Tallafi 5 da Gwamnatin Tarayya ta Bude
Tallafi 5 da Gwamnatin Tarayya ta Bude
Barka da zuwa dandalinmu na Haskenews.com.ng a cikin wannan labarin, za mu kawo maku sabin tallafi guda hudu da gwamnatin tarayya ke ci gaba da bawa yan kasar, kamar yadda kuka sani gwamnati Najeriya ta bude sabin tallafi ga yan kasar musamman masu karamin karfi da jari hakan ya bamu damar kawo maku su, kamar yadda zaku gani a kasa:
Shirin Bayar da Kuɗi don yin Ƙanana da Matsakaicin Kasuwanci da kuma Taimakon Ƙungiyoyin Al'umma Mai taken RAPID
Manufar shirin ita ce a taimaka wa al'ummomin karkara da masu fama da matsalar tattalin arziki don amfani da albarkatun da ake da su don bunkasa masana'antu da za su iya samar da ayyukan yi, inganta yanayin rayuwa, ba da gudummawa ga ci gaban kasa da kuma magance rashin tsaro da ya samo asali daga halin da ake ciki na matasa.
Ziyarci: rapid.boi.ng/register
Cibiyar Nazarin Matasan Najeriya -Nigerian Youth Academy (NiYA)
Cibiyar Nazarin Matasan Najeriya (NIYA) wani dandali ne na kan layi wanda aka gina da nufin karfafa matasan Najeriya ta hanyar ilmantarwa, gina al'umma, basu tallafin fara kasuwanci, harkokin siyasa, damar yin aiki, da damar samun albarkatun rayuwa. Manufofin cibiyar shi ne samar da tsare-tsaren da suka hada da karfafa matasa miliyan 7, samar da ayyukan yi miliyan 5, da habaka tattalin arzikin Najeriya.
latsa nan domin cikewa: https://niya.ng/
Hukumar Kula da Lamuni ta Najeriya - Nigeria Consumer Credit Corporation (CrediCorp)
Hukumar Kula da Lamuni ta Najeriya (CrediCorp) na da niyyar kara samar da lamuni na masu amfani da shi ga kashi 50 na ‘yan Najeriya masu aiki nan da shekarar 2030. Suna magance matsalolin, suna ba da garanti, da hada kai da cibiyoyin kudi. Aiwatar ta hanyar credicorp-register.ng/apply tare da keɓaɓɓen buƙatun kuɗi, da cikakkun bayanan aiki kafin tashar ta rufe nan ba da jimawa ba.
latsa nan domin cikewa: https://credicorp-register.ng/apply
Tallafin Gwamnatin Tarayya - N50,000 FG Grant/Loan
Gwamnatin Tarayya Ta Bude Sabon Tallafinnan na Naira N50,000 ga Kananan Yan Kasuwa Mai Suna "Conditional Loan and Grant Scheme to Businesses in Nigeria". Shi dai wannan tallafin an kaddamarda shi ne ga yankasuwa masu kananan da matsakaitan kasuwanci.
latsa nan domin cikewa: https://loan.fedgrantandloan.gov.ng/
Tallafin NITDA na 3million Technical Talent Program 3MTT
Wannan shiri na 3 Million Technical Talent Program 3MTTP shirinena Gwamnatin tarayya karkashin ministry sadarwa wato Ministry of communication wanda da tsohon minista prof. Isah Ali pantami ke jagoranta. Wannan shiri yana daga cikin tsarin shugabannkasa Bola Ahmed Tunibu na ƙirƙiran aiyuka 2m biyu zuwa sheraka ta 2025
latsa nan domin cikewa: https://3mtt.nitda.gov.ng/
0 Response to "Tallafi 5 da Gwamnatin Tarayya ta Bude"
Post a Comment