Yadda Za Ku Cika Sabon Shirin Tallafin Rance na Gwamnatin Tarayya na FarmerMoni 2026
Friday, February 13, 2026
Comment
Yadda Za Ku Cika Sabon Shirin Tallafin Rance na Gwamnatin Tarayya na FarmerMoni 2026
Gwamnatin Tarayya ta sake buɗe shirin tallafin rance na FarmerMoni 2025 a ƙarƙashin shirin GEEP, wanda ke bai wa ƙananan manoma damar samun rance ba tare da biyan kuɗin ruwa ba. Wannan shiri na cikin National Social Investment Programme Agency (NSIPA) domin tallafawa tattalin arziƙi da samar da ayyukan yi ga ‘yan Najeriya.
Menene GEEP?
- GEEP na ɗaya daga cikin shirye-shiryen NSIPA.
- Shirin na bayar da tallafin kuɗi zuwa ga:
- FarmerMoni (manoma)
- TraderMoni (ʻyan kasuwa)
- MarketMoni (kasuwanni)
- Manufarsa ita ce bunƙasa tattalin arziƙi da ƙarfafa ƙananan sana’o’i.
Sabon FarmerMoni 2025
- Bashi mara ruwa har zuwa ₦300,000 ga ƙananan manoma.
- Ba a buƙatar jingina (collateral).
- Ana bayar da shi ne bayan kammala cikakken rajista.
Waɗanda Shirin Ya Mayar da Hankali A Kansu
- Mata
- Matasa
- Masu buƙata ta musamman da sauran rukunin marasa ƙarfi.
Yadda Za Ka Cika Shirin FarmerMoni
- Ziyarci shafin yanar gizo na hukuma:
https://geep.nsipa.gov.ng/ - Zaɓi FarmerMoni a shafin.
- Zaɓi nau’in rajista:
- Individual (kai kaɗai)
- Group (ƙungiya ko haɗin gwiwa)
- Cika bayanai kamar:
- Sunanka
- Lambar asusun banki
- Lambar waya
- Sauran bayanai da ake buƙata
- Upload ɗin takardun kamar:
- NIN slip
- Sauran takardun da ake buƙata
0 Response to "Yadda Za Ku Cika Sabon Shirin Tallafin Rance na Gwamnatin Tarayya na FarmerMoni 2026"
Post a Comment