Yadda Za Ku Nemi Aiki a Cibiyar Tsare-Tsaren Birane ta Najeriya (Nigerian Institute of Town Planners – NITP)
Yadda Za Ku Nemi Aiki a Cibiyar Tsare-Tsaren Birane ta Najeriya (Nigerian Institute of Town Planners – NITP)
Hukumar Nigerian Institute of Town Planners (NITP) ta sanar da bude damar aiki ga duk masu sha’awar neman aiki, ciki har da ma’aikatan cikin gida da na waje.
Ana gayyatar ’yan Najeriya masu cancanta da su nema domin cike guraben ayyuka daban-daban a sassan Gudanarwa, Kudi, Tsare-tsaren Birane (Town Planning), Fasahar Sadarwa (ICT), tsafta da lambu.
Guraben Aikin da Aka Bude Sun Hada da:
Executive Secretary
Town Planning Officer I
Accountant
ICT Officer
Cleaner
Gardener
Abin da Masu Nema Za Su Yi:
Su rubuta takardar neman aiki guda biyu (2)
Su hada da cikakken CV
Su makala kwafin takardun shaidarsu (certificates)
Su sanya dukkan takardun a cikin ambulaf da aka rufe (sealed envelope)
Inda Za A Kai Takardun:
The National Secretary
Nigerian Institute of Town Planners (NITP)
NITP Bawa Bwari House
Plot 2047 Michael Okpara Way
Wuse Zone 5, P.M.B. 7012
Garki, Abuja, FCT
Ranar Rufe Karɓar Aikace-aikace:
Kafin karfe 12:00 na rana, 31 ga Janairu, 2026
Ana shawartar duk masu sha’awa su hanzarta neman aikin kafin ranar rufewa. Wannan dama ce mai kyau ga masu kwarewa da masu neman ci gaban aiki.
Allah Ya bada sa’a.
0 Response to "Yadda Za Ku Nemi Aiki a Cibiyar Tsare-Tsaren Birane ta Najeriya (Nigerian Institute of Town Planners – NITP)"
Post a Comment