-->

FOLLOW HASKE NEWS WHATSAPP CHANNEL

FOLLOW HASKE NEWS WHATSAPP CHANNEL
To continue receiving our daily updates on news, jobs, and opportunities, please follow our new channel above, Thank you for your continued support Haskenews Media & Publishing Services
Mercy Corps Na Neman Ma'aikatan Tattara Bayanai (Enumerators) Na Kwana 10 A Abuja – Albashi ₦20,000 Kullum

Mercy Corps Na Neman Ma'aikatan Tattara Bayanai (Enumerators) Na Kwana 10 A Abuja – Albashi ₦20,000 Kullum

Mercy Corps Na Neman Ma'aikatan Tattara Bayanai (Enumerators) Na Kwana 10 A Abuja – Albashi ₦20,000 Kullum

Shahararriyar kungiyar agaji ta duniya, Mercy Corps, ta sanar da gurbinsu na aikin tattara bayanai na wucin gadi (Enumerators) a karkashin shirin samar da wutar lantarki a karkara (CORE Project).

Wannan babban zarafi ne ga matasan da ke zaune a Abuja, musamman masu sha'awar aikin jinkai da tattara bayanai ta amfani da na'urorin zamani.

Bayanai Game Da Aikin:

  • Matsayi: Enumerator (Mai tattara bayanai).

  • Wurin Aiki: Rubochi da Kaida, Abuja (FCT).

  • Tsawon Aiki: Kwana goma (10) ne kacal (Kwana 1 na horo, kwana 9 na aiki).

  • Albashi: Za a biya ₦20,000 a kowane rana guda (Jimillar kudi ₦180,000 na tsawon kwanakin aikin).

Wadanda Suka Cancanta Su Nema:

  1. Ilimi: Akalla kana da Degree (B.Sc), HND, OND, ko NCE.

  2. Kwarewa: Sanin yadda ake amfani da wayar Android wajen tattara bayanai (Mobile data collection).

  3. Harshe: Dole ka iya magana da rubutu a harshen Turanci da kuma Hausa (ko wani yaren yankin) sosai.

  4. Sadarwa: Iya hulda da mutane cikin girmamawa da sanin al'adun karkara.

Ayyukan Da Za A Yi:

  • Haltar horo na kwana daya.

  • Ziyartar gidaje a Rubochi da Kaida domin yin hira da mutane kusan 20 a kowace rana.

  • Dora bayanan da aka tattara a manhajar da za a bayar a kullum.

  • Tabbatar da cewa bayanan da aka tattara gaskiya ne kuma ingantattu.

Yadda Za A Cike (Method of Application):
Ga masu sha'awar wannan aiki kuma suke zaune a Abuja, za su iya neman wannan gurbi ta hanyar shafin daukar ma'aikata na Mercy Corps ta amfani da lambar bincike (Requisition Number: UNBNG006560).

👉 Danna Nan Domin Neman Aikin:

https://recruiting2.ultipro.com/MER1024MERCY/JobBoard/444c1b88-2406-42f4-9273-a99cc3bb34e2/OpportunityDetail?opportunityId=8b7ec495-19e4-43ac-bd60-6f02b1cb0bb0&utm&fbclid=IwVERDUAQtw_lleHRuA2FlbQIxMABzcnRjBmFwcF9pZAwzNTA2ODU1MzE3MjgAAR7h7dy1lsGPUJODie9TOdOrMjw0FkyHUFEB6t2PlYOq57CbK1KBVIo55F1UXA_aem_MHNaV5qSqOMdyFQ9-Ffs8A

https://jobs.jobvite.com/mercycorps/jobs
(Zaka iya neman aikin ta hanyar rubuta 'Enumerator Abuja' a wurin search na shafin).

Muhimmi:
Wannan aiki ne na dan takaitaccen lokaci, kuma za a biya kudin ne bayan an kammala dukkan aikin da kuma tabbatar da ingancin bayanan da aka tattara.

Kada ku bari wannan dama ta wuce ku, hanzarta cike naku yanzu!



0 Response to "Mercy Corps Na Neman Ma'aikatan Tattara Bayanai (Enumerators) Na Kwana 10 A Abuja – Albashi ₦20,000 Kullum"

Post a Comment