Daukar Ma'aikata a AREWA24
Daukar Ma'aikata a AREWA24
AREWA24 itace gidan talabijin din nishadantarwa ta farko mai yada shirye-shiryenta 24/7 da harshen Hausa wacce Hausawa suka kirkira don masu jin yaren Hausa. An kirkire ta a Kano, Nigeria, a halin yanzu AREWA24 tana da shirye-shirye 11 na kashin kanta da suka kunshi nishadantarwa da rayuwar yau da kullum--duk a harshen Hausa. Burin AREWA24 shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, banbance-banbance, girma da kuma nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke a karkashin inuwar AREWA24.
Gidan talbijin arewa24 zasu dauki ma'aikata dabaru, tsare-tsare na wasanni da bincike na musamman don kara wayar da kan jama'a, inganta kokarin Tallace-tallace, nazarin ma'auni na kafofin watsa labarun da haɓaka tallace-tallace na AREWA24 da sauran ayyukan kasuwanci na AREWA24.
Yadda Zaku Cike
Idan kuna da shawar aiki a gidan talabijin na AREWA24 ku aika da CV naku zuwa shafin email Address kamar haka: recruitment@arewa24.com
Karin Bayani: https://arewa24.com/apply
Application Deadline: 5th September 202
No: Only the Shortlisted candidates will be invited for an interview.
0 Response to "Daukar Ma'aikata a AREWA24"
Post a Comment