Gwamnatin Jihar Sokoto ta sanar da dukkan masu neman aikin gwamnati da suka cike fom a shafin daukar ma’aikata cewa an fara fitar da sunayen wadanda aka tantance (shortlisted)
Gwamnatin Jihar Sokoto ta sanar da dukkan masu neman aikin gwamnati da suka cike fom a shafin daukar ma’aikata cewa an fara fitar da sunayen wadanda aka tantance (shortlisted)
Idan kai ma ka nemi aikin, yanzu haka zaka iya duba sunanka ta yanar gizo cikin sauƙi ta bin matakan da ke ƙasa.
Yadda Za Ka Duba Ko An Tantance Ka
Shiga shafin duba sunaye ta wannan link: https://employment.sokotostate.gov.ng
Ka danna “Check Your Selection Status”.
Ka shigar da Reference Number ɗinka kamar yadda yake a takardar aikace-aikacenka ko CBT slip
(misali: SKO-2025-64475).Ka danna alamar bincike.
Idan an tantance ka, zaka iya fitar da (generate) takardar sanarwa ka kuma buga ta (print).
Me Zai Biyo Bayan Dubawa?
Duk wanda aka tantance zai:
Buga takardar sanarwar da ya fitar daga shafin.
Kai kansa zuwa Ofishin Shugaban Ma’aikatan Jihar Sokoto (Head of Service)
Usman Faruku Secretariat .Zo da wadannan takardu:
Asalin shaidun karatu
Rasidin shafin portal
Wannan takarda tana zama shaida ta sanarwa da gayyata domin karɓar takardar daukar aiki (Appointment Letter)
0 Response to "Gwamnatin Jihar Sokoto ta sanar da dukkan masu neman aikin gwamnati da suka cike fom a shafin daukar ma’aikata cewa an fara fitar da sunayen wadanda aka tantance (shortlisted)"
Post a Comment