-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Hukumar Haraji ta Jihar Zamfara (ZIRS) ta Buɗe Shafin Daukar Sabin Ma'aikata

Hukumar Haraji ta Jihar Zamfara (ZIRS) ta Buɗe Shafin Daukar Sabin Ma'aikata

Hukumar Haraji ta Jihar Zamfara (ZIRS) ta Buɗe Shafin Daukar Sabin Ma'aikata



DAUKAR AIKI DAGA HUKUMAR HARAJI TA JIHAR ZAMFARA (ZIRS)

Hukumar Haraji ta Jihar Zamfara (ZIRS) tana gayyatar kwararru kuma gogaggun 'yan asalin jihar Zamfara da su cike guraben aiki daban-daban a hukumar.

📌 MUHIMMIYAR SANARWA GA MASU NEMAN AIKI
Ana sanar da duk masu sha'awar cike wannan aiki cewa, idan aka yi nasarar daukar ku, za a iya tura ku aiki a ko'ina a cikin jihar Zamfara. Wurin aiki ba zai takaita ga Karamar Hukumar (LGA) da mutum ya fito ba kawai. Hukumar ce za ta yi posting din ma’aikata bisa bukata da zabin ta.

GURABEN AIKI DA AKE BUKATA:

  1. Bangaren Kula da Haraji (Tax Administration): Masu Digiri/HND a Accounting, Economics, Taxation ko makamantansu.

  2. Bangaren Shari'a (Legal & Compliance): Lauyoyi (LL.B, BL) masu kwarewa.

  3. Bangaren Wayar da Kan Jama'a (Public Enlightenment): Masu Digiri a Mass Communication, Public Relations ko makamantansu.

SHARUDDAN CANCANTA (General Requirements):

  • Dole ne mai nema ya zama Dan Asalin Jihar Zamfara.

  • Shekaru: Tsakanin 18 zuwa 35 (ga masu farawa).

  • Mallakar Digiri (B.Sc/HND) mai daraja ta biyu (Second Class Lower) ko makamancinsa.

  • Mallakar takardar kammala NYSC ko takardar daukewa (Exemption).

  • Mallakar Lambar Haraji (TIN) mai aiki.

  • Iya amfani da Na'ura mai Kwakwalwa (Computer/ICT skills).

  • Lafiyar jiki (daga asibitin gwamnati) da kyawawan dabi'u.

LOKACIN CIKEWA:

  • Farawa: Juma'a, 05 ga Disamba, 2025 (12:00 PM).

  • Rufewa: Alhamis, 18 ga Disamba, 2025 (12:04 AM).

YADDA ZA A CIKE:
Ana bukatar masu sha'awa su ziyarci tashar yanar gizo ta hukumar daukar aiki domin cike fom din neman aiki:

👉 www.recruitment.zamfara.gov.ng

Domin karin bayani, za a iya aika sako ta imel: info@recruitment.zamfara.gov.ng

Allah ya bada sa'a.

0 Response to "Hukumar Haraji ta Jihar Zamfara (ZIRS) ta Buɗe Shafin Daukar Sabin Ma'aikata"

Post a Comment