-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Shugaban Kungiyar Kannywood, Sani Mu'azu

Shugaban Kungiyar Kannywood, Sani Mu'azu

Shugaban Kungiyar Kannywood, Sani Mu'azu

MOPPAN: Har Yanzu Ba A Samu Kamar Sani Mu'azu ba!

Ga masana da masu kishin Kannywood na gaskiya, sai yanzu ake gane irin gagarumar gudunmuwar da Sani Mu'azu ya bada ta fuskar hadin Kan 'yan Fim a lokacin da ya rike shugabancin kungiyar MOPPAN. 

Tun da ya bar shugabancin MOPPAN kungiyar da shiririce. Tun da ya bar shugabanci aka samu rarrabuwar kawunan da ba a taba samu a tarihin Kannywood ba. 

Sani Mu'azu bai taba nuna bambanci a tsakanin abokan sana'ar shi ba. A yau, mafi yawan shugabannin MOPPAN da su ka zo bayan shi, da haushin wasu su ke hawa karagar mulki. Ba za su yi mu'amala da kowa ba sai wanda kawai su ke ganin shi ne nasu.

Abin arziki bai taba tasowa Sani Mu'azu ya bambanta tsakin Kano da Kaduna ko Filato da Katsina ba, kowa na shi ne. Me ya sa hakan ta gagara a yau? Rashin rungumar kowa a jiki ya na daya daga cikin musabbabin tabarbarewar al'amurra a Kannywood. Shi ya sa mafi rinjayen matasan 'yan Fim ba su san tasirin MOPPAN a zahiri ba, a suna kawai su ka San ta. 

Wadanda su ka assasa ta ma tuni an maida su 'yan amshin Shata.

Duk wanda ya samu shugabanci sai ya maida MOPPAN tamkar Kamfanin da ya kafa da kudin sa, babu mai amfana da ita sai su da wanda su ke so kawai.

A yau dai zumunci ya Zama tarihi a Kannywood, shugabannin MOPPAN sun dagula komai, duk wanda ya hau bai iya tsinana komai sai neman kudi da MOPPAN a karkashin kasa shi da wadanda kawai ya ke so. 

MOPPAN dai ta 'yan Fim ce, ba ta shugabannin ta ba, Ehe! 

Kuma idan har ba a yi gaugawar daukar matakin da ya dace ba, na tabbata wata rana sai wani ya yi gangancin yi mata rajista a matsayin jam'iyyar siyasa! 

Daga: ALIYU ABDULLAHI GORA II

0 Response to "Shugaban Kungiyar Kannywood, Sani Mu'azu"

Post a Comment