Cikakken Bayani Kan Yadda Za Ku Yi Rijista da Samun Takardar Shaidar Kasuwanci ta SMEDAN Tare da CAC a Najeriya (Mataki-mataki)
Cikakken Bayani Kan Yadda Za Ku Yi Rijista da Samun Takardar Shaidar Kasuwanci ta SMEDAN Tare da CAC a Najeriya (Mataki-mataki)
Barkarmu da sake haɗuwa da ku a wannan shafin namu mai albarka na HaskeNews Media and Publishing Services (www.haskenews.com.ng).
A satin da ya gabata, mun karɓi saƙonninku da dama kan yadda za a mallaki takardar shaidar kasuwanci daga Small and Medium Enterprises Development Agency of Nigeria (SMEDAN), tare da haɗin gwiwa da Corporate Affairs Commission (CAC). Don haka, ku biyo mu a cikin wannan kasida domin samun cikakken bayani.
Mataki na Farko: Yin Rijista
Idan ba ku taɓa yin rijista ba, wajibi ne ku fara yin rijista ta hanyar danna wannan adireshi:
👉 https://portal.smedan.gov.ng/signup
A nan za ku cike bayanai kamar haka:
Sunan farko (First Name)
Sunan ƙarshe (Last Name)
Imel (Email Address)
Kalmar sirri (Password)
Idan Kun Riga Kun Yi Rijista
Idan kuwa kun riga kun yi rijista, ku danna wannan adireshi domin shiga:
👉 https://portal.smedan.gov.ng/signin
Bayan haka, ku shigar da:
Imel ɗinku
Kalmar sirri (Password)
Da zarar shafin ya buɗe, ku tabbatar kun cike dukkan bayanan da hukumar SMEDAN ke buƙata.
Rijistar CAC
Bayan kammala cike bayanan SMEDAN, ku je gefen hannun hagu na shafin, ku nemi inda aka rubuta CAC Registration, sannan ku cike dukkan bayanan da ake buƙata.
Muhimmiyar Lura:
Ku tabbatar kun shigar da bayanai cikin cikawa daidai, domin yana iya ɗaukar kwanaki kaɗan kafin a amince (approval) da rijistar CAC.
Allah Ya sa mu dace baki ɗaya. Amin.
0 Response to "Cikakken Bayani Kan Yadda Za Ku Yi Rijista da Samun Takardar Shaidar Kasuwanci ta SMEDAN Tare da CAC a Najeriya (Mataki-mataki)"
Post a Comment