-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Matasan Arewa Dama Ce Gare Ku: An Buɗe Rijistar Taron Matasa na Ƙasa (Confab 2025) - Cika Fom ɗin Taron Matasa

Matasan Arewa Dama Ce Gare Ku: An Buɗe Rijistar Taron Matasa na Ƙasa (Confab 2025) - Cika Fom ɗin Taron Matasa

Matasan Arewa Dama Ce Gare Ku: An Buɗe Rijistar Taron Matasa na Ƙasa (Confab 2025) - Cika Fom ɗin Taron Matasa

Taron Matasa na Ƙasa 2025 (Confab) - Rijista Ta Fara!

Shafin: Haskenews Media and Publishing Services

An buɗe rajistar halartar Taron Matasa na Ƙasa 2025 (National Youth Conference - Confab), mafi girman dandalin tattaunawar matasa a Najeriya. Wannan taro zai haɗa matasa daga mazabu 360, shiyyoyin ƙasa shida(geopolitical zone), da ƙasashen waje domin kawo sabbin mafita ga Najeriya.

📌 Muhimman Bayanai:

  • Lokacin Rijista: 16 Yuni – 30 Yuli, 2025

  • Wurin Taro: Abuja (da kuma ta yanar gizo ga 'yan ƙetare)

  • Masu Cancanta: Matasan da ke da shekaru 18 zuwa 35 (kashi 10% daga sama da 35)

  • Jinsi: 50:50 tsakanin maza da mata

  • Mutanen da ke da nakasa (PWD): Ana maraba da su, an tanadi bukatunsu

🎯 Manufar Taron:

  • Haɗa matasa cikin yanke shawara na gwamnati

  • Saka ra’ayoyin matasa a cikin tsare-tsaren ƙasa

  • Samar da sabbin hanyoyin magance matsaloli

🧭 Jigon Taro:

Next Gen Nigeria – Samar da Mafita, Mallakar Makoma

🔍 Batutuwan da za a tattauna:

  • Shiga harkokin mulki

  • Kasuwanci & ayyukan yi

  • Sauyin yanayi & makamashi mai tsafta

  • Ilimi da ƙwarewa (Seven-Star Skills)

  • Fasaha & ƙirƙira

  • Tsaro & haɗin kai

📝 Yadda Za Ka Yi Rijista:


Yi rijista yanzu, ka taka rawar gani a gina makomar Najeriya!
🔗 Cikakken bayani: https://nationalyouthconfab.gov.ng


Allah yasa mu dace baki daya 

5 Responses to "Matasan Arewa Dama Ce Gare Ku: An Buɗe Rijistar Taron Matasa na Ƙasa (Confab 2025) - Cika Fom ɗin Taron Matasa"