-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

SHAWARA GA MATA: Shin kina godiya ga mai gidanki idan ya yi miki kyauta?

SHAWARA GA MATA: Shin kina godiya ga mai gidanki idan ya yi miki kyauta?

SHAWARA GA MATA: Shin kina godiya ga mai gidanki idan ya yi miki kyauta?

TUNATARWA: Yana daga zubar da mutuncin mutum da raguwar kima ga ɗan Adam shine, CIN AMANA.

Cin Amana: Ba abu ne mai kyau ba, yana daga cikin halayen munafurci. Manzon Allah (SAW) ya lissafa wasu halaye guda uku, ya ce duk wanda yake da su a cikin halayensa, to hakika shi ne munafiki, ko da ya yi sallah, ya yi azumi, ya bayar da zakka, ya yi hajji, ya yi umrah, ko da ya ce shi Musulmi ne! Subhanallah!!!

Cin amana yana daga cikin abubuwan da suke tauye wa imanin mutum. Matuƙar mutum zai rinka cin amanar mutane, to imaninsa kullum raguwa yake yi.

Cin amana yana daga cikin halayen da suke kaskantar da darajar mutum a wajen Allah. Matuƙar mutum bai riƙe amanar bayin Allah ba, to Allah ne zai zama abokin rigimarsa ranar tashin kiyama! Subhanallah!!!

Cin amana yana sa mutum ya yi bakin jini a cikin al'umma, darajarsa da mutuncinsa zai zube, sannan kuma al'umma su rinka gujensa.

Cin amana yana zama sanadiyar dulmuyewar mutum cikin wutar Jahannama kamar yadda ya zo a Alƙur'ani mai girma. Allah zai sanya amanar a can ƙasan wutar Jahannama sannan ya umarci shi mai cin amanar cewa ya shiga ya ɗauko ta. Sai ya shiga ya ɗauko ya hauro wani babban tudu, sai ya kama, amanar ta subuce ta koma can ƙasan ramin Jahannama. Sai mala'iku su daka masa tsawa ya koma ya ɗauko ta. Haka zai ci gaba da yi har abada.

Cin amana yana zubar da albarkar dukiya, domin kuwa duk yawan kuɗi idan har aka cuɗanya su da kuɗin cin amana, sai ya lalace. Ya ku 'yan'uwa, ya zama wajibi a kanmu mu guji cin amanar, koma menene aka bamu, domin guje wa saɓon Allah, da kuɓutar da mutunci, da guje wa lalacewar lamurra.

SHAWARA GA MATA.

Shin kina godiya ga mai gidanki idan ya yi miki kyauta?

Yana daga cikin halayen wasu matan rashin gode wa mazajensu, a lokacin da suka yi musu alheri, wanda yin hakan butulci ne da rashin sanin ya kamata. To bari ki ji:

Mace nagartacciya a duk sanda mai gidanta ya yi mata kyauta, takanyi godiya kuma ta yabawa kyautar, ko da kyautar ba ta yi mata ba. Idan kuwa ba ta yi mata yadda take so ba, sai ta bi wata hanyar hikima daga baya ta fahimtar da shi, ba tare da an samu matsala ba. Idan kika kasance mai bin nagartattun hanyoyi da nazari, zaki kasance cikin farin ciki a zaman aurenki. Manzon Allah (SAW) yana cewa ba ya kallon macen da ba ta gode wa mijinta.

Haka kuma, wani hadisi ya ce: butulcin mata ga mazajensu yana daga abin da ya sa suka fi yawa a cikin wuta. Allah ya tsare mu, ya kiyaye mu, Allah ka kuɓutar da mu, ka sa mu dace.

0 Response to "SHAWARA GA MATA: Shin kina godiya ga mai gidanki idan ya yi miki kyauta?"

Post a Comment