi tsaye ko sai na kama ki?".

Nace "zan iya, jikina yayi karfi yanzu".

Tayi dan murmushi, "well, ai dole. Ruwa da kika sha!". Na murmusa kawai ina girgiza kai. A hankali na mike tsaye, karfin jikin nawa ba sosai bane, haka nan na lallaba na shiga bandaki. Sai da nayi wankan ne ma naji jikina ya danyi karfi ma, nayi brush tare da dauro alwala na fito. Janan bata dakin, na zauna na shafa mai tare da bude wardrobe dinta na ciro wata buba ta wani jan yadi mai taushi na saka. Da yake haka na taho shekaranjiya zikal dina, kayanta nake amfani dasu. Don ma yanayin jikinta da nawa kusan daya ne, abinda zan nuna mata kawai cikar kirji, amma bayan haka babu wani bambanci mai yawa a tsakaninmu. 


Na shimfida abin sallah na tayar da sallah, bayan nayi na jero nafilfili, na zauna ina jan casbaha. Janan ta shigo dakin, na bita da kallo tana ajiye wani babban flask, fita ta sake yi ta dawo da gorar ruwa da faranti da cokali. Sai data ajiye sannan ta kalleni, "taso ki ci abinci, ki sha magani".


Sai da tayi maganar abinci sannan naji cikina yana juyawa, ba musu na tashi na cire hijabin jikina na ninke ta da abin sallar. Tun kafin in zauna kamshin kifi ya cika min hanci, naji yawun bakina ya guda. A kasa na zauna muna fuskantar juna, ta turo min plate cike da faten doya. Anyi garnishing dinshi da green beans, peas, alayyahu, hanta da aka yanka kanana, ga kifi da dafaffen kwai a gefe. Ina yin loma daya na lumshe idanuna, kai na hau girgizawa, "ramgwadi! Gaskiya yau ba karamin baje basira kika yi wajen girkin nan ba, meye sirrin?".


Ta kalleni, "ke yanzu nace miki ni na dafa wannan abincin yarda zaki yi? Yanzu na amsa shi wajen Anty Sarah".

Na bude baki cikin mamaki, watakila lokacin da yan kirki suke kan Anty Sarah bamu taba sa'ar cin karo dasu ba sai a wannan lokacin. Iyaka sanina da ita, wannan baya daga cikin halayen dana santa dashi. Amma zata iya yiwuwa dama can hakan take, kila sanin hakan ne bamu taba yi ba. 

Nace "ta kyauta sosai, nagode".

Ta kai cokali daya bakinta, "ta shigo ne taga yanayin jikina fa sai ta ganki da drip a hannu. Dazu kuma sai ta turo Mimah tace in je in amsar mana abinci". Na gyada mata kai. Har muka gama cin abincin babu wanda ya sake yin magana. Bayan mun gama, Janan ta kauda kayan can gefe, ta dauko magungunan ta fara balla tana miko min. Da kyar na iya watsa su a baki na hadiye. Wannan yana daga cikin dalilan da suka sa naki tashi dazu da safe zuwa asibiti yana nufin allura da magunguna, ni kuma bana son allura da magunguna. 


Janan ta harareni lokacin dana hadiye kwayar maganin karshe da kyar, na fara kakari. Tace "dazu ai da ana tsira miki allura a jiki ko a jikinki".

Nace "kema kin san saboda bana cikin hankalin kaina ne, amma ina ji ina gani in zauna a tsira min allura? hauka nake?".

Ta kwashe da dariya, na harareta, "muguwa kawai!". Gwalo ta min kamar wata karamar yarinya. 


Tashi tayi ta dauki kwanukan ta fita. Na lallaba na lalubo wayata daga bayan katifa inda na jefata jiya. Nasan anyi ta nemana babu kakkautawa, musamman ma Muhammad. Na kunna wayar na tsaya tayi loading kafin na bude ta, nayi gaskiya kuwa. Sakonni daga Muhammad sun fi cikin kwando, tambayarshi daya, lafiya? Na hade fuska lokacin dana kula daga cikin sakonnin akwai na Umar, ko kara kallonsu ban yi ba na goge su gabadaya. Na tafi dungurungum nayi blocking dinshi daga wayata. 


Komawa nayi daya bayan daya ina karanta sakonnin shi. Duk karantawar da zan yi, zuciyata kara narkewa take yi cike da begen shi, Allah ya sani, a kullum kaunar bawan Allahn nan kara yado take yi a sassan zuciyata. Ban sani hakan ko abu mai kyau bane ko kuma akasinsa. Kafin in gama karantawa jikina yayi wani irin sanyi, daga cikin kalaman shi kawai, babu tantama zaka karanci tsananin kulawa, tsantsar so, da kauna mara iyaka a cikinsu. Jikina yayi sanyi saboda babu mahalukin daya taba nuna min kwatankwacin irin wannan so, kauna da kulawar da wannan bawan Allahn yake nuna min. A duniya yanzu waye yake damuwa kawai don ya kira wayar wani daga dare zuwa safe ya ji a kashe? Sai Muhammad. Sai daya kai ga tambayar ko dai wani laifi yayi min ne, a cikin sakon. Ina gama karanta shi na lalubo lambar shi na danna kira, ban ma san me zan ce mishi ba. Sai dai cewa aka yi line busy, alamun yana waya. Don haka naci gaba da karanta sauran sakonninshi, nasan idan yaga missed call dina zai kira. 


Janan ta dawo dakin da waya a kunnenta, daga yanayin yadda take maganar da Yaya Bilal take wayar. Hankalina yana kan sakonnin M.B da nake ta nanatawa, kamar wani karatu. Don haka sama-sama nake jin muryarta a kaina. Bayan ta gama ta zauna a gefena, tace "Yaya ne ya kira yana tambayar ko kin tashi nace eh. Yana Funtua shi da Anty Ameerah, wai ya kaita wajen sunan kawarta," ta fada tana tabe baki, ni kuma na dan murmusa saboda yadda ta bani dariya, "yace a duba ki da jiki dai kafin ya dawo". 

Nace "babu komi wallahi, ai na warware".


Tace "yauwa, na ma tuna! Ummah tace tana so ta duba ki itama". Ta ciro wayarta ta kirata, bayan sun gaisa sun yi yar hira, Janan ta miko min wayar na amsa, na gaisheta cike da girmamawa kamar tana gabana. Tace "Janan dai ta goga miki, daga zuwa jinya sai kema ki buge da jinya?", ni da Janan muka yi dariya sosai. Mun jima muna hira da ita, Ummahn su Janan ta iya bi da mutum cikin sanyin kalami kaji ka saki da ita, akwai lokuta da dama da zamu fara hira da ita cikin dari-dari ko rashin sakin jiki, amma cikin dan kankanin lokaci zan ji na saki da ita sosai, inji na hau hira da ita sosai. Wasu lokutan sai daga baya zan zauna ina mamakin hakan. Munyi sallama da ita tana ta zuba mana addu'o'i kamar yadda ta saba, na kashe wayar na mikawa Janan. 


Kwanciya tayi rigingine tana kallon ceiling din dakin, ni kuma na lalubo game din candy crush a wayata ina bugawa. Shiru ya ratsa dakin na dan wani lokaci, can naji tace "Nan da sati biyu Yaya zai tafi umarah shima".

Na kalleta cikin mamakin dalilin da yasa ta fada min, nace "and?".


Ta kalleni tana wani yin kasa-kasa da idanu, "don Allah kizo ki taya ni zama kafin ya dawo!".

Na zaro ido, "wa? Ni?? Ki rufa min asiri in mutu maza su kaini ba mata ba! Ana zaman lafiya, da hankalin kaina, anya kina ma so na kuwa?".

Ta harareni, "yo meye na wani zaro ido? Wuta nace ki zo ki taya ni zama?".

Na koma na kwanta ina dariya, "lallai ma, zama a gidan nan naku ai sai wanda ya shirya, ni kuma ban shirya ba. Jira nake goben nan tayi, idan na cira kafa na bar nan gidan sai kuma baba ya gani. Idan da son rai na ne ma, har in bar Zaria ba zan kara zuwa nan ba!".


Tace "inaa, kema kin san wasa kike yi coz you are stuck with me babe, babu yadda zaki yi dani. Sannan gobe babu inda zamu je sai jikinki ya kara yin kwari sannan, maybe zuwa talata?".

Na kalleta ina dan murmushi cike da jindadi, "babu wani hutu da nake bukata don ni nan garas nake ji na, amma kuma wa zai ki hutu koda na kwana daya ne musamman daga wannan asibitin?". Itama tayi murmushi. 


Karan da wayata tayi ne yasa na kalli hannuna duk da kida na musamman ne, na riga nasan mai kiran. Na turo baki cikin shagwaba, ban san dalili ba, duk lokacin da nake tare da Muhammad, na kan ji ni kamar wata yarinya karama, kamar wata sabuwar halitta. 

Cikin shagwabar na daga, yana ta magana nayi shiru, yace "haba baby na, come on, talk to me mana. Nayi laifi ko? Am sorry!". Nayi shiru ina jinshi ya cigaba da cewa "haba baby na, baki so in ji daddadar muryar nan taki ne? Come on...".


Na turo baki kamar yana gabana, "ba kai bane ka ki daga wayata dazu ba?".

Ya saki murmushi mai sauti, "tuba nake gimbiyata, ina amsa wata waya mai muhimmanci ne. And you are the one to talk, idan maganar gaskiya ake yi ai nine ma yakamata ace nayi fushi. Na ga tun jiya nake kiran wayarki a kashe. Baki ji warin kunar da zuciyata ta dinga yi bane?!".


Ban san lokacin dana kwashe da dariya ba, nace "oohh, da gaske?".

Yace "sosai ma, da yadda nayi ta kiran sunanki. Duk baki ji ba?".

Na sake yin wata dariyar ina girgiza kai cikin wani irin matsanancin farinciki, nace "ban ji ba gaskiya!".

Yace "nayi tunanin gabadaya mutanen Zaria sun ji!". Na cigaba da kyalkyala mishi dariya. 


Mun jima sosai muna kwasar hirar soyayyarmu, har na rasa tracing din lokaci. Lokacin da muka yi sallama dashi, bakinshi yana furta I miss you's da I love you's. Zuciyata fara kal, kamar farar takarda. 

Janan da tunda na fara wayar take kallona baki a dage, ta kalleni tana murmushi, "anyi nisa a lambun soyayya!!".

Nayi dariya ina birgima a tsakiyar dakin, "baki san komi ba Jan... You've no idea. Ya Allah, I love that man!!".

Dariya ta saki, ta taso ta rungume ni, ban san dalili ba, amma nima rungumeta din nayi. Tace "na taya ki murna, dear. Congratulations!". Nayi murmushi. 










#F.W.A



[23/03 9:40 AM] Jiddah Lawal: 🌟 *⋆☆A ZATO NA...!☆⋆* 🌟



        *⋆©Jeedderh Lawals⋆*





                             *☆⋆18⋆☆*






Yinin ranar a daki muka yi shi. Bayan munyi sallar la'asar, Janan ta kunna mana film din X-Men a wayarta muka fara shi tun daga farko. Babu abinda ya dinga tada mu sai sallah da cin abinci. 


Bayan isha'i, Janan ta tado ni muka fita waje, a cewarta kafa zamu dan wasa musamman ni da babu inda na fita tun yau. Ban damu ba, na dauki hijabi ta na saka muka tafi. Garin tun da yamma tayi yayi alamun hadari, ga wani irin zafi da aka yi kamar zai kona mutane. Sai dai zuwa yanzu ya dan yi sanyi, iska mai sanyi yake bugawa a hankali. 

Muka taka ni da ita har bayan layin su, can wajen irin masu suyar wara da doya da fulawa dinnan don Janan tace abinda take son ci kenan yanzu. 

Matar inyamura ce, sana'ar hannu take yi tun karfinta, safe, rana, dare, babu hutu balle kakkautawa. Shi yasa wajenta kullum cike yake da kwastomomi da kuma ma'aikatan da suke kama mata aiki.

Saboda yawan mutane yasa bamu samu mun siya da wuri ba, lokacin da muka tsaya a gabanta, ta kallemu cikin murmushi. Ba laifi mun dan saba da ita, saboda a yawancin lokuta a wajenta muke sayen buns da eggroll da rana. Ta kalli Janan tace "kwana biyu kun dauke mana kafa!".

Ni da Janan murmushi kawai muka yi muka gaisa da ita. Ta kulla mana wanda muka saya a cikin leda, muka amsa muka mata sallama muka juya. 


Cikin rashin sa'a kafin mu karasa gida ruwan sama ya sauka mai karfi, muka daga kafa cikin sassarfa muka kara sauri. Duk da haka kafin mu karasa gida, jikinmu ya jike sharkaf! Har digar ruwa muke yi. Da sauri muka karasa cikin falo, a dan corridor dinsu kafin a shiga falo muka tsaya domin mu dan kafe kada mu bata musu carpet din falo da lema. 

Muna tsaye anan sai karan turo kofa muka ji, muka juya muna kallon Yaya daya shigo shima yana linke umbrella din daya shigo da ita. Muka zaro idanu mu duka a tsorace muna kallonshi, nayi zaton a gidan Anty Ameerah yake yau, ko kuwa ba acan yake ba? Aka fara kallon-kallo tsakaninmu dashi. 

Ba Janan kadai ba, ni kaina sai da naji zuciyata tana tseren tashin hankali. 


Ya hade fuska kamar yaga wasu mala'ikun daukar rai, "daga ina kuke?!". Ya tambaya murya a cune. 

Janan ta fara kokarin ja da baya a tsorace, cikin in'ina ta fara cewa "um... nan.. ne baya!".

Ya daga murya, "ina ne nan bayan exactly?! Ba na hana ki fita waje da dare ba? Ban da rashin hankali kawai sai ku kama kafa ku fita daga gida da dare babu tunanin komi, kuna ganin hadari kuma! Ku duba yanda ruwa yazo ya muku duka, musamman ke da kike rashin lafiya! Karatun da kuke yi kenan dama? Idan fa jikin ki ya kara rikicewa?". Ya maido tambayar kaina. Na dan yi tsalle a tsorace, na koma bayan Janan na lafe kamar ita zata kare ni daga fadan shi. 


Allah ne ya bata kwarin gwiwar iya daga baki don ni gabadaya jikina rawa yake yi, tace "kayi hakuri Yaya, abinci muka fita muka sayo".

Yace "abincin waje a gidana? An hana ku dafa abincin ne? Waye ya hana ku?!".

Janan tayi saurin girgiza kai, "babu ko daya wallahi, kawai mun ji marmarin awara ne, shine muka fita muka sayo. Bamu yi zaton ruwan zai same mu a hanya bane amma kayi hakuri...".

Ya dan sauke ajiyar zuciya alamun ya dan sauko, yace "to shikenan, amma kada ku kara". Muka hau gyada kawuna kamar wasu kadangaru. 

Yace "to ku wuce kuje ku canza kaya kafin wani abin ya kama ku". Bamu jira ya sake cewa komi ba, muka bar wajen a sukwane. 


Sai da muka shiga daki muka maida kofar muka rufe, sannan muka sauke wata nannauyiyar ajiyar zuciya, kafin muka kalli juna muka kwashe da dariya. 

Bayan mun canza kayan jikinmu, mun shanya wadanda muka cire, muka cigaba da kallonmu muna cin awarar. 



*



Washegari bamu tashi da wuri ba saboda mun san cewa ba asibiti zamu je ba. Da muka yi sallar asuba, Janan ta wa wata sister Mairo matron dinmu text akan cewa ba zamu samu damar shigowa ba saboda rashin lafiya, bayan ta turo mata da amsa akan babu damuwa Allah ya bamu lafiya, muka koma gefe muna dariya kafin muka koma barci. Sai wajen karfe tara na safe muka tashi. Janan ta fita kicin zata dora mana abinda zamu ci, ni kuma nayi amfani da wannan damar na shiga bandaki na watsa ruwa. 


Kafin in fito ta dafo mana indomie, muka zauna muka ci ta sake daukar kayan ta fita dasu. Ta dawo ta zauna a kusa dani ina duba wasu textbooks dinta, zuwa yanzu naji na warware sosai, kamar ban taba yin wata rashin lafiya ba, amma duk da haka sai da Janan ta takura min ba sha magani. 

Tace "ki zo muje ki taya ni in yiwa Yaya doughnut da cin-cin don Allah".

Nace "nayi zaton ya tafi?".

Ta girgiza kai, "sai gobe. Abin azumin da za'a fara gobe, yana can babban gida, jiya da yau yayi rabon azumi".


Na ajiye textbook din ina kallonta, "amma banda abinki Jan, saboda Allah me zai yi da doughnut da cin-cin da azumi?".

Tace "ya dinga sahur ko shan ruwa mana!".

Na fashe da dariya ina girgiza kai, "gaskiya Ummah tana da sauran aiki a gabanta wallahi, haka zaki yi aure kije ki dinga soyawa miji cin-cin da azumi?".

Ta mintsileni a gefen cinya tana dariya, "bana son iskanci wallahi, zaki taya ni ne ko yaya?".

Na mike ina laluben abinda zan sakaya jikina dashi, "kin san ni bana wuce tayin kayan zaki dangin fulawa". Muka fita daga dakin muna dariya bayan na dauki karamar hijabi data tsaya a ruwan cikina na sa. 


Gidan shiru, haka falon babu kowa hatta da TV a kashe take. Na san kila sun tafi makaranta, wannan ko kuma suna daki suna barci. Muka fada kicin muka fara aikin daya kaimu. 

Bamu yi minti talatin cikakke ba, muka ji an bude daki an fito. Ba'a jima ba Salama da Haleemo suka shigo kicin din cikin kayan barci, na kallesu na kauda kai cikin girgiza kai. Haka suke yawo wani lokacin a gidan cikin kaya masu bayyana jiki, a ganina duk da a gidan Yayarsu suke ai hakan bai kamata ba. Ba fa kowane mutum bane na Allah. 


Haleemo ta dan dakata data ganmu a kicin din, sai kuma ta maze ta kallemu, wai "sannunku!". Muka yi banza ni da Janan muka kyaleta kamar ba damu take ba. Salama tayi dariyar mugunta tana bude firjin, tace "Allah ya kara, uwar sanabe da neman gindin zama!". Ta dauki abinda zata dauka ta fita daga kicin din ta bar Haleemo a tsaye. 


