-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

A SANADIN MARAICI Hausa Novel

A SANADIN MARAICI Hausa Novel

 đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

          *A* *SANADIN* *MARAICI* 

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž      Story and writing

                  By

      Rufaida(Rufeey)

 

 *_MARUBUCIYAR_* 


 *KAUNA* *CE* *KO* *KIYAYYA* 

  *BANFARGABA* 

  *Na* *fada* *tarkon* *sonshi* 

  

      *And* *now* 

   *A* *SANADIN* *MARAICI* *🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*


     *M. W. A* 


 ```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. đŸ€™đŸ»``` 

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

_________________________  *Wannan* *labarin* *kirkirarren* *labarine* *banyi* *dan* *wata* *ko* *wani* *ba* *Wanda* *yaga* *labarin* *yazo* *dai*  *dai* *danasa*  *toh* *akasine*  *ban* *yarda* *a* *chanzamin* *labari* *ba* *Wanda* *ya* *chanzamin* *ban* *yafeba* ,


 *BISMILLAHIR* *RAHAMANIN* *RAHIM* 


PAGE1️⃣↪️5️⃣


〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Wata yar budurwa nagani,zaune a cikin  wani kayataccen parlour tayi tagumi nakira mata ido sosai naga hawaye nabin kuncinta kyakyawace  ajin farko gata fara tas ga daradaran idanu,ga hanci har baka badan karamin  pink lip dinta gaskiya budurwar nan yar kimanin shekaru, sha 17 ta hadu masha Allah tana cikin kukan datakene naga wata mata dawata budurwa tana biye da ita abaya suna zuwa gurin budurwar nan naji matar da wannan dayar tabayan nata suna cewa toh shegiya wato bakiyi aikin da yar leletasa kiba koh? toh wlh yau bazakici abinci ba nan tafara kwalawa ma aikatan gidan kira!.
Nandanan kuwa segasu sun shigo suna fadin Hajiya gamu tace yawwa dama kiran kunai infada muku kar Wanda yabawa yar iskar yarinyar nan abinci a cikin gidannan duk Wanda yabata abakin aikin sa wallahi kunji nafada muku Dan haka kukiyaye sukace toh Hajiya.

Sannan Hajiya tace daga yau kezaki dinga komai nacikin  gidannan sannan kumasu ai'ki karwanda yatayata kunjini ko? sukace eh tace zaku iya tafiya haka suka fice suna Allah wadai da halin Hajiya.
       Suna fita Hajiya tace ke KHAMEENI ki tashi kije ki gyara wa yar lele dakin ta sannan ki gyara nawa kiwanke toilet wallahi idan beyi kyau ba se jikinki yagaya miki haka wacce naji ankira da KHAMEENI ta tashi tahau sama tanufi wani daki Dan tayi ai'kin da akasata.
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

  Wani kyakyawan saurayi nagani  dawasu samari su 2  suma ba laifi suma sunada kyau Amman dayan duk yafisu kyau suna zauna ne acikin wani club kowanne da yanmatansu, ga kayan shaye shaye a gaban su dakagansu kasan abuge suke daya dagacikinsu naji yana cewa KHALIFA kutashi mu wuce wannan kyakyawan saurayin naji yace ok HILAL.Nan naga kowannansu yaja budurwa 1 sun fice daga club din sunnufi motocinsu sun bar gurin naga sundau hanya nima nabisu naga sun tsaya a wani katafaran gida sukai horn kasancewar dare ne yasa megadin yafito yazo yaduba yana ganin su yakoma da gudu yabude musu get suka shige sukayi parking suka fito megadin yarugo da gudu yazo gaban wannan saurayin da aka kira dazu wato KHALIFA yana cewa yallabai kayi hakuri dazu bansan kaineba shiyasa KHALIFA bekulashiba suka shige.
Suka shiga wani haddan parlour, gaskiya parlour ya had`u naga kowannansu yaja budurwar sa sun shige bedroom...
Toh fans anan zan tsaya senaga ruwan comments zancigaba 😁😁😁
 *BY* *Rufaida*✍️Comments and share please🙏🙏🙏🙏


đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

      *A* *SANADIN* *MARAICI* 

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


     Story and writing

                 By

     Rufaida(Rufeey)


 *MARUBUCIYAR* 


 *KAUNA* *CE* *KO* *KIYAYYA* 

 *BANFARGABA* 

 *NA* *fada* *tarkon* *sonshi* 


        *And* *now* 

      *A* *SANADIN* *MARAICI* *🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*


     *M. W. A* 


 ```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. đŸ€™đŸ»``` 

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

_________________________


 *Wannan* *labarin* *kirkirarren* *labarine* *banyi* *dan* *wata* *ko* *wani* *ba* *wanda* *yaga* *labarin* *yazo* *dai* *dai* *danasa* *toh* *akasine* *ban* *yar* *da* *a* *chanzamin* *labari* *ba* *Wanda* *ya* *chanzamin* *ban* *yafeba* .


 *BISMILLAHIR* *RAHAMANIN* *RAHIM*


PAGE6️5️⃣↪️1️⃣0️⃣


〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Bangaran Khameeni kuwa duk ai'kin da Hajiya tasata se da tayi haka tagama ta fito tana fitowa Hajiya tace kingama  kenan? Khameeni tace eh Ummi na gama tace ok suna tsaye Sega yar lele tashigo parlour ta zauna.
Tana cewa Ummi tagama ai'kin kenan Ummi tace eh geki duba kigani haka y`ar lele tashiga bedroom d`inta tana shiga tafito tace Ummi beyimin ba gaskiya ta kara gyarawa.
Ummi tace ke jeki kuma gyara mata haka Khameeni tashiga d`akin tacewa yar lele haba "Kausar yanzu wannan d`akinne be gyaru ba".? tace bansani ba idan zaki kara gyara wa ki gyara idan kuma bazaki gyara ba bari na kira Ummi.
Khameeni tace toh zan gyara haka tahau gyara d`akin tana hawaye tana gamawa tasauka naga tashiga wani d`akin da alama nanne d`akinta tashiga toilet tayi alwala ta tada sallah tana idarwa tad`au alkur'ani tana karanta wa seda akayi issha ta idar sannan tai addu'a ta fito parlour Dan yunwa takeji.
Tana fitowa taga Ummi ita da Kausar a parlour suna cin abinci a dining area taje tace Ummi yunwa nakeji Ummi tace yinwar uwarki a'i nafad`a miki yau bazakici abinci a gidannan ba.
Khameeni tace Ummi dan Allah kiyi hakuri kafin takarasa Ummi ta d`auketa da mari tace tashi kibani guri mayya tayi gadan iyayen ta shegiya kawai.
Haka Khameeni ta tashi tashiga d`akinta tana kuka tazauna tayi tagumi tana cewa Ammi na da Abbah na da kunanan dabazanyi wannan rayuwar ba Allah kana ganin halin danake ciki Allah ka isarmin haka tadinga cen dai tashiga toilet tad`auro alwala tazo ta tada sallah.

Ummi ce da Kausar a d`aki Ummi tace a'i "wannan yarinyar mayya ce shegiya duk ai'kin danakeyi akanta baya tasiri Amman zata gane kuranta zanje gurin Hajiya Safiya A'i nasan zata bani shawara a kan abinda ya kamata muyi.
      Washe gari

Bangaran Khalifa kuwa suna tashi da safe suka sallami y`an matan su sannan kowa yakama gaban sa Khalifa dai gida yanufa yana zuwa megadi ya bud`e masa yana shiga yayi parking.
Yafito yanufi cikin gidan yana shiga naga wata mata a zaune a kayataccen parlour ita da wata y`ar budurwa.
Yana shigowa y`ar budurwar nan ta tashi dagudu ta rungume shi tana cewa yaya sannu dadawowa yace yawwa Soomeey matarnan dake zaune a parlour tace ke dalla ki 'kalemin yaro ya huta Khalifa yace aa Mami kibarta nida 'kanwata haka yazo ya zauna kusa da Mami ya rungume ta tace son kaje kahuta yace toh Mami yatashi yafice daga parlour yanufi part d`inshi.

Khalifa nafita Mami tabishi da harara tana cewa shege matsiyaci senaga bayanka gashi nafara samun nasara d`abi unka sunfara chanzawa da sannu zan wargaza rayuwar ka Soomeey tace haba Mami wai me yaya Khalifa  yayi miki haka agaban idan shi kinuna kina sanshi abayan idan shi kuma kita tsine mishi gaskiya Mami kidena Mami tace toh uwata bazan denaba shegiya me halin ubanta haka Soomeey ta tashi tabar mata parlour.Khalifa kuwa yana shiga d`akinsa yashiga toilet yayi wanka yad`auro alwala  yafito yashir ya yatada sallah yana idarwa yafara hawaye yana magana yana cewa ni Khalifa meke damuna nadena sallah kan lokaci nike shaye' shaye neman mata ya Allah ka yafemin Allah kafitar dani daga wannan halin danake ciki yakuma fashe wa da kuka.....Wacce Khameeni

Wanene Khalifa 


Seku cigaba da bina dan jin cikakken labarin su
Comments and share please🙏🙏🙏
 *By* *Rufaida* ✍️


đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

     A SANADIN MARAICI

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


    Story and writing

                By

     Rufaida(Rufeey)


 *MARUBUCIYAR* 


 *KAUNA* *CE* *KO* *KIYAYYA* 

 *BANFARGABA* 

 *NA* *fada* *tarkon* *sonshi* 


       *And* *now* 

    *A* *SANADIN* *MARAICI* *🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*


     *M. W. A* 


 ```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. đŸ€™đŸ»``` 

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

_________________________


 *Wannan* *labarin* *kirkirarren* *labarine* *banyi* *dan* *wata* *ko* *wani* *ba* *Wanda* *yaga* *labarin* *yazo* *dai* *dai* *danasa* *toh* *akasine* *ban* *yar* *da* *a* *chanzamin* *labari* *ba* *Wanda* *ya* *chanzamin* *ban* *yafeba* .


 *BISMILLAHIR* *RAHAMANIN* *RAHIM*


PAGE1️⃣0️⃣↪️1️⃣5️⃣


〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

         WACCE KHAMEENI

Khameeni Abbas shine cikakken sunan ta.Mahaifin ta Alhaji Abbah su 2 iyayen su suka haifa Adam shine babba se Abbas shine karami suntaso suna kaunar junansu basa bari abu yasami d`ayan su haka suke rayuwar su dayake mahaifin su yana da hali suna makarartan boko da islamiyya suna zaune a garin katsina.
Dayake tazarar su bata da yawa sosai hakan yasa suke aji d`a'ya komai tare sukeyi a haka harsukayi candy sukaci gaba da karatu fannin kasuwanci suka karanta masha Allah sunsami nasara sosai dan a lokaci kankani sukayi kud`i kasuwancinsu yafi karfi a garin kano hakan yasa suka dawo kano da iyayen nasu dama sunyi gida kowanne da gidansa.
Alhaji Adam ne yafara samun mata yayi aure ya auri wata yar kusa da gidansu mesuna Zainab watansu biyar da aure Alhaji Abbas shima yasami mata mesuna Khadeeja  me hankali da nutsuwa tanasan iyayen sa  sabanin Zainab da bata da mutunci bata ganin kowa da gashi Zainab ta tsani Abbas da matarshi batasan ganin su kokad`an.
Bayan wata tara Zainab ta haifi y'ar ta mace ransuna akasamata KAUSAR Zainab take cemata yar lele shekara yar lele 1 Khadeeja mata haifi y`ar ta mace ransuna akasamata KHAMEENI.
Kausar da Khameeni sunyi wayo sosai Kausar duk inda taga Khameeni setaci zalinta Zainab ma indai taga Khameeni seta daketa.
Mahaifin su Alhaji Abbas Allah yaimasa rasuwa sakamokon  rashin lafiya dayayi mutuwar tataba mahaifiyar su itama bata jimaba tabi mijinta.

Khameeni tana tsoran Hajiya Zainab da y`ar ta Kausar shekara Khameeni 2 akasata a makaranta boko da islamiyya tare akasa su da Kausar kullun se Kausar taci zalin Khameeni gashi Khameeni tana da hakuri sosai.Shekaru nata tafiya 

Haka rayuwa taci gaba da tafiya Hajiya Zainab tafara bin boka duk asirin datake baya kama Alhaji Abbas da matar shi da Khameeni sabida a tsaye suke da addu'a shiyasa bata samin galaba akansu.

Alhaji Abbas ya wayi gari da matsananciyar rashin lafiya baya iya komai sedai komai A'i masa sun shiga tashin hankali anje asibiti Amman ba sauki gaba d`aya yana kasa a lokacin shekarun Khameeni sha 12 Allah yaiwa Alhaji Abbas rasuwa hakika sunji mutuwar sa itakuwa Zainab tayi farin ciki sosai dama tana neman hanyar da zata shekasa lahira sabida tasan aikin boka yayi shiyasa Alhaji Abbas yana kasa sekuma Allah yatakaitamasa wahala yad`auki rayuwar sa gaba 

d`a'ya.Alhaji Abbas yabar ma Khameeni dukiya me yawa yanzu Alhaji Adam ne ze cigaba da juya mata.


Haka aka share makoki bayan shekara 1 Khameeni tayi saukar alkur'ani a lokacin tana da shekaru 13 haka Ammi n ta tacigaba da kula da ita.
Khameeni ta haddace alkur'ani me girma Ammi ta had`a mata walima anci ansha walimar ta 'kayatar sosai haka akagama walimar.

Hajiya Zainab tasami wata 'kawa hatsabibi ya itakekaita gurin boka wato Hajiya Safiya.
Kausar kuwa dama batasan karatu barima na islamiyya tama dena zuwa gaba d`aya Alhaji Adam kuwa Zainab ta rufe masa baki baya iya magana kometayi.
Bayan shekara 4 lokacin Khameeni tagirma shekarunta 17 kuma tayi candy yanzu tana jiran saka mako.
Washe gari Ammi tatashi  da ciwan ciki me tsanani ko asibiti ba ajeba itama tace ga garinkunan Khameeni taji mutuwar sosai tayi kuka haka akakaita makwancinta na gaskiya.Zainab tayi farin ciki Dan kuwa gurin wani hatsabibin boka taje shine yasawa Khadeeja ciwan ciki.


Haka Khameeni ta hakura Alhaji Adam ne yatasota a gaba tadawo gidansa tunda ta dawo Zainab da 'yar ta Kausar suke tsangomarta kullun Khameeni tana cikin kuka sedai tai taiwa iyayen ta addu'a.

Alhaji Adam kuwa duk abinda Zainab takewa Khameeni yasani yanaso yayi magana Amman ya kasa sabida anrufe masa baki.
Khameeni kuwa a tsaye take da addu'a Zainab kullun burinta taga bayan Khameeni Amman Allah baya bata dama.
Khameeni yanaso taci gaba da karatu Amman Zainab ta hana hakan yasa ta hakura.
Hakika Khameeni tana shan wuya a gidan Ummi wato Zainab da yar lele Kausar suna gallaza mata matuka.Toh masu karatu kunji wacce KhameeniComments and share please🙏🙏🙏
 *By* *Rufaida* ✍️


đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

    *A* *SANADIN* *MARAICI* 

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


   Story and writing

               By

     Rufaida(Rufeey)


MARUBUCIYAR


 *KAUNA* *CE* *KO* *KIYAYYA* 

 *BANFARGABA* 

 *Na* *fada* *tarkon* *sonshi* 


      *And* *now* 

    *A* *SANADIN* *MARAICI* *🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*


     *M. W. A* 


 ```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. đŸ€™đŸ»``` 

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

_________________________


 *Wannan* *labarin* *kirkirarren* *labarine* *banyi* *dan* *wata* *ko* *wani* *ba* *Wanda* *yaga* *labarin* *yazo* *dai* *dai* *danasa* *toh* *akasine* *ban* *yarda* *a* *chanzamin* *labari* *ba* *Wanda* *ya* *chanzamin* *ban* *yafeba* .


 *BISMILLAHIR* *RAHAMANIN* *RAHIM*


PAGE1️⃣5️⃣↪️2️⃣0️⃣


〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

        WANENE KHALIFA

Khalifa Muhamud shine cikakken sunan shi.


Mahaifin shi Alhaji Muhamud attajirin me kud`ine  matar shi Hajiya Salma  sunyi auren soyayya suna zamansu Lapiya seda sukai shekara 3 da aure sannan Allah yabawa Hajiya salma ciki.
Haka suka dinga rainan cikin har Allah ya sauketa lafiya ta haifi d`anta namiji aka Samasa KHALIFA.
Khalifa kyakyawan yarone yataso cikin soyayyar iyayen nasa yayi wayo sosai yana da shekara 3 akasa shi makaranta boko da Islamiyya.
Khalifa yana da kokari sosai Khalifa nada shekara 5 mahaifiyar shi tarasu saka makon haihuwa da tazo yi da ita da abinda ta haifa duk Allah yaimusu rasuwa.
Alhaji Mahmud yaji mutuwar matar tashi Khalifa kuwa kuka yadin gayi wai ina Maman sa sedai ararrasheshi kawai a haka har a kayi arba'in.
Bayan shekara 5 a lokacin shekarun Khalifa 10 yayi saukar alkur'ani yan zu hadda yake a lokacin ne Alhaji Mahmud yaga yakamata yayi aure dan Khalifa yana bukatar kulawa.
Alhaji Mahmud ya nada wani abokin Alhaji Adam yana zuwa gidan Alhaji Adam anan yaga kawar matar Alhaji Adam wato Safiya yanuna yana Santa dama ita Safiya tunda taganshi taji tana sanshi.
Ba a d`au wani lokaci ba a kayi auren ta tare Safiya tunda taga Khalifa ta tsaneshi Amman se bata nunaba.
Se take nuna tanasan Khalifa shikuma Alhaji Mahmud dayaga haka se yaji dadi sosai Khalifa ma seyasaki jiki da ita dan kuwa tana nuna mai kauna sosai.Bayan shekara 6 Hajiya Safiya ta haihu yarta shekarun ta 5 Soomeey suke cemata Soomeey tanasan yayan ta Khalifa shima yana San kanwar tashi 

Khalifa ya girma shekarun sa 16 haryayi candy ayanzu  Khalifa  zetafi China karatu Soomeey tasha kuka sosai da 'kar aka lallabata.
Khalifa yatafi karatu Hajiya Safiya ta dage dabin bokaye ta mallake Alhaji Mahmud se abinda tace akeyi.
Hajiya Zainab da Hajiya Safiya hatsabibai ne shiyasa halinsu yazo d`a'ya aminan junane sosai tare sukebin bokaye.
Khalifa yanada addini sosai gashi baya wasa da addu'a hakan yasa Hajiya Safiya bata samin galaba  akan shi.
Khalifa yana karatun shi yanda ya kamata yakusa gamawa ma.
Soomeey tagirma yan zu shekarun ta 14 da akwai ranar da Hajiya Safiya taje da ita gidan kawarta Hajiya Zainab tunda Soomeey taje gidan taji ta tsani 'kawar Mamin nata wato Ummi da 'yar ta Kausar 'yar lele Soomeey taji bata sansu harsuka dawo gida Soomeey bata dariya Mami kuwa bata kula taba.
Khalifa yagama karatun shi yadawo gida Hajiya Safiya tamishi tarba me kyau.
Khalifa yacigaba da kula da kasuwancin mahaifin nasa da companys kuma masha komai yana tafiya daidai.
Bayan shekara 3 da dawowar Khalifa ne Hajiya Safiya ta karbo wani magani a gurin bokansu indai yaci maganin toh zedena ibada daganan se asan meza ayi masa haka tadawo gida cike da murna.
Tana dawowa ta had`awa Khalifa abinci dan taga yakusa dawowa daga office.
Khalifa yana dawowa daga office yaje part d`inshi yayi wanka sannan yaje ya gaishe da Mami ta amsa fuska asake sannan tace yarona ga abinci A'i kuwa dama Khalifa yinwa yakeji haka yaci abincinnan.
Tunda Khalifa yaci abincinnan komai nasa ya chanza yadena ibada Mami kuwa tana kula dashi dan haka takoma gurin bokan.

