-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Kalaman Soyayya Masu Dadi 2024/2025

Kalaman Soyayya Masu Dadi 2024/2025

Kalaman Soyayya Masu Dadi 2024/2025

KALAMAN SOYAIYA.

Sakon text zuwa ga masoyinki, na musamman, zaki tura masa da kalaman masu dadi na bazata damun sashi farin ciki, zaki fara da sallama kamar haka.

 Assalam, abin sona abin alfaharina, ina fatan kana cikin koshin lafiya, da fatan katashi lafiya, rabin raina ya kake ya aiki, akwai wata magana da nakeso na gayama, agaskiya ina sonka, kuma na mallaka maka duka rayuwata gaba daya saboda ka isa kuma kakai, akwai wasu sunaye ma banbanta da nake kiranka dasu saboda kaidin na musammanne kuma sunayen kowanne akwai ma anar kiranka dashi, nasan zaka so kaji, hubbyna abinda yasa nake kiranka da rayuwata kaidin ka zamo min wani babban bangare na jikina Wanda idan babu kai babu bazan cikaba, abinda yasa nake kiranka da jigon rayuwata shine, kaidin garkuwane agareni Wanda idan babu kai zan tagayyara, abinda yasa kuma nake kiranka da rabin jikina shine, kaidin kamar jinine na jikina Wanda idan babushi zan kafe, baby abinda yasa kuma nake kiranka da rabin raina shine, kaidin wani bangarene na jikina Wanda idan babu ze zamo matsala, abinda yasa nake kiranka da zuciyata shine, kaidin kamar ruhine na jikina wanda idan babushi babuni, abinda yasa kuma nake kiranka da my prince shine, kaine yarimana kuma sarkina mai mulki abirnin zuciyata harda ni kaina duka,

Abinda yasa kuma nake kiranka da my Sweet heart shine, Kaine kake kara sawa rayuwata tai dadi kuma kara mata annushuwa da nishadi, abinda yasa kuma nake kiranka da sahibul kalbi ma ana ma abocin zuciyata, saboda Kaine mai rarrashina mai sharemin kukana mai cireni a damuwa, abinda yasa kuma nake kiranka abokina shine saboda Kaine aminina mai bani shawara mai dorani ahanya, zakaji ina kiranka da nurul hayaty, ma ana hasken rayuwata, saboda Kaine mai kara haskaka rayuwata kuma mai budemin hanya idan na gaza ganewa kuma mai fahimtar dani rayuwa, uwa uba kuma abinda yasa nake kiranka da miji shine, saboda ina sa ran ka zama mijina wataran bada dadewa ba kuma uban yayana, ina fatan ka fahimta my dear

0 Response to "Kalaman Soyayya Masu Dadi 2024/2025"

Post a Comment