Kame-kame ta fara, "uhmn, Na'ilah nace., ni fa ban san wannan gayen saurayinki bane! Shi ya fara zuwa wajena, kuma sai daya ne, na rantse da Allah...".

Na katseta ta hanyar juyawa ina watsa mata harara, nace "ni fa kinga Haleemo, idan na raina kasuwa ko sako bana badawa cikinta. Ban tambayeki alakar ki da tsohon saurayi ba ba, ko kallon banza ban miki ba, saboda baki kai matsayin da zan zauna ina cacar baki dake akan wani saurayi ba wallahi. Alfarma kika min babba da kika lallaba kika hillace shi, godiya ma yakamata in miki, don haka ki kwashi jikinki ki bar nan wajen wallahi, duk abinda mutum yayi dai ai kansa ya yiwa, walau mai kyau ko marar kyau!".


Ta saki baki tana kallona, sai kuma ta juya ta bar kicin din da sauri. Naja dan siririn tsaki. 

Da yake kwabin doughnut din da muka yi babu yawa, nan da nan muka gama soya shi. Muka fara na cin-cin din, zuwa lokacin rana ta fara yi. 


Ni kadai ce a kicin din lokacin da Raheemah ta fado kicin din kamar wata kububuwa, Janan ta leka waje zata samu wani yaro ta suka can bakin titi. 

Na gaidata a kaikaice, hankalina yana kan fulawar da nake murzawa.


Maimakon ta amsa, sai naji ta ja dan tsaki, "uhumm, ihunka a banza kenan! Ina amfanin wadda za'a kwace saurayi a hannunta tana zaune? Hakan yana nuna aikin banza ne, kuma abu mai wahala ace za'a iya kwace miji! Don ma dai mutum yaji ya sani, idan ma saboda mijina ne ake min zarya ana min shige da fice a gida, to wallahi mijina yafi karfin haka. Nima kuma nafi karfinshi!".


Allah sarki, naji maganganunta sun bani takaici sun kuma bani dariya, na girgiza kai a hankali ina dan murmushi. Banda tsabar hauka da rashin tunani, har ta wani kalleni tace wai zanyi kwacen miji? Tsakanin ni da ita ko wa yayi kama da wanda zai yi kwace? Na sake girgiza kai. 


Ta kama kugu tana wani jijjiga jika ganin ban tanka ta ba, tace "ke Baiwar Allah dake nake, aha! Ni dai na fada na sake fada miki, mijina yafi karfinki!".

Na juya na kalleta ina murmushi, "ai na fiki sanin haka, saboda haka ki kwantar da hankalinki, mijinki naki ne ke kadai, ban iya snatching ba wallahi!".

Sai ta hau wasu tsalle-tsalle cikin masifa, "dariya ma kike min kenan? Ke wallahi na ga alamun iskancin ki yawa yake yi fa! Ke har kin isa ki zauna kina min ba'a? Wacece ke, yaushe aka haifeki? Aikin banza dana wofi!! An ga mijina mai kudi an makale mishi kamar maganadisu, ana ta wani shige da fice a gida har da rashin lafiyar karya. To ta Allah ba ta mutum ba wallahi, kuma duk dan iskan da yace zai kara dani wallahi shi zai ji jiki. Haka nan za'a koma gida aci gaba da cin tuwon datsa miyar kuka tsanwa, mu dai mun fi karfin mutum!!".


Na janye robar hannuna gefe ina kallonta, raina ba karamin baci yayi da maganganunta ba, amma na danne, nasan so take take raina ya baci in biye mata. Na fuskanceta sosai, ina watsa mata wani wulakantaccen kallo, babu shiri ta shiga taitayinta. Nace "na farko, ban san abinda na miki ba da zaki zo haka kawai ki hau zagina, sai dai bari in tabbatar miki da wani abu daya, I'm not into your husband! Hakan da kike yi ya tabbatar min da cewa ko dai kema kwacen mijin kika yi, ko kuma dama can kwacen samari da mazaje a jininku yake. Kowanne ne dai wannan matsalar ku ce, don ni ban saba ba, ban iya ba, kuma ba zan yi ba. Ke gida da dukiyar miji suka dama, dama don su kika aure shi. Mijinki baya cikin yan kayana, ki godewa Allah, da ba don haka ba wallahi da sai na sa kin zubda hawaye, don haka baiwar Allah, ki shiga taitayinki. Gida ne, daga gobe idan kika kara ganina a cikinshi ki min duk abinda kika ga dama!".


Ta daga baki zata yi magana, amma ta kasa. Tayi haka yafi sau uku, kafin tayi kwafa a fusace ta juya ta bar kicin din da sauri, na ja tsaki ina furta "sakarkaru" a kasan raina. Raheemah sakara ce, daukar zugar kanne da kawaye yana nema ya jefa rayuwar aurenta cikin garari da matsala. Wani abun ban dariya da takaici shine, zasu zuga ta ta wa miji ko danginsa rashin mutunci, ta hau kai ta zauna, su kuma su koma gefe suna mata dariya da ba'a, me amfanin hakan kenan? 


Muna gamawa na koma daki na bar Janan zata gyara kicin din ta kuma hade kan kayan. Na wuce mutanen gidan a zaune su duka, muna kallon-kallo dasu daya bayan daya. Ni har mamaki nake, anya kuwa karatu suke yi? Ita dai Raheemah dama tun daga karatun diploma tace ta yanke karatu, su kuma su Salama da suka zo suka zaune a gidan da cewar karatu suke yi, ba makarantar suke zuwa ba. A sati idan suka je sau uku, to wannan shine highest. Babu aikin da suka iya sai kinibibi da gulma. Ban san daga ina Raheemah take samun idea din wai saboda Yaya nake zuwa gidanta ba, abin is so absurd. Tunanin hakan a karan kaina idan nayi sai inji kaina yana juyawa. Na dauki kudurin daga wannan lokaci, ni da gidan Yaya sai dai ziyara amma banda kwana. Ziyarar ma da ace har in gama karatuna in bar Zaria ban kara yin ta ba, da naji dadi. 


Karan wayata ya katse min tunanin da nake yi nayi nisa a tunani ko karan ban ji ba sai daya kusa katsewa. Yana katsewa aka sake kira, na dauka naga Yaya Mudatthir ne, don haka na daga. Bayan mun gaisa da tambayar mutanen gida, yace ya ba wani abokinshi da zai je Kaduna gobe sako zai kawo min, zai tsaya ya kwana a Kano sai ya taho da safe, ina ganin zan iya fitowa bakin hanya in karba? Nace mishi ehh, yace to ya bashi lambar wayata zai kira ni. Nace to, tare da mishi godiya, muka yi sallama. 


Komawa nayi kan katifa na kwanta zuciyata cunkushe da tunanika, har Janan ta dawo dakin hannu dauke da plate shake da abubuwan da muka yi. Ranar su muka yi ta ci ko abinci bamu nema ba. 


Washegari talata aka tashi da azumi. Bayan mun shirya, mun saka uniform dinmu, muka wuce asibiti. Allah ya taimaka wanda zai kawo sakon muna fita ya mana waya, don haka muka tsaya muka amsa muka wuce asibiti. Hostel kawai na wuce na ajiye su ko dagawa ban yi ba, muka wuce ward dinmu. 










#F.W.A

[23/03 9:40 AM] Jiddah Lawal: 🌟 *⋆☆A ZATO NA...!☆⋆* 🌟



        *⋆©Jeedderh Lawals⋆*





                             *☆⋆18⋆☆*






Azumi bai taba bani wahala irin na ranar Alhamis ba. Muna dawowa daga hutun sallah zamu zana wata irin exams da suke kira 'council exam', wannan exam ita zata yi deciding din kasancewar ka nas a cikin wannan shekarar ko kuma akasin hakan. Don haka hankulan kowa a tashe yake, karatu kowa yake yi babu sassautawa balle takaitawa. Ga projects da suka sako mu a gaba. Kafin mu gama projects uku zamu yi, bayan mun gama TP dinmu munyi daya, yanzu haka preparation din proposal muke yi cikin wannan azumin. Ga kuma wani da muka fara cikin wannan satin. Yanzu haka dawowata daga cikin makaranta kenan ganin supervisor dina, wani inyamuri mai dan banzan rashin mutunci. Allah kadai yasan wahalar daya bani yau. Nayi zarya zuwa department dinmu ta kai sau goma yau, yana cewa inje in dawo, hawa bene ma kadai ya isheni. Cinyoyina masifar ciwo kawai suke yi, ga rana, ga azumi. Tun ruwan ranar Lahdi da aka yi ruwa ya mana duka, ba'a sake yin ruwa ba har yanzu, dama daminar ba karfi tayi ba. 

Komawata ofishin Mr. Akafyi a karo na kusan goma, na riga na rantse na kuma maya, wannan karon idan naje ya sake cewa inje in dawo, to warewa ta kawai zanyi, in yaso na dawo washegari. Don na gaji. 


Na sameshi da daya dalibar da aka hado mu wajenshi da ita a zaune akan lumtsumemiyar kujerar ofishin suna kwasar hirar abinsu. Dama ina jin kishi-kishin cewa mutumin irin yan adawa da musulmai ne, duk mai saka hijabi da nikabi, apparently shi a wajenshi makiyi ne. Nayi kwafa a kaikaice, wato ita wannan da yake tasha izgar doki aka ta fiddo cinyoyi da hannuwa waje, zai iya bata lokacinshi kacokam a kanta, tunda zai iya taba ta yadda yake so, duba da irin zaman da suka yi. Duk da akan teburi ne, sai da yayi yadda yayi yake taba hannunta. 


Na gaida shi ya amsa yana wani cijewa, Allah kadai yasan iya dauriyar da nayi ban sakar mishi tsaki ba. Da ace ina da hanyar da zan bi a canza min supervisor, wallahi da da gudu zan bita, a canza min shi in huta. Sai dai a babbar makaranta kamar wannan, babu wani abu da yake zuwa ta sauki ba tare da hanya ba. Wadanda suke samun wannan garabasar it's either iyayensu suna da kudi, ko sun san wasu da suka san wasu manyan a cikin makarantar, ko kuma ke kinsan wasu manya a cikin makarantar, ta nan ne kawai zaki samu yanda kike so. Ire-iren mu mu ya-ku-bayi, da bamu san kowa ba kuma kowa bai san mu ba, haka nan muke cije duk wani wulakanci ko kaskanci da za'a nuna mana, muyi ladab, domin mu samu mu gama karatunmu cikin sauki ba tare da an janyo mana wata matsala da zata fi karfinmu ba. 


Kusan mintuna na talatin a ofishin shi, yana min bayani amma rabin hankalinshi yana kan yarinyar dake gabanshi, abin ban takaici shine daga gani yayi diya da ita in ma ba jika ba. Nayi Ala-wadai a cikin zuciyata, na samu ya sallameni ni dai na bar musu ofishin, in yaso ma su cinye kansu kowa ma ya huta. 


Bayan na fita daga makaranta na tsaya a banki da niyar cire wata naira dubu daya da nayi tanadinta a cikin akawun dina. Abin ban haushi da takaici sai da layi yazo kaina bayan na sha uwar rana da jira, wai kuma suke ce min 'insufficient balance', haushi yazo min iya wuya. Na gwada ciro naira dari biyar, shima a lokacin suka ce babu. A matukar fusace na karasa hostel. Na san ko hauka nayi ba zan cewa Baba ya turo min kudi ba. Ni yanzu haka taraddadin yadda zan ce ya turo min kudin jarabawar da zamu yi nake yi. Kudi ne kusan naira dubu hamsin da doriya. 


Na haye kan katifa na kwanta kawai na lumshe idanuna, gajiya, tunani, yunwa, zafi kai komai ma, suka taru suka min rubdugu sai dana rasa ina zan jefa kaina inji sauki a ciki. Sai da yamma tayi likis, ban ma sani ba sai da Esther ta fara tambayata wai yau ba zan yi dafe-dafen karya azumi ba? Sannan na mike ina dingishin wahala. Sauran kayan miyar da suka rage min basu da yawa, dama nufina idan na ciro kudin in tsaya a kasuwa in siyo kayan miyar in kuma karo wasu abubuwan, to kuma ga abinda ya faru. Sauce nayi, na dafa farar spaghetti da zan ci da ita. Nasan zasu isheni in sha ruwa in kuma yi sahur. 


Na sauka kasa dakin wata student da take saida ruwan sanyi da kankara, na sayo. Zobon dana yi saura jiya na kara gyarawa na juye a cikin jug. Naje na dauro alwala na dawo na zauna akan abin sallah ina lazumi har aka kira sallah. Na dauko dabino kwara uku da Yaya Bilal ya bani ranar talata, irin yan makkah dinnan gida hudu, nasan har azumi ya kare ina ci, na ci. Sai da nayi sallah sannan na ci abinci. 

Ina gama sallar isha'i naji wata irin gajiya da kasala ta saukar min, haka nan na daure nayi tarawihi. Zuciyata na rada min in kwanta kawai in huta, it has been a long day, yayin da wata take kara karfafa min jiki akan in dai daure in tafi karatu. Bayan dogon nazari da saka da warwara dai na daure na warci wayata da littafai na tafi aji. Kwana biyu ko zaman kallon ma bana yi. Yawancin fina-finan da nake kallo kafin, ko lokacin sallar tarawihi ake yinsu, don haka na ajiye su gefe. Idan na samu lokaci ina hawa YouTube in kalla dai. Yanzu ma nasan idan na shiga common room ba karatun zanyi ba, shi yasa na fara zuwa class.


Karfe sha daya tana yi, na fara haramar hada kan kayana. Na rungumi littafan dana dauko na fito daga cikin theatre hall din. Yanayin wajajen musamman da dare, zaka ji shi shiru, babu zirga-zirgar komi sai ta ababen hawa da basu cika yin wajen hostel din ba sai da can babban titi sai kuwa dalibai da suke zuwa aji ko kuma masu dawowa. Na kan ji yawancin mutane suna korafin tsoron wucewa ta wajen da dare, sai dai ni ban taba ganin dalilin da zai sa naji tsoron ba. Naga a cikin waje mai tsaro muke, idan ba wani Iko na Allah ba, babu abinda zai faru da mutum. 

Idan nayi addu'ata na shafa ni kam shikenan, sai in jona earpiece in done kunnena, in rufe komi kwata-kwata sai karatun da nasa, ko kida ko kuma wa'azi. Babu irin yanayin da nake matukar so irin wannan. Na kan ji ni free, without worries. 


Yanzun ma abinda nayi kudirin yi kenan, musamman yadda ranar yau ta kasance min. Ji nake kamar inyi tsuntsuwa in ganni akan katifata. Sai dai banyi nisa da fara tafiya ba, kiran Muhammadu na ya shigo wayata. Ina jin wannna muryar tashi yana ambatar "baby na!", I was a goner. Mantawa nayi da komi dake cikin duniyar nan, har ni kaina kuwa, sai shi kadai. Rakiya ya min har cikin dakin da nake, muna ta hirarmu cikin raha, kafin muka yi sallama dashi. Na cire kayana na sa na barci na dauro alwala nazo na kwanta. 

Karfe uku alarm din dana sa ya buga na tashi, na fita na dauro alwala na zo na fara nafilfili har lokacin sahur yayi, nayi na sake tado wata sallar har dai aka kira sallah nayi na zauna ina karatun Al-Qur'ani kafin lokacin fara shirin shiga cikin asibiti yayi. 



Kamar yadda nayi tunani, maganar kudin jarabawa bata zo min da dadi ba. Yadda Baba ya rufe ido yana masifar shi bashi da kudi, ina nema in tatuke shi, abin ya bani mamaki. Tun bayan kudin school fees daya turo min, naira dubu goma ta sake hada ni dashi. Yanzu kusan wata na biyu kenan a Zaria, amma ba halin in daga baki inyi maganar kudi sai ya hau zagina. Ko provision yawanci Yaya ne yake turo min su, sai kuwa kudin da yake turo min jifa-jifa, dasu nake amfani in sayi kayan bukata. Bayan doguwar wayar da muka yi dashi a ranar Assabar kenan, daki na koma na kwanta. Esther ta tafi weekend gidan kawunta, Maimunah kuma bata ma dakin tun jiya, babu wanda yasan inda ta tafi. Don haka ni kadai na kwana a daki. 

Nayi lamo akan katifa cikin tunani iri-iri, kala-kala, ban taba jin karatun nan ya fita a raina ba sai yau. A raina na raya wai da wanne ake so inji ne? Abu ne da bai taka kara ya karya ba, wanda na tabbata yafi karfin Baba, amma kullum cikin ja wa kanshi babu yake, kullum babu, kuma babun a kaina kadai take. 

Yawancin matsaloli irin haka idan suka taso dama sai dai in tuntubi Yaya da maganar, idan bata fi karfinshi ba ya maganceta, in kuma tafi sai ya kai ga dangana da su Malam. To ita kuma rayuwa ba zai yiwu taci gaba a haka ba, ba zai yiwu ace kai kullum cikin bani-bani da a maka-a maka kake ba, kowa ma dama zai ji ya gaji. 


Sai dai idan nayi duba ta wani bangaren, sai inga yaushe na cika bani-bani kamar yadda Baba yace? Tsakanina dashi kawai kudin handout ne, sai abinda yaga dama ya dan lafo min ciki kawai. Dama can yawancin hidima da dawainiya Yaya ne yake yi, idan aka samu ya biya school fees da kyar, ya hado min provision, to sauran fa sai dai yadda hali yayi, sai na sha matukar wahala ya kuma yazga ni yadda yaga dama sannan zai turo min na bukatun yau da gobe. To maganar gaskiya na gaji yanzu, yanzu haka kwanciyar da nayi ina tunani, tunanin hada kan kayana nake in koma gida kawai, azabar ta isa.


Sai kuma naga idan ma na koma, ni zan kwari kaina, babu wanda zai ji a jikinsa dai sai ni. Don haka naci gaba da tunani ina laluben mafita. Nasan mafita daya itace in fadawa Yaya, amma gani nake kamar abin yayi yawa. Shi shikenan kullum cikin ji da matsalata, kullum babu hutu?. 


Ban tashi daga kwanciyar ba sai da aka kira Sallar azuhur, ashe wani wahalallen barci ne ya daukeni. Wani irin barci mai dauke da wasu irin sarkakkun mafarkai. Na tashi ina mika da hamma, maimakon inji gajiyata ta tafi, sai naji kamar an dauko gajiyar duniya ne an dora min aka. Haka nan na lallaba na watsa ruwa a jikin nawa ya dan min karfi, sannan nazo nayi sallah. 