Tana zuwa tace wa bokan tanaso Khalifa yadinga bin mata yadinga shaye_shaye A'i kuwa boka yaimata ai'ki nan take ta ajiye masa makudan kud`i ta tafi.Bayan 'kwana 2 Khalifa ya fara shaye_shaye da bin mata shine zuwa club a club d`innema ya had`u da wasu abokai HILAL da BASHIR to sudama halin sune.
Tun mahaifin shi be ganewa haryazo yana ganewa sabida yaga baya 'kwana a gida tunyana masa magana haryadena sedai addu'a dayake wa d`annasa itakuwa Mami idan Daddy yana yiwa Khalifa fad`a setace gaskiya yadena takurawa Khalifa dayake  shima ta mallakesa shine yadena magana Amman yanaso yayiwa d`annasa magana Amman yakasa yana mamakin chanzawar d`annasa.
Soomeey kuwa yanzu tayi candy kullun tanayiwa yayan ta Khalifa addu'ar Allah yashir yashi dan kuwa batasan Mami ce tajefashi a wannan halin ba.
Khalifa kuwa abinda yakeyi wataran yana damunsa har kuka yakeyi yarasa meyake damunsa....
Toh masu karatu kunji wanene Khalifa         CIGABAN LABARIN
Comments and share please🙏🙏🙏


By Rufaida✍️


đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

   *A* *SANADIN* *MARAICI* 

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


    Story and writing 

                By

     Rufaida(Rufeey)


 *MARUBUCIYAR* 


 *KAUNA* *CE* *KO* *KIYAYYA* 

 *BANFARGABA* 

 *Na* *fada* *tarkon* *sonshi* 


       *And* *now* 

       *A* *SANADIN* *MARAICI* *🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*


     *M. W. A* 


 ```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. đŸ€™đŸ»``` 

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

_________________________


 *Wannan* *labarin* *kirkirarren* *labarine* *banyi* *dan* *wata* *ko* *wani* *ba* *Wanda* *yaga* *labarin* *yazo* *dai* *dai* *danasa* *toh* *akasine* *ban* *yarda* *a* *chanzamin* *labari* *ba* *Wanda* *ya* *chanzamin* *ban* *yafeba* .


 *BISMILLAHIR* *RAHAMANIN* *RAHIM*


PAGE2️⃣0️⃣↪️2️⃣5️⃣


〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

          CIGABAN LABARIN

 Washe gari Ummi ce take waya da 'kawar ta Hajiya Safiya tana cewa yau zasuzo ita da Kausar idan Allah yakaimu zanzo zamuyi wata magana.
Mami tace sekinzo nima da akwai maganar danakeso muyi dake tace toh shikkenan haka sukai sallama takashe wayar.Ummi tana kashe tafito parlour tashiga d`akin Khameeni tatarar da ita a 'kwance tana barci akan dadduma A'i kuwa tasa 'kafa ta, takata  da karfin tsiya Khameeni cikin bacci taji azaba da sauri ta, tashi tana tashi taga Ummi ce. 
Ummi tace shegiya wato 'kwanciya kikayi koh? toh kitashi ki gyaramin bedroom  kizo ki d`ora breakfast idan kin gama kishiga d`akin 'yar lele idan ta, tashi daga bacci ki gyara mata d`aki Khameeni tace to Ummi haka tatashi ta fita.
Duk abinda Ummi tasata tayi shi tashiga d`akinta Kausar taga haryanzu bata tashiba hakan yasa ta shiga toilet tana wanke wa.
Kausar kuwa tun shigowar Khameeni idanta bi'yu hakan yasa ta d`uki ruwan roba ta zubawa kanta ta fasa wata uwar kara.Da gudu Khameeni ta fito daga toilet d`in hannun ta d`auke da kofin ruwa daidai lokacin Ummi tashigo a zabure tana tanbayar 'yar lele lapiya meya sameki? Kausar ta saki kukan muna furci tace Ummi kinga Khameeni ina bacci ta zubamin ruwa ta, tasheni daga bacci.

Ummi tace toh bakar muguwa yanzu Kausar d`in kika watsawa ruwa? A'i kuwa zakici uban ki nan tafara jibgar Khameeni haka tagama jibgar ta, tace tacigaba da gyaran d`akin Ummi tafice tana ta tsinewa Khameeni da zaginta.
Ummi nafita Kausar tasaka dariya ta dungurewa Khameeni kai tashiga toilet.
Itakuma Khameeni tacigaba da gyara d`akin tana hawaye a haka tagama ta fita taga Abbah a parlour ta gaishe shi ya amsa yabita da kallan tausayi yarasa meyasa baya iyayiwa Zainab magana akan abinda takewa Khameeni.
Khameeni tashige d`aki tayi wanka tafito parlour lokacin har su Ummi sunyi breakfast suna zaune a parlour.Ummi tana cewa Kausar anjima zasuje gidan Hajiya Safiya ta shirya Kausar tace toh Ummi.
Itakuwa Khameeni taji dad`in fitar dazasuyi dan tad`an sake kafin su dawo.

       °°°°  °°°°  °°°°  °°°°  °°°°  °°°°

Bangaran Khalifa kuwa yau beje ko inaba yana gida abinsa.Mami ce take cewa Soomeey saura idan su Hajiya Zainab sunzo kinuna musu bakin halin naki Soomeey dai ba tace komai ba.Nandai Mami ta 'karaci surutun ta tayi shuru.
      °°°°  °°°°  °°°°  °°°°  °°°°  °°°°  °°°°

Su Ummi ne suke shirin zuwa gidan Hajiya Safiya ita da Kausar sun shirya Ummi ta 'kwalawa Khameeni kira!.Da sauri ta fito Ummi tace toh shegiya zamu fita saura kishiga d`aki kita bacci har lokaci ya 'kure baki d`aura abincin dinner ba kiga yanda zanyi dake wallahi.
Itadai Khameeni batace komai ba haka suka fice Kausar ce keyin driving haka harsuka 'karasa gidan su Khalifa me gadi yabud`e musu get suka shiga sukayi parking suka fito.
Khalifa yana zaune a farfajiyar gidan yana charting a wayar sa Kausar tasaki baki da hanci tana kallan sa.......
Comments and share please🙏🙏🙏🙏By Rufaida✍️


đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

   *A* *SANADIN* *MARAICI* 

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


    Story and writing 

                By

     Rufaida(Rufeey)


 *MARUBUCIYAR* 


 *KAUNA* *CE* *KO* *KIYAYYA* 

 *BANFARGABA* 

 *Na* *fada* *tarkon* *sonshi* 


       *And* *now* 

       *A* *SANADIN* *MARAICI* *🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*


     *M. W. A* 


 ```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. đŸ€™đŸ»``` 

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

_________________________


 *Wannan* *labarin* *kirkirarren* *labarine* *banyi* *dan* *wata* *ko* *wani* *ba* *Wanda* *yaga* *labarin* *yazo* *dai* *dai* *danasa* *toh* *akasine* *ban* *yarda* *a* *chanzamin* *labari* *ba* *Wanda* *ya* *chanzamin* *ban* *yafeba* .


 *BISMILLAHIR* *RAHAMANIN* *RAHIM*


PAGE2️⃣5️⃣↪️3️⃣0️⃣


〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Kausar kallan shi take kamar wata mayya dataga nama Khalifa kuwa besan tana yiba ma Kausar tunda take bata ta'ba ganin kyakyawan daya tafi da hankalin taba irin  Khalifa.


Taji wani irin sanshi nashiga zuciyar ta taji masifar sanshi Wanda bata ta'ba jiba Kausar takusa kifewa sabida kallan Khalifa da take da sauri Ummi tarukota tana cewa kiname zakije kijiwa kanki ciwo? Kausar tace bakomai.


Itakuwa Ummi taga dai Khalifa Amman batasan Kausar shi take kalloba harta kusa 'kifawa. Ummi tace toh dai kikula hakadai suka shige parlour Kausar harda kuma jiyowa ta kalli Khalifa harsuka shige..


Suna shiga parlour sukaga Mami da Soomeey suna kallo suka karasa ciki Soomeey ta gaida Ummi ta amsa Kausar ma ta gaida Mami ta amsa Soomeey ta, tashi tabar parlour tafita inda Khalifa yake zaune.


Ummi tace wa Mami yanzu naga wannan shegen Khalifa nan Ummi tace tsinanne A'i akan shi nakeso kibani shawara Ummi tace nikuma kan wannan tsinanniyar yarinyar nan ne Mami tace A'i matsalar iri d`a'ya ce. Ummi ta kalli Kausar tace Kausar kije gurin Soomeey mana Kausar tace toh Ummi nan ta, tashi tafice.


Mami tace yawwa kawo kunnanki kiji nan Mami ta rad'awa Ummi wata magana wanda ninakasa jin abinda ta rad'a mata nan naga sunyi shewa sun tafa.


Ummi tace gaskiya Safiya ke shed`ani yace nan Mami tace kinmantani ne? Ummi tace yaushe  zamu sami su Alhaji da maganar? Mami tace nanda 'kwana bi'yu dai Ummi tace toh shikkenan sannan Ummi takuma cewa  toh kina ganin idan muka sami su Alhaji da maganar zasu amince? Mami tace A'i dole su amince A'i kafin 'kwana bi'yu zamuje gurin boka LAMARUDU yakuma rufe musu baki kinga kuwa dole su amince.nan sukasa shewa suna wata makirar dariya..


Kausar nafita ta hangi Soomeey ita da Khalifa da sauri takarasa gurin tazauna a d`a'ya daga cikin kujerin dasuke gurin tace sannunku Soomeey ce kad`ai ta amsa Khalifa kuwa ko kallanta beyiba ballema ya tanka mata, Shi dai hirarsu kawai suke shida Soomeey.


Kausar se, saka musu baki take Soomeey ce metanka mata Kausar se wani yau'ki take kamar wani ku'bewa tana wani karairaya. Soomeey tarigada tagano Kausar..


Ita Soomeey abinma dariya yadinga bata Kausar tana magana tana wani kashe murya Khalifa kuwa tunda ya kalleta sau d`a'ya bekuma kallan taba sabida yafuskanci yarinyar tafiya rawar kai gaba d`a'ya ma yarinyar batai maiba.


Hakan yasa yacewa Soomeey shize shiga ciki bayasan surutu Soomeey tace toh shikkenan Yaya Kausar kuwa kamar tayi kuka dan  haushi Soomeey kuwa dariya takusa  zuwar mata Amman  seta basar itama Soomeey tabar gurin.


Hakan yasa Kausar takoma parlour tacewa Ummi suzo su tafi gida dama su  Ummi sun gama tattau nawa hakan yasa Ummi ta, tashi suka fito Mami ta rakasu Ummi tace kinga shegen yatashi Mami tace Hmmm wallahi Zainab natsani yarannan Ummi tace kedai ki 'kwantar da hankalinki badai aikin boka yafara kama shiba aike kinmaji dad`i nikuwa kullun kashe kud`i nake Amman mayyar yarinyar nan  haryanzu ba abinda yasa meta..


Mami tace ki 'kwantar da hankalinki komai zeyi daidai nandai su Ummi suka shiga mota Kausar taja motar suka fice daga gidan suna tafiya Kausar tace Ummi nifa naga Wanda nakeso kuma shizan aura Ummi tace masha Allah tana murmushi tace wanne shi kuma a ina yake? Kausar tace Yayan Soomeey a zabure Ummi tace wacce Soomeey? Kausar tace ta gidan Mami mana A'i kuwa Ummi......
Comments and share please🙏🙏🙏🙏🙏By Rufaida✍️

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

   *A* *SANADIN* *MARAICI* 

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


    Story and writing 

                By

     Rufaida(Rufeey)


 *MARUBUCIYAR* 


 *KAUNA* *CE* *KO* *KIYAYYA* 

 *BANFARGABA* 

 *Na* *fada* *tarkon* *sonshi* 


       *And* *now* 

       *A* *SANADIN* *MARAICI* *🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*


     *M. W. A* 


 ```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. đŸ€™đŸ»``` 

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

_________________________


 *Wannan* *labarin* *kirkirarren* *labarine* *banyi* *dan* *wata* *ko* *wani* *ba* *Wanda* *yaga* *labarin* *yazo* *dai* *dai* *danasa* *toh* *akasine* *ban* *yarda* *a* *chanzamin* *labari* *ba* *Wanda* *ya* *chanzamin* *ban* *yafeba* .


 *BISMILLAHIR* *RAHAMANIN* *RAHIM*


PAGE3️⃣0️⃣↪️3️⃣5️⃣


〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Ummi tace me!!? Toh wallahi baki isaba wannan d`an iskan yaran mashayi me neman mata toh wallahi baki isaba tun wuri ki janye wannan 'kudirin naki mezaki da mashayi? Kausar tace gaskiya nidai Ummi ina sanshi a haka.


Ummi tace toh wallahi baki isaba kar nakumaji kinyi zancen shi Kausar tace chab toh nidai shi nakeso Ummi bata kuma kula Kausar ba harsuka je gida Kausar se cin magani take haka tashige d`akinta tana tunanin yanda zata bullowa lamarin dan itadai tanasan Khalifa ga kyau ga kud`i dolema ta auri gayan nan gaskiya ya had`u.


Tanata, tunanin meya kamata tayi yazama dole tasamo number sa a gurin Soomeey toh Amman anya Soomeey zata bata number kuwa? seta tuna Soomeey da Khameeni suna shiri  yazama dole gobe taja Khameeni suje gidan su Soomeey nandai hankalinta ya 'kwanta.


Kausar tanufi d`akin Khameeni tana zuwa ta ganta tayi tagumi Kausar tace gobe zamuje gidan su, Soomeey Khameeni tace toh Kausar tafice daga d`akin tanufi nata d`akin dan bata bi takan Ummi ba.


Khameeni taga yamma tayi tafito dan ta d`aura abincin dinner haka tashiga kitchen ta d`aura abincin tana gamawa ta jera a dining area takoma d`aki dan tayi sallah tashiga toilet tayi alwala tafito ta, tada  sallah tana idarwa ta d`auki alkur'ani tana karatu sheda  tayi sallar issha sannan ta fito ta d`ibi abinci tai d`akinta tana gamawa ta fito ta wanke abinda ta bata..


Sannan takoma d`aki tayi wanka tai shirin bacci tayi addu'a ta 'kwanta bacci.


Kausar kuwa se tunanin Khalifa take San shine ke nukurkusar zuciyar ta Allah , Allah take gobe tayi hakadai bacci ya d`auke ta cike da tunanin Khalifa.


Ummi kuwa tunda Kausar tazo mata da zancen Khalifa takeso taji ta kara tsanar shi inbandama abin Kausar me zatayi da wannan shegen yaran duk a fili Ummi take wannan maganar..


Washe gari weekend Khameeni tayi duk abinda ya dace ta gyara wa Ummi d`aki sannan tashiga tana gyara na Kausar tana cikin gyara Kausar tace anjima wajen karfe 4pm tashirya zasu gidan su Soomeey Khameeni tace toh haka tagama gyaran d`akin tafita..


    °°°°  °°°°  °°°°  °°°°  °°°°  °°°°

Bangaran Khalifa kuwa yau weekend ne ba inda zashi se zuwa dare ze fita haka yazo ya gaishe da Daddy da Mami Soomeey kuma tagaidashi  sannan sukayi breakfast yakoma part d`inshi yad`anyi shaye_shayen sa bacci ya d`auke shi bashi yatashiba se wajen karfe 3pm sannan yai alwala yayi sallah yana idarwa yashiga wanka yana fitowa yasa kaya yad`auki wayar sa yana charting..


    °°°°  °°°°  °°°°  °°°°  °°°°  °°°°

Bangaran Khameeni kuwa harta shirya tana jiran Kausar , Khameeni abaya ce ajikinta tayi kyau sosai kamar balarabiya, Kausar kuwa atanfa tasaka riga da skirt ne ajikinta sun kamata sosai gata kamar kara ba Shape ba komai gashi tad`ame jiki setayi kamar tsuntsuwa..😂😂


Gashi tasaka wani munafikin mayafi dashi 'kwara babu haka suka fito Ummi tacewa Kausar inazakije da mayyar nan Kausar tace rakani zatayi Ummi tace ok itadai Khameeni batace komai ba haka suka fita Kausar nazagin Khameeni dan taga Khameeni ta fita kyau haka suka shiga mota Suka fice daga gidan Kausar ta kalli Khameeni tace yawwa inaso idan munje gidan su, "Soomeey kice mata dama wata 'kawar kice tace tanasan Yayan ta shiyasa tace dan Allah kizo gidan su kikarbar mata number sa kinji na fad`a miki kuma sena tashi daga gurin sannan zaki fad`a mata wallahi idan bakiyi yanda nace ba wallahi kin shiga uku dan sena had`a miki sharrin a gurin Ummi Khameeni tace toh haka suka karasa gidan megadi yabude musu get suka shiga dai,dai lokacin dasuka fito daga motar Khalifa yana tsaye jikin window d`in d`akin sa ya hango su ba wacce idansa yasauka akanta se Khameeni..


Gabamsane ya yanke yafad`i harseda yadafe kuma yakasa d`auke idansa daga kanta har suka shige.


Suna shiga sukaga Mami a parlour suka gaishe ta, ta amsa tana hararar Khameeni Kausar tace Mami Soomeey tananan? Mami tace tana d`akin ta hakan yasa suka shiga d`akin suka ganta tana charting a wayar ta Soomeey tana ganin Khameeni ta sakar mata murmushi haka suka zauna haka sukad`anyi hira se Kausar ta kashewa Khameeni ido sannan tafita ashe Soomeey taganta nan Khameeni tafad`awa Soomeey abinda Kausar tasata Soomeey tai murmushi tace Khameeni bansanki da karya ba dan haka kifad`an gaskiya nan dai Khameeni tafad`awa Soomeey gaskiya Soomeey tace A'i nasani tace ok bari nabaki number seki bata indai Yaya Khalifa ne zata gane..


Nandai Soomeey tabawa Khameeni number Khalifa sannan suka fito parlour bakowa a parlour hakan yasa suka fito waje suka hango Kausar a zaune suka 'karasa gurin suma suka zauna Soomeey takoma ciki takawo musu ruwa da lemo.


Kausar tana sane tazubawa Khameeni  lemo a jiki Amman seta nuna bata saniba Soomeey tace haba Kausar bakiga abinda kikai mata bane? Kausar tace toh a'i  bansani ba Soomeey tace Khameeni taso muje ki chanza kaya Khameeni tace aa Soomeey kibarshi kawai.


Duk abinda yafaru akan idan Khalifa yafaru hakan yasa yakara jin tsanar Kausar takaru a zuciyar sa.....Comments and share please🙏🙏🙏🙏By Rufaida✍️đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

   *A* *SANADIN* *MARAICI* 

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


    Story and writing 

                By

     Rufaida(Rufeey)


 *MARUBUCIYAR* 


 *KAUNA* *CE* *KO* *KIYAYYA* 

 *BANFARGABA* 

 *Na* *fada* *tarkon* *sonshi* 


       *And* *now* 

       *A* *SANADIN* *MARAICI* *🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*


     *M. W. A* 


 ```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. đŸ€™đŸ»``` 

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

_________________________


 *Wannan* *labarin* *kirkirarren* *labarine* *banyi* *dan* *wata* *ko* *wani* *ba* *Wanda* *yaga* *labarin* *yazo* *dai* *dai* *danasa* *toh* *akasine* *ban* *yarda* *a* *chanzamin* *labari* *ba* *Wanda* *ya* *chanzamin* *ban* *yafeba* .


 *BISMILLAHIR* *RAHAMANIN* *RAHIM*


PAGE3️⃣5️⃣↪️4️⃣0️⃣


〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Khalifa yaji yakuma tsanar Kausar sabida abinda taiwa Khameeni. Kausar ce tacewa Khameeni ta, taso sutafi gida haka Khameeni ta, tashi suka nufi gurin mota suka shiga sukabar gidan Kausar se zagin Khameeni take Kausar tayi parking tace bani number mugani Khameeni ta mika mata Kausar ta kar'ba tasa a wayar ta sannan ta kalli Khameeni tace dan ubanki fitarmin daga mota.


Khameeni tace dan Allah kiyi hakuri wallahi bani da kud`in dazan koma gida Kausar tace toh inaruwana dalla fitarmin a mota Khameeni haka tafito daga motar.


Kausar taja motar ta ko tausayi babu gashi unguwar shuru ba mutane a tsorace Khameeni take  tafiya abin tausayi hawaye ne kezuba a idanuwan ta wada bata damu data gogeba haka taci gaba da tafiya.


Tana cikin tafiya se wasu samari suka tareta gashi layin ba mutane samarin sukace 'yan mata meya kawoki nan? Khameeni bata kulasuba ta wuce sabida ta fuskanci irin 'yan iskan samarinnan ne sukuma hakan datai saiya 'bata musu rai hakan yasa suka bita suka zagayeta suka fara zaginta. 


Khameeni kuwa kuka kawai take tana basu hakuri d`a'ya daga cikinsu ya wanka mata mari  suka fincike mayafin abayar jikinta nankuwa gashin kanta yazubo suna shirin yaga rigar jikin ta wata mota tazo tayi parking a kusa dasu da sauri nacikin motar yafito dan harsun fara yaga rigar jikin ta yana fitowa naga ashe Khalifa ne yana zuwa gurin yafara jibgar samarin dasuka ga ba haza suka gudu.


Abinda yasa Khalifa zuwa gurin shine su Khameeni basu dad`e dafita daga gidan su ba Khalifa yafito dan yaje gurin abokanan sa toh shine yazo wucewa yaga wayannan samarin shi bemasan Khameeni bace.


Se sannan Khalifa ya kalli inda take a tsaye da sauri yazaro ido ganin wacce yagani d`azu agidan su itace da sauri ya mika mata mayafin ta karba ta yafa Khalifa yace me kike anan? Tace bakomai yace ok ina wacce kuke tare? Khameeni tad`ago da sauri tana kallansa toh wannan a inayasan mu bi'yu ne kamar yasan tunanin datake yace ni Yayan Soomeey ne sunana Khalifa kefa? Tace Khameeni yace wow nice name tace thank u.


Yace ok mekike anan? Da zata masa karya toh kuma gashi bata iyaba yasa tace Kausar ce tace baza tafi daniba na saukar mata a mota yace ok toh ita meyasa aka bata mota kekuma ba abakiba? Khameeni tayi shuru Khalifa yace kodai Abbah Ku besan tana d`auka ba? Khameeni tace ansani yace ok toh ke meyasa baki da ita.?Khameeni tece A'i ni Ammi na da Abbu na Allah yaimusu rasuwa tagad`a a sanyaye Khalifa yace ayya sorry ban saniba Allah yajikan su tace Ameen nagode yace karki damu yace ok kishiga mota nakaiki gida tayi shuru yace karki damu bazan cutar dakeba tace A'i nima bance zaka cutar daniba yace ok toh muje.


Haka tashiga motar yatada motar suka wuce yana cewa kimin 'kwatancen gidan nankuwa yaimasa kuma yagane haka yaita janta da hira cen kuma seyace kibani number ki mudinga gaisawa tace A'i bani da waya yace ayya yace inbaki tawa kinaso? Tace aa yace meyasa tace bakomai yace ok shikkenan.


Daga nesa da gidan Khameeni tace ya sauketa ba musu ya tsaida motar sannan ya kalleta yace gobe zan aiko Soomeey gurin ki tace nikuma? Yace eh mana tace toh sannan tace masa ta gode sannan tafita daga motar tashiga gida Khalifa yai murmushi seda yaga shigewar ta sannan yatafi.


Yanata tunanin Khameeni ko ba' a fad`amasa ba yasan  yarinyar tashiga zuciyar sa tafarar d`a'ya tasace zuciyar sa yai murmushi yama fasa zuwa inda zashi yakoma gida yana komawa yakira Soomeey tana zuwa yace sister zauna kiji wani labari nan ya fad`a mata duk abinda yafaru Soomeey tace Yaya wallahi Kausar d`innan muguwa ce nan Soomeey tabashi labarin Khameeni bata 'boye masa komai ba Khalifa ya tausayawa Khameeni sannan Soomeey tad`ora dacewa Yaya Kausar fa sanka take nan tafada masa yanda sukayi yau Khalifa yace Hmmm toh nimezanyi da ita nifa barikiji 'kanwata inada wacce nakeso kuma ita zan aura insha Allah Soomeey tace Yaya wace yace Khameeni Soomeey tadaka tsalle tace Amman naji dad`i wallahi toh Amman fa Yaya a 'kwai matsala yace tame? Soomeey tace kasan Kausar nasanka shiyasa nace a kwai matsala yace ki 'kale batun wannan nifa asawun marasa  hankali na d`auke ta.


Soomeey tasa dariya Khalifa yace Yawwa tace min bata da waya Soomeey tace eh yace ok yanzu kishirya muje se asiya mata Soomeey tace A'i ashirye nake yace ok muje haka suka fito suka shiga mota basu tsaya ko inaba se gurin da akesaida wayoyi suka shiga yacewa Soomeey ta zabar mata tace Yaya a siya matadai yar saffasaffa sabida halin yan gidan su yace ok toh zabar mata Soomeey taduba taga wata iPhone7+ tace Yaya a siya mata wannan haka suka biya suka fito yace mata gobe zaki kai mata tace toh Yaya haka suka koma gida.


