Babban labari ga kwararrun matasa masu neman aiki a fannin jinkai (NGO)! Gidauniyar GOALPrime Organization Nigeria (GPON), wadda take sahun gaba wajen taimakawa yara, matasa, da masu kula da su, ta sanar da bude shafin daukar sabbin ma'aikata na shekarar 2026.
Gidauniyar GPON tana gudanar da ayyukanta a jihohi da dama a Najeriya, amma a halin yanzu tana neman ma'aikata ne na musamman da za su yi aiki a yankunan Dikwa, Ngala, da Kala-Balge da ke Jihar Borno.
Guraben Ayyukan Da Aka Bude:
Ana neman kwararru domin cike wadannan matsayoyi:
WASH Officer (Ngala da Kala-Balge)
Nutrition Officer (Dikwa da Ngala)
Project Assistant (Kala-Balge, Ngala, da Dikwa)
Wadanda Za Su Iya Nema (Requirements):
Ilimi: Masu Degree (BSc), HND, OND, ko NCE.
Kwarewa: Ana bukatar mutanen da ke da kwarewar aiki ta shekaru 1 zuwa 5.
Takardu: Dole ne ka kasance kana da takardun karatu (Certificates) da kuma takardar shaidar gogewa (CV da Cover Letter).
Yadda Za A Cike (Method of Application):
Idan kana da sha’awar yin aiki a daya daga cikin wadannan wuraren kuma ka cika sharuddan, zaka iya cike fom din neman aikin kai tsaye ta wannan mahadar (link) dake kasa:
👉 Danna Nan Domin Cikewa: https://docs.google.com/forms/d/e/1FAIpQLSeiuLQ5_6ESn-xbYNruXvv8mvqNxGe8OeyMWaqpV1X5HlbgBg/viewform
Muhimmi:
Za a bukaci ka dora (upload) takardun karatunka a matsayin takarda guda (single document).
Haka zalika, za a bukaci ka hada CV da Cover Letter dinka waje daya a matsayin PDF kafin ka dora su.
Kada ku bari wannan dama ta wuce ku, hanzarta cike naku yanzu sannan ku raba wannan labari ga wasu kwararrun domin su ma su amfana.
0 Response to "Gidauniyar GOALPrime Organization Nigeria (GPON) Ta Bude Guraben Aiki ga Masu OND, NCE, HND Da Digiri"
Post a Comment