Ina cikin karatu Janan ta kirani. Roko na ta dinga yi akan inje in mata weekend, kai tsaye nace mata a'ah, ta dawo tana magiyar to inje in tayata shan ruwa, nan ma nace a'ah. Ni dai tunda na samu nayi sa'a, Allah ya taimakeni na baro gidan, ai an wuce wurin. Ta gaji tayi fushi ta ajiye wayar. Da yake ba a cikin yanayi mai dadi nake ba, kyaleta nayi kawai. 

Yinin ranar haka na yi shi sukuku, can da yamma wai sai ga Maryam, mun gaisa da ita gari-gari, wai in na shiga kasuwa in sayo mata sarka da yan kunne idan ma naga da halin takalmi in karo, naji kamar in hau rusa mata ihu na dai cije nace mata to kawai, na ajiye wayar. 



*



Dole kanwar naki haka na dage na kira Yaya zuwa ranar talata, domin duk ta inda na buga abubuwan babu sauki, babu wata mafita. Na zayyane mishi matsalar da muke ciki da Baba, Yayan yayi shiru yana tunani, kafin daga baya yace zai kira shi sai yayi mishi bayani. Na mishi godiya nace to, na kashe wayar. 

Allah ya taimakeni cikin satin aka turo mana kudin scholarship da aka saba bamu. Kuka ne kadai banyi ba ranar saboda murna, dama nayi karaf, bani da ko sisi. Haka kayayyakin da suka rage min duk sun tasamma karewa. Yawanci idan aka turo min ina fadawa Baba, amma wannan karon da yake a wuya nake da kowa, babu wanda yaji labari. Kasuwa kawai na fada. 



*


Abu wasa-wasa, tun ana yau azumi, har gashi mun zo mun ci tsakiyar shi. Yaya ya samu ya shawo kan Baba da kyar ya turo min kudin, naje na biya. Allah ya taimakeni basu kai ga rufewa ba. Abubuwa zuwa yanzu sun yi min sauki nesa ba kusa ba, ba kamar satin daya gabata ba. Ban bar wannan abin ya dameni ba ko kuma ya hana ni aikata abubuwana na yau da gobe. Allah ya kan jarabci bawanshi ta kowace irin hanya. Zata iya yiwuwa ta kankanin abu, ko babba, ko iyaye, ko 'ya'ya, ko cuta, ko kuma sauran abubuwa. Na yarda hakan yana daga cikin jarabawata, don haka ban damu ba sosai. Fatana Allah ya bani ikon cinyeta. Nasan watarana idan da rai, hakan zai zamo tamkar ba ayi ba. Don haka nake godewa Allah a kullum, kuma a koyaushe. 


Jiya Yaya Bilal ya tafi Umarah shi da Anty Ameerah. Ba'a tafi da Raheemah ba saboda last year da ita aka je a cewar Janan. Bata ji dadin hakan ba, saboda haka sai da suka dan yi rikici da Yayan akan wai yana gwada mata rashin adalci kafin ya tafi. Bayan tafiyar tashi kuma sai abin ya koma kan Janan, tsangawamar yau daban, ta jibi daban. Wai kicin ma suke rufe mata yanzu, bayan da Yayan zai tafi sai daya cika kicin din ya batse shi da duk kayan amfani. Nace ta kira shi a waya ta gaya mishi mana, tace wai bata son ta dinga tada musu zaune tsaye, nace "ai sai kiyi tayi!". 

Kawai sai ganinta nayi da dubu dai-daya har guda goma, wai inji Yaya inyi sayayyar azumi. Abin ya bani mamaki matuka, na karba nayi godiya. Da yake ma hannuna da kudi, cikin wannan satin wata karamar kwangila da Yaya yayi ta fito, cikin kudin da aka samu ne nima ya dan tsakuro min. Na hada su waje guda na ajiye ban tasar musu haikan ba, nasan a hankali a hankali idan na tattala zasu dade min. 


Tunda Yaya Bilal yayi tafiyar nan, kusan kullum anan wajena Janan take shan ruwa. Wasu lokutan ma sai mun gama sallar tarawihi sannan take tafiya gida, idan kuma Allah ya taimaketa Is'haq ya shigo ta nan wajajen, sai ya dauketa su tafi. 


Kasancewar ba wani dogon hutu zamu yi ba, yasa na yanke shawarar bin Janan Kaduna kawai inyi sallata acan. Don haka na lallaba Maryam ta karban min kayan sallar da aka bani, atamfa da leshi da takalmi kala daya, ta bayar ta motar haya aka kawo min na kai wajen dinki. Tun dai ana saura kwana biyar muyi tafiyar na kira Baba na fada mishi, yace babu laifi. 

Shi dama Yaya da yake ya riga yasan Janan, itama wasu lokutan idan muka samu hutu gajere muna zuwa Gashua da ita. Sannan idan Allah yasa yayo ta wajen Zaria ya biyo mu gaisa, suna haduwa da ita. Ya santa sosai har su Ummahn, saboda haka koda na fada mishi acan zanyi sallah cewa yayi hakan ma yafi, tunda yafi kusa. Shima dubu biyar ya turo min wai in samu karamar atamfa in saya in dinka, na mishi godiya sosai kuwa. 


Ranar da muka dauki azumi na ashirin da takwas, ranar muka wuce Kaduna. Sallah ta rage kwana biyu ko daya kenan. Itama Ummah a daren ranar zata dawo, yayin da Yaya Bilal kuma sai washegari.










#F.W.A

[26/03 8:03 AM] Jiddah Lawal: 🌟 *⋆☆A ZATO NA...!☆⋆* 🌟



        *⋆©Jeedderh Lawals⋆*





                             *☆⋆19⋆☆*






Ranar sallah muka sha kwalliyarmu, da safe muka bi yaran gidan muka je idi. Jiya da dare bamu kwanta da wuri ba saboda hidimar abincin sallah. Mun yi miyar taushe, aka soya nama, kaji, har da su snacks. Da safe da zamu tafi idi muka bar yan aiki suna soya masa ta farar shinkafa. Don haka muna dawowa aka fara rabon abinci, gida-gida. 

Ummah mace ce mai mutane sosai, saboda haka yinin ranar mutane ne yara da manya, yan gida ko yan unguwa, suna ta shigi da fici kamar wata hidimar biki ko suna. 


Gidansu Janan babban gidane, Alhaji Salisu Makarfi mahaifinsu Janan babban mutum ne kuma dan dangi, tsohon soja ne amma yanzu yayi ritaya. Kafin ya auri Ummah yana da mata wadda ta mutu ta bar manyan 'ya'ya maza har su hudu, bayan sunyi aure da Ummah kuma ta haifi Janan, daga baya ne ya sake aurar Usaina babar su Harira da suke kira Yaya. Mutum ne shi na mutane, ya kuma rike zumunci sosai, shi yasa iyalanshi suka taso cike da zumunci da kauna ta yan uwantaka, idan kaje gidan baka banbance dan gida dana waje, baka banbance dan daki da dan daki. Yawancin diyan yan uwanshi a gidan suka girma har suka riski lokacin aure wasu kuma tare da nashi diyan suka yi makaranta wanda shi yake biya musu kudin makarantar. Shi yasa kullum baka raba gidan da mutane. 

Samarin gidan da suka taso a gidan, ko bayan da suka yi aure, wasu lokutan idan kaje gidan zaka gansu ko a kofar gida, ko kuma a cikin gidan karkashin daya daga cikin bishiyoyin gidan suna hutawa ko suna hira. Da yake babban gidane, akwai part daban da aka ware wanda mazan gidan suke amfani dashi. 


Yau ma haka gidan ya wuni, jama'a ta ko'ina musamman yara jikoki. 

Muna dakin Ummah da yammacin ranar, yawanci duk kowa ma a dakinta yake. Ummar yara ma suke ce mata, yayin da suke kiran mahaifinsu Baban yara.

Nayi kwalliya cikin leshin da Baba ya bani, Janan kuma atamfa ta saka. Mu kusan biyar ne a dakin, Ni, Janan, Harira da Firdausi diyan Yaya sai wata Umaimah matar Yayansu Haneef. Danta Shamsu yana kan cinyata yana wasa da motar roba ina taya shi, hirarsu suke yi cikin raha, ni kam rabin hankalina yana ga hirar da suke yi, rabi kuma yana kan tunani akan Muhammad. Yace min zasu shiga can cikin wani kauye a Benin field work tun cikin azumi, yace ba lallai mu dinga samun damar yin waya dashi ba, amma fa yana min text kullum. Nayi tunanin zasu samu su fito daga kauyen tunda yau sallah, amma shiru kake ji. Yau ko albarkacin text din nashi ma ban gani ba. Tun safe nake zuba ido akan wayata, da naji tayi kara sai in zabura in wawureta a tunanina shine, sai inga wani ne daban. Wani lokacin har tsaki nake saki a kule.

Na tura mishi text amma shiru ba reply, idan kuma na kira wayarshi sai inji a kashe. Jikina ya fara sanyi. Nayi kewar mutumin nan, ina kan kewarshi. Sati biyu da muka yi bamu waya dashi, ji nake kamar shekaru biyu ne. Ban san cewa nayi mugun sabo dashi ba sai a wannan lokacin.

Janan ta tabo ni, nayi sauri na kalleta, ban san lokacin da Shamsu ya sauka daga jikina ba, sai yanzu na kula da cewa yana hannun mahaifiyarshi yanzu. Ta kalleni cikin nuna damuwa, da baki ta min alamar tambayar "lafiyarki lau kuwa?".

Nayi saurin girgiza mata kai, alamun babu komi. Nayi kokarin saka bakina cikin hirar da suke yi akan samarin su Harira muna ta kwasar dariya, amma fa lokaci zuwa lokaci idanuna su kan sauka akan wayata cikin fata. 


Ummah ta shigo dakin da sauri, su Yaya Hafiz sune manyan mazan gidan. Shine na farko, suna ce mishi Babba saboda sunan mahaifin Baban Yara gareshi, sai Yaya Auwal, Yaya Haneef da Yaya Kabeer. Janan itace take bi musu, sai Harira, Firdausi da kuma auta Faisal, kanin Janan ne. Shekarunshi sha daya yanzu. Yaje gidan Yaya Hafiz hutunshi na sallah Abuja shi yasa bamu hadu dashi ba. 

Karamar walima ce suke hadawa, a lokaci irin wannan, duk suna taruwa a gidan duk da kasancewar suna garuruwa mabanbanta wajen aikinsu duk cikinsu Yaya Haneef ne kadai yake zaune a Kaduna. Ina ga saboda kara karfafa zumuncinsu ne. Ummah ce akan hidimar hada musu abincin da zasu ci, shi yasa tun dazu ta kasa zaune tsaye ita da Yaya, mu kanmu tare damu aka yi aikin abincin da rana, sai bayan mun gama ne sannan muka yi wanka muka shirya. 


Tace "wai dama kuna nan a zaune kuka barmu da aiki? Ku taso maza-maza aje a shirya wajen can, har sun fara zuwa".

Firdausi tace "Ummah ai kece da kin daukar shawara wallahi, sai da Yaya Babba yace za'a dauko wadanda zasu kula da hidimar nan, kika ce a'ah, sai anjima kuma kizo kina ta jajen ciwon kafa da baya!". Su Janan suka kwashe da dariya, nayi dan murmushi ina girgiza kai. 


Ummah ma dariyar tayi, ta wa Firdausi dakuwa, "karbi nan ja'irar yarinya kawai. Da karfina da lafiyata sai in ki hidimtawa diyana? Idan suka dauko yan aiki ni ina zaune, to meye amfanina kenan?".

Harira tace "ki huta mana Ummah, muma kinga da yanzu ai bamu tashi daga zaman nan ba!".

Ummah tace "wai zaku taso ko kuma sai na zo na tada ku?". Babu shiri muka tashi gabadayanmu, muka bar Umaimah a falon. 


Can bayan gidan inda aka ware musu kicin dinsu na gargajiya muka wuce tunda acan ake aikin. Akwai makeken kicin daya sha kayan zamani na yayi, amma ya zama na kwalliya kawai. Saboda basu cika amfani dashi ba, idan kaga matan gidan a ciki sai dai idan karamin abu ya kaisu, dafa ruwan zafi ko kuma wani abu dai. Yaran gidan ne ma suke amfani dashi. 


Tuni an riga an zuzzuba komi a cikin abinda ya dace, saboda haka muka fara daukar kayan tare da wasu daga cikin yan aikin zuwa sashen maza. Babban falo ne sosai daya saitin manyan kujeru, dinning room shima babba, sai kuma dakuna. A dinning room din muka shirya komi, wasu daga cikinsu suna falo suna hira, wasu kuma suna waje yayin da wasu suke can kofar gida.

Muka shirya komi da zasu bukata, hatta da cokali, drinks da ruwan sha sai da muka ajiye komi sannan muka bar wajen. 

A cikin yan hirar falon muka hango Yaya Bilal da Yaya Jameel a zaune, suna ta hirar sports da Yaya Auwal. Yawan zuwa yasa suka saba da yan gidan musamman mazan kasan zumunci irin na maza, shi yasa in ka gansu kamar yan uwa. 

Zamu wuce Yaya Jameel ya kira Janan, mu kuma muka yi gaba. Can ta biyo bayanmu da kudin barka da sallah wai inji shi. Yau kam barka da sallah da muka samu daga yan gidan, da baki masu zuwa gidan Allah kadai yasan iyakarta. Ban taba zuwa sallah gidan ba sai wannan karon, shi yasa abubuwan duk suke zuwa min a mamakance. 


Daga nan makotan su Ummah muka wuce, kannen Al-Mustafa suka zo muka hadu dasu ana ta cafta da kashe flashes din hotuna, kamar kada yinin ranar ya kare. Bamu samu kanmu ba sai da dare. 


Muna falon Yaya da dare, hayaniyar gidan ta ragu kowa ya tafi gida, wasu kuma sun nemi makwanci. An gyara ko'ina ya fito fes, yana ta kamshi. 

Janan ta ritsa ni da tambaya akan abinda yake damuna, nace mata babu komi. 

Tace "wai karamar yarinya kike son maida ni ne? Tun da safe fa a haka kike, kina da wanda zaki gayawa matsalar ki ne bayan ni?". Ina shirin bata amsa da wata babu komi din, Firdausi ta shigo falo hannu dauke da babban tray da aka hada fruit salad a ciki. Dama shi muke jira, don haka duk muka sauka kasan carpet din dakin muka zauna. 


Shiru babu wanda yayi magana tunda muka fara ci, sai talabijin da take ta faman aiki kawai duk da ba kallon ba muke yi. Firdausi ce ta fara sako hirar, cikin alamun gulma tace "ni fa nayi zaton Anty Ameerah zata tsaya ne anan, ko kuma tazo yau".

Da yake ta Kaduna suka sauka, sai da suka fara biyowa ta nan a jiyan. Gabadayanmu munyi zaton anan zasu zauna, har Ummah ta fara maganar azo a gyara musu daki, sai kuma suka ce wucewa zasu yi, amma shi Yayan zai dawo yau. Babu wanda ya tambayesu dalili. 


Janan tace "lallai ma, wasa kuke yi da Anty Ameerah wallahi. Jiyan ma ganin idon Yaya ne yasa tazo, da ita kadai ce wallahi ko yace tazo ba zata zo ba".

Firdausi tace "amma dai kinsan tafi Anty Raheemah ko? Na tabbata ko tare suke da Yaya ba lallai tazo nan ba".

Harira tace "kinsan ai tunda Ummah ta hana aurensu da Yaya Bilal daga farko, take kulle da ita. Amma ni nafi son ta akan Anty Ameerah wallahi, bata da kirki ko kadan!".


Janan ta gyada kai cikin amincewa, yayin da Firdausi ta jefa mata harara, da yake shekara daya ce a tsakaninsu, kusan kansu tsaya, zasu iya yin sa'a da Maryam. Tace "Lallai ma baki san kirki ba, ke ni fa da mutum ya dinga gwada min mutunci saboda ganin ido, gwanda muyi ta zuba rashin mutunci dashi nasan dama can ba so na yake yi ba!". Kafin kace me! Muhawarar ta koma kan wanda aka fi so tsakanin matan Yayan. Nan da nan falon ya rikice da hayaniya. Ni kam ina gefe, ina zuba musu dariya idan wata ta fadi abin ban dariya. 


Yaya ta shigo falon, muka yi tsit muna kallonta. Tace "idan kuka kuskura daya daga cikin Yayanku yaji wannan magana sai ya bata muku rai. Ina ruwanku da rayuwarsu? Ba tasu bace ba? Kuma kuji da taku mana!". Ta shige dakin barcinta. 

Muka bita da kallo har ta shige, hirar dai ba'a daina ba, dorawa aka yi daga inda aka tsaya sai dai wannan karon cikin yin kasa-kasa da murya.


Firdausi ce mai cewa "ni wallahi wani lokacin har tausayi yake bani, kamata yayi ace zuwa yanzu ya samu yayi settling a waje daya, da matanshi da 'ya'yanshi. Amma ace kullum yana hanyar Abuja, Kaduna da Zaria? Baya gajiya ne wai?". Duk maganar da suke yi sai lokacin na gyada kai cikin nuna amincewa, ni kaina ina mishi wannan tunani. Sai dai a ganina, hakan duk shi yaso. Kasan cewa matan nan a karkashinka suke, to meye na zama kana rara-gefe akan tituna kamar wani mara galihu? A ganina idan ya nuna musu karfin ikonshi na mijin da yake aurensu, a sukwane zasu bishi. 


Harira tace "ni kaina wallahi ina tausaya mishi, ko meye mafita a rayuwar aurenshi?".

Janan tace "aure kawai ya kamata yayi. Ya samu wata rikakkiya da tasan sirrin rayuwa ya aura". Suka fara gyada kai da sauri. 


Kofar da aka turo aka shigo yasa muka maida kanmu can. Yaya Bilal da Yaya Jameel suka fado falon, jin mu kake yi munyi kus, kamar ruwa yaci mu. Har suka zauna akan kujerun falon. Yaya Jameel ya kallemu cikin murmushi, "gulmar me ake yi ne?". 

Da sauri muka hau girgiza kai, Firdausi tace "laa, babu komi Yaya. Kawai hira ce muke yi!". Yaya Jameel ya kwashe da dariya. 