    °°°°  °°°°  °°°°  °°°°  °°°°  °°°°

Bangaran Khameeni kuwa tana shiga taga Ummi da Kausar a zaune a parlour Ummi tace daga gidan ubanwa kike? Khameeni tace Ummi Kausar tace nasaukar mata a mota shine nasauka shiyasa ban dowo da wuri ba Kausar tace Ummi karya take wani dan iskane yazo suka tafi tare Ummi tace shegiya 'yar iska karuwa kawai ni wuce ki d`aura mana abincin haka tawuce ko d`aki Ummi bata bari ta shiga ba tace ta wuce kitchen suna ta zagin ta Allah sarki haka ta d`ora abincin tana gamawa ta jera a dining table ta wuce d`akin tafita.


Tashiga toilet tayi wanka ta d`auro alwala tafito ta, tasa sallah tana idarwa ta d`auki alkur'ani tana karanta wa seda akayi sallar issha ta, tashi tad`ebo abinci taci tana gamawa taje ta wanke sannan tadawo d`akin ta, tayi tagumi tana tunanin halin datake ciki..


Kausar ta gama abinda zatayi tahau kan bed ta 'kwanta tad`auko wayar ta ta kira number Khalifa tanata ringing ba a d`auka ba haka taita kira a 'kalla tayi kira yakai 10 Khalifa daya gaji da kiran ya d`auka Amman beyi magana ba Kausar dataji an d`auka tace.


Kausar: hello masoyina.


Khalifa: place wacece.?


Kausar: masoyiyar kace Kausar.


Khalifa kuwa yagane ko wace dan haka yace 


Khalifa:wace kuma Kausar.?


Kausar: nidai wallahi tunda naganka a gidan Ku naji zuciya ta, takamu da sanka.


Khalifa: ok waidama kece seki cemin wannan yarinyar ce me rawar kai senafi ganewa toh bari kiji nafad`a miki ni Khalifa bana sanki baki minba mezanyi dake baki da kamunkai baki da abinda zaki burgeni dan haka  karki 'kara kirana nafad`a miki yai tsaki ya kashe wayar sa.


Kausar kuwa kuka tasa tana tunanin maganar daya fad`a mata.


Ummi ce suke waya da Mami tana cewa insha Allah dawuri zan shirya semu tafi gurin bokan haka sukai sallama.


Khalifa kuwa se tsaki yakeja Yanata mita shi kad`ai secen kuma yai murmushi daya tuna Khameeni haka ya 'kwanta cike da tunanin ta da mafarkin ta..


Washe gari wajen karfe 10 nasafe Ummi ta, tafi gidan aminiyar tata dan zuwa gurin boka LAMARUDU.....Toh fans anan zan tsaya semun hadu a next pageComments and share please🙏🙏🙏


By Rufaida✍️đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

   *A* *SANADIN* *MARAICI* 

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


    Story and writing 

                By

     Rufaida(Rufeey)


 *MARUBUCIYAR* 


 *KAUNA* *CE* *KO* *KIYAYYA* 

 *BANFARGABA* 

 *Na* *fada* *tarkon* *sonshi* 


       *And* *now* 

       *A* *SANADIN* *MARAICI* *🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*


     *M. W. A* 


 ```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. đŸ€™đŸ»``` 

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

_________________________


 *Wannan* *labarin* *kirkirarren* *labarine* *banyi* *dan* *wata* *ko* *wani* *ba* *Wanda* *yaga* *labarin* *yazo* *dai* *dai* *danasa* *toh* *akasine* *ban* *yarda* *a* *chanzamin* *labari* *ba* *Wanda* *ya* *chanzamin* *ban* *yafeba* .


 *BISMILLAHIR* *RAHAMANIN* *RAHIM*


PAGE4️⃣0️⃣↪️4️⃣5️⃣


〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Ummi tana zuwa taga Mami harta shirya haka suka d`auki hanya sunyi tafiya menisa sannan suka shiga wani daji sukayi parking motar su a gurin suka fito suka shiga cikin dajin suna ta, tafiya a kasa sannan suka tsaya adede wani dan gida suka shiga ciki suna shiga naga wani bakin mutum bakaya ajikinsa sewasu ganye daya d`add`aura suka shiga suka zauna yace tunkan kuzo nasan dazuwan ku.


Ya kallesu yace abinda kuke shirin yi ze iya zama matsala nan gaba sukace boka mudai kawai A'i mana aikinnan yace shikkenan toh sannan yabasu wani kullin magani yace su sakawa mazajen nasu a, abinci ko abinsha indai sunci kome zakuce musu ba zasuyi musuba nan suka zubemai kud`i suka fito.


Mami tace toh idan muka zuba musu sukaci bayan 'kwana 1 semuje musu da zancen sukayi shewa suka tafa suka fito daga gidan bokan.


Kausar Ummi nafita itama tasa 'kafa tafita zuwa gidansu 'kawar ta.


Soomeey tashirya dan zuwa gurin Khameeni Khalifa ne ya kaita beshiga gidan ba yace idan tagama taimai waya yazo yad`auke ta, tace toh shikuma yatafi itakuma tashiga gidan.


Tana shiga parlour gidan tayi sallama Khameeni ta fito tace Soomeey kece? Soomeey tace eh Khameeni ke kad`aice a gidan? Khameeni tace eh wallahi duk sun fita Khameeni tace tawo mu shiga d`akinta haka suka shiga Soomeey tazauna Khameeni kuma taje takawo mata lemo da ruwa.


Soomeey tasha ruwan sannan tabud`e jakarta ta fito da wata leda tami'kawa Khameeni , Khameeni tace meye a ciki? Soomeey tace bud`e kigani Khameeni tana budewa taga 'kwalin waya tabud`e 'kwalin tace Soomeey waya ce fa Soomeey tace eh takice A'i Khameeni ta zaro ido tace nikuma? Soomeey tace eh mana Khameeni tace aa Soomeey badai niba..


Soomeey tace Yaya Khalifa yace nakawo miki Khameeni tace Soomeey kiyi hakuri Amman bazan iya kar'bar wayar nan ba Soomeey tace sabida me? Tace kinsan Kausar da Ummi Soomeey tace toh inaruwan ki dasu? Khameeni dai shuru tayi Soomeey kuwa tad`auko wayar ta a jaka takira Khalifa tace Yaya tace bazata kar'baba Khalifa yace bani ita Soomeey tami'kawa Khameeni wayar ba musu ta karba.


Khalifa yace haba Khameeni kinsan ba kyau maida  hannun kyauta baya place ki karba dan Allah Khameeni tace toh  Yaya Khalifa nagode yace bakomai sannan tami'kawa Soomeey wayar Soomeey tanunawa Khameeni yanda zatai amfani da wayar dama tun a gida Khalifa yasaka mata number sa yayi saving.


Soomeey tanuna mata komai sannan tace tadinga boye wayar karsu gani ta mata wayar a silent A'i kuwa ba, a jimaba Khalifa yakira yace anjima zasuyi waya tace toh.


Soomeey tana gamawa tace Khalifa yazo ya d`auketa be jimaba se gashi Soomeey tace Khameeni tazo tarakata haka taje tarakata suna fitowa Khalifa ya kurawa Khameeni ido yana jin Santa nakara shiga zuciyar sa suna karasa wa Khameeni ta gaishe shi ya amsa sannan tace ita zata koma ciki karsu Ummi su dawo tayiwa su Soomeey sallama takoma ciki sukuma suka wuce gida..


Bayan awa d`a'ya da tafiyarsu Ummi tadawo taga bataga Kausar ba tahau kiran Khameeni, Khameeni tana zuwa taiwa Ummi sannu dazuwa Ummi bata amsa ba tace ina Kausar ? Khameeni tace nidai naga tafita Ummi tace ok bata rufe bakiba Sega Kausar tashigo Ummi tace ina kikaje? Kausar tace gidan su Zulaihat naje Ummi tace ok Kausar tace Ummi wallahi inasan Yayan Soomeey place kiyiwa Abbah magana yaje yasami Daddy sa Allah Ummi idan ban aure saba rayuwa ta, tana cikin hatsari Ummi tadaka mata tsawa!! kedalla rufemin baki mezakiyi da mazinaci mashayi toh wallahi tun wuri ki cireshi a ranki.


Khameeni duk tana gurin ake wannan budirin abinda kemata yawo a kai shine mazinaci mashayi su suka tsaya mata tace toh mehakan kenufi? Hakadai ta, tashi tanufi d`aki jikinta ba 'kwari.


Kausar ta saka kuka ta wuce bedroom d`inta tana shiga tazube kan bed ta na kuka.


Ummi tayi tsaki ta wuce d`akinta itama.


Khameeni tana shiga bedroom d`inta bajimawa Khalifa yakira ta haka ta d`auka yace gimbiya ta dafatan kina lapiya itadai Khameeni mamaki yake bata sosai hakadai Khalifa yasanarwa da Khameeni abinda ke zuciyar sa Khameeni tace Amman Yaya Khalifa Kausar fa tana sanka yace nikuma bana Santa kenakeso hakadai Khalifa yaita zubawa Khameeni kalaman soyayya a haka harsukai sallama dan lokacin d`aura abincin dinner yayi haka Khameeni taje ta d`aura abincin tagama tajera a dining table takoma bedroom d`inta ta kunna data taga Khalifa yamata magana Soomeey ma tamata nandai taimusu reply sannan tashiga toilet tayi wanka ta d`auro alwala tafito ta yi sallah duk abinda tasabayi shi tayi sannan taci abinci tazo tayi shirin 'kwanciya bata dad`e da 'kwanciya ba Khalifa yakira ta.


Ummi tazubawa Abbah maganin a cikin abincin kuma yaci Mami ma hakan takasan ce.


Washe gari da karfe 10 nadare Mami tasami Daddy a d`akinsa tace masa Alhaji magana nakeso muyi yace inayinki tace dama akan Khalifa ne.


Alhaji meze hana ayimasa aure dannaga abin nasa gaba yakeyi Daddy yace toh wakike ganin za'a aura masa? Tace Alhaji ga 'yar gidan marigayi Abbas 'yar 'kanin abokin ka wacce yake riko A'i kaga yarinyar a kwai hankali zatatemaka gurin gyaruwar sa Daddy yace tabbas yarinyar a kwai hankali zan yiwa Alhaji Adam maganar insha Allah nan farin ciki ya cikata burinsu ze cika.


Ummi ce taje gurin Abbah yana bedroom d`inshi ta shiga tana shiga ta zauna tace Alhaji dama magana nazo muyi da kai yace ok inajin ki tace dama Alhaji akan Khameeni ne naga yarinyar tana shirin lalacewa ne shine nakawo shawara A'i mata aure tunkan ta jawo mana abin fad`a kawai Alhaji kaiwa abokin ka magana Ku hada yarannan aure kaga zumincin Ku ya'kara karfi Abbah yace gaskiya naji dad`in shawarar ki.


Ummi tai murmushi tana jin dad`i a zuciyar ta farin ciki kamar ya kashe ta Abbah yace insha Allah gobe zan jenasame barima nakirashi.


Abbah yad`auki waya yakira Daddy suka gaisa Abbah yace dama da a kwai maganar danakeso gobe zamuyi zanzo insameka a office Daddy yace toh a'i nima inaso mu had`u Allah dai ya kaimu goben haka sukai sallama..


 Washe gari wajen karfe 2 na rana Abbah yaje office d`in Daddy suka gaisa Abbah yace dama magana zamuyi meze hana muhad`a auren yaran mu dan kara karfin zumunci Daddy yace kamar kana raina nima maganar danakeso muyi kenan Abbah yace toh masha Allah Daddy yace kasan dai Khalifa yasauya hali hakan kana ganin ba matsala Abbah yace bakomai A'i Khameeni tana da hankali insha Allah zata bashi gudun mawa wajen shiryuwar sa Daddy yace gaskiya naji dad`i nagode sosai Abbah yace ba godiya a tsakanin mu.


Daddy yace kasan bawani lokaci za asa meyawa ba Abbah yace haka ne  Daddy yace wata 1 yayi kuma sannan karmu sanar da yaran musamman ma Khalifa dan za'a iya samin matsala itakuwa yarinyar nasan bata da matsala dan haka se biki yayi saura sati d`a'ya semu sanar wa da yaran Amman yanzu musanar wa da iyayen su mata sesu fara shiri haka sukaita tattaunawa akan lamarin sannan Abbah yaiwa Daddy sallama yatafi..


Daddy yana komawa gida yasanar wa da Mami yanda sukai da Abbah tayi murna kamar tazuba ruwa akasa sa ta sha.


Abbah ma yana komawa yasanar wa da Ummi yanda sukayi da Daddy itama dai tayi murna.


Bayan sati d`a'ya soyayya me karfi tashiga tsakanin Khameeni da Khalifa soyayya suke sosai Khalifa yanaso yazo gurin Khameeni Amman bayaso yaja mata matsala haka dai suke soyayyar su a waya Khalifa yana San Khameeni kamar me itama dai tana sanshi sosai.....
Inayinku sosai ❤đŸ˜đŸ’ƒđŸ„°

Fareeda

Ummu Haneefa

Anty Jameey

Anty Bintu

Soomeey

Beeebat

Heendart

Mrs xayyad

Maman twins

Maryam

Milhaat

Shamsiyya(Aisha)

Aysha Lawan Adam


Inayinku irin over dinnan😍Comments and share please🙏🙏🙏By Rufaida✍️đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

   *A* *SANADIN* *MARAICI* 

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


    Story and writing 

                By

     Rufaida(Rufeey)


 *MARUBUCIYAR* 


 *KAUNA* *CE* *KO* *KIYAYYA* 

 *BANFARGABA* 

 *Na* *fada* *tarkon* *sonshi* 


       *And* *now* 

       *A* *SANADIN* *MARAICI* *🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*


     *M. W. A* 


 ```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. đŸ€™đŸ»``` 

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

_________________________


 *Wannan* *labarin* *kirkirarren* *labarine* *banyi* *dan* *wata* *ko* *wani* *ba* *Wanda* *yaga* *labarin* *yazo* *dai* *dai* *danasa* *toh* *akasine* *ban* *yarda* *a* *chanzamin* *labari* *ba* *Wanda* *ya* *chanzamin* *ban* *yafeba* .


 *BISMILLAHIR* *RAHAMANIN* *RAHIM*


PAGE4️⃣5️⃣↪️5️⃣0️⃣


〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Khameeni da Khalifa soyayya suke sosai gashi sun sha'ku sosai kullun suna tare a waya Soomeey ma kullun seta kira Khameeni sunsha hirarsu sosai Soomeey ke 'kaunar Khameeni..


Soomeey ce da Khameeni suke waya Soomeey tacewa Khameeni gobe zanzo gurin kifa Khameeni tace Soomeey kina ganin ba matsala? Karsu Ummi sud`auka koda wani abu Soomeey tace bazasu d`au komai ba Khameeni tace toh shikkenan Allah yakaimu goben..


Kausar abin duniya ya isheta gashi wani irin San Khalifa ke damun ta, tarasa ya zatayi gashi duk yayi blocking d`inta hakan yasa ta yanke shawarar zuwa gidan su Khalifa..


Wajen karfe 5 nayamma Kausar tashirya ta fito parlour Ummi tace ina zaki? Kausar tace gidan su Soomeey tayi ficewar ta Ummi namata magana tayi banza da ita tayi tafiyar ta.


Ummi tace jimin shegiyar yarinya ina kiranta tayi banza dani tace zata dawo ai senaci ubanta tunda ita bata da hankali duk abin da ya faru Khameeni tana tsaye tana jinsu.


Ummi ta kalli Khameeni tace toh mayya kin tsaya kina raba idanu kina kallona wuce ki gyara min wardrobe d`ina Khameeni ta wuce bedroom d`in Ummi dan tayi abinda tasata haka tafara gyara wa..


Kausar nafita daga parlour tanufi motar ta, tashiga tafice daga gidan tana tafiya tana mita itadai wallahi kome Ummi zatayi seta auri Khalifa inbanda Ummi bata ganewa ai da ita zata jajirce dan na aure shi Amman dayake bata fuskanta gashi ta'ki tagane.


Hakadai Kausar taketa mita harta 'karasa gidan su Khalifa tayi horn megadi yabud`e mata., 


tashiga tayi parking ta fito daga motar tanufi part d`in Khalifa tana shiga parlour taga ba kowa hakan yasa ta haura sama ta tsaya tana tunanin wane bedroom zata shiga. 


 Ta bud`e d`a'ya taga ba kowa hakan yasa ta bud`e nakusa dashi tana shiga Sega Khalifa yafito daga wanka yana d`aure da towel seda yazo tsakiyar bedroom d`insa yaga kamar mutun yana d`agowa suka had`a ido hakika Khalifa ya tsorata.


 Amman daya gane Kausar ce seya basar yace kewacce irin jahilace zaki shigo min d`aki? Wama yabaki damar shigo min part? Duk a tsawace!! yake mata magana Kausar jiki yad`au ki rawa.


Khalifa yace banza wawuya kawai wallahi kokibar min part kona karyaki nakarya banza inbanda rashin hankali da rashin kamun kai meye naki nabiyoni har cikin part dina..


Toh bari kiji Kausar kike kowa? Wallahi bana sanki bana kaunar ganin ki kuma karki kara shigo min part d`ina kinji nagaya miki.


A tsawace!! Yace kifitar min daga d`aki wawuya kawai Kausar data daskare agurin kallan shi kawai take ita duk abinda yaimata bada metaba kallan shi kawai take tana mamakin kyan da Allah yaimasa..


Tanajin sanshi nakara shigarta da sha'awar sa tashiga wani mawuyacin hali.


Khalifa ganin Kausar tamaidashi mahaukaci gashi ta kuresa da ido hakan yasa ya d`auko jallabiya zesa kawai yaji Kausar ta rungume shi tabaya  tana cewa haba masoyina wallahi ina sanka.


Na mallaka maka kaina kayi yanda kakeso dani tana maganar tana wani shassha fashi ta ko ina tana kaimasa kiss tako ina..


Khalifa yajuyo a fusace ya d`auke Kausar dawani mahaukacin mari Wanda yakusa shid`ar da Kausar Khalifa ya hankad`ata tafad`i a kasa kanta yabigi kasa.


 Khalifa yace mezan yi da jikinki  dubeki wawuya yar kauye kazama dake tashi kibarmin daki wallahi ko jikinki yagaya miki.


Kausar ta, tashi dakar tana cewa haba my 1 nifa mesan kace dan Allah kasoni ko kadanne tana kara matsowa kusa dashi Khalifa dayaga haka ya zaro belt yashiga jibgar Kausar.


Kausar iwu take Amman bame jinta Khalifa kuwa ya zage se labtar ta yake yafarfasa mata jiki Kausar dataga ba haza ba haziyi yasa tafice a guje tai motar ta.


Tana shiga ta, tada motar a guje tafice daga gidan tanata rusa kuka.


Khalifa kuwa dariya yake harda rike ciki yana tuna dukan dayaiwa Kausar yana cikin dariya Soomeey tashigo d`akin da sallama da 'kar Khalifa ya amsa tashigo tana cewa yaya Khalifa meya faru kake wannan dariya haka.? 


Khalifa ya tsaya  korawa Soomeey bayani Soomeey ma , me zatayi inba dariya ba seda sukai me isharsu sannan Soomeey taimai sallama ta fice shikuma ya shirya dama gurin abokansa zashi toh se Kausar ta batamai lokaci.


Yana gama shirya wa ya fito yashiga motar sa yanufi gidan Hilal abokinsa..


Kausar kuwa tana zuwa gida tayi parking tafito da'kar dankuwa tadaku ba karya haka tashiga cikin parlour Allah yasota ba kowa hakan yasa tashige bedroom d`inta tana shiga tacire kaya tashiga toilet tayi wanka tana fitowa ta shirya zazzabi ne yarufe ta hakan yasa ta 'kwanta bacci me nauyi ya d`auke ta.


Khalifa yana zuwa yatarar da Hilal da Bashir suna zaune nan suka gaisa chen Khalifa yafashe da, dariya sabida ya tuno da abinda yaiwa Kausar sosai yake dariya su Hilal sukace Khalifa lapiya irin wannan dariya tameye? Khalifa yashiga basu labari abinda ya faru.


Suma dariya suke sosai Hilal yace Allah sarki Amman taban tausayi wallahi Khalifa yace ok sekaje ka sameta ai.


Hilal yace toh ai bani tace tana soba Bashir yace toh Khalifa meyasa bazaka sotaba Khalifa yace nifa ina da wacce nakeso Hilal da Bashir har suna had`a baki wajen cewa wacece?.


Khalifa yayi murmushi yace Khameeni sukace wow sunan ta me dad`i nan Khalifa yabasu labarin had`u warsu sannan yace kumafa ita Kausar d`in yar uwar Khameeni ce sukace chab tashin hankali.


 Hilal yace Toh Amman meyasa ita Khameeni kake Santa? Khalifa yace sabida yarinyar tana da hankali da nutsuwa kuma ni auren ta zanyi Hilal yace anya kuwa auren ta zakayi? Khalifa yace wallahi da gaske auren ta zanyi.


Tsakani da Allah nake Santa Bashir yace toh Allah yasa karka `bata yarinyar mutane Khalifa ya kaimasa duka yace kaikasan bana 'bata yaran mutane sedai sukawomin Kansu Bashir yace toh ai ita kace kana Santa dan haka akuladai karka `batamusu yarinya dan nasanka shidai Khalifa beku lasu ba.


Hilal yace yaushe zaka kaimu mugunta ne? Khalifa yace ai kuda kuganta semunyi aure sukace toh ai shikkenan tunda rowarta ake mana Khalifa yace eh an muku d`in.


Haka suka cigaba da hira sannan suka fice daga gidan suka nufi club inda suke sheke ayarsu.


Khameeni kuwa tana gama aikin da Ummi ta sata tasauko tashiga kitchen ta d`aura abincin dinner tana kammalawa tajera akan dining table.


Sannan tanufi d`akin ta, tashiga toilet tayi wanka tana fitowa tayi  sallah seda tayi issha ta, tashi tafito tad`anci abinci ta koma d`aki.


Kausar na d`aki a kwance zazzabi ya rufeta se rawar sanyi take Ummi dataji shuru yasa ta shigo d`akin dan taga ko Kausar d`in tadawo.


Tana shiga ta ganta 'kwance kan gado ta kudindine guri d`a'ya dasauri ta karasa ta yaye bargon taji zafi a jikin 'yar ta,  tace meke damun kine? Kausar tace Ummi zazzabi nake.


