-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Yadda Zaki Hada Faten Wake Da Dankali

Yadda Zaki Hada Faten Wake Da Dankali

Yadda Zaki Hada Faten Wake Da DankaliAbubuwan Bukata;

1. Wake 

2. Dankalin turawa 

3. Tarugu da albasa (grated)

4. Ganyen albasa (lawashi)

5. Manja

6. Albasa

7. Maggi da gishiri

8. Kyan gamshi 

9. Busashen kifi

 Yadda Zaki Hada;

Da farko dak zaki gyara wakenki ki fidda shi tass sai ki sa ruwan tafasa wake a tukunyarki ki daura a wuta ki zuba waken da kika gyara aciki, ki dan barbada kanwa sai ki rufe ki barta ta dahu. Bayan waken ki ya dahu ( kada ki bari yayi lugub), sai ki dauko tukunyanki ki daura akan wuta ki sa manja, idan yayi zafi sai ki kawo albasarki ki yanka a ciki ki soyata sama sama kada ta kone.

Sai ki dauko busashiyar kifinki da kina gyara kika wane, ki zuba acikin man tareda Mayan kanshi ya soyu. Bayan kinyi wannan sai ki gyara attarugu da albasa da tattasai kiyi grating (jajjaga) dinsu. Bayan kinyi hakan sai ki dauko grated tarugu da albasan ki kisa a cikin man da kike suya ki soya su tare, sai kina juyawa Dan kar ya kama.

Idan kayan miyarki sun soyu sai ki dauko spices dinki ki sa a ciki da su maggi da gishiri, sai ki juye a ciki ki juya. Daga nan sai ki kawo ruwan zafi kadan (idan a kwai ragowar ruwan dahuwar wakenki) ki sa aciki, sai ki rufe tukunya ki har sai Kinji Ya fara tafasa.

Daga nan sai ki dauko wakenki tare da dankalin da already kin fere kin yankashi iya girman da kikeso, sai ki sa a ciki ki juya a hankali ki rufe tukunyanki nadan wani lokaci. Idan kika ga yabfara dahuwa sai ki dauko  ganyen albasarki ki sa a ciki, ki rufe tukunyanki na dan wani lokaci. Shikenan idan yayi yadda kikeso sai ki sauke.

 

0 Response to "Yadda Zaki Hada Faten Wake Da Dankali"

Post a Comment