MUHIMMIYAR SANARWA: SHIRIN RENEWED HOPE-WAVE 774
Mutane da dama sun riga sun sami saƙon shirin Renewed Hope-WAVE 774 a adiresoshin imel (email) ɗinsu. Ana kira ga duk waɗanda suka samu saƙon su tabbatar sun halarci taron kai-tsaye (Live Session) domin fahimtar manufar shirin da yadda yake gudana.
Lura: Nan ba da jimawa ba za a rufe damar yin rajista.
Game da Shirin RH-WAVE 774
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da shirin Renewed Hope Women Agro-Value Expansion Programme (RH-WAVE 774) domin ƙarfafa mata masu harkar noma da kasuwancin amfanin gona a dukkanin ƙananan hukumomi 774 na Najeriya.
An ƙaddamar da shirin ne a watan Yunin 2025 ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a matsayin wani ɓangare na Ajandar Renewed Hope wadda ta mayar da hankali kan:
Ƙarfafa mata ta fannin tattalin arziki.
Samar da wadataccen abinci a ƙasa.
Bunƙasa tattalin arziki mai haɗa kowa da kowa.
Abubuwan da RH-WAVE 774 ke Bayarwa:
Tallafin Kuɗi: Tallafin kuɗi har zuwa ₦1,000,000 ga kowace mace da ta cancanta.
Bunƙasa Kasuwanci: Tallafi na musamman domin faɗaɗa kasuwancin noma.
Hanyoyin Kasuwa: Samar da sauƙin kai amfanin gona zuwa kasuwanni da faɗaɗa darajar amfanin gona.
Tallafi ga Rukunoni: Tallafin ya haɗa da manoma mata, masu sarrafa abinci, ƙungiyoyin noma, da ƙananan 'yan kasuwa (SMEs).
Manufar Shirin
Wannan shiri zai taimaka wa mata su tashi daga noma na rufin asiri zuwa zama manyan 'yan kasuwar noma, masu sarrafa kayayyaki, da masu fitar da kaya zuwa ƙasashen waje.
Su Wane Ne Ya Kamata Su Nema?
Shirin a buɗe yake ga mata a dukkan ƙananan hukumomi 774 na faɗin ƙasar nan.
Idan ke manomiya ce, ko kina harkar sarrafa abinci, ko kina cikin kowane fanni na harkar noma — wannan dama ce taki!
Kada a barki a baya!
Ku sanar da 'yan'uwa mata, iyaye, abokan arziki, da duk wadda kuka sani tana harkar noma ko kasuwancin abinci (agribusiness).
0 Response to "Kada Ku Bari A Barku A Baya: Abin Da Masu Neman Tallafin RH-WAVE 774 Ya Kamata Su Yi Yanzu"
Post a Comment