Sanarwa ta Musamman:
Ga duk masu bukatar mallakar takardar shaidar kasuwanci ta CAC (Corporate Affairs Commission) kyauta ba tare da biyan ko kwabo ba, wannan dama ce ta musamman da hukumar SMEDAN ta samar.
Domin samun nasarar yin wannan rajista ba tare da kuskure ba, akwai wasu muhimman abubuwa guda biyu (2) da ya zama dole ku kiyaye:
1. Hoton NIN (National Identification Number)
Yayin da kuke cike wannan rajista, ana bukatar ku dora (upload) hoton NIN Slip dinku ko kuma NIN Card (Plastic).
Sharadi: Dole ne hoton ya kasance a bayyane (very clear). Idan hoton bai fita radau ba, za a iya kin amfar bukatarku (rejection).
2. Date of Commencement (Ranar Fara Kasuwanci)
A wajen cike bayanan mai kowa da kowa (Proprietor Details), akwai sashin da aka rubuta Date of Commencement.
Yadda zaku cike: Ku saka kwanan watan (Date) da ranar da kuke yin wannan rajistar a yanzu. Wannan zai taimaka wajen saurin amincewa da takardarku.
Yadda Zaku Cike?
Kuna iya shiga shafin yanar gizo na SMEDAN kai tsaye ta wannan hanyar:
DANNA NAN DOMIN CIKAWA
Sakon Kira ga Yan Uwa:
Don Allah kada ku tsaya ku kadai kuji wannan labari. Kuyi SHARE wannan sakon zuwa ga wasu yan uwan namu domin kowa ya amfana da wannan damar. Taimakonka zai iya zama dalilin samun nasarar wani.
0 Response to "Yadda Zaku Cike Rajistar CAC Kyauta (Free) Ta Hanyar SMEDAN: Ga Muhimman Abubuwan Lura"
Post a Comment