Cikin yayun biyu, shine mai fara'a da faram-faram, yafi Yaya Bilal sakin fuska nesa ba kusa ba. A sauran halayya ma suna da banbancinsu, duk da ko a kamanni ma suna da banbanci. Shi Yaya Jameel yafi kama da Ummah da Janan, daka gansu shi da Janan kasan kaga yan'uwa. Shi kuwa Yaya Bilal ina tunanin ko mahaifinsu ya dauko, saboda kamanninsu da Ummah ba wai wani can bane. Sai dai kawai abubuwan da ba'a rasa ba, wanda haduwar jini yake haddasawa. 


Duk muka gaida su cikin girmamawa suka amsa. Yaya Bilal ne yace "ina Yaya?".

Firdausi ta tashi taje ta kirata, tare suka fito da ita, ta samu kujera dan nesa dasu kadan ta zauna. Suka dan zame daga kujerar suka gaida ta, ta amsa cikin fara'a, bayan sun gaisa suka ce mata wucewa Zaria zasu yi yanzu, tace "ba zaku hakura ku kwana ba ku kuwa? Dare ya fara yi, karfe tara fa!".

Yaya Jameel yace "ai babu komi Yaya, in shaa Allah zamu isa lafiya, nan ne da Zaria fa".

Tace "to shikenan ai, Allah ya tsare ya kuma kiyaye hanya. Ubangiji Allah ya albarkaci rayuwa data iyali". Duk suka amsa cike da jin dadi, suka mata sallama suka bar falon muma muna musu Allah kiyaye. 


Suna tafiya muma duk muka tashi. Dakin mata muka wuce muka yi shirin kwanciya. Kananan kadajen kwatako guda uku ne a dakin, sai spare din katifa, ita nake shimfidawa ina kwanciya akai. Ni kam ina kwanciya na rufa da bargo har ka a kaina, ina jinsu har lokacin suna tafka mahawararsu naki motsi. Damuwar cikina na ma ta ishe ni. Shirun Muhammad ya tsorata ni, ko dai shima irin na Umar zai min??!.




*



Kwana biyu hidindimun sallah sun riga sun wuce, amma banda gidan su Janan. Har yau wannan gida a cike da iyali yake yini. Yau Assabar, kwana biyar da gama sallah kenan, gobe kuma muke shirin komawa Zaria. Har yau shiru babu labarin Muhammad, nayi text har na rasa abinda zan rubuta tunda wayar bata shiga, ina cikin damuwa. Wani laifi na mishi dana cancanci wannan hukunci haka? 

Yau tare muka wuni da iyalan Yaya Hafiz, sai yau suka zo tasu barka da sallah din. Matarshi mace ce mai mutunci da sanin yakamata, haka ma 'ya'yansu masu shiga rai. 

Da yamma da kanta ta saka mu a mota dasu Harira muka shiga kasuwa tayi musu sayayyar komawa makaranta. A makarantar yanmata ta kwana ta FGGC Munjibir suke. Muma sai gamu mun shigo cikin sayayyar. Muna dawowa suka mana sallama suka tafi.


Washegari muma muka yi sallama da su Ummah, suma su Firdausi da safe aka tafi aka kaisu tasu makarantar. Mun fito daga dakin Baban Yara, mutum mai tsananin mutunci da kirki, yana ta mana addu'o'i da fatan alkhairi, muka samu su Ummah a falo. Tuni an fitar mana da kayanmu waje, nan muka musu sallama, har waje suka raka mu suma. Direban da zai kaimu yana tsaye a jikin motar gidan, yana ganin fitowarmu ya shiga ya tayar. Muka sake sallama dasu Ummah muka shige motar, direba ya ja muka fita daga gidan muka dau hanyar Zaria. 











#F.W.A

[26/03 8:56 PM] Jiddah Lawal: 🌟 *⋆☆A ZATO NA...!☆⋆* 🌟



        *⋆©Jeedderh Lawals⋆*





                             *☆⋆20⋆☆*






Tun da asubahi naji wayata tana kara babu kakkautawa, washegarin ranar da muka dawo kenan wadda ta kama litinin. Ko a cikin nisan duniyar mafarki, nasan kalar ringtone din, na kuma san ko waye mai kiran tun ma kafin in duba. Saboda haka duk da a cikin magagin barci nake, ban kasa rarumar wayata ba na latsa tare da kaita saitin kunnena na fara watsowa Muhammad tambayoyin da suka jima suna susar bangon zuciyata:

"Muhammad! Lafiya dai ko? Kayi rashin lafiya ne? Accident kuka yi a hanyarku ta dawowa daga Benin? Ko kuma wayarka aka sace maka ko ta lalace? Kayi welcome back ne? Ko kuma ka fara mantawa da ni ne?... Muhammad?!". Na saurara da tambayoyin da nake jera mishi sakamakon jin shiru da nayi ta daya bangaren da yake. 


Sai daya ji na saurara sannan naji ya saki murmushi mai sauti, yace "naji dadi da kika damu dani har haka baby na... Sannan na farko babu abinda ya sameni, waya ta bata lalace ba, sannan lafiyata kalau kamar dai yadda kike ji na!".


Na hade fuska tamkar ina gabanshi, "shine kuma sati biyu cur ka dauke min wuta babu wani bayani. Kana ganin jerin texts din dana dinga turo maka a cikin wadannan kwanakin kuwa?".

Yayi shiru kamar ba zai yi magana ba, can kuma yace "kiyi hakuri, ina da dalili!".


Duk wani haushi da takaicin dana dinga tarawa ina makalewa a cikin raina na kwanaki masu dama sai suka zo suka tarar min a lokaci guda. Cikin tafasar zuciya nace "kana da dalili? Wane dalili?". Yayi shiru. Nan na sake zuwa wuya, nace "kada ka ma damu da yi min wani bayani, na gane. Wato ka gaji kana neman hanyar da zaka bullo ka rabu dani ko? To menene na wani boye-boye da kashe waya? Ka fito kayi rayuwarka yadda kake so, ka fada min cewa ka gama dani, ba damuwa zanyi ba, ba kuma binka zan dinga yi ba, bai kamata ka wahalar min da zuciya ba. Kasan iyaka damuwar dana shiga a cikin yan satikan nan kuwa? Kodayaushe tunanina ya ta'allaka a kanka, gani nake kamar wani mummunan abu ne ya faru da kai, gani nake kamar zan rasa ka har abada! Shine yanzu har kake da bakin dagawa ka fada min wai lafiyarka lau?!". Na karasa fada cikin dan karajin bacin rai, ban damu da cewa duku-dukun safiya bane, zan iya tashin sauran yan dakinmu. Bacin da raina yayi a lokacin ba karami bane. 


Yace "baby...!", muryarshi na nuna tsantsar nadama da damuwa, har sai dana kusa bude baki a take a lokacin ince mishi koma menene na yafe, amma na cije bakina. Nayi shiru ina jira inji abinda zai ce, amma shiru, daga wannan kalma bai sake maimaita wata ba. Kusan sakanni talatin tsakanin ni da shi babu wanda yake furta uffan, don haka nayi kwafa, nace "tunda haka ne sai anjima  idan ka samu bakin magana sai ka kira ni!". Na kashe wayar nayi jifa da ita can karshen katifata na mike zaune. Tashi nayi na fita naje na dauro alwala, na dawo daki na samu wayata na kara, na duba naga shine kawai na kashe karan wayar na tada sallah ta. 


Koda na gama ina ganin yadda take ta haske tana mutuwa alamun ba'a hakura da kiran ba, don haka na tashi na dauki wayar tare da fita waje na amsa saboda kada in damu yan dakin. Na dauka nayi shiru kawai ina sauraron abinda zai ce. 


Yace "baby please ki saurareni. Na rantse ba da gangan nayi hakan ba, ba kuma da son raina bane, please!".

Duk da yadda magiyar ta shige ni, amma sai na dake nace "ina jinka ai", cikin basarwa. 


Yace "ina son ki Na'ilah, fiye da tunaninki wallahi!". 

Maganar tazo min a bazata, don haka na rasa abinda zan ce mishi, jin nayi shiru yasa ya cigaba da maganar shi. 

"Tsorata nayi. Ina so in zo in ganki, ina so in bayyana miki ko ni wanene. Sanin cewa muna soyayya dake kuma har mun aminta da juna, amma kuma baki san ko ni din ainihin wanene ba, yana damuna sosai fiye da tunaninki. Saboda haka na fara tunanin sanar dake ko ni wanene, sai dai tsoron in fada mikin nake yi. Baby, ba zan juri kiyi rejecting dina ba don ba zan iya daukar hakan ba. Wadannan tunanika su ne dalilan da yasa na kashe wayata, saboda ina so in lalubar mana mafita daga ni har ke, wadda zata zaunar damu karkashin inuwar aure, ta kuma zaunar mana da soyayyarmu ni da ke".


Na ajiye wani dogon numfashi, tuni naji zuciyata tayi sanyi, ta kuma yi haske kamar ya sanya soso da sabulu ya wanketa tas! Nace "haba dai, akan wannan ne dama ka tashi hankalinka nima ka tada min nawa?".

Yace "ba zaki gane bane Baby".

Nace "kaine dai ka kasa ganewa, kana da wata nakasa ne? Ko kuma kana tunanin baka da kyau ne, don nima ai ba kyawun gareni ba. Rashin aikin yi ne?". Duk ya amsa min da a'ah, ya kara da cewa, "matsalar ta wuce inda kike tunani, ni dai fatana a duk yanayin dana bayyana a gareki, ki karbeni don Allah!".


Nace "ni ai na riga dana gama karbarka, wace irin karba kuma kake so inyi maka ne?".

Yace "dari bisa dari nake so ki karbeni!".

Nace "tuni ka samu wannan karbuwar, believe me!".

Yace "zamu gani ne dai, amma yanzu naga lokacin fita zai kure miki kada ki makara. Zan kira ki anjima. I love you!".


Nayi murmushi a dan kunyace nace mishi "you too!", na kashe wayar da sauri ina dan murmushi. Sai lokacin na kula da yadda garin yayi haske alamun gari ya waye sosai. Allah yasa ina azumi, don haka ban tsaya wani kokarin hada abin kari ba kawai nayi abinda ya kamata na fita da sauri. 



*



Wannan karon muna bangaren yara ne. Tunda muka je wani likita, Dr. Habib Na Abba ya sanya min ido kamar yaga wata danyar nama, bibiyata yake tun karfinshi tun cikin azumi. Yanzu ma muna tsaye ni da Janan muna rubutu a register, Janan din ta tabo ni. Na dan daga kai distractedly na kalleta, tace "likitan can fa tunda ya shigo idanuwanshi suna kanki".


Na daga idanuna a hankali na dubi inda take yi min nuni, aikuwa muka hada ido dashi, na janye nawa da sauri na maida kan littafin gabana ina jan dan siririn tsaki, "na tsani yawan kallo wallahi, haka kawai ka wani saka ni a gaba kana kallo kamar ka samu wata talabijin? mtsww!", na sake jan wani tsakin. 

Tayi yar dariya, "hala har yanzu baku shirya da Muhammadun naki bane? Na jiki yau gabadayanki a wuya kike, kamar wadda take jira a tabota, sai ki hau fada". Na jefa mata harara ina shirin maida mata amsa daidai da ita, sai naga Dr. Na Abba yana tunkararmu, don haka muka kama baki muka bame kar yaji muna magana a kanshi, har yazo ya tsaya a inda muke muka gaida shi. 


Ya ja tunga ya tsaya yana watsawa Janan tambayoyi game da aiki da kuma ward din, duk wannan abin da ake yi idanunshi suna kaina amma. Ji nayi gabadaya na takura, na tsani kallo. Gashi shi kuma yazo ya mana wani kememe bashi da alamun motsawa ma. Don haka na ajiye littafi da biron da nake rubutu dasu, na kalli Janan nace mata "bari in dan fita", na juya zan bar wajen. 


Maganar da yayi ce ta dakatar dani, "haba sister, daga zuwana kuma sai ki tafi sai kace ina korarki? Idan dai saboda nine, yi hakuri ki dawo ki zauna, sai in tafi".

Na juya ina kallonshi cikin dan murmushin da bai wuce fatar baki ba, nace "ba don kai bane likita, kawai naji ina son fita in dan shaki iska ne".

Yace "to idan haka ne, muje in raka ki shan iskan mana? Nima wajen na nufa yanzu ai".

Nace mishi "babu komi likita!".


Na zagaya kusa dashi muka jera muka fara tafiya. Muna ba Janan baya ya juyo ya kalleni, "to ya sunan malamar?".

Nace "Na'ilah!".

Ya maimaita sunan, "Na'ilah! So unique, I like it!". Nace mishi "nagode".

Muka cigaba da tafiya yana min kananun hirarraki har muka fita wajen, muka cinye karshen ginin. Ko dai ya fita, ko kuma ya hau sama ko kuma ya koma inda muka fito. Ya tsaya ya ja tunga tare da juyowa ya kalleni hannuwa cikin aljihun fara kal din rigar labcoat daya saka tana ta sheki a cikin ranar da muka tsaya a ciki, ya juyo muna fuskantar juna dashi. 


Yace "ni fa son malamar nake, ya za ayi ne?".

Banyi mamaki ba, don dama nasan ko ba dade ko ba jima sai ya fadi hakan, nace "ni kuma?".

Ya langwabar da kai gefe, "yanzu duk alamomin da nayi ta jefo miki, kina so kice min baki taba kula ba?".

Na girgiza kai ina kallonshi, "ko kadan, ta yaya kake so in kula da hakan? I mean, ba tambari bane a goshinka da idan na ganka zan ga hakan kai tsaye ba".

Ya kyalkyale da dariya, "I like you, kina da ban dariya gaskiya. Ga murmushinki mai kyau". Na dan saki murmushi kawai. 


Yace "nasan ke ba karamar yarinya bace, kin fahimceni tunda ba tun yau kike a cikin ward dinnan ba, amma tunda haka kika ce, zan bi ta hanyoyin daya kamata tuntuni, ko zan iya samun lambar malamar?".

Na dan girgiza kai ina murmushi, mutumin nan is very charming, da dai ace wani Muhammad bai sace min zuciya ba. Nace "ni fa kayi hakuri likita, an riga anyi mun miji a gida".

Ya kalleni tun daga sama har kasa yana wani murmushi, "ke din?". Na gyada mishi kai.

Yace "well then, na makara kenan. Amma shi mutum ai baya cire rai daga rahamar Allah, don haka ba zan saddakar ba tun yanzu...", ya ciro dan katinshi daga cikin aljihunshi ya miko min, nasa hannu na karba, ya cigaba da magana, "ina fata zamu cigaba da gaisawa haka nan, don maganar gaskiya kina burgeni sosai. Ina fata zaki taimaka min da lambar wayarki?". Wannan babu musu na karbi wayarshi na zuba mishi lambobina, ya karba yayi saving. Ya dago ya kalleni da dan siririn murmushi akan siraran fatar lebenshi, "sai kin ji daga gareni dear, thank you", ya kanne ido daya tare da juyawa abinshi ya tafi. Na bishi da kallo, yar karamar dariya na subuce min, na girgiza kai kawai. 


Ban yi cikakken minti biyar ba na juya na koma, Janan ta kalleni tana wani murmushi tunda na shiga har na je kusa da ita, na ja kujera na zauna ina kallonta a daddage. Tace "meye kike wani hade fuska? Tambaya ce sai na miki ita, you and the doc?".

Na kwantar da kaina akan benci, "ni fa babu abinda yake tsakaninmu, ke da kika san komi, ina zan kai Muhammadu na kuma?".

Tayi murmushi, "ke da Muhammadun nan naki, Allah dai ya mana zabi nagari. Zaki shiga makaranta gobe, ko kuma zaki raka ni ne?".

Nace "zan raka ki dai kawai, ka samu dan hutu daga wannan wahalar". Ta kwashe da dariya, "daga dawowa har kin gaji?".

Na maida kaina na kwantar kawai. 



*



Wajen karfe goma muka shiga cikin makaranta washegari bayan mun dauko excuse, da yake akwai sauran abokanmu dake cikin hostels din makarantar, Janan ta wuce department wajen supervisor dinta, ni kuma na shiga cikin makaranta da niyar idan ta gama dashi zata kira ni sai mu hadu da ita a gate mu koma asibitin. Ni sai gobe zan ga nawa supervisor din. 

Dakin wata kawata Fatima da muka yi mutunci da ita naje sai aka ce min ai tana sick bay ma bata da lafiya, don haka na karkata na tafi wajenta. Na dan jima a wajenta muna hira da yake jikin nata da sauki, har ma ana za'a sallameta anjima. Janan ta kira ni tace min ta gama yanzu zata fito daga department, don haka na yiwa Fatima sallama da fatan karin sauki, na fita. 


A daidai bakin gate naga Yaya Jameel sun shigo shi da Anty Sarah, abin ya bani mamaki da naga ciki a jikinta, dama ciki gareta? Suka wuce ni a mota ni kuma na wuce na fita. Sai dana ganta ne ma sannan na tuno cikin Sailuba itama, nasan cikinta ya tsufa yanzu, haihuwa ko yau ko gobe. 

Akan hanya na kirata nake tambayarta, tace ai tana ma cikin asibiti, suna expecting din baby nan da sati daya. Nan muka yi sallama da ita muka kashe wayar. 


A bakin gate muka hadu da Janan, muka jera muka fita daga cikin makarantar. Cikin asibiti zamu koma gabadayanmu. Nace mata "baki fada min Anty Sarah tana da ciki ba".

Tace "a ina kika gansu ne? Ashe baki kula da cikinta ba, kodayake last zuwan da kika yi baki ganta ba sosai, amma naji suna cewa ya jima ai".

Nace "a sick bay na gansu, naga ma kamar irin dadadden nan".

Tace "kinsan dogayen mutane dama, yanzu haka idan ba ido kika sanya mata ba, ba lallai ki gane tana dauke da ciki ba".

Na gyada kai, nace "haka ne, Allah ya raba lafiya". Tace "ameen".


Muka samu bus muka hau, tunda muka hau babu wanda yayi magana a cikinmu, da alamu kowa da tunanin da yake damunshi. Ni yawanci akan yadda zan karke rayuwata a gida ne idan na koma kafin inga yadda Allah zai yi dani, ko mai zai faru? Ita kuma Janan ban sani ba, har muka sauka daga bus din dai muka shiga cikin asibitin. Sai da muka fara tunkarar ginin asibitin sannan ta kalleni, murya cike da damuwa tace "ko yaushe matan Yaya Bilal zasu haihu ne?".

