-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Matsayar Shirin NSIP

Matsayar Shirin NSIP

Matsayar Shirin NSIP

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kafa kwamitin shugaban ƙasa da zai binciki ayyukan hukumar NSIP mai kula da shirye-shiryen rage raɗaɗi a ƙasar.

Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasar Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce an kafa kwamitin ne domin maido da martabar shirye-shiryen da ya fara zubewa a faɗin ƙasar.

Matakin na zuwa ne bayan da a ranar juma'a shugaba Tinubu ya sanar da dakatar da shirye-shiryen rage raɗaɗin talauci huɗu da gwamnati ke aiwatar wa a ƙasar na tsawon makonni shida.

Shirye-shiryen rage raɗadin da dakatarwar ta shafa sun haɗar da shirin N-Power da, tallafin kuɗi ga marasa ƙarfi, da shirin tallafa wa masu ƙanana da matsakaitan sana'o'i da kuma shirin ciyar da 'yan makarantun furamare.

Shugaba Tinubu ya amince da kafa kwamitin shugaban ƙasar na musamman, ƙarƙashin jagorancin ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun, don gudanar da bincike kan yadda ake tafiyar da shirye-shiryen rage raɗaɗin talaucin a ƙasar.

Shugaban ƙasar ya kuma ɗora wa kwamitin alhakin gaggauta gudanar da cikakken nazari da binciken kuɗi da tsare-tsare da ƙa'idojin shirye-shiryen domin sake musu fasali ta yadda za a inganta su ta hanyar kawo cikakken tsari a tafiyar da shirye-shiryen domin sake inganta su.

Mambobin kwamitin sun haɗar da Ministan kuɗi da tattalin arziki a matsayin shugaba.

Sai ministocin lafiya da walwalar jama'a, da na kasafin kuɗi da tsare-tsare da na yaɗa labarai da na sadarwa da kuma ƙaramin ministan matasa a matsayin mambobi.

Shugaba Tinubu ya ce kwamitin na musamman zai yi aiki don maido da martaba da kimar da shirye-shiryen suka rasa a zukatan 'yan ƙasar.

Ya kuma ce kwamitin zai tabbatar da inganta shirye-shiryen ta yadda za su riƙa isa wajen masu ƙaramin ƙarfi a ƙasar waɗanda dama domin su ne aka ƙirƙiro da shirye-shiryen.


Copy daga BBCHausa

1 Response to "Matsayar Shirin NSIP"

  1. This is a good movement towards reducing hardship Nigerians are facing particularly in the North East of the country.

    ReplyDelete