-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

MU KYAUTATA RAUWARMU

MU KYAUTATA RAUWARMU

 MU KYAUTATA RAUWARMU



 kazama mai kula, yadda ake samun rayuwa mai dadi, kada ka tsani kowa duk girman rashin mahimtarka da yayi, ba Wanda yasan me ze faru tsakaninku a  gobe. Idan ka samu daukaka anaso ka rayu cikin saukin kai da saukakawa cikin mu amalar, kasani duk irin  damar da Allah yabaka, da irin dukiyar da Allah ya baka wani na gaba dakai. Duk halin daka samu kanka kayi hakuri kuma kai tunani mai kyau, ka tuna cewa baka da wata mafita da wuce ka dogara ga Allah, hakika komawa ga Allah nasan dukan kuncin rayuwa da kake ciki wata rana ze zama se alabari. Kada ka raina kanka idan ka tashi tin alheri, ka bayar da yawa Karka matse hannu komai karancin abinda kake samu, kasani matse hannu da rowa ba halin mumunai bane, daure ka cigaba yin sallama ga wadanda suka juya maka baya suka manta dakai , sanan kai yafiya ga wandanda suka bata maka, insha Allahu watarana zasuyi nadamar butulci da muguntar da sukaita kulla maka, Karka dena yin addu ar alheri ga kanka da wadanda suke sonka suke mutuntaka, kasani kullum kana ransu kuma idan alheri ya sameka kullum sunajin far in ciki koda basu gaya makaba, Idan zakai tunani kayishi ahankali amma idan zaka aiwatar kayishi cikin hanzari, Babbae hanyar da zatasa a girmamaka shine ka girmama mutane, kyakyawar hanyar da zatasa kaji magana mai dadi itace ka fadi magana mai dadi, dayawa mutane sunfi damuwa da warware matsala, maimakon kaucema faruwarta, kazama mai gudun magana da kaucewa faruwar matsala ko wace irice. Kadaure ka kyautata rayuwarka domin gobenka data yayanka nan  gaba.

0 Response to "MU KYAUTATA RAUWARMU"

Post a Comment