-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Ana ci Gaba da Cike Shirin Renewed Hope Ward Development Programme - Yadda Renewed Hope Ward Development Programme Zai Amfanar da Matasa, Mata da Manoma

Gwamnatin Tarayya ta ci gaba da aiwatar da Renewed Hope Ward Development Programme, wani muhimmin shiri da aka kirkira domin tallafa wa al’umma a matakin ward ta hanyar bunkasa tattalin arziki da rage talauci a fadin kasar nan.

Shirin na mayar da hankali ne kan:

  • Tallafa wa sana’o’i da kananan kasuwanci

  • Inganta harkokin noma da samar da ayyukan yi

  • Karfafa matasa, mata, da sauran marasa galihu

  • Aiwar da ayyukan raya kasa a matakin ward

A halin yanzu, ba a fara yin rajista ta yanar gizo ba. Maimakon haka, Enumerators na shirin suna zagayawa daga ward zuwa ward domin tattara bayanan mutanen da za su amfana da shirin.

Duk wanda ke da sha’awar shiga shirin ana shawartar sa ya tuntubi Karamar Hukumar da yake, inda ake da Coordinators a dukkan kananan hukumomi 774 na Najeriya domin samun karin bayani da shiriya.

Gwamnati ta jaddada cewa wannan shiri ba wai palliative na wucin gadi kawai ba ne, illa shiri ne na dogon lokaci da aka tsara domin taimakawa wajen samar da hanyoyin samun kudaden shiga, da kuma inganta ci gaban al’umma daga tushe.

Za mu ci gaba da bincike tare da kawo muku cikakkun bayanai kan yadda ake aiwatar da shirin a kowace jiha, In sha Allahu.

2 Responses to "Ana ci Gaba da Cike Shirin Renewed Hope Ward Development Programme - Yadda Renewed Hope Ward Development Programme Zai Amfanar da Matasa, Mata da Manoma"