-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Shawara ga Masoya

Shawara ga Masoya

Mu KYAUTATA RAYUWARMU. 
Shawara ga Masoya



Ka zama mai kulawa da rayuwar ka, kada ka biyewa dan adam, aduk yadda ka kai dajin kanka, ko kuma zama nagari, to wani yana can shi kallon banza yake maka, kuma ko meza kai masa, baze dena yi maka irin Wanan daukar ba, saboda ahaka ya tsarawa raywarshi jin haishinka, wani kuma yana gefe kaunar ka ta cika masa zuciya, amma baze iya furta makaba saboda kunya, ko kuma wani abu daban, indai mutunene ba a iya musu, kullum zuciyar su canza wa take game da, mutane don haka kada ka rudu da tarin mabiya, ko masoya masu yabon ka, kada kace za kaiwa mutum mugun fata da mugun tunanin koda makiyinka ne shi, akullum Wanan mugun fatan da tunanin da kake shine yake kewa yowa ya dawo kanka kullum abinda kake so ya samu mutane shine zeta samunka, don haka ba ruwanka, ka zamo mai shigar da farin ciki cikin zuciyar musulmi, ita zuciya an dabi antar da itane, da son mai kyautata mata, Allah madaukaki kuwa yana son mai amfanar da mutane, manzon Allah yace mafi soyuwa mutane awajen Allah shine Wanda yafi amfanar da mutane, kuma mafi soyuwar aiyuka agurin Allah madaukaki, farin ciki da zai shigar ga zuciyar musulmi, ka shigar da farin ciki zuciyar dan uwanka musulmi ta hanyar. Dadaddar magana, kyautata mu a, malantarsa, biya masa bashi, yaye masa wata damuwa koda ga hanyar shawa rane, da maganganu masu kwantar da hankali,  yi masa kyauta, ziyartarsa, biya masa wata bukata tasa da zaka iya, kiransa awaya Ku gaisa, da duk wani nau in kyautata wa da nuna kulawa da zesa yaji dadi da farin ciki aransa. Bakai asara ba don ka don ka bawa Dan uwanka musulmi kulawa, da kyautatawa, ka daure kasa dan uwanka cikin farin ciki, iyayenka,  da  iyalanka, da yan uwanka, da abokai da wanda ka  sani  da Wanda baka saniba. Kada ka zauna dole se sun nuwa bukatuwar su gareka, sanan kayi wani abu ko se anyi maka sanan kayi, ko se an furta maka sanan ka aikata, tabbas zukafa basu maraba da irin wanan marowa ciyar zuciya. Babu Wanda ze fahimci hakan se wanda ya jarraba, kaidai ka tsaya ka tsarkake zuciyarka, kayi domin neman ladan.

Kai zama mai kula, wanan yana da muhimmanci arayuwarka, Ka mance sharrin da halitta tai muku, domin yin hakan zesa ka zama Baka da abokin gaba acikin mutane, har ya zama kun riki kowa masoyi, Baku da makiyi acikin halittar Allah. Ka mance Alkhairin da kaiwa halitta, domin tunawa da kayiwa wani kaza, hakan zesa kaji ka isa, wanda hakan ze shafi aiyukan Alkhairin da kakeyi, riya ta shigo ta bata aiyukan ka. Abubuwa biyu karmu mancesu har a bada. Karka manta Alkhairi da halitta taimaka, idan kullum bawa na tuna Alkhairin da halitta tai masa, to ze dauwa ma cikin sakawa halittar Allah da abubuwan Alkhairi, har yakai ga ya tabbata cikin kyautata zato ga dukkan halittar Allah, da neman yarda kuma ya zauna dasu lafiya.

Ka zama mai kulawa da rayuwaka. Yana daga dabi ar dan adam yawan gaza gani, wato komi ya gani seya samu ta cewa, wani ya fadi mai dadi wani ya furta shirme, kaidai ka zamo mai kyatata zato, ka zamo mai sawa harshenka linzami, kome zaka fada ka tauna, kafin furtawa. Ka sani ko wani mutum da irin kallon da yake maka arayuwa, wani na fadan Alkhairi akan ka, yana maka zaton Alkhairi, wani ko akasin hakane tunanin Sa ,da ambaton Sa akanka, kaidai kada ka damu kuma kada ka manta Allah shi kadai yasan hakikanin yadda kake, don haka karka damu da zato, ambato, ko tunanin da mutane zasuyi akan ka, kai dai nemi yaddar Allah

Ka zama mai kula, kada ka dauka, duk wanda yai shuru, kurma ne, wani yayi shurune yana jiran lokaci, wani yayi shurune don yana yanayi, wani kuma kawai cinsa shine maganar sa, kada ka damu idan kanayi ba a gedewa, magabata sunce, shi aikin jama a ba a iyawa ba a gamawa, ba a yabawa, idan Allah ya yaba aikin shikenan. kada ka zamo me yawan jayaiya, yawan jayaiya alamar girman kaice, kada ka zamo mai yawan surutu yawan surutu alamune na masu tabun hankali, ka zamo mai kawaici, kawai ado gareka,  ka zamo mai yawan kyauta, kyauta halin girma ne, ka zamo me yawan yafiya, yin yafiya na janyo daukaka, kada ka zamo mai yabon kai, yabon kai jahilcine. Kada ka zamo me kuntatawa raywarka da tunani barkatai, don wani abu ya sameka, idan kana cikin damuwa ka jira samun sauki daga Allah, wanan jiran da kakeyi ibada ne domin kyautata zatone ga Allah, Wanda ya kyautata wa Allah zato kuwa, lallai kuwa Allah ze isar masa. Shi Dan Adam kamar fensir muke, rayuwa zaga rika fekeshi, yan sake rubutu harya zo ya kare, idan ka mutu babu abinda za rage se abinda rayuwarka ta rubuta, ka zamo mai hankalta, domin mafi hankaltar mutane, shine, Wanda yabar duniha tun kafin ta barshi, ga gyara kabarinsa tin kafin ya shiga cikinsa, ya yadda  ubangijinsa tin kafin ya hadu dashi, yayiwa kansa hisabu tun kafin ayi masa, kada ka rinka saurin  fushi, saboda bakaza iya ganin gaskiya lamariba kana fushi, ka zamo mai kame bakinka idan kana fushi, saboda magana cikin fushi baha haifar da Alkhairi,

0 Response to "Shawara ga Masoya"

Post a Comment