Nace mata "ita haihuwa ai ta Allah ce, idan ya nufa sai kiga an sameta ba zato babu tsammani".


Tace "haka ne, amma ina tausaya mishi wallahi. Shekaru suna ja suna kara wucewa, yakamata ace kamar yanzu dai ya fara ajiye nashi iyalin, kowa a cikin dangi ma abinda yake fada kenan".

Nayi shiru ina jinta, ni kaina wasu lokutan ina wannan tunanika, sai dai mafiya yawanci ban san akan wani tunani zan tsaya ba. Tsakanin Yaya da matanshi ban san waye bai haihuwa ba zata kuma iya yiwuwa wata kaddara ce daga Allah. Don haka na dafa kafadarta, nace "kada ki damu, in Allah ya yarda Allah zai kawo masu albarka".

Tace "Allah ya yarda". Muka cigaba da tafiya ba tare da mun sake yin magana ba har muka shige cikin ward din. 


Ko bayan da muka tashi dakina muka wuce da ita, na mana danwake da yake Janan tana matukar son shi, ina cikin yin danwaken ita kuma tana gefe tana yanka mana cocumber, tumatiri da dafaffen kwai Esther kuma tana gefenmu tana taya mu hira, har na gama muka zauna muka fara ci bayan mun zambada yaji kamar na kamun mayu. Bayan mun gama ci muka sauka kasa ni da ita muka wanke kayan muka dauro alwala daga can muka dawo daki muka yi sallah. Tana sallame sallah wayarta ta dauki ruri kamar dama jiranta ake yi, ta daga wayar tayi murmushi tare da nuno min, sunan Yaya Bilal ne yake ta tsalle akan screen din wayar,  na taya ta murmushi cike da mugunta. 


Ta daga wayar a ladabce tana wani yin kasa-kasa da kai da kuma murya, hakuri kawai naji tana badawa, daga karshe dai ta kashe wayar tare da mikewa tsaye, ko babu tambaya nasan tafiya zata yi don haka nima na dauki hijabina na saka na bita a baya. Kamar kullum, sai dana rakata ta hau bus sannan na juyo na dawo hostel. 

Ina dawowa sallah nayi na, dana gama na koma kan katifa na zauna tare da dauko littafaina ina kara reviewing takardun da zan kaiwa supervisor dina gobe, dana gama kuma na dauko textbooks ina kara karatun exams din da zamu yi sati mai zuwa. Har wajen karfe goma tayi Muhammad ya kira ni, na hada kan littafan na ajiye na amshi wayar. 



*



Washegari sai da rana Mr. Akafyi ya min waya akan inje in sameshi, don haka na tafi makaranta. Bayan ya dudduba takarduna da sauran gyare-gyaren da zai min, yace inje inyi printing din wata chapter, na sauka kasa da sauri nayi, ina tsaye mutumin yayi da yake babu yawa kuma babu layin mutane, ya gama na biyashi na koma na kai mishi. Abin haushi da takaici, ina kai mishi yace ai ba wannan chapter din yace ba, wata ce daban, meaning na bata lokacina da kudina a banza. Tun farko kuma shi yace ba sai na dinga printing ba, kawai in dinga rubutawa ina kai mishi, gashi yanzu yana kokarin janyo min ciwon kai ta dalilin haka. 


Nan na sake sauka kasa na bashi takardun, kusan zaman awa daya nayi a wajen yana aikin typing, ya gama ya miko min. Ina komawa ofishin mutumin aka ce ai har ya tashi, wani dan banzan makoko da kududu ya tsaye min a makoshi, naji kamar in kurma ihu. Takardun kawai na tura mishi ta karkashin kofar ofishin na tura mishi text akan na ajiye su, na tafi. Na kula mutumin da alamu sai na biyo mishi ta bayan gida sannan zamu rabu lafiya dashi. 


Ina fita daga cikin department din naji ana kiran sallar la'asar, don haka na tsaya a masallaci nayi sallah sannan na wuce. A bakin gate na tsaya na sayi yoghurt mai sanyi, da niyar dana koma asibiti kafin in shiga ciki zan tsaya in sha saboda tun dazu cikina yake kiran ciroma, dama ban wani ci abin kirki ba yau da safe. Bayan na biya kudin an saka min a leda, na karbi canjin da suka rage min na maida cikin purse dita. Typing din da Mr. Akafyi ya saka ni sun cinye min kudi, nasan sai na sake zama na tsara yadda zan tafiyar dasu kafin in kashe su ban tantance ba. 


Na daga kafa da niyar tafiya kenan, naji karan horn a bayana. Banyi tunanin da ni ake ba daga farko, don haka na daga kafa na fara tafiya. Sai naji an sake a karo na biyu, an kuma kara, na dan juya gefen inda naji karan a kaikaice, gabana naji yayi wata irin faduwa lokacin da muka hada ido da Yaya Bilal. Na kalli gefena domin in tabbatar da cewa ni yake yiwa horn, da dai naga alamun da ni yake, don gashi nan har yanzu ni yake kallo, sai na daga kafa a hankali na tsallaka ta inda ya tsayar da motarshi a bakin titi. 


Kofar gidan gaba ya bude min, don haka na silala na shiga a hankali kamar wata mai takatsan-tsan. Nace "Yaya ina yini?".

Yana kokarin tayar da motar ya amsa da, "lafiya lau, daga ina haka?". 

Nace "naje ganin supervisor dina ne, amma cikin asibiti zan koma yanzu".

Ya gyada kai tana humming, amma bai sake cewa komi ba, kawai motar naga ya ja ya abinshi. 


Kamar yadda na kula da motar shi baka rabata da tattausan kida ko karatu, yau ma tattausar kidan wakar mawaki 'Zayn Malik_Let Me' ce take tashi. Ina son wakokin mutumin sosai. Na kwantar da kaina akan gilashin murfin motar, kamshin turaren Polo na RL da kamshin fresh strawberries na turara mota da kuma sanyin ac dake tashi a cikin motar, yasa na lumshe idanuna. Wata irin natsuwa dana rasa daga ina take naji tana shigata, naji kamar ana zare min duk wata gajiyar dake jikina. Ban san lokacin da barci ya fara daukata ba.


Sai da wani irin awkard feeling ya dameni a bayan kaina sannan, irin wannan feeling din da zaka ji idanu a kanka, kallo kuma na kurilla. Na tuna wata rana lokacin daya daukoni daga gidanshi, irin wadannan abubuwan na dinga ji har na dinga tunanin ko kuma kawai ina imagining hakan ne. 

A hankali na saci kallon inda yake, karaf sai muka hada ido. Yayi saurin janye idanunshi daga kaina ya maida kan titi, sai dai ba'a jima ba muka sake hada wani idon dai. 

Wannan karon ni na janye nawa idanun da sauri, na maida su na rufe, ban sake dagowa ba. 


Tafiya da Yaya Bilal a rufi daya na mota ba yau muka fara yinshi ba, tun muna SBRS ya sha zuwa ya daukemu muje muyi hutun karshen mako a Kaduna, haka ma bayan mun dawo Zaria. Duk da cewa yawanci tare da Janan muke yin tafiyar, amma akwai daidaikun lokuta da yake rago min hanya daga gidanshi. Amma hakan bata taba faruwa ba, idan ma ta taba ko kuma tana faruwan, ni ban taba kula ba sai a dan wadannan lokuta. Shirun cikin motar yayi yawa, kidan ma ya tsaya cak kamar da can babu shi, it was unsettling. 

Cikin sa'a muka karasa asibiti cikin dan kankanin lokaci, da kwatance na kwatanta mishi inda muke, yana gyara parking din motar na fita a sukwane kamar wadda ake mintsila, sai dana maida murfin motar na rufe sannan na leka ta saitin motar ina zuba mishi godiya. Ko jira inji ko ya amsa ko bai amsa banyi ba, na kara gaba kamar zan tashi akan iska saboda sauri. 

Na rasa dalilin da yasa Yaya ya kirkiro da wasu irin halaye da bai saba ba sam cikin wadannan kwanakin. Koma dai menene, ni dai ina fata Allah Yasa lafiya. 





*



Ranar Juma'ah, har na kwanta da dare kiran wayar Muhammad ya tashe ni, donhaka na daga wayar cikin barcin daya fara daukata, mun kwaso gajiya a asibiti yau. 


Maganar daya fara min bayan mun gaisa ne tasa na bude idanuwana sosai, yace "are you ready baby?".

Nace "ready for what?".

Yace "ganina mana baby!! Kin shirya gani na gobe?".


Na tashi zaune sosai akan katifata, nace "da gaske?! Don Allah kada kace min wasa kake yi!".

Yace "kin san babu irin wannan wasan a tsakaninmu baby, da gaske nake. Kin shiryawa gani na gobe?".

Na hau gyada kaina da sauri kamar ina gabanshi, "oh God yes, I'm hella ready!!".


Ya saki yar dariya mai sauti, "yayi kyau. One thing though, ina neman alfarmar kiyi min fahimta mai kyau, ki kuma fahimci kyakkyawar manufata a gareki. Don Allah idan na bayyana miki kaina Na'ilah, kada ki guje ni!".


Tunda muke dashi yau ne karo na farko da naji ainihin sunana ya fita daga fatar bakinshi, naji jikina yayi sanyi, nasan he's serious. Nace "in shaa Allah Muhammad, zan yi iyaka kokarina".

Yace "good, and no matter what kada ki manta cewa ina son ki Baby". 

Sai kuma naji gabana yana duka sosai, maganganunshi suke nema su tayar min da hankali, nace "wani abu yana faruwa ne Muhammad? Kana tsorata ni!".


Yace "babu abinda ya faru baby, ki kuma kwantar da hankalinki. Am sorry idan yanayin halayena suna tsorata ki, I couldn't help myself".

Sai muka yi shiru, kamar wasu wadanda aka wa rasuwa, can kuma sai yayi gyaran murya, yace "don't mind me fa, insecurities ne irin nawa, amma babu komi we are safe. Saboda haka ki koma barcinki yadda zaki tashi da wuri kin shirya delicacies na tara na, tuwo za'a dafa min ne ko kuma shinkafa?!".


Nan da nan na warware, muka fara magana akan abinda ya dace in tanadar mishi. Sai daya tabbatar da cewa na ware, sannan ya min sallama, bakinshi yana kara nanata min kalamomin so da kauna. 


Muna gama wayar na koma na kwanta tare da janyo filo na rungume a kirjina, zuciyata cike da farinciki mara misaltuwa. Gobe zan ga Muhammadu na!!.






~Godiya mara adadi yan uwa, Alhamdulillah na warware sosai. Nagode kwarai da addu'o'inku da kuma goyon bayanku, Allah ya bar kauna. Son so 😍










#F.W.A

[27/03 9:33 PM] Jiddah Lawal: 🌟 *⋆☆A ZATO NA...!☆⋆* 🌟



        *⋆©Jeedderh Lawals⋆*





                             *☆⋆21⋆☆*





Daren ranar nayi barcin da ban taba yin irinsa ba koda wasa, cike da mafarkai masu dadi wasu kuma very weird.

Abu na farko daya fara fado min a cikin raina lokacin dana farka daga barcin daya daukeni bayan nayi sallar asubahi shine, 'what a ridiculous dream!', wani irin mafarki dana rasa gane kanshi balle gindinshi. A ganina meye hadin biri da kaska?! Na yakitar da wannan mafarki domin kwata-kwata bai ma yi kama da abinda zan kasa a cikin raina ya dameni a banza a wofi ba. 


Tunda na tashi da safe na rasa inda zanyi da raina saboda murna da jindadi. I practically glowed all day. Tun da safe na gama duk wasu abubuwa daya kamata inyi, nayi wankin kayan uniform dina, bayan sun bushe na goge su na ajiye, sannan na kara gyara kayana.

Munyi dashi akan sai yammaci likis sannan zai zo, ban san abinda yakamata in mishi ba wanda zai ci ba, don haka bayan na gama wanki na hada meat pie wanda nayi filling da minced meat har da su carrots da dankalin turawa. Na hada mishi zobo hadadde saboda in dai harkar hada drinks ne musamman na gargajiya, ni kaina nasan cewa na iya sosai. Mawuyaci ne wanda ya sha ya kushe. Bayan nan na sayo lemun exotic na abarba da kwakwa da ruwan cikin gora, na kaishi dakin wata yar ajinmu da take da firjin na roketa ta ajiye min zuwa anjima da yamma yadda zai yi sanyi, tace babu damuwa. 

Gabadaya na kasa zaune na kasa tsaye, motsi kadan na lalubo waya, ko in duba lokaci ko kuma in turawa Muhammad text. Ji nake kamar in janyo yinin ranar saboda nisan da naga yayi min. 


Karfe hudu na yammacin ranar, ina zaune a gefen kujerata ina nade gashin kaina. Jiya na warware kalbar kalbar sallah da Janan ta min, na je saloon na wanke shi. Yanzu dana taje shi sai ya zubo har gadon bayana, yana ta sheki da tashin kamshin shampoo. Da yake ban cika son nuna gashi a waje ba, sai nake nade kayana in saka cikin dakwali ko hula. 


Wata bugaggiyar doguwar rigar atamfa ce na saka, irin dinkin yan Senegale dinnan ne. Atamfar kanta yar can ce, wata tafiya da Yaya Mudatthir yayi zuwa can gudanar da wani aiki, ya kawo min ita a dinkenta. Sau daya kacal na taba sakata. Dinkin zanen single ne, rigar kuma kamar half buba dinnan ce, data tsaya min a gwiwa, dankwalin mai fadi ne sosai, na kashe daurin Zara Buhari a kan nawa. Dana tsayawa karewa kaina kallo a madubi, ni kaina sai dana burge kaina. Allah ya azurtani da baiwar wani irin tattausan kyawu, irin kyawun nan da ba'a gani kai tsaye, sai a hankali a hankali yake fita. Wai a hakan ma don ba wata kwalliyar kirki nayi ba, hoda kawai na shafa tare da murza kwalli a idanuna, nayi amfani da brush na taje gashin girata, daga shi ban kara komi ba. 

Abinda Esther ta dinga yiwa korafi kenan, tace in zo ta min kwalliya ko da simple one ce, "bai kamata ki je wa saurayin da zaku hadu dashi yau a karo na farko haka ba, ba kya tsoron yaji baya yi dake?".


Na rolling idanu sama tare da jefa mata baki, nace "a haka nake so ya ganni ya kuma so ni, ni fa ba rokon ya so ni nake yi ba. Sannan ke kina ganin nayi miki kama da wadanda maza zasu kalla suji basa so ne?".

Ta girgiza kai tana murmushi, "ba karya abokiyar, kinyi fa! Ai karya ne wani da namiji ya kalleki yace baki yi ba, ko matan ma tankawa suke yi balle kuma maza. Abinda kawai nake so ki sani shine, ku hausawa da kanku ne kuka ce idan kana kyau ka kara da wanka. Kinga duk da kina da kyanki tubarkallah son kowa kin wanda ya rasa, ina ga da kin dan kara koda mascara ne da eyeshadow yadda zaki kara fitowa sosai, ki kara rikita shi, kin gane ai".


Ni duk bayanan da take watsawa sauraronta kawai nake yi ba wai don ina fahimtarta ba, duk wucewar dakika daya, fargabar dake cikin zuciyata karuwa take yi. Nerves sun cika min ciki. 

Nace mata "ni duk ban damu da irin wadannan abubuwan ba, fatana kawai ya karbeni a yadda nake. Zan fi son ya ganni a ainihin wacece ni, ba wai kyale-kyalin banza ba".

Tace "kinyi yar gaskiya kuma". Ni dai na kauda kaina gefe kawai don bana jin zan iya tsayawa yin doguwar hira a halin da nake ciki yanzu. 


Karfe biyar da rabi daidai, sai ga kiran wayarshi. Hannuwana har rawa suke yi lokacin dana dauki wayar na karata a saitin kunnena. Nace "hello?", da kyar kamar wadda take koyon magana. 

Yace "yanzu na karaso kofar hostel din, ina daga waje ina jiranki", cikin wani irin husky voice, deep and soothing a lokaci guda. Sai naji kamar yau na taba jin muryar. Naji wata irin rawar cikin jiki ta ziyarceni, kamar na fito waje cikin muku-mukun sanyinnan, na kakaro sautin "to", daga can kasan makoshi na kamar an shake ni. Na kashe wayar na ajiye a gefena ina maida numfashi da sauri da sauri kamar wadda tayi gudun ceton rai. 


Sai dana tabbatar da natsuwata ta dawo cikin jikina, sannan na tashi tsaye, duk da haka sai da naji kamar zan kifa saboda yadda kafafuna suke rawa. Wani tray dana amsa wajen Esther, mai fadi ne ba laifi, da zanen manyan jajayen furanni a jiki. A cikin jug dinshi na zuba zobon da nayi, na yanka cucumber da kankana kanana a ciki bayan na cire 'ya'yan, su kuma kananun cups din jug din na kifa guda biyu akan tray din. 

Na shirya meat pie din akan wani karamin plate, na kawo foil paper na rufe shi. Na dora lemun dana amso da ruwan akan tray din, aka yi sa'a ya kwashe duka. 


Na kara duba fuskata a cikin madubi naga lafiya lau, na dauki gyale mai dan fadi nayi yafawar zamani, na kawo turaren fantasy na kara badawa a jikina. Duk wadannan abubuwa da nake yi, cikin takatsan-tsan da rawar jiki nake yinsu. Na dauki takalmi mai dan tudu baki na saka, sannan na dauki tray din wannan da wayata na fita. 


Akwai wani karamin waje daga can gefen hostel din, yawanci dalibai kanyi karatu a ciki musamman irin group assignment da aka hada maza da mata a ciki, nan suke zuwa suyi karatun. Ko kuma idan wata daliba tayi baki nan take zuwa dasu idan maza ne. Nima can na fito da rana na samu wata yar kwana, inda babu yawan giccin mutane sosai na share na kuma goge kujerun da aka kera na sumunti a wajen da niyar nan zan jagoranci Muhammad din idan yazo. 


