LABARI MAI DAƊI: Masu Neman Tallafin NASSCO Na ₦75,000 Su Shirya Karɓar Alert Nan Ba Da Jimawa Ba
Duk wanda ya sami saƙon tes (SMS) daga hukumar NASSCO ta layin wayarsa, ana sanar da shi cewa ya jira shigowar kuɗi (Credit Alert) a cikin wannan makon ko kuma mako mai zuwa.
Mene ne NASSCO?
Hukumar NASSCO (National Social Safety Nets Coordinating Office), hukuma ce a ƙarƙashin Gwamnatin Tarayya wacce ke kula da raba tallafi ga gidajen 'yan ƙasa marasa ƙarfi. Waɗannan mutane su ne waɗanda bayanan su suke cikin Rajistar Al'umma ta Ƙasa, wato National Social Register (NSR).
Tsarin Biyan Tallafin ₦75,000 na 'Renewed Hope'
A makon da ya gabata, hukumar NASSCO ta umarci wakilanta na jihohi (State Representatives) da su tura bayanan duk mutanen da aka tantance domin ci gaba da ba su tallafin Renewed Hope Cash Transfer. Wannan tallafin yana gudana ne kamar yadda aka yi a shirye-shiryen RRR da kuma Conditional Cash Transfer (CCT) na baya.
Sabon Tsarin Buɗe Asusun Banki (UBA Account)
Domin kauce wa cunkoso da dogon layi a wuraren tantancewa, hukumar NASSCO ta fito da wani sabon tsari mai sauƙi. A yanzu, hukumar tana buɗe wa mutane asusun banki kai tsaye da bankin UBA domin tura musu tallafin ₦75,000 ɗin su ba tare da wani jinkiri ba.
Wannan ne ya sa kuke ganin saƙon tes yana shigowa wayoyinku mai ɗauke da lambar asusun banki (Account Number).
Gargaɗi Zuwa Ga Jama'a:
Idan ka sami irin wannan saƙon, kada ka goge shi! Sannan kada ka ɗauka cewa na masu damfara (scammers) ne. Wannan saƙo ne na hukuma wanda ke tabbatar maka da cewa asusunka ya buɗu kuma ana sa ran za a tura maka kuɗin nan ba da jimawa ba.
Muna ƙarfafa ku da ku yaɗa wannan bayani (Share) zuwa ga wasu domin su amfana kuma su daina goge saƙonnin su saboda rashin fahimta.
Domin samun sabbin bayanai kan tallafin Gwamnatin Tarayya da guraben aiki, ku ci gaba da bibiyar shafinmu na Haskenews.com.ng.
0 Response to "LABARI MAI DAƊI: Masu Neman Tallafin NASSCO Na ₦75,000 Su Shirya Karɓar Alert Nan Ba Da Jimawa Ba"
Post a Comment