-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Shirin Tallafi na TVET Initiative: Idan Ka Cike Wadannan Bangarorin - Daure ka Karanta

Shirin Tallafi na TVET Initiative: Idan Ka Cike Wadannan Bangarorin - Daure ka Karanta

Shirin Tallafi na TVET Initiative: Idan Ka Cike Wadannan Bangarorin - Daure ka Karanta 



KARIN HASKE TVET INITIATIVE na ci gaba da tafiya yadda aka tsara. Jiya da daddare, dubban mutane sun samu saƙon imel, musamman waɗanda suka cike ɓangaren dinki kamar su Fashion Design da Garment Making.

Waɗanda suka nemi shiga wannan ɓangaren an tura musu saƙo cewa akwai wani sabon ɓangare na musamman da ya shafi Masu Sana'ar Fata (Leather Workers).

Su waye Masu Sana'ar Fata (Leather Workers)?
Masu sana'ar fata su ne waɗanda ke sarrafa fata domin yin takalma, jakunkuna, da sauran kayayyaki makamantan su.

Shirin TVET Initiative ya buɗe dama ga waɗanda suka zaɓi ɓangaren Fashion Design, yanzu za su iya canzawa zuwa ɓangaren Masu Sana'ar Fata idan suna so kuma suka ga saƙon da aka tura musu.

Wannan saƙon ba daga 'yan damfara ba ne, daga hukumar TVET Initiative ne. Duk wanda yake buƙatar canji, sai ya bi hanyar da aka turo masa a cikin imel ɗinsa.

0 Response to "Shirin Tallafi na TVET Initiative: Idan Ka Cike Wadannan Bangarorin - Daure ka Karanta"

Post a Comment