Lokacin dana fito waje ban ga kowa ba, da alamu a can wajen gate ya tsaya, don haka na fara kai kayan hannuna wajen da zamu zauna na ajiye su, sannan na taka a hankali zuwa wajen gate din. Idan wani ya kalleni a lokacin, nasan babu bata lokaci zai ce tafiyar yanga ce nake yi, sai dai a zahirin gaskiya, tsananin fargaba da tsoro ne suka sa nake tafiya kamar wadda take jan kafarta. Ban san dalilin wannan sudden tsoro da naji ya dirar min ba, amma nafi danganta hakan da cewa kila saboda kawai haduwarmu ta farko kenan yau. 


Na fita daga gate din, idanuwana suka fara karade ilahirin wajen da kallo, ina duba gefena na dama, na hango shi. Jingine da motar rav4 baka kirin, sanye yake da wata jikakkiyyar danyar shaddar getzner ruwan kasa mai haske, ta sha dinkin surfani na zare shima ruwan kasa amma mai duhu sosai, takalmin kafarshi shima ruwan kasar ne irin flats dinnan na maza, ko ba'a fada maka ba kasan ba karamin kudi da daraja zasu yi ba. Daga inda nake, babu abinda zan iya karaswa game da features dinshi, kawai dai nasan dogo ne, ya danyi min nisa, ban hangi komi a fuskarshi ba, musamman da yake a daidai wannan lokacin ya nutsa wayar tashi cikin wayar hannunshi. Sai hular kanshi kawai. 


Na samu kaina da takawa a hankali zuwa inda yake, kaina a kasa ban iya dagowa na kalleshi ba saboda wani irin nauyinshi da naji ya dirar min, amma duk da kan nawa a kasa yake, ina jin zafin kallonshi a cikin jikina. Sai dana fara ganin kyawawan jerin dogaye kuma zara-zaran yatsun kafarshi da suka yi matukar kyawu cikin kyakkyawan takalmin kafarshi, sannan na iya daga kaina a hankali. 


'Assalamu Alaik...", sallamar da nayi niyar yi mishi, ta makale a makoshina lokacin da na dago kai a lokacin, muka hada idanu hur-hudu dashi. 

Fuskarshi bata nuna mamaki, al'ajabi ko rikicewar tunani kamar yadda na tabbatar suna zane akan fuskata ba baro-baro. A tsaye take kyam, maimakon hakan ma, sai wani tattausan murmushi daya bayyana akan fatar bakinshi. 

Yace "wa alaikumussalam wa rahmatullah... Har kin fito?".


Na tsinci kaina da karkata kaina gefe guda cikin tsananin mamaki, can kasan zuciyata kuma ina maimaita kalmar 'har kin fito?', ko me yake nufi da hakan?.


Na dan duka cike da girmamawa nace "Yaya Bilal ina yini?". Gabadayan idanunshi fuskata suke karewa kaina kallo kamar yau ya taba ganina, yace "lafiya lau Na'ilah! Ya kike?".

Na gyada kai kawai, zuciyata cike da tambayoyi, yayin da a gefe guda kuma naci gaba da dube-dube ko zan hango Muhammad. Ya nake ganin kamar mu kadai ne a gaban hostel din? Ko kuma bai zo ba yace min yazo?.


Na furta tambayar da take ta ci min rai tunda naci karo da Yaya ne, nace "ko kazo wajen wata ne anan ko wani?", a raina nace ko dai wani auren yake nema ne? Na danyi shivering lokacin da tunanin abinda hakan yake nufi ya darsu a cikin raina. 


Ya cigaba da jefa min irin wannan kallo da tunda muka hadu dashi yake jefa min, yana kuma gyada kai a hankali, "wata".

Na dan zare ido cikin mamaki, kafin nayi kokarin maida mamakina na kulle, sai anjima Janan zata sha labari, nace "uhmm, to. Dama nima akwai wanda na fito gani ne dama, tunda bai zo ba kuma bari in koma, ka samu wadda kazo ganinta ne ko kuma kana bukatar in dubo maka ita ne?".


Idanuwanshi na fitar da wasu alamu, awe and mischief, yace "a'ah, no need. Nagode. Na ganta ai, gata nan a gabana!".

Na dan juya bayana cikin tunanin in hadu da wadda take nufi din, sai naga wayam. Na girgiza kai kamar wadda take kokarin shaking din wani feeling, gabadaya abinda yake faruwa yanzu yana da matukar daure kai, na kasa banbance tsakanin karya da gaskiya. Ina bukatar in ganni a cikin dakina, in kwanta akan katifa inyi tunanin abinda yake faruwa. 


Na gyada kai a hankali, a hankalin dai nace "to shikenan, zan koma ciki ni, a gaida gida". Kafin ma ya samu damar daga baki ya maido min amsa, maybe juya da sauri na daga kafata na fara tafiya. 

Yace "Na'ilah, Muhammad ne fa!".


Naji na tsaya cak, kamar wadda aka kafe. A hankali na juya, zuciyata tana bugu da karfin masifa, cikin idanunshi nake kallo directly, ina laluben wani alamu da zai nuna wasa yake yi a cikin idanun nashi. Tunani nake, ta yaya aka yi yasan zance na da Muhammad? Ko dai yana daga cikin abokanshi ne? Haba, babu mamaki. Kila ma Muhammad din abokinshi ne, kila shi yasa zai biyo shi su zo tare ko. Na dauke idanuna daga kanshi zuwa cikin motarshi, so nake inga ko akwai alamun mutum a ciki, amma duhun gilasan motar ya hana in hango komi. 


Kallon-kallo muka fara yi dashi, ganin bashi da niyar yi mun karin bayani akan wannan katoton al'amari, yasa ni na bude baki kamar wadda take tsoron magana, nace mishi "a ina kasan Muhammad? Ka san shi ne?".


Akwai wani nag feeling da yake damuna, daga can kasan zuciyata, wani bangarene yake jefo min tambayar, anya? Amma nake danne shi tun karfina, babu wata anya ko tantama, babu abinda yake faruwa. Yaya Bilal ba wani bane face aboki, ko kuma wani daya san zancena da Muhammad, and nothing more!. 


Maimakon ya bani amsar tambayar daya min, sai ya daga kafa ya fara takowa a hankali har ya iso daf dani, ni kuma saboda tsabar rikici, na rasa ta yaya zan iya daga kafata inyi baya duk da cewa mun danyi kusanci dashi. A hakan ina iya shakar kamshin turaren daya fesa, kamar tufafin na nutsa a fuskata. 


Ya daga yatsarshi manuniya yana nuna saitin kirjinshi, yace "ni nan, Na'ilah, nine dai Muhammad din da kike jira, Muhammad naki, wanda zai so ya ganki!".


Na kura mishi idanu kawai, idan banda bugun zuciyata babu abinda ya canza daga yanayin motsin jikina. Kila ma sandarewa nayi a tsaye ban sani ba. Ban san me yasa Yaya Bilal zai ji bukatar yayi min irin wannan wasan ba, halayenshi na kamewa da rashin son wasa yasa kwata-kwata na kasa yarda da cewa tsokana ce kawai kamar yadda nake nanatawa kaina domin karyata abinda zuciyata take fada min tunda na bayyana a gaban Yaya Bilal yanzu. 


Allah kadai yasan iya lokacin dana dauka a haka, kawai ina kallonshi kamar wata bakuwar halitta. Na rasa gane a duniyar da nake, shin duniyar mafarki ce ko kuma ta gaske?.


Na samu kuzarin daga baki da kyar, bayan dogon lokacin nan, nace "wane Muhammad kake magana akai, Yaya?".


Ya saka hannu cikin aljihun rigarshi, ni kuma kamar sakara na bi hannun nashi da kallo har ya ciro wata kirar iPhone, fara kal da ita. Ina kallo yayi unlocking dinta ya fara danne-danne, ba'a dauki lokaci ba wayata ta hau kara da vibrating a hannuna. Sunan Muhammad ya fito baro-baro a jiki, yayin da a gefe guda kuma Yaya yake nuno min wayar hannunshi fuskata. Lambar wayata ce itama gata nan, da sunan 'baby na' a jiki, ga kuma hotona akai. 


Yace "ko baki yarda da cewa nine Muhammad ba? Kina bukatar wata shaida ne daban?".


Na rikice, na rasa abinda zan tunana a cikin raina, me ke faruwa ne wai?!. Mafarki nake yi ne? Ko kuma kwalwata ta fara samun matsala ne? Ko kuma kwalwar Yaya Bilal din ce ta samu matsala?".


Kamar wata mahaukaciya sabon kamu, haka na fara ja da baya ina girgiza kaina, komi juya min yake yi, shi kanshi Yayan dake gabana bana ganinshi sosai. Da alamun hawaye ne suka ciko min idanu, naga lokacin da Yaya ya fara biyo ni shima, tun yana tafiya a hankali har ya daga kafa sosai ya tadda ni, ya kai hannu da niyar kamo ni yana mai ambatar sunana, "baby na!!".


Ko rufe baki bai kai ga yi ba, na juya na daga kafa a sukwane na fada hostel. Wani daga cikin security yana tambayata lafiya lau? Me ya faru?? Amma na kasa amsa mishi. 


Tunani daya ne zuwa biyu a cikin raina a wannan lokacin, lallai na cika sakara mara tunanu. Ta yaya aka yi duk tsayin wannan lokaci da muka dauka muna waya dashi ban taba daukar muryarshi ba, ta yaya idanuna suka rufe ne? Ta yaya nayi sake irin haka? Kuskure ne ko kuma rashin sani??. 


_'Na sanki farin sani!...'_


_'Sunana M.B!...'_


_'Ina aikine da wani kamfanin buga takardu...'._


Of course ya sanni farin sani, Yaya Bilal ne shi fa after all. M.B yana nufin Muhammad Bilal. Yana aiki da kamfanin buga takarda, dama mutumin da yake aiki da daily trust ai dole ma ya sarrafa takardu. 

Mai yasa ban taba yin irin wannan tunanin ba, sai yanzu da ta faru ta kare? Babu zancen komawa baya??!.











#F.W.A



[01/04 2:19 PM] Jiddah Lawal: 🌟 *⋆☆A ZATO NA...!☆⋆* 🌟



        *⋆©Jeedderh Lawals⋆*





                             *☆⋆22⋆☆*






A kofar daki muka ci karo da Esther ita kuma zata fito. Ta biyo bayana da sauri ganin yadda na wuceta a rikice tana jefa min tambayar lafiya? Amma na kasa daga baki in bata takamaimaimiyar amsa.

Na hade da gyalena da wayata nayi jifa dasu kan katifa, ni kuma na silale na zauna a tsakiyar dakin. Gabadaya na rasa abinda yake min dadi, shin wai ko dai mafarki ne nake yi?.


Esther ta dafa ni tana dan shafa bayana in a comforting manner, tace "Na'ilah, me yake faruwa ne? Wani abu ya faru da Muhammad dinne?", na bita da kallo kawai, ban ma san me zan ce mata ba. Kai ko na daga baki ma bana tunanin magana zata iya fita. Don haka na cigaba da binta da kallo kawai.


Wayarta tayi kara, ta duba mai kiran, da sauri ta juyo tana kallona, "sorry Na'ilah, ana jirana a waje. Don Allah kiyi hakuri kinji? Bari inje in dawo yanzu". Ta fita da sauri.

Bayan fitarta na tallafo kumatuna da duka hannuwana biyu, na kurawa wayata dake yashe a kan katifata kamar ita zata bani amsar tambayoyina. Abin gwanin ban dariya gwanin ban haushi, yanzu ashe duk wannan waya da muke sha da shi, duk tsayin wannan lokacin, dama da Yaya Bilal muke waya? Haba, biri yayi kama da mutum! All those stolen glances idan muka hadu a karkashin rufi daya dashi wadanda daga farko na dauka ko ni ce nake wassafa hakan a cikin raina, kallon daya dinga jefa min ranar nan da nayi rashin lafiyar nan, har na dinga tunanin zafin zazzabi ne yasa nake ganin hakan, dama da gaske ne? Dama duk wannan lokacin, kallona kawai yake yi a dage, yana min kallon wata sakara wadda bata san abinda take yi ba? Da kuma maganganun daya dinga min a jiya, ba karamin godewa Allah nayi ba da bai sa giyar soyayya ta kwasheni na dauki alkawarin da ba zan taba cikawa ba. Yanzu da na amince mishi fa aka sa mana aure ko aka daura ba tare dana taba ganinshi ba? Nasan mutuwata ce tazo kawai.


Hankalina ya kasa kwanciya, duk inda na juya idanun Yaya Bilal kawai nake gani a cikin dakin, haunting me. Naji na fara damben warto numfashina da naji ya fara guduwa, ina warto shi da kyar.

Ban san lokacin dana rarumi wayata ba na dannawa Janan kira.


Ta dauka cheerily, murya cike da tsokana, "hey.., har Muhammadun naki ya tafi ne?!".


A rikice na hau kiran sunanta ina maimaitawa kamar karatu, "Janan... Janan...!!".


Nan da nan ta rikice, tace "subhanallahi, Na'ilah me ya faru ne?".

Nace "Yaya ne! Yaya Bilal ne... Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Yau ya zanyi da rayuwata? Hasbunallahu wa ni'imal wakil!!".


Ai sai na kara rikitata, naji alamun motsa kaya daga can inda take, "me ya samu Yayan? Kun hadu dashi ne? Wai meke faruwa ne? Kiyi min bayani please!".


Na daga baki da niyar yin magana, amma sautin komi ya kasa fita.

"gani nan" kawai tace, kafin inji ta kashe wayar. Na koma na jingina da bango ina lumshe idanuna.


Abin kamar a almara haka nake jin shi. Yau da safe dana tashi, mafarki na farko dana fara tunawa wanda nayi ne akan Yaya Bilal. Maimakon abin ya bani mamaki, sai ma ya bani dariya. A tunanina meye hadin kifi da kaska? Tunanin Yaya Bilal da ni a waje daya, abu ne da bai taba, ina nufin koda wasa bai taba gittawa ta cikin raina ba, ko a mafarki ban taba ganin hakan ba sai a yau din. Shi yasa ko a dazun abin ya matukar bani dariya, saboda babu wani abu daya kamata inyi a wannan lokacin da yafi inyi dariyar.

Amma yanzu da naga abin yana shirin ya zama gaskiya, sai kuma abin yake shirin ya sanya ni kuka. 


A yadda nake dinnan, a haka Janan tazo ta sameni. Ta tattagoni jikinta cikin tsananin nuna damuwa, ko bata furta ba fuskarta da idanuwanta sun nuna min hakan baro-baro. Hakan yasa naji jikina yana relaxing, na kwantar da kaina akan kafadarta, totally vulnerable.


Kusan mintunanmu biyar a hakan, kafin ta dago kaina daga jikinta, murya a tausashe, kamar wadda take tsoron idan ta dan kara daga muryarta zata saka ni kuka. Kodayake, hakan ne, ni nasan a yadda nake jina dinnan, zuciyata a wuya, to abu kadan da bai gamshe ni ba a yansu zai iya sa ni fashewa da kuka.


Tace "me ya faru ne? Wani abu ya faru da Muhammad dinne? Me kuma ya jefo Yaya Bilal cikin wannan magana?".


Na daga baki nace "Janan, Muhammad... Shi.. Yaya Bilal...". Nan da nan na fara hargitsewa. Tayi saurin taba kafadata, tace "kinga, nutsu kin gane? Yauwa, just calm down. Everything's good, ok?".


Na gyada mata kai a hankali, na fara jan numfashi ina saukewa a hankali har naji bugun zuciyata ya daidaita. A hankali na bude baki nace "Muhammad, Yaya Bilal ne! Yaya Bilal ne Muhammad Janan!!".

Naji wata zazzafar kwalla ta ciko min idanu, nayi saurin kokarin maida ta. Sai da na fadi maganar da karfi ta shiga kunnuwana, sannan naji gaskiyar lamarin yana shigata. 


Janan ta zuba min idanu tana kallo, kamar wadda take jira in ce mata tsokanarta nake. To ai ni kaina jin abin nake kamar a mafarki ko a almara. Ni kaina na kasa yarda wai hakan ta faru.


Zuwa can tace "ta yaya?".

Nan na gyara zama na fede mata biri har wutsiya, ban rage mata komi ba. Tun daga fitata daga hostel, maganar da muka yi dashi har gudowar da nayi. Ban san cewa hawaye nake ba, sai dana sauke aya. Naja numfashi na ajiye, sannan naji lema tana bin kumatuna. Na sa hannu na share, amma ina dauketa wata ta sake gangarowa.


Na dora da, "Me yasa ni? Me yasa Yaya zai yi min haka? Me yasa hakan zata faru dani? Janan ya zanyi?".


Tace "mafita daya ce, kiyi hakuri ki danne zuciyarki, ki saurareshi kiji abinda zai ce".


Na tabe baki ina jinjina kai, "tab, lallai ma! In saurareshi ince mishi me? In gaya miki gaskiya ni da Yaya yanzu sai dai hange daga nesa, kai ko daga nesar na hango shi, zan canza hanya ne a sukwane ba tare da bata lokaci ba!".


Tace "amma kuma hakan ba mafita bace Na'ilah. Kika san ko yana da wani kwakkwaran dalili da yasa yayi hakan ne? Kada fa ki yanke hukunci cikin fushi Na'ilah, daga baya kuma ki zo kiyi dana sani!".


Nayi wata yar dariya da daga jinta babu digo ko alama ta farinciki a cikinta, sai akasin sa. Nace "wane dalili ne daya wuce ya muzanta ni, ya maida ni sakara? Da ba don nasan Yaya ba sosai, da sai ince baki ya hada da Umar ko wani akan suyi wasa da hankalina. Kodayake, ban san shi ba yanzu anymore!".


Janan ta kalleni, frowning. Tace "Ni nasan Yaya Bilal sosai, ba zai taba stooping that low to do something like this ba. Kamar yadda nace, da ace baya da kwakkwaran dalili, to ina mai tabbatar miki da cewa da ba zai taba ma bata lokacin shi tsawon lokutan nan ba!".


Na turo baki, "yanzu kuma kina bin bayan Yayanki ne, zaki yace min baya?".

Ta matso kusa dani da sauri, "koda wasa wallahi, haba, akan me zan miki haka? Ni fa shawarar da nake gani zata fissheki ce naki baki ba wani abu ba".


Na tashi tsaye, "whatever dai, ni dai an gama min wasa da hankalina, bana kuma tunanin zan iya tsayawa in sake sauraron shi".


Janan bata ce komi ba, ta zuba min idanu. Ni kuma na fara cire kayan jikina.


