-->

FOLLOW HASKE NEWS WHATSAPP CHANNEL

FOLLOW HASKE NEWS WHATSAPP CHANNEL
To continue receiving our daily updates on news, jobs, and opportunities, please follow our new channel above, Thank you for your continued support Haskenews Media & Publishing Services
Gwamnatin Tarayya Ta Sake Buɗe Rukunin na Biyu na Shirin TVET – Ga Yadda Zaku Zaɓi Cibiyar Horarwarku

Gwamnatin Tarayya Ta Sake Buɗe Rukunin na Biyu na Shirin TVET – Ga Yadda Zaku Zaɓi Cibiyar Horarwarku

Gwamnatin Tarayya Ta Sake Buɗe Rukunin na Biyu na Shirin TVET – Ga Yadda Zaku Zaɓi Cibiyar Horarwarku



Gwamnatin Tarayya ta sanar da sake buɗe rukunin na biyu (Cohort/Batch) na shirin TVET, wanda hakan wata babbar dama ce ga matasa a faɗin ƙasar nan domin koyon sana'o'in hannu tare da samun tallafin alawus na naira ₦22,500 kowane wata.

Idan kuna da sha'awar cike wannan tallafi, ko kuma kuna fuskantar ƙalubale wajen zaɓar cibiyar horarwa (Training Center), wannan bayani zai taimaka muku daki-daki kan yadda zaku kammala rajistarku cikin nasara.

Game da Shirin TVET:

Shirin TVET wani babban mataki ne na Gwamnatin Tarayya da aka tsara domin ƙarfafa matasan Najeriya ta hanyar koya musu sana'o'in dogaro da kai da kuma ba su tallafin kuɗi a lokacin horon.

Matakan Zaɓar Cibiyar Horarwa:

  1. Shiga Shafin Yanar Gizo:
    Ziyarci babban shafin TVET a nan: https://www.tvet.education.gov.ng/

  2. Danna Maballin "Apply Now":
    Yayin da shafin ya buɗe, taƙaita ƙasa ka nemo inda aka rubuta “Apply Now” sannan ka danna.

  3. Yin Rajista ko Shiga (Login):
    Idan ka riga ka yi rajista a baya, shiga (Login) kawai zaka yi. Idan kuma sabon mai nema ne, sai ka buɗe sabon asusu (Register).

  4. Amincewa da Ƙa’idoji (Terms & Conditions):
    Wani sako zai bayyana mai ɗauke da ƙa’idojin shirin. Taƙaita ƙasa ka danna “I Agree”.

  5. Cike Bayanan Kai (Personal Details):
    Shigar da adireshinka na yanzu, Jiha (State), Ƙaramar Hukuma (LGA), imel, da lambar wayarka, sannan ka danna “Proceed”.

  6. Zaɓar Sana’a (Skill):
    Danna “Select Skill” domin ganin jerin sana'o'in da ake koyarwa. Zaɓi sana'ar da kake so, sannan ka danna “Proceed”. Lura: Tsawon lokacin horo yana tsakanin watanni 6 zuwa 12 dangane da sana'ar da ka zaɓa.

  7. Amsa Tambayoyin Bincike (Quick Survey):
    Zaka amsa tambayoyi guda uku game da sana'ar da ka zaɓa:

    • Gwanintarka (Proficiency): Zaɓi “Average”.

    • Yawan yin sana'ar (Frequency): Zaɓi “Occasionally”.

    • Dalilin koyon sana'ar (Motivation): Zaɓi “To uplift my skills” ko “To scale up my business”.

    • Daga nan ka danna “Proceed”.

Yadda Ake Zaɓar Cibiyar Horo (Inda Matsalar Take):

Wannan matakin yana da ɗan wahala saboda wasu cibiyoyin ba sa bayyana nan take. Idan ka tarar babu cibiyar horo a wurinka, ka gwada sauya sana'ar da ka zaɓa, ko ka sauya Jiha ko Ƙaramar Hukuma akai-akai har sai ka ga cibiyoyin da suke buɗe sun bayyana. A halin yanzu, akwai cibiyoyin da suke buɗe a jihohin Lagos, Zamfara, da Borno.

Idan kun bi waɗannan matakan daki-daki, zaku iya samun nasarar zaɓar cibiyar horo da ta dace da sana'ar da kuke son koya.

Kada ku karaya, ku ci gaba da gwada hanyoyi daban-daban har sai kun samu gurbi. Shirin TVET dama ce mai kyau ta samun ilimin sana'a da kuma tallafin kuɗi a lokaci ɗaya.

0 Response to "Gwamnatin Tarayya Ta Sake Buɗe Rukunin na Biyu na Shirin TVET – Ga Yadda Zaku Zaɓi Cibiyar Horarwarku"

Post a Comment