-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

YADDA ZAKI ZAUNA DA KISHIYA

YADDA ZAKI ZAUNA DA KISHIYA

YADDA ZAKI ZAUNA DA KISHIYA

yar uwa kada kishiga hakkin kishiyarki koya za ai kiji tsoron Allah, kisa a ranki cewa bazata iya yimiki komaiba face abinda Allah ya kaddara miki, kirike imani ki kasance mebin dokokin mijinki akoda yaushe, ki kasance mai tsafta jiki gida yaranki kada ki yadda tana yawan ganinki kacakaca, kada ki yadda tasan abinda yake bata miki rai saboda idan ta sani , to tana sane zata rinka yimiki wanan abun da ranki yake baci, idan ranki ya baci kada kibari ta gane matsalarki, kishiga daki kita jan hasbunallahu wa ni imal wakil, idan ya zamana dole se kinyi kuka, kiyi kukanki acikin daki ki wanke fuskarki kada kibari taga alamun kuka afuskarki, kada ki taba kai kararta gurin mijinku, kizama Kamar doki agado, ita kuma ki nuna mata miji be dameki ba, ki mata marhaba afarkon haduwarku, ki mutumta daginta, da iyayenta duka, iyayenta nakine kada su zamo kishiyoyonki, yaranki natane kada ki hanasu zuwa gurinta hakama danginki idan sunzo kada ki hanasu zuwa gurinta, kada ki rinka bata ta awajensu saboda sunrinka ganin laifinta, hakan ba daidai bane, ki dauketa abokiya zama ba kishiyaba, idan wani Abu ya faru da ginta idan an agaiyaceki kije,  kada ki zamo mai nuna isa da izza da daga kai yayin da kuka hadu da daginta, ko kuma adangin mijinku, kada ki zamo me batata adangin mijinku wai don kiyi suna afi sonki fiye da ita, saboda wataran gaskiya zata baiyana, idan kuma suka gane karya kike , abin bazeyi kyauba, kada ki zamo fitinanniya, mai fada, da yawan korafi, da tada husuma, da kananun magan ganu wadanda basu daceba, idan kina irin wadannan abubuwa dana ambato to tabbas zakiyi bakin mijin awajen mijinku, kada ki zamo mai habaici da yada bakar magana, domin yin hakan ze jawo miki raini awajenta, tin tana shuru wataran zata mayar miki, Wanda hakan kuma zubda kimane da kuma girma, kija yayanta ajikinki tamkar naki kada ki nuna banbanci atsakaninsu kiyi iya kokarinki wajen kwatanta adalci atsakani, akoda yaushe kizamo mejan mutumcinki da girmanki koda kece amarya ko uwargida, idan tai miki magana, kada kiyi gaggawar amsawa da sauri barkatai, ki amsa cikin nitsuwa, kibada Kamar 30% sec, kafinna kiyi tunani kibata amsar daya dace, iya girki babban maka mine, ki kware wajan iya girki, ki zama mai tattali ba rowaba, ki cireta aranki kada kiyadda shedan yasamiki  aranki cewa tazo ta takura miki ko kuma kiyita tunanin ta, kada kiyi haka kiyi abinda yake gabanki, tinda ba zamanta kikeyiba, ki zama ya kwalisa akullum, kada ki yadda arinka gane ranar girkinki da nata, ko ranar girkinki ko ba ranar girkinkina kizama fes cikin shiri da tsafta, kada kiwaita surutu, da magana, ki rage yawan hira keba radio ba ba television bace, ranar kwanakin ki ke actor ce ranar nata kuma ke boss ce, kiraka mai gidanki da tarairaya da kissa da lafazai masu dadi, idan ze koma dakinta, kada ki nuna kishinki afili, idan ya kiraki da sunanta amsa, ze rasa abinda ya furta, kada kirinka maganarta da wasu bata shafekiba baruwanki, domin yin hakan yana jawo matsala wataran ko baki ceba za ace kince, daga nan kuma seya zama rigima keda ita, komai zafin Abu kada kiyi dambe ko cacar baki da ita hakan ba girmanki bane, kuma kada ki manta hada kashi kishiya da kishiya ana dambe na kawo talauci da tsiya, koda ace ba wanan, tabbas zubar da mitumcine da kima da kuma asara dambe da kishiya, duk sanda kika sake kukai dambe da kishiya, to kisani kin  bude kofofin shigar raini atsakinku kisan me kikeyi me kika zoyi aure kikazo, yin ibada kikazo, baki da lokacin tsayawa ki bata lokacinki akan wata kuna sabani, yin hakan asarane, Wanan kenan,  daga cikin yadda zaki zauna da kishiya.

0 Response to "YADDA ZAKI ZAUNA DA KISHIYA"

Post a Comment