Yadda zaki hada kunun rida kwa kwa
Monday, November 28, 2022
Comment
Yadda zaki hada kunun rida kwa kwa
Abubuwan Bukata;
Ridi
Kwa kwa
Dabino
Sugar
Madarar Ruwa
Kayan qamshi,
Milk Favour
Yadda Zaki hada;
Da farko samu ri dinki ki gyarashi da kyau, sai kiwankeshi tas ajiye. Bayan kinyi wannan sai dauko kwakwanki kiyankata, saiki wanke kizuba shi acikin ri dinki saiki dauko dabinonki ki gyara ki wanke kizuba shi. Bayan kinyi wannan sai kizuba kayan qamshinki kikai nika, ki tabbatar cewa an wake injin sosai kafin niqa miki, ko kuma zaki iya niqawa da blender idan kinada ita. Bayan an nika shi sai kitaceshi kisaka suger da milk flavour da kuma madaran ruwanki. Daga nan sai ki jujjuya su sosai, sai kizuba agora kisa a gidan sanyi yadau.
Shikenan kununki ya hadu, sai serving!
0 Response to "Yadda zaki hada kunun rida kwa kwa"
Post a Comment