Gidauniyar Life at Best Development Initiative (LABDI), wadda take sahun gaba wajen tallafawa kananan yara, mata, da gidajen da rikici ko annoba suka daidaita, ta sanar da bude shafin daukar sabbin ma'aikata kwararru a Najeriya.
Wannan gidauniya, wadda aka kafa tun lokacin da rikicin Boko Haram ya fara tsananta a shekarar 2009, tana fadada ayyukanta a jihohin Borno da Yobe domin samar da abinci, matsuguni, ilimi, da kariya ga mabukata.
Wadanda Za Su Iya Nema:
Ana neman mutanen da ke da wadannan matakan karatu dangane da aikin da mutum ya nema:
ND / NCE
HND / Bachelors Degree
Masters Degree
Guraben Ayyukan Da Aka Bude:
Akwai guraben aiki masu tarin yawa a matakin jami'ai (Officers) da mataimaka (Assistants), ciki har da:
Matakin Jami'ai (Officers & Focal Persons):
Nutrition Officer
Accountability Officer
Finance Officer
Media and Information Officer
MEAL Officer / GBV Officer
Child Protection Officer
Safety and Security Officer
Nutrition and Health Technical Focal Person
Matakin Mataimaka (Assistants):
GBV Assistant / Child Protection Assistant
CVA Assistant / HR Assistant
MEAL Assistant / Nutrition Assistant
Procurement Assistant / Logistics Assistant
Media and Information Assistant
Ranar Rufe Shafin:
Dole ne duk mai sha’awar wadannan ayyuka ya cike fom din sa kafin ranar 27 ga watan Maris, 2026.
Yadda Za A Cike (Method of Application):
Idan kana da sha'awar wannan aiki kuma ka cika sharuddan da ake bukata, zaka iya cike fom din neman aikin kai tsaye ta wannan mahadar (link) dake kasa:
Danna Nan Domin Cikewa: https://docs.google.com/forms/d/e/1FAIpQLSfHcjEVqIE8nPtd37RzPvYSu-ydvMyYzOzu9dpJ5QV0LCuSMg/viewform
Muhimmi:
Wannan babban zarafi ne ga wadanda ke da kishin aikin jinkai a Arewa maso Gabas. Ku hanzarta cike naku yanzu sannan ku raba wannan labari ga wasu domin su ma su amfana.
0 Response to "Gidauniyar LABDI Ta Bude Shafin Daukar Sabbin Ma'aikata MasuSSCE, ND, NCE, HND, Da Digiri [Akwai Albashi Mai Tsoka]"
Post a Comment