Idan da ace wani zai gaya min cewa a haka yinin na yau assabar zai kare min, da tuni zan karyata shi. Idan ma raina ya baci sosai, in kara da fada mishi bakar magana. Yau dana tashi da safe, ba haka na hango ni ba, ban taba tunanin akwai wani abu da zai zo yayi ruining yinin nawa na yau ba, sai gashi tun ba'a je ko'ina ba, yinin yayi bacin da ban taba tunani ba.

Na kalli kayan jikina dana cire, naji wani makokon takaici ya kawo ni wuya, ko linke su banyi ba na cukuikuyesu na jefa cikin kayana. Na dauki towel babba na daura a jikina. Ban cewa Janan komi ba, na dauki bokiti na sauka kasa na tari ruwa naje na watsa ruwa a jikina haka nan.


Ina cikin yin wankan naji an kira sallar magriba, don haka na daura alwala na koma sama. 

Ina shiga dakin naci karo da Esther a zaune, da kayan dana baro a inda na ajiye. Ni na ma manta dasu. Daga ita har Janan suka bini da kallo.

Esther ce ta fara magana, ban san me Janan tace mata ba, amma naji bata tado min zancen dazu ba. Na dai ji ta tana mitar, "Ni wallahi nayi zaton ko accident ne suka yi ko wani abu a dazun, har na tsorata. Daga yace wani abu na gaggawa ya taso, sai ki wani rikice har haka? Lallai kina da babban aiki kuwa yarinya!". Ni dai na shareta ban ce komi ba.


Kayan dana ke sanyawa na shan iska na sa, na tada sallah nayi. Ina gamawa itama Janan ta shigo dakin, don haka na koma gefe na bata waje itama tayi. Tana gamawa Esther ta kallemu, tace "ni fa yunwa nake ji, kuma na rantse ba zanyi wani girki ba alhalin ga abinci nan ina gani a gabana. Idan ba zaki ci wannan abun ba, ki bani inci don ba zan so ayi asarar su ba gaskiya".


Nace "gashi nan kiyi ta ci".

Tayi tsalle ta rarumo kayan, Ina ji Janan tana itama a ajiye mata bari tayi sallah ta zo taci, nayi banza dasu su duka.


Ana kiran sallah na tashi nayi. Janan ma tana gama nata, ta zauna ta tada meat pie din da Esther ta rage mata da sauran drinks din. Dama guda biyar ne nayi babu yawa. Janan tana gamawa ta kalli agogo, tace "bari in tashi in tafi kafin Yaya ya dawo, yayi fada".


Ai jin an ambaci sunan Yaya, sai naji raina ya kara dagulewa. Na koma kan katifa na zauna, na harde hannuwa a kirji ina turo baki ina kallon Janan tana gyara zaman hijabin jikinta a wuyanta, ta gama ta juyo tana kallona, "mai kike jira ne, ba zaki raka ni ba?". 


Na kara turo baki, "a'ah, ki gaida mutan gida!".

Ta daga hannuwa sama in mocking surrender, cam cikin idanunta alamun dariyar da take ta kokarin boyewa ne. Na harareta, ta kara yin murmushi, tace "yi hakuri ki maida wukar, ba ni na kar zomon ba kin gane? Bari in karasa gida ni kam. Don Allah kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki, kada ki bari wannan abin ya taba zuciyarki kinji?".

Na kalleta kawai, sanya abu a cikin rai na nawa kuma?

A haka dai ta mana sallama ta tafi.


Ina zaune ina kallon Esther data tashi tana hada kayan, tana cewa ita dai ba zata yi wanke-wanke ba fa, "Sai dai idan kin tashi gobe ki wanke kayanki amma ba zan iya ba". 

Ta dai gaji da mitar ta tayi shiru ganin ban tanka mata ba. Tana gama abinda zata yi, tace min ta tafi class. Exam dinmu ranar monday ne, amma nasan ko giyar wake na sha ba zan iya yin karatu ba yanzu. Don haka na kwanta kawai ina ta faman saka da warwara a cikin raina.


Har wajen karfe goma sha daya na dare idanuna biyu kyar, babu alamun barci a cikinsu. Juyi kawai nake yi, ba tare da takamaiman wani abu da nake tunani a kai ba. Wayata ta fara kara, daga farko cak nayi a zaune, hatta da numfashina sai daya tsaya sakamakon jin kalar karan. A hankali na juya na kalli wayar, babu shakka sunan Muhammad ne, ko kuwa Yaya Bilal zan ce? Yake yawo akan wayata.


Ban iya motsawa ba har ta katse, tana katsewar aka sake kira. Na hau gyada kai ina kara girgizawa cikin tsananin mamaki, yanzu har Yaya yana da sauran kunyar da zai iya kirana a waya dama? Oh duniya ina zaki damu?!.


Na dauko wayar da niyar kasheta, hannuna ya silale ya taba answer and speaker button ba tare dana kula ba, sai dana ji muryar shi radam kamar a cikin dakin yake yana magana, "hello? Oh thank God! Baby kina ji na? Baby...?!".


Da sauri na danne wayar har ta mutu, na dafe saitin zuciyata data hau bugawa da sauri kuma da karfi. Jin muryar shi a yanzu, sai naji kamar an tado min wani tsumi. Ko ba'a fada ba, nasan yau munyi baram-baram ni da barci.





                 Kuyi hakuri da wannan zuwa gobe don Allah. Jiya sai dana yi typing, nayi zaton na turo na goge, sai daga baya naga ashe ban turo ba.







#F.W.A

[01/04 2:19 PM] Jiddah Lawal: 🌟 *⋆☆A ZATO NA...!☆⋆* 🌟



        *⋆©Jeedderh Lawals⋆*





                             *☆⋆23⋆☆*






Washegari na tashi da wani azababben ciwon kai wanda ban taba zaton wani mahaluki zai taba yin kamar sa ba sai a ranar. Ni dama nasan za'a rina, yadda jiya na kwana ina sake-sake, barci ma sai gab da sallar asubahi sannan ya daukeni. Dalili kenan da yasa na so in makara sallah yau. Ina yin sallar kuma dana koma barci ma, kasa komawa nayi, sai can rana har ta ma fara fitowa sannan nayi barcin. 

Yanzu kam zaune nake akan katifata da misalin karfe goma da rabi, kaina da yake bugawa kamar ana kwankwasa guduma tallabe cikin hannuwana guda biyu. Dakin babu kowa, Esther ta tafi church, Maimuna kuwa dama rabona da ita tun ranar juma'ah da safe da zan bar daki, ban kara ganinta ba.


Na samu na lallaba da dafa bango na tashi na fita. Ruwan wanka na jona a jikin heater, kasancewar ruwan da aka yi yau da asuba, yasa har yanzu garin sanyi garai. Yana dan yin zafi na je nayi wanka, nayi brush hadi da dauro alwala. Sai dana fara yin sallar walaha sannan na sake dafa wani ruwan a cikin kofi karami, na hada hot chocolate shi kadai na sha. Bayan na sha na balli paracetamol guda biyu na afa a baki na kora da ruwa. 


Bayan na gama kin komawa in kwanta nayi, na kuma ki zama in saka tunanin Yaya Bilal da al'amuranshi a cikin raina. Sai kawai na dauki wayata na jona ta a jikin caji ba tare dana kunnata ba, na hada kan kayan wanke-wanke na kulle dakin na sauka kasa nayi. 


Bayan na gama na koma dakin, ciwon kan ya dan sauka kadan, amma jifa-jifa na kan ji ya sara min har yanzu. Na bude dakin na shiga tare da maida kofar dakin na rufe. Kasancewar yau students suna ta hutawa kuma safiya ce, wasu kuma sun tafi gida, yasa hostel din yayi shiru babu hayaniya, yadda kasan ma babu kowa. 

Na fara da kunna wayata. nasan dai ba zan dawwama a haka ba, komi daren dadewa nasan dole in fuskanci wannan chakwakiya. Ban shirya ba, amma nasan dole ne. Don haka naga gara in fara tun yanzu, the earlier, the better. 


Ko minti goma cikakke banyi da kunna wayar ba, ta hau kara. Na saurara da goge-gogen da nake yi tare da tsayar da kira'ar Sheik Minshawi da dan yaro a cikin suratul-Mulk dake tashi daga cikin laptop dina, na dauki wayar. Ganin sunan Yaya Mudatthir na daga da sauri, cike da tunanin ko Anty Sailu ce ta sauka. Sai dai ina dagawa, tun ma kafin inyi magana ya riga ni, yace "wai ni Illo don Allah menene amfanin wayarki ne? Ke kullum aka kira wayarki a kashe? Me yasa ba zaki ajiye wayar kawai ki cire komi nata ba kowa yasan baki amfani da waya?".


Nayi dan murmushi, "Yaya, nasan amfanin wayata ni fa, wasu lokutan rashin caji ne yake sawa idan kun kira kuke ji a kashe".

Yace "kwarai kuwa, ai da yake duk Nigeria baby garin da ake wa kwauron wutar lantarki kamar nan ko?".

Nayi yar dariya, "ni ban ce haka ba. Anty Sailu ta sauka ne?".


Yace "tukuna dai, yanzu haka muna asibiti ma".

Nan da nan naji gabana ya fadi, nace "lafiya? Jikin ne ya motsa?".

Yace "a'ah, amma likitocin sun ce tana bukatar zama a asibitin zuwa lokacin da zata haihu domin su dinga monitoring dinsu ita da babyn. Amma so far dai komi lafiya lau".


Na dan sauke ajiyar zuciya, "Masha Allah, Allah ya sauketa lafiya. Amma nayi fatan ace ina nan yanzu tare daku wallahi".

Yaya yace "to ya zaki yi? Haka karatun ya gada ai. Ina fata dai idan ta haihu zaki zo ko?".

Nace "sosai ma! Ai ko muna exams sai na kansileta nazo!".


Yaya ya saki yar dariya, "ba wani nan. Ke dai kawai kiyi fatan kina free lokacin".

Nace "to shikenan. Ya su Inna? Kwana biyu ma bamu gaisa dasu ba".

Yace "a asibiti na baro ta, ni na dan fito yanzu. Amma idan na koma zan kira ki sai ku gaisa dasu".

Nace "to shikenan, sai ka dawo din".

Yace "babu dai wata matsala ko?".

Nayi dan murmushi a hankali, nace "babu Yaya. Sai anjima". Muka yi bankwana na ajiye wayar. 


Aikin da nake yi na komawa, ina yi ina bin kira'ar har na gama. Ina gamawa na fara gyaran wajen da nake. A takaice sai wajen karfe daya na gama komi. 

Bayan nayi sallah na fita waje can wajen yar kasuwar su na siyo kayan miya na dawo daki na hada miya na dafa farar shinkafa na ci. 


Na dauki system dina na fara aiki akan project din da nake to har zuwa lokacin da Janan ta kira ni, sannan na dakatar da aikin na dauki wayar. Bayan mun gaisa ta watso min tambayar lafiya ta lau dai ko? Na kada idanu kamar ina ganinta, "ehh, ga wanda ya kwana ya wuni cikin tashin hankali da damuwa da rashin barci har da karin ciwon kai, lafiyata lau Jan. Ina fata kinyi kin tashi kin kuwa wuni cikin koshin lafiyata?".


Janan tayi yar dariya, "ai daga ji ma babu tambaya lafiyarki lau, ba sai kin janyo min wani dogon bayani ba. Ya karatu, ina fata dai kinyi ko?".

Na dan saci kallon tulin jotters da textbooks dana fiddo dazu wadanda suke jiran in daga su, tare da sauke ajiyar zuciya lokacin dana tuna akwai fa sauran gingimemen aiki a gabana. Nace "ban fara ba wallahi, amma anjima da yardar Allah zan fara tunda dama revising ne kawai zan yi".

Tace "hummm, nima hakan take. Allah dai ya bamu sa'a". Nace "ameen".


Tayi shiru, hesitating, banyi kokarin katseta ba ko tambayar lafiya, nasan tunda naji haka akwai magana da take son muyi, wadda kuma bata wuce ta mutum daya. Sai da tayi radin kanta tace "me zai hana ba zaki saurari Yaya ba don Allah? Ko sau daya ne Janan, ya cancanci wannan damar daga gareki".


Nayi shiru ina sauraronta, sai data dire aya sannan nace a hankali, "dalilin kenan da yasa kika kira ni dama? Saboda Yaya?".


Itama ta danyi shiru kafin tace "wai me yasa kike cewa haka ne Na'ilah? Ke kinsan cewa tsakanina dake ai babu wannan abin, wallahi jin ki nake kamar yar uwata ta jini, sai dai shima Yayan ina jin shi a cikin jinin jikina. I just want what's best for you Na'ilah, shine kawai!".


Na san duk abinda ta fada hakan take, idan kuma da kunya da kara, bai kamata in watsawa dan uwanta kasa a ido ba, sai dai bana tunanin zan taba iya wannan abu da Janan take kokarin sanyowa, ba zan iya yin wannan karar ba. 

Nayi kasa da murya, cikin tsananin son yi bayanin da zata fahimta, wanda kuma ba zata kullace ni ba, nace "Janan... Ke kinsan abinda yake damuna, kin kuma fi kowa sanin yadda nake kin wannan akidar, don haka don Allah don Annabi Jan, ki taimake mu ki daina sako wannan maganar. Kince you just want what is best for me, barin wannan maganar shine mafi a'ala a gareni, don haka don Allah mu daina yin ta kawai. Don Allah kice min kin fahimce ni?".


Tace "na fahimce ki, sai dai Na'ilah, wannan fa ba karamar magana bace ko kuma maganar wasa da zaki ce a barta kamar bata taba faruwa ba. Yaya ma ba zai taba kyaleki ba in gaya miki gaskiya, shirun da kika ga yayi kawai ya baki iska ne ki hada tunaninki waje daya. Ina ga da kin hakura kun yi magana, kiji abinda zai ce mikin".


Na fara gajiya da maganar wannan, tun jiya muke nanatata kamar cin kwan makauniya, cikin nuna alamun gajiya da maganar nace "kamar yadda nace miki, kawai mu bar maganar nan. Babu wani abu da zamu tattauna tsakanina da Yaya Bilal, ke kin sani. Ba zan taba mika wuyana a sare shi ba alhalin ina cikin hankalin kaina, haba Janan, idan har kin tabbatar kina so na kuma kina kaunata, bai ma kamata ace kina nema kiyi convincing dina ba koda wasa".


Itama cikin nuna alamun gajiyawa tace "whatever Na'ilah, ni dai iyaka shawarar da naga zan iya baki kenan. A gani na idan kuka yi maganar, kika yi mishi bayani, zai iya ba zuciyarshi hakuri ya nemi daidai dashi wadda zata iya zama dashi da matan shi tunda ke kin ce baki iyawa. A ganina kenan. Sauran kuma, Yana gareki. Dabara ta rage ga mai shiga rijiya, sai mun hadu a asibiti gobe!". Ta katse wayar. 

Na bi wayar da kallo. Daga jin yadda muryarta ta dan daga, ranta ne ya fara baci. Ban yi kokarin sake kiranta ba, na maida wayar na ajiye. Bana tunanin wani abu zai iya canza min kudirina, ciki kuwa har da fushin Janan. 

Na fahimci kaunar da take yiwa dan uwanta ce ta haddasa hakan, sai dai me yasa ni ba zasu fahimceni ba? Me yasa ba zata yi kokarin fahimtar dalilina ba??!. 

Nayi kokari na kauda tunanina daga kan wannan magana na ci gaba da abinda nake yi. 


Sai bayan la'asar sannan na fita karatu. Har aka kira magriba ina can, sai masallaci naje nayi salla. Akan hanya na tsaya na sayi doughnut da yoghurt, na koma class. Sai wajen karfe goma na koma daki. Ina komawa ko kayan jikina ban iya cirewa ba na zube akan katifa saboda barcin daya cika min ido.




*



Washegari kuwa garas na tashi, bayan nayi sallah na fara duk wasu al'adu dana saba kafin in fita zuwa asibiti. Jikina a dan sanyaye yake saboda nerves din jarabawa, kodayake nasan kusan kowa ma haka yake ji, an riga an saba. Na shirya a nutse, ban dora abin karyawa ba saboda azumin sitta shawwal da nake yi, zuwa gobe zan gama gabadaya in Allah ya yarda. 


Akan hanyata ta zuwa venue din da zamu yi jarabawar, wayata ta fara pinging alamun shigowar message. Ina dubawa naji gabana yana dukan uku-uku, Yaya ne. Kin dagawa nayi, ina tsoron in daga in karanta abinda zai hana ni sukuni bayan ina da muhimmmiyar jarabawa a gabana. 

A kalla kafin in karasa venue din, ya kara turo wasu sakonnin kamar guda uku haka. Na tsaya na bada ajiyar wayar wajen securities bayan na kasheta, sannan na shiga ciki. 


Seat dina yana kusa dana Janan ne, yadda muka rabu da ita jiya nayi tunanin ko kallon arziki ba zan samu daga gareta ba, sai ta bani mamaki data haskeni da murmushin man nata, ta dan matsa kadan yadda zata bani waje sosai tana cewa "sai yanzu? Wato kema kin koyi makara ko?".

Na dan saki murmushi a tausashe, duk da yanayin da nake ciki, sai naji raina ya dan yi sanyi, na zauna kusa da ita, "ai kin san zama da madaukin kanwa...".


Tayi yar dariya, "idan ma dani kike, bani na goga miki ba, can zaki je ki nemo wanda ya goga miki yarinya!". Muka yi musayar murmushi. 

Ba abin mamaki bane ga halayyar Janan, sanyin zuciya irin nata da kawar da kai har kullum shine abinda ya tsananta tsayin abotarmu da ita. Ina girmamata saboda hakan. 


Muka fara revising ya junanmu gami da tambayoyi game da abubuwan da muka karanta, har zuwa lokacin da masu tsaron jarabawar suka shigo. Da misalin karfe tara kenan. 

Jarabawar ta daukemu awanni biyu da rabi cur, kusan tare muka gama ni da Janan amma ta riga ni fita. Na mika takardar bakina dauke da addu'o'i iri-iri, idan nayi rashin sa'a jarabawar nan ta dawo min ban san ya zamu karge da Baba ba.


A bakin kofar wajen na sameta tana jirana, na amshi wayar hannuna, muka jera ni da ita hannu da hannu har zuwa cikin hostel. Allah ya taimaka yau sun daga mana shiga cikin asibiti har sai zuwa gobe. Muna ta tattaunawa game da jarabawar har muka shiga hostel din.