Ummi tace tashi muje asibiti Kausar tace aa Ummi kibani magani ma zanji sauki bayanda Ummi ta iya haka taje ta kawowa Kausar abinci da magani.


Nan Ummi ta lalla'ba Kausar taci abinci tabata magani tasha ta 'kwanta ganin tayi bacci yasa Ummi tafito ta nufi bedroom d`inta danta 'kwanta.


Khameeni ce 'kwance kan bed d`inta takasa bacci dan yau Khalifa bekirata da daddare ba harwajen 12pm hakan yasa ta d`auki wayar ta, ta kirashi har sau 2 ba d`agaba a na uku takusa tsinkewa ya d`aga.


Khameeni tayi sallama


Assalamu Alaikum.


Khalifa: ya amsa wa'alaikumus salam.


Khameeni: yakake ya gida ya Soomeey.?


Khalifa:duk lapiya lau.

Baby please kiyi hakuri ban kiraki ba.


Khameeni: ya Khalifa bakomai wallahi Amman naji muryar ka haka meke damunka.?


Khalifa: Baby bakomai kawai dai inajin bacci ne.


Khameeni: eyya sorry bansani ba natasheka a bacci.


Khalifa: bakomai baby.


Khameeni:ok sweety gud night sweet dreams.


Khalifa: ok bye my baby I love u.


Khameeni: love u more sweetheart.


Nan sukayi sallama Khameeni Tanajin San sweety n nata a zuciyar ta.


Shikuwa Khalifa lokacin da Khameeni ta kirashi basu dad`eda, dawowa daga club ba shiyasa Khameeni taji muryar sa haka Allah yaso shima abinda yasha yafara sakinshi Khalifa ya godewa Allah da Khameeni bata gane halin dayake ciki ba haka yayi sallolin da ake binsa sannan ya 'kwanta bacci ya d`auke shi..


     Washe gari 

Khameeni ta shiga kitchen ta d`aura breakfast tana gamawa tayi duk abinda ya dace ta wuce bedroom d`inta tayi wanka ta shirya sannan taci abinci.


Kausar kuwa jikinta yad`anyi sauki Amman ba sosai ba ita Kausar duk abinda Khalifa yaimata bataji haushi ba.


Kujifa Mara zuciya😏


Khalifa kuwa shida Soomeey suna zaune a farfajiyar gidan Khalifa yace da karfe nawa zakije gurin Khameeni? Soomeey tace kamar 4 haka yace ok wajan 6 sena dawo na d`aukeki Soomeey tace eh nan suka cigaba da hirarsu.


Kausar ce take yiwa Ummi kuka itadai Khalifa takeso Ummi tace wai Kausar meke damunki ne? Nace miki wannan da kike gani dan iska ne mashayi ne manemin mata sokike ki aure shi yasaka miki cuta koh? Sokike kullun yadunga jibgar ki kinsan mashaya idan suka shawo toh jibgar matansu sukeyi dan haka kicire ranki a auren sa kinji nafad`a miki.


Kausar Ummi wallahi nidai inasanshi a haka ko kasheni zeyi Ummi tace baki jiba koh? Toh kije kitayi kece a wahale tunda ke ba'a gaya miki magana kiji kuma wallahi baki isa ki auri makiyin muba sedai kimutu Ummi tafice a fusace tabar Kausar na rusa kuka.


Nikuwa nace Kausar kina da aiki dan kuwa kece a wahale ta bakin Ummi😂😂😂


Soomeey ce ke shiri tana gama shiryawa  tanufi part d`in Khalifa taga shima ya shirya haka suka fito suka shiga mota suka d`auki hanyar gidan su Khameeni , Khalifa a waje ya tsaya Soomeey tafito daga motar tace yaya seka dawo yace ok sister seda yaga tashiga ciki sannan ya tafi.


Tana shiga parlour taga Ummi ita 'kad`ai Soomeey ta gasheta, ta amsa dan kar Ummi ta zargi wani abun yasa Soomeey tace Ummi ina Kausar? Ummi tace tana bedroom d`inta batajin dad`i ne Soomeey tace ayya bari nashiga na dubata haka tashiga bedroom d`in Kausar ta ganta 'kwance Soomeey dariya takusa 'kwace mata Amman ta dake tayiwa Kausar sannu da jiki sannan tafito daga d`akin.


Ai kuwa tana fitowa taga Ummi bata parlour hakan yasa tashiga bedroom din Khameeni, ta ganta tana game a waya Khameeni naganin Soomeey tasakar mata murmushi.


Nan suka gaisa suna ta hira Soomeey tace ai gurin Kausar nafara zuwa ashe bata da lapiya? Khameeni tace nikam banma saniba Soomeey tace toh ai kuwa bata da lapiya nan Soomeey tabawa Khameeni labarin abinda ya faru jiya.


Khameeni tayi dariya Amman ta, tausayawa yar uwar ta-ta hakadai Soomeey da Khameeni sukaita hira har wajen 6 suna cikin hirarsu wayar Soomeey tashiga ringing tana dubawa taga Khalifa ne tad`aga tace yaya gamunan.


Takalli Khameeni tace tashi muje Ku gaisa dama doguwar Riga ce a jikinta ta d`auki mayafin rigar tayafa suna fitowa Allah yasosu ba kowa haka suka fice.


Tunda suka fito Khalifa ya ke kallan Khameeni har suka karasa gurin shi...
Comments and share please🙏🙏🙏🙏By Rufaida✍️


đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

   *A* *SANADIN* *MARAICI* 

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


    Story and writing 

                By

     Rufaida(Rufeey)


 *MARUBUCIYAR* 


 *KAUNA* *CE* *KO* *KIYAYYA* 

 *BANFARGABA* 

 *Na* *fada* *tarkon* *sonshi* 


       *And* *now* 

       *A* *SANADIN* *MARAICI* *🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*


     *M. W. A* 


 ```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. đŸ€™đŸ»``` 

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

_________________________


 *Wannan* *labarin* *kirkirarren* *labarine* *banyi* *dan* *wata* *ko* *wani* *ba* *Wanda* *yaga* *labarin* *yazo* *dai* *dai* *danasa* *toh* *akasine* *ban* *yarda* *a* *chanzamin* *labari* *ba* *Wanda* *ya* *chanzamin* *ban* *yafeba* .


 *BISMILLAHIR* *RAHAMANIN* *RAHIM*


PAGE 50↪️55


〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Tunda suka fito Khalifa yake kallan Khameeni har suka karasa gurin shi suna zuwa sukayi mai sallama ya amsa Khameeni ta gaida shi ya amsa yana sakar mata murmushi..


Sannan yace Baby yakike? Ta amsa da lapiya suka d`anyi hira itadai Khameeni a tsorace take dayaga haka yace taje gida sunyi waya dan kar Ummi tanemeta Khameeni dama jira take taimusu sallama tashiga gida shi  Khalifa dariya ma tabashi yace kai Amman anyi matsoraciya Soomeey ma dariya tayi suka shiga mota suka nufi gida..


Bayan sati 3

Toh su Abbah da Daddy shirye shiryen biki kawai suke dan yanzu saura sati d`aya kuma sunyanke hukuncin dama ana saura sati d`a'ya zasu sanarwa dayaran..


A 'bangaran Khalifa da Khameeni kuwa shakuwa da soyayya me karfi takuma shiga tsakanin su Khalifa ya yanke hukuncin zeje yasami Abbah da zancen Khameeni dan Abbah yaje yanema, masa auren Khameeni.


Washe gari 

Tunda Khalifa ya tashi yakejin fad`uwar gaba hakadai yake abu jiki duk ba 'kwari..


Khameeni ma dai hakan take agurin ta jinta take wani iri batajin dad'i ko, kad`an da'kar tayi aikin gidan ma..


Bayan sallar issha Daddy ya dawo duk suna parlour Mami da Soomeey da Daddy, Daddy yace Soomeey jeki, kiramin Yayan ki Soomeey ta, tashi tanufi part d`in Khalifa tayi sa'a kuwa yananan tashiga tasanar masa da sa'kon Daddy tare suka fito..


Suna shiga yaji gaban sa yafad`i dam dam hakadai yadaure yashiga ya gaishe su suka amsa Mami tanata dariyar mugunta a ranta.


Daddy ya kalleshi yace dama nakirakane na fad`a maka cewa nanda sati d`a'ya za'a d`aura auren ka da yarinyar abokina....Comments and share please🙏🙏🙏🙏


Yawan comments yawan typingBy Rufaida✍️


đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

   *A* *SANADIN* *MARAICI* 

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


    Story and writing 

                By

     Rufaida(Rufeey)


 *MARUBUCIYAR* 


 *KAUNA* *CE* *KO* *KIYAYYA* 

 *BANFARGABA* 

 *Na* *fada* *tarkon* *sonshi* 


       *And* *now* 

       *A* *SANADIN* *MARAICI* *🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*


     *M. W. A* 


 ```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. đŸ€™đŸ»``` 

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

_________________________


 *Wannan* *labarin* *kirkirarren* *labarine* *banyi* *dan* *wata* *ko* *wani* *ba* *Wanda* *yaga* *labarin* *yazo* *dai* *dai* *danasa* *toh* *akasine* *ban* *yarda* *a* *chanzamin* *labari* *ba* *Wanda* *ya* *chanzamin* *ban* *yafeba* .


 *BISMILLAHIR* *RAHAMANIN* *RAHIM*


PAGE 55↪️60


〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Ai Khalifa najin abinda Daddy yafada yamike a zabure yana cewa Daddy meyasa zakamin haka? Daddy ni wallahi inada wacce nakeso..


Dan Allah Daddy kabar zancen nan Allah Daddy inada wacce nakeso kuma itama tana sona please Daddy karkamin haka.


Daddy yadakawa Khalifa tsawa! Yace karufemin baki kaika haifemu komumuka haifeka? Toh bari kaji baka isa kasani abinda nayi niyya ba kaji nafada maka kuma dole ayi auren kada yarinyar nan sati me  zuwa kaji na fada maka shashasha kawai.


Mami tace aa Alhaji kabishi a hankali dan Allah Daddy yace nidai nagama magana Mami tace yarona tashi kaje abinka Khalifa yafita jiki a sanyaye Soomeey ma jikinta yayi sanyi ta, tausayawa Yayan nata dan tasan irin kaunar dayake wa Khameeni haka itama ta shige bedroom d`inta tana tunanin yanda Khameeni zataji idan taji Khalifa zeyi aure sosai Soomeey tashiga damuwa..


Khalifa kuwa yana zuwa part din shi yawuce bedroom yana shiga yazauna yarasa meyake masa dadi ya za'ayi Daddy yaimasa haka Amman shikkenan koma wace yarinyar da za'a aura mai wallahi seyayi maganin ta.


Khalifa yace Allah sarki Khameeni na kekadai nakeso bazan taba hada sanki da nawa taba Amman kiyi hakuri Daddy ze aura min wata kafin ke Amman bazan taba San taba ke daya nakeso haka yaita sanbatu abin tausayi..Bangaran Khameeni kuwa Khameeni ce a d`akinta tana kwance kan bed gashi duk taji jikinta yayi sanyi tarasa meke Damunta.


Ummi ce da Abbah a zaune a parlour Abbah yace Ummi taje takira Khameeni sosai Ummi take farin ciki haka tashiga bedroom d`in Khameeni..


Tana shiga taganta kwance Ummi tace toh shegiya mayya kije Alhaji nakira tayi ficewar ta Khameeni jiki a sanyaye ta fito parlour..


Taje ta tsugunna tace Abbah gani Abbah yace yawwa nakirakine nafada miki cewa sati mezuwa za'a daura auren ki da yaron abokina..


Tunda yafara maganar Khameeni tashiga tashin hankali Wanda bata, taba shigar shiba sosai tashiga tashin hankali.


Hawaye ne kawai yakebin kuncinta shikkenan sunrabata dame Santa Yaya Khalifa ta masoyinta me kaunar ta maganar da Abbah yayi itace tadawo da'ita daga duniyar tunanin data shiga Abbah yace Khameeni kindaiji menace ko? Tace eh Abbah yace yawwa tashi kije.


Haka Khameeni tashige bedroom d`inta tana zubar da hawaye tana shiga tadauki wayar ta, ta danna number Khalifa....Pls kuyi hkr dawannan banajin dadi ne Comments and share please🙏🙏🙏🙏 By Rufaida✍️


đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

   *A* *SANADIN* *MARAICI* 

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


    Story and writing 

                By

     Rufaida(Rufeey)


 *MARUBUCIYAR* 


 *KAUNA* *CE* *KO* *KIYAYYA* 

 *BANFARGABA* 

 *Na* *fada* *tarkon* *sonshi* 


       *And* *now* 

       *A* *SANADIN* *MARAICI* *🌎MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*


     *M. W. A* 


 ```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. đŸ€™đŸ»``` 

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

_________________________


 *Wannan* *labarin* *kirkirarren* *labarine* *banyi* *dan* *wata* *ko* *wani* *ba* *Wanda* *yaga* *labarin* *yazo* *dai* *dai* *danasa* *toh* *akasine* *ban* *yarda* *a* *chanzamin* *labari* *ba* *Wanda* *ya* *chanzamin* *ban* *yafeba* .


 *BISMILLAHIR* *RAHAMANIN* *RAHIM*


PAGE 65↪️70


〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

"Khameeni tace toh shikkenan Soomeey nagode sosai kema kitayani addu'a Amman wallahi inasan Yaya Khalifa Amman bayanda zanyi Allah ne yakaddara haka zata faru "Soomeey tace eh kedai kita addu'a hakadai sukadanyi hira sannan sukayi sallama Soomeey ta, tashi tafara shirin zuwa kasuwa..


Tana gama shiryawa tafito tashiga bedroom din Mami itama tagama shiryawa haka suka fito suka shiga mota driver yajasu se kasuwa..


Bangaran Kausar kuwa duk abinda akeyi bata saniba kuma Ummi bata fadamata ba sabida dama bataso tasani  tasan muddun Kausar tasani a kwai tashin hankali shiya sama Ummi tacewa Abbah yacewa Kausar auren Khameeni za ayi dawani yaro Amman basu fadamata ko wane ba hakan yasa taketa yiwa Khameeni dariyar mugunta..


Yanzu hakama Kausar tana zaune a parlour ita dawata kawarta Zulaihat, suna hira Kausar tana bata labarin abinda Khalifa yaimata.


"Zulaihat tace Amman gaskiya baki da zuciya wallahi duk wulakancin dayake miki baki gani gaskiya kinban kunya ga samarinan a gari kizabi Wanda kikeso Amman kin tsaya yana miki wulakanci gaskiya kinban kunya".


"Kausar tace toh yazanyi wallahi bakiji sanda nakemasa ba kemadin dan baki ganshi bane Amman dakin ganshi bazaki cemin haka ba gayan yahadu ba karya wallahi Zulaihat tace kedai kika sani idan zakiyi hakuri toh kiyi idan bazaki hakuri ba toh kekika sani wulakanci yanzu kika fara ganinshi..


Kausar tayi dariya tace bazaki ganeba Zulaihat tace kina jidai Ummi bata sanshi Amman kin nace masa toh nidai Allah shikara dama ya karyaki wallahi tunda ke mayya ce "Kausar tace kinga ni banasan rashin mutunci Zulaihat tace kekika sani dai suna cikin haka Khameeni tafito dan tashiga kitchen tadaura abincin rana tana fitowa Kausar tace toh mayya zonan Khameeni takarasa gunsu tace gani Kausar tace waike za ayimiki aure kina wani daga kai koh? Toh bari kiji shiwanda za'a daura  miki auren dashi basanki yakeba wahala kawai zakisha idan ma murna kike toh kidena dan kuwa ubanki zakici shegiya aljana kawai mayya wuce kibani guri kona karyaki Khameeni bata kula taba tashige kitchen dan kuwa Khameeni tasaba da irin haka..Kausar tace shegiya Zulaihat tace waike Kausar me Khameeni tayi miki haka? Kausar tace ke ni wallahi natsani yarinyar nan senaji yan 'kwanakinnan nakara tsanarta akan da fa Zulaihat tace ai kuwa yarinyar baruwanta bansan meyasa kika tsane taba? Kausar tace hmmm bazaki gane bane haka suka cigaba da hira..


Khameeni kuwa ta gama abincin tafito tashige bedroom d`inta tayi wanka tadan 'kwanta ko bacci zedauketa ai kuwa tayi sa'a baccin yadauketa.


Khalifa kuwa yarame ko fita bayayi Amman idan yatuna maganar Khameeni seya hakura abin tausayi yauma yana 'kwance a bedroom d`insa yanata tunani  daya tuno nasihar Khameeni seyayi murmushi hakan yasa yamike yashiga bathroom yayi wanka yafito yashirya ya nufi gidan abokinsa Bashir...Soomeey kuwa sunyi siyayya sosai kome Soomeey tagani idan tasan zewa Khameeni kyau seta daukar mata hakan yasa Mami kamar tayi kuka gashi badamar tayi magana dan tasan halin Soomeey setagayawa Daddy hakan yasa tazama yar kallo kawai Soomeey kuwa kaya  kawai take jibgowa harta kananun kaya Soomeey ta jibgosu seda taga yamma takusa sannan tacewa Mami sutafi gida gobe a karasa siyan kayan da a 'kwatunan Mami kuwa takasa magana haka Soomeey tasa driver yasa kayan a mota suka nufi gida......Hhhhhh Soomeey aikinki na kyau😂😂😂
Heendart yar uwa Rabin jiki❤

Soomeey sweety❤

Beeebat sweety❤

Shuraihat dear❤


Inayinku over wlh lv u wujiga wujiga 💃💃💃💃Comments and share please🙏🙏🙏🙏By Rufaida✍️


đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

   *A* *SANADIN* *MARAICI* 

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


    Story and writing

                By

      Rufaida(Rufeey )


 *MARUBUCIYAR* 


 *KAUNA* *CE* *KO* *KIYAYYA* 

 *BANFARGABA* 

 *Na* *fada* *tarkon* *sonshi* 


      *And* *now* 

      *A* *SANADIN* *MARAICI* *🌍MANAZARTA*

*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*

      *M. W. A* 


```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.đŸ€™đŸ»```

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

____________________________________


 *Wannan* *labarin* *kirkirarren* *labarine* *banyi* *dan* *wata* *ko* *wani* *ba* *Wanda* *yaga* *labarin* *yazo* *dai* *dai* *danasa* *toh* *akasine* *ban* *yarda* *a* *chanzamin* *labari* *ba* *Wanda* *ya* *chanzamin* *ban* *yafeba*.


 *BISMILLAHIR* *RAHAMANIN* *RAHIM*


PAGE 75↪️80


〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

Su Soomeey suna zuwa kasuwa Soomeey tadinga jidar kaya kamar ba gobe da Mami ta gaji tace "wai Soomeey kina da hankali kuwa."? "jifa kayan dakike dibar mata toh wallahi zakici uban ki yanzu shegiya banza makiyar tamu kikewa haka koh."? Soomeey tace "kai Mami ai naga Daddy ne yace nasuyomata komai da komai dan haka ni abinda yasani zanyi kuma ma ai ita Khameeni ba ruwan ta batasan kuna yibama wallahi"...


Mami tace "la nikike cewa haka."? "Toh wallahi zakici uban ki bani kudin ma".. Soomeey tace "gaskiya Mami kiyi hakuri nidai bazan iya bakiga".


Dabarace ta fadowa Soomeey tayi murmushi tace "Mami bari nakira Daddy din toh tunda kince nabaki kudin" Ai da sauri Mami tace "aa shikkenan cigaba da siyayyar ki" Soomeey kuwa dariya ta guntse ta cigaba da abinda take haka Soomeey tayi siyayya nagani na fada a kwati 12 Soomeey tayi guda 6 baby pink colour sedayar 6 din ita kuma black colour gaskiya a katinan sun hadu sosai haka su Soomeey suka koma gida bakin ciki kamar ya kashe Mami..


Lokacin da Daddy ya dawo Soomeey tanuna masa kayan lefan gaskiya lefan ya hadu ba karya kowacce a kwati cike da kaya Daddy yaji dadi yanda suka hadawa surukar tasa kaya itadai Mami bata data cewa yake kawai ta ke..


Suna cikin haka Khalifa ya shigo parlour yagaisu suka amsa Soomeey ta gaisheshi ya amsa a sanyaye duk yarame abin tausayi Soomeey tana sane tace Yaya Khalifa gafa lefan matar taka kazo kagani Khalifa yasakar mata harara Daddy yace kaleshi yar Daddy kunya yakeji ai sukasa dariya banda Mami da Khalifa shidai Khalifa daya gaji yaimusu seda safe yafice..


Yana fita Soomeey ta dinga dariya Daddy yace lapiyar ki kuwa? Tace Daddy bakomai fa yace ok sannan Daddy ya kalli Mami yace "gobe za akai lefan gidan su yarinyar nayanke hukuncin maza abokaina zasukai lefan sabida kinsan Ku mata kuna da matsala shiyasa nace maza zasukai gobe".. "barima nakira Aminin nawa nafadamai ya shirya kabar lefan yar tasa gobe" haka kuwa a kayi Daddy yakira Abbah yafada masa Abbah yace toh shikkenan Allah yakaimu goben haka sukai sallama..


Suna gama wayar Abbah ya fadawa Ummi, Ummi tace toh shikkenan ai balefi dan maza sunkawo daman yanzu ai susuke kaiwa Abbah yace hakane kam.


Ko wannensu ya kwanta da farin ciki ita Ummi farin cikinta shine wulakantacun lefan da za'a kawowa Khameeni takeyi shikuma Abbah farin cikin ze auran da yar dan uwansa yakeyi..


Daddy madai farin cikin ze auran da yaransa yakeyi ita kuma Mami bakin cikin lefan da za'a kaiwa Khameeni takeyi..


Khalifa kuma bakin cikin rasa masoyarsa yakeyi.


Khameeni ma bakin cikin rasa masoyinna takeyi.


Soomeey kuwa farin cikin auren Khameeni da Khalifa takeyi..


Wannan kenan


Washe gari da sassafe Abbah yakira wata yar uwar mahaifiyar Khameeni a waya, wato Aunty Beeebat.


Aunty Beeebat tana da aure suna zaune a garin Abuja ne  yaranta 4  duk maza kuma duk dagirman su na farko shekarun sa 20 na biyu 18 na uku 16 na karshen kuma 12 Aunty Beeebat tana da mutunci sosai Amman idan katabata kam bata da hakuri shiyasa bata zuwa gidan sabida Ummi dan kuwa basa shiri ko kadan.. Wannan kenan


Tana dagawa tace "ooo mafarki nake dai ko."? Abbah ya kwashe da, dariya yace "ba mafarki bane" Aunty Beeebat tace "ok toh" nandai suka gaisa yake sheda mata ai lefan Khameeni za'a kawo..


