-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

GAREKU YAN UWA MAZA, SIFFOFIN MIJI NA GARI

GAREKU YAN UWA MAZA, SIFFOFIN MIJI NA GARI

GAREKU YAN UWA MAZA, SIFFOFIN MIJI NA GARI ga wasu siffofi da halaye na namiji na gari.

Miji nagari shine Wanda yake ciyar da iyalansa halali idan shima yaci, yake shayar dasu idan shima yasha, kuma yake tufatar dasu idan shima ya suturta kansa bawai se shekara shekaraba, domin yasan darajar kwalliya.

Miji nagari shine wanda ze zamo zaki awaje damo acikin gida, wato mai hakuri ga dukkan lamura, ko kuma ya zamo kamar air-condition wato awaje yake kara amma  aciki kuma sanyi yake bayarwa.

Miji nagari shine Wanda ya hada wasu siffofi guda goma, wanda Allah ta ala ya ambacesu acikin suratul Ahzab aya ta 35.

Miji nagari shine Wanda yake son matarsa bayan aure fiye da yadda ya sota  ya nuna mata kauna ya jata ajiki ya nuna mata kafin aure.

Miji nagari shine Wanda yake kishin matarsa, domin Annabi, s a w. Yace duk Wanda baya kishin matarsa baze shiga aljannaba.

Maiji nagari shine Wanda ya dauki aure amatsayin Ibadan ba wai abin wasa ko abin jin dadiba kawai  ba.

Miji nagari shine Wanda ya dauki matarsa amatsayin abokiyasa kanwarsa kuma abokiyar shawararsa.

Miji nagari shine  baya zagin matarsa, baya cin mutuncinta, baya cin zalinta, baya ha intarta koda abayan idonta.

Miji nagari shine wanda yake zaune da iyalinsa cikin amana da gaskiya  da kyautatawa ba cuta ba cutarwa.

Miji nagari shine Wanda idan ya fahimci halayen matarsa yake hakurin zama da ita tareda kyautatawa domin Neman rahamar Allah. 

Miji nagari shine Wanda idan zeyi magana da matarsa babu yaudara ko karya acikin ayyukansa da  zancensa.

Miji nagari shine Wanda ya dauka a zuciyarshi cewa iyayen matarshi iyayensane yan uwanta ma yan uwansa ne dangintama danginsane.

Miji nagari shine Wanda ya dauka farin cikin matarsa shine farin cikinsa kuma matsalarta shima tasace.

Miji nagari shine Wanda yake kokarin kiyaye Sirrin matarsa kuma yake kokarin kare mata mutuncinta koda awajen yan uwansane tareda hikima.

Miji nagari shine Wanda baya fifita matarsa akan yan uwansa kuma  baya tauye mata darajarta, yana bawa ko wane gefe nasa hakkin kamar yadda Shari ah ta tanadar.

Miji nagari shine Wanda ya tanadi ruwan afuwa da hakuri acikin zuciyarsa domin ya rika kashe wutar tashin hankalin da bacin rai aduk lokacin da hakan ta faru atsakaninshi da matarshi.

Miji nagari shine Wanda akullum yake kokarin tarbinyantar da iyalansa akan rayuwar addinin islama ba rayuwa irin ta yahudu da nasaraba.

Miji nagari shine Wanda yake zaune da matarsa komai wuya ko dadi baze dena nuna mata soyaiya ba wai don ta fara yankwanewa ko kuma karfinta ya fara raguwa.

Miji nagari shine Wanda yake yaba matarsa yake bata kwarin gwiwa aduk lokacin da tayi kwalliya ko kuma tayi girki komai rashin dadinsa.

Miji nagari baya raki baya ihu don yaji abinci yayi yaji ko gishiri yayi yawa,  sedai yace kamar uwar gida yau girkinan yayi dadi iyaka sedai  gishiri yaimana shishigi aciki.

 Miji nagari shine Wanda yake da tausayi aduk lokacin da matarshi bata da lafiya shima seka ganshi kamar bashi lafiya yana tausaya mata matuka yakan dauketa da kanshi ya kaita asibiti domin tausaya mata. Wadanan sune siffofin mazaje nagari.

0 Response to "GAREKU YAN UWA MAZA, SIFFOFIN MIJI NA GARI"

Post a Comment