-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Sirrikan Zama da Kishiya (Abokiyar Zama)

Sirrikan Zama da Kishiya (Abokiyar Zama)

Sirrikan Zama da Kishiya (Abokiyar Zama)

Kowa yasan mata sun tsani Kalmar kishiya amma kuma hakan bai hana ayi musu ita ba kuma a zauna ko da dadi ko babushi. Mata dayawa abunda yasa basason kishiya shine suna gudun tashin hankali ko kuma a nemi fitardasu daga gidan mazajensu, wasu sabida dukiyar miji, wasu kuwa haka kawai don kar ace sunkasa kula da miji. Wanda duk ba wannan ba, idan Allah ya qaddarta hakan to sai ya faru. Idan hakan ya kasance ‘yar uwa ga kadan daga cikin sirrikan zama da kishiya;

  • Kiji tsoron Allah a duk abunda zakiyi.

  • Ki zauna da ita da zuciya daya.

  • Kar ki bari tafiki da komai wurin kula da gida da kuma tarayrayar miji.

  • Karki bari tafiki wurin iya girki da kwalliya, idan baki iya ba ki koya.

  • Ki kasance mai riko da addu’oi’ da kula da ibadarki hakan zaisa Allah ya jibanci lamurranki.

  • Idan tanada yara ki jasu jiki kisa su soki hakan zai kara daga darajarki awurin miji.

  • Kar kiyi mata shishigi kuma kar ki bari tayimiki, kowa ya tsaya matsayinshi.

  • Ki kasance mai dauke kai ga abubuwan da suka shafeta, face in ansawodake shima kiyi taka tsantsan.

  • Kar ki zama cima zaune, kina sana’a ko aikin dazai rinka dauke maki hankali daga zugan shedan.

  • Kiyi kokarin boye bacin ranki koda kuwa tayine domin ranki y abaci, yazaman ba’a ganin bacin ranki.

Allah ya bamu zaman lafiya agidajenmu. Amin

0 Response to "Sirrikan Zama da Kishiya (Abokiyar Zama)"

Post a Comment