-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Kalaman Soyayya Masu Dadi 2024/2025

Kalaman Soyayya Masu Dadi 2024/2025

 KALAMAN SOYAIYA.

Kalaman Soyayya Masu Dadi 2024/2025

Ga Namiji, ze aika mata sakon text kamar haka. Barkanki  dai aminiyata kuma aminiyar zuciyata ma abociyarta, yau na yini da kewarki saboda ban gankiba, se nakeji tamkar bani da lafiya ajikina koma nace gaba daya banajin dadin yanayina, da kene nake samun nutsuwa harma na samu kaina, musamman idan ina tare dake ace gani gaki, ta hakan ne na gano cewa gaskiya yau nayi babban rashi mai girma na rashin kasancewa tare dake, kedin ta musamman ce acikin mutane mutanenma na musamman, kedin ta daban ce awajena mai babbar fada, mai alfarma kuma mafi girma.

Babyna akoda yaushe bazan dena fada miki cewa, hakika aduk lokacin Dana kasance tare dake jina nake wani daban, ina jina tamkar wani sarki ko yarima da aka bawa, sarauta kwanannan.

Kalmomin danake fada miki sunyi kadan na kwatanta abin dake raina kona siffanta, domin kuwa kedin kinkai matsayin da kin wuce komai awajena, kuma kinkai matakin da Dana rasaki gwara na rasa rayuwata, kamar yadda nakeji bazan iya rayuwa babu keba haka nakeji idan na rasaki tamkar zan iya zautuwa,

Nakanji nazama mai rauni tamkar dan yaron daya rasa mahaifiya alokacin da yake tsananin bukatarta, to tabbas idan kika gujeni zan zamo tamkar maraya Mara uwa da uba, haka aduk lokacin dana wayi gari banji sautin  muryarkiba azahiri koda kuwa awayane, nakanji zafi araina mara misaltuwa, uhm dear wasu har cewa suke na tabu wasu kuma suce na zama wawa, su fadi duk abida zasu fada indai akan sonkine bazan damuba, nasan duk abinda nai akanki bazan fadiba, da ace masu cewa na zautu sunsan irin madaran sinadarin zunzurutun Sirrin dake tare da soyaiya dake da bazasu fadi komai game dani akankiba, bana damuwa ko kadan hakan ma karamin karsashi yake akanki masoyiyata.

Wasu kuma suna kirana da  majnun akan sonki, eh nace musu  na yadda ni majnun ne akan haukan  sonki, ammafa bazan yadda na rasaki kamar yadda majnun ya rasa laila, lallai zan jajurce zanyi gwagwarmaya, koda yakine akan sonki ya taso zan iya, zan zama tamkar jan gwarzo afagen fama kuma Kazaran gwajin dafi afilin daga, tareda da dagewa domin ki zamo tawa ni kadai  ba tujewa ko sarewa ko ja da baya indai akanki ne na tsaya, naja tinga, ina jira duk wani mahalukin daze tabaminke baze zauna lafiya,

Inada buri kece burina, kuma muradina, kuma kece mafarkina da nake tunanin ya zamo gaske, akoda yaushe, babban fatana shine ki zamo tawa kuma sarauniyata agefena mai mulkina mai fada a babban birnin zuciyata mai kula da dukkan lamarina, ki zaki rikemin akalata saboda na yadda dake sosai nasan zaki iya kula dani. 

Habibty na ina sonki kada kiyi tunin magulmata makiya yan tsegumi da munafukai zasu narasa araba soyaiyata dake, bazasu iya rabani dakeba mun musu nisa, kuma naji nagani aduk yadda kike haka nake sonki wanan itace kauna tsakani Allah, na mallaka miki kaina duka ni nakine se yadda kikai, nazama ke kin zamani, banji cewa araina na tabajin haushikiba ko kuma kinmin laifi, koda kinyi ma na yafemiki Honey na,

0 Response to "Kalaman Soyayya Masu Dadi 2024/2025"

Post a Comment