Muna shiga ta cire uniform din jikinta, nima na cire nawa. Na ciro mata rigar shan iska, doguwa mai wadataccen fadi, nima na saka shigenta, muka kwanta akan katifata, sai a lokacin na bata labarin Anty Sailu fa tana asibiti, ta jinjina lamarin tare da cewa zata kira ta mata sannu. 


Ba karamin dadi naji ba da bata kara tado min zancen Yaya Bilal ba. Again, nan ma ta bani mamaki. Janan ba irin mutanen nan bane masu saurin sakin abu ba, idan ta sako abu a gaba ko kuma wata magana, bata saki don wasa har sai ta cimma nasara. Shi yasa yanzun nake ta kaffa-kaffa da ita, ban san ko me take tunani ba a cikin ranta. 


Sai da muka yi sallar azuhur bayan mun koma mun kwanta, sannan na bi bayan sakonnin da Yaya ya turo min dazu, hannuna har rawa yake yi. 

Na farkon cewa yayi; _'Hey, you okay?'_


Na biyun kuma: _'Nasan cewa ba ta haka ya kamata in tunkare ki ba, nayi kuskure. Should've thought about it more kafin in tunkare ki ta wannan hanyar, saboda haka ne nake baki hakuri!'._


Sai kuma, _'Baby, na san cewa kina ji a cikin ranki kamar ban kyauta miki ba, ko kuma wasa nake miki da hankali. Ina tabbatar miki da cewa ba haka bane, please let me explain myself!.'_


Akwai kuma wanda na kula ya sake turowa nan da mintuna sha biyar da suka wuce: _'Please baby, da gaske ba zan iya cigaba da zama a haka ba. Nayi kokarin ganin cewa na baki cikakken lokaci domin ki samu kiyi tunani akanmu, I know it's sudden. But that's it! I can't do this anymore.. Let me see you again, please? I promise zan miki bayanin duk abinda kike son ji, kinji baby na?!'_


Ina gama karanta wannan naji wani abu mai zafi ya daki zuciyata, idanuna suka fara min zafi alamun kwalla ta fara taruwa. Na lumshe idanuna tare da kwantar da kaina akan pillow. Yaya Bilal ya riga ya bata rawar shi da tsalle, koda yake tun daga farko dama bashi da wani chance a wajena, amma me yasa raina yake kuna idan na tuna cewa zamu rabu dashi har abada?! Me yasa nake jin kamar ina gab da rasa wani muhimmin bigire na jikina ba? Ko dai zan bi shawarar Janan ne, inyi rethinking wannan bakon al'amari?.

Nayi gaggawar girgiza kaina, inaa! Ba zai yiwu ba!. 


A hankali na sake bude idanuna, har yanzu hasken kan wayata bai mutu ba. Na dinga scrolling sama ina kara karanta sakonnin da muka dinga canzawa a tsakaninmu, kafin in san ko shi din wanene. A da, da ban san ko shi din wanene ba, kawai ina jinshi acan kasan raina ne, yeah, ina son shi, kuma ina kaunar shi, amma yanzu dana san ko shi din wanene finally, sai nake ganin komi daban, at least yanzu idan ina tunaninshi zan ga fuska kuma zan ji murya sosai. Sai dai nasan koma menene nake ji game dashi, dole ne in manta dashi. Ko za'a yi me, nasan cewa ba zan taba amincewa da Yaya Bilal ba. 


Saboda haka na kashe hasken wayar, na ajiyeta a kusa dani na rufe idanuna cike da fatan barci ya dauke ni a lokacin. 



                             ***



"... Na'ilah?!".


Da sauri na bude idanuna, Janan na zaune kusa dani tana kallona cike da yar damuwa a fuskarta. Na sauke idanuna akan agogo, naga har karfe hudu da rabi tayi. Na tashi zaune ina salati. Tace "har an kira sallah, ki tashi muyi mu leka waje mu ga abinda zamu lalubo na shan ruwa, yau anan zan sha ruwa".


Na mike tsaye, ko don barcin da nayi ne? Jikina naji yayi min wani nauyi. Na tashi na dauki hulata na fita, idanun Janan a kaina. Nasan dalili, mafarkin da nayi ne wanda ta tashe ni a daidai lokacin da bana son tashi, daidai lokacin da nake kwadayi, kuma nake marmarin ganin wannan mutumi da duk duniya babu wani mahaluki da yake kada min sassan jiki kamar shi ba. Amma kullum anan nake tsayawa, ban taba ganin fuskarshi, muryarshi ma haka nan nake jinta sama-sama kamar ba a kusa dani yake ba. Wani lokacin ni nake tashi a karan kaina, watarana kuma sai ayi arashi wani ne a kusa dani zai tashe ni. Koma dai menene, na zubawa sarautar Allah ido ne kawai domin ni kam na kasa gane wannan abu. 


Bayan munyi sallah, muka fita zuwa kasuwa muka sayo abubuwan da zamu bukata, muka dawo muka yi yam balls da kunun aya. Har muka gama shan ruwa da ita bata yi alamun sake tado maganar jiya ba, don haka naji na fara relaxing. Cikin annashuwa kamar yadda muka saba muka sha ruwanmu, na tashi na rakata ta hau mota na dawo, na tattare kayan da muka bata na ajiye a inda nake tara kayan wanke-wanke, nayi sallar isha'i. 


Daga nan common naje nayi kallo. Karfe goma na dawo daki. Na samu Maimuna da Esther a daki, na musu sannu suka amsa nayi shirin kwanciya barci na kwanta. 

Wani irin sad feeling da naji ya rufe ni a lokacin, da ace da ne, da yanzu muna nan muna zuba soyayyarmu ni da Muhammadu na. Me yasa Yaya Bilal ne zai zama Muhammad? Mai yasa ba wani mutum ne daban ba, wanda bashi da mata daya balle mata har biyu? Me yasa? Wai me yasa abubuwa suke zo min ne a hagunce? 

Daren ranar yau dai da kuka shabe-shabe nayi barci. 









#F.W.A

[01/04 2:19 PM] Jiddah Lawal: 🌟 *⋆☆A ZATO NA...!☆⋆* 🌟



        *⋆©Jeedderh Lawals⋆*





                             *☆⋆24⋆☆*





Ni a karan kaina nasan cewa idan nace bana yin kewar Yaya Bilal to karya nake yi, ina kewar shi fiye da tunanina. Sai dai wani sashe na zuciyata yasan cewa yaudarar kaina kawai nake yi. Ko zan mutu, ko zuciyata zata tsattsage saboda damuwa, zama da Yaya Bilal ba zai taba zama maganin hakan ba. Don haka nake iyaka bakin kokarina wajen ganin na danne duk ma wata kewa, so da bege da nake ji game dashi. Nasan cewa na dan lokaci ne, nan da lokaci kadan zan daina. 


Sai dai duk wanda ya ganni, yasan cewa ina cikin damuwa. Idanuna kadai sun isa shaida, saboda bana samun barci mai yawa. Ko nayi, saboda tsananin sanya maganar Yaya Bilal da matanshi a cikin raina, haka zanyi ta mafarkinshi. Watarana ma har da matanshi, wani lokacin kuma barcin ne ma gabadaya baya zuwa. 


Yanzu ma muna zaune a cikin ward ni da Janan da wata Aisha, a ranar alhamis kenan. Janan da Aisha ne suke ta hirar su, ni kuwa hankalina yana kan wata calender dake rataye a wajen. A zahiri idan ka kalleni, zaka yi tunanin jerin magungunan dake cikin takardar nake karantawa ko kirgawa, amma a hakikanin gaskiya hankalina ma kwata-kwata baya tare dasu. Tunani nake, tun wannan text din da Yaya Bilal yayi min ranar litinin, har yau bai sake kirana ba, kuma bai sake turo min wani sakon ba. Ta wani bangaren naji dadin hakan, so nake ya barni, ya kyaleni, idan ma da hali ya manta dani. Duk da cewa nasan har abada zan dinga kallonshi da wannan maganar, ba zan taba mantawa ba, sai dai in binne abin acan karshen bangon zuciyata. 

Ta wani bangaren kuma tunani nake, dama kirarin da yake akan cewa yana sona duk kuri ne da cika baki? Har ya manta dani kenan? A yadda yake nunawa dinnan, nayi zaton zai zage damtsensa ne har sai inda karfinsa ya kare. Amma dana fara irin wannan tunanin, sai inyi gaggawar katse kaina, idan ma ya ci gaba da bibiyata babu abinda hakan zai sa sai ma kara min ciwon kai da damuwa da hakan zai yi. Don haka gara ma yaje can ya karata da matanshi ya fiye min alkhairi. Shima wannan kuri ne kawai da zuciyata take yi, can can kasanta, tana fatan ace ba haka bane. 

Kai wasu lokutan sai inji da ace ana cire zuciyata a sake sabuwa, da na garzaya zuwa ko'ina ne na canza tawa. Komi nisan wajen kuwa. 


Nayi nisa cikin tunani, ban ankara ba sai ganin Dr. Na Abba nayi a kaina yana snapping hannuwanshi a fuskata. Nayi firgigit! Kamar wadda ta tashi daga barci na kalleshi. 

Yayi dan murmushi, "haba Nas, wannan dogon tunani haka har ina? Idan dai don nine kada ki damu, gani a gabanki. Ba zan matsa ko nan da can ba har sai kinyi min iznin hakan!".


Ban san sanda na saki dan murmushi ba, Allah ya zubawa mutumin baiwar iya ba mutane dariya koda mutum bai shirya ba kuwa, ko kuwa ni ce kadai?. 

Yace "haba! Ko ke fa? Ba gashi har kyakkyawan murmushin nan naki ya fito ba? Wallahi ba karamin kyau kike yi ba idan kika yi murmushi!".

Nan ma ban iya daurewa ba sai dana kara yin wani murmushin. 


Yace "so what's up? Kwana biyu na daina ganinki anan, nayi zaton ko kin bar ward dinne. Jiya sister Mairo take ce min ba canza ku aka yi. Kin san yanzu evening duty nake yi, ina ga shi yasa bamu cika haduwa ba".

Na dan gyada kai tare da cewa "haka ne kam, ya aiki?".

Yace "Alhamdulillah. Ko kina da yan mintunan da zaki taka min zuwa nan waje Na'ilah? Ba don kowa na shigo da wuri ba sai don ke".


Sai lokacin na kula da cewa yau ba sanye yake da labcoat dinshi ba. Na juya na kalli su Janan da suke yan rubuce-rubuce da danne-dannen waya, amma ni nasan hankalinsu gabadaya a kanmu yake. Na gyada mishi kai a hankali tare da sauka daga kan kujerar da nake, ni dashi muka jera muka fita. 

Bai furta min komi ba, nima kuma banyi yunkurin cewa komi ba har muka fita waje. Kaina a kasa yake, ina dai bin sawun kafarshi ne dake sanye cikin takalmi sau ciki, don haka ban san sanda muka isa wajen ajiye motocin likitocin asibitin dake ta wannan bangaren ba, sai dana ji ya ja birki sannan. Ya jingina da jar motar shi 406, ni kuma na tsaya ina fuskantar shi. 


Yace "Wato Na'ilah dalilin da yasa na so mu kebance muyi magana dake shine, ina so ne inji inda maganar mu ta kwana ne. Shin, har yanzu kina ganin bani da chance ne a wajenki?".

Na dan yi wuri-wuri da ido, kafin in tsaida su waje daya, murya a shake nace "to ni me zance maka kuma, ina tunanin tun ranar nan na fada maka anyi min miji a gida?".


Yayi dan murmushi, yace "Hmm, Na'ilah kenan! Aka yi miki miji ko kuma kika yiwa kanki miji, kika fada min?".

Nace "kamar yaya? ban gane ba!".

Yace "come on mana, daga jin yadda kike cewa 'ai anyi min miji a gida!', ko dan jariri yaji yasan cewa kin fadi ne kawai don kiji dadin bakinki!".


Ban san lokacin dana kyalkyale da dariya ba, musamman lokacin daya make murya wai shi ala dole kwaikwayo na yake yi. Shima yayi murmushin ya kara jingina da motarshi yana dan murmushi, nayi shiru ina girgiza kai, amma murmushin fuskata bai bace ba. 

Yace "da gaske ba. So I'll like it idan kika manta da zancen mijin da ba'a riga an san ko wanene ba, let's talk about us for now. Kamar yadda na fada miki ranar nan, gaskiya kina burgeni. Kuma ina fatan ace zaki bani dama, mu samu fahimtar juna a tsakaninmu. Me kike tunani?".


Nace "magana ta gaskiya ni a halin da ake ciki yanzu likita, babu wannan maganar a cikin raina yanzu. Ina fata hakan bai bata maka rai ba?".

Ya girgiza kai, "ko kadan. Kin san ku mata da jan aji, hakan ba matsala bace a wurina. Zan baki iyaka lokacin da kike bukata, amma ina neman alfarmar dinga yin waya dake zuwa lokacin da zaki sauko?".


Nasan wannan rana ba zata taba zuwa ba, don dai mu rabu lafiya dashi sai kawai na gyada mishi kai. Yayi dan murmushi, "yauwa, nagode. Muje in dan taka miki ko?".

Nayi yar dariya, nace "nayi zaton ni na rako ka?".

Yayi yar dariya, "a'ah, ni na isa? Kawai dai ina so ne mu dan tattauna dake ne a waje dama dai kawai".


Muka sake kwasa muka sake komawa dai, anan ne yake dan fada min tarihin rayuwarshi. Gidansu yana palladan, har kwatance yayi min amma da yake ba sanin unguwar sosai nayi ba ban gane ba. Ya fara min bayani akan irin rayuwar da yayi, da kalar makarantun da yayi, muka koma wajensu Janan. 

Muka yi sallama dashi ya juya ya tafi, ni kuma na zauna akan kujerar da nake. Ina zama naci karo da idanun Janan tana hararata. Nace "malama lafiyarki kuwa?".


Tace "ban sani ba. Ni zo ki raka ni waje inje in sayo wani abu in ci".

Ba musu na tashi na bi bayanta, da yake karfe sha biyu da rabi ta kusa, lokacin tafiya sallah yayi. Muka yiwa Aisha sallama muka fita, nace mata "ai nayi zaton kina azumi ne yau".

Tace "a'ah". Ganin tana amsa min magana dai-daya yasa nayi shiru nima. 


Tace "wannan likitan da kike biyewa, son shi kike yi ne?".

Na dan yamutsa fuska, "wace irin magana ce kike yi haka? Wani irin so kuma?".

Tace "to sai wani yage mishi baki kike yi kina dariya, me hakan yake nufi?".


Na girgiza kai, "don Allah kada mu ja maganar nan tayi tsayi. Ni babu wani son shi da nake yi".

Tace "to sai ki daina bashi fuska, a haka kina leading dinshi ne kawai ba wani abu ba!".

Na daga baki hangamgam, nace "to wai ke meye matsalarki ne? Idan na kula shi ko naki kula shi, meye damuwarki?".

Har ta daga baki zata yi magana, sai kuma ta fasa, tace "oho dai, ke kika sani!".

Muka yi shiru muka cigaba da tafiya, can kuma tace "ya labarin su Sailu?".

Muka karkata hirar zuwa can, wanda hakan ba karamin dadi yayi min ba. 


Mun je ta sayi abinda zata ci, muka biya ta masallaci nayi sallah sannan muka koma ward. Acan taci abincin, muka cigaba da ayyukanmu har lokacin tashin mu yayi. 

Janan ta riga ni tafiya saboda lokacin da aka tashi, wani yaro nake yiwa dressing. Faduwa yayi garin wasa da keke. Don haka ta wuce saboda a cewarta, zata biya kasuwa ta sayi wasu kayan bukatu kafin ta wuce gida. 

Sai wajen karfe biyar da kwata na gama, na yiwa mutanen wajen sai da safe, na fita. 


Sai dai cak! Naja na tsaya lokacin da nayi arba da abinda ban taba tunanin zan gani a daidai wannan lokacin ba. Yaya Bilal ne a tsaye kyam, tsayuwar sojoji, ya zube hannuwanshi duka biyu a cikin aljihun wandon kaftani dake jikinshi. 

Kamar wanda aka ce mishi ya dago kanshi, karaf muka hada idanu dashi. 


Abu na farko daya fara zo min a cikin raina, shine in fyalla da gudu. Sai dai da nayi tunani, sai naga meye na gudunshi to? Hakan ba wata mas'ala bace. Shawara ta biyu ita ce in tafi in raba ta gefenshi kawai in wuce, in nuna kamar ban san shi ba. Sai dai matsalar itace, kafafuna sun kasa motsawa balle har suyi tafiya. Don haka naci gaba da tsayuwa anan inda nake, ina kallon Yaya Bilal. 


Ganin bani da niyar yunkurin yin wani abu, yasa ya tako cikin wani nutsattsen taku ya tunkaroni. Sai lokacin naji kafata ta motsa, na fara ja da baya, amma bai daina tunkarata ba. Da dai naga ya kusa cimma ni, sai na juya na sake fecewa a karo na biyu. 


Can A&E na tafi, na shige can wani lungu da mutane basu cika bi ba na labe kamar wata munafuka. Na kwashe fiye da mintuna ashirin a wajen, zuwa lokacin nasan idan ma nema ne Yaya ya gaji ya kara gaba, don haka na fito daga maboyata. 

Sai dana karewa wajen dana ganshi dazu kallo na tabbatar da cewa baya nan, sannan na daga kafa da sauri kamar wadda aka cilla daga jikin mashi, na dauki hanyar komawa hostel. 


Sai dai da yake kwata-kwata yau sa'a ba a sashe na take ba, sai dana fara hango gate din hostel, har ina kara daga kafa, kawai sai ganin mutum nayi a gabana kamar wanda ya diro daga sama. Nayi tsalle nayi gefe daya a tsorace ina rafka salati, kafin in daga kaina in sauke su akan dodon nawa. Shi din dai da nake ta gudu. 

Na sake juyawa da nufin ranta ana kare, ya sake shiga gabana, juyawar da nayi da sauri, da niyar bi ta wata hanyar, sai naji ni shame-shame a jikin bango. Shi kuwa yayi babakere a gabana, ya tsare gaba da baya, ta yadda babu yadda za ayi in tsere, sai dai idan bangaje shi zanyi. Ko kuma in ratsa ta jikin bangon dana jingina. 









#F.W.A



 
















1 Response to "A ZATO NA Hausa Novel"