FME TVET Initiative — Muhimmin Sako
Tuesday, September 2, 2025
Comment
FME TVET Initiative — Muhimmin Sako
Duk lokacin da kuka samu sako daga FME TVET Initiative, ku tabbatar kun bi umarnin da aka bayar ta hanyar shiga LEARTHRWORK domin tabbatar da bayananku. Wannan tsari ne na hukuma, ba na masu zamba ba, kuma ba aikin scammers ba ne kamar yadda ake yawan gani a wasu lokuta.
Dalilin Neman “Confirmation” daga LEARTHRWORK
- Don tabbatar da cewa kai ne da kanka ka nema, ba wani ya yi amfani da sunanka ba.
- Don hana masu zamba ko shigar da bayanan karya.
- Ku bi dukkan matakan da aka gindaya domin samun amincewa (Approval).
Idan aka turo muku da irin wannan sako, hakan yana nufin akwai yawan masu nema, don haka ana bukatar kowa ya tabbatar da kansa ta hanyar bin hanyar da aka fadi a sakon. Kada ku yi sakaci, ku tabbatar da bayananku ta hanyar danna mahaɗin yanar gizo da aka aiko muku.
0 Response to "FME TVET Initiative — Muhimmin Sako"
Post a Comment