-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Yadda Ake Zama da Talakan Miji

Yadda Ake Zama da Talakan Miji

Yadda Ake Zama da Talakan Miji

Da farko dai shi Zama da kowane irin miji sai mutum yayi hakuri balle a ce talaka ne ai zaman sai mutum yakai zuciyarsa nesa domin bakomai ne dakake bukata zaka samu b. Kuma shi miji talaka bashida wata illa a rayuwa da zaa ce baza a iya Zama dashi b ai shi arziki na Allah ne kuma idan ga rayuwa rabon mutum bazai taba wuceshi b. Idan kinada miji talaka hakuri zakiyi ku zauna a rufawa juna asiri shima abin asoshi ne ba wai gudunshi zaayi b ki rike abinki hannu biyu komai ya kawo komai kankantar sa ki karba ki yaba kiyi godiya ki nuna jin Dadi koda kuwa bakiji Dadi a cikin ranki b hakan shi zai saka gobe ya kara jajircewa wajen kokarin nemo muku abinda zakuci na yau da kullum Amma idan ya kawo ko kuma bai bayar da kudin cefaneba kika nuna bacin ranki ko kikai masa mita akan hakan zai Sanya ya Zama very weak wajen fita ya nemo..a duk lokacin da kikaga bai bayar da abin cefaneba ko kuma bai kawoba tor ki saka a ranki dacewa bayada kudin dazayayi cefanen ne shiyasa.

Sai ki duba ki saka tsoron Allah a cikin zuciyar ki idan kinada hanyar da zaki taimaka mishi kiyi cefanen sai kiyi domin idan kinyi kanku kikayiwa baki daya. Watarana zakaga wasu matan wai tunda mijinsu baya bada kudin cefane shikenan bazaayi wasu yan dubaru ayi abinci a gidan b wanda hakan sam bai dace b ai shi Zaman aure Zama ne a taimakon juna da rufawa juna asiri.

don haka mata idan Allah ya rabceku da samun miji talaka hakuri akeyi a zauna ayi zamantakewa mai kyau da kin saka a ranki ibada kikeyi tor shikenan bakida wata damuwa sai ki safe ki maida hankali wajen neman ladarki a gun mahaliccinki idan da rabo watarana zaiyi arziki kuma kuji Dadi tare Amma idan kina kyamatarsa a lokacinda bashida kudin idan Allah ya azurtashi bazai ji dadin ke kuma ya kyauta miki b saboda zaiyi ta tuna lokacin da bayada kina gudunsa kina ci masa mutunci nan take zakiga yace aure zai kara Amma idan kunyi zama na mutunci mai kyau sai Allah ya kara Sanya albarka a auren kuma yyi maku Budi na alkhairi idan kun dage dayin addua.

0 Response to "Yadda Ake Zama da Talakan Miji"

Post a Comment