Yadda ake Zama da Miji dan kasuwa
Yadda ake Zama da Miji dan kasuwa
Zama da Miji dan kasuwa ba wani dogon banbanci ne tsakaninshi da Zama da Miji maikacin gwamnati ba domin kuwa duk a layi daya suke tafiya kowanne zamanshi a gurin aikinsa yafi zamanshi a gida yawa don haka sai anyi hakuri dama Zama ko wa irin ne hakuri keyin shi Zaki iya samun Mijinki dan kasuwa ne kuma a cikin garin yake kasuwancin Amma bazai samu damar zuwa gida kullum ya ci abinci ba saboda yawan customers saidai ki dinga aika masa a waje wani kuwa zai iya squeezing time dinshi koda 30 minutes ne yazo gida yaci abinci ya danganta kowa da irin Yanda yake iyawa saboda kowa da na shi tsarin rayuwa kuma idan naki mijin ba mai dawo bane gida a lokacin da yafita tor ki daure Kiyi hakuri kuma kimasa fatan alkhairi Allah yasa albarka a cikin abunda yake nema kuma ya mayar dashi gida lafiya domin ko kinyi tashin hankali kinyi fada hakan ba riba bane a gareki domin kuwa dole ne ya fita ya nema domin rufa maku asiri ban dai Hana a zauna a yi magana ba ta fahimtar juna a duk lokacinda wani yakeyin abunda ba daidai ba akan zauna a samu fahimta Amma banda tashin hankali domin kuwa idan kina haka zaiji gabadaya ma me zaiyi a gidan tunda ko yadawo baya samun natsuwa sai yayi zamanshi a wurin kasuwancin shi har sai lokacin dayaji ya gaji sannan ya dawo Amma koda Yana jimawa a waje kece yakamata ki jajirce har kiga kin samu Yanda kike so a tare dashi through nuna masa kauna da soyayya da kuma yan kisisinar mu ta mata har kiga kin jawo hankalinsa ya daina abunda bakyaso sannan da jajircewa kuma wurin addua a koda yaushe so that ku samu zaman lafiya duk inda akace mutum yabar gidansa ya dawo tor kuwa Yana son ya samu Kulawa da nutsuwa sai dai idan hakan bai samu ba Amma ba wanda zaiso ya dawo cikin gidansa ya kasa samun walwala idan ya dawo ki mashi maraba ki tarbe shi hannu biyu babu bacin rai ki nuna masa irin wahalar da yake sha duk saboda ku Kiyi masa addua ta sanyaya zuciya ki basa abinci yaci sannan kudan samu koda 30 minutes ne haka ku tattauna a tsakaninku dangane da abunda ya faru a gida lokacin da yafita sannan halin da kike ciki hakannan shima ya dan baki irin yanayin kasuwancin sa idan yafita inshallah idan ana samun wannan tor bake ba damuwa koma yaushe yakai bai shigo gida ba indai a duk lokacinda ya dawo yana baki time dinshi..domin kuwa wasu mazan zakaga basa yini a gida sannan idan sun dawo matansu Basu samun time dinsu hakan kuwa Yana causing problems da dama domin mata kuwa suna bukatar lokacin mazajensu sannan idan aka duba Yana daga cikin hakkin auratayya yakamata a dinga Kulawa Allah yasa mu dace.
Anwar da aiman
ReplyDelete