-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Illolin Rashin Baiwa Iyali Lokacinsu

Illolin Rashin Baiwa Iyali Lokacinsu

Illolin Rashin Baiwa Iyali Lokacinsu

Kamar yadda mukasani shi aure ibada ne, hanyace ta neman rahamar Allah, natsuwa da kuma kamala. Bayam haka akwai wani bangare na rayuwar aure wanda zai samar da nishadi da kuma shakuwa da soyayya a wurin ma’aurata. Wannan bangaren ya kunshi abubuwa kamar haka;

 • Fira

 • Wassanni

 • Yin ‘yan aikace aikace tare

 • Fita ziyara tare

 • Cin abinci tare

Da dai sauransu.

Duk wayannan abubuwan basa yuwuwa idan namiji ya kasance baya ba mace lokacinta. Duk yanayin aikinka ya kasance akwai a kalla awa guda da zaka ware domin kasancewa da iyalinka, sannan dare yakasance natane domin har sallar nafila idan zaka shige hakkin matarka bai halatta kayiba. Domin kuwa rashin samun kula daga wurin miji kan iya jefa mace cikim hadarin aikata aiyuka marar kyau kamar haka;

 • Zina

 • Kallon batsa

 • Madigo

 • Yawace yawacen banza

 • Bin bokaye

 • Sannan yakan yawo kiyayya, domin sai taji ka fice mata aria.

Duk da anacewa idan ba’a fita bid aba kuma rikici ne, amma  duk yanayin aikinka kayi kokarin ba iyalinka lokaci. Idan ma’aikacin gwamnati ne akwai dare akwai weekend, idan dankasuwa ne sai ka tsar aka cire koda rana dayane dazaka zauna da iyalinka domin hakki ne akanka ka sauke. Tun farko ma idan kai ba mazauni bane sai ka sanar da ita shin zata iya aurenka domin ga yanayin aikinka idan ta ji ta amince shikenan. Ammafa kusani rashin ba mace lokaci a gida yana daya daga cikin abubuwanda suke wargaza aure.

0 Response to "Illolin Rashin Baiwa Iyali Lokacinsu"

Post a Comment