Aunty Beeebat tasaki salati tace "yanzu sabida Allah seyanzu zaka sanar dani."? Abbah yace " dan Allah kiyi hakuri wallahi abinne yazo da gaggawa" tace toh shikkenan insha Allah yanzu zamu shirya mubiyo jirgi idan yaso bayan biki ma dawo gida Abbah yaimata godiya sannan sukai sallama..


Aunty Beeebat suna gama waya da Daddy taje tasanarwa da me gidan ta ai kuwa ya amince yace yanzu su shirya yaran duk sukace baza suba sudai suna gurin mahaifin su.


Itadai Aunty Beeebat tace "toh shikkenan kuyi zaman Ku dama nima badaku zani ba ai" haka taje tayi shirin ta mijinta yakaita airport dayake suna da hanya ba adau lokaci ba akayi mata komai jirginsu ya daga se kano..Wajen karfe 10 nasafe abokansa Daddy suka kawo lefan Khameeni Abbah yananan dama dayake sunsan juna suka gaisa sosai sannan suka tafi Daddy yayi murna daganin irin lefan da Khameeni tasamu haka yasa ma'aikatan gidan suka shigar dasu parlour Ummi.


Abbah ya kwalawa Ummi kira tafito tana fitowa taga a kwatina har goma sha 12 tace "Alhaji lapiya a kwatin waye."? Yace "ai shina kira kigani na Khameeni yanzu suka tafima"...


Ummi kamar tai hauka shikuwa Abbah besan halin data shiga ba yace "se'a sanar da makota da abokan arziki niyanzu zan fita". Ummi tace "toh" kawai dan bakin ciki kamar ya kasheta shidai Abbah yayi ficewar sa kawai.. Yabar Ummi da sakin baki lolđŸ€ŁđŸ€Ł


Ai yana fita ta hau kiran Kausar a zabure Kausar tafito  tana cewa "Ummi lapiya."? Ummi tace "dan ubanki kalli" Kausar Takalli gurin tace "Ummi nawaye."? Ummi tace "na shegiyar nanne fa" Kausar tace "kan ubancen" nan tahau bude a kwatinan tanayi tana zagi Ummi kuwa kusan suma tayi tana zakin aminiyar tata chan tace "Kausar tashi ki dadkomin wayata..


Kausar taje ta dauko wayar ta kawowa Ummi takarba takira kawar ta-ta ko gaisawa basu yiba tahau zaginta daga chan bangaran Mami tace "haba kawata sekace kin manta ni nandai tafada mata abinda yafaru Ummi tace "Amman dai Soomeey nan anyi yar banza". Mami tace "aa fa kidena zagarmin ya" Mami  "tace yanzu dai Ku sami kayan keda Kausar Ku yayyagasu wasu kiduba". Ummi tace "ok toh shikkenan yanzu kuwa"...


Haka sukai sallama Ummi tace "Kausar jeki dauko almakashi muyanka kayannan sannan kikiramin mayyar muyanka a gaban ta"...


Haka Kausar takira Khameeni sannan takawo almakashi se zajin Khameeni sukeyi itadai tayi shuru...Aunty Beeebat ce tasauko daga jirgi sannan takira Abbah tace "masa ai gata jirginsu ya sauka" yace "bari yanzu yaturo driver yakaita gidan"..


Ai kuwa ba jimawa driver yazo tashiga suka nufi gidan suna zuwa megadi yabude musu suka shiga yayi parking ta fito tanufi parlour gidan..Ummi da Kausar nata zajin Khameeni  sunata fito dakayan suna gama pito dasu sun daga kenan zasu yanka sukaji muryar wata tana cewa "idan kuka sake kuka yanka kayannan wallahi tallahi nida kune". Duk acikin tsawa tayi maganar! Ai duk kanninsu tare suka juya wazasu gani inba.....Ngd sosai da addu'ar Ku naji sauki insha Allah zandingai muku typing kanlokaci ngd Allah yabar kaunaComments and share please🙏By Rufaida✍️


đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

   *A* *SANADIN* *MARAICI* 

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


    Story and writing

                By

      Rufaida(Rufeey )


 *MARUBUCIYAR* 


 *KAUNA* *CE* *KO* *KIYAYYA* 

 *BANFARGABA* 

 *Na* *fada* *tarkon* *sonshi* 


      *And* *now* 

      *A* *SANADIN* *MARAICI* *🌍MANAZARTA*

*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*

      *M. W. A* 


```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.đŸ€™đŸ»```

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

____________________________________


 *Wannan* *labarin* *kirkirarren* *labarine* *banyi* *dan* *wata* *ko* *wani* *ba* *Wanda* *yaga* *labarin* *yazo* *dai* *dai* *danasa* *toh* *akasine* *ban* *yarda* *a* *chanzamin* *labari* *ba* *Wanda* *ya* *chanzamin* *ban* *yafeba*.


 *BISMILLAHIR* *RAHAMANIN* *RAHIM*


PAGE 85↪️90


Haka abokan sa suka jashi zuwa gida sukadanyi yar walima shidai Khalifa kallansu kawai yake..


Gashi yana cikin tashin hankali idan yatuna wai yau Khameeni sa akayiwa aure dawani bada shiba shima gashi anzo an aura masa wata chan daban wacce bema santaba besan yatakeba hakadai yaita tunani  har aka gama walima aka tashi..


Khameeni kuwa kuka kawai takeyi Aunty Beeebat kuwa  se aikin rarrashinta take da'kyar dai tayi shuru tanata yimata nasiha me ratsajiki..


     "Tace Khameeni duk abinda kikaga yafaru a rayuwar ki toh mukaddarine daga Allah subhanahu wata'ala dama chan yana daga cikin kaddararki kuma duk wani dan adam akwai tashi jarabawar daga Allah dan haka inaso ki karbi wannan jarabawar data zomiki da hannu bibbiyu kuma insha Allah bazakiyi nadama ba zakiyi alfahari da ita sannan inaso kiyiwa  mijinki biyayya duk abinda yasaki kiyi masa banda yiwa miji rashin kunya dukda nasan baki da wannan halin nasan dai kinada hakuri toh kikara akan Nada sannan naji ance agidan su mijinki zaku zauna toh kiyiwa iyayen sa biyayya ki zauna lapiya dasu ki kyauta ta musu kidaukesu kamar iyayen ki dasuka haifeki nasan bazasuyi nadamar kasan cewarki suruka a garesuba"..


Hakadai Aunty Beeebat tadinga mata nasiha me shiga jiki Khameeni se kuka take tana gamai mata nasiha tashiga toilet tahada mata ruwan wanka me dauke da turaruka masu kamshin gaske tace "Khameeni tashi kishiga toilet kiyi wanka sannan ki dauro alwala kinga yanzu karfe 4:00 tayi." Haka Khameeni tashiga tayi wanka tadauro alwala tana fitowa tayi sallah tana idarwa tayi azkar din data saba..


Tana gamawa Aunty Beeebat tazo tashirya ta cikin atamfa super me tsadar gaske kalar jah da baki da fari atamfar tayi mata kyau matuka sannan ta nad`amata tsadaddiyar lifaya kalar atamfar jikin ta gaskiya Khameeni ta hadu cikin shigar nan kafi su karasa shiri har abokan ango sunzo daukar amarya..


Haka Aunty Beeebat  tadadai mata nasiha sannan aka kaita gurin Abbah da Ummi sosai Abbah yaimata nasiha meshiga jiki Ummi kuwa shuru tayi bakin ciki duk yacika zuciyar ta naganin kayan dake jikin Khameeni Kausar ma dai bakin ciki take...


Kuma tace setaje taga gidan da Khameeni zata zauna hakadai Aunty Beeebat tafito da Khameeni da yake har anyi sallar magriba yasa duk sukayi sallah sannan aka fito da amarya dan kaita gidan mijinta..


Motar datafi kowacce kyau nan Aunty Beeebat da Khameeni suka shiga seda kowa yashiga sannan a kadauki hanya basu jimaba suka isa..


Suna isa aka bude get suka shigo tunda suka shigo Kausar tashiga tashin hankali badai mafarki takeba sosai tashiga tashin hankali..


Khameeni kuwa dayake fuskarta rufe take bata gane gidan ba haka suka shiga cikin part din su Mami suna zuwa sukaga yan uwan Mami basuyi musu tarba me kyauba Mami kuwa dama bata fitowa kuma tasan sunzo seyan aikin ne suka nuna musu part din Khalifa sannan suka nufi part din masha Allah angyara part din sosai yayi kyau Aunty Beeebat tace "Khameeni kiyi addu'a kishiga da kafar dama." Haka kuwa Khameeni tayi sannan suka shiga..


Ai Kausar tana ganin part din da aka shiga takara rikicewa wato zarginta yazama gaskiya ai ba shiri Kausar tafice daga gidan a fusace..


Suna shiga suka shiga bedroom da ita suka a jiyeta kan bed sannan suka fice dan duba gidan suna gamawa Aunty Beeebat tashi bedroom din taimata sallama dan tafiya zasuyi ai kuwa Khameeni tasa kuka da'kar ta lallabata sannan tayi shuru sannan taimata sallama suka tafi sukabar amarya ita kadai..


Basu dade da tafiyaba Soomeey tashigo part din tana dariya dan duk abinda yafaru kan idantane har ficewar  Kausar daga gidan sosai Soomeey ke dariya haka tashiga bedroom din da Khameeni take tayi sallama ai kamar a mafarki Khameeni taji wannan muryar...Pls kuyi hkr da wannan abubuwa sunmin yawa dafatan zakumin uzuriComments and share please🙏By Rufaida✍️


đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

   *A* *SANADIN* *MARAICI* 

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


    Story and writing

                By

      Rufaida(Rufeey )


 *MARUBUCIYAR* 


 *KAUNA* *CE* *KO* *KIYAYYA* 

 *BANFARGABA* 

 *Na* *fada* *tarkon* *sonshi* 


      *And* *now* 

      *A* *SANADIN* *MARAICI* *🌍MANAZARTA*

*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*

      *M. W. A* 


```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.đŸ€™đŸ»```

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

____________________________________


 *Wannan* *labarin* *kirkirarren* *labarine* *banyi* *dan* *wata* *ko* *wani* *ba* *Wanda* *yaga* *labarin* *yazo* *dai* *dai* *danasa* *toh* *akasine* *ban* *yarda* *a* *chanzamin* *labari* *ba* *Wanda* *ya* *chanzamin* *ban* *yafeba*.


 *BISMILLAHIR* *RAHAMANIN* *RAHIM*


PAGE 95↪️100


Kausar "tace wallahi  kota halin kaka seya soni se yasan wacce ya wulakanta  kozanyi yawo tsirara sena rabasu senasa yatsani duk wani abu daya danganci Khameeni sena tarwatsa aurensu".


Ummi tace "Kausar wai meyasa ke banzace nace kirabu da wannan yaran kinki toh ai kuwa bazaki aureshiba"..


Kausar tafashe da kuka tace "haba Ummi ko wace uwa tana nemarwa yarta farin ciki a rayuwar ta kome takeso se uwa tabata Amman banda ni Ummi anya kina sona kuwa?aa baki sona dakina sona duk abinda nakeso zaki samarmin shi dan farin cikina Amman kash gashi yanzu kinga za bani farin ciki a rayuwa please Ummi na kibarni nacika burina"..


Ummi dajikinta yayi sanyi ta jawo Kausar jikinta tace "yi shuru y`ar lele duk naji abinda kika fada kuma zan cika miki burinki kozanyi yawo bakaya sena Samar miki farin ciki kuma indai Khalifa kin sameshi sedai duk abinda zefaru yafaru tsakani na da Mami dan kuwa farin cikin ki shine nawa bana wata banza ba dama wannan ranar nake jira tazo dan haka yanzu *wasan zefara* Kausar tadago tace "Ummi kamarya."? Ummi tace "eh mana ai akan farin cikin ki zan iya yinkomai dankisamu Khalifa Amman seminbi abun a hankali kuma karki bari Mami tagane dan idan tagane komai ze wargatse"..


Kausar tace "toh Ummi na sannan tafice daga dakin tana fita Ummi tace "Mami kindaukeni kawar arziki nidama ai hauka nake seda yar lele tafargar dani yaro ga arziki muci arzigi mubarshi chab aida nayi wauta wallahi." Hakadai Ummi taita surutanta ita kadai..


Kausar kuwa tana shiga daki ba sallah ta kwanta bacci cike da farin cikin zata samu Khalifa..        Washe gari

Khameeni tana tashi tashiga wanka tana fitowa tashirya tana tunanin ina Khalifa yashiga koda yake dama tasan baze shigo ba sabida besan ita bace itama kuma bataso su hadu yanzu..


Tana gama shiri ta gyara d`akin ta sannan tafito parlour ta gyara ko ina tasaka turaran wuta ko ina yadau kamshi tashiga kitchen ta soya potato and egg da crab cakes sannan tayi farfesun kayan ciki tadafa Tea tazuba komai a inda yakamata sannan taje-tajera akan dining table sannan takoma kitchen ta gyara inda ta bata.

   ****  ****  ****  ****  ****

    Crab cakes

Ingredients

1cup crab (use imitation crab);chopped

1/4 cup mayonnaise

1ts. grated lime rind

1Tbsp. cilantro; chopped

2 green onions; chopped

1 Cup breadcrumbs

1 egg

Flour for dusting


Cooking:


Combine the crab meat, mayonnaise, rind, cilantro, green onions, breadcrumbs, and egg in a bowl.

Shape into balls and flatten slightly. Toss in flour. Fry until golden brown; drain on paper towels.


    ****  ****  ****  ****  ****

Khameeni tana gama jerawa a dining area ta koma bedroom din ta takira Aunty Beeebat suka gaisa Khameeni tace "aunty yaushe zaki tafine."? Aunty Beeebat tace "yau insha Allah zantafi." Khameeni tace "kai aunty gaskiya aa segobe." Aunty Beeebat tace "Khameeni kiyi hakuri kinga aina Dade Amman karki damu zamu dunga zuwa akai-akai dama daki kaga bama zuwa sabida wayannan ne shiyasa Amman yanzu ai nasan yanda nake musu danhaka karki damu kinji." Khameeni "toh Aunty na haka sukai sallama takashe wayarta tashiga jera kayanta a Waldrop..Khalifa kuwa sewajen 10 yatashi dayake yasan yau asabar ba office haka yashiga wanka yana fitowa yashirya cikin kananun kaya sezuba kamshi yake haka yafito parlour tunkan ya sakko yakejin wani kamshi yana dukan hancinshi ya lumshe ido haka yakaraso tsakiyar parlour idansa yasauka kan dining area inda gurin aka tsarashi yayi kyau yakarasa gurin yabude kulolin abincin khamshi ya daki hancinsa besan sanda ya hadiyi yawuba harya rufe zebar gurin seyaga baze iyaba hakan yasa yaja kujera yazuba yafara ci yana lumshe ido Khalifa yaci sosai sannan yatashi ya koma bedroom yadauki key din motar sa yafito yaje part din su Mami ya gaishesu yafice daga gidan..Duk abinda Khalifa yayi akan idan Khameeni tadinga masa dariya tana ganin yafita tafito ta kwashe  kayan ta gyara sannan tanufi bedroom din sa tana murdawa taji tabudu tashiga ciki tana shiga mezata gani.....Toh fans kome Khameeni tagani oho


Muhadu a next page danjin me Khameeni taganiComments and share please🙏By Rufaida✍️


đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

   *A* *SANADIN* *MARAICI* 

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


    Story and writing

                By

      Rufaida(Rufeey )


 *MARUBUCIYAR* 


 *KAUNA* *CE* *KO* *KIYAYYA* 

 *BANFARGABA* 

 *Na* *fada* *tarkon* *sonshi* 


      *And* *now* 

      *A* *SANADIN* *MARAICI* *🌍MANAZARTA*

*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*

      *M. W. A* 


```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.đŸ€™đŸ»```

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

____________________________________


 *Wannan* *labarin* *kirkirarren* *labarine* *banyi* *dan* *wata* *ko* *wani* *ba* *Wanda* *yaga* *labarin* *yazo* *dai* *dai* *danasa* *toh* *akasine* *ban* *yarda* *a* *chanzamin* *labari* *ba* *Wanda* *ya* *chanzamin* *ban* *yafeba*.


 *BISMILLAHIR* *RAHAMANIN* *RAHIM*


PAGE 100↪️105


Tana shiga mezata gani kwalaban giya tagani a tsakar dakin azube da sauran kayan shaye-shaye da sauri ta karasa gurin tana dubawa duk dadai batasan kayan shaye-shaye ba Amman dai yanzu tabbas tasan sune nan maganganun Ummi suka shiga dawo mata nacewa Khalifa mashayine nandanan taji hawaye nazuba a fuskarta haka tashare hawayenta tayimai addu'ar shiriya...


Sannan tahau gyara masa dakin tas ta gyara ko ina ta wanke toilet tashinfida sabon bedsheet me kyau tawanke boxers da singlets dinsa gaba daya ta kunna turaren wuta sannan ta fesa room freshener nandanan dakin yahau kamshi me sanyaya zuciya sannan tafito tarufemasa daki duk wannan abin da Khameeni tayi jikinta duk asanyaye haka tafito ta dauki hijab tasa tashiga kitchen ta zuba abincin a kula sannan tafito tanufi part din Su Soomeey...


Tana shiga parlour duk suna zaune ta karasa ta gaida Daddy da Mami...


Daddy ya amsa cike da fara'a Mami kuwa ciki-ciki ta amsa Soomeey na ganin kula tazo ta amsa sannan suka gaisa Soomeey tashiga kitchen da kular tazuba abincin tafaraci tana santi haka taje ta kawowa Daddy ma shima yaci yana santi ita kuwa dama Mami tadade datashi daga parlour din Daddy ma yana gama ci ya fice dama fita zeyi...


Soomeey ta kalli Khameeni tace "matar yaya wai meke damunki ne."? Da Khameeni tayi niyar boyewa Soomeey sedai taga yakamata tasanar da ita nan tashiga fada mata abinda tagani tana gama fada mata Soomeey  tace "Khameeni tashi muje part dinku haka suka fito suka shiga part din suka zauna a parlour Soomeey tace "Khameeni kitsaya kiji abinda zance miki."? Nan Soomeey tashiga bawa Khameeni labarin Khalifa bata boye mata komai ba abu daya taboye shine bata fada mata cewa su Mami da Ummi ne sukai masa wannan abun ba shine kawai ta boyewa Khameeni..


Sosai Khameeni ta tausayawa Khalifa har kuka seda tayi kuma tadau alkawarin yaimasa addu'a kuma insha Allah duk wani abunda yakeyi seta sashi yadena sosai Soomeey tayi farin ciki nan dai suka cigaba da hira abinsu har lokacin sallah yayi sukayi suka cigaba da hira suna kallo..


Suka shiga kitchen suka dafa noodles sukaci har yamma Soomeey tana part haka suka Dora abincin dinner bayan sallar magriba suka gama abincin suka jera a dining table sannan Soomeey tadibi nasu taiwa Khameeni sallama tatafi part din su ita kuwa Khameeni bedroom din ta tashiga tayi wanka ta dauro alwala tayi sallar isha tayi addu'ointa tayi karatun qur'ani tana idarwa tadauki wayarta takira aunty Beeebat dantaji yataje gida masha Allah taje gida lapiya nandai sukaita hira sannan sukayi sallama takashe wayar...


Bajimawa Khalifa yashigo gidan kaitsaye dakinsa yanufa yana budewa wani sassanyen kamshi yadaki hancinsa besan sanda ya lumshe ido ba yakarasa shiga ciki yaga an gyara masa bedroom hakama toilet Amman Khalifa seya bata rai a fusace yace "watoma dan muna furci har bedroom dina tashigo koh? toh bari naje na koya mata hankali"..


A fusace ya jiwo zefita sekuma ya fasa yashiga toilet yayi wanka yazo yayi sallah sannan yasauko parlour yaga anjera abincin a dining area dama kuma yunwa yakeji hakan yasa, yaje ,yaja kujera yafara cin abincin yace "Amman fa yarinyar nan ta iya abinci hakadai yagama ci yadanyi kallo sannan yakashe komai tashige bedroom din shi ya kwanta. 


Khameeni tana ganin yatashi taje takwashe kayan ta wanke sannan tashige daki itama tayi addu'a ta kwanta bacci..Ummi da Kausar nagani a daki Kausar tace "Ummi yaushe za'a fara aikinnan ne wai."? Ummi tace ai dazu munyi waya da banzarnan (Mami) tace ai kokulata bayayi dan haka karki damu kinga yanzu bokan dazamuje gurin sa yayi tafiya sedai idan yadawo kinsan yanzu nachanxa boka dan banaso banzarnan tasan menake shiryawa ai yanzu sedai namaidata sakara muna gama aiki akan Khameeni zan dawo kanta." Nan uwa da y`a suka tafa suna dariyar shakiyanci..


Nikuwa nace Allah ka shirya kasa mufi karfin zuka tanmu Ameen(Yan uwa muguji zuwa gurin bokaye da malaman tsubbu dan ba inda zasukai mutun sedai sukai shi subarosa kuma kayi shirka a matsayinka na musulmi meye ribarka kawai dan wani bukata naka sekaje kafada halaka kuma duk abinda mutun keyi Allah nasane dashi kawai yana ara mana lokacine dan haka yan uwa mukula Allah yasa mudace Ameen)Kwana ki nata tafiya kullun Khameeni seta gyara wa Khalifa daki kullun yanaso yazo yaimata gargadi seya fasa kuma haryanzu basu taba haduwaba..    Yau jumma'a sati d`aya da auransu bayan Khalifa yafita office tashiga bedroom din shi danta gyara tana shiga taga kwalaban giya bama abude suba tayi murmushi mugunta tadibesu duka tazagaya baya tabudesu duka ta tuttular dasu sannan tadebo kwalaban takoma bedroom din shi tajerasu sannan ta gyara dakin ko ina tarufe tafito..Magriba nayi tafito ta daura girki bata gamaba sebayan isha Allah yasotama tayi sallar isha tana gama girkin tadauki nasu Soomeey tanufi part din su..


Tana fita Khalifa nashigowa dayake yayi sallar isha ga yunwa yanaji yasa yanufi dining area kawai yaje yacika cikinsa sannan yanufi bedroom din shi yana shiga kwalaban yagani ajere gashi kuma bakomai aciki ai a fusace yace "kan uba wallahi yausena koyawa yarinyar nan hankali." A fusace yanufi bedroom din Khameeni yatura kofar yashiga yaga ba kowa ya duba toilet nanma bakowa yace "toh ina tataje."? Yace  "toh koma ina taje ai zata dawo"..


Hakan yasa yakoma bedroom din shi yashiga wanka..


Bedade dashiga wanka ba Khameeni tashigo taga haryaci abinci tace "ashe yadawo." Haka tadibi kayan ta wanke sannan tashiga bedroom din ta sannan tashiga wanka..


Khalifa kuwa yana fitowa yashiga shiryawa cikin singlet da boxer yashirya sezuba kamshi yake yayi kyau sosai yana gama shiryawa yanufi dakin Khameeni dan haryanzu a fusace yake..


Yana zuwa a fusace yadaki kofar jikake daram Dede lokacin Khameeni tafito daga wanka daure da towel a tsorace tasaki salati dan kuwa ta jitsoro sosai Khalifa kuwa kasa motsiyayi ganin wacce idansa ke nuna masa...Pls kiyi hkr dawannan wlh bani da chaji ne shiyasa


Comments and share please 🙏


By Rufaida✍️

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

    *A SANADIN MARAICI*

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


    Story and writing

                By

        Rufaida(Rufeey)


*MARUBUCIYAR*


*KAUNA CE KO KIYAYYA*

*BANFARGABA*

*Na fada tarkon sonshi*


      *And now*

      *A SANADIN MARAICI**🌍MANAZARTA*

*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*

      *M. W. A* 


```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.đŸ€™đŸ»```

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

____________________________________


*Wannan labarin kirkirarren labarine banyi dan wata ko wani ba Wanda yaga labarin yazo dai dai danasa toh akasine ban yarda a chanzamin labari ba Wanda ya chanzamin ban yafeba.*


*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*


PAGE 105↪️110


Khalifa kuwa kasa motsiyayi ganin wacce idansa ke nuna masa shifa a ganinsa mafarki yakeyi hakan yasa ya murza idansa Amman haryanzu yana ganinta.. 


