-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

MU KYAUTATA RAYUWARMU KASHI NA BIYU

MU KYAUTATA RAYUWARMU KASHI NA BIYU

MU KYAUTATA RAYUWARMU KASHI NA BIYU

      Ka zama mai kula,                 duk yadda ka shiga yanayin farin, anjima kadan kana iya neman farin cikin nan ka rasa, Rashin hakuri Yayi yawa azukatanmu abu kadan yana iya zama tashin hankali, makwabtanmu sun zama makiyanmu, akoda yaushe neman jin abin assha yake gareja damun yaji dadi dariya, Iyaye na wahala da yayansu damun idan sun girma suji Kansu, amma yanzu babu wanan jinkai awajen yayansu, Ada maza ke rike ragamar gidansu amma yanzu matane ke rike ragamar gida, Ada da wuya kaji mutum na fallasa sirrin gidanshi amma yanzu masu rike sirrinsu kalilanne, Rayuwa ta sauya komai ya canza ya kamata mu zama masu kula adukkan al amaranmu, mu kyautata rayuwarmu domin ta inganta, Hakuri Maganin zaman duniya, amma yanzu idan hakurin yai yawa sekaga mutum kamar me hauka, ko kuma yasama bugun zuciya, abinda ya kamata, mu yawaita istigfari da salatin manzon Allah s a w, da tashi cikin dare muna yawaita nafiloli, da addu oi, da karatun alkur an, karatun Alkur ani abincine ga ruhi, matukar muka nisan ceshi babu mu babu kwanciyar hankali, Mudena yabon kyan yayanmu agabansu da yabansu koda yaushe, hakan yanasa su zama masu girman kai, da alfahri, Murinka Jan yayan mu aji muna nuna musu cewa su manyane watarana zasu girma, hakan zesa kullum su rinka aikin hankali, Gidan da ake zama lafiya tsakanin iyalai da kishiyoyi dashi kansa mai gida, yanasa yara su tashi da tarbiya da hadin kai da kaunar junlafiya,duk gidan da ake zaman lafiya arziki yana sauka agidan, da kuma yayewar kunci da bakin ciki,mu zamo masu uziri da kyautata zaton Alheri ga kowa  yana kawo nutsuwar zuciya da Karin Imani, Duk kudinka bazaka iya siyan abinda ke cikin kasuwa ba, haka duk hakurinka wasu mutanen se sun Kular dakai, seka zamo mekai zuciyarka nesa, Mutuwa kullum daukarmu takeyi Kamar yadda ko waca Safiya da sabon burin da muke tashi dashi, shin mutuwarnan idan yazo jiranmu zatai har burikanmu sesun cika, a ah, bazata jiramuba,mutuwa daukarmu zatai, kuma duk burikan da muke dasu mantawa zamuyi dasu alokacin da kasa ta rufe mana idanuwanmu, don haka Mu kula Mu anakare tun kafin lokaci ya kure mana

0 Response to "MU KYAUTATA RAYUWARMU KASHI NA BIYU"

Post a Comment