Aikin NGO: Cibiyar Crest Research and Development Institute (CRADI Ltd GTE) na Daukar Masu Tattara Bayanai (Data Collectors) Fadin Najeriya
Aikin NGO: Cibiyar Crest Research and Development Institute (CRADI Ltd GTE) na Daukar Masu Tattara Bayanai (Data Collectors) Fadin Najeriya
HaskeNews (www.haskenews.com.ng) na sanar da daukacin masu sha’awar aiki da suka cancanta da su nemi wannan dama ta aiki da Crest Research and Development Institute (CRADI Ltd GTE)
Game da Shirin
Cibiyar CRADI tana gudanar da bincike kan ’Yancin Addini da Imani (Freedom of Religion and Belief) a duk fadin Najeriya. Domin nasarar wannan bincike, ana neman Masu Tattara Bayanai (Data Collectors) guda biyu a kowace jiha ta tarayya.
Wuraren Aiki
Aikin zai gudana a dukkan jihohin Najeriya da suka hada da: Abia, Abuja (FCT), Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Enugu, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Plateau, Rivers, Sokoto, Taraba, Yobe da Zamfara.
Sharuddan Cancanta
Akalla shekaru biyu na kwarewa a aikin tattara bayanai ko bincike a fili.
Dole ne mai nema ya kasance mai gaskiya da rikon amana.
Ya kasance mai iya bin ka’idojin bincike da kiyaye sirri.
Ayyukan da Za a Yi
Halartar taron horaswa kafin fara aiki.
Gudanar da tambayoyi da cike fom din bincike yadda ya kamata.
Tura sahihan bayanai cikin lokaci.
Bayar da rahoton duk wata matsala da aka fuskanta a fili.
Tsawon Lokacin Aiki
Taron horaswa: Laraba, 18 ga Fabrairu 2026
Aikin fili: Alhamis zuwa Asabar, 19–21 ga Fabrairu 2026
Masu nema dole su kasance a shirye su halarta dukkan kwanakin da aka tsara.
Ranar Rufe Aikace-aikace
Karfe 6:00 na yamma, Talata 17 ga Fabrairu 2026.
Yadda Za a Nema
Masu sha’awa su cike fom din neman aiki ta wannan mahaɗin:
https://docs.google.com/forms/d/e/1FAIpQLSezJuXu61FF2J8ooJgrWVqV4AG1hp46M2xlu9yjAM4bsPM_Ww/viewform
Wannan babbar dama ce ga masu neman aiki da ke da kwarewa a harkar bincike da tattara bayanai su ba da gudummawa wajen samar da sahihan bayanai domin cigaban kasa.
Allah Ya ba da sa’a.
0 Response to "Aikin NGO: Cibiyar Crest Research and Development Institute (CRADI Ltd GTE) na Daukar Masu Tattara Bayanai (Data Collectors) Fadin Najeriya"
Post a Comment