Khameeni kuwa dariya takusa kwace mata Amman seta waske ta jawo hijab tasaka tace "yaya Khalifa ya akayi."? Khalifa kuwa maganar Khameeni ce tadawo dashi daga tunanin dayake kuma yanzu ya tabbata Khameeni ce ba mafarki yakeba...


Khalifa yace "Khameeni wai dama ke su Daddy suka auramin."? Khameeni tace "eh mana gashi kagani." Khalifa yace "Allah na gode maka daka nuna min ranarnan"..


Sosai Khalifa yayi farin ciki a hankali Khalifa ya taka inda Khameeni take a tsaye yace "Khameeni nasan ban chan-chanta nazama miji agareki ba a matsayinki na kamilliyar ma...bata bari ya karasaba tace "dan Allah yaya kayi shuru ni ina sanka tsakani da Allah ko meka keyi zan zauna da kai dan haka kadena fadin wannan maganar duk wani abu dake faruwa nasani dan haka basekacemin komai ba"...


Khalifa da yake zubar da hawaye ya gungume Khameeni yana kuka yana cewa "Khameeni hakika nagode wa Allah dayabanike a matsayin mata nagode sosai matata"..


Khameeni tayi sauri ta rufe bakisa tace "bansan wannan godiyar tana share masa hawaye." Yace "Soomeey tasani shine bata fadamin ba koh".? Khameeni tayi dariya tace "eh mana ai tana sane"..


Yace "toh ai gashi yanzu nasani." 


Sannan yace "baby tashi muyi alwala muyi sallah." tace "ai nayi sallah." Yace  "eh ai nasani." Hakan yasa Khameeni tace "toh ai ni nayi alwala ma." Yace "ok toh bari ninayi kijirani." Tace "toh yaya." Sannan yashiga toilet dinta danyayi alwala..


Yana shiga ita kuma ta saka doguwar Riga tasa hijab tana jiran fitowar sa ai kuwa se gashi yafito  nan sukayi sallah sundade suna addu'a sannan Khalifa yashiga tanbayar Khameeni sosai take bashi amsa kuma yaji dadin irin zabin da Daddy sa yaimasa gaskiya yayi farin ciki kuma yaji Santa yana karashiga ko ina na ajikinsa yasan tabbas yaransa zasu sami tarbiya ingantacciya..


Itadai Khameeni tayi tsuru-tsuru kamar wata munafukađŸ€ŁđŸ€Ł 


Shikansa Khalifa abin dariya ya basa Amman seya basar yatashi yafita beyi maganaba bejimaba yashigo hannun sa dauke da roban freshyo da cup yana shiga yazuba a cup ya mika mata yace "karbi kisha." Tace "yaya Khalifa nakoshi fa." Yabata fuska yace "karbi." Da sauri Khameeni ta karba ta shanye..


Sannan yace "waito shi wannan hijab din ba'a cireshi ne."? Itadai Khameeni tayi shuru hakan yasa Khalifa ya karasa yacire hijabin sannan ya dauketa cak yanufi bedroom dinshi da ita tana cewa "yaya Khalifa nidai ka ajiyeni." Be saurareta ba ya a jiyeta kan bed..


Washe gari Khalifa yadinga lallaba Khameeni ita kuma se shagwaba take masa shikuwa ya rikice ga wani irin San Khameeni dayake shiga zuciyar sa se nannan yake da ita kamar ya hadiyeta..


Ita kanta Khameeni tasan Khalifa na mugun kaunar ta har tausayi yake bata sosai suke cin amarcin su dan kuwa Khalifa cewayayi shida zuwa office se nanda sati d`aya ita Khameeni har mamaki yake bata..


Sosai Khameeni ta dage dayiwa Khalifa addu'a shima kuma yanzu tanasashi ya dinga addu'oi Amman baya wani maida hankali Amman dai yanayi..


Bayan sati d`aya Khalifa ya koma office duk wasu yan matansa nada yadena bi takansu gaba daya ta matarshi Khameeni kawai yake..


Soyayyar su kawai suke sosai take bashi kulawa shima yake bata..


Suna kwance a bedroom din shi lokacin karfe 11 nadare wayar Khalifa tafara ringing yasa hannu yajawo wayar yana bubawa yaga FAULAT ce take kiransa.


     FAULAT wata budurwar Khalifa ce Amman ta bariki tana ba la'in sanshi Amman shikam kokadan basanta yakeba yanzu ma taji labarin yayi aurene shine take kiransa Amman yaki dagawa ko yanzuma ita kekiransa.


Yana ganin itace ya ajiye wayar nan kuwa besan Khameeni taga sunan ba Amman kawai ta basar kiranne yakara shigowa hakan yasa Khameeni taisaurin dauka kan ya ankara  harta amsa wayar daga chan Faulat tace "haba sweety tun yaushe nake kiranka Amman kaki dagawa gaskiya bakaimin adalciba haba nawan."? Itadai Khameeni tayi shuru Khalifa kuwa yayi suman zaune faulat dataji shuru tace "sweety tunda bazakayi magana ba shikkenan Amman nayi missing dinka yaushe zamu hadu."? Khameeni ta kashe wayar tamika masa tace "gashi a ana magana." Ya karba bakisa a sake yana kallan ta Khameeni kuwa  ta kwanta hawaye na zuba a idanta Amman tana   gogewa dan karya gani batasan duk yagantaba....Comments and share please🙏By Rufaida✍️

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

    *A SANADIN MARAICI*

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


    Story and writing

                By

        Rufaida(Rufeey)


*MARUBUCIYAR*


*KAUNA CE KO KIYAYYA*

*BANFARGABA*

*Na fada tarkon sonshi*


      *And now*

      *A SANADIN MARAICI**🌍MANAZARTA*

*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*

      *M. W. A* 


```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.đŸ€™đŸ»```

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

____________________________________


*Wannan labarin kirkirarren labarine banyi dan wata ko wani ba Wanda yaga labarin yazo dai dai danasa toh akasine ban yarda a chanzamin labari ba Wanda ya chanzamin ban yafeba.*


*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*


PAGE 110↪️115


Jikin Khalifa duk yayi sanyi duk dama beji me Faulat din tace mataba da sauri ya dagota Amman se Khameeni tai saurin rife idonta dan bataso yafuskanci wani abu shikuwa yasan tana sane tayi haka ahankali yafarai mata magana..


"Baby na please kiyi hakur..bata bari yakarasaba ta, tashi da sauri ta rufemai baki tace "yaya kadena bani hakuri nifa ba kaimin lefin komai ba karka damu kaji mijina." Khalifa yace "Baby nifa banasan wannan yayan dakike kirana dashi kisamin wani sunan." Tace "toh Honey." Sosai Khalifa yaji dadin sunan..


Washe gari duk abinda Khameeni ta sabayi shitayi sannan ta hada musu breakfast Khalifa ya tafi office ita kuma ta nufi part din su Soomeey tana zuwa duk suna parlour banda Daddy dan kuwa shi yayi tafiya..


Tana shiga ta gaida Mami ai Mami se tacewa Khameeni "ke rike gaisuwarki bana bukatar ta munafukar banza kawai." Soomeey tace "haba Mami gaskiya wannan abun dakike wallahi Mami kidena Allah." Mami tace "kedalla rufemin baki kona fasamikishi wallahi." Itadai Soomeey ba tace komai ba taja hannun Khameeni suka fice suka nufi part dinsu Khameeni..


Khameeni ta kalli Soomeey tace "nidai bansan menaiwa Mami ta tsaneni hakaba." Soomeey tace "karki damu wataran zata gane gaskiya mutayata da addu'a kawai"..


Soomeey ta kalli Khameeni tace "Khameeni tun shigowar ki part din mu naga damuwa a fuskar ki meya faru ko yaya ne."? Khameeni ta yi murmushi tace "bakomai Soomeey."  Soomeey tayi murmushi tace nizaki boyewa damuwar ki? koh Khameeni toh shikkenan bakomai." Soomeey tamiki zata fita Khameeni ta rukota tace "wallahi bahaka bane." Soomeey tace "toh meye."? Nan Khameeni ta fadama Soomeey abinda ya faru..


Soomeey tace "toh dai gaskiya ki dage da addu'a kinsan yan bariki seda addu'a." Khameeni tace "insha Allah nagode." Soomeey tace "Amman karki damu ai yaya Khalifa yana kaunarki bazeso ranki ya baciba"..


Nandai sukaci gaba da hirarsu suna dariya..Bangaran Faulat kuwa suna zaune a cikin dakinsu ita da kawarta zuly tana bata labarin abinda yafaru da takira Khalifa tace "ai ingaya miki beyi magana ba inata magana yaimin banza ai senayi maganin yarinyar daya aura." Zuly tace "ai yanzu musamu musan yarinyar daya aura kawai." Faulat tace "eh kuwa yanzu kitashi muje office dinshi." Zuly tace "toh." Nan suka shirya sukasa wasu tsinannun kaya suka fito suka shiga motar Faulat suka nufi company Khalifa suna zuwa office din Khalifa suka nufa..


Khalifa dayake zaune a office din shi suna waya da Khameeni kawai sejin mutane yai a kansa kafin yai wani abu tuni Faulat tafara magana.


"Haba baby meyasa kakemin haka kasan dai irin San danake maka Amman kakemin haka."? "Gaskiya baby nayi missing naka nasan kaima kayi missing dina." Khameeni dataji haka seta kashe wayar wani kuka ne yataso mata Soomeey datake gefanta tace "Khameeni kiyi shuru dan Allah ba kuka zakiyi ba kidage da addu'a sannan kuma semin koyawa shegiyar hankali zataci ubanta." Soomeey tace "wai nikuwa Khameeni ina Kausar tunranda aka kawoki tafito tana kuka ban kuma ganin taba."? Khameeni tace "toh nimadai bansaniba kam"..Khalifa kuwa cikin tsawa yace "uban wa yabaki izinin shigomin office."? Toh wallahi koki fita kona koya miki hankali dan ubanki toh wallahi kika kara nuna kinsan ni senaci ubanki shegiya kawai ke inbanda abinki mezanyi dake dadinma ai kekike kawo kanki dan haka yanzu banyinki kifitarmin a office sosai Khalifa yaciwa Faulat mutunci Wanda harseda tazubar da hawaye sosai daga karshe yasa afita dasu dasukaga haka suka fice..


Suka nufi gida suna zuwa zuly taita rarrashin Faulat tayi shuru zuly tace "gaskiya be kyautaba wannan cin mutuncin dayayi miki akan wata banzar yarinya." Faulat tace "wallahi kozanyi yawo tsirara se nashiga gidan Khalifa a  matsayin matarshi senasa ya tozarta yarinyar dayayimin cin mutunci akanta." Nandai sukaita kulle-kullensu..


Khalifa kuwa seda suka fice yatuno ashefa waya suke da Khameeni wayannan karnukawan suka shigođŸ€Ł da sauri yadau wayar yaga takashe kuma yasan taji maganar su da sauri ya kira Khameeni kuwa bata nuna komaiba ta daga wayar sosai sukayi hira bata nuna masa komaiba akullun wannan hali na Khameeni shiyake dada samiki Santa da Kaunar ta a zuciyar shi domin kuwa yasan yayi sa ar mata..BAYAN WATA BIYU 2


Ummi ne da Kausar a gaban saban bokansu Ummi tace "boka yanzu dai so muke karya kusanceta dan karta samu ciki." Ya kallesu yace "ai aikin gama yagama domin kuwa ya kusance ta sedai kusan abinyi." Kausar wani kishi ne yataso mata Ummi tace "toh yanzu dai tunda ya kusanceta a hanata haiwuwa gaba daya." Boka yace "toh shikkenan." sannan ya dauko magani yace "su samata a abinci ko abin sha indai taci toh ba ita ba haihuwa"...
Toh fa fans kunajin abinda Ummi da Kausar ke shiryawa kozasuyi nasara ko sabanin haka kudai kucigaba da bina danjin yanda zata kasance.Comments and share please🙏By Rufaida✍️

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

    *A SANADIN MARAICI*

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


    Story and writing

                By

        Rufaida(Rufeey)


*MARUBUCIYAR*


*KAUNA CE KO KIYAYYA*

*BANFARGABA*

*Na fada tarkon sonshi*


      *And now*

      *A SANADIN MARAICI**🌍MANAZARTA*

*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*

      *M. W. A* 


```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.đŸ€™đŸ»```

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

____________________________________


*Wannan labarin kirkirarren labarine banyi dan wata ko wani ba Wanda yaga labarin yazo dai dai danasa toh akasine ban yarda a chanzamin labari ba Wanda ya chanzamin ban yafeba.*


*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*


PAGE 115↪️120


Boka yabasu maganin suka karba suna godiya boka yace "toh nidai ba a bani kudi sedai kubiyani da jikinku." Yana maganar yana lashe baki yana karewa uwar da yar kallo Ummi tace "boka kamarya bamu ganeba."? Yace "ina nufi da jikinku zaku biyani kuma da wannan za'a fara." yana nuna Kausar Ummi tace "aa boka nidindai badai y`a taba." Boka yace "toh kubani maganina kutashi kubar nan." Kausar tace "nidai wallahi Ummi nayarda." Tana fadin haka tace "boka nayarda." Yace "yawwa ko kefa tashi mushiga daga ciki." Kausar tamike ko ajikinta Ummi na mata magana tayi banza...Boka yajuyo yakalli Ummi yace "toh ki shirya tana fitowa seke." Ummi tace "toh dan kuwa ta yarda Kausar taje dan susamu susami biyan bukata"..


Su Kausar ana ciki boka yana aiki dan kuwa Kausar ta murzu a hanninshi sosai tasha wahala Amman ko ajikinta dan zasu sami biyan bukata...


Kausar nafitowa Ummi ma tashiga boka yayi aiki sosai basu fitoba se bayan awa 2 Ummi taci kaniyarta😂😂😂


Basu suka baro dajinba se bayan sallar magriba hakan yasa sukayi gida suna zuwa gida kowa yayi makwancinsa...


Ummi nashiga daki ta kira Mami tace mata gobe zasuzo ai Mami tace "toh se kunzo." Sukayi sallama Ummi na kashe wayar tafara zagin Mami tana cewa sakarya kawai kema saura ke senayi maganin ki ai shashasha kawai..Khalifa ne ya dawo daga office bayan sallar isha part din su Daddy yanufa dan kuwa Daddy yace yana nemansa yana shiga ya gaida Daddy...


Daddy yace "yawwa dama abinda yasa nakira ka sabida maganar karatun Soomeey da Khameeni inaso kasamar musu admission a nan B.U.K"..


Khalifa yace "Daddy Soomeey dai ko banda Khameeni."? Yana fada yana Sosa kai Daddy yace "gidan Ku dukkansu zasuyi karatun." Khalifa yana tura baki yace "toh shikkenan Daddy." Nan sukadanyi hira da Daddy sannan yaimasa sallama yafice..


Yanufi part dinshi yana shiga yayi sallama Khameeni tana zaune a parlour tayi kwalliya tayi kyau sosai tasa kananun kaya yana shigowa taje da gudu ta rungume shi tana zuba masa shagwaba tayi masa sannu dazuwa sannan ta jashi bedroom yayi wanka tafito mai dakayan shan iska yana fitowa ya shirya ya kalleta yace "baby meye sirrin naga se kara kyau kike."? Khameeni tayi murmushi tace "Honey ai Kaine sirrin dakake kula dani sosai." Shima murmushin yayi yana jin San matar tashi naratsa ko ina najikinsa...


Haka tajashi sukaje dining table sukaci abinci suna gamawa suka zauna suna kallo Khalifa yace "Baby dazu munyi magana da Daddy yace wai karatu zaku farayi keda Soomeey za a samo muku admission a BUK." Khameeni harda tsalle tanata murna tace "Honey gaskiya naji dadi sosai wallahi." Khalifa ya harareta yace "wato kinaso adinga kallemin ke koh."? Tace "aa honey nidai kawai inasan nayi karatune shiyasa"..


Khalifa yace "ok gaskiya baby ina kishinki hajabi da nikab zaki dinga sawa kinji baby na." Tace "toh my life karka damu nitakace kai daya kaji." Yace "yawwa baby na." Nan sukaci gaba da hirarsu cikin soyayya sannan suka shige bedroom...


Washe gari Khalifa ya karbi takardunsu sannan ya tanbayesu wane course sukeso itadai Khameeni BIS tace takeso se akasami sa'a itama dai Soomeey BIS din tace tanaso haka yakarba yafice..


Wajen karfe 10 nasafe Ummi da Kausar suka shigo gidan su Khalifa suna zuwa suka zauna a parlour suka gaisa da Mami sannan Ummi ta mikawa Mami wannan maganin Mami tace "maye wannan din."? Ummi tace "Maganine nasamo a sawa wannan yarinyar a abinci ko abin sha indai taci toh ba ita ba haihuwa kinsan idan muka sake ta haihu toh mun shiga uku." Soomeey dake labe duk tana jinsu tace "zaku gane kuwa." Tayi kwafa Mami tace "kumafa hakane yanzu toh taya zamu samata a abinci ko abinsha."? Ummi tace "kawai kiyi kunun aya kizuba a ciki kinsan kunun aya yana da farin jini seki bawa Soomeey takai mata koya kikace." Mami tace "kai gaskiya shawarar tayi wallahi hakan za'ayi." Nan suka ci gaba da hira abinsu Soomeey kuwa duk taji abinda sukayi hakan yasa tayi kwafa ta koma daki su Ummi da Kausar basu dadeba suka tafi gida..


Mami tashiga kitchen dan hada kunun aya ai kuwa haka ta hada shi tazuba maganin takira Soomeey..


Bamusu Soomeey taje tace "Mami gani." Mami tace "yawwa Soomeey dauki kunun ayar nan kikaiwa Khameeni kije kidawo kema ganiki." Soomeey tace "aa Mami kawai zamusha tare kawo na kai." Mami tace "aa kema ganakinan fa." Soomeey data kunshe dariyar tace "toh shikkenan Ummi." Nan Soomeey takarba tayi waje tana fita tasakeshi yafadi yazube duka tayi murmushi tawuce ban garan Khameeni sukayi hira Soomeey ta kalli Khameeni tace "waini Khameeni meke damunki yau naganki kamar baki da lapiya."? Khameeni tayi murmushi tace "bakomai fa kawai banajin dadin jikinane." Soomeey tace "eyya sannu." Nan dai sukaci gaba da hirarsu sannan Soomeey tafice..


Mami kuwa ganin Soomeey bata dawoba yasa ta rude tace "Allah yasa yafiyar nan bazamatayi tashaba." Tana cikin haka Sega Soomeey tashigo Mami tace "naga kin dade."? Soomeey tace "eh ai munyi hirane shiyasa." Mami tace "ok tasha kunun ayar kuwa."? Soomeey "eh mana ta sha." Mami tayi murmushi tashige bedroom d`inta Soomeey tayi murmushi itama tashige bedroom d`inta tana Allah wadai da halin uwarta...Kwana biyu dayin haka Khalifa ya chanzawa Khameeni waya me tsadar gaske sannan ya bata mukullin mota sabuwa kar metsadar gaske Khameeni tayi farin ciki kuma tayi murna sosai kulun sesun fita yakoya mata motar cikin sati d`aya ta kware sosai masha Allah..


Mami kuwa ganin Khalifa yasewa Khameeni mota ta rude wato yana Santa kenan nandanan takira Ummi ta sanar da ita Ummi tace "karki damu danyasai mata mota ki kalesu zamuyi maganin su ai." Nandai sukaita kulle-kullensu sannan sukayi sallama Soomeey ma Khalifa yabata mota sabida yasan zasu fara zuwa skull shiyasa yasiya musu...


Yau Khameeni ta tashi da zazzabi sosai gashi kome taci seta dawo dashi yanzu haka a kwance take Khalifa yashigo ya ganta ahaka ya karasa gurinta yace "baby na meke damunki ne wai." Tace "Honey ba komai fa." Badan ya yardaba haka dai ya khaleta suna cikin hira amai yataso mata da gudu tayi toilet tana kwarara amai da sauri Khalifa ya bita yana mata sannu sannan yarikota yagyara mata jikinta yagyara toilet din sannan yashiryata shima ya shirya yace mata dole suje hospital badan tasoba suka tafi suna zuwa yakira wata classmate dinshi dayake likitace a hospital din bata jimaba tazo suka shiga office din suka gyaisa tace wa Khalifa "wanne ce madam din koh."? Yayi murmushi yace "eh itace." Tace "Masha Allah gata kyakyawa da ita tabarkalla." Yayi murmushi kawai nan likitan tadan tanbayi Khameeni abinda takeji ta fada mata sannan tayi mata test gwajin farko yanuna Khameeni nada cikin wata 1 zokuga murna gurin Khalifa sosai yayi farin ciki itadai Khameeni murmushi tayi sannan suka yiwa likitan sallama suka nufo gida....Comments and share please🙏By Rufaida✍️..

