Yadda Za Ku Cire Kuɗin Tallafin Renewed Hope (CCT) Ga Waɗanda Suka Samu Saƙon Buɗe Asusu
YADDA ZA KU CIRE KUƊIN TALLAFIN RENEWED HOPE (CCT) GA WAƊANDA SUKA SAMU SAƘON BUƊE ASUSU
Shirin Renewed Hope Conditional Cash Transfer (CCT) wani mataki ne na Gwamnatin Tarayya domin tallafa wa marasa ƙarfi da nufin rage raɗaɗin talauci. Ana tura wannan tallafi ne kai-tsaye zuwa ga asusun waɗanda aka zaɓa su ci gajiyar shirin.
Idan kun samu saƙon buɗe asusu, ga matakan da za ku bi domin cire kuɗinku:
Sauke Manhaja: Ku shiga shagon Play Store a wayarku, sannan ku nemo tare da sauke manhajar FortisPay.
Buɗe Manhajar: Bayan kun gama saukewa (installing), ku buɗe manhajar.
Shigar da Lamba: Ku saka lambar wayar da kuka yi amfani da ita wajen yin rajista (lambar da kuka samu saƙon a kai).
Tabbatarwa (OTP): Za a turo muku da lambar sirri ta takaitaccen saƙo (OTP). Ku shigar da ita domin tabbatar da mallakar lambar.
Lambar NIN: Bayan kun wuce matakin farko, za a buƙaci ku shigar da lambar ku ta ɗan ƙasa (NIN).
Tantance Fuska: Za ku yi abin da ake kira Face Verification (ɗaukar hoton fuska kai-tsaye domin tantancewa).
Nau'in Asusu: Idan aka kawo muku zaɓin nau'in asusu (Account Type), ku zaɓi "Personal Account".
Lambar Sirri (PIN): Daga nan, sai ku ƙirƙiri lambar sirri (PIN) mai lamba huɗu wadda za ku riƙa amfani da ita wajen tura kuɗi.
Duba Ma'adana: Bayan kun kammala waɗannan matakan, za ku ga adadin kuɗin tallafinku (misali ₦75,000) a cikin ma'adanar ku (Balance).
Tura Kuɗi: Daga ƙarshe, sai ku danna "Transfer" domin tura kuɗin zuwa asusun bankinku na kashin kanku (kamar OPay, ko kowane bankin da kuke amfani da shi).
Jan Kunne:
Kada ku bayyana lambar sirrinku (PIN) ko lambar OTP ga kowa. Ma'aikatan banki ko na gwamnati ba za su taɓa tambayar ku waɗannan bayanan ba.
0 Response to "Yadda Za Ku Cire Kuɗin Tallafin Renewed Hope (CCT) Ga Waɗanda Suka Samu Saƙon Buɗe Asusu"
Post a Comment