-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Ya Ake Zama Da kishiya

Ya Ake Zama Da kishiya

Ya Ake Zama Da kishiya

(Alherinsa A Mahangar Addini Da Rayuwa)

Ta Yaya Ake Iya Zama Da kishiya

Bayan fahimtar abubuwan da suka gabata, yanzu ba abin da ya kamata gare ki sai ki ɗauki kyawawan matakai domin kyautata rayuwa da kishiyarki ko kishiyoyinki, har zamanku ya yi kyau a wannan duniyar kafin makoma lahira. 

Ga hanyoyin da na ke tsammanin za ki iya bi don samun kai wa ga hakan, _in shaa'al Laah_ . Allaah ya sa mu dace.

(i) Rage Kaifin Kishi:

Sanannen abu ne cewa mata suna kishin mazan aurensu, kamar yadda su ma maza suke da tsananin kishin matan aurensu. 

Amma fa duk kishin da ya yi tsanani, har yake sanya mace yin faɗa, ko zagi, ko dambe, ko sihiri, ko ƙona kishiya da wuta, ko kuma ma hallaka ta, ko hallaka wani na ta, kamar 'ya'yanta ko 'yan uwanta da sauransu, wannan sam ba addini ba ne! Hauka ne, kuma abin ƙyama ne a wurin kowane mai hankali.

Don haka, in kina da zafin kishi irin wannan, sai ki yi ƙoƙari cikin gaggawa don ragewa, ta hanyar yawaita addu’a ga Allaah, da yawaita kyakkyawan zato ga kishiyarki da mijinki, da yawaita zikirori a kodayaushe, da yawaita tilawar Alqur’ani. 

Kina iya sanya mijinki ya taimaka miki da addu’ar rage kaifin kishi, kamar yadda Sunnah Sahihiya ta nuna. 

Sannan kuma ki san cewa duk lokacin da zafin kishinki ya sa kika yi wani ta'addanci ga dangi ko kaya ko jiki ko ran kishiyarki, to ke ce abin tambaya a kan haka a duniya da barzahu da lahira. Kuma dole za ki biya ko kuma a yi qisasi!

Kuma lallai! Ki nisanci zuwa wurin bokaye da masu duba da matsafa a kan haka, domin mummunar asara ce ta Addini ba ƙarama ba!


0 Response to "Ya Ake Zama Da kishiya"

Post a Comment