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

    *A SANADIN MARAICI*

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


    Story and writing

                By

        Rufaida(Rufeey)


*MARUBUCIYAR*


*KAUNA CE KO KIYAYYA*

*BANFARGABA*

*Na fada tarkon sonshi*


      *And now*

      *A SANADIN MARAICI**🌍MANAZARTA*

*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*

      *M. W. A* 


```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.đŸ€™đŸ»```

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

____________________________________


*Wannan labarin kirkirarren labarine banyi dan wata ko wani ba Wanda yaga labarin yazo dai dai danasa toh akasine ban yarda a chanzamin labari ba Wanda ya chanzamin ban yafeba.*


*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*


PAGE 120↪️125A mota daga Khameeni tayi motsi zece baby mene? Ita har dariya yake batama wallahi. 


Waya ya dauka yakira Soomeey ya gayamata wannan albishirdin sosai Soomeey tayi murna Amman data tuno su Ummi setaji hankalin ta yatashi sabida tasan halinsu sedai dole zata kula sosai dan karsu cutar da Khameeni da abinda ke cikinta kuma zata tayasu addu'a sosai hakadai taita tunani...


Su Khalifa suna dawowa yace ai dole Khameeni taci abinci ita kuma tasamishi kuka ita ba zata iyacin komai ba suna cikin haka Sega Soomeey tashigo tace "aa matar yaya meya farune."? Khalifa yace "kinji wai bazataci abinci ba kuma fa yau ba abibda taci." Soomeey tace "eyya mutuniyar toh yanzu kifadamin abinda zakici." Khameeni tayi shuru se chan kuma tace "wainar fulawa nakeso da manja da yaji metafarnuwa." Khalifa yace "toh sisi seki tashi kimana abinda mukeso." Soomeey tayi dariya tace "yan Zuma kuwa"..


Haka tashiga kitchen ta kwaba wainar fulawa tasoya da manja sannan taje ta dakko yajin tafarnuwar ta kawowa Khameeni..


Khameeni kuwa tuni tafara cin wainar fulawar ta zabga yaji Khalifa yace "haba Baby yanzu wannan yajin zaki cinye toh wallahi baki isaba." Haka yadauke wainar fulawar ai kuwa Khameeni ta fashe da kuka Soomeey tace "yaya please kabarta kaga kasata kuka." Yace "Soomeey kinga yajin dazata zubama cikinta fa." Soomeey tace "yaya kaidai kabata." Yace "toh shikkenan." Ai kuwa yamika mata ta amsa tana harararsa shikuwa murmushi yayi kawai..


Haka Khameeni taci wainarnan anci sa'a kuwa batayi amaiba bata Dade da gama Ciba bacci yadauketa Khalifa yakaita bedroom ya kwantar..


Daddare Soomeey tasamu Daddy ta fada masa sosai yayi murna shima zesamin jika duk abinda ake Mami bata saniba dan bawanda ya sanar mata..


Washe gari Aunty Beeebat takira Khameeni suka gaisa take tanbayarta meke damunta taji muryarta haka?  Khameeni tace "bakomai fa aunty." Aunty tace "Khameeni kodai dakwai wata matsala."? Khameeni tace "aa aunty bakomai." Aunty tace "toh shikkenan turomin number mijin naki." Khameeni tace "toh aunty." Nan kuwa tatura mata tana tura mata ta kirashi suka gaisa tayi mishi bayani Khalifa yake gayamata ai Khameeni bata da lapiya ne ba kunya yagaya mata..


Ooo su Khalifa ba kunya😂Sosai Aunty tayi murna tayi mata addu'ar sauka lapiya sannan sukai sallama..


Suna sallama Aunty takira Khameeni tace "wato kigayamin abinda ke damunki kikaki toh shi mijin naki yaga yamin ja'ira kawai." Itadai Khameeni dariya tayi kunya ta kamata sukayi sallama takashe wayar suna gama waya da Aunty Beeebat takira Khalifa..


Yana dagawa tasamishi kuka wai dan meyasa zeje yaita wani yadawa har Aunty yaga yawa yanzu gashi yasa taji kunya hakadai ya rarrasheta tayi shuru sannan sukai sallama..


Khalifa nagama waya abokinsa Hilal ya kirashi yace "wai abokina tunda kayi aurannan ka watsar damu kadena nemam mu kadena zuwa club sekace bakaine kake cewa bakasan auren ba." Khalifa yayi dariya yace "aboki ban watsar dakuba kawai dai aikine yamin yawa a office shiyasa kuma dakake  cewa banasan auren yaro da kasani Amman yanzu Dana gane wacce Daddy ya auramin nandai yabashi labarin abinda yafaru." Hilal yace "wato ita taboye mana kai kenan."? Yace "eh mana." Hilal yace "toh gobe zamuzo nuga amaryar tamu." Khalifa yace "dan iska bana nemamku." Hilal yace "kai wallahi seminzo munga wacce ta chanza mana aboki." Khalifa yace "ok toh shikkenan se kunzo." Nandai sukayi sallama..


Khalifa nakomawa gida ya fadawa Khameeni abokansa 2 zasuxo tace "toh Allah yakaimu." Yace "Ameen yawwa Baby hijjabi zaki saka fa." tace "honey kobaka fadaba dama hijjabi zansa ai." Yace "yawwa baby na shiyasa nake kara sanki." Tayi murmushi tace "nima haka." Yace baby nayi missing dinki." Amman ke naga bakiyi missing dinaba." Tace waya gaya maka nima nayi missing naka sosai." Yace "ok toh nunamin yanda kikai missing nawa." Tace "toh my Honey". 


Uhmmm nandai naja musu kofa nace asuba ta gari..


Washe gari kuwa weekend ne Khalifa na gida Soomeey tazo sukayi aiki dan yau abokansa zasuzo Khameeni kawai dauriya take tana aikin dan kuwa cikinta me laulayine Soomeey tayi-tayi taje ta huta Amman taki Soomeey har Khalifa taga yawa shima yayi mata magana tace "ita fa subarta tayi aikin ta kawai." Hakan yasa yakaleta Amman yasan matarshi jarumace akwai dauriya...


Basu sukagamaba se wajen 2 sannan suka Dada gyara gidan dama kuma koda yaushe acikin gyara yake da kamshi..


Ko ina se tashin kamshi yake haka suka gama ko wacce ta nufi toilet Khameeni na fitowa ta shirya ba kwalliya tayi ba mai kawai ta shafa se kolli da powder da lipstick sannan tasa doguwar rigar material sabida yanzu tafisan doguwar Riga duda cikin nata kokadan befitoba idan kagantama bazakace tana da cikiba indai ba kuma yanayin jikinta daya nuna hakan ba tayi kyau sosai kam tana cikin shiryawa Khalifa yashigo..


Ya rumgumota ta baya yace "baby yanzu kinzama me taurin kai da fada koda yake duk lefin babyn mune yake saki haka yana shafa cikinta yake fadar haka." Khameeni kuwa turo dan karamin bakinta tayi tace "ni bawani fada danakeyi fa." Suna cikin haka wayar Khalifa tahau ringing yana dubawa yaga Hilal ne..


Yadaga daga chan ban garan Hilal yace "munfa zo." Khalifa yace "ok Ku shigo mana." Sannan ya katse wayar yadaukowa Khameeni wani katan hijab har kasa yasaka mata Khameeni tace "yaya wannan kadan hijabi haka sekace matar liman gaskiya ni yaya wannan yamin nauyi a jiki fa." Yace "toh bari na dauko wani haka yadauko wani Wanda bekai wannan ba yasa mata..


Soomeey kuwa tana parlour su Khalifa tana game a wayarta Hilal da Bashir sukayi sallama Amman ina bata jiba dasuka ji shuru kawai suka shiga parlour suka dadayin sallama Amman Soomeey bata jiba tana game karar game din dasukajine yasa suka kalli gurin Hilal ne sarki fushi yadakawa Soomeey tsawa Wanda yasa Soomeey tayi wurgi da wayar hannun ta jiki narawa tamike sechan kuma kome tatuna seta haderai Takalli Hilal tace "malam lapiya kakemin wannan twawar kamar wani ubana."? Tanayi tana murgudamasa baki sannan tace "aikin banza kawai." Hilal yazaro ido yace "ke nikikewa rashin kunya."? Tace   "nayi din kozaka kashenine."? Khalifa dake rike da hannin Khameeni yadakawa Soomeey tsawa Wanda ba Soomeey kadaiba hatta Khameeni dake kusa dashi seda ta tsorata hakan yasa ta sumewa...Ooo Khalifa zaka kashe mana Khameeni kunsan abinka da me ciki Comment and share please🙏By Rufaida✍️


đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

    *A SANADIN MARAICI*

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


    Story and writing

                By

        Rufaida(Rufeey)


*MARUBUCIYAR*


*KAUNA CE KO KIYAYYA*

*BANFARGABA*

*Na fada tarkon sonshi*


      *And now*

      *A SANADIN MARAICI**🌍MANAZARTA*

*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*

      *M. W. A* 


```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.đŸ€™đŸ»```

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

____________________________________


*Wannan labarin kirkirarren labarine banyi dan wata ko wani ba Wanda yaga labarin yazo dai dai danasa toh akasine ban yarda a chanzamin labari ba Wanda ya chanzamin ban yafeba.*


*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*


PAGE 125↪️130


Da sauri Khalifa yatarota tafado jikinsa seyakula ai tasuma ma da sauri su Soomeey suka karaso gurin Khalifa yarude sosai yarasa mezeyi da sauri Soomeey ta kawo ruwa ya zuba mata Khameeni ta sauke ajiyar zuciya..


Khalifa yace "Baby na sannu kinji kiyi hakuri." Tace "yaya bakomai." Nan su Hilal da Bashir da Soomeey suka yimata sannu ta amsa..


Soomeey ce tamike tsaye fuskarnan a hade tayi hanyar fita Khalifa yace "Soomeey dawo ki zauna." Soomeey data bata fuska tadawo ta zauna Khalifa yace "meyasa kikewa Hilal rashin kunya alhalin nasan ba halinki bane."? Tace "yaya Khalifa toh bashine ya fara tsokanataba ya dakamin tsawa." Khalifa yace "toh ai kece karama dan haka yanzu kibashi hakuri kuma bansan kikara yiwa koma wane rashin kunya kinji." Tace "toh yaya." Nan tabawa Hilal hakuri shikuma yanuna komai ya wuce..


Amman Soomeey kuwa zabga masa harara take kawai shima yana kallanta Amman sebe kulataba nan suka gaisa da Khameeni sannan suka gabatar musu da abincin nan suka nufi dining table suka haucin abinci Soomeey da Khameeni kuwa sukayi daki..


Khameeni tace "Soomeey wai meya hadaku ne da Hilal." Soomeey tace "dan rainin hankali ne wallahi zanyi maganinshi ai." Nan ta kwashe abinda ya faru ta fada mata..


Khameeni tace "kedai Soomeey Allah yashirya ki gaskiya..


Nan daisukaita hira seda su Hilal zasu tafi sannan suka sakko sukayi sallama dasu Soomeey se hararar Hilal take shikuwa kwafa kawai yake..


Nan suka fito Soomeey ta zagayo ta takawa Hilal kafa kuma tana sane Hilal yaji zafi sosai yace "wayyo kawata." Soomeey ta kunshe dariya nan hankalin kowa yadawo Kansu Khalifa yace "toh mekuma ya faru." Soomeey tace "yaya bansani ba ne natakawa yaya Hilal kafa." Khalifa yace "eyya sannu abokina." Soomeey tamai gwalo tace "sannu yaya Hilal." Shikuwa bekulata ba Amman yadau alkawarin seya koyawa yarinyar nan hankali..


Nan dai suka shiga mota suka fice daga gidan..


Washe gari Khalifa daya tashi daga office yabiya BUK yakarbowa su Khameeni admission later dinsu Masha Allah kuma anbasu abinda suka zaba haka yadawo gida..


Sosai Khameeni da Soomeey sukayi murna..


Bangaran Faulat kuwa sotake taga wacece Khalifa ya aura dayake mata wula kanci akanta sotake setasan wace sannan zata fara aikinta akan su..


Amman haryanzu tarasa yazatayi tasan kowace kuma haryanzu tana bincike akai..


Mami da Ummi da Kausar haryanzu basusan Khameeni nada cikiba ita dama Soomeey bataso Mami tasani Khalifa kuwa aiki yamasa yawa shiyasa besanar mataba shiyadaukama tasani shima Daddy yadauka tasanine shiyasa begaya mataba..


Bayan sati d`aya duk shirya-shiryan skull dinsu an gama ranar Monday zasu fara lectures yau dama weekend ne Khalifa na gida beje ko ina ba suna zaune a parlour. Sega Kausar tashigo ko sallama babu. Basu Dade dazuwa gidan ba su Ummi da Mami sukace Kausar tashigo part dinsu ta kira Khameeni.


Khameeni nakan ciyar Khalifa suna hirarsu kawai maganarta sukaji akansu tana cewa "ke Khameeni kizo su Ummi na kiranki."  Khameeni seda gabanta yafadi  seta dake tace "toh" kawai Khalifa yayi tsaki yace "ke wace irin mahaukaci yaye zaki shigo ba sallama."? Kausar dai shuru tayi secen tace "haba sweety na nifa masoyiyar kace Amman kake wula kantani." Khalifa a fusace yamike yakaimata wani mari da sauri ta goce tayi waje da sauri Khameeni tace "haba honey meyasa kake da saurin fushi da saurin hannu pls mijina kadena kaji." Yace "shikkenan matata nadena." Tace "yawwa bari naje kiran da su Ummi sukemin." Yace "toh shikkenan"...


Haka Khameeni ta fita dama doguwar Riga ce ajikinta tana fargabar abinda zasuyi mata tana shiga kuwa Ummi tabita da ido tana kallan ta ganin irin kyandatayi tayi kiba kamar ba itaba Mami ma kallanta take..


Tana shiga ta karasa ta gaishesu basu amsaba illa zagin da Ummi take mata itadai Khameeni shuru tayi Ummi tace "ke zonan." Khameeni takarasa gabanta ta tsugunna Ummi tace "tashi tsaye." Khameeni ta mike Ummi na kare mata kallo tace "meke damunki ne."? Da mamaki Khameeni take bin Ummi da kallo Khameeni tace "Ummi bakomai." Ummi ta kalli Mami tace "kina ganin abinda nake gani kuwa."? Mami tace ke Khameeni jeki kawai"..


Khameeni itadai jiki asanyaye tafice..


Ummi tace  "kardai yarinyar nan ciki gareta." Mami tace nimadai kamar naga hakan." idankuwa hakane toh zama be kamamuba..Kuyi hkr dajina shuru da kukayi hakan yafaru ne saka makon komawa skull danayi dan haka ba kodayause zaku rika ganin posting ba next week insha Allah zamu fara Exam pls ina bukatar addu'ar Ku ngd 


Inayinku over wlh kuna raina❤️đŸ˜đŸ„°Comments and share please🙏By Rufaida✍️


đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

    *A SANADIN MARAICI*

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


    Story and writing

                By

        Rufaida(Rufeey)


*MARUBUCIYAR*


*KAUNA CE KO KIYAYYA*

*BANFARGABA*

*Na fada tarkon sonshi*


      *And now*

      *A SANADIN MARAICI**🌍MANAZARTA*

*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*

      *M. W. A* 


```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.đŸ€™đŸ»```

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

____________________________________


*Wannan labarin kirkirarren labarine banyi dan wata ko wani ba Wanda yaga labarin yazo dai dai danasa toh akasine ban yarda a chanzamin labari ba Wanda ya chanzamin ban yafeba.*


*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*


PAGE 130↪️135


Ummi tace "ai kuwadai zama be kamamu ba gaskiya." Toh Amman idan hakane batasha kunun ayar nanba kenan."? Mami tace "eh mana tasha Soomeey na aika takai mata kuma tacemin tasha." Ummi tace "anya kuwa tasha kinsan ancemin indai tasha toh ba ita ba haihuwa Amman dai ba damuwa kibar komai ahannuna zan San yanda za ayi kiban nanda sati d`aya." Mami tace "toh shikkenan ai ba damuwa"..


Soomeey dake labe duk tanajin abinda sukace hankalin ta inyayi dubu toh ya tashi Amman tadau alwashin bazata taba bari su cutar da Khameeni da abinda ke cikintaba..


Kausar kuwa wani mugun tsanar Khameeni takeji a zuciyar ta kamar ta kasheta ta huta haka takeji.


Yau Monday Soomeey da Khameeni sunyi shirin skull sunje sungaishe da Daddy da Mami sannan sukai musu sallama suka shiga motar Khameeni suka nufi skull..


Suna zuwa suka nufi inda za'a gabatar da lecture din basu jimaba malamin yashigo yayi abinda zeyi ya fita.


Dayake ranar farkone sun tashi da wuri 2 suka gama lecture suka nufo gida..Bayan kwana biyar Ummi ce da Kausar a gaban sabon bokansu Ummi tace "boka yarinyar nan kamar ciki garetafa." Boka yace "ai bakamar bane cikine ma." Ummi tace "toh Amman boka Kaine kabani maganin nan kace idan tasha ba ita ba haihuwa Amman kuma Sega ciki ya bayya na."? Boka yace "toh gaskiya yarinyar nan bata sha maganin nan ba dankuwa da tasha bazata samu ciki ba ke koda lokacin da ciki toh atake cikin ze zube." Ummi tace "toh yanzu ya za'ayi."? Boka "toh yanzu zan baku maganin da za'a bata tasha shimadai kamar wancen ne idan tasha atake cikin ze xube Amman fa sekun bani hadinkai." Ummi "boka ai indai wannan ne shikkenan ba damuwa." Boka "yawwa toh ke Kausar tashi mushiga daga ciki." Haka Kausar ta tashi, tashiga ciki..


Bayan awa d`aya se gasu sun fito boka yabasu maganin sannan suka tashi suka tafi..


Sosai Soomeey da Khameeni suke karatu Allah yate maki Khameeni cikinta bame laulayi bane sedan abinda ba arasaba.


Soyayya da kauna Khalifa da Khameeni suke nunawa junansu basuso wani abu yasami dayan su kullin cikin kyauta tawa juna suke..


Sosai Khameeni kayiwa Khalifa addu'ar shiriya kuma masha Allah se samin cigaba ake yanzu ya rage shaye-shayen dayakeyi sosai ya rage dama kuma neman matan banza tunda ya auri Khameeni ya dena yanzu sesan banka sosai Soomeey tayi farin ciki Daddy ma yayi farin ciki sosai dan nasa yafara shiryuwa wannan kenan..Bangaran Faulat kuwa tasamu labarin skull din dasu Khameeni suke zuwa dan haka yau take da niyar zuwa..


Sun gama shiryawa ita da kawarta zuly haka suka nufi skull din su Khameeni suna zuwa sukayi zamansu a mota tadauki waya ta kira Wanda tasa yabincuko musu skull din yana dagawa tace "yawwa ko zakayi mana kwatancen ya take yarinyar."? Dayake wayar a hansfree take yace "owk kullin dai da nukab nake ganinta da hijab bantaba ganin fuskar taba sekuma wata wacce nake ganin su tare duk inda zasu tare ita kuma batasa nikab." Tace "owk nagane Amman ita dayar na Santa kanwar shice Soomeey lokacin damuke tare dashi nasanta sosai indai itace zangane ta." Yace "owk toh shikkenan kuji rasu zakuga sunfito tare ai sunkusa gama lecture din." Faulat tace "toh shikkenan ba damuwa seka jini." ta kashe wayar.


Basu jima ba kuwa segasu Soomeey da Khameeni sun fito suna fitowa kawai Khameeni ta yi baya da nikab dinta Faulat da akan idanta suka fito har Khameeni ta dage nikab dinta Faulat batasan sanda tace "nashiga uku ba sabida tsabar rudewar datayi naganin fuskar Khameeni a zuciyar ta take cewa "dole Khalifa ya rabu dani akan ta.


Nan danan taji wani azabban kishi yadaki zuciyar ta da sauri ta fita daga motar tanufi gurin su Khameeni dasuke kokarin shiga mota da sauri zuly tabiyo bayan Faulat tana kiranta Amman kojuyowa bata yiba tana zuwa ta dauke Khameeni dawani mahaukacin mari....Comment and share please🙏By Rufaida✍️


đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

    *A SANADIN MARAICI*

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


    Story and writing

                By

        Rufaida(Rufeey)


*MARUBUCIYAR*


*KAUNA CE KO KIYAYYA*

*BANFARGABA*

*Na fada tarkon sonshi*


      *And now*

      *A SANADIN MARAICI**🌍MANAZARTA*

*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*

      *M. W. A* 


```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.đŸ€™đŸ»```

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

____________________________________


*Wannan labarin kirkirarren labarine banyi dan wata ko wani ba Wanda yaga labarin yazo dai dai danasa toh akasine ban yarda a chanzamin labari ba Wanda ya chanzamin ban yafeba.*


*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*


PAGE 135↪️140


Faulat tana zuwa ta dauke Khameeni dawani ma haukacin mari kamar a mafarki Khameeni taji wannan mari soomeey a fusace tajuyo dan ganin wana shegenne yai gangancin marin Khameeni.


Soomeey najuyowa taga Faulat a tsaye tana huci kamar wata zakanya soomeey dama tasan Faulat tace "kan uba dan ubanki metaimiki zaki mareta".? Faulat tace "ke soomeey badake nakeba dan haka kimin shuru".


Ai soomeey data gama fusata tadaga hannu ta shararawa Faulat mari har guda 4 jikake tas tas tas tas tace "dan ubanki ba kyaleki zanba kuma wallahi sena gayawa yaya khalifa dama sabida shikikai haka toh wallahi sekinyi nadamar dukanmai mata da kikayi".


Soomeey ta kamo hannun Khameeni tasata a mota taja motar suka nufi gida.


Faulat kuwa takaici ya isheta Marin da soomeey tayi mata gashi soomeey tace seta gayawa khalifa tasan yau tashiga uku zuly dake gefe tana tayiwa Faulat dariya a zuciyar ta tana cewa Allah shikara bake baki da hankali ba ai gashinan sosai zuly kemata dariya da kar tatsayar da dariyar ta kamo tasa ta amota suka bar gurin..


Bangaran Ummi da Kausar kuwa yau suke shirin zuwa gidan su soomeey.


Suna gama shiryawa suka nufi gidan su soomeey Mami na parlour tana kallo suka shigo suka zauna.


Soomeey kuwa Suna mota tanata mitan abinda Faulat tayi itadai Khameeni tayi shuru can dai tace "soomeey kiyi shuru kibar maganar nan kuma dan Allah karki fadawa yaya khalifa ki kyaleta kawai." Soomeey tace Chab wlh sena fada masa barima kigani"..


