Bayanin Theory of evolution
Bayanin Theory of evolution
Matsalar da aka samu tun asali, wasu daga musulmi suna daukan cewa kamar Allah ya halicci mutumne "mustaqilli" a lokaci daya. Wasu kuma (kamar yadda yar uwata Maryam take gayamin) sun dauka kamar Allah kwaba kasa yayi sannan yagina Annabi Adamu da ita! Shiyasa zakaji suna cewa basu yarda da "Evolution" ba. Wannan ga wadanda suka fahimci menene "Evolution" din kenan.
Amma ga wadanda basu fahimceshiba (kamar ni a da), anriga anrudasu sun kasa gane me "Theory of evolution" yake nufi. Wadanda basaso su fahimceshi suncemusu wai Charles Darwin yace mutum daga biri yake! Tamkar dai sun kasa gane menene banbancin "ancestry" da kuma "common ancestors" wanda Darwin yayi bayani a littafinsa na "Origin of Species". Wannan kuskurene da yan jarida suka yadashi kuma yaruda fahimtar mutane tamkar yadda Dr. Mustapha Mahmud yafada.
Babu abinda yahada mutum da biri, domin gwajin "DNA" da kuma "RNA" sun tabbatar da cewa babu alaka tsakanin mutum da biri, kuma ko shekara nawa za'ayi babu ta yadda biri zai koma mutum.
Ni wannan "Theory of evolution" baisani na musa samuwar Allahba domin ko shi Darwin yagayawa kiristoci a zamaninsa cewa "theory" din dayakawo baya musa samuwar Allah. Ayoyi dayawa sunyi bayanin wasu abubuwan da suka kamanci "evolution".
Allah yana cewa ya haliccenu a matakai (وقد خلقكم أطوارا)
kuma yace yana kara halittunmu (يزيد في الخلق ما يشاء). Wallahi imani nakarayi da Alqurani kuma na kara gaskata Annabi (saw) domin babu ta yadda za'ai ya iya wannan bayanin matukar ba wahayinsa akayimasaba.
Per Aliyu Dahiru Aliyu (SUFI)
To be continued
Keep following the post
0 Response to "Bayanin Theory of evolution"
Post a Comment