-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Cikakken Bayanin Yadda Ake Rubuta/Tsara C.V

Cikakken Bayanin Yadda Ake Rubuta/Tsara C.V

Cikakken Bayanin Yadda Ake Tsara C.V 

Kun taba rubuta CV na neman aiki ko? Kuma kila har yau Allah bai sa an dace da samun aikin ba, duk da cewa CV din mai kyaune.

To bari kuji inda wata sabuwar matsala take. 

Kun tuna da mutanen nan da kuke sakawa a matsayin referees? To ka cire rana ɗaya ka kira su da number wayar da basu san ka da ita ba. Kayi acting a matsayin kaine recruiter din, kaji abinda zasu ce a kanka..

Ko, zaka iya Bama wani ya kira a gaban ka domin kaji abinda zasu fada, Incase da dan wani recruiter din ya kira su. 

Wallahi wani lokaci da yawa su wadannan Referees din sune suke Bama mutum matsalar da har za'a hana shi aikin da yake nema. Duk da cewa ya cancanta.

Shi yasa ake bada shawarar idan zaka saka referee a CV dinka to ka tabbatar daka saka

1- Wanda ya sanka kuma ka sanshi

2- Wanda zai iya bada shedar arziki a kanka

3- Wanda kasan mutumin kirki ne ba hassada a lamarin shi

4- Wanda kasan yina da ilimin boko bakin gwargwado

5- Wanda ya iya turanci 

6- Wanda yake da fahimta da kuma iya mu'amala

Idan ka rasa mutum mai wadancan features din dana lissafa a sama a matsayin referee dinka, to tabbas zai iya baka matsala a duk lokacin da recruiter ya kira shi.


0 Response to "Cikakken Bayanin Yadda Ake Rubuta/Tsara C.V"

Post a Comment