Soomeey ta dauki wayarta takira khalifa ta fada masa sosai ransa yabaci dan kuwa soomeey harda kara gishiri..


Khalifa yace "shikkenan kukarasa gida zanyi maganin ta yanzu nan.


Suna zuwa gida soomeey tayi parking suka fito soomeey harzatabi Khameeni part dinsu se kuma ta nufi part dinsu kamin takarasa taji Ummi tana fadawa Mami yanda zatayi da maganin kamar dai yanda tayi a wancen soomeey tayi tsaki tace "Allah yashirya zanyi maganin Ku wlh"..


Sannan tashiga ciki suna ganinta tashigo sukayi tsit azuciyar kowanne su yana fatan Allah yasa soomeey bata jiba..


Ita kuwa soomeey tana shiga ta gaidasu tanuna bataji mesuke cewaba sannan tawuce dakinta tana dariyar mugunta..


Basu jimaba suka tafi Mami tashiga kitchen dan yin kunun ayar tana gamawa ta kira soomeey tace "yawwa Khameeni dauki kikaiwa Khameeni kinji soomeey tace "Mami duk abinda kukafada dazu ina jinku hatta wancen maganin  dakuka sawa Khameeni shima duk nasani...


Pls kuyi hkr da wannan nadan samu time ne shiyasa namuku wannan insha Allah next week zaku dinga jina a kai akai ngd


Comments and shere please🙏

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

    *A SANADIN MARAICI*

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


    Story and writing

                By

        Rufaida(Rufeey)


*MARUBUCIYAR*


*KAUNA CE KO KIYAYYA*

*BANFARGABA*

*Na fada tarkon sonshi*


      *And now*

      *A SANADIN MARAICI**🌍MANAZARTA*

*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*

      *M. W. A* 


```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.đŸ€™đŸ»```

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

____________________________________


*Wannan labarin kirkirarren labarine banyi dan wata ko wani ba Wanda yaga labarin yazo dai dai danasa toh akasine ban yarda a chanzamin labari ba Wanda ya chanzamin ban yafeba.*


*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*


PAGE 140↪️145


Soomeey taci gaba dacewa "Mami kadafa kimanta nima gidan wani zani duk abinda kikaiwa yar wani kema za ayiwa taki toh dan haka Mami inaso kidena wannan abinda kukewa Khameeni Mami kituba kikoma ga Allah Mami kinsanfa Khameeni marainiyace kuma kinsan hukuncin Wanda ya zalinci maraini ya Mami kidena biyewa San zuciya kidena biyewa Ummi nasan wallahi Allah Ummi bada zuciya da'ya take zaune dakeba wallahi".


"Ummi ita take kara zugaki kikeyin duk wannan abun Mami yaya khalifa da zuciya da'ya yake zaune dake yadaukeki tamkar mahaifiyar Sa bayasan ganin bacin ranki bayasan damu warki kullun cikin kyautata miki yake Amman Mami duk bakya gani kika biyewa San zuciya da aminiyar ki wato Ummi kuka lalata rayuwar yaya khalifa duk haka be ishekuba kukai masa aure Ku aganinku auren da kukaimai dan Ku muzguna wa marayin Allah nankuwa Baku sani ba duk kanninsu sun dade suna kaunar junan su toh Mami anan ma bakuga isharaba kukai wunkurin hanata haihuwa nan ma Allah bebaku sa'a ba gashi yanzu da cikin ta Amman Baku hakuraba kuke kokarin buz damata da ciki..


"Haba Mami kina tunanin duk abinda kikai ni ba za'amin ba wallahi Mami tun wuri kinemi yafiyar bayin Allah nan tunkan lokaci ya kure miki.


Soomeey ta kamo hannun Mami tace "Mami na karkice namiki rashin kunya Amman wallahi Mami gaskiya nake fada miki Amman idan ranki ya baci kiyi hakuri." Soomeey nagama fadin haka tabar gurin.


Mami kuwa data daskare agurin duk jikinta yayi sanyi sosai tasan kuma duk abinda yarta tafada mata gaskiya ne jiji a sanyaye tabar gurin..


Bangaran khalifa kuwa yana fitowa daga office bezarce ko inaba se gidan Faulat ko sallama beyiba yashiga gidan yana shiga ya ga Faulat ce kadai a parlour tana kallo ya zare belt din wandan shi yashiga laftarta tako ina.


Faulat kamar a mafarki taji saukar duka tako ina tana juyowa taga khalifa ne kemata wannan dukan hakuri take bashi Amman besan tana yibama seda yafarfasa mata jiki tukunna yabarta yayi tagiyar sa..


Zuly dake daki dataji iwun Faulat taleko tana lekowa ta ga khalifa ne yake jibgarta ai kuwa takoma daki tanana dariya tana Allah yakara koda khalifa yafice daga gidan zuly ko fitowa bata yiba balle tatemakawa Faulat din..Bayan kwana biyu 2 Mami tashirya tanufi gidan aminiyar tata tana shiga suka gaisa damasu aiki suka cemata ai hajiyar tana dadinta..


Haka tanufi dakin aminiyar tata tana shirin tura kofar dakin taji wata magana data kusa tasata tazube Amman seta daure abinda taji Ummi na fadawa kausar.


Jitai kausar nace wa "nifa Ummi wannan soomeey na tsaneta kawai kisa boka lama rudu  yayi mana maganinta." Ummi tace "ai bama ita kadaiba har uwar tata senasa yayi maganinsu sena hana wannan soomeey aure a duniya uwar takuwa sonake yasamata cuta harta mutu da ita Amman kibari mugama da Khameeni tukunna..


Sosai Mami tayi mamakin aminiyar tata bata taba tunanin zata mata hakaba ashe maganar soomeey gaskiya ne.


Nan danan hawaye ya wannke mata fuska da sauri tasauko tafito tashiga motarta tayi gida sosai Mami tayi nadamar abinda tayi a rayuwar ta kuma tadauki alkawarin karya asirin dasukaiwa khalifa dama Wanda taiwa majin nata haka takarasa gida tana zuwa taga soomeey a parlour ita kadai soomeey taga Mami tashigo tana kuka da sauri ta tareta tana cewa "Mami lapiya meya faru."? Mami taja soomeey daki suka zauna Mami tashigasanar wa da soomeey duk abinda taji su Ummi sun fada"..


Soomeey tace "Mami dama na fada miki ai Amman yanzu ki kwantar da hankalin ki ba abinda zesamemu insha Allah yanzu Mami kamatayayi kinemi yafiyar Daddy da yaya khalifa da Khameeni insha Allah yanxunnan zannemi yafiyar su kuma a yau dinnan zanje gurin bokan dayai mana aiki duk yakarya asirin.


Soomeey tace "yawwa Mami na yanzu muje part dinsu yaya khalifa tunda yananan be fitaba." Mami tace "toh shikkenan muje haka suka fita suka shiga part dinsu yaya khalifa.


Suna shiga suka gansu duk suna parlour suka karasa Khameeni da khalifa suka gaida Mami ta amsa sannan Mami tace "yarona nazo neman yafiyar ka dakai damatar ka nan tadafa masa abinda suka aika bawanda baya kuka acikinsu da sauri khalifa yakarasa ya rungumeta yana cewa Mami dan Allah kiyi shuru kidena durkusamin kina rokan yafiyata wallahi Mami nayafe miki duniya da lahira kuma haryanxu kina a matsayin dakike ba abunda yatsanza matsayin ki..


Sosai Mami take kuka hakika khalifa bawan  Allah ne Khameeni ma tayafewa Mami sosai Mami tayi farin ciki..Mami nafitowa daga part dinsu yaya khalifa tanufi motarta ba inda tanufa se gurin bokan tana zuwa tagaya masa abinda  yakawota yace "toh shikkenan yanzu zan karya asirin sabida naga kinyi nadama sosai kuma dama kece baki saniba Amman nadade dasanin wannan kawar taki ba tsakani da Allah take sankiba kuma naji dadi dakika gyara rayuwar ki nima nan dakike gani nayi nadama Allah yashiryeni dan haka yanzu zan karya asirin atake agurin ya karya  asirin duka sannan yace tadage da addu'a dankuwa wannan kawar tata hatsabibiya ce"..Mami tayiwa boka godiya ta tafi..


Tana zuwa gida lokacin Daddy yadawo haka tanemi yafiyar Sa yayi haryace tabar masa gida seda khalifa yaita bashi hakuri tukunna ya hakura ..Ummi takira Mami dan taji ko cikin Khameeni ya zube ai kuwa Mami bata nuna mata komaiba tace mata ai aranar datasha aranar yaxube sosai Ummi da Kausar suke murna..Ai kuwa rayuwa tayiwa iyalan gidan dad'i kullin cikin farin ciki suke sosai Mami ke kula da Khameeni se nannan take da ita khalifa kuwa ruyuwarsa tada tadawo yanzu shiyakewa Bashir da Hilal fada kuma alhamulillah suma sun fara shiryuwa dan kuwa sundena neman mata sundena zuwa club yanzu sunfara shiryuwa sosai sedai masha Allah kuma yanzu Hilal San soomeey yake kuma yagaya khalifa sosai khalifa yayi murna yace shikkenan yaje yanemi soyayyar soomeey..


Lokacin dayazowa soomeey da zancen kin amincewa tayi seda Khameeni ta bata shawara tukunna ta amince suka fara soyayyar su shima Bashir yasamu wata yar uwarshi..


Ansa bikin soomeey da Hilal wata 1 sena Bashir ana gama nasu Hilal da sati 2 senashi..


Bayan wata 1 shirin bikin soomeey da Hilal ake dan kuwa gobe za'a fara bikin..💃💃💃💃💃💃Toh fans A SANADIN MARAICI yakusa zuwa karshe se kucigaba da bina dan jin karshen labarin Comments and share please🙏


đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

    *A SANADIN MARAICI*

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


    Story and writing

                By

        Rufaida(Rufeey)


*MARUBUCIYAR*


*KAUNA CE KO KIYAYYA*

*BANFARGABA*

*Na fada tarkon sonshi*


      *And now*

      *A SANADIN MARAICI**🌍MANAZARTA*

*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*

      *M. W. A* 


```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.đŸ€™đŸ»```

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

____________________________________


*Wannan labarin kirkirarren labarine banyi dan wata ko wani ba Wanda yaga labarin yazo dai dai danasa toh akasine ban yarda a chanzamin labari ba Wanda ya chanzamin ban yafeba.*


*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*


PAGE 145↪️150


A yaune aka fara bikin soomeey da Hilal masha Allah amarya da angonta sun hadu sosai sunyi kyau sesan barka..


Khameeni ma da khalifa ba'a barsu abayaba wajen haduwa subyi kyau masha Allah cikin Khameeni yafara fitowa yanzu watan shi 5 sedai fatan sauka lapiya.


Anyi walima anyi kamu anyi dinner ranar lahadi aka daura aure iyaye da yan uwa kowa yamata nasiha akan rayuwar aure  bayan magriba aka kai amarya gidan mijinta Hilal sedai muyi musu fatan alkairi.


Soomeey amarya Allah yabaku zaman lpy dake da angonki Hilal banda fadan da aka sabadai😜😜😜😜😜Bangaran Faulat kuwa tadau alkawarin seta auri khalifa kome ze faru.


Faulat nagani gabam wani kasurgumin boka bashida kyan gani ma ko kaya babu a jikinsa tsirara yake haihuwar uwarsa ita kanta daka kalleta kasan `kankaninsa takeji Amman dayake zuciyar ta, tamutu da mugunta da zalinci yasa ta daure..


Ya kalleta yace "ina jinki mekikeso ayiwa yarinyar."? Tace "boka kawai sonake asamishi tsanar yarinyar fiya dakomai yaji yatsaneta bayasan ganinta duka yan uwansa asa mishi tsanar su sannan kasa mishi tsananin sona a zuciyar shi yaji bawacce yake kauna seni." Boka yace "indai wannanne karki damu anyi angama zan baki turare kitabbatar kinfesashi yajikanshin a jikinki idan yaji shikkenan komai yayi daidai yazama naki Amman da sharadi idan har kika gama amfani da turaren toh karki yarda kolbar dan idan har kolbar ta fashe toh atake agurin asirin ze karye dan haka kikiyaye baruwana nagaya miki sharadin kinjini dai ko."? Faulat tace "eh boka naji kuma zan kiyaye".


Haka boka yamika mata kolban turaren ta diremasa makudan kudi tatafi abinta tana tunanin yanda zataga khalifa..


Ummi da kausar ma nasu makircin suke sosuke kawai khalifa ya tozarta Khameeni ya auri kausar Amman dai duk abanza suke tunda besan sunayiba kuma haryanzu basusan Khameeni cikin ta nanan bezubeba..Bayan sati 3 har anyi bikin Bashir da matarsa salma sedai San barka.Faulat yau take daniyar zuwa gurin khalifa tagama shiryawa abinta ko zuly bata sanarwaba tafice ba inda ta nufa se office din khalifa batasha wahalaba ma'aikatan suka barta tashiga tana zuwa bakin office din nashi ta tsaya taciro kolban turaren ta fesa sannan ta bude kofan tashiga. 


Khalifa nazaune kan kujeran office din nashi yaji shigowar mutun yana dago kansa waze gani Faulat ce tsaye akansa tana masa murmushi a fusace zemata magana Amman wani irin kamshine yadaki hancinsa Wanda yasashi lumshe ido gaba daya yakasaimata masifar dayai niyar yimata..


Yaji wani irin mugun Santa yasoki zuciyar shi lokaci da'ya yaji duk duniya ba wacce yake so kamar  ta gaba daya yakasai mata masifar dayayi niyya..


Faulat ganin haka yasa ta tako gabanshi tace "ina matukar kaunarka swty na." Shikuwa khalifa murmushi kawai yake mata haka dai faulat taita zubamai kalamai shima yana mayar  mata da martani..wannan kenan.Haka rayuwa taita tafiya khalifa ya tasani Khameeni bayasan ganinta gaba da'ya yadenacin abincinta maganama yadenai mata bayasan ganinta..


Khameeni tashiga damuwa sosai kamar me Amman kullun tanakai kukanta gurin Allah madaukakin sarki..


Hatta iyayensa faulat tarabashi dasu dakowa nasa ita kadaice acikin zuciyar khalifa yanzu duk abinda tace masa shiza'ayi komenene..Bangaran Ummi kuwa kwance take kan bed tarame tayi baki kamar ba itaba yan zun haka gudawane ajikinta tayi a kwance sedai masu aiki sutemaka su wanke mata sabida Allah kausar kuwa bama ta kulata idan tafice se dare take dawowa gaba da'ya abin  duniya ya ishi Ummi gashi Abbah yadade  baya kasarma gaba da'ya..


Bayan wata 4 


Next page insha Allah zan gama book dinnan Comments and share please🙏


đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž

    *A SANADIN MARAICI*

đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒ·đŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒžđŸŒž


    Story and writing

                By

        Rufaida(Rufeey)


*MARUBUCIYAR*


*KAUNA CE KO KIYAYYA*

*BANFARGABA*

*Na fada tarkon sonshi*


      *And now*

      *A SANADIN MARAICI**🌍MANAZARTA*

*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*

      *M. W. A* 


```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.đŸ€™đŸ»```

https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa

____________________________________


*Wannan labarin kirkirarren labarine banyi dan wata ko wani ba Wanda yaga labarin yazo dai dai danasa toh akasine ban yarda a chanzamin labari ba Wanda ya chanzamin ban yafeba.*


*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*


🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚


PAGE 150↪️160


Bayan wata 4 

Abu buwa dadama sun faru masu dadi da akasin haka ciki kuwa harda haihuwar da Khameeni tayi tahaifi yaranta na miji kyakyawa dashi mekama da ubansa ansama yaran sunan mahaifin Khameeni wato ABBAS amman suna kiransa da ANNUR. 


Khalifa baya wani kula da yaran sosai yanzu Khameeni bata damuwa da abinda khalifa kemata karatunta kawai take tana kula da yaranta..


Soomeey ma nanan da karamin cikinta.


Salma ma matar Bashir itama da nata cikin.


Sedai fatan sauka lapiya. Wannan kenan


Kausar da Ummi rayuwa ta juya musu baya dan kuwa itama kausar yanzu bata da lapiya anrasa meke damunsu gashi duk masu aikin gidan sun gudu gashi haryanzu Abbah bedawoba sosai rayuwa tayi musu kunci.Abbah nahango yana shigowa parlour gidan yanata sallama yaji shiru.


Dama megadi yasan za'ayi haka shiyasa ya biyoshi ciki yace "ai Alhaji kausar da Hajiyan suna ciki ai sundade basu da lapiya kuma duk ma'aikatan gidan sun gudu nikadai narage a gidan." Abbah yace "subhanallah bari nashiga ciki se muje asibiti." Abbah yanufi dakin Ummi.


Kwance take tayi mugun baki ta rame kamar me shikansa Abbah daya ganta seda yatsora tsabar yanda tadawo haka yakarasa gurin datake tana ganinshi tafashe da kuka shi kuma yadakkota yafito da ita yasa a mota sannan yanufo dakin kausar.


Itamadai kwance take tayi baki ta rame gawani wari dayake fita daga gabanta ga tsutsosi se yawo suke a jikinta Abbah yace "subhanallahi meyake damunki haka kausar."? Itadai kausar batamasan anayi ba  dan kuwa ta sume haka Abbah yadauketa yasa amota itama sannan suka nufi asibiti suna zuwa aka karbesu.


Anyi gwaje gwaje saka mako yafito Ummi da Kausar na dauke da cutar kanjamau wato HIV kuma kausar mahaifarta ta rube sedai acireta gaba da'ya.


Ai ana fada Ummi ta zunduma wani uban iwu sekuwa tafara soshe soshe tana dariya tana fadar abubuwan dasuka shuka tafara cire kayan jikinta nan danan aka daureta aka sata a wani daki aka kulle dan kuwa Ummi hauka take tuburan.


Abbah hankalinsa yatashi sosai haka yasa shima likita ya dubasa kuma alhamdulillah baya dauke da cutar.


Sosai kausar tayi nadama gashi bata sami biyan bukataba gashi yanda rayuwar ta takasance.


Bayan sati da'ya anyiwa kausar aiki ancire mahaifarta sosai tayi nadamar abinda ta aikata a rayuwar ta.


Ita kuwa Ummi tana gidan mahaukata a daure.Ban garan khalifa kuwa yau yazowa da su Daddy maganar aurenshi da Faulat Daddy yace shibeyarda bada ya wunsaba dayake khalifa bayin kansa bane yasa yace eh shiyayarda.


Dan haka sati mezuwa za'a daura auren khalifa da Faulat.


Khameeni ma tasan da maganar auren da khalifa zeyi tayi masa fatan alkairi.


Faulat ce da kawarta zuly, zuly ta kalli Faulat tace "wai nikuwa kawata taya kika shawo kan khalifa harya amince da auren ki."? Faulat tace "ooo namata ban gaya miki yanda nayiba ai ingaya miki gurin wani boka naje yamin aiki yabani wani turare barima kiga turaren." Haka tadauko turaren tace "kinga turaren kuma bokan yace idan kolban turaren yafashe asirin ze karye shiyasa nake boyeta." Zuly tace "chab gaskiya ne kawata ai zamusha biki kam." A zuciyar zuly kuwa tadau alkawarin seta fasa kolbar dan kuwa bazata bari rayuwar khalifa da matarshi ta tarwatseba dan kuwa ita yanzu Allah yashiryeta tadena karuwanci kuma tadau alkawarin tana wargaza shirin Faulat zata koma garinsu tanemi yafiyar iyayenta.

Wannan kenanAna gobe za'a daura auren khalifa da Faulat zuly tafito da kolbar nan taje gaban Faulat tadagata sama tasaketa jikake tas tas kolban turaren yatarwatse a kasa a zabure Faulat tamike tace "zuly baki da hankali."? "Wayyo Allah na zuly kin kasheni Allah ya isa tsakanina dake." Zuly ta fashi da dariya tace "ai dama nadau  alkawarin tarwatsa shirinki muguwa kawai insha Allah sekinga karshenki." Tana gama fadar haka tashiga tajawo akwatinta tafice daga gidan gidan su khalifa tanufa tana zuwa tashiga part dinsu Mami tashiga tana shiga ta gaida Mami da Daddy sannan tafada musu duk abinda Faulat tayi mami da kanta taje takira Khameeni da khalifa.


Khalifa dama shi tun dazu yakejinshi wani iri kansa se sarawa yake suna shiga zuly ta maimaita abinda Faulat tayi tana gama fada khalifa yafadi a sume Bayan yafarfadone ya nemi yafiyar su suka yafemai.


Ita kuma zuly tayi musu sallama ta tati..


Faulat kuwa zuly nafita itama ta fita a motarta tanufi gurin boka tana cikin tafiya amotarta wata katuwar tirela tazo tabi takanta.


Da sauri mutanen gurin gurin sukayo gurin da abin yafaru ai motar Faulat tayi raga raga ita kanta Faulat din ta dagargaje abin ba kyan gani Faulat ankoma ga Allah.


Allah kaimana kyakyawan karshe Ameen Bayan shekara biyar 5 


Soomeey da Hilal yaransu 2 mace da namiji Haneefa da Haneef Allah yarayaku.


Bashir da matarshi salma suma yaran su 2 duk mata Muneeba da Mubeena Allah yarayaku..


Sosai abotarsu tayi karko sosai gashi kota ina arziki ya zauna musu duk su ukun3 matansuma haka suke zuminci sosai duk kanninsu sun gama karatu aikine dai mazajen nasu suka hanasu.


Khameeni da khalifa rayuwa suke medadin gaske abin  se Wanda ya gani yanzu yaransu 3 Bayan ANNUR takara haihuwar yan biyu duka mata Ammarah da Amrah Allah yarayaku.


Sosai suke rayuwar farin ciki khalifa arziki ya bunkasa sosai sedai godiyar Allah..


Alhamdulillah

Alhamdulillah

Alhamdulillah


Tammat bi hamdullah duka duka anan nakawo karshen labarin nan mesuna A SANADIN MARAICI duk abinda nafad`a daidai Allah yabani ladansa abinda nayi kuskure aciki Allah yayafemin.


Allah nagodemaka daka bani damar kammala wannan labarin nawa.


Toh masoyana semun hadu a Saban book dina me  suna AMAYA DA AMAN 

Da kuma ITADIN ALKAIRICE (A RAYUWAR SA)

Muhadu a wayannan  kayatattaun labaran nawa kada kubari a Baku labari💃💃💃💃Comments and share please🙏


By Rufaida✍️0 Response to "A SANADIN MARAICI Hausa Novel"

Post a Comment